Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka Abinda ta manta shine Shifa dan uwanta ne na jini kuma nono daya suka sha Hakama horon yaki dana tsafi duk tare aka basu Duk wani abu da take takama dashi to shima yana dashi Ballantana kuma yanzu da yake da fifikon karfin damtse dana sihiri fiye da ita Kuma ya kasance murucin kan dutse wanda bai fito ba saidaya shirya Abindaya bata mamaki shine ko kadan baiyi motsi ba daga inda yake ba Da ganin haka sai ya bushe da dariya yace Lallai yarinya kinyi matukar burgeni amma duk da haka kin cancanci Mutuwa dalilin da zai hana ni kasheki kawai shine Duk inda mutum yake anaso ya sami makiyi Ni kuma yanzu na fuskanci banida makiyin daya fiki Saboda haka ga fili ga mai doki sai mu zuba muga wanda zaiyi nasara Yanzu zan hallakar da mutanen garin nan idan ke kuma kin isa saiki hanani Wannan shine babban kuskurenda ya aikata a rayuwarsa Domin ya manta cewa komai kankantar makiyi abin tsorone Yana gama fadin haka sai take taga ya rikide ya zama Wata bakar guguwa mai karfin gaske, take guguwar ta Hargitsa birnin gabadaya kura ta turnuke ko ina Faruwar wannan abu keda wuya sai ta fara jin sautin ihun mutane a cikin wannan guguwar Daga can sai taga guguwar ta tarwatse saiga sassan jikin su sarki kalkus Ta zube kasa daga cikin guguwar Koda ganin haka sai itama ta rukide ta zama bakar guguwa Ta tafi da gudun gaske ta tari daya guguwar da nufin su kachame da yaki Koda haduwarsu sai wata iriyar kara mara dadin ji ta tashi Ta cika birnin gaba dayansa wanda hakan ya kara firgita Mutane fiye da farko har saida dajijjikan da suke da makobtaka dasu Suka amsa kuwwa dabbobi kuwa suka dinga faduwa suna mutuwa saboda karfin karar Daga can saiga guguwar jaruma walisa an jefo ta kasa Koda faduwarta saita rikide ta koma ainihin siffar ta Jikinta duk yayi jina jina da jini kuma a lokacin ne Itama daya guguwar ta rukide ta koma siffar yarima walisu Jikinsa ko kadan babu wani tabon rauni kawai sai ya kalli Walisa yayi mata murmushi mai kama dana mugunta Ko kuma na raini sannan ya sake juyawa ya tashi sama Ya koma kan jamaa'r gari yana tsinke musu kawuna Da wannan sarkar tsafin da take hannunsa Kaico hakika zalunci bashida dadi sai kaga mutum yana gudun ceton ransa amma an kamashi an kashe Saboda rashin tausayi Koda walisa taga abinda yake faruwa sai take itama ta daka tsalle ta mike tsaye Kamar babu wani rauni ajikinta kawai ta shuri wani katon Bargo wanda zai debi mutane da yawa akansa saboda kawarinsa Sannan ta tafi daga inda yake wannan barna domin tasan indai Yana gurin bata isa ta iya tsinana wani abu ba saboda banbancin su abayyane yake Dolene saita jira wani dan lokaci wanda zata iya samun galaba akansa Domin ta tabbatar da cewa a yanzu yafi ta karfin sihirin tsafi Babu yadda zata iya gaba da gaba dashi saidai kawai tayi kokarin ceton rayuwar 'yan yara kanana Wannan shine dalilin dayasa ta dauki wannan katon bargo Kawai saita shiga cikin garin ta dinga surar yara tana dorawa akai Sai dai kaga ta shuri bargon da duk mutanen da suke Kansa ta tashi dasu sama tamkar tsummokara tana kaisu Cikin wani dan karamin kauye wanda yake karkashin masarautar madaril adfam ta ajiyesu Lokacin data dawo cikin wannan birnin kawai saitaga Walisu har ya gama kashe mutanen birnin saura wani Yaro guda daya wanda ya zauna agefe daya yanata rusa kuka Shikuwa walisu ya nufi gurin yaron da nufin ya yi masa kisan farat daya Kwatsam sai walisa tazo da gudun tsiya kamar daga cikin baka Aka harbota ta shuri yaron kamar shaho ya shuri dan tsako ta tashi sama tana mai falfala azababbben gudu ta daure yaron a jikin kirjinta Kamar gudun tauraruwa mai wutsiya Koda ganin wannan abu sai nantake walisu ya fusata Ya bude bakinsa Take wata iriyar bakar wuta ta fito daga cikin bakin nasa Tabi inda walisa tayi da matsanancin gudun gaske sai Gashi sunata gasar tsere da ita da wannan wutar inbadon ma tana zulle mata ba da tuni wutar ta kamata ta babbake ta Amma duk da haka sai gashi wutar taki yarda ta zarce Ma'ana taki ta daina bin su abaya sai zulle zulle suke yi Shi kuwa wannan yaron data dauko tuni ya dada rudewa Domin bai taba ganinsa a sararin samaniya ba kuma Gashi a wannan lokaci gudun mutuwa akeyi dashi yana Kallo sunata gifta birane da kuma manyan duwatsu akasansu Koda aka jima ana wannan faman tseren gudu kuma Ta tabbatar da cewa wannan wutar ba zata taba daina binta ba Kuma idan har ta gaji to tabbas karshenta yazo kawai saita Fara yin tunanin hanyarda zata bi domin tsira da rayuwarta Kwatsam saita hango wani katon ruwa acan nesa Da inda take, koda ganin wannan ruwa saita kara zage damtse Ta tafi inda yake sannan ta sauka kasa cikin ruwan ta nutse gaba dayanta Take itama wannan wutar ya sauka akan ruwan Koda faruwar hakan Sai wata kara mata dadin ji ta tashi sama tareda wani Irin bakin hayaki Faruwar hakan keda wuya sai ruwan gaba dayansa ya kafe ya zama tabo Tamkar dama can haka yake ruwa bai taba taruwa a wajen ba Amma duk da haka saida tartsatsin hasken wannan wuta ya taba bayanta Amma ko kadan bai sami wannan yaron ba Nan fa ta fara kokarin ta fito dasu daga cikin wannan tabon Koda ta dago kanta daga can karkashinsa zuwa sama Kawai sai tayi arba da walisu adaidai saman wannan Tabon yana kallon ko ina na cikin dajin ko zaiga gawar walisa Koda ya gama nazarin dajin yaga baiga gawarta ba sai Kawai ya bushe da dariyar mugunta kamar wanda aka yi masa kyakykyawan albishir Sannan kuma ya murtuke fuskarsa cikin daga murya Nasan cewa kina raye baki mutuba kuma kina nan kusa dani To dama ni haka nakeso amma da nayi niyyar hallaka ki da yanzu kin dade da shekawa barzahu farinciki na dayane shine ganin cewa wannan wutar ta kona miki gadon bayanki Kuma dolene kiyi jinyar wannan ciwo komai sihirin tsafinki Bai isa ya warkar miki da wannan ciwon lokaci daya ba Don haka sai kije kiyi jinya sannan idan kin warke ki dawo Daga yanzu ba zamu kara haduwa ba ni dake sai bayan Dan lokaci mai tsawo kuma komai irin kokarin da zakiyi Domin ba zan sake kai hari wani gurin ba har sai na jira kin sami lafiya Ba zaki sake ganina ba sai idan ni ne na bukaci haka Mu ci gaba da farautar juna ina miki fatan samun lafiya cikin kankanin lokaci Koda gama fadin haka sai nan take ya bude fuka fukansa Ya tashi sama cikin gajimare ya bace mata da gani Domin karfin gudunsa ya ninka nata sau hamsin Koda bacewar sa sai nan take walisa ta doro wannan karamin yaron akan kafadunta Sannan ta rarrafo da kyar ta fito daga cikin wannan tabon Alokacin da taji gaba daya jikinta yayi mata tsami saboda Tsananin wahalar data sha koda ta gama fitowa saita Sauke yaron daga kan kafadunta sannan ta dauki ruwa ta kafa abakinta ta kwankwada Saboda tsananin kishirwar da take damunta Bayan nan ta dauki magani ta zuba akan gurin data kone Tana gamawa ta sami guri ta kwanta domin huce gajiyar jikinta Koda ganin haka sai wannan yaron ya karaso gabanta yace Yake wannan jaruma mai abin al'ajabi ina matukar godiya agareki bisa ceton rayuwata da kikayi daga hannun wannan azzalumin amma idan ba zaki damuba inaso na tambayeki Koda jin haka sai tayi murmushi tace Inajinka amma kafin ka tambayeni inaso ka fara fada mini sunanka Yaron yace da farko sunana zaljus agabana wannan azzalumin ya kashe iyayena ke kuma kikazo kika ceceni Tambayar da zanyi miki itace Shin dama kinsan wannan mutumin? domin naga yadda yake yi miji magana kamar dama can ya dade da saninki Dajin wannan tambaya sai kawai ya gyada kai tace Kwarai kuwa yasanni kuma nima nasanshi Asalima uwarmu daya ubanmu daya dashi kuma a rana daya Aka haifemu nice babba sannan kuma shi Duk wannan abu da kaga yana aikatawa shima ba'a saninsa Yakeyi ba domin ruhin wani takadirin boka ne ya shiga jikinsa Wanda ake kiransa da sahibul ukub to shine ya canja masa kwakwalwarsa Kuma yake saka shi aikata wannan ta'addancin da kaga yana aikatawa Wannan dalilin ne yasa nahaifina sukayi bincike da manyan bokayensa Kan yadda za'a shawo kan wannan matsala amma sai biciken ya Nuna musu cewa dolene nima na fito nemansa domin Nice kadai zan iya gaba da gaba dashi ba tareda na mutu ba Kuma yanzu na gamsu da duk abubuwan da suka fada Domin gashi nazo na tareshi da yaki duk da cewa yafini karfin sihiri Amma gashi ina raye har yanzu ban mutuba bayan haka Harma yanzu na sami damar ceton yara kanana wannan babbar shedace Da ta tabbatar mini da cewa nice zan iya hanashi aikata wannan mummunar dabi'a Kuma zan cigaba da bibiyar sa har zuwa sanda zai dawo cikin hayyacinsa Idan kaga na daina wannan aiki to sai dai idan na daina numfashi Koda jin wannan labari sai zaljus ya girgiza kai saboda tsananin daure masa kai da al'anarin yayi Kawai sai ya dago kansa kwallar tausayi tana zubowa Ya dubeta yace Gaskiya nayi matukar tausaya miki domin ban taba ganin irin wannan al'amari ba Ni abinda na sani kawai shine a halayyar mutanen wannan nahiya kana iya samun dan uwa da dan uwa suna farautar juna saboda tsananin kiyayya Amma ke kuma kina kokarin ki hana naki aikata aikin barna ne amatsayinsa na dan uwanki Sannan shi kuma yana kallon ki ne amatsayin abokiyar gabarsa Daga wannan maganar suka tsaya da yin wannan hirar da sukeyi Kawai sai walisa ta tashi ta rarrafa cikin wani katon kogon dutse Da fitilar ice a hannunta ta dudduba ko'ina acikin kogon Ta tabbatar babu wani abu wani abu mai cutarwa sannan Ta yiwa zaljus shimfida, itama itama tayiwa kanta Duk suka samu suka kwanta SHIN MAI ZAI FARU ACIKIN WANNAN KOGON DUTSE? INA LABARIN SARKI FADARUL MUNNAR MAHAIFIN SU WALISA SHIN INA JARUMI WALISU YA TAFI? MY HADU A KASHI NA GABA DAGA HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++++++ 2PART C LBR +++++++++++++++ HABIBULLAH KBR Kwanciyarsu keda wuya sai duk barci mai nauyi ya daukesu Saboda tsananin gajiyar da take jikinsu haka sukayita shara barci mai nauyi abinsu Basu farka ba saida safiya tayi lokacin da hasken rana Ya fito ya shigo har cikin kogon dutsen ya dallare musu idanunsu, bashiri duk su biyun suka farka Walisa ce wacce ta fara farkawa, Tana tashi kawai sai tayi mika sannan ta shuri kwari da bakanta Da nufin ta fita ta farauto musu abin da zasuci Kawai sai zaljus ya sha gabanta yace Haba ya 'yar uwata shin ina zakije ko kin manta da ciwon da yake bayanki? Kodajin wannan tambaya sai tayi murmushi tace Haba tayaya zan iya mantawa da ciwon da yake jikina Wannan fitar da zanyi dolece ta saka zanyita domin nemo mana abincin da zamuci dani da kai Kafin na sami wani garin da zan ajiyeka Karka damu babu abinda zai sameni zan fita kuma zan dawo cikin nasara Ina mai umartarka da ka zauna acikin kogon nan kada ka kuskura kace Zaka fita ko ina daga cikinsa har naje na dawo Tana gama fadar haka haka sai ta kama hanya ta fice daga cikin kogon Koda fitowarta daga cikinsa sai ta kama hanya tana tafiya Hannunta na hagu na ruke da kwari na daman kuma ruke da kibiya Tana tafiyane cikin sanda ko zatayi arba da wata dabbar wacce zata farauta Gaba daya cikin dajin yayi tsit bakajin sautin komai face Na giftawar iska sai bayan ta shafe ýan lokuta tana tafiya sannan Ta hango wata katuwar damisa daga can nesa da inda take Koda yin arba da wannan damisar sai kawai ta dora kibiyarta Akan baka ta saita tsakiyar cikin damisar ta harba Cikin rashin sa'a sai damisar ta goce kibiyar taje ta cake ajikin dutse Take damisar ta juyo sukayi ido biyu da walisa Kawai sai ta falfalo da azababben domin tazo ta bangajeta Ta kashe ta domin itama abinci ta fito farauta kuma gashi ta samu abati Ita kuwa jaruma walisa sai ta tsaya cak ko motsi taki tayi tana jiran karasowar wannan ta Koda ta iso inda walisa take sai ta daka tsalle sama da nufin ta turmushe ta Ta kama fuskar ta ta yayyaga, take itama walisar ta sunkuya ta kaucewa harin damisar Dukkansu su biyun sai suka yi turjiya akan kasa kura ta tashi Sannan suka juyo suka kara afkawa juna da yaki koda fara wannan gumurzu Sai gurin ya rinchabe kura ta tashi saboda kokawar da suke Burin damisar kawai shine ta bangajeta ta fadi Ita kuwa tana yin fadan ne domin kawai taga iyakar karfin ita wannan damisar Saboda ta lura cewa damisar a haukace take saboda yunwar da takeji Kawai hanya takeso ta samu wadda zata cutar da ita amma ta kasa Koda walisa taga wannan damisar ta kasa cutar da ita kuma tana bata mata lokaci Sai kawai ta shureta ta dagata sama ta buga kanta ajikin wani dutse Take kuwa kanta ya dagargaje kwakwalwarta ta zuba akan kasa Sannan ta dauketa ta dorata akan kafadarta ta kama hanyar Komawa kogon dutsen da suke zaune, tafiya kadan tayi ta isa bakin kogon Kai tsaye ta dannan kanta ciki har takai karshensa Alokacin zaljus yana zaune yanata faman tunanin abindaya faru jiya Kafin walisa tazo ta ceci rayuwarsa, don haka har ya shigo cikin kogon bai sani ba Saidata dafa kafadunsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa Walisa tace dashi kai kuma tunanin me kakeyi ne haka Dajin wannan tambaya sai zaljus yace Ina tunawa ne da tsohon birnin mu gaskiya ina mai matukar godiya agareki Domin badon keba da tuni na dade da zama matacce Dajin wannan magana sai walisa tayi murmushi tace Bai kamata ka dinga tunawa da abinda ya riga ya wuce ba Abinda zai faru nan gaba shi zaka dinga fuskanta Nayi maka alkawarin Zan kaika wani gurin da zaka ci gaba da rayuwa acikinsa cikin Kwanciyar hankali kuma anan ne zan rabu dakai inje domin na karasa aikin da yake gaba na Koda gama fadin haka sai kawai tayi shiru da bakinta Ta tashi ta dauki wannan damisar ta jata gefe ta fara aikin gyaranta Cikin kankanin lokaci ta gama gyara naman damisar Sannan ta hada itatuwa ta kunna kyastu wuta ta kama ta gasa naman da ita Bayan ta gama gasa naman sai ta juyo ta dawo gurin zaljus Ta ajiye masa nasa kason agabansa tayi masa izini daya dauka yaci Sannan itama ta fara cin nata naman sunaci suna hira abinsu Kamar dama can sun dade da sanin junansu, Hankali suka gama cinye naman sannan walisa ta tashi ta fara hada kayanta Domin su ci gaba da tafiyar da suke yi Cikin lokuta kadan ta gama sanya kayan yakinta ajikinta Amma bata rufe gadon bayanta ba saboda wannan kunar da take jikin gadon bayanta Sannan ta tashi ta kama hanyar fita daga cikin kogon dutsen Babu shiri shima zaljus ya biyota abaya suka fice daga cikin kogon dutsen Suka kama hanyar da zata kaisu birni Wanda ake kira da suna shawana, gaba daya mutanen wannan birnin sun kasance zakwakuran mayakane masu matukar karfin damtse da iya yaki wanda shakkar wadannan mayakance tasa kasahen da suke makobtaka dasu suke matukar shakkar su duk da cewa sun ninninkasu a yawa Kasancewar shima shugaban wannan birnin ya kasance matashine mai jini ajika, gashi ya kasance kyakykyawan matashi Wanda ýan mata da yawa suke rubibin neman soyayyarsa Amma bai taba kulasu ba, domin tunda ya taso bai taba ganin wata mace ba wacce ta burgeshi ba Har yaji ya kamu da soyayyarta, wannan dalili ne yasa shi ya karyata soyayya cewa ba gaskiya bace ba karyace Koda ýan majalisarsa sukaji haka sai suka bashi shawara kan cewa Yayi shiru da bakinsa kada ya bari wannan magana ta shiga kunnen mutanen gari Don kada wataran yaji kunya saboda wannan maganar daya furta Kuma wannan sarki ya kasance gawurtaccen mayaki, sannan a fannin karfin sihirima ba'a barshi abaya ba Domin anan fannin ma shi ba kanwar lasa bane, bayan haka kuma shi bai kasance azzalumi ba Kuma bai hana zalunci ba Amma duk wanda ya zalunci wani to wanda aka zaluntar yana da ikon kai kara wajen sarki kuma a bi masa hakkinsa Lokacin dasu walisa suka kama hanyar tafiya birnin shawana Sai sukayita kutsawa ta cikin dajijjika iri iri agabansu Kuma sunayin tafiya suna hira a tsakaninsu Tazarar inda suke da kuma birnin shawana tafiyar rabin sa'a ce Don haka basu dade suna tafiyarba suka iso wannan birnin Tun daga nesa suka hango kofar birnin abude kuma ga dakaru nan Suna aiki tsaron kofar kai da ganin wadannan dakaru Kasan cewa dolene su kasance zaratan jarumai kuma gaba daya jikinsu A rufe yake da sulken yaki koda wadannan dakaru suka Hango jaruma walisa daga nesa tareda yaro zaljus sai duk suka dora hannuwansu akan kufen takubbansu Suna masu jiran karasowarta suji me ke tafe da ita Lokacin da ta karaso bakin kofar wannan birnin sai Dakarun suka tareta wani daga cikinsu wanda ya kasance Shine shugabansu yazo ya sha gabanta yace Yake wannan bakuwa shin ke wacece kuma menene yake tafe dake Sannan wannan wanne yaro ne atare dake? Munaso ki fada mana iyakar gaskiya Kada ki boye mana komai dangane da abubuwan da muka tambayeki Idan har kinason shiga wannan birni namu mai albarka Kodajin haka sai tayi murmushi ba tareda ta yi musu maganaba Kawai sai ta zaro hatimin sarautar birninsu na madaril adfam Ta nuna musu Koda sukaga wannan hatimi sai dukkansu suka rissina Agabanta cikin girmamawa sukace Ki gafarce mu ya shugabarmu bamu san kece gimbiya walisa ýa ga mai girma sarki fadarul munnar ba Muna neman afuwarki sannan munayi miki barka da zuwa bayan haka kuma munayi miki tayin babbar gasar jarumta wacce aka saba gabatarwa a birnin nan duk sanda shekara tazagayo kamar yanzu Ahalin yanzu birnin nan ya gama cika da jaruman gasa daga ko ina na wannan nahiyar Don haka kema zamuso ki shiga wannan gagarumar gasa Domin ki nanawa kowa jarumtakarki wacce muka saba jin labarinta Amma kuma ina dan uwan naki ya shiga wato yarima walisu? Kodajin wannan tambaya sai kawai walisa ta gyada kai tace Ai yanzu ba tare dashi muke ba, ni kadaice Wannan kuma yaron da kuke gani na tsinceshi ne a hanya Tana gama fadin haka sai kurum ta kama hanya ta shige cikin birnin Koda ta shiga cikin garin sai kawai taga birnin yacika ya batse Da mutane masu yawan gaske kowa sai tafiyar da harkokinsa Yake cikin kwanciyar hankali, ko'ina ka kalla saidai ka dinga ganin kabilu kala daban daban Kuma zaratan karti masu kirar mutanen farko, ruke da mugayen makaman yaki suna aikin wasa su Wasu kuma saidai kaga suna baiwa kansu horon yaki na daban Lokacin data shiga cikin birnin shawana sai ta dauko wani Bakin kyalle ta rufe fuskarta dashi yadda babu wanda zai iya ganin koda kwayar idanunta Ba komai ne yasa taga mutane kowa yana shirye shiryen wannan gasa ba Face saura kwana uku kacal a fara gabatar da wannan gasar Kuma tun daga lokacin da aka fara gabatar da wannan gasar tsawon shekaru takwas Sarkin garin ne mai suna aryan ne yake cinye wannan gasar ba'a taba samun sabani ba asaboda haka ne ma Yasa yake yiwa kansa kirarin cewa shine gagara badau Sadaukin da babu kamarsa a wannan karni Jin wannan cika baki da sarki aryan yake yine yasa jarumai da yawa suka dauki alwashin cewa Wannan shekarar sai sun ruguza masa tarihin jaruktakarsa To a wannan shekara jarumai sun bayyana daga sassa daban daban na wannan nahiyar domin kawai burin suga cewa sun sami nasarar kawo karshen tarihin jarumtarsa Shi kuwa sarki aryan ko kadan wannan alwashi da sukaci Bai dameshi ba domin yayi imani kan cewa shine wanda zai cinye wannan gasar Komai wuya ko rintsi, don haka nema yasa kyautar dukiya mai yawan gaske ga duk wanda ya sami nasara akansa Aban garen jaruma walisa kuwa ko kadan bata shigo wannan birnin Don halartar wannan gasa ba, kawai dai ta shigone don ta sami wanda zata baiwa amanar yaro zaljus ne Sannan kuma su sami inda zasu yada zango tsawon ýan kwanaki Sannan ta tashi ta kama hanya tabar wannan garin ta kara gaba Haka dai sukayita tafiya acikin birnin shawana su biyu rak Duk inda suka wuce saidai kaga anata kallonsu, kai tsaye ta nufi hanyar da zata kaita gidan sarkin kasuwa Wanda ya kasance dattijo ne dan kimanin shekaru hamsin Gidansa yana daga can karshen kasuwa kuma agurinsa Duk wani bako yake samun gidan da zai zauna domin yin haya a wannan birni Kuma mutumne shi mai son baki da kuma girmama mutane Wannan dalilin ne yasa kowa yake yabonsa acikin birnin Tafiyar dakiku kadan sukayi sannan suka iso gidan sarkin kasuwa Suna zuwa suka tarar da dakaru kimanin su goma suna gadin gidan Koda ganin wadannan dakaru sai kawai walisa ta karasa gabansu Ta tsaya ta dubi shugabansu tace inaso kayi mini sallama da mai gidan ku wato yimana Kodajin wannan batu sai mai gadin yace To ke kuma wacece kuma mai yasa kike son ganin yimana? Dajin wannan tambaya sai tayi murmushi sannan tace Tabbas ku baku sanni ba, amma shi mai gidan naku da zarar yaji muryata Nasan zai shaida ni koda bai kalli fuskata ba Kodajin wannan batu sai badakaren ya girgiza kansa Sannan ya juya ya shiga cikin gidan, bai dade da tafiya ba sai gashi Ya dawo tareda sarkin kasuwa yimana, koda fitowar su Sai yimana ya dubi walisa yace ke kuma wacece kuma Me kike da bukata a gurina? Dajin wannan tambayar sai walisa tace Ni bakuwa ce daga can wata nahiyar daban kuma nazo ne domin ka taimaka mini da masauki Lokacin da takeyin wannan bayani sai kawai dakarun sukaga yimana ya kame kyam kamar gunki Yana nazari akan muryar wannan budurwa Daga can kuma sai sukaga ya bushe da dariya yace Lale marhaban da zuwan gimbiya walisa kuma basadaukiya Mai abin al'ajabi nayi matukar farin cikin sake haduwa dake a rayuwa ta Kuma inayi miki barka da shigowa cikin birnin mu mai albarka Nandai yayi mata jagora suka shige cikin gidansa tare gabaki dayansu Ahaka sukayita shigewa ta cikin soraye har suka kai tsakiyar wani babban falo Sannan yayi mata nuni da wata kujera ya umarceta data zauna akanta Take kuwa ta sami guri ta zauna ,bayan sun dan jima a zaune dayan su Baice kala ba, sai yimana ya katse shirun da yake tsakaninsu da fadin cewa Yake walisa ya akayi na ganki a wannan lokaci ke kadai Ba tareda dan uwanki yarima walisu ba? Ki sani nayi matukar kewarku, kuma bazan taba mantawa Da irin taimakon da kikayi mini ba ke dashi, alokacindana taba shigowa Yankin birninku domin yin kasuwanci ba, Har wasu mugayen ýan fashi suka zo suka tare mini hanya zasuyi mana kwacen hajar da mukazo da ita Ku biyu ne kadai kukazo kuka tarwatsa su da karfin tsiya suka gudu ki sani cewa inba don wannan taimakon da kukayi mini ba Da tuni na dade

Chapter 4 of 17