Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da shekawa barzahu, don haka lokaci yayi da nima zan saka muku akan abinda kukayi mini Dajin wannan batu sai ta gyada kai sannan ta kwashe labarin komai ta bayyana masa Dakuma taimakon da takeso yayi mata Kodajin wannan labari sai ya kame kam kamar gunki yana mai yin tunani acikin ransa Daga can kuma sai ya ajiye gwauron numfashi yace Lallai duniya abar tsoro ce, kuma ina matukar tausaya miki ke da mahaifinki Kuma nayi miki alkawarin zan baki mazaunin da zaki zauna har zuwa Sanda zaki bar wannan birni, sannan zan ruke miki wannan yaro amana, Yana gama fadin haka sai ya kwallawa wasu kuyanginsa kira Take kuwa sukazo gabansa suka russina ya dubesu yace Inaso ku raka wannan bakuwar tawa zuwa dakin saukar baki na musamman Sannan shi kuma wannan yaron ku kaishi can dakin da ýaýana suke kwana Domin shima yanzu ya zama dana babu banbanci atsakaninsa dasu Bayan haka inaso ku kai musu abinci mai kyau kuma isashshe Wanda zai ishesu gaba daya Kodajin wannan umarni sai dukkansu suka ce munji wannan umarni naka Take suka tashi sukayiwa su walisa jagora zuwa can dakunan da aka umarcesu dasu kaisu Bayan 'yan dakiku kadan aka kai kowa masukinsa Dakin da aka ajiye walisa Daki ne madaidai ci, wandake dauke da gado da dukkan kayan kawa acikinsa Sannan kuma agefensa akwai bandaki wanda mutum zai shiga domin biyan bukatarsa MAI ZAI FARU ACIKIN WANNAN BIRNI DA WALISA TA YADA ZANGO ACIKINSA SHIN ZATA SHIGA GASAR JARUMTAKAR DA ZA'A GUDA NAR ACIKIN BIRNIN KO KUMA BA ZATA SHIGA BA SHIN WAYE ZAI LASHE NASARAR WANNAN GASAR JARUMTAKAR TSAKANIN SARKI ARYAN DA KUMA JARUMAN GASAR? DON JIN AMSOSHIN WANNAN TAMBAYA SAI MU HADU A LITTAFI NA 3 DON JIN KARASHEN WANNAN LITTAFI DAGA NI HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT++++++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++3 PART A LBR ++++++++++++ HABIBULLAH KBR Atakaice dai wannan daki an kawatashi daidai na rayuwar ka wanda bazaka takura ba acikinsa Dukda dai bai kai dakinta ba, ba tareda bata lokaci ba Ta shiga cikin bandaki tayi wanka domin ta huce gajiyar da take jikinta Bayan ta fito ne taga tuni anzo an ajiyemata abinci mai mai da lafiya Ba tareda bata lokaci ba ta zauna ta fara cin abincin cikin kwanciyar hankali ba tareda fargabar komai ba Bata gama cin abincin ba taji ta fara jin barci sosai, don haka sai ta Kwanta akan gadon da yake dakin domin yin barci aikuwa Bata dade da kwanciya ba sai barci mai nauyi ya sace ta Acikin barcin ne tayi mafarki da wani matashin saurayi mai cikakkiyar kamala fuskarsa tana wani irin sheki da kyalkyaki kayan jikinsa kuwa duk farare ne Ya nufo inda take hannunsa ruke da wata farar sanda ajikinta anyi wani irin rubutu wanda bata iya gane abinda aka rubuta ajikinta domin wani irin yare ne na daban wanda batama san sunansa ba Kallo daya zakayi masa ka tabbatar da cewa gwarzon mayaki ne kuma namijin duniya A saman kansa kuwa wasu fareren balbelu ne suke binsa Duk inda yabi abin dai abin ban sha'awa, a hankali matashin saurayin yazo Inda take tare da yi mata murmushi Her ta bude baki zatayi magana sai taji yace da ita Yake gimbiya walisa ki sani aikin da kika daukowa kanki aikine mai matukar wahala Kuma acikin wannan birnin da kike zaki fuskanci wani babban kalubale Wanda har sai kinyi yaki da zuciyarki, sannan zaki sami nasarar abinda kika fito nema Amma ina mai shawartarki daki kara zage damtse akan aikin dake gabanki Ina tabbatar miki zaki sami nasara amma dolene sai kin cika wani sharadi Cikin mamaki walisa tace dashi wanne irin sharadi ne wannan? Saurayin yace Zan sanar dake wannan sharadin idan lokacin hakan yayi Amma yanzu zanyi miki taimako guda daya akan ciwon kunar da yake bayanki Take taga ya taho gurin da take sannan ya runtse idanunsa Tare dayin wani karatu sannan ya tofa mata agadon bayanta Yin hakan keda wuya sai ta sa hannunta agadon bayan nata Ko zataji wannan kunar amma bisa mamaki sai taji babu komai agadon bayanta ma'ana kunar wutar ta warke sumul Cikin mamaki ta juyo ta dubi wannan saurayin tace kai wanene Kuma me kake takama dashi? Tabbas wannan sihirin naka mai karfine Kodajin haka sai saurayin yayi murmushi wanda ya kara fito da tsantsar kyawunsa Yace mata ni bana tsafi kuma ban yarda dashi ba Dangane da sanin ko waneneni kuwa da kike son sani To nine……… Adaidai wannan lokacin ne taji ana hayaniyar mutane tana tashi a kasan tagar da take kusa da gadon da take kwance Hayaniyar ce ta zama silar farkawarta daga barcin da takeyi ba tare da taji sunan saurayinba Tana farkawa daga barcin cikin sauri ta sanya hannunta ta shafo inda ciwon yake Take kuwa taji gaba daya babu ciwon ajikinta amma duk da haka bata yarda ba Sai da taje jikin madubi kasancewar akwai hasken farin wata Ta duba bayan nata aikuwa saita cika da mamaki domin ko tabon kunar bata gani ba ajikinta Take ta cika da tsananin mamaki fiye da farko akan wannan al'amari Domin ki a tarihi bata taba jin labari kwatankwacin wannan ba Amma sai ta bar zancen a zuciyarta ta dawo bakin taga domin taga abinda yake faruwa acikin birnin Koda lekawarta sai tayi arba da jama'a suna gudanar da shirye shiryen wannan gasa kamar da rana Ba komai bane ya haddasa haka ba face acikin daren ne Sarki yasa akayi sanarwa cewa washe gari da safe za'a fara gudanar da wannan gasa Wannan shine dalilin dayasa kowa ya katse barcinsa suka cigaba da baiwa kansu horon yaki Saboda kawai kwadayin wannan dukiyar da zasu samu idan suka ci wannan gasar Koda ganin wannan al'amari dai kawai tayi tsaki tace Aikin banza yanzu kawai saboda dukiya suketa wahalar da kansu kan abinda basu da tabbacin samun nasara acikinsa Abinda ta manta shine babu wanda yake da tabbas akan abinda zai faru dashi arayuwarsa Kuma babu wanda yake da ikon canja kaddararsa, shiyasa ake cewa Mai rabon shan duka sai ya sha, kuma nasara tana tare da mai nema Haka dai walisa ta koma kan gadonta da nufin kwanciya barci Amma sai taji ta kasa, domin hoton fuskar wannan bakon jarumin ce kawai takeyi mata yawo akan idanunta Da kuma irin maganganun daya fada mata masu ratsa zuciya Take ta tambayi kanta shin me yake nufi da wadannan kalamai nasa? Kuma wanene shi Amsar data kasa baiwa kanta kenan, Don haka saita rusa uban ihu har tasa hannu ta naushi ginin da yake kusa da ita Saboda karfin naushin saida ginin ya huje hannunta ya fito waje ta baya Hakadai jaruma walisa ta cigaba da zama tanata tunani kan abubuwan da suka faru acikin barcinta Har safiya tayi Sannan ta tashi ta shiga bandaki ta sake sabon wanka Kafin ta fito daga wankan har anzo an ajiye mata abinci da abin sha, Ba tareda bata lokaci ba kuwa ta zauna taci abincin dan kadan Sannan taje ta dauki kayanta na yaki ta sanya ajikinta Ta fito falon gidan, tana fitowa sai tayi arba da sarkin kasuwa yimana Tareda yaro zaljus koda zaljus ta hango ta tana tahowa Sai shima ya taho da gudun gaske ya rungume ta suka jera tare suka sami kujeru suka zauna sannan suka gaggaisa Zamansu keda wuya sai yimana yace da ita, yake wannan jaruma Amma dai jiya da daddare kinji sanarwar cewa yaune za'a fara gudanar da gasar jarumta ko? Kodajin haka sai take ta tuna da abin daya faru acikin barcinta Don haka saita kwashe labarin komai ta fada masa sannan ta tambayeshi Ko ya san fassarar wannan mafarki nata Kodajin wannan labari sai kawai ya girgiza kansa yana dan tunani Daga can ya kalleta yace Yake wannan jaruma tabbas acikin acikin wannan mafarki naki akwai babban abin al'ajabi Domin bantaba ganin aikin da akayi a cikin mafarki ba kuma ya faru agaske ba sai wannan Don haka nake shawartarki daki yi taka tsantsan acikin wannan tafiyar taki kada ki yarda wani abu yazo ya rusa miki duk shirin da kika dade kina tanadi akansa Daga yau har zuwa sanda zaki kammala shi Saidai a yadda kika siffanta mini wannan jarumi inada kyakyawan zaton cewa Dolene shima ya kasance sadaukin gaske kuma gagara badau ko kuma ince dodon maza kamar dai yadda Iyayena suka taba bani labarin wani hamshakin sadauki kuma jarumin jarumai, ko kuma ince dashi dodon maza, wasu kuma suke yi masa kirari da fasa taro, abangaren talakawa kuwa suna yi masa lakabi ne da dodon azzalumai Sarakuna kuwa suna kiransa da murucin kan dutse wanda bai fito ba sai daya shirya Alokacin da sadauki hasanul basari yake raye yayi jarumtakar da har duniya ta nade baza'a taba mantawa dashi ba Domin saidaya rikirkita gabaki daya azzaluman sarakuna da bokaye na zamaninsa Dajin wadannan kalamai sai walisa ta dubi yimana tace Dama kasan tarihin wannan gwarzon mayakin. Naji sunansa abakin iyayena alokacin da zan rabu dasu naji har suna cewa shine Sadaukin mayakin daya kashe boka sahibul ukub a wancan zamanin Lokacin da sahibul ukub ya addabi duniya da bakin zalunsa Kuma naji ance tsafi baya tasiri ajikinsa kuma duk abindaya sanya agabansa Sai yayi nasara acikinsa wannan dalili ne yasa har ya mutu Ba'a sami gawarsa ba, kuma babu irin binciken da matsafa basuyi ba Domin su gano inda gawarsa ta boye da kuma tarihinsa Amma abu ya gagara domin da suka matsa ayin binciken sai da madubin tsafin nasu Suka dinga fashewa ,bisa dole suka hakura, Amma kai kuwa ya akayi kasan tarihin jarumtarsa? Dajin wannan tambaya sai yimana yayi murmushi sannan yace Kadafa ki manta ni asalin bafatake ne, kuma na gaji wannan sana'ane agurin mahaifina Tun ina yaro, a wannan lokacin ne wata rana mun tafi yawon fatauci mukazo giftawa ta birnin misra Bayan mun shiga cikin birnin ne muka kama shago acikin kasuwa Muka baza hajar mu, muna cin kasuwa, kawai sai muka hango wadansu matasan yara guda biyu 'Yan kimanin shekaru 15 dauke da wata akwati sun gifta ta inda muke Har sun wuce sai kuma suka dawo babban ya dubi mahaifina yace masa Kaine shugaban wannan tawaga, sai mahaifina ya amsa masa da eh Sai kawai yaron ya miko masa wannan akwatin yace da mahaifina Mahaifin mu ne ya rasu kuma days mutu bai bar mana gadon komai ba sai na wannan akwatin Yace damu mu sayar dashi ga mutumin kirki, wanda zai saye shi ba tareda ya zalunce mu, Kuma yace kudin wannan akwatin zai isheni rayuwa dani da ýar uwata Koda jin haka sai mahaifina ya mika hannu ya karbi akwatin Sannan ya budeta Koda ganin abindaya ke ciki sai mutane suka fara yiwa matasan dariya Sai da mahaifina ya daka musu tsawa sannan suka daina Kawai sai ya zura hannunsa ya dauko wannan littafin Koda daukoshi sai ya kame kyam atsaye sakamakon ganin rubutun da akayi ajikinsa Ba komai aka rubuta ba face HIKAYAR SADAUKI HASANUL BASARI anyi rubutun ne da bakin alakalami, cikin tsananin mamaki Mahaifina yace dasu shin wanene mahaifin naku? Wanda ya iya rubuta wannan babban tarihi haka? Dajin wannan tambaya sai macen tace mahaifin mu shine Habibullah kbr, bai kasance komai a wannan garinba face talaka Wannan shine dalilin dayasa ya bata rayuwarsa wajen binciko tarihin wannan namijin duniya ya rubuta kuma yanzu haka shi kadaine yake da wannan kundun tarihi kuma yayi mana alkawarin Indai muka sayar da shi zamu sami abinda zai ishemu gudanar da rayuwarmu Kodajin haka sai nan take mahaifina ya kirgo dinare masu yawan gaske ya mika musu Suka karba suna murna, amma mai makon mahaifina ya sayar da wannan littafi don ya sami riba sai yaki Kawai sai ya ajiye shi a cikin dakinsa yake zama kullum yana karanta shi don ya debe masa kewa Saboda labarin Ni kaina nayi matukar mamakin dalilin daya hanashi sayar da wannan littafi akwai tsantsar abin al'ajabi da jarumtaka gami da soyayya acikinsa Kuma har sanda ya mutu bai daina karanta littafinba aduk sanda yake bukatar debe kewa Bayan ya mutu ne nima na gaji wannan littafi Kuma nima na zauna na karantashi daga farko har karshe Sai a sannan ne nasan dalilin daya hanashi sayar da littafin koda jin wannan labari sai tace dashi Yakai yimana ina neman alfarmar idan kana da lokaci ka bani tarihin wannan sadaukin duniya idan bazaka damuba Dajin haka sai yayi dariya sannan yace Ai wannan labarine mai matukar yawa da kuma dadin gaske Amma zanyi kokari na takaice miki wannan labari kafin lokacin fara gasa yayi idan kuma har lokaci yayi to zamu tsayar da wannan labarin mu tafi kallon wannan gasar jarumta domin bazan iya hakura da kallon wannan gumurzun mazan ba Yana gama fadin haka sai yayi gyaran murya sannan ya fara labari kamar haka 0=======(::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::> A wani zamani can baya mai tsawo daya shude acan nahiyar larabawa Anyi wata babbar kasa mai suna fasawana, birnin fasawana ya kunshi manyan birane wadanda suke karkashinsa Sarkin da yake mulkin wannan babban birni adalin gaskene ana kiransa da suna mayasin kuma sadauki uban sadaukai Sarki mayasin yana da ýa guda daya wacce ta kasance kyakkyawar gaske Da duk nahiyar babu mai kyawunta, wasuma suna hasashen cewa Ba mutum bace ba ita, wasu kuma suna cewa wai ýar abin bautarsu ce Shiyasa ya halicceta da kyawun dayafi na dukkan matan wannan karni Ana kiranta da suna gimbiya bahjaht, ko kadan gimbiya bahjaht bata kasance jaruma ba sabanin mahaifinta Amma duk da haka mahaifinta yana matukar kaunarta fiye da yadda yake kaunar kansa Hatta bacci baya iyawa sai yaje cikin turakarta ya tabbatar da lafiyarta kalau Ýa ýan sarakuna da dama sun nemi aurenta amma taki yarda Tace ita har yanzu bataga saurayin daya burgeta ba Domin Ita da kanta takeso ta zabarwa kanta wanda zata aura Duk da kasancewar birnin fasawana ta kasance babbar kasa ce kuma ta kunshi kabilu daban daban ,da addinai kala daban daban Sarki mayasin bai hana kowa gudanar da addininsa ba Saidai acikin biranen da suke karkashinsa akwai wani dan karamin kauye wanda adadin mutanen cikinsa basu wuce mutum dari uku ba Gaba daya mutanen kauyen mafarauta mazansu da matansu wadanda Suka dogara da sana'ar farauta, ana kiran jama'ar wannan kauye da suna banu sudais Kuma suna kan bin turbar addinin musulunci ne Asalin wannan kabila sun kasance basu da tsayayyen gurin zama Domin suna yawone acikin dajijjika duk inda suka tarar zaiyi dadin rayuwa sai su yada zango acikinsa na tsawon kwanaki sannan su tashi su kara gaba Duk sanda sukazo giftawa ta wani babban birnin sai su wakilta shugabansu Wani dattijo mai suna maharaz akan ya shiga cikin garin ya sayar musu da fatun dabbobin da suka tara saboda kowa ya yarda da amanar sa Maharaz ya kasance yana da da guda daya wanda ya kasance kyakkyawan da babu irinsa aduk fadin nahiyar kuma sadaukin gaske Domin tun yana dan shekara shida idan ya fita farauta baya taba dawowa sai ya kamo manyan dabbobin daji irinsu zakuna da dai sauransu kamar guda goma acikin sa'a guda Idan kuwa ya fara zabga gudu baya taba gajiya har tsawon makonni biyar Karfin gudunsa kuwa idan yanayi kamar na giftawar tauraruwa mai wutsiya haka yake yinsa Idan ya saka hannunsa ya naushi dutse dashi saidai kaga dutsen ya dagargaje Ba tareda shi hannunsa yayi koda kwarzane ba, idan kuwa yana gudu acikin daji mai yawan bishiyoyi saidai kaga yana tsalle. Asamansu kamar wani dan buri Idan kuwa yayi nutso akasan teku sai ya yini aciki yana iyo ba tareda ya dago kaiba koda sau daya Kai saboma da wannan baiwa tasa wasu cewa sukeyi shi ba mutum bane aljani ne shi, domin tun yana shiga cikin daji farauta sai suma dabbobin suka firgita da lamarinsa Ya zamana cewa da zarar sun hangoshi daga nesa ya nufo cikin dajin Sai nantake kaga sun fara gudun ceton ransu domin suma sun gama firgita da lamarinsa Bama su kadaiba hatta manyan 'yan fashi da suke suke tare dajijjika Sun san labarinsa Duk wadannan abubuwa suna faruwa ne tun yana karamin yaro Lokacin daya cika shekaru ashirin kuwa sai kyawunsa da jarumtakar sa suka ninku fiye da da kuma acikin wannan shekarun ne Mahafinsa maharaz ya mutu lokacin daya mutu mutane sunyi matukar bakin ciki musamman ma shi hasanul basari Domin tun tasowarsa mahaifinsa kadai ya sani domin mahaifiyarsa ma ta mutu tun lokacin data haifeshi Bayan rasuwar maharaz ne sai aka nada shi amatsayin shugaban wannan kabila, aka dora masa duk alhakin kula da kowa A rayuwarsa gaba daya baisan wata aba wai ita soyayya ba Domin labarinta kadai yakeji abakin mutane Kuma 'yan mata da dama sun nemi da yayi soyayya dasu amma bai taba yarda da bukatunsu ba Ana cikin hakane wata rana bayan kabilar su sun tara fatun dabbobin daji masu yawan gaske Suka wakiltashi kan ya tashi ya shiga cikin babban birninku wato birnin fasawana don ya sayar musu dasu SHIN JARUMI HASANUL BASARI ZAI SHIGA BIRNIN SHAWANA? SHIN WANENE HASANUL BASARI? YAYA MAGANAR GASAR JARUMTAR DA ZA'A GABATAR A BIRNIN FASAWANA ? DON SANIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN++++++++++++++++ZUBAR DA JINI ++++++++3 PART B LBR +++++++++++++++HABIBULLAH KBR Take kuwa jarumi hassanul basari ya karbi wannan fatun dabbobin ya kama hanyar sa abinsa Abinka da wanda ya kasance mai kuzari, cikin azababben gudu Yake tafiya saboda burin yaje birnin shawana ya dawo da wuri Cikin lokaci kankani ya isa birnin shawana, ka sancewar kowanne daga cikin su yasan wanene shi hakane yasa basu tsaya tuhumarsa ba suka bude masa kofa ya shiga Da shigar sa cikin birnin kai tsaye sai ya nufi hanyar da zata kaishi kasuwa Kasancewar da yawa daga cikin mutanen birnin masu shiga daji farauta duk sun sanshi, kai hardama wadanda basa shiga labarin jarumtakarsa yaje musu harma an sami wasu kwararrun masu zane suna zana taswirar fuskarsa suna sayarwa a cikin kasuwar garin Aikuwa da shigowarsa cikin birnin sai mutane maza da mata suka dinga fitowa sunata rububin ganinsa Wasu tsananin kyawunsa ne da sukaji ana fada ne yake burgesu Wasu kuma sadaukantakarsa da kuma baiwar da yake da itace take basu sha'awa Kai idan kaga yadda suketa rububin kallonsa awannan lokaci saika dauka cewa dan sarauta ne shi, Shi kansa saidaya tambayi kansa yace Wai menene yasa mutane suketa faman kallona ne kamar basu taba ganin mutum ba Ko kuma kayan da suke jikinane basuyi mini kyau ba? Wata zuciyar kuma tace dashi kai wata kila kuma soyayya ce tasa suke yi maka haka Dayin wannan tunani sai yace godiya ta tabbata ga ubangijin daya bani irin wannan farin jinin . ++++++++++++++++++++++ Acan cikin gidan sarautar shawana kuwa yau gimbiya bahjaht ta tashi cikin tsananin nishadi, da kuma son fita rangadi domin ta zagaya kasuwar garin nasu da kafafunta domin dama ta saba a duk rana irin wannan takan debi dakaru da fita rangadi cikin birnin Saboda tana matukar jin dadi taganta acikin mutane kowa yanata rububin kallonta kamar zai cinyeta, ta zama tauraruwa guda daya tak acikin dubunnan mutane don haka sai taji girmankai ya shigeta Don kowa daina kasuwancinsa yakeyi ya taho hanyar da take wucewa domin yaga tsananin kyawunta Kai wasu ma daga wasu garuruwan suke tahowa saboda yadda labarin kyawunta ya zaga ko'ina acikin nahiyar Tun da duku dukun safiya ta tashi ta caba kwalliya wata kuyanga tazo ta caba mata kwalliya ta gaban kwatance domin ta dada daukar hankalin mutane Sannan kuyanginta guda goma suka kawo mata kwanikan abinci kala daban daban Suka ajiye mata suka fita, fitarsu keda wuya sai wasu kuyangin suma guda goma suka shigo da abubuwan sha kala daban daban sannan suma suka fice daga cikin turakar tata, Fitarsu keda wuya gimbiya bahjaht ta zauna akan teburan abincin taci dan kadan domin bata fiye cin abinci da yawa ba Wannan ne dalilin dayasa koda yaushe cikin ta yake sumul kamar bata cin abinci Tana gama cin abincin ta tashi ta kara zuwa gaban madubi Ta tabbatar da cewa kwalliyar tata tayi kyau kuma zata dauki hankalin mutane acikin birnin Sannan ta kamo hanya ta daga cikin turakar tata ta nufi hanyar da zata kaita turakar mahaifinta Duk inda tazo giftawa acikin gidan sarautar saidai kaga dakaru suna zubewa har kasa suna gaishe ta Ahankali har ta isa cikin turakar mahaifinta Da zuwa saita iskeshi zaune akan kujera ya zauna jikinsa gaba daya yayi sanyi da alamun damuwa karara akan fuskarsa Cikin fara'a ta karasa gareshi cikin gudu ta fada kansa Sannan tace dashi ya abbana shin menene dalilin dayasa naga fuskarka cike da damuwa awannan rana ? Dajin wannan tambaya sai sarki mayasin ya dubeta yace Yake ýata tunda kiyi sani cewa zuciyata gaba daya bata amince da wannan rangadi da zaki fita ba, domin inaji ajikina cewa akwai wani abu da zai faru dake acikin wannan rangadin Ina mai baki shawara da kar ki fita wannan rangadi ki jira sati mai zuwa sai ki fita Dajin wannan batu sai jikinta yayi sanyi amma sai ta dubeshi tace Ya abbana hakika kamar yadda kake jin wani abu zai sameni to tabbas hakane Ammani abinda jikina yake bani zai faru dani a wannan rangadi na alheri ne Wanda zai sa zuciyata ta kwanta kuma nutsuwa ta sameni har abada Ina mai rokonka da kada ka hanani fita wannan rangadi Dajin haka sai shima jikinsa yayi sanyi domin bayason Ya hanata abinda duk tayi niya, don haka sai yace To shikenan na amince amma zan hadaki da dakaru masu yawa Wadanda zasu rakaki wannan rangadi don su tabbatar da tsaron lafiyarki Take sarki ya kira sarkin yakinsa mai suna ukairu ya umarceshi daya debi dakaru masu yawa su rakata wannan rangadi Take kuwa ya cika umarni bayan fitarsa da ýan dakiku sai gimbiya bahjaht ta tashi Ta bishi abaya Fitarta keda wuya sai ta riski dakaru sunyi sahu sahu suna Jiran isowarta, don haka bata bata lokaci ba ya shige gabansu ta tsaya Sannan wasu kuyangi kimanin su dari suka tsaya abayanta Suka ruke doguwar rigarta wacce take jan kasa da hannayensu Wasu kuma suka ruke mata lema saboda kare mata zafin rana Sannan suka dunguma suka shiga cikin gari kamar yadda ta saba Koda sukayi tafiyar ýan dakiku saita cika da mamaki domin gani tayi a wannan rana ba'a cikaba wajen kallonta kamar yadda aka saba Duk da cewa kuwa akwai mutane da yawa wadanda suka tsaya kallonta, wadanda suka hada maza da mata ,yara da manya, Amma kuma ba'a cikaba kamar yadda aka saba ba, domin a saninta duk sanda ta fito wannan rangadi wasu mutanen ma basa samun gurin tsayawa Don haka saidai su hau kan katangu su tsaya kamar ana gabatar da wani gagarumin bikin shekara Kodayin wannan nazari sai taji zuciyarta ta buga da karfin gaske Tace a ranta anya kuwa ba maganar mahaifina bace take shirin faruwa ba? Domin naga gaba daya al'amura sun sauya ba kamar yadda nasansu abaya sukeba amma sai wata zuciyar tace da ita A'a bahjaht kada ki karaya kawai ki ci gaba da tafiya tunda dai akwai sauran tafiya agabanki kafin ki isa kasuwa wata kila kowa yana kasuwar yana jiranki Da gama wannan tunani saita sami kwarin gwuiwa Adaidai wannan lokacin ne taga mutane suna dawowa daga hanyar kasuwa Don haka sai tasa aka kira mata wata budurwa daga cikinsu Take kuwa wani badakare yaje ya zo mata da wannan budurwa Gimbiya bahjaht ta tambayeta shin menene yake faruwa acikin kasuwar birnin? Take kuwa kuyangar ta kwashe labarin komai ta fada mata cewa Ai wani bakon jarumi ne ya shigo birnin wanda labarin tsantsar jarumtakarsa Da kyawunsa suka cika nahiyar gaba daya shine ya shigo birnin Mutane suke rububin kallonsa don su ganewa idanunsu Kodajin wannan labari sai zuciyar ta ta buga da karfi take ta sallami wannan budurwa Sannan taji wani irin kishi ya kamata, tace aranta wai jarumin da take jin labarinsa Abakin kuyanginta shine ya shigo har cikin birnin mu ya kwashe mini gaba daya mutane na, Ya zama dole naje gurinsa na hanashi shigowa cikin wannan birnin aduk irin

Chapter 5 of 17