Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai gashi suna kawo masa mugayen hare hare da makamansu ME ZAI FARU A WANNAN FAFATAWAR ? WANENE MAI NASARA A TSAKANINSU? INA LABARIN ALJANI KHADIMUL ISLAM? SHIN HASSANUL BASARI YANA SAMUN NASARAR DAUKE GIMBIYA BAHJAHT? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS***************ZUBAR DA JINI ****************8 PART C LBR **************** HABIBULLAH KBR Lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin hassanul hassanul basari da wadannan dakarun na boka sahibul ukub Sai suka kasance suna masu kai masa munanan hare hare ta kowanne sashi sama da kasa Shi kuwa ya wanzu shi kadai a tsakiyarsu yana mai karewa tareda mai da musu martani Nanfa ya zame musu kadangaren bakin tulu domin duk da wannnan yawa nasu sai ya zamo na banza domin sun kasa samun nasarar koda shafar fatar jikin Kuma babban abinda yake firgita wadannan dodannin shine Wannan hasken da yake fita daga jikin sandar tasa domin yasa ma basa iya ganin abinda yake gabansu Saboda haka nema yasa duk bangaren da hassanul basari yakai duka da tsini ko kaifin sandar dake hannunsa Duk wanda ya samu take zakaga ya kumbura sannan kuma yayi bindiga ya fashe Cikin kankanin lokaci ya gigita su ya zame musu kamar guguwar annoba Duk inda ya ratsa saidai kaga suna zubewa kasa kamar ana sassabe agona Jini kuwa ya dinga fallatsa sassan jiki suka dinga yawo a saman iska Ihun su da gurnaninsu ya cika filin gaba daya shi kansa boka sahibul ukub yayi matukar mamakin yadda hassanul basari yake da tsananin zafin nama juriya da bajinta kamar jikinsa bana jini da tsaka bane Ba komai ne ya bashi wannan karfin ba face addu'o'in da yake karantawa acikin zuciyarsa Cikin kankanin lokaci ya gama kashesu gaba ki dayansu guda daya baiyi saura ba acikinsu Ya zamana daga hassanul basari sai boka sahibul ukub a tsaye suna kallon juna Sahibul ukub har wani gyatsine yakeyi da fuska saboda matukar fusatar da yayi Cikin shammace sai kawai ya shammaci hassanul basari ya watso masa wata iriyar bakar wuta ta tsafi Cikin bakin zafin nama hassanul basari ya daka tsalle ya kaucewa wannan wutar Take kuwa wutar ta nutse acikin kasa wanda sanadin hakan saida ta haddasa katon rami a gurin tareda girgizar fadar gaba dayanta Kafin hassanul basari ya kara motsawa daga inda yake tuni ya bayyana a kusa dashi tareda kawo masa mahaukacin duka da wannnan sandar ta hannunsa Nantake shima ya sanya tasa sandar ya kare wannan dukan Sakamakon haduwar sandunan nasu ne ya haddasa wata irin tsawa da walkiya a agaba daya ilahirin gurin Saboda karfin dukan saida hassanul basari ya durkushe kasa bisa kafafunsa Shi kuwa sahibul ukub ji yayi gaba daya sandar tsafinsa ta dauki wani irin zafi sakamakon haduwa da sandar hassanul basari wanda a baya bai taba jin irin wannan sabon yanayi ba Don haka sai ya fahimci tabbas akwai wani babban al'amari akanta Koda gama yin wannan tunani sai nantake ya rintse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi Ai kuwa yana gamawa sai nan wata iriyar iska mai karfin tazo ta shuri hassanul basari tayi sama dashi ta dinga wujijjiga shi Kamar ba bil'adama cikin kankanin lokaci kuwa ya fara neman fita daga hayyacinsa Don haka baisan lokacin daya kwala kabbara da karfi ba Ai kuwa nantake sai wannan guguwar ta sakeshi Kai a wannan lokaci saida sahibul ukub yayi sihiri sama da kala dubu domin yaga ya hallaka shi amma abu ya gagara Don haka nantake yayi wani sihiri na karshe wanda yasa fadar gaba dayanta tayi duhu sosai yadda koda tafin hannunka ba zaka iya gani ba Ba komai ne yasaka shi aikata hakan ba face yasan cewa dolene bazai gudu yabar fadarsa ba saidai acikin biyu ayi daya Ko shi da hassanul basari wani ya kashe daya ko kuma dukkansu su biyun suyi ragas Ai kuwa koda duhun ya gama mamaye fadar sai duk su biyun suka afkawa junansu da mahaukatan hare hare masu matukar hatsari da barazana ga rayuwa Duk wannan abu da yake faruwa tsakaninsu gimbiya bahjaht da bawa zamnal suna can gefe daya a daure suna kallo Kuma boka sahibul ukub ne da kansa ya daure su ajikin wata dirkar gini tareda rufe musu bakunansu bayan ya dawo dasu ainihin suffarsu Acan kuwa al'amarin manyan gwarazan kuwa koda duhu Ya mamaye fadar sai suka afkawa junansu da gagarumin yaki Fiye da wanda sukayi da farko domin wannan shi ake cewa gumurzun sadaukai Karar haduwar makamansu ta cika dodon kunne duk wanda ya kaiwa wani farmaki idan ya kauce duk abinda da suka sama saidai kaga take sun dagargazashi Hakama idan ganuwar ginice komai girmanta saidai kaga sun raba ta biyu kamar an bara tuffa Wani irin tartsatsin wuta ya cika ilahirin gurin Tartsatsin wuta kuwa ya dinga fallatsa a ko'ina sanadin hakane yasa wuta ta dinga kamawa ako ina Kamar anayin gobara saiga karfi yana neman yazo daya Domin kowanne daga cikinsu yana matukar jin jiki shi kansa hassanul basari saida yayi mamakin irin karfin damtsen da sahibul ukub yake dashi Daga karshe saiya kaddara azuciyarsa cewa lallai wannan karfin damtsen ba nasa bane aikine duka na sihiri Abinda bai sani ba shine boka sahibul ukub ya dade yana baiwa kansa horon yaki mai tsanani saboda gudun zuwan irin wannan rana Kuma shima tun yana yaro karami allah yayi shi mai karfin gaske Domin tun kafin ya fara samun sihirin tsafi da karfin damtsensa yake zaluntar yara sa'anninsa kai har dama wadanda suka girmeshi kuma tun farkon fara wannan fafatawar tasu duk sihirin tsafinsa ya daina tasiri Wannan dalilin ne yasanya Hatta sarkokin daya daure su gimbiya bahjaht duka suka tsitstsinke Amma dukajsu sai suka buya suka ki yarda su fito suna kallon wannan bakin artabu Ba komai ne ya hanasu fitowa ba face ganin yadda manyan dirakun gini suke zubuwo kasa suna turmushe duk abinda yake gurin Wuta kuwa ta dinga ci a ko'ina acikin fadar kamar ana zuba mata makamashi Saida suka shafe sa'o' masu yawa suna wannan fafatawa ba tareda dayansu ya sami nasara akan wani Don haka sai sahibul ukub ya wullar da sandar dake hannunsa gefe daya Ya tsaya cak cikin nuna alamun yarda da kansa yace Ya kai wannan matashin saurayi kuma abokin gabata Na fuskanci cewa idan zamu shekara muna wannan fadan namu da makami babu wanda zai yi nasara akan wani Don haka nake ganin idan har ka yarda da kanka ka ajiye naka makamin kazo mu gwada ýar kashi Kodajin haka sai shima hassanul basari yayi murmushi sannan ya ajiye sandarsa agefe daya ya fuskanci sahibul ukub suka afkawa junansu da fada mai matukar muni A wannan lokaci sai fadan nasu ya banbanta fiye da farko Domin nan da nan suka fara hadawa junansu jini da majina saboda yadda suke kaiwa junansu Bugu da naushi, hannu da kafa Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda sahibul ukub yake iya shanye dukan da hassanul basari yake iya kai masa duk da cewa kuwa tsufa ya fara kamashi ,har ma yake iya maida martani Haka shima hassanul basarin yake iya shanye dukkan hare haren da sahibul ukub yake kai masa Suna cikin fadan ne kawai sai sahibul ukub ya shammace shi ya debo wani garin magani ya watsa masa a cikin idanunsa Nantake kuwa hassanul basari yaji wani irin zafi da zugi sun ratsa cikin idanun nasa da kwakwalwarsa Har ma yaji idanunsa gaba daya sun daina gani Koda ganin wannan gagarumar nasara daya samu sai ya bushe da wata iriyar mahaukaciyar dariya wacce ta amsa kuwa acikin fadar tasa gaba daya Sannan ya dubi hassanul basari yace lallai yaro kayi kuskuren. Kawo kanka ga halaka Kai in banda ma rashin basira irin taka tayaya zaka yarda makiyinka wanda kuke yakar juna dashi zai baka shawara kuma ka yarda To yanzun nan zan kashe ka kuma da zarar na kasheka dukkan sihirin tsafina zai dawo da dukkan abubuwan dana rasa sanadin ka bayan nan kuma na sa a dauki wannan sandar taka mai matukar sihiri irin naku ma'abota addinin musulunci a konata Bayan nan naje can sansaninku na kama gaba daya kabilar ku acikin dakiku nayi musu kisan wulakanci wanda ko a tarihi ba za'a dinga tunawa dasu ba Abu na karshe kuma da zan fada maka shine zan aure wacce kake burin aura wato gimbiya bahjaht Yana gama fadin haka sai ya tashi yana dingishi ya dauki sandarsa ta tsafi A wannan lokaci gaba daya hassanul basari baisan inda kansa yake ba saboda tsananin azabar da yake sha Take ya jefo wannan mashin da nufin yayiwa hassanul basari kisan farat daya dashi Idan ya mutu sai ya kafe gawarsa a saman fadar tasa Kwatsam ba zato ba tsammani kafin tsinin sandar ya sauka ajikin hassanul basari tuni gimbiya bahjaht ta fito daga inda take idanunta na zubar. Da kwalla ta taho cikin azababben gudu ta sha gaban hassanul basari Take tsinin sandar ya fasa kirjinta tareda zuciyarta ya faso ta gadon bayanta Nanfa ta kwallara uban ihu saboda tsananin zafi da zugin da taji sannan wani irin jiri ya debe ta ta sulale ta fadi Karar sautin ihun natane ya ratsa cikin kunnuwan hassanul basari ya gane cewa lallai wani abinne ya faru ga masoyiyarsa Ai kuwa nantake yaji duk wani zugi da yakeji ya fice da cikin idanunsa Bai san sanda ya daka tsalle ba daga inda yake shima ya shuri nasa sandar ya jefawa sahibul ukub shi Take sandar ta tafi ta fasa makogaron sahibul ukub ta faso ta wuyansa ya fadi kasa yana shure shure Cikin sauri hassanul basari ya taho kan gimbiya bahjaht wacce take kwance jini yana zuba daga kirjinsa Sannan shima uzumnal din ya taho kan gimbiya bahjaht yana zubar da kwalla domin irin wannan ranar yake jiye mata tsoro tun daga ranar data fada soyayya da hassanul basari Ya dauki kanta ya dora akan cinyarsa yadda suna iya kallon juna dukkan su hawaye na zuba daga idanunsu Yace da ita Me yasa zakiyi mini haka kinsan irin kuskuren da kika aikata kuwa ? ko kinsan cewa rayuwarki tafi tawa mahimmanci bai kamata ki sayar da rayuwarki saboda ni ba Dajin haka sai itama tasa hannunta ta goge hawayen da yake zuba akan fuskarsa tace Yakai masoyina duk wannan abu da nayi ba komai baneba akan abinda kayi Ka sani Cewa na zabi na mutu kai ka rayu domin kai kafi cancanta daka rayu Domin kaine ka fara sayar da rayuwarka domin ceton tawa rayuwar da kuma miliyoyin rayuka Idan har na kuskura ka mutu duk wahalar daka sha abaya ta tashi a banza domin sahibul ukub zai aureni ne kuma zai cigaba dw gudar da zaluncinsa adoron kasa Na sani kaine kadai zaka iya hanashi aiwtar da wannan mugun nufin nasa Idan har na kuskura ka mutu to tabbas nima zan biyo bayanka Kuma ina godiya agareka bisa wannan sadaukar da rayuwarka da kayi domin tawa Yanzu haka duk irin alkawarukan daka daukar mini tabbas na gani ka cika mini su har dama wadanda bakayi mini ba suma ka cika Don haka nima zan cika maka alkawarin dana daukar maka Ina rokonka daka gaggauta shigar dani wannan addini naka kafin ajalina ya riskeni Domin yanzu na gamsu cewa babu wani addini na gaskiya face addinin musulunci Koda jin haka sai nantake farin ciki ya lullube zuciyarsa Ba shiri ya karanta mata kalmar shahada itama ta maimaita Tana gama biyawa sai duk jikinta ya sandare idanunta suka kafe ta mutu Koda ganin wannan al'amari sai nantake ya fashe da kukan gaske Yana cikin kukan ne ya jiyo kakarin boka sahibul ukub acan gefe daya Ba shiri ya tashi ya koma inda yake ya daga hannunsa zai gabza masa naushi da nufin yayi masa fashin albasa Kawai sai yaga sahibul ukub din yayi masa murmushi sannan yace Ina tayaka murnar samun nasara akaina a wannan lokaci Amma ka sani kamar ka kashe macijine baka sare sare kansa ba Domin domin ruhina zai tafi can wata nahiyar ne, inda babu wanda ya sani Sai bayan shekaru daruruwa zan sake bayyana ajikin wani hamshakin sadaukin Da kuma dukkan karfina har ma nafi yanzu shara da bunkasa na sani cewa kai ba zaka kai wannan lokaci ba shi yasa nake baka labari Idan har ka isa kaima sai ka biyoni wannan lokacin domin ka hanani idan har ka iya biyoni wannan lokacin kuma ka kasheni to shikenan ba zan sake bayyana ba na mutu har abada Koda gama fadin haka sai nantake ya sandare kawai sai wani haske ya fito daga cikin jikinsa mai siffarsa ya tashi sama yana kyalkyala dariya Ya ratsa saman rufin fadar ya fice Hassanul basari na cikin kallon wannan hasken ne kawai sai yaji uzumnal yace Yakai wannan sadauki tabbas nima na gamsu cewa addinin ka shine gaskiya don haka ina rokonka nima ka shigar dani cikin addinin nan naka Koda jin haka sai nantake farin ciki ya lullube hassanul basari ba tareda bata lokaci ba ya biya masa kalmar shahada Ya maimaita sannan dukkansu suka fito daga cikin fadar boka sahibul ukub suka sauko daga kan tsaunin da fadar take kai Suka sami waje sukayi mata suttira suka bunneta tareda yi mata addu'o'i daga wannan guri ya nemi alfarma agurin uzumnal daya koma can farkon wannan daji ya hadu da aljani khadimul islam ya daukeshi ya kaishi can sansaninsu domin ya koyo ibada acan sannan ya sanar dasu cewa shi ba zai sami damar dawowa ba Anan suka rabu kowa ya kama hanyarsa daban ya tafi Hassanul ya koma can wani daji daban a tsakanin wasu kananun duwatsu Gurin ya kasance mai matukar ni'ima da dadin rayuwa yaci gaba da rayuwarsa akullum babu abinda yake face ibada da kuma begen masoyiyarsa gimbiya bahjaht har ya tsufa ajalinsa ya riskeshi bai yarda ya sake haduwa da wani bil'adama ko aljani ba Wannan dalilin ne yasa har yanzu ba sake ganinsa ba kuma ba'a sami labarin inda yake ba Babu yarda bokaye da sarakuna da masana tarihi basuyi ba domin ganin wannan guri ba amma sun kasa Haka shima boka sahibul ukub babu wanda yasan inda yake WANNAN SHINE KARSHEN HIKAYAR SADAUKI HASSANUL BASARI DA KUMA IRIN SOYAYYAR DA SUKAYI A ZAMANINSU YA LABARIN GIMBIYA WALISA DA DAN UWANTA WALISU? SHIN HASSANUL BASARI YANA SAKE BAYYANA A WANNAN ZAMANIN? WANENE SAURAYIN DA WALISA TA GANI ACIKIN BARCINTA ? KUMA YA SOYAYYARTA DA SARKI ARYAN ZATA KASANCE? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS*************ZUBAR DA JINI *******************9 PART A LBR HABIBULLAH KBR Koda sarkin kasuwa yimana yazo karshen HIKAYAR SADAUKI HASSANUL BASARI DA GIMBIYA BAHJAHT sai a sannan suka lura cewa har dare yayi kuma gari ya waye Saboda yadda suka dingajin sautin carar zakaru Don haka sai yimana ya dago da kansa suka hada idanu da gimbiya walisa sai yaga idanunta sun cika da kwalla Da alama ta jima tana kuka bai sani ba koda suka hada idanunsu Sai yace da ita yake ýata kinji yadda wannan hikaya take da kuma abubuwan al'ajabin data kunsa Tabbas soyayya abace mai dadi wacce take tafiya da kuma zautar da wadanda suka fada cikinta Kuma tafi komai samar da kwanciyar hankali a zukata Itace take iya maida mai ido ya zama makaho, mai kunne kuma ta mai dashi kurma ya dainajin komai sai zancen wanda yake so Mutum baya sanin farin ciki ko bakin ciki sai ya fada tarkon soyayya Amma kuma duk wannan dadin da take dashi sai ta zama hatsari mai girman gaske Ga duk wanda yake da burin zama wani hamshakin ko kuma yake bukatar cika wani buri nasa Takan iya saka mutum ya rasa duk dukiyarsa, daukakarsa, matsayinsa Irin haka ta faru akan mutane da dama kamar su sadauki hantaru da dai sauransu Idan har kinaso ki cika burin mahaifinki to dolene ki hakura da batun soyayya idan yaso daga baya idan bukatar ki ta biya sai ki fuskanci sabuwar rayuwar da take shirin tunkarar ki ta soyayya Ina fatan yanzu kin fahimci duk dalilan da suka saka nake shawartarki daki ajiye batun soyayya agefe daya Kodajin haka sai walisa tasa hannayenta ta goge hawayen dake zuba daga ciki Sannan tace Gaskiya tunda nake ban taba jin labarin soyayya wanda ya ratsa zuciyata kamar wannan hikayar ba Hakika yanzu na gamsu da duk sharwarin da kuma kokarin da kake na ganin ban fada tarkon soyayya ba Amma ina da wata tambaya kuma inaso ka bani amsa iya gaskiyarka kada kayi mini karya shin yanzu kai ka yarda da cewa addinin su hassanul basari shine addinin gaskiya ba wanda muke kai ba? Dajin wannan tambayar sai sarkin kasuwa yimana yayi shiru kamar ba zaice komai ba daga can kuma sai ya dago da kansa ya dubeta yace Tabbas kinyi tambaya mai girma wacce duk wanda ya fiya furtata to rayuwarsa zata shiga hatsari kuma dolene manyan sarakuna da matsafa su dinga farmakin rayuwarsa amma kuma ya zame mini dole na amsa miki ita Azahirin gaskiya duk kan wadannan addinan da muke kansu addinai ne na karya wadanda aka ginasu kan son zuciya, zalunci, kyamatar juna da kuma nuna banbanci tsakanin talaka, mai kudi da kuma talakawa Dukkan su wasu daga cikin tsageran aljanu ne suka kirkireshi domin su dinga bautar da mutane agaresu Wasu kuma sun riki wadannan addinaine domin su tara dukiya da bayi kota wacce irin hanya Atakai ce babu wani addinin gaskiya face addinin musulunci Domin shine addinin da a koda yaushe yake nuni da a aikata gaskiya sannan kuma abar barna da zalunci Duk wannan rashin kwanciyar hankali hankalin da ZUBAR DA JININ da akeyi duk anayinsane saka makon rashin riko da wannan addini Kodajin wannan bayani sai walisa ta girgiza kanta tana mai tunani akan abubuwan daya fada mata Daga can sai tace Ai kuwa indai hakane babu abinda ya fiye mana sauki a rayuwar mu face mu ajiye son zuciyar mu mu karbi wannan addini Amma inda matsalar take shine babu wanda yasan inda za'a sami mabiya wannan addini Don haka yanzu zan fice na bar wannan birnin naku na shiga cikin duniya na ci gaba da neman wannan dan uwa nawa Sannan kuma na hada da cigiyar ma'abota wannan addinin na musulunci Kodajin haka sai yimana ya ja da baya a firgice yace Me zakiyi a gurin wadannan mutane? Walisa tace Idan har na hadu dasu to nima zan karbi wannan addini nasu ne Dajin haka sai yimana yaja da baya a razane yace Ina mai shawartarki idan har kinaso ki cika burin ki da wuri da kada ki karbi wannan addini Ki bari harsai kin gama cika burin ki sannan ki karbi addinin musulunci Koda jin haka sai walisa ta kyalkyale da dariya sannan tace Lallai yanzu na fahimci cewar kaima kana daga cikin mutanen daka lissafa masu son zuciyar su Akan me kake tunanin zanki karbar gaskiya idan tazo mini? To ka sani ko yanzu nayi arba da ma'abota addinin musulunci saina karbeshi na ajiye addinin tsafin da na gada tun iyaye da kakanni Domin tun ina yara mahaifinmu abinda yake koya mana shine yaki da zalunci da kuma kafa gaskiya a duk gurin da babu ita don haka idan har kana ganin zaka iya hanani abinda naga dama to ina mai umartarka daka dauki makaman yakinka Amma bayan haka ina godiya agareka abisa bani gurin zama da kayi cikin amanarka Koda gama fadin haka sai walisa ta mike ta kama hanyar fita daga cikin Shi kuwa sai yabita da kallo ya rasa yadda zai yi ya hanata fita Koda fitowarta a wannan karon saitaki ta daura kyallen da take rufe fuskarta dashi Kawai ta kutsa kanta cikin ta nufi hanyar da zata fita daga cikin birnin gaba Duk inda ta ratsa saidai kaga mutane suna kallonta wasu suna barin ayyukansu suna komawa gefe suna tseguminta Domin sunyi matukar mamakin yadda ta iya karawa da sarkinsu ba tareda ya sami nasara akanta ba Ita kuwa sai tayi burus dasu har ta kusan zuwa bakin kofar garin sai kawai ta tuna cewa tunda ita kadaice ya kamata yanzu ta nemi wani abin hawan don rage tafiya Koda gama wannan tunani saita wuce kai tsaye zuwa kasuwa ta sayo wani farin ingarman doki kosashshe ta haye kansa ta sakar masa linzami ta nufi kofar fita daga birnin Tafiya ýar kadan tayi daga inda take sannan ta isa bakin kofar birnin Aikuwa tana zuwa ba tareda gardamar komaiba dakaru suka bude mata kofa ta fice daga birnin gaba daya ta nausa cikin ta ci gaba neman dan uwanta yarima walisu WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN GIMBIYA WALISA DA SARKIN KASUWA YIMANA ****** ********* ******** A can kuwa al'amarin yarima walisu tun lokacin da fafata yaki da ýar uwarsa wato gimbiya walisa kuma yayi mata alkawarin ba zai sake kai wani farmakin ba harsai lokacin data sami lafiya Sai ya koma can cikin kogon tsafinsa ya zauna yana ta tunani kala daban daban Acikin tunanin ne kawai sai ya tuna da tsohuwar rayuwarsa tabaya Wato shekaru dubunnai baya lokacin yana kan sharafin mulkinsa da zaluncinsa Har ya zamana ko sunansa aka ambata agurin mutane take suke rudewa har su saki futsari awando ba tareda sun sani ba Sannan ya tuna da batun masoyiyarsa wato gimbiya BAHJAHT wacce babu mace mai kyawunta duk duniya a wancan zamanin kuma shine ya kasheta da hannunsa Har zuwa abubuwan da suka faru tsakaninsa da SADAUKI HASSANUL BASARI Koda gama wannan tunani sai ya takarkare ya kwarara uban ihu Wanda sanadinsa har saida komai na cikin fadar ya dinga bindiga yana fashewa Har saida yayi shiru sannan komai ya koma kamar yadda yake abaya Har dama wadanda suka lalace sai suka hade suka koma kamar yadda suke Kawai sai ya fara zancen zuci yana cewa Duk yadda akayi wannan takadirin sadaukin ya dade da shekewa barzahu Don haka nima ya zame mini dole na binciko gawarsa na nemota a duk inda take Domin in zuba masa garin maganin da zan tashe shi kuma ya zama bawana Tahanyar yin hakan ne kadai zan huce bakin cikin rabani da tsohuwar rayuwata mai dadi da yayi Koda gama fadin haka sai ya karasa kan karagarsa ta tsafi wacce aka sana'anta ta da haske ya zauna akanta Take yayi nuni da hannunsa zuwa jikin bangon fadar tasa Nantake saiga taswirar ko ina na duniya ta bayyana ajikin bangon fadar Amma babu hoton inda gawar hassanul basari take Koda ganin haka sai ya kara tsananta binciken sa akan haka Kai sai da takai cewa ma maimakon hoton wani abu ya fito Sai bangon ya fara baki yana neman tsagewa yayi bindiga Bisa dole ya hakura da binciken ya yanke hukuncin ya tashi ya fita da kansa domin neman gawar hassanul basari basari da kansa ko ta halin kaka Koda gama fadin haka sai nantake ya sake mikewa tsaye Wasu irin manya manyan fuka fukai suka fito daga cikin jikinsa Kawai sai ya mike tsaye nantake ya kada fuka fukansa ya tashi sama Sai da yayi kololuwa acikin sarararin samaniya yadda hatta manyan duwarwatsu kananu yake kallonsu a kasan sa Kawai sai ya tsaya cak yana tunanin gurin daya kamata ya fara zuwa Sai daya dan debi ýan dakiku yana nazari kawai sai ya kada fuka fukansa ya nufi gabashin dajin Cikin tsala azababben gudu WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA WALISU BAYAN FAFATAWARSU DA WALISA ***** ****** ******** Al'amarin gimbiya walisa kuwa lokacin data shiga cikin daji akan ingarman dokinta Koda ta fita daga cikin birnin saita sakarwa dokin linzami Cikin tsala azababben gudu ta nausa cikin daji ba tare da sanin inda ta dosa ba Duk inda ta gifta saidai kaga kura tana tashi sakamakon kartar kasa da kofaton dokinta yake Kuma tana tafiyar ne tana karanta dalasiman tsafi na daure kasa domin gajarce doguwar tafiyar dake gabanta A haka ta dinga ratsawa ta cikin manyan dajijjika masu matukar hatsari kuma duk tana iya ketare su da karfin damtsenta dana sihirinta Saboda haka sai data shage kwanaki tana

Chapter 15 of 17