tsaya mata a rai ta rasa dalili ga wata irin fad'uwar gaba da take faman yi tunda ta rinki labarin tafiyar
Inna gaje dake jin mike faruwa tashi tayi zata waje sai kuma ta tsaya tana cewa "zan iya zuwa fa waccar matar in mata tabbayar arzik'i ta tare ni da fad'a bari kiga nayi zama na dan Gwaggo itace dai-dai da Amaryar nan" dan kuwa taga take-taken Narnah Amarya bata da mutumci itama dan kuwa magana tasha had'a su tana yab'a mata magana danma tana da baki itama amma Gwaggo ta fita iya gaya bak'ar magana.
A d'akin Abba kuwa kukan munafirci Narna keyi Malam yace "wai ya kike so nayi miye abun kuka nan kefa kika jata harta fad'a miki magana ai gobe ma kin k'ara" da sauri ta kallesa "Malam ni kake cewa na k'ara haba Malam ka duba irin cin fuskar data min amma ka barta haka ta tafi" cewar Narnah "Ah to bugunta kike so nayi ko mi gaba take dake fa in....... Tunkan ya ida maganar ta tashi zunbur ta fice daga d'akin tana kunbure-kunbre girgiza kai yayi yana binta da kallo yana cewa "mata mata halinku saiku wallahi" ita kuwa Narnah cewa take "lallai saita nunawa Gwaggo turo kalo d'inta wallahi hmm" ta ida maganar tana zarya a d'akinta...........✍️
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/4, 12:35 PM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦♀️💔 ITA CE K'ADDARATA 🤦♀️💔*
*©ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️
*ROYAL STAR WRITIN'S ASSOCIATION*
PAGE2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣
Washe gari haka na tashi jikina sukuku na d'an shirya kayana daba wasu masu yawa bane na shirya ina zaune gaba na sai fad'uwa yake sallamar Laure naji wani irin masifaffan fad'uwar gaba ce ta riske ni fashewa nayi da kuka bansan dalili ba dafa ni naji anyi Sakina ce tace "haba Khaleesat tun jiya kuka dai kiyi hakuri shine kawai" tashi nayi nace "Sakina wallahi kawai naji kukanne kawai zai sani naji sanyi a zuciya ta kinji yadda gabana ke fad'uwa kuwa daga tafiya " "hakane saiki rink'a kiran sunayen Allah" cewar Sakina ta k'ara cewa "ki tashi kar Mama ta shigo ta tadda mu a nan ga Laure can tazo".
Tashi nayi jikina a mace kamar wacce bata da lakka koda muka fito duk suna zaune saida na shiga d'akin Abba yana zaune da Inna gaje da Amarya wadda kullum tana manne dashi nace "Abba zamu wuce" idona a k'asa dan innace zan kalle shi to kuwa kukane zai kubce min zaiyi magana Amarya ta rigasa da cewa "kai wannan abu baiyi dad'i ba daga ganin yarinya bama so take ba" ta ida ta tab'e baki da sauri Malam ya kalle ta cewa "Narnah bana son haka yanzu da Gwaggonsu na kusa kike Wannan magana fa kinsan ba zakuyi ta dad'i ba so please mi daina shiga harkar daba taki ba" ya ida maganar a hargitse dan baya son tashin hankali amma ita ya lura nan tafi amki Inna gaje kuwa cikin zuciyar cewa take maganinki kenan ace ayo mace sai shishshigin tsiya a fili kuwa addu'a tayi min Amarya Narnah kuwa tashi tayi cikin fushi ta fice lallai da sake dole Malam ya daina mata gaddama gaskiya tayi sake data shigo bata gama mallake sa ba take fad'a a zuciyar ta.
Koda muka fito Abba yaban kud'i masu yawa ko zanyi anfani dasu ya bini da addu'a shima haka ina ji ina gani Laure ta fita dani cikin gidan mu nida Sakina sai hawaye muke Gwaggo kuwa sai cewa tayiwa Sakina "munafuka harda wasu hawaye sai kace ance mutuwa zatai dalla can saketa su tafi karna mangare ki a nan" da sauri ta sakeni muka tafi.
Kai tsaye tasha muka nufa muna zuwa kuwa saura mutum biyu motar kano ta cika muna hawa mota ta tashi cikin ikon Allah muka isa Kano ta dabo tunbin giwa koda mi kazo an fika lallai nasha kallo dan kuwa rabo na da Kano tun Umma na raye tana y'ar uwa a Kano wadda ita kad'ai ta rage mata a cikin y'an uwa muna ce mata Aunty Haleema taso ta d'auke ni wajanta amma Abba ya hana da makircin Gwaggo Shi yasa duk nacinta ta hakura sai dai tana lek'o ni badai sosai ba saboda rayuwa tayi tsada.
Koda aka sauke mu nidai duk inda Laure tayi can nake yi dan kuwa ni bak'auya ce a cikin Kano abin hawa maka hau naji tace "mai adai-daita tudun yola zaka kaimu" amsawa yayi muka shiga tsaka ga Allah nasha kallo indai duniya baka fita cikin duniya to kuwa ba sakasan duniya yadda take ba ai kallo ma saida muka shigo unguwar ma gaba d'aya unguwar ta masu dashi ce gidaje ne masu matuk'ar kyau dai-dai wani mashahurin gida mai masifar kyau ni a gani nama yafi duk na unguwar had'uwa da tsari mai kyau sakin baki nayi ina cewa a zuciyata anya Laure tana da hankali kuwa ta ina tasan mutanan gidan nan ji nayi Laure namin magana "kizo mu wuce kin tsaya kallon mutane saura in mukaje ciki ki nona k'auyanci naki dan wallahi k'annan matar gidan su biyu dake zaune tare da ita ba mutumci ne dasu ba sai kinbi a sannu kinji na gaya miki in sukai miki cin fuska bance ki kyale su ba dan in kika nuna tsoro to kuwa kina cikin wahala dan nasan sanki ko a gida in wulak'ancin yayi yawa wallahi ki rama dan akwai wata d'iyar k'awar Hajiya Sa'adha itace matar gidan to d'iyar k'awar ta tana zaune a gidan karatu take mai suna Maryam duk ta fiso rashin kunya dan kuwa ita son mai gidan take har yanzu Hajiya Sa'adha bata son da wacce manufa take zaune gidan ta ba dan kuwa Hajiya Sa'adha tana da tsananin kishi indai mace ta shiga shirgin Mijinta Alhaji MUSTAPHA YUNUSAH ba wadda bai san Alhaji Mustapha Yunusa mutum ne mai kirkin gaske duk da arzik'in da Allah yayi masa hakan baisa yana wulak'anta mutane ba yana daraja su matar sa ma ba laifi tana d'an kirkinta itama ammafa in baka shiga harkar mijinta ba bata had'a mijinta da kowacce mace ba, sai k'an nan ta guda biyu mata Hanan da Ummeeta suma dai ba k'anan y'an rainin hankali bane kina jina Khaleesat abinda yasa nake baki wannan d'an labarin mutanan gidan nan dan ki kiyaye duk wani abunda zai had'a ki dasu duk ko baki shiga harkar tasu ba su zasu shiga to kinji halayan kad'an daga cikin mutanan gidan nan saiki koyi zama dasu" ta ida maganar tana kallona ni kuwa dana k'ara tsurewa to sabowar K'addara ce ta kawo ni gidan nan ni irin tsoron gidan da mutanan gidan ya dirar min jawo ni tayi muna nufar k'ara mar k'ofar get d'in tana k'ara cewa "karki sake su gane kina tsoron su dan kuwa zakisha bak'ar wahala ne" wani dai banda bakin magana sai da Laure ta buga get d'in sana mai gadi ya lek'o ganin Laure ce an santa yace "ahh Laure yau kune a garin" cewar mai gadin Laure kuwa murmushi tayi tace "ai kuwa nice kasan Hajiya ta sani samo mai aiki to ita na kawo" kallo na mai gadi yayi cike da mamaki yake kallo na irin tsananin kyan da Allah ya zuba min bai k'ara cewa komai ba muka wuce gaba nane ya fad'i ganin irin ginin gidan ga motaci kota ina kala-kala runfarsu kanta wata abar kallo ce sai ginin gidan daka d'aka kanta part biyu ne ko wannan su hawa biyu ne ga wasu fulawowi da suka zagaye gidan masu masifar kamshi da suke fiddawa kai aljannar duniya tsarki ya tabbata ga Allah mai kowa mai komai da yayi tallaka da mai kud'i aljannar kenan nidai kyan gidan ne ya k'ara rud'a tunani ya za'ai kana cikin wannan irin gidan harka san da wani wai shi talaka bare kasan ana rana ko ana ruwa ai bazaka sani ba ga y'an aiki kota ina suna hada hadar su mai kula da fulawowi daban masu wankin mota daban driver's daban ji nayi mun tsaya ji nayi magana a tsakiyar kaina y'an matan gidanne zaune suna shan iska sanye suke da k'ananun kaya ko wacce tana danna wayarta mai shegiyar tsadar gaske ganinmu yasa suka fara tabe baki suna kiran Laure da yake sun san ta nidai ina bayan Laure Hanan ce tace "Lauran k'auye ya akai ne" dariya suka saki su duka ta shak'iyanci Laure kuwa cike da rashin jin dad'i abinda suke mata tace "sannunku da hutawa akware kuwa ai kinsan kowa asalinsa k'auye ne in....... Tunkan ta ida Maryam tace "ke dalla can ita waccan d'ayar bak'auyar bata iya gaida mutane bane ta wani shige bayanki kai Allah ya rabamu da k'auyanci wallahi" tana wani yatsine baki da sauri Laure ta rad'a min cewa "kin gani ko indai kina maida masu ya yadda zasuyi dake dan kuwa ko sunkai k'ara wajan Hajiya ba zata kula su ba saboda tasan ba mutumci ne dasu ba amma karki bari su kulla miki munafurci wallahi sai kinyi taka tsantsan dasu" tana idawa tana janyoni gabansu gaida su nayi cikin sanyin murya ta da sauri su duka har suna rige-rigen d'agowa ganin wace mai wa Wannan zak'in muryar ai mutuwar zaune sukai bare Maryam zuciyar tace ta wata mahaukaciyar bugawa tana kallon tsantsar kyau da Allah ya zubama Wannan yarinyar kamar ita tayi kanta innalillahi lokaci d'aya taji wata irin tsanata ta d'arsu a zuciyar ta tsaki tayi tana barin kallo na su kuwa su Hanan suma kyan dai nawa ne ya tsone masu ido cike da wulak'ancin Hanan tace "kun tsaya mana a kai Hajiyar na ciki ai sai ku shiga" ta ida maganar tana wani yatsine baki.
Laure kuwa dariyar mugunta tayi tana jana muka bar wajan cikin Porlon gidan muka nufa tofa nanne naga banga komai ba wajan had'uwa da kyau irin yadda aka tsara porlon kamar a k'asar waje wasu irin lumtsuma-lumtsuman kujero ne sun zagaye parlon ga wani kafat mai shigen taushi inka takasa kamar katifa ga wani irin darning mai masifar kyau ban tab'a ganin irinsa ba sai a irin gidajan sarautar nan kai komai dai na gidan sai wadda ya gani ga sanyin Ac dake busowa da wani irin k'amshin turare mai masifar kamshi mai kwantar da hankali wajan kalle-kalle na bansan Hajiya Sa'adha ta fito ba har sai da Laure ta zungure ni tana Zaune a kan kujera daka kalle ta kasan ilimin boko hutu naira suna aiki a jikinta ba laifi kyakkyawa ce amma ko k'afar Khaleesat bata kaiba ita kanta data ga Khaleesat sai data girgiza da kyawunta amma saita basar dan tasan tabbas mijinata bazai kalle wannan y'ar k'auyan ba gaida ta nayi ta amsa ba yabo ba fallasa ni dai k'asa nayi da kaina magana suke da Laure ta sallami Laure tayi min ban kwana harda y'ar kwallata haka ina ji ina gani Laure ta tafi ta barni cikin wannan gida mau mai cike da rud'u ina nan zaune a k'asa Hjy bata k'ara cewa ko cikanki ba na daiji tana waya da wata y'ar aiki suma da wayar da ake kirinsu saboda da fad'in gidan sai da waya take ce mata ga wata mai aikinta tazo ta kaita d'aki amma a cikin Part d'inta a bata d'aki d'aya da Asabe tunda itama abinci take a nan ina ji sauke wayar ba'a dad'e ba mukaji sallamar wata da sauri Hjy takai dubanta ga wadda ke shigo cike da d'an mamaki tace "Dr Aysha kece tafe yaushe rabonki da nan tun randa mukai maganar nan ban k'ara ganinki ba" ita kuwa Dr Aysha k'ara sowa tayi ta zauna kusa da Hajy ta k'are min kallo cikin d'an mamaki kamin tayi magana saiga wadda aka kira Hjy tace "yau gata nan ki nuna mata d'akin nasu sana kicewa Asabe ta koya mata komai daya kamata zaku iya wucewa" matar kuwa d'an duk'awa tayi alamar girmamawa tace "an gama Hjy" kamani tayi tana min murmushi muka nufi wani lungu dake k'asan porlon wata y'ar hanya ce sai gamu wajan wani k'aton kitchen can daga bayansa wani d'aki ne shiga mukai d'akin katifa ce guda biyu a shinfid'e a k'asa sai tayis d'in dake malale a k'asa sai wata y'ar waduraf mai guda biyu sai ban d'aki dake a cikin d'akin ba laifi dai d'akin ga dai d'an aiki Asabe data gama salla tace "a'a Lantana badai ita bace wacce Hjy ke cewa za'a kawo ta tayani girkin gidan nan?" "Eh ita ce Asabe gata itama tace gata ki nuna mata komai daya dace dan kinsan aikin abincin gidan nan sai da mataimaki mutum d'aya bazai iya ba saboda yaran gidan nan sai sun bari ma ka gama suce ai ba kaza suke su suci ba ai ga abinda suke su" cewar Lantana ta ida maganar tana kallona ta k'ara cewa "yarinya saifa kinyi hakuri gidan nan" Asabe tace "ai da alama zatayi hakuri nidai sunana Asabe wannan kuma Lantana duk da nasan yanzu kinma san sunan fatan zamuyi hakuri da juna" da kyar na bud'e baki na da yayi min nauyi nace "inshallahu" "yarinya ki saki ranki kinji" cewar Asabe Lantana tace "bari na wuce kinsan aikina wanki karsu zo su tadda ban gamaba sumin rashin ta ido" sallama sukai ta wuce a zuciyata nace to har mai wanki daban kenan hmm lallai in kana da kud'i ba abinda ba zakai ba, jana da fira Asabe ta farayi cikin sakin fuska tun ban sake wa harna fara tashi mukai ta fara nuna min yanayin kitchen d'in inda nake jin labarin cewa mai gidan baya nan yaje taro Abuja gobe ne dawowar sa shi yasa aka fara shirya-shiryan dawowarsa.
A wajan Hjy Sa'adha kuwa Dr Aysha tace "K'awa ina kuka samo wannan yarinya kyakkyawa haka?" Hjy tace "wallahi mai aikice wai aka samo min har school nace zan sata shi yasa ubanta ma ya yarda" sauke ajiyar zuciya Dr Aysha tayi ta gyara zama tace "amma Hjy baki ganin yanzu ne ya kamata ki aiwatar da kudirinki a kan wannan yarinyar tunda naga tana da natsuwa sai naga zatayi in akai mata dashan nan zata iya d'auka" Hjy Sa'adha kuwa shuru tayi sai can tace "hakane ni banma yi wannan tunanin ba wallahi lallai zatayi amma fa kinsan akwai had'ari tunda sai an fita k'asar waje fa Kuma...... Da sauri Dr Aysha tace "haba Hjy Sa'adha ba wani had'ari kuna da kud'i fa zaki iya zuwa Abuja muna da doctor's wadda suka iya aiki basai anje k'asar waje ba tunda muna da abun mijin naki dashan kawai za'ai mata fa kuma bazata gane ba inya su cikin indan ya girma jikinta sai ayi mata bayani yadda zata gane koya kika gani?" "Hakane kam amma kinsan Alhaji Mustapha bai sani ba kuma bazai tab'a bada goyan baya ba ko sperm d'insa da muka d'iba bai sani ba fa" cewar Hjy Sa'adha Dr Aysha tana kallon Hjy Sa'adha tace "to sai mi saiki zauna ki biye mai wallahi kina zaune zaije ya k'ara aure akan wannan rashin haihuwar gara kiyi wannan abun kema kiga gudan jinin ki" Hjy Sa'adha kuwa jin an fad'i zau k'ara aure da sauri ta tashi zunbur tana girgiza kai cewa "ina Dr ki daina ma wannan maganar ki shirya mana komai zuwa sati mai zuwa nasan gobe zai dawo zai koma bakin aikinsa dake nan Kano baida lokaci zan shirya mai cewa zani unguwa Abuja ita kuma danta yarinya mai sauk'i ce tunda tana k'ark'ashi na" Dr Aysha cike da murna tace "yau y'ar uwa ta shi yasa kike k'ara burgini ai keda kishi sai dai a lahira an anayi...............✍️
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)🥰✍️*
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/5, 6:37 PM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦♀️💔ITA CE K'ADDARATA🤦♀️💔*
*©ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️
*ROYAL STAR WRITIN'S ASSOCIATION*
PAGE2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣
"Laure ina jinki kin kaita ko? Ya maganar Allah yasa dai kinje wajan Malmin kuma Allah yasa ba boka bane dan wallahi tunda naji wani wa'azi ban marmarin in k'ara zuwa wajan boka itama kanta Gaje ta daina?" Ta ida maganar tana kallon Laure Sauke ajiyar zuciya Laure tayi tace "nima kaina kinsan bana bin bokaye saidai Malamai masuyi sa ayar Allah to can naje kinga wannan abun zaki rink'a turarawa kina zuk'unni dashi Insha Allah abunta zai koma Mata" "yau Laure shi yasa wani lokacin kina fad'ar gaskiya amma fa wallahi kinsanni da zafi duk wadda ya tab'a ni saina tab'a sa ba boka ba Malam ta rubuta ta aje dai-dai nake da ita wallahi" cewar Gwaggo Laure kuwa gyara zama tayi tace "amma k'awa mi yasa bakya son wannan yarinyar Khaleesat ne?" Da sauri Gwaggo tace "hmm bawai bana sonta bane nima kaina ban san miya sa inna ganta a gabana nake jin saina mata rashin mutumci zuciyata ke samun sa'ida amma zanyi k'ok'arin na daina k'ila Amma" dariya Laure tayi tace "ke k'awa baki da dama anya ba'a shiga tsakaninku ba kuwa" shuru Gwaggo tayi bata k'ara magana ba Laure ta dad'e gidan sana sukai sallama tace mata komai kenan indan maganin yayi sayi waya zata d'an kwana biyu bata lek'oba.
Ai kuwa tundaga wannan rana Gwaggo ta fara anfani da maganin cikin ikon Allah ya fara mata aiki harda ma Inna gaje dan kuwa sunga can ji sai dai a b'angaran Amarya hankalinta a tashe yake dan kuwa Malam ya daina kusartar ta kamar yadda take so daya fara saiya gaji ita kuma gata da y'ar banzar jarabar tsiya bata k'oshi da abun sosai ta shiga tashin hankali sai zarya take bin bokaye kwata-kwata ta daina zama gidan bata Dutse bata Kankia Malam kuwa yawonta ya fara damunsa sosai kamar yauma bai tab'a shiga d'akinta ba yazo dai-dai shiga yaji tana waya da y'ar uwarta cewa "haba Zuby bazaki gane ba kwata-kwata wannan abun da mukai ma Malam wa'incan matan nashi soma fa sun tashi tsaye kinsan ban dad'e da zuwa wajan boka nakan tudu ba yake gayamin ko haihuwar danake sonyi dashi ba lallai in k'ara haihuwa ba a duniya ina cikin Matsala fa sosai..... Tunkan ta idasa taga shigowar shi zama yayi da sauri cike da wata irin rud'ewa ta yada wayar bata sani ba shi kuwa kallonta yake da mamaki ita kuwa Narnah a zuciyar cewa take shikenan ai asiri na ya tunu waima miya kawo Malam har d'aki na ne shida baya shigowa Malam kuwa da yake namijin gaske ne saiya share maganar kamar baiji ba yace "kwana biyu kina yawan fita dama nazo na gaya miki cewar indan kika k'ara fita gidan nan bada yawuna ba to a bakin auranki" yana gama maganar ya tashi zai fita da sauri ta manta da furicin da tayi tace "haba Malam kamar ya ina fita kawai kace matanka son zugaka ne shi yasa taya za'a ce wai in daina fita" ta ida maganar tana tuno cewar sunyi da Zuby jibi zasu had'a suje wajan wani mai aiki kamar yankan wuk'a ganin cewa baiyi mata maganar abunda take fad'a a wayar ba saita d'auka ai baiji ba, sai dai abinda bata sani ba ya riga da yaji komai koma kad'an yake jira ta k'ara yimai wani laifin ya sawwak'e Mata dan kuwa bazai iya zama da wacce take son kassara shi ba, duk da cewa mata dama baka raba so da irin haka bai shidar kowa cikin su amma ai ita ya riga da yaji komai katse mai tunani tayi da cewa "da kai nake fa Malam kayi banza Dani" juyowa yayi a hargitse yace "nadai gaya miki kuma in kina ganin wasa kisa k'afa ki fita ki gani yadda zan d'au mataki" yana ida fad'ar maganar ya wuce a zuciye tsaki Narnah taja aikin banza kawai ai wallahi saina fita kad'au matakin da duk zaka d'auka dan ina da tabbacin kaida sakina sai dai a lahira in anayi".
KANO
Tunda safe Asabe ta tashe ni muka shiga kitchen muka fara aiki mu dafa wannan mu sauke wancan na gaji sosai inda ko wanne Asabe ke gaya min cewa dukansu sai an masu abincin da suke so lis na nan a rubuce ko wacce rana da abinda za'a dafa ga abincin mai gidan kansa da za'a fara anjima an gyara gidan ko ina tashin k'amshi yake wadda masu gidan ko tashi basuyi ba duk an jera komai a darning bamu zauna ba nida Asabe muka fara aikin abincin mai gidan wadda naje ana cewa wai yau zai dawo aiki muke duk abinda yafi so shi Hjy Sa'adha ta gayawa Asabe muke yi abu hud'u mukai farfesun kayan ciki da danbun nama sai fankasun da akae mai miyar dage-dage sai Soyayyar shinkafa wadda taji kayan lanbu da naman kaji sosai muka aikato muka ajiye a inda ya dace d'aki Muka shiga domin hutawa nidai saida nayi wanka na d'akko wata rikata y'ar kanti abaya Bak'a wacce akaima kwalliyar duwatsu rigar ba k'aramin kyau take min ba wadda Abba ne ya saya mana nida su Haneefa akan rigarma sai da akai masifa da dan kuwa sai da Abba ya fara kawo min da nad'au wata kalar ruwan k'asa ina son kalo d'in amma inaji ina gani Gwaggo ta amsheta taban ta Sakina bak'a sai gashi ma bak'ar tafi min kyau ta haska farar fatata.
Asabe dake kallona tace "kai Masha Allah son kowa k'in wadda ya rasa kin ganki kuwa kai gaskiya Masha Allah ke mai kyau ce" ta ida maganar tana murmushi zanyi magana kenan mukaji an shigo d'akin Maryam ce wani tsaki ta saki tana cewa "ina wani kyau a nan kuda baku saba ganin masu kyau ba" ta ida maganar tana Hararar Asabe da in a girme ne ta girmi Maryam d'in Asabe kuwa k'asa tayi da kanta bata k'ara tankawa ba Kallona Maryam tayi tana wurga min wani mugun kallo mai cike da tsana tace "to kun gama Abinci uban wani zayi seving namu ne ko so kuke muyi da kanmu ne kuma" ta nunani da yatsa ta k'ara cewa "ki tabbatar kin cire kayan nan ki sake wasu ko an gaya miki dama dan kwalliya kika zo ne koma ubanwa zai kalleki in kinyi kwalliyar kar naga kin fito dasu" ta ida maganar tana yin kwafa ta juya tana ficewa ji take kamar ta jawo ni ta yayyage min fuska ta b'ata kyan nawa.
Nidai sauke ajiyar zuciya nayi ina binta da Addu'ar shiriya kuma duk wani shirri ya koma ga mai shi da sauri Asabe tace "kiyi hakuri kad'an ma kenan tunda suka fahimci kin fiso komai kinga tashi ki cire wannan kayan mu fita ko nayi gaba kin biyo ni" ta ida maganar tana ficewa dan kuwa kad'an daga aikinsu suyi sana diyar barin naka aikin nima da sauri na cire kayan nawa nasa wasu riga da zani suma dai ba kara min kyau sukai min ba Hips D'ina ya k'ara fitowa sosai ga k'irjina dake cike kayan sunyi min mahaukacin kyau fiye da waccan rigar ma da sauri na d'auki gyale na na fito porlon suna zazzune su duka da sauri na k'ara sa wani irin bak'in ciki ne ya tukare su lallai wai ita waccan yarinyar komi tasa yi mata kyau suke ne basu da mai basu amsa Hjy Sa'adha kuwa data ci wani uban gayu tana danna wayarta ko kallo bamu isheta ba dan bata cika shiga harkar mutane ba Ummeeta kuwa wata mugunta ta shirya tace "ke Khaleesat kike kowa zu ki zuba min abinci Nan" matsawa nayi kusa da ita ina zuba mata a hankali nake yin komai wai dan kar nayi ba dai-dai ba ita kuwa d'agowar da zatayi tana sane ta b'arar da abincin sai akan k'afata wani irin rad'ad'in azaba naji da sauri na saki sauran abinci ya b'are a k'asa har yad'an tab'a jikinta da sauri ta tashi zunbur tana wani uban huce sai dai naji an d'aukeni da wani irin mari mai zafin daya sani dafe kumatu na hawaye na b'alle min ga zafin mari gana k'onewar da nayi ta nunani da yatsa dukansu tashi sukai suna kallonmu cikin tsawa "ke mahaukaciyar inace baki iya komai