Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafiya sannan ta iso wani daji wanda dagashi an fita daga yankin nahiyarsu an shiga wata nahiyar daban Tunda ya doshi wannan dajin sai tasha jinin jikinta cewa dole ba za'a rasa wasu mugayen halittu ba acikinsa Saboda irin manyan tsaunika d kuma bishiyoyi masu matukar tsawo da fadin ganyaye data dinga gani acikinsa Koda shigowarta cikin wannan dajin saita ja linzamin dokinta ta rage masa karfin gudu Ta fara tafiya ahankali acikinsa kamar tana yin sanda kuma ta zare takobinta daga cikin kubenta ta rikita ahannunta na dama tana mai kallon ko wane sashi na cikin dajin hagunta da damarta don tabbatar da tsaro ba komai ne ya janyo hakanba face ji da tayi a jikinta cewa tabbas akwai abubuwa masu hatsari acikin wannan dajin kuma koda yaushe zasu iya kawo mata farmaki Kuma wani abu daya bata mamaki shine kasan dajin gaba daya cike yake da busassun ganyaye babu danye ko daya Yadda da zarar ka taka su zasu dinga bada wani sauti ta yadda zai fargar da halittun cikinsa don haka sai tayi amfani da karfin sihirin tsafinta wajen hana wadannan ganyayen fitar da sauti Ai kuwa koda ta shafe dakiku dari da goma sai kawai taji wani irin sautin kuka yana.saukowa daga saman kanta Cikin sauri ta daga kanta sama domin ganin menene yake saukowa Kwatsam sai tayi arba da wasu irin manya manyan kunami masu fuka fukai suna saukowa daga saman wadannan bishiyoyi da kuma duwatsun Kowacce daya daga cikin kunaman takai girman rikakken kare Sannan adadinsu sunfi dubu da doriya sautin kukansu kadai ya isa ya zautar da mutum Su dai wandannan kunami sun fi shekara dari takwas a wannan dajin Kuma rana guda suka bayyana acikinsa babu wani wanda yasan makasudin bayyanarsu da kuma inda suka baro suka taho wannan dajin Aranar da suka bayyana ne suka dinga kashe duk wasu halittu dake cikin dajin Haka kuma suka hana mafarauta shiga cikin wannan da kuma fatake masu wucewa Domin duk wanda ya shiga cikin wannan dajin baya taba fitowa araye Matsafa da jarumai marasa adadi sun sha yin gangami su shiga wannan dajin don su yaki wadannan kunami amma ko daya daga cikin su bai taba dawowa a raye ba Bisa dole suka hakura suka daina ratsawa ta cikin dajin saboda kar su rasa rayukansu Don haka suka dinga yiwa dajin lakabi da suna iyakar halaka SHINE ABINDAYA FARU GA JARUMA WALISA BAYAN TA SHIGA CIKIN DAJIN IYAKAR HALAKA ******* ******** ******* Acan birnin shawana kuwa tun daga lokacin da sarki aryan yaje gidan sarkin kasuwa yimana sukayi gaisawar sirri da gimbiya walisa inda ya bayyana mata soyayyarsa agareta Ita kuma kuma tace dashi dole tana bukatar tayi nazari akan bukatar sa bayan ya koma gida Sai ya kasa zaune ko tsaye har dare ya raba babu abinda yakeyi acikin gidan face sintiri su kansu dakaru sunyi mamakin abinda yasa sarki aryan yake sintiri acikin gidan sarautar alhalin kowa yasan cewa tun farkon dare sarki aryan yake kwanciya bar ci kuma idan ya kwanta baya tashi sai hasken rana ya fito To a wannan ranar gaba daya sai ya kasa samun damar kwanciya barcin Ba komai ya janyo haka ba face fargaba da tsoron kar gimbiya walisa taki karbar soyyayyarsa Da wannan tunanin ya kwana acikin zuciyar sa, ba tareda ya koda runtsa idonsa da niyyar yin barci ba Don haka koda safiya tayi sai ya yanke hukuncin ya koma gidan yimana domin ya kara tattaunawa da ita Aikuwa ba tareda bata lokaci ba don ko abinci bai tsaya yaci ba Ya fice daga gidan sarautar kallo daya zakayi masa ka gane cewa baiyi barci ba daren jiya Cikin sauri ya nufi gidan yimana ba tareda yayarda wani daga cikin dakarunsa ya rakashi ba Koda isarsa kofar gidan sai ya iske dakaru a tsaitsaye suna gadin gidan amma koda sukayi arba da sarki aryan sai dukkansu suka rissina agareshi Sannan suka bude masa kofar gidan da kansu ya shiga suka mayar da ita suka rufe Lokacin da sarki aryan ya shiga cikin gidan sai ya tarar da kofar arufe ta ciki don haka sai ya kai hannunsa ya kwankwasa kofar Ba'a jima ba sai ga yimana ya bude kofar gidan ya fito Koda yayi arba da sarki aryan sai fuskarsa ta fadada da murnushi yace Lale marhaban da sarki mai daraja ai sai ka shigo cikin gidan Take ya bada hanya sarki aryan ya shige sannan shima yabi bayansa Shigar su keda wuya sai sarki aryan ya sami kujera ya zauna sannan yace da yimana Ina jaruma walisa ta shigane inaso ka kirawo mini ita yanzu yanzu Dajin haka sai jikin yimana yayi sauri sannan yace ya shugabana kayi hakuri domin kuwa kunyi sabani da ita domin kuwa da safen nan ta fice daga cikin birnin nan ta tafi neman dan uwanta Yanzu ina mai tabbatar maka cewa ta fice daga cikin birnin nan Dajin haka sai sarki aryan ya kwarara uban ihu na bakin ciki baisan sanda ya doki teburin da yake gabansu da hannayensa ba Take kuwa teburin ya kakkarye ya zube kasa Kawai sai ce dashi ai kuwa nima ya zame mini dole in fita nemantada kaina . Dajin haka sai yimana yace ya shugabana karka aikata haka zaifi kyau ka zauna ka cigaba da kula da masarautarka Idan kuma ka tafi waye zai cigaba da kula da ita? Kodajin wannan tambayar sai aryan yayi murmushi yace kada ka damu zan bada ajiyar karagatane agurin wazirina Kuma ina da tabbacin ba zaici amanata ba saboda na jarraba shi ba adadi na yarda da karfin amanarsa Ni koda na zauna acikin birnin nan ba zan iya cigaba da mulki cikin kwanciyar hankali ba Koda gama fadin haka sai ya kama hanya ya fice daga cikin gidan yimana ya hau kan dokinsa Ya kama hanyar komawa gidan sarauta domin daukar makanan yakinsa da kuma guzuri SHIN SARKI ARYAN YANA HADUWA DA GIMBIYA WALISA? SHIN YARIMA WALISU ZAI SAMI INDA GAWAR HASSANUL BASARI TAKE HAR YA SAKE TASHINSA? TA YAYA WALISA ZATA KUBUTA DAGA SHARRIN WADANNAN MUGAYEN KUNAMAN? DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS***************ZUBAR DA JINI *************** 9 PART B LBR ***************HABIBULLAH KBR Lokacin da sarki aryan ya bar gidan sarkin kasuwa yimana ya kama hanyar sa ta tafiya gida Sai ya kama hanya yana mai tsala gudu akan dokinsa Don haka cikin kankanin lokaci ya isa gidan sarautar tasa Koda isarsa sai ya kira sarkin gida ya umarce daya kirawo masa dukkan ýan majalisunsa da gaggawa cikin girmamawa sarkin gida ya amasa da an gama ya shugabana Take ya kama hanya ya fice daga gidan sarautar cikin sauri Shikuwa sarki aryan sai ya shige cikin gidan ya kama hanyar komawa cikin turakarsa duk inda ya gifta saidai kaga dakaru da hadimai suna ta rissinawa suna gaishe shi Har ya isa cikin turakar tasa. koda isarsa cikin turakar sai ya shiga kewaye yayi wanka sannan ya fito ya tarar tuni hadimai sun ajiye masa abinci da abin sha akan teburinsa Ai kuwa ba tareda bata lokaci ba ya zauna yaci abincin Sannan ya shiga cikin kuryar dakinsa ya dauko wasu kayansa na yaki masu matukar kyau da kuma kwarin gaske ya sanyasu ajikinsa Su dai wadannan kaya gaba daya an kerasu ne da zallan bakin karfe mai matukar kwari kuma baya saka wadannan kayan face zai fita gagarumin yaki Yana gama saka wadannan kayan sai akwatinsa ya dauko makanansa na yaki Masu kaifin gaske irin wadanda ake cewa gayawa jini na wuce Hakika wadannan kayan daya saka ba karamin kyau sukayi masa ba Bayan ya gama shiryawane ya kira wani badakare dayaje ya debo abincin guzuri yakai masa jikin dokinsa ya daure Dajin haka sai badakaren ya kamu da mamaki kuma hankalin sa ya tashi sakamakon ganin irin shigar da yayi ta yaki Sannan kuma da batun guzurin da yaji ya ambata amma saboda gudun kada yayi laifi sai yaki yin tambaya kawai ya juya domin cika aikin da aka umarceshi Fitarsa keda wuya sai sarki aryan ya biyo bayansa ya nufi hanyar zuwa fada duk inda ya gifta dakaru ne a tsaitsaye suna mamakin wannan yanayi da sarki ya shiga tsakanin jiya da yau Kafin sarki aryan ya karasa fada tuni ýan majalisunsa sun gama hallara Don haka sai yayi musu bayanin cewa a yanzu lokaci yayi da zai sami abokiyar rayuwarsa domin ya sami magajinsa wanda zai gaji sarautar sa Sannan yayi musu bayanin masifar da take fuskantar duniya wato bayyanar boka sahibul ukub ajikin yarima walisu da irin hatsarin da yake dashi aduniya Akarshe yayi musu bayanin cewa ita wacce yake burin aura a yanzu ba kowa bace face. Gimbiya walisa ýa ga sarki fadarul munnar Yanzu haka ta fita daga cikin birnin nan ta tafi aikin dake gabanta na neman dan uwanta Don haka shima zai taimaka mata domin cikar burinta Akarshe ya shaida musu cewa zai bar rikon karagarsa a hannun wazirinsa Yana gama fadin haka saiya mikawa wazirinsa mai suna yabulas kambun sarautar sa Sannan ya umarci kowannensu dasu kasance masu biyayya agareshi Hakadai sarki aryan yayi musu bayanin da zai musu dakuma ban kwana kan cewa su tayashi da addu'a kan ya sami nasara kan abinda zai fita nema Bayan haka sai sarki aryan ya kama hanya ya fice daga cikin gidan sarautar dakaru da mutanen gari suna biye dashi suna koke koke Yana cikin tafiyane yayi arba da dakaru wadanda suke sunturi acikin garin don tabbatar da tsaro inda ya tambayesu kofar da walisa ta fita ta cikinta Take kuwa dakarun suka nuna masa Cikin sauri shima ya sakarwa dokinsa linzami ya nufi hanyar Tun daga nesa da dakaru masu tsaron kofa suka hangoshi sai sukayi sauri suka bude masa kofa ya fice daga cikin birnin Ai kuwa da fitowarsa sai yaga sawun kafar dokin da walisa ta hau Cikin sauri ya kada linzamin dokin nasa ya nufi hanyar cikin azababben gudu WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A BIRNIN SHAWANA BAYAN SARKI ARYAN YA FICE DAGA CIKINSA DON NEMAN GIMBIYA WALISA ******* ******* ******* Al'amarin gimbiya walisa kuwa lokacin da wadannan kunaman suka afka mata da nufin su yi mata kaca kaca da jikinta Sai tayi sauri tasa takobinta ta kadesu da ita sannan suka sake afkomata a karo na biyu Nanfa suka kachame da azabben yaki atsakaninsu Dajin ya cika da sautin kukan wadannan kunaman wanda kan iya sawa dodon kunne yayi bindiga Kafin a dau wani lokaci mai tsawo tuni kunaman sunyi mata rubdugu ta ko'ina suna neman su hanata sakat saboda matukar yawansu Shi kansa dokin da walisa take kai in badon tana kareshi ba da tuni sun dade da hallakashi Kasa kuwa ta dinga girgiza ganyaye suka dinga zubewa akasa Kamar ana sassabe agona koda aka kara daukar wasu lokuta masu tsawo ana wannan fafatawar sai walisa ta fusata Nantake ta karanta wadansu dalasiman tsafi a fili koda gama karanta wadannan dalasimai sai take itama tareda dokinta suka rikide suka zama wata irin guguwa mai karfi Nanfa guguwar ta dinga diban kunaman nan tanayin jifa dasu a sama kamar ana yin jifa da tsumma Saidai kaga kunaman suna yawo a saman iska sannan ta doka shi da kasa, ko jikin bishiya Amma duk wannan abu da yake faruwa sai ya zama na banza Domin da zarar sun fado kasa saidai kaga sun sake mikewa tsaye sun karkade jikinsu Koda walisa taga ko kadan wannan abu babu abinda yake akansu domin ko kadan baya cutar dasu Sai kawai ta sake rikidewa zuwa ainihin siffarta ta sake afkawa kansu Tana mai kai musu sara da suka da takobinta su kuma tako wanne bangare kawo mata harbi da cizo suke ta ko ina Tabbas inbadon tana da tsananin zafin nama ba da tuni sun dade da sheketa Kuma babban abinda yake tayar mata da hankali shine ko kadan kaifi da tsini baya tasiri ajikinsu Don haka har zuwa wannan lokacin bata sami halaka koda guda daya daga cikin su ba Koda walisa ta fahimci tabbas in aka cigabada yakin a ahaka zata iya gajiya kuma su sami nasara akanta Sai ta rikide ta koma irin siffarsu daga ita har dokin nata suka cigaba da fafatawa a haka Abindaya bata mamaki shine duk da ta rikide zuwa siffarsu sai taga suna iya banbanceta a cikinsu Hikimar data sanya walisa rikidewa shine tanaso ne tayi amfani da wannan damar domin gano lagon su ne Amma duk da aikata hakan da tayi sai shima ya zama na banza Ana cikin wannan fafatawar ne kwatsam sai daya daga cikin kunaman mai matukar naci ya shammaci walisa ya dankara mata harbi akan kafarta guda daya Nantake walisa ta kwallara ihu mai karfin gaske saboda tsananin zafi da zugin da taji Don ba shiri ta dawo ainihin siffarta ta yagi gefen rigarta ta daure gurin da aka harbeta suka cigaba da fafatawar ahaka Amma duk da haka sai taki basu damar da zasu sami nasara akanta duk da cewa tsananin zafi da zugi suna yawo ajikinta kamar ana fede mata fatarta daga jikinta Su kuwa kunaman gasu nan fada sukeyi kamar ana dada kara musu kuzari ajikinsu domin babu alamun gajiya atattare dasu Koda aka dauki wasu ýan lokuta ana wannan fafatawar sai taji jiri yana neman dibanta ta fadi kasa Kodayin wannan tunani sai hankalinta ya dugunzuma domin bata san hanyar da zata sarrafa tsafinta yayi tasiri akansu ba Amma data zurfafa tunaninta sai kawai ta rikide ta koma bakar wuta Take wutar ta afka kan wadannan kunaman Ai kuwa koda faruwar hakan sai al'amarin ya sha ban ban domin take kunaman suka fara kamawa da wuta suna konewa kurmus Da ganin haka sai wutar ta dinga bin kunaman da gudun gaske tana bin jikinsu tana konasu Su kuwa sai suna fara gudun ceton ransu domin yau sunga bala'in da basu taba gani ba Tabbas gaskiya ne da ake cewa gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta domin duk da tsananin taurin kai irin nasu sai gashi suna gudu saboda ganin mutuwa muraran Wannan itace damar da ta samu akansu dukda tsananin yawansu sai gashi ya zama ba banza Domin cikin kankanin lokaci walisa ta gama karar dasu gaba daya koda guda daya bai tsira ba daga cikinsu Aikuwa adaidai lokacin data gama karar dasune jiri mai karfi ya debe ta Ta rikito kasa daga sama saboda tsananin dafin da yake jikinta da kuma jigatar da tayi Cikin sauri ta kwance jakar dake jikin kugunta ta kwanto wani garin magani ta shafa a inda ciwon yake Take taji wani irin zafi da radadi sun ratsa dukkan jikinta irin wanda bata saba jin irinsa ba Bata san sanda ta kwarara wani uban ihu ba Kawai lokaci guda sai ta fadi kasa sumammiya Bata farka ba sai bayan rana ta fadi sannan kuma dare ya Raba sosai acikin dajin hatta tafin hannunka ba zaka iya gani ba saboda tsananin duhun dajin Bakomai ya janyo haka ba face dogayen bishiyu da kuma ganyayen da suke jikinsu Duk sun rufe sararin samaniyar dajin yadda koda hasken farin wata Bazai sami damar iya ratsasu ya hasko cikin dajin ba Koda farkawarta sai taji wata irin kasala mai karfi ta lullubeta Cikin karfin hali ta samu ta mike tsaye a lokacin ne taji wani irin ciwon kai mai karfi ya kamata Kawai sai tunanin dokinta ya fado mata acikin ranta ko wani abu ya same shi Dayin wannan tunani sai ta buda tafin hannayenta ta karanta wadansu dalasiman tsafi Faruwar hakan keda wuya sai wani irin haske mai karfi ya bayyana akan tafin hannuwan nata Koda bayyanar hasken sai ta hangi dokinta acan nesa kadan da inda take yana ta faman kiwo abinsa har yana harbin iska da ka ganshi kasan babu abinda ya sameshi Take ta bude jakar guzurin ta dauko abinci taci dan kadan Sannan ta sha ruwa tana gamawa saita lallaba ta karasa inda dokinta yake ta hau Wannan hasken na hannunta yana haska mata hanya Tunda suka fara tafiya a wannan lokaci ba suji sautin koda karamin tsuntsuba Domin tuni sukayi gudun hijira daga wannan dajin saboda bala'in wadannan kunaman Koda sukayi nisa da fara tafiya ba zato ba tsammani sai walisa taji wani irin barci mai karfi ya saceta ba tareda ta sani ba Amma duk da haka wannan hasken yana nan yana ci gaba da haska hanyar Hakannne yasa dokinda take kansa ya dinga saitawa kansa hanya Ba tareda saninta ba ya dinga shiga da ita cikin surkuki duk inda yaga zai iya wucewa ta cikinsa Sannu sannu kwana nesa har dokin yazo giftawa da ita ta bakin wata babbar kasa wacce take karkashin mulkin wata mashahuriyar matsafiya wacce ake kira da suna suzaila Sarauniya suzaila ta kasance mace mai kamar maza kuma basadaukiyar gaske Hakanne yasa take amfani da karfin damtsenta dana sihirinta tana zaluntar talakawanta Gaba daya sarakunan da suke mulkin wannan nahiyar suna matukar shakkarta da tsoron ta Sai da takaicewa gaba daya fatake da ýan kasuwa sun daina ratsawa ta cikin birninta Domin da zarar ka shiga zatazo da kanta ta yanka ma haraji mai yawa tace sai ka biya Idan kuwa kaki take zata sa akama ka a kaika can cikin kurkunta ayita gana maka azaba mai radadi har sai ka mutu Sannan tasa a kwaso dukiyar daka shigo da ita gaba daya a ajiye mata ita acikin taskarta Lokacin da sarauniya suzaila ta fahimci cewa duk ýan kasuwa Sun daina ratsawa ta birnin ta sai ta baza dakarunta acikin daji cewa duk inda suka ga bako yazo giftawa to su kamo matashi ko wane su kawo shi fadarta domin a yanke masa hukunci Lokacin da dokin walisa yazo ratsawa ta bakin birnin sai dakarun suka hangoshi daga nesa yana tafiya Sannan ga mahayin dake kansa akwance kamar matacce Sai dakarun suka taho da sauri suka kewaye dokin sannan shugabansu wani kakkaura ya karaso inda walisa take yasa hannu a daidai kan hancinta yaji alamun tana numfashi Sai yayi dariya ya dubi abokan aikinsa yace Da alama wannan kyakkyawar budurwar tasha wahala akan hanya kafin ta iso nan Domin tunda nake ban taba ganin wahalar data saka matafiyi ya iya barci akan doki ba Dajin haka sai suma dakarun suka kalli junansu sannan suma suka kyalkyale da dariyar mugunta daya daga cikinsu yace gaskiyane mai gida amma ai duk wahalar nan data sha ta zama ta banza tunda har ta iso birnin durgan Dajin haka sai shima yayi murmushi ya umarci wani daga cikinsu daya janyo dokin da walisa take kai ya biyoshi dashi abaya Da gama fadin haka sai take ya juya ya shige gaba su kuma ragowar dakarun suka biyoshi abaya har suka shiga birnin durgan Har suka shiga ciki bata farka daga barcin da take ba WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA GIMBIYA WALISA BAYAN TA KUBUTA DAGA SHARRIN WADANNAN MUGAYEN KUNAMAN ******* ******** ******* Al'amarin sarki aryan kuwa lokacin daya bar birninsa Ya fito neman walisa sai ya shiga cikin daji yana ta faman gudu Acikinsa kuma yana bin sawun doki guda daya wanda ya fita daga cikin birninsa Kuma ba sawun kowa bane face sawun dokin da walisa take kai Koda yayi nisa yana tafiya acikin dajin sai kuma yaga sawun dokin ya hargitse masa daga daya zuwa masu yawa Da alama akwai alamun wasu dawakan da sukabi hanyar bayan ita Koda ganin wannan al'amari sai kawai ya sauko daga kan dokinsa Ya sunkuya kasa ya kalli kasar gurin sosai yana nazarinta Daga can sai ya debi kasar gurin ya shinshinata da hancinsa Koda yin haka sai ya girgiza kansa tareda yin murnushi Sannan ya sake mikewa tsaye ya kama dokinsa ya haye yaci gaba da tafiya Saida yayi kwanaki biyu yana tafiya ba tareda ya hadu da wata matsala ba Sai arana ta ukune akan hanyarsa yayi arba da wani irin murgujejen mummunan aljani Wanda tunda yazo duniya bai taba jin labarin aljani mai irin siffarsa da kuma girmansa ba SHIN SARKI ARYAN ZAI KUBUTA DAGA SHARRIN WANNAN ALJANIN KUWA? ME ZAI FARU GA GIMBIYA WALISA IDAN AKA KAIFA FADAR SARAUNIYA SUZAILA? DUK AMSAR WADANNA TAMBAYOYI SUNA CIKIN KASHI NA GABA SAI MUN HADU DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS**************ZUBAR DA JINI ************---9 PART C LBR ------------------------HABIBULLAH KBR Lokacin da sarki aryan yayi arba da wannan basamuden aljanin agabansa Sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak sakamakon firgitar da dokin yayi har yana daga kafafunsa na gaba sama yana shirin ya juya da baya saboda tsabagen firgitar da yayi Girman aljanin kadai ya isa abin tsoro ballantana kuma munin halittar da yake da ita Shi dai wannan aljani idan ka ganshi zakaga jikinsa yana da matukar tsawo amma bashi da kauri sosai Domin girman kansa ma ya ninka jikinsa a kauri sau hudu Idanuwansa kuwa jajayene kamar garwashin mahauta Haka kuma hannayensa zankal zankala ne wadanda sunkai jikin nasa tsawo saidai suma basu da tsawo Hakama kafafuwansa sirarane kamar yadda jikinsa yake Idan kana kallonsa sai kayi zaton idan iska mai karfi ta taso zata iya dagashi sama ta maka da kasa Ko kuma kayi zaton cewa nauyin kan nasa zai iya rinjayar jikin nasa ya rikitar dashi Bakinsa kuwa dogo ne kamar irin bakin ungulu saidai shi nasa tsawonsa yakai tsawon bishiyar dabino Kai duk sanda kayi arba da wannan aljani dolene ba zaka sake fatan sake yin arba dashi ba domin ganinsa ma ba zai barka kayi rayuwa cikin kwanciyar hankali ba Koda yaja linzamin dokin nasa sai ya tsaya cak suka fara kallon kallo da aljanin Daga can sai aljanin ya sunkuyo da kansa kasa daidai dana sarki aryan sannan ya bushe da dariya wacce saboda tsabar karfin sautin nasa sai da yaji kamar dodon kunnuwansa zasu fashe sannan yace Yakai wannan bil'adama hakika yau kayi gamo da ajalinka Domin kuwa wannan shine karona na farko dana fara haduwa da bil'adama saidai kawai ina samun labaranku a gurin ýan uwana Tun da aka haifeni yau shekara dubu goma cif kuma ban shigo wannan duniyar taku domin komai ba face Burin cika burina na samun damar da zan zama sarkin yaki a can nahiyar mu Bincike ya tabbatar mini da cewa wannan burin ba zai taba cika ba face Na shigo cikin duniyar ZUBAR DA JINI wato wannan duniyar da kuke rayuwa acikinta na mallaki kokunan shahararrun mayaka na wannan duniyar taku na hade su guri daya na hada wani sihirin tsafi dashi Sannan zan sami damar zama sarkin yaki kamar yadda na fada maka da farko Kuma sai gashi tun bayyanata akaron farko tsautsayi ya hada ka dani kuma ina ratsuwa da sihirin tsafina ba zaka tsira daga sharrina ba Koda jin haka sai shima ya murtuke fuskarsa ya kurawa aljanin idanu daga can sai shima ya bushe da dariya Wacce dariyar tasa ta baiwa aljanin mamaki har yaji kamar yasa hannunsa ya talitse shi Daga can kuma sai ya tsuke bakinsa ga barin dariyar ya dakawa aljanin tsawa yace Karyarka ta sha karya ka cika burin nan naka akaina Domin kuwa ni ban kasance mara sa'a ba a rayuwata kuma babu wanda ya taba samun galaba akaina Bayan haka ina tabbatar maka da cewa tsafinka yaudarar ka yayi domin inda yasan sharrin bil'adama da bai turoka cikinsu ba Wannan duniyar tamu tafi karfin iko da nasara don haka ina sauraronka I dan har ka isa ka cutar dani ko kuma dokin da nake Kansa Kodajin haka sai zuciyar aljanin ta harzuka har yaji jikinsa nayi masa karkarwa Cikin zafin nama yasa hannunsa guda ya shuri sarki aryan tareda dokinsa da nufin ya matse su da hannun nasa yadda hatta kashushuwan jikinsa sai ya kakkarya su Koda ya debesu sai nan take duk su biyun suka narke suka zama kamar ruwa suka sulale ta cikin tsakankanin yatsun aljanin suka sauka akasa sannan suka koma ainihin siffarsu Koda ganin haka sai zuciyar sa ta kara harzuka ya kawo masa wani irin mahaukacin duka da kafafuwansa Cikin bakin zafin nama sarki aryan tareda dokinsa suka dunkule jikinsu guri daya Take suka zama kasa

Chapter 16 of 17