kusa da ita tace "Mama amma ya kamata musa kaya masu kyau ko saboda.... Tunkan ta ida Gwaggo ta buga mata wani uban dundu a bayanta dan kuwa tana kusa da ita Sakina kuwa gantsare wa tayi tana tab'e baki dan kuwa taji bugun Gwaggo ta bud'e baki tace "amma dai ku bansan shashashu bane mararsa kishin uwarsu da bikin wannan y'ar duniyar zakuce zaku gwangwaje in..... Da sauri Haneefa ta tsayar da ita da cewa "haba Mama bafa wani abu bane kinji yadda Laure tace miki fa ki d'an fara shige mata in bazaki iya ba mu kibarmu a hankali za muji dame take tafe itama in munyi gayun nanma fa Mama itace zatai bakin ciki cewa ai auran nata da shigowa gidan namu bai damemu ba kuma indai gidanmu ne ai gata gashi" da sauri Gwaggo tace "ashe dai Haneefar tawa tana da hankali haka kuwa za'ai bari dai Allah ya kaimu goben".
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dad'e ba'a je ba washe gari tun wajan k'arfe sha d'aya Abbanmu ya shirya kai da ka kallesa kasan Ango ne sai wani murmushi yake tafe yake zai shiga d'akin Gwaggo shiga yayi yayi sallama da kyar ta amsa bud'e baki yayi yace "to mu zamu tafi d'aurin aure" Gwaggo kuwa bakin ciki takeji a zuciyar ta amma saita danne tayi shuru bata ma dai tanka mai ba dan kuwa intace zatai magana to kuwa ba magana mai dad'i zata fito daga bakinta ba, ganin cewa bafa zata tanka mai ba yasa ya juya yana girgiza kai ya nufi d'akin Inna gaje,
Yana fita Gwaggo ta saki wani uban tsaki da cewa "wai shi nan Ango dan Allah jibeshi da wasu kaya wai Ango andai ji kunya wallahi gashi da y'ay'a mata rid'a rid'a bai masu auran ba saishi yake shirin k'arawa ai wallahi andai ji kunya wallahi" ta ida maganar da d'an d'aga murya da sauri Haneefa ta matsa kusa da ita tana cewa "haba Mama yana jinki fa nace miki Mama ki rink'a tausasa zuciyar ki fa" ta ida maganar da d'an turo baki sauke ajiyar zuciya Gwaggo tayi tace "hakane kun sanni dai dan wallahi ni ba hakuri ne dani ba abunne yake tab'an zuciya shi yasa" "ai shi yasa sai kin rink'a dannewa baki ga Inna gaje ba yadda take nunawa ne" cewar Sakina Gwaggo kuwa tsaki taja tace "ai waccan matar bata zuciya a k'irjin ta" shuru sukai dan in suka tanka sunsan halin Mahaifiyarsu zata iya makesu yanzu gashi sun samu ta d'an sakko tashi tayi ta nufi tsakar gida saiga Laure da sauri Gwaggo ta tare ta da cewa "dama ke nake jira" Laure kuwa kallon gidan tayi tace "yo ina y'an uwan Malam nake ganin gidan kamar bana biki ba" Gwaggo tace "in banda abunki Laure wannan har wani biki ne na azu a gani cewa yayi basai kowa yazu ba in aka kawo Amaryar sazo su ganta kinsan yawanci y'an uwansa ba nan Kankiar suke ba kuma ba wasu masu yawa bane shi yasa ya hutar dasu yanzu dai kinga kayan abinci can ya bari na y'an bikin in mutane zasu shigo sai muje mu fara aikin ga waccan matsiyaciyar matar can Gaje harta fara hanka alayyahu" da sauri Laure tace "ayya ashe abun haka yake yoni na zata zanzo inga mutane cike da gida" tsaki Gwaggo taja tana cewa "kema Laure kina da abin haushi wallahi kinga idasa ki kama mata aikin inje wajan waccan Khaleesat d'in dan ubanta itama" ta ida maganar tana idasawa d'akin ni kuwa bacci ma nake dan kuwa jiya ciwon ciki ne ya hanani bacci sai gaba nin asuba nayi bacci dan kuwa in zanyi al'ada haka nake fama da ciwon cikin nan, ganin bacci ma nake yasa ta fara girgiza kai da cewa "ahh lallai ganin na sarara miki kwana biyu shine harkin samu sake ko" da sauri ta d'akko sauran ruwan dana sha magani dashi ta watsawa min a fuska wani irin numfashi naja Kamar wadda ta suma da sauri na tashi jikina na kyarma dan kuwa ni wallahi tsoro ma taban kallonta nake Gwaggo kuwa ganin kallon da nake mata yasa ta buga min tsawa da cewa "dalla can ni dena kallo na shegiya da idanu kamar na mayu kin wani tsareni da idanu dalla can zoki wuce muje aiki zakiyi ke gaki y'ar hutu ko ai hutu bai kamaki ba yarinya indai bauta ce yanzu ma zaki fara dalla can muje ko in d'auke ki da mari yanzun nan wallahi" ai da sauri na fice daga d'akin dan kuwa ba k'aramin aikin Gwaggo bane ta mari ni d'in,
Koda muka fita kama aikin nayi sai yawanci duk aiki ya dawo kaina dan ita Gwaggo ko abu bata fara ba bare yaranta can mutane suka fara shigowa makwamta gidan ya fara d'aukar harami ba laifi to kunsan a taro na mata sai tsegumin auran ake ana zuga Gwaggo ita kuwa sai hawa take dan ma da Laure kusa duk wadda ba abun arzik'i ya kawosa ba Inna gaje je tashi tayi mai tas dan itama fa ba daga baya ba wajan iya yab'a bak'ar magana nidai da naga na gama aikin wasu ma abinci ya kawo su da kyar na ida d'aki na ina ganin su Haneefa anci uban gayu sai wani yauk'i suke ni abun nasu ma dariya yaban da kyar na ida d'aki na dan kuwa cikin nawa ne naji yana murd'a min dan kyar na shiga wanka ina fitowa dama na d'ibi d'an ruwan zafi da turirinsa nasha zufa sai hanko min take da d'an tsakuri abincin da aka ban tun ina jin hayaniyar mutane har bacci mai nauyi ya kwashe ni,
Sai can wajan dare motar amarya ta k'araso mota biyu basuyi wata d'ibar mutane sosai ba mota biyu ce harda motar Hamza wadda shine dai ya zuga Abba yayi auran to a motarsa aka d'akko amaryar y'an uwanta sai wani bud'a suke suna k'arawa lokacin da yawan mutane sun rage sai d'ai-d'aiku shigowa sukai cikin gidan duk su Gwaggo ana tsakar gida ganin mutanan gidan na waje yasa aka tsayar da Amarya suka gaisa Gwaggo dai da kyar Laure ta tausheta ta tanka masu amarya na lullub'e jikinta kawai ake gani Gwaggo kallonta take yanzu wannan matar Malam ya jajib'o masu mata ba kyan jiki bare na fuska sai uwayan mazaune tana tafiya suna juyawa ko kyan gani babu suma ga fuskar ta ana gani a cikin d'an yalulan mayafin da tasa bak'ace sosai ga hanci kamar an taka kashi (kai Gwaggo banda sharri🤣) ,
Amarya kuwa kallon su take tsaf tana karantar su baka isa ka gane wane irin hali Gwaggo take ciki ba bare yaranta da suka ci uban wanka Inna gaje kuwa kamar ba kishiya ba sai hada-hadarta take Nahna Amarya kuwa ba haka taso ba ai ta zata zata gansu hankali a tashe yadda y'an uwanta suka bata labari a k'agare take su shiga d'aki.
Suna shiga d'akinta ta yaye mayafin wadda dashi gara ma babu tana karewa d'akin kallo sai kuma ta juyo wajan y'an uwanta tace "wai ya naga hakane kuda kukace min d'ayar ta nuna hali ko in kula daku alamun hankalinta a tashe yake ai nafi so naga haka amma yana ga akasin hakan ne" ta ida maganar tana kallonsu wata k'awarta wadda suke Kira da Talatu y'ar Tasha ce ta k'arshe tana da hujen hanci ta bud'e baki ta tufar da cigam d'in da take ci tace "keda kike zo da shirin ki na rusa duk wani farin cikin su" da sauri Nahna tace "kware kuwa dan har fidda su nake so nayi na kasance ni kad'ai a wajan Malam dan na rantse da wadda raina ke hannunsa da zarar aikina ya fara dukan su sai sun d'and'ana kud'ar su tunda suka bari na shigo gidan nan" k'awayen kuwa shewa suka saki da y'an uwanta Talatu tace "shi yasa nake sonki k'awa ba kya wasa fa" suna tafawa...........✍️
*YANZU MA WASAN YA FARA MASOYA KU GYARA ZAMA*
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/3, 5:32 PM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦♀️💔ITA CE K'ADDARATA🤦♀️💔*
*©ZAHRAH ROYAL STAR CE*🌟🖊️
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*
Chapter1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣
Washe gari muna tsakar gida su Gwaggo Abba ya tarasu muna jin tashin maganar Gwaggo haka suka fito ransu a bace bare Gwaggo koda suka fito Inna gaje tace mana "kuje Abbanku na nemanku ku gaida Amarya" ta ida maganar itama ba walwala a fuskar ta da alama abunda suka tadda ne can d'akin Abba ya b'ata masu rai,
Muda su Haneefa tashi mukai nufi d'akin Abban sallama mukai amsawa akai muka shigo abinda na gani ne yaban mamaki su Haneefa kuwa fuska ba fara'a illa abunda muka gani shine duk sallamar Nan da mukai ganin zamu shigo baisa ta matsa daga jikin Abban namu ba tana mak'ale dashi shima kuma koya yayi mata magana ko shi yasa naga su Inna gaje rai ba dad'e sun fito daga d'akin, ni abunma kunya yaban gaida ta mukai sai binmu take da kallo da y'ar fara'a ta amsa cinkin kissa irin ta gaggun y'an duniya tace "sune yaran nawa Masha Allah" Abba dake washe baki amsa da"eh wannan itace wadda mamarta ta rasu" ya ida maganar yana nunani amarya kuwa da sauri tace "ayyah Allah ya jik'an musulmi" a zuciyar ta kuwa cewa take ai gara ma data margaya ga yarinya mai kyau kamar y'ar aljanu hala haka Mahaifiyarta take gara data tafi taji da wa'inchan k'azaman matan nasa, dan kuwa gani take basu waye ba basu iya komai ba basu kai ta had'a miji dasu ba sai da taji muryarmu muna magana da Abba tayi saurin katse tunaninta kar a fad'i maganar da bata ji ba sadda zata d'ago ma harmun fice,
Tunda Amarya ta tare girkinta sati d'aya ana shan amarci wani salo data d'akko shine sa kaya k'anana ana matse jiki za'ai miji gayu wadda ba k'ara min haushi su Inna gaje ke k'unsa ba, kamar yauma tazo wuce muna zaune daga ita sai y'ar ficiciyar riga sai wani lages tana tafiya d'uwawukan na jujjuyawa Gwaggo hakurinta daya k'are ta bud'e baki yadda zataji tace "gaskiya mu za'a b'ata mana yara haka kurum wannan ai rashin tarbiyya ne" Amarya kuwa data ji mi suke cewa sherewa tayi ta shige d'akin Abba yana zaune idasawa tayi kusa dashi ta zauna sai kuma can ta saki kuka da sauri Abba ya fara tabbayar miya faru fara zayyane mai k'arya da gaskiya tayi "dan mi zan rink'a ma kwalliya wai ni y'ar tasha ce banda tarbiyya" ta idasa maganar tana sakin kukan munafirci,
Abba kuwa jikinsa har yana kyarma ya tashi ya nufi tsakar gida muna zaune saida tsayuwar mutum muka gani ya fara zazzaga masifa inda yake shiga bata nan yake fita ba kuma bai ware kowa ba daga Inna gajen har Gwaggo ya k'ara cewa "dan mi za'a ce baza tai kwalliya ba shin bani takewa ba karna k'ara ji karna k'ara gani wani ya shiga harkar ta a gidan nan" zai juya ya tafi Gwaggo data cika sauran kad'an ta fashe ganin zai tafi bata mai da magana bata amayar da abinda ke cikinta ba dan in bata fad'i abinda take jiba k'ila sai tayi zazzab'i🤣 (kai Gwaggo matsifa)ta tashi da sauri tace "ahh lallai Malam munga wannan kai gaka mijin zamani ko daga magana ance za'a b'ata mana yara ai bamu kad'ai bane a cikin gidan ko? kuma koba haka ba ai bak'i na shigowa zata rink'a irin wannan shiga in ma yi zatai saita sa hijabi intaje d'akin naka saita cire can ku k'arata wani ke buk'atar ganin kwalliyar tata jiki ba kyan gani ma" tana ida maganar tayi shigewarta ta d'aki dama ita Gwaggo tana gama maida ma magana zata barka sake da baki tayi yafiyarta Amarya kuwa jin cin fuskar da akai mata yasa ta fito daga d'akin tana zazzaga tijara cewa "ai bak'in ciki ake da surar da Allah yayi mata" Inna gaje ganin abun nasu bamai k'arewa bane yasa ta shige d'aki ita abun nasuma dariya yake bata shin miye abun bak'in ciki a wannan surar da ba kyan gani su dukansu daga ita har Gwaggon sun fita jiki mai kyau.
Nidai dama da tun d'azo na shiga d'an d'aki na anya wannan Amaryar daga zuwa ko sati batai ba har an fara lugudan leb'e tab'e baki nayi ina gyara kwanciya ta dan nima kwata-kwata matar bata kwanta min a rai ba.
Ranar da Inna gaje zata amshi aiki ran nan Inna gaje taga kissa sai Amarya ta k'irk'iri rashin lpy tana kukan kissa tana jikin Abba Gwaggo kuwa tsaki taja tana cewa "wallahi Gaje inkika bari wannan ta k'ara kwana d'akin Malam wani abun ta shirya wai ita bata so ta rabu da miji wallahi wannan rashin lafiyar ta k'arya ce" ta ida maganar tana ficewa d'akin Abban binta sukai da kallo Amarya kuwa ayyanawa take a cikin ranta lallai zata ci uban wannan Gwaggon kuwa, Inna gaje ganin Amarya ta wartsake tana kallon inda Gwaggo tabi tace "to nidai zan kwanta ko inka gama Malam ina jiranka ta shige uwar d'akan Abban Amarya wani bakin ciki ne ya turnik'e ta tashi tayi tana dariyar mugunta a zuciyar ta a zuciyar tana cewa naga uwar da zai iyayi daku kuda Malam sai dai kallo wallahi, Malam dake mata magana sai cewa tayi karya damu jikin da sauk'i ai tana ficewa daga d'akin ta nufi d'akin ta kwana tayi tana zarya batai bacci ba saboda mugun abu,
A wajan Inna gaje kuwa abunda ya d'aure mata kai shine Malam naso ya kusanceta dan kuwa Allah yayi mata ni'ima indai kwananta ne Malm bai iya barinta amma yau kwata-kwata ya kasa abar ma ko tashi bata yi shima dai abun ya d'aure mai kai Inna gaje kuwa da abun ta kwana,
Wasa wasa dai har Inna gaje ta gama kwananta Malam bai iya wani abu da ita akwai matsala kenan lallai kuwa Amaryar nan da shirinta ta shigo amma ita bazata kaita wajan wani Malam ko boka ba akwai Allah ai tabar abun a ranta.
Sai dai abunda bata sani ba koda Gwaggo ta amshe girkin itama dai baya iya wani abu da ita itama Gwaggo ta zata gajiya ce sai da girkin ya sake zagayowa kanta nan ma tayi uzuri sai da taje unguwa ta dawo kusan kwananta biyar da wowarta saiya kasance girkinta ne nanfa ta gane akwai matsala dan kuwa jiya iya yau ta sami Malam d'in cewa kodai baida lafiya ne sai cewa yayi lafiyarsa lau saboda in yana wajan Amarya lafiya lau zai kasance cikakken namiji baya samun matsala a wajanta Gwaggo kuwa tashi tayi tana girgiza kai d'akinta ta nufa tana shiga a hargitse da sauri Haneefa tace "lafiya kuwa Mama?" "Inafa lafiya lallai Haneefa saina ci uwar wannan Amaryar uban naku saina gyara mata zama wallahi ta tab'o ruwan dafa kanta" cewar Gwaggo da sauri Sakina da Haneefa har suna had'a baki wajan cewa "mi yake faruwa ne Mama" Gwaggo kuwa kallonsu tayi tace "wannan ba maganar ku bace" ganin ranta a bace yasa suka fita waje fitarsu keda wuya saiga Laure tayi sallama ni kuwa dake wankin kayana ina jin sallamar ta gaba na ya fad'i dan kuwa yanzu wallahi tunda akace ita zata kaini aikatau na k'ara tsanarta dana ji sunanta sai gaba na ya fad'i kallon gidan namu take tana kallon shashin Amarya dan ita bata cika fitowa ba bare ta zauna cikin mu muma kuma ba wadda keta tata ni harma mantawa nake da ita wallahi.
Laure kuwa shigewa d'akin Gwaggo tayi bayan sun gaisa dasu Haneefa Gwaggo daketa zarya a d'aki dan bata san ma Laure ta shigo ba Laure ganin k'awar tata cikin matsala yasa da sauri ta matsa wajanta tana tab'a ta da cewa "mi yake faruwa ne?" Gwaggo kuwa harta d'an firgita sauke ajiyar zuciya tayi tana zama kusa da Laure da cewa "ke dai bari matsala babba ma kuwa" "to k'awa miyake faruwa ne ni da harna zo miki da Albishir gobe ne zanzo tafiya da Khaleesat Kano" cewar Laure Gwaggo ta gyara zama tace "ai dan wannan ba matsala Allah ya kaimu yau zan sanar da shi Malam d'in amma ba wannan ba k'awa kinsan wannan Amaryar ba k'aramin shiri tayi ba..............✍️
*ZAHRA ROYAL STAR CE*✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/3, 5:33 PM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦♀️💔 ITA CE K'ADDARATA🤦♀️💔*
*ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️
*ROYAL STAR WRITIN'S ASSOCIATION*
PAGE2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣
Laure tace "ina jinki k'awa wane irin shiri ne haka" sauke ajiyar zuciya Gwaggo tayi tace "Laure bazaki gane wannan matar y'ar Akuya bace bari kiji mitayi Mana" nan Gwaggo ta sanar da ita komai "wai kina nufin Malam baya iya komai dake sai ita kam ubancan" cewar Laure Gwaggo kuwa da sauri yace "wallahi kuwa abin na damuna kuma ina gaya miki har ita kanta waccan Gajen tana fuskantar irin matsalar da nake fuskanta wajan Malam tayi shuru ne saboda munafurci kuma na rantse kyaleta tayi nidai Laure na rantse da wadda raina ke hannunsa saina maida mata duk wani mugun abunta" ta ida maganar tana huce Laure ta rik'e baki cike da mamaki tace "to ita kuma ta nan ta b'ullo kenan karki damu k'awa gobe idan na dawo daga kano kai Khaleesat zanje wani gari hayin rafi akwai wani Malam a can yana aiki sosai zan amsu miki taimako inshallahu abinta zaiya koma kanta kai" ta idasa maganar tana rik'e haba dan ita abun ba k'ara min mamaki yake bata ba mata daga zuwa sai fara tsubbace-tsubbace inta san wata ai bata san wata ba sallama sukai tana k'ara jaddada mata kan cewa in shirya da wuri harda zata tafi ina sakar gida yau kwata-kwata tunda Laure ta shigo gidan namu naji wata irin fargaba sai gashi daza ta fita take cemin wai sai tazo d'auka ta wata irin masifaffar fad'uwar gaba ce ta riske ni har saida na dafe k'irjina ina,
Ina kallon Gwaggo tazo ta wuce ni ko a jikinta irin halin dana shiga shikenan zataje ta tsara Abba ina tsaye ina kallonta ina hawaye harta shige d'akin, ji nayi an tab'a ni waigowa nayi Sakina nace cike da tausayi na tace "kiyi hakuri can baya mun miki abubuwa da yawa amma tunda naji Mama zata kaiki aikatau wallahi lokaci d'aya tausayinki ya shiga raina kayi hakuri Allah na tare dake" ta ida maganar cike da tausayina a ranta ni kuwa dad'in dana ji ina son y'an uwana duk da su ba haka bane can baya gara yanzu na fara ganin sauyi rungume juna mukai can saiga Haneefa wani wawan tsaki taja tana shigewa d'aki nidai ban damu ba itama inada sa ran zata sakko dan kuwa ina hangen sona a cikin idonta kawai ra'ayin mahaifiyarsu ce ta canza masu ra'ayi.
Koda Gwaggo ta shiga d'akin wani kayan takaici ta gani dan kuwa Amarya tana mak'ale da Malm wani tsaki taja tana zama kusa dashi tace "Malam ina son magana da kai" tana kallonsa ko shashin inda Amarya take bata kalla ba ita kuwa Narnah sai wani kallon banza take mata, Gwaggo a zuciyar ta cewa take kai wannan mata da mugun hali take da girkinta daba nata ba kullum tana mak'ale da miji ai wallahi anyi sa'a ba wajanta Malam yake ba yau dasai ta yab'a mata bak'ar magana shegiya sai jarabar tsiya, katse masu tunani yayi da cewa "ina jinki" gyara zama tayi tace "yau dama Malam inada y'ar uwa kano tana buk'atar mai tayata aiki ne shine nace ga Khaleesat nan kuma kaga zata sata a makaranta ta gaba da secondary a can dasu Haneefa zankai to basu gama karatu ba su tukun" ta ida maganar cike da kissa irin wadda yasan takan zance gyaran murya yayi yace "kai Masha Allah tunda har makaranta za'a sata ai ba matsala" Gwaggo kuwa wani irin dad'i ne ya sub'oce mata dan kuwa tasan lagon Malam yana son karatu shi yasa sukafi shiri da Khaleesat d'in saboda tana da k'ok'ari sosai da sauri Amarya cike da makirci tace "haba Malam wane irin karatu kuma garda-gardar mata ai kyau ace anyi masu aure yanzu bawai suyita zama a gabanmu ba suna jerawa damu kuma ai nake ga kamar aikatau nefa za'a kaita" ta ida maganar tana wuraga Gwaggo harara wani irin ashar Gwaggo tayi tace "to fad'i ba'a tabbayeki ba bari kiji na gaya miki idan kika kara shiga harkata wallahi kinji na rantse saina yimiki rashin mutumcin da baki tab'a tsammani ba" ta sake Kallon Malam tace "Malam kayi mini iyaka da Amaryarka dan kuwa jiya Haneefa ke gaya min zasu school sunzo tabbayarka kud'in tara shine ta hana su shiga wai ai basa sallama in suka ganku wani hali fa kai tsakani ga Allah yaran nan sun tab'a shigoma d'aki ba sallama yarana basu kai irin wannan rashin tarbiyya da kike tunani ba irin ta gidanku dan haka wallahi ki fita harkar yarana indai kika tab'a min yara a gidan nan bazaki sake marmarin tab'a wasu yara ba inba naki ba kuma rashin tarbiyya da kike cewa ai tana gindinku wallahi yara kuma da kike cewa wai su jera damu ina ruwanki ke kika haifesu ne iyeee koda yake kema ba sanin darajar ilimin kikai ba ai Dan.......... Tunkan ta k'ara fad'ar wani abun Malam ya d'aga mata hannu danya lura Amarya ta cika saura kad'an take jira zata iya zuwa tace zasu buga yace "ya isa haka ke kuma Narnah baki kyauta ba muna magana bai kamata kisa baki bama saboda kedai yaran nan taddasu kikai a tare kuma aure ai lokaci ne in...... Fashewa tayi da kuka tunkan ya ida maganar tana cewa "haba Malam yanzu ka goyi bayanta kenan ka duba fa ka gani irin cin kashin da tayi min harda had'awa da y'an gidanmu" ta ida maganar cikin kuka da kissa da sauri Malam yace "ni ban goyi bayan kowa ba shi yasa akace in zaka fad'i magana ka fad'e ta dai-dai dan baka san wadda za'a dawo ma da itaba kinga yanzu ta fad'a miki maganar dake kika fara shiga harkata" juyawa yayi wajan Gwaggo yace "ke kuma bai kamata ki fad'i haka ba yanzu dai tashi kije Allah ya kaimu goben" cike da murna har biyu tasa Amarya kuka ta b'ata zaman cike da kissa irin ta mata tace "to Malam ka sanni dai bana barin ta kwana kayi hakuri" tana idawa ta tashi ta fice tana dariya k'asa-k'asa cikin zuci kuwa cewa take kad'an kika gani shegiya ba tak'a marki bariki ba hmm kinzo wajan dan wallahi dai-dai nake dake saima na gagareki zama cikin gidan nan tukun,
Lokacin datazo shiga d'aki taganmu nida Sakina bata d'auka wani abu ba tace "ke Khaleesat gobe ki shirya gobe ne tafiyar ku" ta ida maganar tana kallo na ni kuwa cike da jin haushi nace "wacce tafiya kuma Gwaggo?" "Ke naci ubanki fa ni zaki d'auka shashasha ko mi nasan kinsan maganar zaki wani tsareni da idanuwankin nan kwala-kwala saura goben karki shirya da wuri kiga yadda zan dake in..... Da sauri Sakina tace "haba Mama ya kike hakane ai saiki yi mata bayanin wacce unguwa ko" dak'uwa ta dank'ara Mata tace "ungo nan Sakina ki kiyaye ni wallahi nace ubanki ni zaki kalla kice wai in mata bayani kin d'auka bata sani bane makira ko fita idona in rufe wallahi naci mutumcin ku wallahi" fad'a ta farayi sai tsiya take zazzaga masifa take dama jira take a d'akin Abba bai bari ta k'arasa fad'ar abinda take niyar fad'a ba sai ta had'a da abinda Amarya tayi mata ta fara yada magana, su kuwa su Sakina tashi sukai suka bata waje taja Khaleesat da har yanzu take hawaye dan Tafiyar ta