Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta rufe fuskarta gaba daya idanunta kadai ake iya gani ta cikin kofar bakin kyallen Ba kowa bace wannan budurwa ba face gimbiya walisa A tarihin rayuwarsa ba'a taba kaishi kasa ba afilin daga Amma sai gashi yau an sami budurwa mace wacce ta iya yi masa dukan Da badon yayi da gaske ba sai ya fadi kasa Dalilinta kawai na shiga wannan gasa shine tana son ta gwada jarumtakarta akan ta sarki aryan Domin ta gani da idanunta tabbas sarki aryan ba kanwar lasa bane a fannin jarumtaka Nanfa aka tsaya ana kallon kallo atsakaninsu ya tambayi kansa Yace wannan wacce budurwace mai irin wannan karfin dukan Daga can sai duk su biyun suka kwarara uban ihu sannan suka falfalo da gudun gaske Kan juna suna masu kaiwa junansu mugayen hare hare cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta Wohoho hakika fadan manyan dawa daban yake dana kanana Ai kuwa suna fara fadan ne filin ya hargitse fiye da baya kai kace mutum dari ne suke kafsawa Karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne, idan makamansu suka hadu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi Kura kuwa ta turnuke tsakiyar filin tun ana iya hangosu har saida ya zama sun biya acikin kura sai kana da karfin ido sosai sannan zaka iya hangosu Wohoho! ! Hakika irin wannan fadan ake cewa turnuku fadan iblisai Sai gashi mutum biyu kacal sun debe gaba daya hankalin ýan kallo Da zarar daya daga cikinsu ya kaiwa wani hari idan ya kauce takobinsa ta sauka akasa saidai kaga ya haifar da wani wawan rami Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda iya yakinsu ya kusan zuwa daya tamkar a makaranta daya aka koyar dasu Shi kansa sarki aryan yayi matukar mamakin yadda akayi ya kasa samun galaba akanta farat daya Domin bai taba haduwa da mutum mai karfin damtsenta ba Haka itama abangarenta tayi matukar mamakin yadda karfin damtsensa da nata suka kusan zuwa daya Alhalin tunda take bata taba shafe dakiku sittin tana fada da wani ba ba tare da tayi nasara akansa ba face dan uwanta yarima walisu wanda yanzu take kan hanyar nemansa Kai wani lokacin ma sai kaga har tashi sama suke kamar tsuntsaye suna kaiwa junansu hari a sama Kai sai kayi zaton cewa mikiyoyi ne guda biyu suke fada Saida suka shafe sa'a biyu suna wannan fafatawar ba tareda dayansu ya sami nasara aka daya ba Bisa dole duk su biyun suka ja da baya suka tsaya suna kallon kallo kamar zakaru Sai a sannan ne sarki aryan yaji akaron farko na rayuwarsa ya hadu da macen data burgeshi Kuma yaji a yanzu babu abinda yake bukata face yaga fuskarta domin tun daga kallon yanayin dirin jikinta dolene ta kasance kyakykyawar budurwa ta gaban kwatance Dayin wannan tunani kawai sai ya kudurce a ransa cewa dolene sai ya san hanyar da yabi ya kwance bakin kyallen da bakuwar jarumar ta rufe fuskarta dashi don yaga wacece ita Koda gama yin wannan tunani sai duk su biyun kamar hadin baki sukayi kukan kura suka kara afkawa junansu da harin daya zarce irin farko Wannan karon sai duk su biyun suka sauya salon fadan da sukeyi suka fara hadawa da kai naushi gami da kutufo, hannu da kafa Kai kace dama can sun kasance abokan gaba sai gashi duk su biyun suna laftar jikin junansu shi kuwa sarki aryan a wannan lokaci burinsa kawai shine ya bude fuskar wannan bakuwar jaruma Koda suka sake shafe wasu dakiku masu yawa suna wannan fafatawar kuma gimbiya walisa taga ta kasa samun nasara akan sarki aryan Sai kawai ta fusata ta shureshi sama kamar wani dan yaro tayi wulli dashi Ai kuwa sai shima ya wulkila jikinsa kamar dan biri sannan ya diro kasa Sannan shima ya daka wani mahaukacin tsallen yayo kan jarumar da nufin yasa hannunsa ya cire kyallen data rufe fuskarta dashi kota halin kaka Cikin sauri gimbiya walisa ta sunkuya ya shuri iska sannan suka sake dawowa suka kara kachamewa da wani sabon fada Ai kuwa ana fara fadan ne aryan ya sammaci jarumar ya doki kafafunta da kafarsa guda don ta fadi kasa Aikuwa take ta sulale kasa zata fadi amma sai ta saka hannayenta ta tokare bata yarda itama taje kasa ba Kai tun suna iyayin fadan a tsaye saida ya kai sun kasa tsayawa Sai azaune suketa hadawa junansu jini da majina Suna cikin wannan fafatawar ne kwatsam sai dan kyallen da walisa ta rufe fuskarta dashi ya kwance ya fadi kasa Take anan gurin kowa ya gane ko wacece ita shi kuwa sarki aryan sai ya kame kamar wanda aka zare masa lakar jikinsa Ya tsaya kyam yana kallonta ko kifta idanu bayayi, domin ji yayi akaron farko ya hadu da budurwar da zuciyarsa ta kamu da soyayyarta take fuskarsa ta fadada da murmushi Ya manta da gurin da yake da kuma matsayinsa kawai sai ya dubeta yace Yake wannan jaruma tabbas kece gimbiya walisa ýa agurin mai girma sarki fadarul munnar Shin menene dalilin dayasa kika boye kanki agaremu ba tareda kin bayyana kanki ba domin mu hada taron yi miki barka da zuwa wannan birni namu mai albarka ? Kuma me yasa na ganki ke kadai a wannan lokaci ba tareda dan uwanki yarima walisu ba? Tabbas tun farkon fara fadana dake jikina ya bani cewa dole ina fada ne da gimbiya walisa Domin duk manyan jaruman da suke wannan nahiya dama wasu nahiyoyin inada hoton fuskasu a masarauta ta Da kuma salon yakin kowanne daga cikinsu, ni kaina na tabbata da ace mun cigaba da yaki dake nasan kece wacce zatayi nasara akaina Domin sadaukantaka da sa'a acikin jininku yake ke da dan uwanki yarima walisu Don yanzu hakama ýan kallo shaida ne kan cewa kece wacce tayi galaba akaina Domin kin yi mini kyawawan duka har guda biyu ni kuma nayi miki daya Saboda haka ayanzu ma kece kikayi nasara akaina kuma koda an ci gaba da fada yanzu tsakanina dake To na rantse harda karagar mulkina kece zakiyi nasara akaina Acan bangaren ýan kallo kuwa hankalinsu gaba daya ya tafi zuwa tsakiyar fili Suna ganin abinda yake faruwa tsakanin sarki aryan da gimbiya walisa Koda gimbiya walisa taji tambayoyin da sarki aryan yayi mata sai kawai tayi guntun murmushi wanda ya bayyana mata tsananin kyawunta Sannan tace Ya kai wannan adalin sarki ka sani cewa dalilin dayasa kaga ban sanar daku shigowata wannan birni ba shine Yanzu haka na baro gidane domin gudanar da wani uzurine wanda mahaifina ya saka ni Tambayar da kayi kuwa game da dan uwana yarima walisu shine Yanzu haka bana tare dashi kuma ban san inda yake ba Bayan haka ina neman afuwarka kan rashin shiga gasa da wuri da banyi ba nazo amakare Amma na biya alkalin gasa gaba daya kudin tikitin da kuke bukata Koda gama fadin haka sai kawai tayi girgiza ta zama wani farin hayaki sannan hayakin ya tashi sama cikin gajimare ya bace bat Shi kuma sarki aryan sai ya daga kansa yabi hayakin da kallo har saidaya bace masa bat da gani Koda mutanen da suke filin sukaga wannan al'amari daya faru sai gaba dayansu suka cika da tsananin mamaki kuma suka dada tabbatarwa cewa itadin shu'umar yarinya ce WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A FILIN GASA BAYAN GIMBIYA WALISA TA BAR FILIN GASA ***** ******* ******* ****** Acan kuwa al'amarin gimbiya walisa koda tabar filin gasar Bata baiyana ako'ina ba sai cikin gidan sarkin kasuwa yimana Ranta a matukar bace domin bataso fuskarta ta bayyana ga mutanen gari ba Ta gaba da gasar da takeyi domin ita kanta Jarumtakar sarki aryan ba karamin burgeta tayi b Da kuma irin salon kalaman daya dinga furta mata kawai sai ta tashi Ta tafi jikin madubi domin ta duba fuskarta, koda ta karasa gabansa sai taja da baya a tana mai zare takobin ta Ba komai ta gani ba face fuskar sarki aryan fuskarsa cike da murmushi Ya taho yana shirin rumgumeta akirjinsa sai daga baya ta fuskanci cewa idanunta ne suka nuna mata haka Koda ta fuskanci haka sai kawai tayi murmushi taje ta sami waje ta zauna Zamanta keda wuya sai tunanin dan uwanta yarima walisu ya kara fado mata aranta Da kuma irin kalaman da wannan saurayin yake fada mata amafarki Koda yin wannan dan tunani sai taji gaba daya hankalinta bai kwanta ba Taji kamar ta tashi ta fice daga cikin garin ta tafi nemansa Koda yin wannan tunanin sai kawai ta dauko madubin tsafinta ta shafeshi Aikuwa koda ta shafeshi saiga hoton ko'ina na cikin duniya ya bayyana ajikinsa Kuma gashi nan kowa yana gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali kamar yadda suka saba Amma duk da haka sai taji hankalinta bai kwanta ba da zaman garin dolene tayi kokari ta fice daga cikinsa cikin kankanin lokaci Kafin shirinta ya fara neman rushewa domin a yanzu ta fahimci akwai bakon al'amarin dayake shirin faruwa agareta Tana cikin wannan tunanin ne kawai sai taji an kwankwasa kofar dakin da take ciki Take tayiwa mai kwankwasawar izinin shigowa Ba kowa bane ba face sarkin kasuwa yimana ya bude kofar dakin ya shigo fuskarsa cike da alamun damuwa karara akanta Da shigowarsa sai ya sami waje kusa da ita ya zauna ya fuskanceta yadda suna iya kallon juna atsakaninsu Tsawon ýan dakiku babu wanda yacewa daya kala, Daga can sai yayi gyaran murya yace yake walisa tunda dai Yanzu an gama wannan gasar to ina mai baki shawara daki kama hanya ki tafi gabatar da aikin da yake gabanki Domin na fuskanci akwai alamun soyayyarki ta shiga zuciyar sarki aryan Nasan cewa sarki aryan bai isa ya tilasta miki akan ki soshi ba . Amma ita soyayya shegiyar abace domin tana da matukar hadari fiye da makami Akoda yaushe soyayya tana iya shiga zuciyar mutum kuma da zarar ta shiga Shikenan zata sa shi ya manta kansa da asalinsa daga karshe kuma tana iya sakashi ya rusa duk wasu burika nasa na rayuwa Idan har kinaso ki cika burinki da kuma burin mahaifinki dolene ki gaggauta barin wannan birni tun kafin sarki aryan ya gano cewa a gidana kike zaune yazo ya sameki da kansa ya bayyana miki sirrin zuciyarsa Kuma ayanzu zai iya haukacewa akanki har ya gwammace daya rasa komai nasa muddin zai sameki Tunda kema da kanki kinji labarin abindaya faru akansu SADAUKI HASSANUL BASARI DA KUMA GIMBIYA BAHJHAT Kodajin haka sai ta kara dubansa da sauri tace ai har yanzu ban karasa jin wannan daddadar hikayar ba Ina mai rokonka don darajar iyayenka daka karasa bani labarin wannan hikayar yanzu kafin na tafi na bar muku wannan birni in tafi aikin da yake gabana Dajin haka sai yimana ya gyada kansa kamar yanayin wani nazari daga can kuma sai yace ai shikenan sai mu karasa farfajiyar gidannan tunda anan na ajiye wannan kayataccen littafi Da gama fadin haka sai ya shige gaba ya fice daga dakin Sannan itama walisa tabishi. Abaya har suka isa farfajiyar Da zuwansu sai duk su biyun suka sami guri suka zauna Kawai sai yasa hannunsa ya janyo wannan littafin wanda HIKAYAR SADAUKI HASSANUL BASARI DA GIMBIYA BAHJHAT YAKE CIKI ya bude daidai shafin da suka tsaya ya fara karantashi a fili kamar haka ****- ****** ****** ****** Lokacin da boka sahibul ukub ya rikide ya koma siffar bakar guguwa Sai gaba daya fadar tasa ta dinga girgiza kamar zata tashi tabar kan doron kasa Take guguwar ta ratsa ta cikin saman rufin fadarsa fit ta fice Cikin abinda bai wuce kiftawar ido ba, sai gashi yana tsala azababben gudu a sararin samaniya kamar giftawar tauraruwa mai wutsiya Duk garin daya zo giftawa ta gabansa saidai kaga ana ruwan duwatsu a garin Halittun da suke rayuwa a yankin suna faduwa kasa matattu Hakika duk inda cikakken mara imani yakai to boka sahibul ukub ya wuce wannan matsayin Domin babu abinda yake sakashi farinciki dajin dadi sama da ya ga jini yana fantsama akasa, da kuma ganin ýan uwa suna kukan rabuwa da masoyansu Shi kuwa in banda kyalkyala dariya babu abinda yake domin shi burinsa kenan Yaga jini yana gudu akan kasa ,a haka cikin lokaci kankani ya isa birni shawana Alokacin sarki mayasin yana kan karagar mulkinsa yana gudanar da harkon mulkinsa ga fadawa nan da mutanen gari duk a zazzaune babu wanda yake da matsala Adaidai wannan lokacin ne boka sahibul ukub ya baiyana acikin birnin cikin sararin samaniya Da zuwansa sai gaba daya sararin samaniyar birnin harma da makotansu tayi duhu Kai sai kayi zaton tsakiyar dare ne, koda bayyanarsa sai kawai ya karanta wadansu dalasiman tsafi Faruwar hakan keda wuya saiga wasu irin manyan bakaken mikiyoyi suna saukowa daga sararin samaniya Kowanne daya daga cikinsu yakai girman bishiyar kuka Suna da baki mai tsawo da kuma tsini wanda idan suka caki abu dashi take yake hudashi koda kuwa dutsene Kafafunsu ma dogayene kamar na jimina sannan suna da farata masu matukar tsini Adadin wadannan mikiyoyi yakai kimanin dubu biyar Kuma dukkansu girman jikinsu daya babu wanda yafi wani daga cikinsu Ai kuwa koda gama bayyanarsu sai nantake boka sahibul ukub ya umarcesu dasu dasawa mutanen birnin shawana wawa Ai kuwa nantake mikiyoyin suka sauka kasa sukayi dirar mikiya acikin birnin Suka dinga fadawa kan mutane suna ragargaza naman jikinsu Babu ruwansu kai komai rashin imanin mutum dolene ya tausaya mutanen wannan birni Ganin yadda wadannan tsuntsaye suka dinga farka cikin mutane suna hadiye kayan cikinsu Da kuma soke idanunsu da tsinin hakoransu suna kwakule kwayar isonsu Su tauneta saidai kaga mutum babu kwayar idanu jini yana zuba daga kurmin idanun yana ta faman ihu Sannan wani mikiyar yazo ya karasa farke cikinsa ya kwakule kayan cikinsu Sannan su tashi sama Cikin kankanin lokaci birnin ya cika da iface ifacen mutane Kuma gawarwaki suka barbazu ako'ina na cikin babu kyan gani SHIN BOKA SAHIBUL UKUB ZAI SAMI NASARAR KASHE MUTANEN BIRNIN SHAWANA KUMA HAR YA DAUKE GIMBIYA BAHJHAT YA KAITA CAN FADARSA? TSAKANIN SARKI ARYAN DA GIMBIYA WALISA WANENE YA KAMU DA SOYAYYAR WANI? WANNE MATAKI SARKI MAYASIN ZAI DAUKA AKAN BAYYANAR BOKA SAHIBUL UKUB? DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT **************ZUBAR DA JINI ****************6 PART A *****************LBR HABIBULLAH KBR Ihu da iface ifacen mutane ya cika birnin yimana gaba daya Duk inda ka kalla babu abinda zaka gani face jinin mutane yana ta malala akasa Kamar an bude magudanar ruwa babu abinda zai baka tausayi Face ganin yadda za'a kashe da a gaban Mahaifinsa Ko kuma akashe uba agaban dansa, babbar matsalar wadannan mikiyoyi Itace Ko kadan makami baya tasiri ajikinsu kuma gasu da karfin tsiya Domin koda ace cikin gida mutum ya shiga don ya buyar musu Sai sun biyoshi ciki komai kwarin ginin gidan nasa kuwa Domin suna iya rusa gini duk kwarinsa kamar mutum ya sami biskit Shi kansa kukan wadannan mikiyoyi ya isa abin tsoro Domin shi kansa yana iya razana mutane mai jin fitsari yayi a wando. Ba tareda ya sani ba Ko mace mai ciki ta haife dan dake cikinta ba tareda lokacin haihuwarsa yayi ba Awannan lokaci sarki mayasin yana tsaka da fadanci sai kawai ji sukayi Saman rufin gidan sarautar ya fara girgiza yana zabtarowa kasa yana danne mutane Take itama fadar ta hargitse kowa ya fara neman gurin buya amma ina sun makara domin ko sun buyan ba zasu kubuta daga sharrin mikiyoyin ba Tunda suke basu taba ganin bala'i kwatankwacin wanda suke ciki yanzu ba Kafin suyi wani yunkuri tuni mikiyoyin sun yaye rufin fadar gaba dayansa Suka shigo ciki suka cin karensu babu babbaka nanfa gaba daya manyan gari suka cakude da talakawa har suna turereniya atsakaninsu don kawai su samu su tsira da rayuwarsu Kai koda sarki mayasin yaga irin barnar da wadannan sihirtattun halittun sukeyi masa sai ya kwarara uban ihu Sannan ya zare takobinsa ya tunkari wadannan mikiyoyi suka kachame da azababben yaki Wohoho ai kuwa koda ya shiga cikin wadannan mikiyoyin sai ya dinga kai musu mugayen hare hare Don ganin ya tarwatsa su da karfin tsiya amma abin da bai sani ba shine Su wadannan mikiyoyi ba irin wadanda ya saba gani bane Domin su an kirkiresu ne daga duwatsun wuta masu karfin gaske Don haka babu wani makami wanda zaiyi tasiri ajikinsu Koda ya shiga cikinsu sai kawai suka kachame da azababben yaki atsakaninsu Amma duk abinda yake takobinsa taki tayi tasiri ko kadan ajikinsu Kuma cikin kankanin lokaci ya gaji sakamakon yawan wadannan mikiyoyi Don haka sai ya fara neman hanyar da zai gudu ba shiri ya tarwatsa su da karfin tsiya Ya falfala da gudun gaske ya fito daga cikin gidan sarautar Ai kuwa da fitowarsa sai yaga birnin ya cika makil da gawarwakin mutanen kasarsa Babu ko mutum daya wanda yayi saura acikinsu sai shi kadai Koda ya daga kansa sama sai yaga ta cika makil da irin wadannan mikiyoyi Sai shawagi sukeyi kamar kudajen zuma Nantake ya tuna da batun ýarsa wacce yake matukar kaunarta aduniya wato gimbiya bahjaht Wacce ya wulakantata agaban talakawansa ya kaita gidan kurkuku ya kulle kawai saboda ta kamu da soyayyar SADAUKI HASSANUL BASARI Inda ace hassanul basari ya san irin danyen hukuncin daya yiwa masoyiyarsa gimbiya bahjaht ya tabbata sai ya dau mataki akansa Inda ace kuwa ya barshi tareda ita kuma ya jawoshi jikinsa Da ya tabbata shi kadai zai iya karesu daga sharrin wandannan mugayen halittu kamar yadda ta karesu daga sharrin wannan basamuden dodon Kodayin wannan tunani sai nantake yaji nadama tazo masa akaron farko na abindaya aikata Koda gama wannan tunani sai kawai ya yi kukan kura ya daina gudun ceton ransa domin ya tabbatar da cewa mutuwa zaiyi Ya tunkari wadannan mikiyoyin ya cigaba da kai musu sara da suka Ba karamin kokari sarki mayasin yayiba a wannan karon Amma kuma duk kokarin sai ya zama na banza domin ko guda daya daga cikinsu ya kasa kashewa kuma tuni sun fara ji masa ciwuka Ana cikin hakane wani katon mikiya ya taho ta bayansa Ya caka masa faratun kafarsa agadon bayansa suka fito da kirjinsa sannan yayi sama dashi Nantake sarki mayasin ya kwarara uban ihu saboda zafin fitar rai Kawai sai ya saki takobinsa ta fadi idanuwansa suka kakkafe ya zama gawa Ai kuwa take mikiyoyin suka dasa masa wawa kowa yana cirar abinda yake bukata Kafin kace kwabo sunyi masa filla filla ma'ana sun gama cinye naman jikinsa saura kashushuwa kadai ne suka rage Amma kowa na garin babu wanda bai mutuba, koda ganin irin mutuwar wulakancin da sarki mayasin yayi Sai boka sahibul ukub ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta amsa kuwa agaba daya ilahirin rusashshen birnin Kai hardama biranen da suke makobtaka dasu,kawai sai ya dauko mushen kan shaho ya kafe a tsakiyar garin sannan ya sake rikidewa ya kara komawa bakar guguwa Ya tafi can gidan kurkukun darul maut wadannan mikiyoyi suna biye dashi abaya Idan ka gansu sai kayi zaton dandazon kudajen zuma ne Cikin dakika guda suka isa kurkukun darul maut aikuwa Suna isa sai wadannan mikiyoyin suka saki fuka fukansu suka sauko kasa Awannan lokaci gimbiya bahjaht tana cikin dakin da aka daureta Shikuwa uzumnal yana can adaure dakaru sunata gana masa azaba Kwatsam adaidai wannan lokaci sai ji sukayi wani irin sautin kukan tsuntsaye mara dadin ji ya cika gidan kurkukun gaba dayansa Kafin su ankara tuni mikiyoyin sun tarwatsa rufin fadar sun faso cikinta Suna ta cinye komai da kowa dake cikii,nanfa itama wannan kurkuku ta hargitse ta cika da ihun mutane domin kowa ganin mutuws yake muraran agabansa Kafin cikar dakika hudu har sun gama cinye komai na kurkukun Abu biyune kadai basu taba wadannan abubuwa kuwa ba komai bane su ba face gimbiya bahjaht dakuma hadiminta uzumnal Aikuwa koda mutuwar kowa dake cikin kurkukun sai duk wadannan mikiyoyin suka bace bat kamar basu taba wanzuwa ba Kawai sai wata iska mai karfi tazo ta shuri su gimbiya bahjaht tayi sama dasu har zuwa inda boka sahibul ukub yake Da isarsu daidai inda yake sai ya tsaya ya kare musu kallo sama da kasa Sai ya bushe da dariya, wacce kararta ta zagaye nahiyar gaba daya sannan yace Nayi farincikin samunku araye domin yanzu daku zan tafi can fadata Har sai masoyinki hassanul basari ya kawo kansa sannan zan hadaku gaba daya nayi muku kisan gilla Dajin haka sai bahjaht ta dubeshi fuskarta a murtuke tace Karya kakeyi azzalumin banza ka sani inamai tabbar maka da cewa kai baka isa kayi galaba akan mu ba muddin kukayi ido hudu da kai da hassanul basari ina yi maka rantsuwa da ubangijinsa sai yayi nasara akanka Koda boka sahibul ukub yaji ta rantse da ubangijin da hassanul basari yake bautawa sai ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa sannan yace Lallai yarinya kin tafka babban kuskure da har kika yarda da ubangijin musulunci kuma har kike tunanin zai iya taimakon hassanul basari har ya sami galaba akaina Ina tabbatar miki da cewa inda ace gaba daya mutanen duniya dama na wasu duniyoyin zasu hadu domin yakata basu isa su sami nasara ba akaina ballantana kuma wani mutum guda daya wanda bashi da sihirin komai a tare dashi Amma nayi mamakin abinda shi hassanul basari yayi miki wanda yasa har kikayi saurin yarda dashi kika bijirewa mahaifinki Har kuma yasa ki kika fara yarda da ubangijinsa ,kike nema ki bijirewa addinin da kika gada ke da iyayenki na bautar gumaka Wanda duk duniya shine addinin gaskiya Kodajin wannan batu sai kawai sai tayi murmushi sannan tace Babu wani abu dayayi mini kawai dai ni da kaina naji na gamsu da addininsa fiye da wanda naga iyayena sunayi Domin da idona naga karfin ubangijinsa alokacin daya taimaki hassanul basari ya bashi karfin daya iya kashe masifar maridin daka aiko mana Tabbas yanzu na gane ko wanene kai, Kaine boka sahibul ukub wanda naji sunanka abakin maridin dodon daka turo domin ya baje birnin mu Ganin maridin naka ya kasa samun nasara ne akanmu yasa kayi tattaki da kanka kazo har birnin mu ka ruguzashi Shine yanzu kazo nan domin ka daukeni ka kaini can fadarka domin kayi garkuwa dani……. . Tun kafin ta karasa maganar da takeyi sai boka sahibul ukub ya daka mata tsawa Wacce tasa taji kamar zuciyarta zata faso kirjinta ta fito waje Kawai sai yace da'ita wannan kuskure nane da har na tsaya ina cacar baki dake Kinyi sa'a inada buri akanki amma badon haka ba da yanzu take zan hallaka ki dake da hadimin naki Yana gama fadin haka sai ya hura musu wata irin iska daga cikin bakinsa Take iskar ta Shiga cikin jikinsu gaba daya Sai gashi duk su biyun sun fara kankancewa suna zama kanana Kafin dakika biyu su cika har sun kankance sun zama kamar girman jinjirayen maguna Sannan ya dauko wata ýar karamar akwati duk su biyun ya zurasu aciki Sai gasu duk su biyun sun zauna acikinta kamar suna cikin daki ba tareda sun matsuba Sannan ya zura akwatin acikin aljihunsa, ya kara rikidewa zuwa siffar bakar guguwa Ya kama hanyar komawa fadarsa WANNAN SHINE ABIDAYA FARU ACIKIN BIRNIN SHAWANA BAYAN BOKA SAHIBUL UKUB YA SHIGA CIKINSA YA KASHE KOMAI DA KOMAI NA CIKIN SA SANNAN YA SACE GIMBIYA BAHJAHT DAGA GIDAN KURKUKU YA TAFI DA ITA CAN FADARSA WACCE TAFI KO'INA NA DUNIYA HATSARI 0======(::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Acan kuwa al'amarin jarumi hassanul basari tun daga ranar da suka gana da gimbiya bahjaht sanda ta kawo masa ziyara lokacin yana cikin daji Sai ya koma gida cikin farinciki da begen gimbiya bahjaht domin a wannan ne farkon fara yin soyayyarsa kuma sai tayi masa mugun kamu Ma'ana ta shiga zuciyarsa da karfi yaji ayanzu duk duniya babu abinda yake so kuma yake burin gani kamar gimbiya bahjaht Kai tsaye ya kama hanyar komawa gida yanata tunanin gimbiya bahjaht da kuma begenta acikin zuciyarsa Domin ko iskace tazo giftawa ta kunnensa babu abinda yakeji face sautin muryarta Hoton fuskarta suka dinga yi masa gizo akan idonsa Ahaka ya koma sansaninsu cikin

Chapter 10 of 17