[9/3, 5:32 PM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦♀️💔ITA CE K'ADDARATA🤦♀️💔*
*© ZAHRAH ROYAL STAR CE*🌟🖊️
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*
Chapter1️⃣➡️2️⃣
__________________Duk'e take tana uban wanke-wanke sauri take ta gama dan kuwa school take so taje dan kuwa wanke-wanke yafi k'arfin tunaninta tanayi amma kamar k'aro su ake,
Jitai an buga mata kwano an wallosa harya buge mata k'ugu tafe wajan tayi dan kuwa taji zafi Haneefa ce tsaye kanta tana mata kallon banza sanyi take da kayan makaranta itada Sakina sai wani kallo suke mata na raini kallon su tayi zatai magana Haneefa ta tareta da cewa "keee Khaleesat maza wanke min wannan kwanon abinci zamu ci mu wuce ke dama ai makaranta bata dace dake ba" ta ida maganar cike da isgilanci zanyi magana dan kuwa nima ba hakuri ne dani ba duk da jibgata suke kamar kayan wanki amma haka zan zage in tabbaka masu rashin kunya nace "ai kinsan wadda yake dakiki a cikin makarantar dan kuwa kinsan wadda yafi dacewa da makaranta cikinmu" wani irin uban huce take ta cakumo wuyan rigata tana d'aukini da mari da cewa "kee har kin isa ina fad'a kina fad'a dan uwarki" wani irin bacin rai ne ya turnik'e ni jin an zagar min uwa na tsani a zagar min uwa kasancewar bata a raye.
Zan sake gaya mata wata maganar naji saukar duka a bayana nasan ba kowa bace face Gwaggo Mahaifiyarsu Haneefa cike da tsanar da taimin tace "ance uwarki ubanmi zakiyi kuma makaranta yau baki zuwa naga gidan ubanda zaki shegiya mai kama da aljanu zaki duk'a ki cigaba damin aiki ko sai jikinki ya gaya miki" wasu zafafan hawaye ne suka fara sintiri kan kumatu na Gwaggo kuwa ganin na tsaya ina hawaye ta buga min wata uwar tsawa har saida na firgita da cewa "zaki cigaba da aikin ko kuwa kinsan Allah zan iya suke miki karatun gaba d'aya ma inga ta tsiya" ta ida tana kunfar baki,
Ai da jin haka na duk'a dan kuwa kad'an daga aikin Gwaggo ta dak'ile karatun nawa dan kuwa taga ina matuk'ar son karantun ita kuma ba abinda take buri irin ta kuntata min a rayuwa,
Ina kallonsu suka ci suka k'ushi suka wirgo min kwano suna min dariyar mugunta suka wuce makaranta Innah gaje ce ta fito itama matar Babanmu ce sai dai duk Gwaggo tafi fawa a gidan dan kuwa sai abinda tace duk da itama Inna gajen badaga baya ba itama wajan bin malamai ina shan wahala a gidan nan kamar ba gidan mu ba dan itama Inna gajen wajan mugunta amma kara ita dan bata shiga harkar kowa inba dole ba,
Tana zuwa ta d'auki gwano tayi gaba abinta ko a jikinta sai da ta dad'e a d'akin ta k'ara fitowa ta ajemin kwanon da alama abinci taci haka ake min ina wankewa ana d'auka ana dawo min dashi kuma dole in wanke dan gidanmu mo wajan rabon abinci sai sun yada hali kwata-kwata basa shiri da Gwaggo da Inna gaje so kuma abincin a had'e akeyinsa kowacce in girkinta yazo saita cuci y'ar uwarta wajan abincin shi yasa su fito suyita bala'i a tsakar gida shi dai Babanmu wadda suke kara da malam bai iya tsawartar wa Gwaggo dan kuwa shima ta gama dashi sai dai yayi fad'ansa ya gama ya tafi da bacin rai rabonsa da farin-ciki tun mahaifiyata na raye in yaga suna min wannan cin kashin bazai iya tankawa ba saidai ya girgiza kai cike da tausayi ya wuce.
Wannan kenan
Bayan naci uban wanke-wanke da gyar nake tashi saboda bayana zuk'unniyar da nayi naje ina sallama a bakin k'ofar d'akin Gwaggo "kewai miye haka kinzo kin damu mutane" cewar Gwaggo bud'e baki nayi da gyar nace "Gwaggo abinci nafa?" Gwaggo kuwa bud'ar bikinta sai cewa tayi "an cinye saiki bari saina rana yazo kuma saboda Haneefa ce bata k'ushi ba ta had'a da naki" ta fad'a ko a jikinta wani irin bak'in ciki ne ya tokare min zuciya yanzu duk uban aikin dana sha ba'a aje min abinci ba saboda son kai taba d'iyarta ta cinye dama inzata shirya min mugunta haka take min saita had'a min abinci da su Haneefa gasu da shegen cin tsiya haka zasu yimin mugunta su tsinye abincin banci komai ba wai a hakama ina rama wani abun an suka yimin.............✍️
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏

Chapter5️⃣➡️6️⃣
Kwafa tayi kawai ta shige d'aki kamar zata tashi sama haka nan taci abincin tana ayyana irin muguntar da zatai mata itama,
Washe gari da safe ma saida aka fiddo da sauran abincin saboda yawansa basu cinyesa ba haka inaji ina gani na zubar dashi saboda bazai ciwo ba sauri nake in gama aiki na dan yau wallahi nayi al'k'awarin sai naje school koda na gama duk sun fito sai wani ya tsina suke saida suka riga ni tafiya,
Nasa takalmi na kenan naji Gwaggo daga d'aki na kwala min kira ai da sauri na fice a goje sai makaranta a zuciyata nace mun had'u inna dawo amma yau kam sai naje,
Gwaggo dake aikin kiran Khaleesat jin shuru ta fito waje ganin ba kowa yasa tace "yanzu fa naji motsinta hmm zakizo ki same nine y'ar banzar yarinya"
Tsaki taji an ja mata waigo tayi da sauri Inna gaje dake zaune tana yanke farci tana wak'ar irin ta karin magana "ahayyeee nanayee ai dole girma ya zube ahayyee nanayee" wata uwar ashar ta buga tana nona Inna gaje da cewa "Ohoo dai yara dai ba wadda ya isa iko dasu saini in an isa a haifa mana in hisari banza ne kaza tayi mana" wani tuk'uk'in bakin ciki ne ya tasowa Inna gaje ta tsani ai mata gorin haihuwa ita ta hana kanta ne tashi tayi tana cewa "yo komai miye dai zama dani dole a matsayin kishiya ni kadan garan bakin tulo ce wallahi" tayi shigewarta d'aki tabar Gwaggo sake da baki sai kunfan baki take tana zazzaga masifa ita d'aya,
Koda naje school muna ta shirye-shiryen zana exam d'in k'arshe ta gama secondary School su kuwa su Haneefa saboda rashin k'ok'arin su har yanzu sun gagara su gama suna SS2 har yanzu dan su ko a jikinsu wai cewa na wuce su,
Bayan an tashi sun riga ni isa gida ina shigowa Gwaggo ta daka min tsawa da cewa "ke dan k'aniyarki kina jina ina magana d'azo ke mai kunnan k'ashi kohh? Tohm aiki ne dai sai kinyi shi kinma jama kanki ke Haneefa maza d'akko kayan wankin ko duka saita wanke su" cike da murna Haneefa ta kwasu uban wanki wadda yafi k'arfin tunanina ta jifgesu a gaba na tana wargo min harara ramawa nayi dan cike nake da haushin su "keee dan kutumar ubanki ni kike harara" kamo ni tayi ta buga min dundu a baya zata sake kaimin wani dukan Gwaggo ta d'aga mata hannu da cewa "barta haka ai Wannan wankin ma ya isheta kuma wallahi indai bai fita ba sosai duk yawansa saikin sake sa kinji na gaya miki".
Cike da damuwa a fuska ta na aje jikkata nazu na fara wankin ga uban daud'a da kayan ke gare su wankin nake sosai ina durzar hannuna duk yayi jawur abu ga farar fata haka na daure ina share hawaye dan na tsani wanki wallahi saida na kusa gamawa saiga Haneefa da kayan school wai suma saina wanke tashi nayi nace "na rantse na gaji" saukar wani gigitaccan mari naji a k'unci na dafe wajan nayi ina kallon Haneefa dake huce "ke harkin isa a kawo abu kice wai kin gaji ai ba abinda ya dace dake sai aikin banza shashasha kawai" tana rufe baki taji itama an wanketa da marin daya sa k'ararsa karad'e gidan namu Gwaggo dake d'aki da gudu ta fito Inna gaje ma fitowa tayi ba kowa bane face Abba ya nuna Haneefa da cewa "ke dai bakuda mutumci ko duk abinda take muku bakwa gani..... Zai sake magana Gwaggo ta d'aga mai tsawa "haba Malam wannan ai san kaine saika tsaya kiyi bincike mana wannna yarinyar mai kama da aljanu dan kawai dama baka son yarana zaka nuna banbanci iyeee" shuru yayi ya kasa maida mata magana dan kuwa ta riga ta gama dashi bai iya maida mata magana,
Haneefa dake kukan munafirci ta k'ara b'arkewa dashi da sauri Gwaggo tace "yi shurun ki ke kuma badai Ubanki ya rama miki ba zaki shigo hannu nane" kwafa tayi suka shige d'aki Abba da tun d'azu ya wuce cike da bak'in ciki a ransa,
Fitowar sa waje ya samo wani abokinsa Hamza Abba ya zauna yana sauke ajiyar zuciya kallon sa Hamza yayi yace "yadai malam na ganka haka?" Abba ya d'an gyara zama yace"ba komai" "hmm anya kuwa ba matan nan naka bane wai mi yasa ba zaka k'ara aure bane inada wata y'ar uwa dake Dutse baza warace ta auranta ya mutu mi zai hana ka neme ta" cewar Hamza Abba yace "haba Hamza in k'arowa kaina aiki fa" Hamza yace "a'a fa zaka samu mai mayema gurbin Ayshatu (Mahaifiyar Khaleesat) kenan dan kuwa Abba yafi sun ya zauna da mata uku ya saba da hakan Hamza yayi ta zuga sa k'arshe yace zai duba ya gani..............✍️

Chapter3️⃣➡️4️⃣
_________________ Hakama ina rama wani abun in suka yimin ban ankaraba naji an bangaje ni za'a shiga d'akin Gwaggo su Haneefa ne suka dawo ko tashi ba'ai ba dan kuwa kwata-kwata basa son makaranta kawai dansu kuntata minne ni kar naje,
Harara suka b'alla min zasu shige tsaki na danna masu nima dan cike nake da haushin su wallahi birki Sakina taja tana waigowa da yimin mugun kallo tace "ke dan uwarki dawa kike?" Murgud'e d'an k'aramin baki na dake d'auke da jan leb'e nayi nace "badai uwata ba wallahi" da hanzari zata ruk'o ni tana uban ihu da gudu na matsa dan kuwa Sakina rusheshiya ce ga tsawo ni kuwa y'ar figigiya dani kwata-kwata banda jiki tsaka tsakiya nake sai uban k'ugu da Hifs da k'irjina dake cike kamar ba y'ar shekara 19 ba ga tsanin kyau da Allah yayi min kamar aljana shi yasa Gwaggo ke mugun bak'in ciki dani daga ita har yaranta kasancewar nafisu komai.
Sakina ce ke kunfan baki "dan ubanki zakizo ki same nine dani kike zancan" ta shige d'aki tana huce Gwaggo tace "waiku har an tashi ne zaku dawo?" Haneefa ce tace "a'a kawai tara aka tashi shine muka dawo sai kuma gobe" tab'e baki tayi dan itama ba wani sanin dad'in ilimin tayi ba.
Ni kuwa ganin na tsira na samu waje na zauna ina sauke ajiyar zuciya d'aki na shiga wadda yake kama da akurkin kaji amma da yake inada tsafta baka tab'a ganin k'azanta a d'akin,
Ina zaune na d'akko littafi na ina karatu nayi nisa cikin karatu dan harna manta da wani jan fad'a da nayi naji an fisge littafin dake hannu na tare da yayyagasa d'agowa nayi da nufin inyi rashin mutumci kawai naga Gwaggo tsaye a kaina "ke dan kutumar ubanki har rana tayi baki d'ora sanwa ba iyee saura yarana su fara jin yinwa zaki tashi kosai na makeki a nan" da sauri na tashi ina k'unk'uni da sauri Gwaggo tace "mi kike cewa ne iyee?" Nace "ni ba abinda nace" "yo kimayi magana kiga yadda zanyi dake a gidan nan saura inkin gama kibar min sanwa waccan bak'ar matar tazo ta tab'a min" tana nufin Inna gaje kenan
Innah gaje dake zaune dan itama bata barin ta kwana tace "hmm yoni mi zanci da shinkafa ita daice kike ma had'ama itace dai kikeso dama tazo ranar girkinki ai gashi tazo akan naki girkin mi zanyi da ita wadda aka ban ta anfane ni wallahi kinsan masu cikin ci a gidan nan" Gwaggo wata uwar ashar ta danna tana kunfar baki da cewa "wallahi kinsan nafi k'arfinki daga ni har yarana bakin ciki dai kike sanwa dai tazo kaina a'ato sai dai ki mutu wallahi" Inna gaje kuwa d'aki ta shige tana tab'e baki,
Ni abin nasu ma dariya ya bani dan kuwa gidan mu sau biyu ake samu aci shinkafa sauran ranakun kuma bai wuce tuwo ko irin su d'an wake ko danbu to in kana su kaga bakin ciki da kishi ya tashi ace ranar girkin Inna gaje ne cin shinkafa ya kama duk da itama Inna gajen tana munguntar dan kuwa wani lokacin har da safe sai an hiddo ta ko aikin Gwaggo kuwa har suci da safe har a zubar a tsari saboda san kai ni kuwa duk aikin Gwaggo ni nake yi amma sai wadda aka ban in tana so ta shirya min mugunta saita had'a dasu Haneefa dan kawai kar naji abincin ranar juma'a ne da Laraba ake cin shinkafar ko wacce burinta ace itace da aiki ranakun,
Nidai shuru nayi har ta gama kunfan bakin nata tayi gaba d'aki yau ta kasance juma'a yaune Gwaggo ta afsa aiki nayi miya daban nayi wake daban shinkafar kanta daban sana nazo na yanka salat ba wadda yace min sannu ko ya tayani dama na saba na gaji sosai haka na gama naje na sanar mata wanka nayi na fito,
Fitowar da zanyi tana raba abincin kamar yadda ta saba ta raba saida ta tabbatar ta fara d'aibarma Abba sana ta zuba a y'ar kular Inna gaje iya rabin kula y'ay'an ta kuwa saida ta cika masu kowa da nasa kular dan ita Inna gaje bata da yara a gidan sana sake d'abar masu tare dani,
Kirana tayi wai gashi nida su Sakina fuskata ce ra canza zuwa damuwa yanzu duk uban aikin nan da nayi zata had'a ni su haka nan amsa suna zaune tsakar gida na zauna muka fara cin abincin Sakina dake cike da haushi na dan mugunta ta rink'a cika hannu tana tusawa a biki kamin ta cinye wani ta d'ebo wani kamin in ankara sun cinye tas duka bai wuce luma biyu nayi sai wani d'an kad'an da suka bari shima Sakina na tashi tasa k'afa ta barar dashi ta juya ta shige d'aki ko a jikinta can saiga Abba ya shigo gani na haka yasan lallai sunmin muguntar da sauri ya jawoni d'akinsa ya d'ebar min cikin nasa yace "kiyi hakuri kinji Khaleesat wata rana ko ance suyi bazasuyi iya ba" nace "Abba ba komai wallahi" na ida maganar cike da k'aunar Abban nawa da sauri nabar d'akin dakar Gwaggo ta inda ni,
Koda na fito na tadda Inna gaje tazo d'aukar abincin naga ta tsaya tana kallon abincin sai girgiza take cike da bakin ciki a ranta kwafa tayi kawai ta shige d'aki kamar zata tashi sama..............✍️
*FATEEMAH RABI'U CE (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️

Chapter7️⃣➡️8️⃣
Tofa tunda ga sana Abba ya fara neman aure Gwaggo da Inna gaje basu sani ba dan kuwa har waya suke da wadda zai aura d'in kwata-kwata ta fara d'auke mai hankali dan kuwa y'ar duniya ce ta k'arshe kusan auran ta bakwai duk inda taje saita haihu.
Tafe Abba yake yana waya wadda har ya shigo gida bai sani ba ina tsaye ina faman sharar gida Inna gaje na sanwa yau ita keda girki danbu ne take sai uwar zufa take ga hayak'i wutar damuna da wuyar sha'ani, waya yake yana zuba murmushi da sauri ya hanke wayar ganin Inna gaje na fitowa daga madafa ni kuwa dake kallon Abban namu gani nayi yasha mur ya shige d'aki ni kuwa girgiza kai nayi dan koh a jikina duk da bansan miya ke shirin faruwa ba.
Ina gama sharar Inna gaje tace "ke Khaleesat jeki wajan Gwaggonku su kawo wajan abincin su" da to na amsa tsayawa nayi bakin d'akin saida nayi sallama kusan sau uku sana Haneefa dake bakin k'ofar ta wani hankad'e labule kamar zata makeni "kewai ya akai ne kin wani ishe mutune" ta idasa tana warga min harara tsaki naja can ciki wato suna jina kenan koh hmm na fad'a a zuciya ta juyawa nayi ina cewa "dama wajan abincin ku zaku kawo shine dama" Haneefa dake kallo na ganin na wuce kwafa tayi ta shige d'akin nasu tana sanar da Gwaggo Aiken,
Gwaggo kuwa kwano kusan hud'u ta had'a taba Haneefa takai koda Haneefa takai Inna gaje kallon ta kawai tayi sai kuma ta tsaya mata a kai d'agowa tayi Haneefa bako kunya take kallon ta ido cikin ido Inna gaje tace "kin wani tsaya min a kai bana son haka fa in uwar taku na aiki zuwa nake na tsaya mata ne?" Gunguni Haneefa ta farayi ta juwa ta koma wani waje ta zauna sai da Inna gaje ta raba ta zuba kwano uku tabar masu d'ayan ai basu hud'u bane d'akin ita za'a rainawa wayo,
Saida ta gama tad'au nata takae d'aki takai na Abba ta kirani nad'au nawa ranar girkin Inna gaje ne kawai nakeci na k'ushi duk da bata wani yimin magana ai bata min mugunta Haneefa dake cika tana batsewa ganin saida ta gama sana tace "kya iya zuwa kid'au naku" tayi shigewarta d'aki Haneefa shiga madafar tayi ganin ba'a sa kwano d'ayan ba da sauri ta d'auka tayi d'akinsu tana shiga ta fara da cewa "kin gani koh Mama abinda tasa mana harda rage kwano d'aya kinga uban wadda ta d'iba kuwa" tashi Gwaggo tayi ta fara zazzaga masifa fitowa tayi tana cewa "kina ina y'ar gidan matsiyata dangin yunwa kece wacce baki saba cin abinci ba ba'a saba ba daga gidan tsoho" Inna gaje duk da taji zafin maganar kawai ta share ta tamak'i fita saima ta jawo kwano ta fara cin abincin ta tana y'ar rera wak'a Gwaggo kuwa sai zazzaga masifa take inda take shiga ba nan take fitaba sai da ta gaji dan kanta tana kwafa da cewa "kinma maida ni shashasha ai zamu had'u ne wallahi" ni Koh dake zaune saura kad'an in gama cin nawa rai a b'ace tazo wuceni tasa k'afa ta hanb'arar dani sauran danbun ya b'are ni kuwa abin nata ma dariya yake ban rufe baki nayi dariya na tasu min a kaina za'a huce kenan
Juyawa tayi kaina "ke kuma wallahi kibar ganin Abban naku ya dakar min y'a wallahi nasan mizan miki ki jirani" tana juyawa fuuuu a fusace ta shige d'aki zuciya tace tayi wata irin bugawa Gwaggo fa ba imani ne da itaba komiye zata iya domin kuntata min..........✍️

*©ZAHRAH ROYAL STAR CE*🌟🖊️

Chapter9️⃣➡️🔟
Tafe muke yau mun dawo school gaba d'aya dan har an fara mana exam ta fita secondary wadda ni kad'ai ke zana jarabawar wani lokacin sai dai in sab'ewa Gwaggo dan tana sane zata sani uban aiki dan duk karna zana jarabawar haka wani time d'in zan tafi a makare ina hawaye cikin ikon Allah gashi har mun kusa gamawa tafe nake ina tunanin dana rasa ma na miye ma harna d'an bangaje Haneefa da muke tafiya tare da sauri ta juyo dani tana d'uma min dundu a baya da cewa "wai ke bakya ganin gabanki ne ke kinma rainani ni zaki bangaje" nidai bance komai ba sai d'an murgud'e d'an k'aramin baki na da nayi kwafa tayi tana bina a baya har muka isa gida,
Koda muka isa gida wani tashin hankalin muka tadda dan kuwa Inna gaje ce da Gwaggo suna fad'a kamar kaji akan dai abinci dan yau Inna gaje ta fita girki Gwaggo ta zuba mata wani d'an abinci shine tace "wallahi bazanci wannan abincin ba wannan ai rashin imani ne" koni dana kalli abincin kamar wadda k'aramin yaro zaici haba,
Gwaggo ta k'ara da cewa "yo kada Allah ya baki ikon ci ace ayo mutum saicin tsiya ya k'ara afki ai" Inna gaje tana gaji da wannan cin kashin da ake mata tace "wallahi bari malam ya dawo bazan iya ba gara ya raba mana abinci dani dake" "ahayee nanayee tunkan kizo gidan nan akeyin abinci a had'e kuma ba'aza tab'a rabawa ba kima bud'e kunnan ki kiji da kyau" cewar Gwaggo,
Abba dake shigowa tun d'azo yake jin hayaniya wannan abu ya ishesa yace "inma zaku gyara ku gyara dan kuwa abinci dai bazan iya rabawa ba kuna gida d'aya kai koma ba gida d'aya kuke ba zan iya sawa ayi a kaima ta wajan" yana gama fad'a ya shigewarsa d'aki Gwaggo kuwa shewa ta saki taja yaranta sai d'aki Inna gaje kuwa wasu irin hawaye masu zafi ya zubo mata da sauri ta share matsowa nayi kusa da ita duk da bamu cika magana ba nace "Inna gaje kiyi hakuri gidan namu sai hakuri kam" da sauri tace nagode ta shige d'aki itama d'aki na shiga saida na gama abinda nake na zauna k'ofar d'akin Gwaggo,
Sallama naji an dank'ara amsawa nayi ina kallon matar dake shigowa k'awar Gwaggo ce y'ar duniya daka kalle ta kasan tasan dakan duk wani tugu gaidata nayi ina binta da harara sai wani yatsina take tana taunar cingam saiga Gwaggo ta fito da sauri jin muryar aminiyarta shewa suka saki Gwaggo tace "ahh Laure yau kece a gidan namu" Laure kuwa dake kallon Gwaggo tace "ai kuwa yau akwai magana ai mu shiga ciki tukun" "ai dama ke ba'a ganinki a haka nan ba wata data" cewar Gwaggo shigewa sukai d'aki ni kuwa tab'e baki nayi wai suma sunsan wata data ina ji su Haneefa na gaisheta amma kosu fito su basu waje saima k'ara b'ararrajewa da sukayi Laure kuwa bata damuwa ba tunda itama ba cikakkiyar tarbiyya ce da itaba,
Gwaggo tace "na k'agara inji da wane labari kike tafe ne k'awalli" "hmm kedai bari nayi mamakin ganinku haka cikin kwanciyar hankali...... Da sauri Gwaggo ta tace "ban gane ba daya kikeso ki ganmu iyee" tana bata kallon banza da sauri Laure tace "ke haba kefa baki cin ribar zance ai kya tsaya kiji k'arshen zancen ko?" Gwaggo ta k'ara cewa "tohm ina jinki kuma fa hakane" gyara zama Laure tayi tace "wani labari nake ji a cikin gari wai malam zai k'ara aure shine nayi mamaki kodai bakuda labari in.... Da sauri Gwaggo ta d'aga mata hannu jikinta ma kyarma ta tashi zunbur da cewa "ke Laure wane malam d'in kike nufi Wai?" "Malam dai mijinki" cewar Laure Gwaggo kuwa dake kallon ta cike da d'unbin mamaki tace "to ke a