Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Koda suka fito daga cikin gidan sarautar sai suka wuce kai tsaye izuwa bargar dawakai Ta zabi wani ingarman farin doki matashi Mai jini ajika ta dauka ta hau Sai gashi dokin ya dace da ita kamar saboda ita aka halicci dokin Daga wannan guri sukayi bankwana da sarki fadarul munnar Ta kama hanya ta nufi hanyar fita daga birnin Duk inda ta gifta sai dai kaga dakaru da mutanen gari suna rissinawa suna gaisheta Tareda yi mata addu'ar samun nasara Ahaka har ta fice daga cikin birnin gaba daya ta shiga cikin daji Tana zabga azababben gudu Tun tana cikin yankin birninsu har ya zamana ta fice daga cikin nahiyar gaba daya Kuma duk inda ta hadu da mutane saita dauko hoton yarima walisu Ta nuna musu shi ko sun ganshi akan hanyar su Amma ko sai daya bata hadu da wasu mutane wadanda suka ce sun taba haduwa dashi ba 0=====[============> Can kuwa al'amarin yarima walisu tun daga lokacin da fatalwar boka sahibul ukub ta shiga jikinsa Alokacin yana kwance acikin turakarsa Abinda ya faru shine Lokacinda dare ya tsala yana cikin sharara barci abinsa harda minshari Kamar wanda bazai taba farkawa ba daga dogon barcin da yakeyi Kwatsam sai yaji wata irin tsawa daga Cikin sauri ya farka firgigit daga dogon barcin da yakeyi Tareda zare takobinsa azatonsa wasu dakarun mamayar bazato ne suka kawo masa hari Bisa mamaki sai yaga shi kadai ne acikin dakin babu kowa Amma duk da haka ba'adai na wannan walkiyar ba Don haka sai ya kwantar da hankalinsa domin ya zata hadari ne Ya hado ake shirin yin ruwan sama Amma sai yaga wannan tsawar bata tsayaba har ma dakin nasa gaba daya ya canja fasali Ba kamar yadda yake da ba Domin gani yayi komai na cikin dakin yana yawo akan iska Sannan ya dinga jin kamar ana kyallara dariya daga cikin wannan tsawar da take tashi Ba zato ba tsammani sai kawai yaji kamar an kama jikinsa an daure .yadda ko dan yatsansa bazai iya dagawa ba Daga can kuma sai yaji an bushe da dariya wacce bai san daga inda take tasowa ba Kuma duk wannan abu da yake faruwa shi kadai ne yake ji kuma yake gani Duk hadiman gidan sarautar basa iya ganin komai Ana cewa cikin wata kakkausar murya mai kama da kukan jaki Yakai wannan jarumi daga yanzu babu wanda yake da iko akanka Sai abinda muka saka ka kawai zakayi ko kanaso ko baka so Dole ne ka zama bawanmu daga nan har karshen rayuwarka Kuma dakaine zan cika burina na ganin duk wata teku ya rine da jinin bil'adama Kafin yace wani abu sai kawai yaga wani irin haske mai kama da suffar bil'adama Tsoho tukuf fuskarsa cike da furfura idanunsa kuwa jajaye ne wuluk babu alamar fari acikinsu Yana tafiya akan iska tareda kyalkyala dariya ya taho gurinda yake Yarima walisu yana ji yana gani amma bashi da ikon koda bude bakinsa Balle yayi magana wannan tsohon matsafi yazo ya shiga gangar jikinsa Take walisu yaji gaba daya jikinsa yayi sanyi kuma nantake gaba daya tunaninsa Ya juye ya manta ko wanene shi da asalinsa da kuma mahaifarsa Nantake yaganshi yana tafiya akan iska ba kan kasa ba Ahaka ya dinga ratsawa ta cikin ginin gidan sarautar tasu Kuma duk inda ya gifta babu wanda yake iya ganinsa Domin ta gaban dakarun ya dinga wucewa wasuma ratsawa ta jikinsu Ya dingayi yana wucewa ahaka har ya bar cikin birnin Kuma wata irin tafiya ya dingayi ta ban al'ajabi domin tafiya mai tsawo Yana tamkar gudun kibiya haka yake yawo acikin iska Ahankali har ya bayyana agaban wata katuwar bishiyar kuka Acikin wani irin bakin daji itadai wannan bishiyar kukar ta kasance katuwar gaske Domin komai karfin idon mutum bai isa ya ita ganin karsheta ba Koda zuwansa gaban wannan bishiyar sai kawai kasar gurin ta dare gida biyu Wata iriyar katuwar kofa ta bayyana akasanta kamar kofar gari Nantake ya shiga cikin wannan kofar har yakai karshenta Wohoho hakika wanda baiyi yawon duniya ba bai morewa idonsa kalloba Sai gashi ya bayyana acikin wata katuwar fada mai girman gaske Kai da ganin yadda wannan fadar take kasan cewa an dade ba'a shigo cikinta ba Domin gaba daya komai na cikin fadar a lullube yake da yana da kuma kura Nantake walisu ya dubi gaba daya fadar da kwayar idanunsa Take wata iriyar iska mai karfi ta fito daga cikin idanun nasa Ta karkade gaba daya yana da kuma kurar da suke cikin fadar Sannan gaba daya kurar ta bace gaba dayanta Bayan nan kuma sai wani irin ruwa ya fito daga cikin idanun nasa Ya wanke komai na cikin fadar kuma atake komai ya bushe kamar ruwa bai taba sauka ajikinsu ba Bayan komai ya koma yadda yake sai ya tafi kai tsaye zuwa inda wata kujerar tsafi take ya zauna akanta tareda dora hannayensa akan cinyoyinsa Bayan 'yan dakiku sai yaji jikinsa ya fara karkarwa Take ya fadi kasa ya fara farfadiya Bakomai ne ya jawo hakaba face alokacin ne ruhin boka sahibul ukub yake da bukatar fita daga jikinsa Nantake wannan hasken ya fita daga jikinsa shima ya dawo hayyacinsa Koda ya dawo cikin hayyacinsa yayi arba da ruhin boka sahibul ukub Sai ya daka masa tsawa tareda cewa Wai shin kai wanene kuma me kake nufi dani sannan inane kakawo ni nan? Ka gaggauta saki na ko kuma yanzun nan na hallaka gaba daya Dajin haka sai ruhin boka sahibul ukub ya bushe da dariya sannan yace Kai yaro hakika kana yaudarar kanka ne domin da ace ka sanni da bazakayi wannan maganar ba Nine kadai atarihin duniya shu'umin dagaba daya duniya suke bauta masa Domin babu wanda yake da karfin sihirin da nake dashi Kuma nine wanda ya gagari duniya gabaki dayanta har ya zamana Kowa yafi tsorona fiye da yadda yake tsoron mutuwarsa Yanzu kai tayaya kake tsammanin zaka kasheni bayan dama can ni mataccene? Kaine zaka zame mini gangar jikina awannan zamanin Domin na ci gaba da BUWAYAR SADAUKAI da kuma manyan SARAKUNA da kananun BOKAYEN wannan zamanin naku Wadanda gaba daya sihirin nasu baifi cikin cokali ba Ballantana kuma kai kanka ta taya kake tsammanin zaka iya tarata da yaki? Bayan na dade da shudewa ? Ka sani cewa indai bana jikinka to sihirin tsafi na ba zai taba yin tasiri ba Amma kuma idan duk duniya zasu taru basu isa su hanani shiga jikin ka ba Kafin ya gama fadar abinda yake bakinsa tuni jarumi walisu Ya dako tsalle daga inda yake ya kawowa ruhin boka sahibul ukub Mummunan sara da nufin ya tsargeshi gida biyu Bisa mamaki sai yaga takobin ta ratsa jikinsa ta wuce kamar Ya sari haske ba tareda yaga jini ajikin takobinba kawai Sai yaji boka sahibul ukub ya sake bushewa da wata mahaukaciyar Dariya fiye da wacce yayi a baya wacce tasa fadar ta fara amsa kuwwa da amo Komai na cikinta ya fara girgiza kamar zai rufto kasa Harsaida yayi shiru sannan komai ya koma kamar yadda da yake abaya Ya sake kallon walisu yace Kai yaro kadaka taba yaudarar kanka da tunanin ganin karshena Domin nine sa gudu kuma ki gudu duk hatsabibancin mutum ko aljan yana shakka haduwa dani Kuma ina mai tabbatar maka da cewa ni din nan murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya Daga yanzu acikin wannan fadar zaka ci gaba da zama har iya karshen rayuwarka kuma ina mai tabbatar maka da cewa bazan bari ka mutu da wuri ba Dole sai bukata ta gama biya ta ganin na zama cikakken gagara badau Koda ruhin boka sahibul ukub ya gama fadar haka sai nantake ya tarwatse Ya sake dawowa ya shiga jikin walisu faruwar hakan keda wuya saiga launin fuskarsa ta sauya daga launin mutanen arziki zuwa ta azzalumai Take wasu irin zabga zabgan fukafukai suka fito daga jikinsa Sannan ya mike ya tashi sama ya ratsa ta jikin wannan ginin fadar Ya luluka. Cikin sararin sama cikin azababben gudu kamar iska WANNAN SHINE DALILIN DAYA SA GABA DAYA BOKAYEN DUNIYA SUKA KASA GANO INDA YARIMA WALISU YAKE Babu inda jarumi walisu ya nufa face wani katon birni Wanda ake kiransa da suna keraya, birnin keraya babban birnine kuma karkashin mulkin wani azzalumin sarki mai suna ukibanu Yana da matukar karfin sihiri da kuma karfin damtse Kuma shima ya dauki ZUBAR DA JINI ba abakin komai ba Hatta talakawan birninsa irin halinsu kenan wannan dalilin ne yasa Kowa baya shakkar mutuwa akullum zubar da jinin bil'adama ake acikin Wannan birni Wata rana suna zaune ana tafiyar da harkokinsu na yau da kullum Kuma a wannan lokaci wani katon kakkarfan mutum Mai kirar mutanen farko ya kamo wadansu dattijai guda biyu Da kuma 'ya'yansu yara kanana ya daure su a tsakiyar kasuwa Yana sa wuka yana yankan naman jikinsu yana gasawa acikin wuta Sannan ya jefawa wadansu karnuka da suke bayansa su cinye Su kuma wadannan daurarun mutanen sai kuka sukeyi Gefe kuma ragowar mutanen gari ne sun tsaya suna kallonsu Suna ta kyalkyala musu dariya don ko kadan babu alamar tausayi akan fuskokinsu ME KAKE GANIN ZAI FARU A WANNAN BIRNI? KUMA SHIN WALISA ZATA HADU DA DAN UWANTA JARUMI WALISU? WANNE IRIN TASHIN HANKALI MUTANEN DUNIYA ZASU SHIGA SAKAMAKON BAYYANARSA? SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++++++1 PART C LBR ++++++++++++ HABIBULLAH KBR Kai wasuma har faduwa suke saboda dariya mazansu da matansu Har ma zugashi wannan azzalumin sukeyi akan ya kara tsananin azabar da yake yiwa wadannan daurarrun Wannan itace al'adar mutanen wannan gari indai kai ba jarumi bane Koda yaushe irin wannan abu zai iya faruwa dakai domin bakin zaluncin su Suna cikin wannan bakar al'adar tasu ne kawai sukaji wata iriyar Bakar guguwa ta taso daga sama wacce ta haddasa tashin kura acikin birnin gaba dayansa Wani irin bakin hadari ya tokare sararin samaniya kai kace ruwan sama za'ayi Nanfa hankalin mutane gaba daya yabar kan wannan bakin azzalumi Suka daga kawunansu sama suna kallon abinda yake shirin faruwa Kafin su ankara sai sukaji wata irin tsawa mai karfi ta amsa kuwwa A gaba daya birnin kamar zata fasa dodon kunne kai saboda ma karfin karar saida suka durkushe kasa suka sa hannuwansu suka toshe kunnuwansu Sannan suka tashi suka fara gudun neman wajen tsira Daga can kuma sai kasa ta fara tsagewa mutane suna ruftawa cikinta Nanfa hankalin gaba daya mutanen birnin ya tashi suka Gudu suka bar kallon wannan bakin azzalumin domin Shima gudun ceton ransa yayi bai san inda ya nufa ba Mutane kuwa garin gudu wasu har fadawa suka dingayi Cikin ramuka ba tareda sun sani ba, wasu kuma suna sane suka dinga jefa 'yan uwansu Domin suma su tsira da rayukansu, manyan gine ginen birnin ma suka dinga zabtarewa suna fadowa kan mutane Ana cikin wannan haline kawai sukaga kasa ya tsage Ta haifar da wani wawakeken rami wanda basa iya ganin karshensa Ta cikin ramin kuma sukaga jarumi walisu ya fito jikinsa Dauke da manya manyan fukafukai har a wannan lokaci bai daina kyalkyala dariya ba Koda sukayi arba da walisu sai suka kara firgita fiye da ko yaushe Yana gama fitowa daga cikin ramin sai sukaga ya sunkuya yasa hannunsa guda daya Ta shake wuyan wannan azzalumin mutumin take wuyan ya zabtare kamar zabira akasa aka yanka wuyan nasa da ita Sannan ya juya kan wadannan daurarun mutanen suma ya firge musu kawunansu Faruwar hakan keda wuya jini yayi tsartuwa daga jikin dungulmin wuyan nasu Koda ganin abindaya faru sai mutane suka rusa uban ihu Suka fara guje gujen neman wajen tsira amma ina babu damar hakan Domin duk inda suka nufa saidai kaga walisu yayi nuni da hannunsa Zuwa inda mutum yake saidai kaga kokon kansa ya fita daga jikin wuyansa Jini yayi fallatsi a sama, ana cikin wannan artabune kawai sai dakarun sarkin garin suka iso karkashin Jagorancin sarkin garin ukibanu koda sarki ukibanu yaga Irin mahaukaciyar barnar da jarumi walisu yake masa Saiya kwallara uban ihu sannan ya umarci dakaru masu kibiya dasu harbi jarumi walisu Take kuwa suka cika umarni suka zaro wasu dogayen kibiyoyi suka harbowa jarumi walisu Hakika rashin sani yafi dare duhu inda wadannan dakarun sun san abinda zai samesu da basuyi yunkurin cutar da walisu Saidai su koma kan maigidan nasu Ai koda suka harba kibiyoyin sararin samaniya sai kawai sukaga Kibiyoyin sun dawo ta saman kansu suka fasa kokon kansu Sannan suka hudo ta kasan duburarsu take sukayi mutuwar tsaye Saidai kawai kaga jini yana bulbulowa ta kasan duburarsu kamar ruwan fanfo Nantake suka sulale kasa matattu koda ganin abindaya faru ga wadannan dakaru Saiya kwarar uban ihu ya falfalo da gudun gaske zuwa kan walisu Koda yazo baifi taku hudu ba atsakaninsu sai sarki ukibanu Ya daka tsalle da nufin ya kaiwa walisu harin bazato Koda takobin ta kusa sauka akan wuyan jarumi walisu Sai wani irin tiririn hayaki ya fita daga jikinsa ya shiga jikin sarki ukibanu Take jikinsa ya sandare a saman kamar wanda ya kasance dama can ba'a taba halittarsa ba Daga can kuma sai jini ya dinga fita daga cikin kowacce kofar gashi da take jikinsa Kafin cikar dakika biyu duk jinin jikinsa ya gama fita kuma yazama gawa Koda yaga ya gama da sarkin garin sai ya koma kan mutanen birnin Yaci gaba dayi musu kisan gilla, Kaico ! Kai komai rashin imanin mutum idan yaga yadda walisu yake yiwa mutane kisan gilla dolene ya tausaya musu Saidai kaga kawai walisu yana nuni da hannunsa yana Fizgewa mutane kawunansu gaba daya garin babu abinda kakeji face Koke koken mutane yara da tsofaffi amma shi babu abindaya dameshi Cikin abinda bai wuce dakika ashirin ba ya gama hallakar da duk mutanen birnin yayiwa kasa ado da jininsu kai hatta jikin ginannika Babu abinda zaka gani face jinin mutane wanda yayiwa ginin fenti Kasa kuwa gatanan ta rine da jinin bil'adama ya cudanya da jini Koda gama aikata wannan munnar barnar tasa sai ya dauko kokon kan wata mujiya ya tsireta ajikin mashi sannan ya bude fukafukansa ya tashi sama tamkar bai taba wanzuwa abirnin ba WANNAN SHINE LABARIN JARUMI WALISU 0======[=========≠=====> Acan kuwa al'amariin jaruma walisa tun daga sanda Ta baro gida ta fito neman dan uwanta jarumi walisu Sai ta shiga cikin manyan dajijjika da kogunan duwatsu Ko zataganshi ko kuma ta sami labarin inda yake amma harta gama karade wadannan dajijjika bata hadu da shi ba Fargabar da takeyi acikin zuciyarta itace wanne birni zataje ta hadu da walisu Kuma ta yaya zata iya hanashi ai watar da mummunar dabi'arsa Tana cikin tafiyane acikin daji kawai sai ta jiyo karnin jini Daga can nesa da inda take, take ta juyar da linzamin dokinta Zuwa inda take jiwo wannan karni, koda ta karasa sai taga gurin ya Cika makil da wakilan wasu manyan sarakunan sunzo Domin suga abindaya faru a wannan guri, kowa acikin su Ya toshe hancinsa da hannunsa saboda tsananin karnin da yake tashi awannan birni Koda walisa ta iso wannan guri saita cika da tsananin mamaki Ta sami wani daga cikin mutanen da suke gurin wanda ya kasance dattijon mutum tace Wanne irin bala'i ne ya faru a wannan guri, ko kuma wasu bakaken aljanun ne Suka kawo musu harin bazato? Kodajin wannan tambaya sai wannan mutumin ya kalleta yace Dukkanmu nan bamuda masaniyar amsar wannan tambaya taki Domin gaba dayan mu bamusan faruwar wannan al'amari ba Kuma ina mai tabbatar miki da cewa ba aljanu ne sukayi wannan abuba Saidai wani shararren matsafin domin sarki ukibanu hatsabibin mutumne Shine yake mulkin gaba daya aljanun da suke wannan nahiya Don haka kinga aljanu basu isa suyi masa wannan mummunan kisa ba Kodajin haka sai zuciyar walisa ta buga da karfi tace acikin zuciyarta Anya kuwa wannan ba aikin dan uwana walisu baneba? Lallai akwai abin al'ajabi acikin wannan al'amari, tana cikin wannan Zancen zucin ne ta iso inda gawar sarki ukibanu take Har a sannan yana sandare a sama bai fado kasa ba Saidai takobinsa ita kadaice ta fadi daga hannunsa Wannan abin ne ya tabbatar mata da cewa lallai wannan aikin walsu ne Tace acikin ranta shin ina ya kamata taje inda zata hadu dashi? Dolene tayi saurin hanashi aikata wannan mummunar barnar da yake yi Tana gama wannan zancen zuci sai kawai ta yanke shawarar Shiga cikin wani birnin da suke makwabtaka da wannan birni 0=====[=========≠====> Birnin kufa babban birnine wanda yake cike da kabilu kala kala Kuma yana karkashin mulkin wani hamshakin sarki matashi Maisuna kalkus, Kalkus amini ne ga marigayi sarki ukibanu kuma akwai shakuwa Mai tarin yawa a tsakaninsu domin tun suna yara suke abokan taka da juna Har zuwa girmansu, kuma ya sami labarin abindaya faru a birnin da abokinsa yake mulki wato ukibanu Kuma har yaje da kafafunsa ya gani da idonsa abindaya faru Don haka sai ransa yayi matukar baci ya hada dakarun sa masu yawa Yayi shirin fita neman wanda yayi wannan danyen aiki da kansa Har sun fito kofar gidan sarautar kawai sai sukayi kicibus Da babban bokan birnin wanda akewa lakabi da shamshan Shidai shamshan ya kasance dattijone mai shekaru kimanin tamanin da biyar Fuskarsa cike take da furfura, sannan yana da matukar kwarjini Kallo daya zakayi masa kasan cewa ya sha gwagawar mayar duniya Hannunsa ruke yakeda wata sandar tsafi irinta shahararrun matsafa Cikin sauri boka shamshan yazo gaban sarki kalkus ya russina yace Ya shugabana ina mai shawartarka da kada kayi gaggawar wannan tafiya Domin bincike na ya nuna mini cewa idan har ka fita daga cikin birnin nan ba zaka dawo a raye ba wannan aiki dake gabanka Daidai yake da fita farautar mutuwar ka Koda jin wannan batu sai sarki kalkus ya kwarar uban ihu saboda bakin ciki Bisa dole ya hakura ya koma cikin gidan sarauta boka shamshan yana biye dashi abaya Da isarsu cikin fadar sai sarki ya sami guri ya zauna Sannan shima boka shamshan ya zauna suna fuskantar juna Bayan sun danyi shiru na kankanin lokaci sai bokan ya katse shirun da yake tsakaninsu da fadin cewa Ya shugabana ba komai ne yasa na hanaka fita daga cikin birnin nan ba Face binciken danayi yanzu akan wannan al'amari shine yayi matukar razanani Domin babu irin binciken da banyi ba akan na gano Wanda ya aikata wannan mummunan aiki ba amma na kasa Kai dana tsawaita bincikema sai madubin tsafin nawa ma ya fashe gaba daya Tun da nake ban taba ganin al'amari mai firgitarwa ba face wannan Sai dai idan mukayi amfani da kwakwalwar mu zamu iya gano Silar faruwar wannan abu gasu sarki ukibanu Idan har zaka iya tunawa tun daga sanda aka haifemu Irin haka bata taba faruwa ba a wannan duniya saidai Kuma mun sami labari daga gurin kakanninmu cewa A shekarun baya an tabayin wani hatsabibin boka wanda a wannan zamanin Babu wanda ya kaishi shu'umanci har zuwa yanzu Duk rashin imanin mutum bai isa ya kwatanta rashin imani ko irin azabar sa ba Wannan daliline yasa ake masa lakabi da sahibul ukub Wasu kuma sunayi masa lakabi da tauraruwa mai wutsiya saboda ganinsa ba alheri bane Duk inda ya baiyana sai yayiwa kasar gurin ado da jinin mutanen da suke rayuwa agurin Har wasuma nayi masa kirari da guguwar annoba Babu irin salon zaluncin da bai sani ba Domin duk azzaluman da kake ganin sun cika zalunci to shi suke kwaikwaya Inta kaice makama duk duniya a wancan zamanin saida suka koma bauta masa Na sami labari agurin kakana cewa shi wannan bokan Ya taba haduwa da wani sadaukin jarumi ma'abocin addinin musulunci ana kiransa da suna hassanul basari Suka fafata kazamin yaki dashi daga baya ya sami nasarar Hallaka boka sahibul ukub, saidai ba anan gizo yake sakar ba Domin an kashe maciji ne ba'a sare kansa ba, Saboda ita kanta gangar jikinsa bacewa tayi ba'a sake ganinta ba Saidai masu bincike sun tabbatar da cewa nan da wasu shekaru masu zuwa zai sake bayyana da wata bakuwar fuskar wacce ba'a santa ba Don haka idan mukayi tunani akan abindaya faru zaka ga cewa Duk cikin nahiyar nan in banda kai babu mutum mai karfin damtsen ukibanu Sannan kuma shi mutum ne mai tsananin karfin sihiri Idan kayi la'akari da irin kisan da aka dinga yiwa mutanen birnin keraya Zakaga cewa kisan ba'ayi amfani da makami ba alokacin yinsa Kuma da ace da karfin damtse akayi wannan fafatawa Dolene labari yazo har nan ya samemu har muje mukai musu dauki Ballantana ma uwa uba cewa Nayi amfani da gaba daya sihirina amma na kasa ganin wanda ya aikata wannan barna Abisa wannan daliline yasa na tabbatar da cewa boka sahibul ukub ne Ya dawo a cikin wannan zamanin da muke ciki Idan kuma baka yarda ba inaso ka danyi hakuri daga nan zuwa kwanaki biyu Zaka gasgata maganata, kai in takaicemaka hatta shi kan wannan mujiyar daka gani an ajiye atsakiyar birnin keraya itace shaidar da boka sahibul ukub yake bari aduk inda yakai hari Abinciken da nayi yanzu na gano cewa akwai wata budurwa Wacce ta baro gida domin neman shi boka sahibul ukub din Domin tsafi ya tabbatar da cewa itace zata hanashi aikata wannan zaluncin Tabbas itama jarumace ta hakika amma kuma bata da karfin sihirinsa Zatasha wahala duk lokacin da suka hadu da ita amma duk wuyar da zata sha ba zata mutu ba Saboda akwai alaka mai karfi atsakaninsu Dajin haka sai hankalin sarki kalkus ya tashi ya tambayi shamsal yace Shin a ina zan sami wannan budurwa inje in tareta mu hada karfi da karfe Mu kawo karshen sahibul ukub? Dajin wannan tambaya sai boka shamshan ya bushe da dariya sannan yace Ai zaifi kyau kahakura ka zauna acikin masarautar nan taka don wanda yayi karo da sahibul ukub to kamar yayi karo da ajalinsa ne Koda jin haka sai sarki kalkus ya daka masa tsawa yace Kai karya kake yi dolene nima na fita nemansa da kaina domin na kare kimar kasata Nanfa boka shamshan ya fara kokarin shawo kansa amma yaki hakura Ya kama hanya ya fita daga gidan sarautar 0======[=========≠=====> Lokacin da walisa ta kama hanya da nufin idan ta sami wani garin ta yada zango acikinsa Tana cikin wannan tafiyar ne ta iso bakin wata katuwar korama Wacce ruwa yake gangarawa cikinta a wannan lokaci daga ita har wannan dokin nata sun gaji saboda

Chapter 2 of 17