Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai isheshi , tareda diban dukkan makaman yakinsa Ya dawo wajen malan ramadan, sannan suka dunguma duk su biyun suka tafi izuwa bayan gari Tafiya ýar kadan sukayi sannan sukazo wani daji mai yawan rairayi da ni'ima wanda duk wanda yake rayuwa acikinsa zaiji dadin zaman Koda zuwansu wannan wuri sai sai malan ramadan ya kira sunan aljani hadimul islam sau uku Take kuwa wata irin iska mai karfi ta fara kadawa asararin samaniya Wacce ta tayar da kura a gurin, har saida suka sa hannunsu suka kare fuskokinsu don kada kurar ta shiga cikin idanunsu Sannu a hankali sai ga wani shirgegen aljani yana saukowa kasa daga sararin samaniya Shidai wannan aljani ya kasance matashin aljani fari kuma sanye yake da fararen tufafi Shekarunsa ba zasu wuce dari takwas da doriya ba Kallo daya zakayi masa kasan cewa Yana tashen ji da samartaka, fukafukansa kuwa kwaya biyune rak amma sun kasance manyane masu girman gaske A hankali wannan aljanin ya sauka akasa sannan ya kai gaisuwa ga malan ramadan sannan yace Ya kai wannan shehin malami me kake bukata da har yasa ka kirani adaidai wannan lokaci ? Dajin wannan tambayar sai yace dashi Yakai hadimul islam yanzu haka dalilin kiranka shine inaso yanzu ka dauki hassanul basari ka kaishi can farkon dajin duniyar mutuwa ka ajiyeshi anan sannan kayi zaman jiran dawowarsa Ku dawo nan gaba daya Kodajin wannan batu sai fuskarsa ta fadada da murmushin jin dadi sannan ya kara da cewa To ai kuwa indai hakane ya kamata ace nima na shiga cikin wannan daji domin nima na sami damar yin shahada Kodajin wannan batu sai malan ramadan yace dashi Kayi hakuri akwai babban dalilin dayasa nace karka shiga wannan daji ka zauna ka jirashi Aljani hadimul islam yace to ai shikenan sai yazo mu tafi Yana gama fadar haka sai ya rankwafa doron bayansa Sadauki hassanul basari ya daka tsalle ya haye gadon bayan nasa Sannan suka yiwa malan ramadan sallama suka luluka cikin sararin samaniya Tun malan ramadan yana iya hangosu har saida suka bace masa da gani Take hadimul islam ya juya ya nufi hanyar da zata kaisu can kudancin duniya inda anan ne fadar boka sahibul ukub take Sai gashi sunata keta manyan dajijjika masu girman gaske da kuma hatsari Kai hatta tsaunika ma sai suka zama ýan kanana agunsu saboda yadda suka kule a sararin samaniya wanda yake kasa ma baya iya hangosu WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA SADAUKI HASSANUL BASARI BAYAN YA FITO NEMAN MASOYIYARSA GIMBIYA BAHJAHT DA KANSA, DA NUFIN ZUWA FADAR BOKA SAHIBUL UKUB ****** ****** ******* ******* Acan fadar boka sahibul ukub wacce take akan tsuburin hayatul sihir wanda ke tsakiyar duniyar mutuwa kuwa Yana dawowa daga kurkun darul maut sai kujerarsa ta haske ta bayyana akan iska ta tsaya cak sannan ya sami guri ya zauna. Akanta Yanata kyalkyala dariyar mugunta domin ganin ya sami nasarar ruguje birnin shawana Har ma ya dauko gimbiya bahjaht ya taho da ita fadar sa Wannan shine abinda yake sakashi kyalkyala dariyar muguntar da yake Amma kodaya tuna cewa kamar ya kashe macijine bai sare kansa ba Domin har yanzu HASSANUL BASARI yana raye sai ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar da yake Kawai sai ya saka hannunsa ya cire rigar da take jikinsa da nufin ya sakaleta ajikin bango Kawai saiga akwatin dasu gimbiya bahjaht suke ciki ta fado kasa daga cikin aljihunsa Sai da yaga wannan akwatin ne ya tuna da batun su gimbiya bahjaht da hadiminta uzumnal Koda ganin wannan akwati sai ya sunkuya ya daukeshi Ya bude kofarsa ya leka ciki da idonsa kwaya daya kawai sai yaga gimbiya bahjaht da uzumnal duk a razane Saboda duk jikinsu ya bugu sakamakon fadowar da sukayi daga aljihunsa Kawai saiya daga akwatin da hannunsa daya ya zazzagesu akasa duk suka zubo daga ciki Sai gasu sun zama ýan mini mini agabansa basu wuce girman jira jiran maguna ba Koda ya kare musu kallo sai kawai ya kara bushewa da dariya akaro na biyu Sannan ya dubi bahjaht yace Yanzu ke banda rashin kunya irin taki har kina tunanin wai akwai wani mutum wanda zai iya zuwa ya ketare duk dajijjikan da suke kewaye da fadata araye kuma har ya shigo cikin nan ya kwace ku ya tafi daku? Gaskiya indai kuna wannan tunani na tabbatar muku cewa yaudarar kanku kukeyi Hatta sauro bai isa ya ketare dajin farko na zuwa nan a raye ba balle dan adam kuma makiyina Kuna nan zakuga yadda zanyi masa kisan gilla agaban idanunku Sannan kai kuma uzumnal a sannan ne zan kasheka Ke kuma gimbiya bahjaht zan aureki ta dole ko kinaso ko bakya so Koda jin haka sai tsoron komai ya gudu daga zuciyar bahjaht ta kalleshi tace Karyarka tasha karya baka isa ka aureni ba indai kuwa har kaga ka aureni to saidai in ka auri gawata Dajin haka sai sahibul ukub yayi murmushi sannan ya cillo mata wata siririyar wuka ya umarceta data kashe kanta da ita Take kuwa ta daga wukar ta buga a cikinta da nufin kashe kanta Koda wukar ta sauka acikinta sai taki ta huda cikin saidai ma narkewa da wukar tayi Sannan ya miko mata guba acikin kofi ya umarceta data sha Aikuwa koda ta kurba sai taga itama gubar taki ta cutar da ita Kai atakaice sai data jarraba bin hanyoyi da yawa don ganin ta kashe kanta amma duk sai suka ki yin tasiri Kawai sai yace da ita Yanzu dai kinga babu hanyar da baki bi ba don ganin kin kashe kanki amma sunki tasiri Saboda haka nake gargadinki da kada ki sake yin kuskuren yunkurin kashe kanki acikin gidan nan domin koda kinyi ba zaki sami nasara ba Saboda komai na gidannan a hannuna yake sai yadda na sarrafa shi kai in ta kaice muku ma yanzu kusan nine nake sarrafa wannan duniyar gaba daya don ke yanzu bara na nuna miki irin mutuwar da mahaifinki yayi akan idonki kuma babu abinda zaki iyayi Yana gama gama fadin haka sai yayi nuni da hannunsa zuwa jikin bangon fadar Take anan sai hoton duk abubuwan da suka faru a can birnin shawana ya bayyana har zuwa sanda mikiyoyin sihirin nan sukayi masa rubdugu sukayi masa kaca kaca da naman jikinsa Koda ganin wannan abu sai nantake taji tausayin mahaifinta sarki mayasin ya kamata har saida kwallar tausayi ta zubo daga cikin idanunta ita da uzumnal Koda ganin wannan kwallar acikin idanunsu sai sahibul ukub yayi guntun murmushi yace To yadda kukaga mutuwar wannan sarkin to haka a wannan bangon zakuga mutuwar shi hassanul basarin da kuke dora burinku akansa Koda gama fadin haka sai ya sake daukar su ya zura acikin akwatin ya tafi dasu can wani daki ya ajiyesu Wanda ya kasan babu komai acikinsa face wasu akwatinan irin wanda su bahjaht suke ciki Sannan ya dawo ya zauna akan kujerarsa ta haske ya cigaba da kallon duk abubuwan da duniya take ciki domin daga nan kan kujerar tasa Yake aikata shedancin a duniya Adaidai wannan waje sarkin kasuwa yimana yayi shiru ga barin labarin da yake baiwa gimbiya walisa Sakamakon jin karar kwankwasa kofar turakarsa Take ya rufe littafin da yake dauke da tarihin SADAUKI HASSANUL BASARI ya ajiye shi agefe sannan ya tashi a hankali yaje ya bude wata ýar karamar taga dake jikin kofar ya leka domin ganin wanda yake shigowa Koda ganin mai kwankwasa kofar sai jikinsa yayi sanyi Cikin sauri ya juyo da baya cikin sanda ahankali yace da gimbiya walisa Kinga abin danake ji miki tsoro ko ina mai baki shawara daki gaggauta ficewa daga cikin gidan nan domin yanzu haka sarki aryan ne yazo da kansa kuma na tabbata gurinki kamar yadda ba fada miki da farko Kodajin haka sai jikinta yayi sanyi ta kasa cewa uffan Sannan tace dashi kada ka damu bai kamata nayi amatsayinsa na sarki mai daraja bai kamata ayi masa haka ba Abinda yafi dacewa kawai shine mu tsaya muji abinda yazo dashi Wata kila zaton da kakeyi ba gaskiya bane akwai wata muhimmiyar maganar yakeson mu tattauna Tana gama fadin haka saita mike da kanta taje ta bude masa kofar Koda ta gama budewa sai tayi arba da sarki aryan cikin wata kyakykawar shiga irin tasu ta manyan sarakuna Kanshin turaren da yake jikinsa yazo ya bugi hancinsa kai saida ya kamsasa gidan da suke gaba dayansa Take duk su biyun suka tsaya kyam suna kallon juna kamar wadanda aka zare musu rayikansu Daga can sai gimbiya walisa tayi murmushi wanda ya kara fito da kyawunta Tace dashi sannunka da zuwa wannan gida Kai kuwa me kake bukata wanda har yasa ka taho da kanka baka aiko cewa mu muzo da kanmu ba ? Dajin wannan tambaya sai aryan ya maida mata da martanin murmushi Yace ai ba haka ya kamata ki karbi bakoba idan har yazo inda kuke Dukda naga cewa kinyi mini shumfidar fuska amma dukda haka ina bukatar kiyi min shimfidar tabarma don na samu darajoji guda biyu Take kunya ta kamata domin ta fahimci lallai maganarsa gaskiyace Sai kawai tace Kayi hakuri yakai wannan sarki mai daraja tabbas kayi gaskiya acikin maganar ka Tana gama fadin haka saita matsa ta bashi hanya ya wuce ya shige cikin falon da suke zaune ya zauna Cikin sauri sarkin kasuwa yimana ya mike ya kai gaisuwa ga sarki aryan Sannan ya tashi cikin sauri ya fice daga cikin falon ya barsu su biyu rak aciki domin yasan cewa ba gurinsa sarki aryan yazo ba Fitarsa keda wuya sai gimbiya walisa ta dawo kusa da kujerar da yake zaune ta zauna suka fuskanci juna Tsawon dakiku babu wanda yace da wani kala Daga can sai sarki aryan ya katse shirun dake tsakaninsu Ta hanyar yin gyaran murya sannan yace Tsawon lokaci babu wanda yace da wani uffan atsakanin mu Don haka amatsayina na namiji nine zan fara gabatar da kaina Yake wannan ýar sarki ki sani cewa ranar wanka ba'a boye ciki Don haka nakeso na sanar dake cewa Tun farkon sanda na ganki acikin filin gasa kafin fuskarki ta bayyana agareni Zuciyata ta kamu da tsananin kaunarki ba don komai ba sai don saboda kece mutum na farko wanda ya taba yi mini dukan da ya sakani har na kusa faduwa kasa Saboda karfin dukan naki, musamman ma lokacin da fuskarki ta bayyana agareni Sai take na kamu da tsananin kaunarki acikin zuciyata Ki sani tunda nake ban taba soyayyaba kuma ban taba ganin macen da zuciyata ta kamu da soyayyarta ba sai ke kadai Tundaga kuruciyata har zuwa girmana ban yarda da soyayyaba sai akanki na karyata kaina saboda yadda soyayyarki ta farmaki zuciyata alokaci daya Ina fatan ba zaki watsa mini kasa a ido ba ki ki karbar soyayyata Kodajin wannan batu sai gimbiya walisa gyada kai tana yin nazari acikin zuciyarta Daga can sai tace dashi yakai wannan sarki ayanzu banida ikon yanke hukunci akan bukatar dakazo da ita Saboda yanzu haka daka ganni bana baro gida bane kawai don in zagaya duniya ba Na rabu da iyayena kawai saboda neman dan uwana wanda kake tambayata dazu wato YARIMA WALISU YAYA ZATA KASANCE TSAKANIN SARKI ARYAN DA GIMBIYA WALISA? SHIN SU GIMBIYA BAHJAHT ZASU KUBUTA DAGA HANNUN BOKA SAHIBUL UKUB? SHIN SADAUKI HASSANUL BASARI YANA SAMUN NASARAR KETARE DAJIJJIKAN DA SUKE IYAKA DA TSUBURIN HAYATUL SIHIR? DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU AKASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR KUYI MINI UZURI SAKAMAKON RASHIN POST DA WURI AYYUKANE SUKE YI MINI YAWA HAKAN YASA BANA SAMUN DAMAR YIN RUBUTU KULLUM AMMA DUK DA HAKAN KULLUM SAI NA SAMI KORAFI AKAN RASHIN POST DA WURI DUK DA CEWA TUN KAFIN NA FARA POST DINSA NA FADA DUK KWANA 3 ZAN DINGA YIN POST DINSA************ZUBAR DA JINI *******;********7 PART A LBR ****************HABIBULLAH KBR Gimbiya walisa taci gaba da fadawaa sarki aryan cewa Babban burin mahaifinmu shine ganin cewa yarima walisu ya zama magajinsa idan shi ya mutu Tunda shi kadai ne namiji sai kuma ni da nake mace Kuma a ka'idar masarautar mu mace bata hawa kan karagar mulki Yanzu haka dan uwana ya kamu da wani wanda za'a iya kiransa da daukewar tunani Domin yana aikata mugayen abubuwa ne ba tareda saninsa ba Sakamakon ruhin wani takadirin boka wanda ya shiga jikinsa Shi dai wannan boka ana kiransa da sahibul ukub Tun daga sanda wannan ruhi ya shiga jikinsa tun daga nan ya koma zautacce Domin yana aikata mugayen ayyukane ba tareda saninsa ba Yanzu haka yaci birane da yawa yaki kuma atsawon wannan lokaci sau daya kurum na iya haduwa dashi Acikin biranen daya rushe kuwa akwai birnin da sarki ukibanu yake mulki Da kuma birnin tehran wanda sarki kalkus yake mulka Kuma acikin wannan birnin ne na hadu dashi gaba da gaba muka fafata yaki dashi Tabbas naji ba dadi ayayin wannan haduwa tamu domin saidaya bar mini babban tabo agadon bayana Take tasa hannunta ta kwaye gadon bayanta ta nunawa sarki aryan tabon kunar da jarumi walisu yayi mata Taci gaba da cewa kaga wannan kunar bata wuta bace Ta sihirinsa ce domin yanzu idan jarumtaka kakeji da ita Ko kuma karfin sihiri to walisu yafika domin koda matsafa da jaruman duniya zasu hadu bazasu taba samun nasara akansa ba Amma ni yanzu tabbas ina ganin alamun nasara acikin aikin dana fito domin nice kadai wanda ya tabayin gaba da gaba dashi ba tareda ya hallaka ni ba Asalima dalilin dayasa yanzu ya dakata da kai hare hare shine Wai ya daga mini kafane har sai na sami lafiya sannan zai cigaba da zaluncin da yakeyi Abinda bai sani ba shine tuni na sami lafiya daga wannan ciwon sakamakon haduwa da wani saurayi acikin mafarki na Nantake ta kwashe labarin abindaya wakana tsakaninta da wannan bakon saurayin ta fada masa Duk wannan maganganu da takeyi sarki aryan jinta kawai yakeyi domin bashi da burin daya wuce yaji ta bashi amsar bukatar daya nema agurinta Saboda haka kawai sai ya girgiza kai yace Gaskiya acikin maganganun nan da kikayi mini akwai ban al'ajabi acikinsu Amma yanzu abu daya kawai nakeso ki furta mini shin zaki amshi soyayyata ko kuma ba zaki amsaba? Dajin wannan tambayar sai tayi murmushi tace karka damu amma ni yanzu banidA ikon amsar soyayyar kowanne da namiji har sai na cikawa mahaifina burin rayuwarsa Ni kuma nayi alkawarin daga wannan lokacin zan baka amsar wannan bukata taka Kodajin wannan batu sai sarki aryan yayi murmushi sannan yace Ai shikenan rana bata karya zan jira zuwan wannan lokaci kuma zanyita kewarki har zuwa sanda zaki dawo Yana gama fadin saiya tashi yayi mata sallama sannan ya kama hanya ya fice daga cikin gidan Fitarsa keda wuya sai mayasin ya shigo cikin dakin Da zuwa saiya dubi walisa yace kinga abinda nake fada miki ko Ina mai hada ki da girman iyayenki ki tashi ki tafi cika aikin dake gabanki Kafin soyayyar sarki aryan tayi miki kamun da zai haifar miki da matsala akan aikin dake gabanki Yanzu haka baki san irin mugun barnar da yake aikatawa ba acikin duniya Ya kamata ki fita yanzu ki je ki ceci rayukan miliyoyin rayuka daga halaka Dajin haka sai tayi sauri ta tari bakinsa tace Duk abinda kake zaton zai faru ni na tabbatar maka da cewa bazai faruba Domin nasan darajar aikin da yake gabana Kuma idan har ina cikin birnin nan ina mai tabbatar maka da cewa Walisu bazai kara yukurin kai wani farmakin ba Ni yanzu na sallami sarki aryan kuma na tabbatar bazai dawoba Don haka saika zauna yanzu ka karasa mana hikayar SADAUKI HASSANUL BASARI Har zuwa karshe domin naji yadda zata kasance tsakaninsa da boka sahibul ukub Dajin wannan batu sai kawai mayasin ya garzaya ya dauko littafin Ya ajiye amma shi azuciyarsa ba haka yaso ba Take ya bude littafin yaci gaba da bata labari kamar haka ****** ******** ******* Al'amarin sadauki hassanul basari da aljani hadimul islam kuwa lokacin da suka nufi hanyar da zata kaisu can dajin duniyar mutuwa Sai sukayita tsala azababben gudu na gaban kwatance acikin sararin samaniya Suna wucewa ta saman kasashe, duwatsu da tekuna Saida suka shafe mako biyu suna gudu asararin samaniya babu abinda yake sauko dasu kasa face Idan lokacin ibada yayi, ko kuma wani uzurin daban Kuma atsawon wadannan makonni kullum tare sukeyin hirarsu ta abindaya shafi rayuwa hakane yasa abota mai karfi ta shiga tsakaninsu Akwana na sha biyar dinne suka iso wani babban daji Mai cike da rairayi kai da ganinsa kasan cewa dole ne ayi rashin ruwansha acikinsa Domin ko dabbobin daji masu rayuwa babu acikinsa Koda isowarsu bakin wannan daji sai aljani hadimul islam ya saki fukafukansa ya sauko kasa bisa turba har saida kura ta tashi sakamakon saukar su Sannan ya juyo yace da hassanul basari yanzu haka mun iso dajin da yake dagashi sai shiga dajin duniyar mutuwa Yanzu tazarar dake tsakanin mu da dajin duniyar mutuwa tafiyace ta rabin sa'a Kuma anan ne kukayi alkawarin rabuwa dakai ni zanyi zaman jiranka Har zuwa sanda zaka dawo mu kama hanyar komawa gida tare Kodajin haka sai nan take sadauki hassanul basari ya daka tsalle daga kansa ya durgo kasa Yace ai shikenan yanzu saika jirani naje na dawo, dajin haka sai hadimul islam yace Inayi maka fatan nasara kuma sai ka zage damtse domin kubutar da duniya daga barazanar da wannan azzalumi ya sa musu Nima naso ace dani za'a shiga cikin wannan daji amma babu yadda zanyi dolene na tsaya anan domin cika umarnin malan ramadan Nantake hassanul yayi masa sallama sannan ya yakama hanyar shiga cikin dajin duniyar mutuwa Bisa kafafunsa Awannan lokaci baice zaiyi gudu ba kawai tafiya yake cikin nutsuwa kuma ko kadan babu alamun tsoro ko kadan akan fuskarsa Bai dade da fara tafiya ba ya fara hango farkon dajin duniyar mutuwa Dajine wanda ya fita daban da sauran irin dajijjikan duniya Cike dajin yake da wasu irin manyan duwatsu farare kal Kuma kowanne dutse yana da siffar bakaken aljanu a jikinsa Irin wadannan duwatsu gasu nan birjik ako ina a cikin dajin duk inda ka duba su zaka gani burjik kuma dole saika ratsa ta cikinsu sannan zaka wuce gaba Kallo daya zakayiwa wadannan duwatsu kasan cewa dole akwai tuggun da aka shirya agurin Koda isowarsa bakin wannan dajin sai kawai ya danna kansa ciki ba tareda shakkar komai ba Tamkar yana tafiya ne acikin gidansa, kuma duk da hakan yana tafiyar yana hadawa da yin nazarin wadannan duwatsu Saida ya shafe sa'a guda yana tafiya atsakanin wadannan duwatsu Sai kawai ya dinga gani wadannan duwatsu sun fara wata irin kara mara dadin sauraro kuma suna kara kumbura girmansu yana daduwa fiye da yadda suke abaya Kafin adau wasu lokuta masu yawa kawai sai wadannan duwatsu suka dinga fashewa suna tarwatsewa a sama Wasu irin mugayen aljanu masu matukar muni da girman gaske suka dinga fitowa daga cikin wadannan duwatsu Adadin aljanun kuwa yakai kimanin dubu goma kowanne daya daga cikinsu Yana da matukar girma da munin gaske domin idan mutum ya fiya kallonsu ma saisu iya sakashi yayi amai Wani irin bakin yawu mai kumfa yana fitowa daga cikin bakin nasu Kai da ganin wadannan aljanu dolene su kasance azzalumai kuma masu cin naman bil'adama Koda bayyanar wadannan bakaken aljanu sai sukayiwa sadauki hassanul basari kawanya suka sakashi a tsakiya ta yadda babu yadda zai iyayi ya wuce face ya ratsa ta tsakaninsu Koda suka gama zagaye sai kuma suka taho da gudu kamar da hadin baki sai suka taho da gudun gaske da nufin su dasa masa wawa ta yadda wani ma ko digon jini ba zai samu ba Koda ya rage baifi saura taku daya su turmushe hassanul basari ba Sai kawai yayi sauri ya zare takobinsa sannan ya daka tsalle ya tashi sama kamar tsuntsu atsakiyarsu Koda suka hadu a tsakiya sai suka dinga gware da kawunansu suna zubewa kasa ba tareda sun sani ba Kafin su ankara tuni ya falfala da azababben gudu ta saman kawunansu ya wuce gaba Daga inda suke har ya fice daga cikinsu ya sauka acan karshensu Tare da tsayawa da gudun ya tsaya cak hannunsa daya rike da takobinsa Dayan kuma yana yafuto su dashi da nufin yana kiransu da nufin in sun isa su taho a kafsa Koda aljanun sukaga abinda yake musu sai Nantake suka dinga mikewa zumbur Suna wani gurnani mara dadin sauraro suka rugo da gudun gaske inda yake Koda suka riske shi sai suka kachame da azababben yaki na gaban kwatance mai matukar firgitarwa Nanfa aljanun suka dinga kawo masa mugayen hare hare da wasu adduna dake ruke a hannayensu da nufin su yi gutsun gutsun da namansa Shi kuwa kokadan yaki ya basu damar hakan sai gashi yana saransu da takobinsa kamar jikinsa bana jini da tsoka bane Nanfa aka hada wani gagarumin gumurzu wanda za'a iya kiransa da turnuku fadan iblisai Domin mutum dayane kachal ya shiga tsakanin dubunnan aljanu yana kafsa yaki dasu kuma ko kadan sun rasa yadda zasuyi dashi Domin ya zame musu kamar kadangaren bakin tulu Shi kuwa kawai saransu yakeyi suna zubewa kasa Amma saboda tsananin taurin ransu sai kaga suna mikewa tsaye suna dada dawowa kamar babu abindaya samesu Sun kara dawowa an ci gaba da kafsawa duk da cewa ga jini nan yana zuba ajikinsu amma hakan bai damesu ba Wannan al'amari ba karamin baiwa hassanul basari mamaki yayi ba Don haka sai ya canja salon fada kawai sai ya dinga hadawa da hannunsa da kafafuwansa wajen yi musu kyakykyan naushi da kuma duka Duk wanda ya daka da hannunsa ko kafarsa saidai kaga duk inda ya daka da hannunsa saidai kaga ya karya kashushuwan jikinsa saboda tsananin karfin dukan nasa Kafin ajima yayiwa sadannan aljanun mummunar barna Koda aljanun sukaga yadda yake ta illatasu ba tareda sun sami nasarar koda lakutar fatar jikinsa ba Sai dukkansu suka fusata suka kara tasowa kansa da dukkan karfinsu da nufin su tattakashi ta yadda zasu dagargaza naman jikinsa Koda hassanul basari ya fuskaci mugun nufinsu sai take yayi kukan kura wanda saboda karfin ihun nasa saj da zuciyoyinsu suka buga da karfi Kawai sai ganinsa sukayi yana daka tsalle atsakiyarsu yana kama kawunansu yana murdewa da hannayensa Wohoho hakika jarumtaka baiwa ce kuma wanda allah ya bashi baiwarta ys wuce raini agurin kowa Domin wata irin jarumtaka ya dingayi wacce hankali bazai daukaba Saidai kaga idan ya kama kan aljani duk girmansa saidai kaga ya jijjige kan daga daga jikin gangar jikin ya cizgeshi ya wullar dashi agefe Take gangar jikin zata fadi bisa doron kasa matacciya ba tareda koda ta shura ba Nanfa salon fada ya canja salon gani in banda sautin karar karyewar kashushuwa da jijiyoyin wuyan aljanun babu sautinda kunne yakeji Kafin a dau lokaci mai tsawo tuni yayiwa aljanun muguwar barna Kuma ya zubar da kaso biyu cikin ukunsu Nanfa dajin ya cika da gawarwakin wadannan aljanu ko ina ka duba babu abinda idonka zai nuna maka face gawarwakin su ko ina birjik da kuma jinin jikinsu wanda yayiwa kasa ado Kafin a kara daukar wani lokaci tuni ya gama zubar dasu akasa babu wanda yayi saura acikinsu Sannan ya tashi ya cigaba da tafiya bisa kafafunsa ya nufi hanyar da zata kaishi daji na gaba Acan cikin fadar boka sahibul ukub kuwa lokacin dayaga su sadauki hassanul basari da aljani hadimul islam sun iso bakin daji na farko Sai ya kawai ya karanta wasu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya saiga akwatin daya ajiye su gimbiya bahjaht ta bayyana agabansa Sannan yasa hannu ya bude akwatin ya zube su agabansa Yace dasu kamar yadda nayi muku alkawari tun farko cewa tare daku zamuga irin mutuwar da wannan babban makiyin nawa zaiyi To zan cika muku wannan alkawarin don haka sai ku zauna ku zuba idonku ajikin bango fadar nan kuga mutuwar wulakancin da zaiyi Dajin haka sai bahjaht ta girgiza kanta sannan tace lallai har yanzu baka san kowanene hassanul basari ba amma yau zaka fara sanin kowanene shi Tana gama fadin haka sai ta zauna agefe suka harde kafafunsu Ita da uzumnal Suka zuba idonsu akan bangon fadar Nanfa suka fara ganin

Chapter 12 of 17