Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
KOMAI RASHIN IMANIN MUTUM A WANNAN LOKACI SAIYA TAUSAYAWA GIMBIYA BAHJAHT DUBA DA KASANCEWARTA SHAHARARRIYAR ÝAR SARAUTA AMMA YAU ITACE A WANNAN HALIN, (KUMA IRIN WANNAN DALILIN NE YASA NAKE TSORON FARA SOYAYYA) Safiya nayi wani badakare yazo da bushashshiyar gurasa Ya dinga bi daki daki yana rabawa fursunonin, koda yazo dakinda bahjaht take sai ya daka mata tsawa Firgigit ta mike zaune, kawai sai wannan badakaren ya cilla mata gurasa guda daya ta cikin taga Sannan yace da ita Ke yarinya ki gaggauta cin wannan domin nan ba gidan sarautar ku bane idan kuma kinki sai yunwa ta kasheki Yana gama fadar haka sai ya miko mata wani dan karamin kofi dauke da ruwa acikinsa .wanda yawansa bai wuce kurba biyu ba Sannan ya wuce daki na gaban nata, tafiyarsa keda wuya sai ta dauki wannan busashshiyar gurasar ta dingaci Kwallar bakin ciki na zuba acikin idanunta ta fara tunani acikin zuciyarta kamar haka Wai wanne irin laifi na aikatawa mahaifina da har ya yanke mini wannan danyen hukunci? Shin ko dan na kamu da soyayyar hassanul basari ne? Indai kuwa don na kamu da soyayyar hassanul basari ne to tabbas saidai ya kasheni Domin soyayyarsa tafiye mini rayuwa ayanzu, Ahaka ta gama cin gurasar sannan tasha ruwa zuciyarta cike da sake sake Tana cikin wannan haline kawai taga an bude kofar kurkukun Sai ta hangi mahaifinta sarki mayasin tare da dakaru suna take masa baya Ahankali suka karaso bakin dakin da take har a sannan zuciyar sarki mayasin batayi sanyi ba Ragowar dakarun kuma suka tsaya abaya yadda ba zasu ji me zasu tattauna ba Da zuwansa sai ya tsaya abakin kofar dakin da take suka tsaya suna kallon juna atsakaninsu Sarki mayasin yace Yake ýata ina mai gaggauta shawartarki daki janye alkawarin dake tsakaninki Da sadauki hassanul basari muddin kinaso ki dawo mu ci gaba da rayuwa kamar yadda muke ada Ina mai tabbatar miki cewa ni zan samo miki wani masoyin wanda zai maye miki gurbinsa azuciyarki Domin ke yarinya ce baki san matsalar soyayya da ma'abota addinin musulunci take da ita ba A duniya babu abindana tsana sama da ma'abota wannan addini kuma nima haka na gada daga iyaye da kakanni Don haka baki isa akanki a canja tsarin masarautata ba Idan baki sani ba to inaso ki sani akan sarautata da kuma kimata babu abinda bazan iya hakura dashi ba Hatta ke din nan zan iya hakura dake akan kimata da sarautata Ki sani cewa a rayuwata babu abindana tsana face ma'abota addinin musulunci Wannan dalilin ne yasa nayi alkawarin jini na bazai taba auren nasu ba , Idan kuwa kikaki karbar tayi na to anan zaki ci gaba da rayuwa har karshen rayuwarki Kinga baki isa ki sake ganin hassanul basari ba kuma shima bai isa ya san inda kike ba balle har yazo domin ya ganki SHIN GIMBIYA BAHJAHT ZATA YARDA DA TAYIN DA MAHAIFINTA YAYI MATA ? MENENE DALILIN DAYASA SARKI MAYASIN YA TSANI MA'ABOTA ADDININ MUSULUNCI? SHIN SADAUKI HASSANUL BASARI YASAN HALINDA GIMBIYA BAHJAHT TAKE CIKI ? WACCE IRIN AMSA GIMBIYA BAHJAHT ZATA BAIWA MAHAIFINTA DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++ZUBAR DA JINI 4 +++++++++++PART C +++++++++++++LBR HABIBULLAH KBR Koda gimbiya bahjaht ta gama sauraron maganar mahaifinta wato sarki mayasin Sai kawai ta bushe da dariya sannan tace Tabbas yanzu na gane gaba daya manufarka da kuma banbancin dake tsakanina da kai Kai ka fara yaki dani ne ta hanyar tozarta ni a idon talakawa Saboda kawai muradin zuciyarka da kuma fifita sarautar ka akan ýarka ta cikinka Hakika yanzu na fuskanci cewa duk soyayyar daka nuna mini abaya ta rushe Kuma shin kana tunanin idan har na fito kimata da kuma daraja zata dawo a idon duniya? Ina mai tabbatar maka da cewa koda na fita daga wannan kurkuku indai kaine ka fitar dani to zan hadiyi zuciya ne na mutu Kuma dani dakai duk muna kan tafarki guda ne kai ka zabi sarautar ka akan darajata da kuma kimata Ni kuma na zabi soyayyar wanda zuciyata ta gama nutsewa cikin soyayyar sa Kuma a halin yanzu shine kadai muradin rayuwata zan iya hakura da komai kuma zan iya fuskantar kowanne irin wahala da tozarci Indai akan soyayyarsa ne, Saboda haka kamar yadda kake ganin cewa ba zaka iya janye Makaman yakinka akaina ba, to nima haka a shirye nake daka dandana mini kowacce irin azaba ce Don zamana anan a halin yanzu yafiye mini zama tareda kai Kuma ina mai baka shawara idan har kanason mulkinka Yaci gaba da dorewa to kada ka kuskura labarin wannan tozarci dakayi mini yaje kunnen sadauki hassanul basari Don sai ya shigo cikin birninka yaci ka da yaki sannan a gaban idonka zaizo har nan ya ruguza wannan kurkukun taka ya fitar dani Muje mu kafa sabuwar rayuwa ni dashi Dajin haka sai mayasin yayi mata murmushin mugunta yace Lallai na fuskanci har yanzu akwai sauran kuruciya atare dake Shin a halin yanzu har akwai wanda zai iya tunkarar birnina da yaki? Kuma yayi nasara? Gaskiya kina yaudarar zuciyarki Kuma daga yanzu na yanke duk wata alakata dake anan gidan kurkukun zaki karaci rayuwarki har karshen rayuwarki Ina dada tabbatar miki cewa bakin ciki shine zai kashe ki. Awannan gida Gama fadin haka keda wuya sai sarki mayasin ya juya mata baya ya kama hanyar komawarsa gida Dakaru na take masa baya Su kansu dakarun ba karamin tausayi gimbiya bahjaht ta basu ba Suna tafiya har waiwayowa baya suka dingayi fuskokinsu cike da alamun tausayawa Fitar sarki keda wuya sai gimbiya bahjaht ta koma ta zauna Ta hadiye duk bacin ranta kamar babu wani abu a cikin zuciyarta Tana cikin zaman ne sai badakaren daya kawo musu abinci yazo ya dinga bi daki daki yana kwance daurarrun. Da suke ciki Domin haka ka'idar kurkukun take akullum sai an zo an kwance fursunoni domin su dan zagaya su motsa kafafunsu Bayan ya gama kwancesu sai dukkansu suka dinga fitowa Suna harkokinsu da wasanni ,wasu ma harda gwajin karfi sukeyi a tsakininsu Shi kuwa uzumnal a wannan lokaci yana kwance yana shara barci acikinsa domin jiya da dare bai samu ya rintsa ba Babban kuskuren da akayi ginbiya bahjaht bata san dakin da aka daure uzumnal ba Bare taje su zauna tare saboda dashi kadai ya saba, tun lokacin yarinta Don haka kawai saita ware gefe guda ita kadai ta zauna Tana yin zancen zuci da kuma tunane tunanenta ,wasu kuma a cikin fursunonin sai nunata sukeyi sunata gulmarta Da shaci fadi akan laifin data aikata wa mahaifinta har ya kawo ta wannan wuri Acan bangaren da maza suke kuma masu manyan laifuka acikin fursunonin kuwa akwai wani gabjejen bakin kato kakkarfa Wanda bashi da buri arayuwarsa face ya kama kyawawan ýan mata yayi musu fyade Kuma wannan danyen aiki shine kadai sana'arsa domin har zuwa gurin bokaye yake neman sa'a Hakanne yasa duk macen da yaje wajenta ta karfi saita bashi hadin kai A dalilin hakane ýan mata suka dinga gudunsa da zarar sun sami labarin ya biyo hanya sai su Dinga ratsewa suna canja hanya Koda yaga ya debe lokuta ba tare da ya sami matan da zai lalata ba sai ya dinga bi gida gida yana haurawa ciki yayiwa ýar mai gidan fyade Ana cikin hakane watarana aka sami bacin rana ya fada hannun malan maharaz Mahaifin sadauki hassanul basari alokacin shima ya shiga cikin birnin fasawana kamar yadda ta saba Shine suka hadu da shi wannan gabjejen kwarton wanda akewa lakabi da karmus Ya kamashi ya mika shi ga sarkin yakin birnin shi kuma ya mikashi ga sarki mayasin Aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku Tun daga sanda aka kawo shi cikin kurkukun ya addabi fursunoni mata da suke ciki Ba'a taba samun samun wanda zai taka masa burki ba Wannan ne yasa yake cin karensa babu babbaka, To tun daga lokacin da karmus yayi arba da gimbiya bahjaht Shikenan sai ya kasa tsaye ko zaune domin gani yake yau ga dama tazo masa har gida Wannan daliline yasa a daren gaba daya baiyi barci ba Lokacin da aka fito da fursunonin sai kawai karmus Ya fara laluben inda zaiga gimbiya bahjaht saidaya duba ko ina bai ganta ba Kwatsam sai yayi arba da ita acan gefe guda ta fada cikin kogin tunani A wannan lokaci gaba daya hankalinta ya fita daga jikinta Tunda karmus yayi arba da ita a wannan yanayi sai fuskarsa ta fadada da murmushi Domin ya tabbatar da cewa ya sami macen da bai taba samun mai kwatankwacin kyawunta ba Kai tsaye ya durfafi gurin da take zaune, Su kuwa ragowar fursunonin da suke gun duk sai sukayi tsuru tsuru suna kallonsa aka rasa wanda zaice masa kala saboda suna matukar tsoronsa Koda ya isa gurin da bahjaht take kai tsaye ya dora hannunsa akan kafadarta Cikin sauri ta juyo bayanta domin taga kowanene atsaye abayanta Kallo daya gimbiya bahjaht tayi masa kawai saita hade fuskarta Domin ta san ko wanene shi agabanta aka tuso keyarsa aka kawo shi gidan kurkukun nan Kawai sai tasa hannunta ta ture hannun nasa tace yakai karmus Ka gaggauta janye mugun nufinka akaina domin bazan taba baka hadikai ba Idan har kaga bukatarka ta biya to saidai idan bana nunfashi adoron kasa Dajin haka sai karmus ya bushe da dariya sannan yace Lallai yarinya kin fiya tsaurin ido shin da wanne karfin zaki iya hanani biyan bukatata akanki? Ke ina tabbatar miki cewa kamar yadda cikin gari yake mallakin mahaifinki To nima nan gurin mallaki na ne nine nake tsara yadda nakeso acikinsa don haka sai mu zuba mu gani, Da gama fadin haka saiya shuri ginbiya bahjaht da hannuwansa Da nufin ya shige da ita cikin dakinsa Nantake ta bude bakinta ta kurna uban ihu karar ihun natane ya farkar da uzumnal daga barcin da yakeyi Koda ya kasa kunnuwansa ya tabbata wannan ihun bahjaht ne saiya Daka tsalle ya mike zumbur ya fito daga cikin dakin da yake Ha nufi can bangaren da yake jiyo sautin ihun nata Tundaga nesa ya hango karmus dauke da gimbiya bahjaht akan kafadunsa Sai ya kara karfin gudunsa kafin karmus ya karasa cikin dakinsa tuni uzumnal ya rugashi Ya sha gabansa ta yadda babu ta yadda zai iya shiga cikin dakin harsai ya ture uzumnal Cikin daka tsawa karmus yace da uzumnal kai kuma wanne irin tsautsayine ya kawo ka gabana ? Ka gaggauta kacewa idan ba hakaba yanzu na karya maka kashushuwan jikinka Dajin haka sai uzumnal ya mayar masa da martanin murmushi yace. Lallai indai kanaso ka biya bukatar ka da gimbiya to dole saidai idan bana nunfashi Amma muddin ina nunfashi bazan taba bari ka cika mugun nufinka akanta ba Domin ni har a yanzu ina kallontane amatsayin shugabata Don haka ko wanne hali za'a shiga ni ina matsayin hadiminta ne kuma mai tsaron lafiyarta Kafin wani abu ya sameta to dole sai ya ga bayana Don haka sai ka ajiyeta mu fafata idan har kayi nasara akaina sai ka dauketa ka biya bukatarka Dajin haka sai karmus ya sake bushewa da dariya sannan yace Lallai bakasan ko wanene ni ba shi yasa kake cika baki akaina amma muje zuwa sai mu zuba mu gani Da gama fadin haka sai ya ajiye gimbiya bahjaht a gefe kamar wata kankanuwar yarinya Cikin shammace ya kaiwa uzumnal mummunan duka a muka mukinsa da nufin ya karya masa kashin muka muki Cikin bakin zafin nama nama uzumnal ya kauce masa ya naushi iska Nan take shima ya afka masa suka kachame da azababben fada hannu da kafa Nanfa suka dinga kaiwa junansu naushi gami da kutufo Azahirin gaskiya karmus yafi uzumnal karfin damtse domin dakyar uzumnal yake iya jure karfin dukan nasa Nanfa hankalin gaba daya fursunonin gidan ya juyo zuwa kansu Suka tsaya suna kallon wannan danbe da suke yi, Abu daya ne kawai yake taimakon uzumnal a wannan lokaci Ba komai bane face tsananin zafin namansa da kuma iya zulliyarsa Don badan haka ba da tuni karmus ya gama hada masa jini da majina Tun suna yin kokawar a kofar dakin har saida suka koma can tsakiyar farfajiya Duk sanda wani ya kaiwa wani duka idan ya kauce saidai duk abinda ya samu saidai kaga ya tarwatsashi Cikin kankanin lokaci suka kakkarya duk bencina da kujerun da suke cikin gidan Take duk su biyun suka sunkuya suka dauki katakwayen karyayyun kujerun suka kama fada dasu Fara hakan keda wuya sai kuma fada yasha banban domin uzumnal yafi karmus iya fada da makami Cikin ýan dakiku kadan ya rikirkitashi,ya hada masa jini da majina ta ko'ina Koda karmus ya fuskanci uzumnal yafishi iya dada da makami sai Nantake ya shammace shi ya sa kafa ya doke katakwayen dake hannunsa Sannan shima ya zubar da nasa kawai sai ya shako wuyan uzumnal da hannunsa na hagu ya dagashi sama ya dinga zabga masa naushi Saboda karfin naushin sai da fuskar uzumnal tayi fata fata da jini Idanuwansa suka dinga ganin taurarin wuya saboda tsananin zafin naushin Tun yana iya sa hannunsa da nufin karewa harya zamana ya kasa koda daga hannun nasa Ya zama kamar gawa kafafunsa sai reto suke a sama Awannan lokaci babu abinda zai iya yi domin ceton rayuwarsa Koda ganin abinda ke shirin faruwa sai nan take hankalin gimbiya bahjaht ya tashi ta fara tunanin hanyar da zatabi domin ceton uzumnal Tana cikin wannan halin ne kawai ta tuna da kibiyarta wacce take tufke gashin kanta da ita Koda yin wannan tunani kawai sai ta zaro kibiyar ta rugo da sauri gurin karmus Kamar tana rokonsa akan yayiwa uzumnal afuwa ya kyaleshi Koda ta iso inda yake saita shammace shi ta caka masa kibiyar atsakiyar wuyansa Nantake kibiyar ta huda makoronsa ta faso zuwa wuyansa Baisan sanda ya kurma uban ihu ba saboda tsananin zafin fitar rai Kawai saiya saki uzumnal ya fadi kasa sannan shima ya fadi kasa matacce Adaidai lokacin ne dakarun da suke tsaron kurkukun suka karaso da saurinsu Koda sukaci karo da gawar karmus suka dago a fusace sukace shin acikinku wanene ya aikata wannan danyen aiki? Cikin rashin tsoro bahjaht tace nice domin yayi nufin ka aboki na Shi yasa ni na kasheshi, Dajin haka sai shugaban dakarun murtuke fuska yace Lallai yarinya kin aikata babban kuskure wanda dolene a hukuntakj akansa Yana gama fadin haka sai yayiwa wasu dakaru inkiya Take guda hudu suka dauke mushen karmus hudu kuma suka dauki uzumnal Wasu guda hudun kuma suka daurawa gimbiya bhajaht sarka aka tafi da ita can dakin horo. WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA GIMBIYA BAHJAHT ACAN CIKIN KURKUKUN DARUL MAUT INDA MAHAIFINTA YA KAITA YA DAURETA SABODA TA FARA SOYAYYA DA MA'ABOCIN ADDININ MUSULUNCI 0======[:::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Acan yammacin duniya kuwa wata irin annoba ce ta shiga cikin nahiyar Wacce ta addabi dukkan sarakuna, jarumai da kuma matsafa Babu irin kokarin da masu fada aji basuyi ba domin takile wannan annoba ba amma sun kasa Wannan annobar kuwa ba komai bace ba face bayyanar wani mashahurin kasurgumin matsafi wanda sihirinsa Ya shafe na dukkan matsafan da suke cikin nahiyar babu Abinda yafi tayar musu da hankali face tsananin rashin imaninsa Domin bayyanar sa daidai take data tauraruwa mai wutsiya Wacce akewa lakabi da ganinta ba alheri bane duk inda ya bayyana sai yayiwa kasar gurin ado da jinin halittun da suke rayuwa a yankin Zaluncinsa bai tsaya kan mutane kadai ba hatta dabbobin kan kasa dana cikin ruwa bai kyaleba, Kai in takaice maka bama iya su kadaiba hatta shedanun aljanu suna matukar shakkarsa Acikin sha'aninsa baya tausayin yara, tsofaffi, mara lafiya da mace mai ciki Ba kowa bane wannan bokan ba face wanda akewa lakabi SAHIBUL UKUB IBN ZALUM Gaba daya bashi da wani buri wanda yafi yaga jini yana kwaranya akan kasa Domin tun yana jariri idan har ya fara kuka duk irin rarrashin da za'ayi masa bazai taba daina kuka ba har sai mahaifinsa wanda shi ya gado a gurin sha'anin zalunci da tsafi Yazo da mutum mai rai ya yanka agaban idanunsa sannan zai daina kukan da yakeyi Da irin wannan mummunar dabi'ar ya girma bayan ya girma ne Ya fara neman hanyar da zai daukaka duniya ta sanshi kuma adinga jin tsoronsa Bayan ya kammala binciken ne ya gano cewa muddin yanason cikar burinsa To dolene saiya kashe mahaifinsa ya sha jinin jikinsa Koda gama wannan bincike bai tsaya bata lokaci ba ya shiga dakin da mahaifinsa yake Gudanar da tsatsube tsatsubensa a wannan lokaci zalum ya nutsa cikin halwar tsafi Da zuwan sahibul ukub gurinda mahaifinsa yake bai tsaya bata lokaci ba kawai ya kama kan mahaifinsa ya murde masa wuya Take zalum ya fadi kasa matacce shi kuwa sahibul ukub saiya sami guri ya zauna Ya ci gaba da binciken da mahaifinsa yake acikin halwar Faruwar hakan keda wuya sai yaga ashe irin burinda yake nema Irinsa nahaifinsa yake bincike akansa, ma'ana shima yana burin samun daukakane acikin matsafan duniya domin ya zama gagara badau Koda ganin wannan al'amari sai sahibul ukub ya takarkare ya kwarara uban ihu Sannan ya tofawa gawar mahaifinsa yawu yace Lallai kayi babban kuskure tunda har kake tunanin taka matsayin da nakeson takawa Ka sani koda kana raye baka ka yi jayayya dani ba Yana gama fadin haka sai ya hurawa gawar wutar tsafi Take ta kama da wuta ta kone kurmus tamkai bai taba wanzuwa ba adoron kasa Tundaga wannan rana yaci gaba da tara sirrikan tsafi Harsaida ya cika cikakken hamshakin matsafi a ranar daya kammala hada sirrikan tsafinsa ne Cikin dare daya ya sana'anta wasu manyan maridan dodanni guda hudu. Ya rabasu gabas, yamma, kudu da arewa Acikin abinda bai wuce dakiku goma ba dodannin sukaci haba daya nahiyoyin da yaki SHIN GIMBIYA BAHJAHT ZATA KUBUTA DAGA CIKIN WANNAN KURKUKU? KO KUNA MAHAIFINTA NE ZAI JANYE KUDURINSA AKANTA SHIN SAHIBUL UKUB YANA CIKA BURINSA KUWA ? MENENE DALILIN DA YARIMA WALISU YA DAINA BARNAR DA YAKE? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU AKASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOUARAGEMENT******************ZUBAR DA JINI ******************5 PART A LBR ************** HABIBULLAH KBR Nahiya dayace kadai wannan aiki bai kammala ba itace Nahiyar larabawa domin a itane aka sami akasi har sadauki hassanul basari ya baiyana ya tarwatsa masa dukkan shirinsa Ma'ana ya hallaka maridin daya sana'anta a lokacin daya sauka abirnin fasawana Babban burinsa kuwa shine yaga ya dasawa duniya duniya gaba daya tsoronsa acikin zukatansu Yadda zata kai har su dinga bauta masa, duk abindaya faru tsakanin wannan hadimin maridin dodonsa Da kuma sadauki hassanul basari duk ya gani tareda kuma irin tsananin karfin damtsen da yake dashi Koda gama ganin wannan al'amari sai ya takarkare ya kwarara uban ihu Wanda yasa fadar tasa ta fara girgiza komai ya dinga sauyawa kansa mazauni Aka fara Wata irin tsawa tare da walkiya wacce ta dinga fadawa cikin birane da kuma dajijjika tana kona komai da kowa dake cikin yankin Kasa kuwa ta dinga girgiza tana darewa tare da ruftawa cikinta Mutane da dabbobi kuwa suka dinga gudun ceton rayukansu Ba komai ya janyo haka ba face fushin boka sahibul ukub Daga can kuma sai ya tsuke bakinsa tareda shafar madubin tsafinsa hoton komai ya bace Sannan ya fara sambatu shi kadai yana cewa Lallai hassanul basari ka janyowa kanka bala'in da baka isa ka iya ketareshi ba Zan nuna maka cewa ka tabo tsuliyar dodo wanda bai san hakuri Nayi maka alkawarin kaine zaka kawo kanka gareni da kanka Idan har naje na dauko masoyiyarka gimbiya bahjaht na tabbata kaine zaka kawo kanka gareni sannan nayi maka mummunan kisa wanda ban taba yiwa wani kwatankwacin irinsa ba Kuma bama kaiba hatta kabilarka ma'abota addinin musulunci Sai na shafesu daga doron kasa gaba daya an manta da tarihinsu Yadda baza taba tunawa dasu ba har abada Koda gama fadin haka sai nantake ya rikide daga siffarsa Ya zama guguwa mai karfin gaske Take guguwar ta tashi sama kamar gudun tauraruwa mai wutsiya Ya ratsa ta cikin ginin fadar tasa kamar kiftawar ya bace bat ya kama hanyar da zata kaishi can birnin shawana WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ACAN FADAR BOKA SAHIBUL UKUB HAR ZUWA SANDA YA FITO DOMIN ZUWA SATO GIMBIYA BAHJAHT DA KANSA …… 0======[::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Koda sarkin kasuwa yimana yazo daidai nan a labarinsa Sai ya sa hannu ya rufe littafin dayake karanta musu Cikin sauri gimbiya walisa ta tareshi tace Akan me zaka tsaya da bani wannan kayataccen labari lokacin da ya dauki dadi? Dajin wannan tambaya sai yi mana yayi murmushi yace Haba saurin me kikeyi ne? ki kwantar da hankalinki a hankali zan karasa miki wannan labari Yanzu dare ya raba sosai zaifi kyau muje muyi barci domin gobe mu tashi da wuri muje mu halarci filin gasa da wuri Dajin haka sai tayi ajiyar zuciya gami da gwauron numfashi tace Gaskiya tunda nake bantaba jin kayataccen labari mai kwatankwacin dadin wannan ba Domin na fuskanci akwai soyayya mai karfi da kuma jarumtaka acikinsa Naso ace nima nazo a wannan zamani domin naga yadda jarumtakar sadauki hassanul basari take da idona Dajin haka sai yimana yace Ai haka dai zakiyita sake sake azuciyarki, don babu wanda zaiji wannan labari face yayi sha'awar kasancewa a wannan zamani Hakika ni kaina ba karamin tausayawa gimbiya bahjaht nake ba Domin akanta kadai an nuna matsalolin da zurfafawa acikin soyayya yake haddasawa da kuma yadda masoya suke rike alkawarin juna babu cin amana atsakaninsu Don haka inayi muku fatan tashi lafiya, yana gama fadin haka Sai ya mike ya kama hanyar da zata kaishi dakinsa ya barsu azaune Su kadai tsawon ýan dakiku gimbiya walisa da yaro zaljus suna zaune suna tunani akan wannan labari Daga can sai walisa ta katse shirun dake tsakaninsu Tace da zaljus ai sai ka tashi kaima kaje ka kwanta yadda zamu iya tashi da wuri Tana gama fadin haka sai itama ta mike ta nufi nata masaukin Tana isa ta tarar har kuyangi sun ajiye mata abinci tare da abubuwan sha kala daban daban Tuni kuyangi sun ajiye mata, kai hatta makwancinta ma an gyara mata shi ba tareda bata lokaci ba kawai ta shiga bandaki tayi wanka saboda ta huce gajiyar da take damunta, Bayan ta fito kuma ta zauna taci abincinta ta take cikinta sannan ta kurbi lemo Ta koma kan gado ta kwanta bayan ýa dakiku kadan sai barci ya saceta ***** ******** ****** Acan gidan sarauta kuwa bayan sarki aryan ya shiga cikin gidan sarauta Saiyasa aka kirawo masa alkalin da yake kula da gasar jarumta Cikin kankanin lokaci alkalin gasa yazo gaban sarki aryan ya tsaya yace gani ya shugabana Sarki aryan ya nunawa alkalin gasa kujera tareda umartarsa daya zauna akanta Take kuwa ya cika umarni, kawai sai sarki aryan ya sake umartar wani badakare wanda yake tsaye abakin kofa umarni daya rufe tagogin turakar gaba dayansu Cikin biyayya badakaren yace angama ya shugabana take kuwa ya rufe duk tagogin sannan ya ja kofar turakar ya kulle ta ta waje Daga can sai sarki aryan ya dubi alkalin gasa yace Yakai basdar Ban kiraka wannan ganawar sirri ba sai don nayi maka tambayoyi guda biyu akan wadannan jaruman gasa guda biyar da sukayi saura afilin gasa Tambaya ta farko da zanyi maka itace awanne lokaci wadannan jarumai suka sayi tikitin shiga wannan gasar jarumtakar kuma daga wadanne birane suka zo nan? A zahirin gaskiya ba wai na karaya akan wannan gasa bane Inaso in san wasu sirrika ne akan wadannan jaruman guda biyar domin dukkansu na fuskanci ba wai gasar bace a gabansu dole akwai abinda suke boyewa acikin zukatansu shine yasa suka fake da wannan gasa suka shigo cikin birnin nan kuma da alama sun dade suna tanadi akan wannan gasar Da idona na lura da wasu abubuwa wadanda suka dinga gudana acikin gasar wadanda ba kowane ya lura dasu ba Wanda yasa na fuskanci akwai wadanda suke da mugun tanadi akan wannan birni namu Kai na lura ma har burin kashe rayukan junansu sukeyi damar hakance kawai basu samu ba shi yasa suka hakura Don haka ina mai umartarka da'a canja tsarin wannan gasa daga gobe Za'a baiwa kowa ikon hallaka abokin gwaminsa da idonka zaka gasgata maganata da idanunka Idan akayi haka kuwa kaga mun rage masu nufin

Chapter 8 of 17