Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan ranar Da gama wannan zancen zuci sai kawai tayi murmushi sannan taci gaba da tafiya HAKIKA RASHIN SANI YAFI DARE DUHU INDA ACE TASAN ABINDA ZAI FARU DATA HAKURA DA WANNAN RANGADI GABA DAYA TA KOMA GIDA Aikuwa tana cikin yin tafiyar tatane tare da dakarunta Ba zato ba tsammani sai taga gari yayi duhu yadda ko tafin hannunka bazaka iya gani ba Daga can kuma sai kasa ta fara girgiza tana haifar da wawakeken rami Koda ganin wannan al'amari sai nantake dakaru sukazo sukayiwa gimbiya bahjaht kawanya domin bata tsaro Daga can kuma sai sukaji an bushe da dariya mai kama da kukan jaki wadda tayi sanadiyar tayar da kura abirnin gaba ki dayansa Sannu ahankali komai ya lafa gari yayi haske kwatsam sai suka ga wani katon basamuden dodo ya bayyana Ko'ina ajikinsa a murde yake kamar curin duwatsu, idanuwa kuwa basa iya ganin karshen tsawonsa Domin ya tokare ko'ina saidai ka gani iya kallonka Hannunwansa kuwa guda saba'in ne, kowanne daga cikinsu yana dauke da dogayen yatsu masu dauke da kaifi da tsini, Koda bayyanar wannan dodo sai nantake sarkin yaki ukairu ya nunashi da yatsa da nufin ya jefishi da kibiyoyin tsafi Take kuws kibiyoyin sukayi fitar burgu daga jikin yatsunsa sukayi kan wannan dodon Koda saukar kibiyoyin ajikinsa sai take suka kakkarye suka zube kasa Kafin suyi wani yunkuri tuni dodon ya zuro hannunsa guda daya ya shuri gabaki daya dakarun harda dawakansu Ya dagasu sama ya watsasu cikin wakeken bakinsa mai girman gaske gaba dayansu ya taunesu, Kodasu gimbiya bahjaht da kuyanginta da mutanen gari sukaga abindaya faru ga wadannan dakaru Sai dukkansu suka figice Suka fara gudun ceton ransu, da ganin haka sai wannan dodon ya bushe da dariyar mugunta Take kashushuwan mutane dana dawakan nan suka dinga zubowa ta cikin hakoransa, Da ganin haka sai kowa ya kara firgita suna ihun neman taimako domin sunyi imani da cewa basu isa su tsira daga sharrin wannan azzalumin dodo ba 0=======(:::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Acan cikin kasuwa kuwa sadauki hasanul basari tafiyar sa kawai yakeyi Ba tareda sanin dalilin dayasa mutane suketa faman rububin kallonsa ba Har ya isa bakin wata katuwar rumfa wacce ajikinta aka kafe allon sanarwar cewa suna sayen fatun dabbobin daji Da kyar da makyarkyata mai rumfar ta roki mutane kan suyi hakuri Idan hasanul basari ya fito sai su hadu dashi acan wajen Sannan ya zo sukayi cinikin fatun dabbobin ya dauko dinare masu yawa ya bashi Suka rabu sadauki hasanul basari ya fito daga rumfar ya kama hanyar komawa can kauyensu kenan Kawai sai yaga bakin hadari ya hado da kuma girgizar kasa acikin garin Koda aka dan jima sai yajiwo ihun mutane daga can nesa da inda yake Dajin wannan ihun sai nan take ya falfala da zababben gudunsa Mai kama dana tauraruwa mai wutsiya ya nufi gurin da yake jiwo wannan ihun Adaidai wannan lokacin ne dodon ya zuro hannunsa kasa da nufin ya shuri gimbiya bahjaht ya watsata abakinsa ya tauneta kenan Kwatsam sai ga sadauki hasanul basari ya baiyana agurin Yana zura sai yayi sulu ya tafi akwance yabi ta karkashin kafafun dodon Kafin hannunsa ya sauka kan gimbiya bahjaht tuni hasanul basari ya shureta kamar jaririya Yayi can gefe da ita, Itakuwa awannan lokacin ta kame domin ta saddakar da cewa ta mutu Ba tareda bata lokaci ba ya juyo ya fukanci wannan dodon gaba da gaba Koda dodon yayi arba da shi agabansa sai kawai ya sunkuyo da kansa kasa yace dashi cikin wata kakkausar murya Kai yaro hakika kayi matukar kuskuren kawo kanka zuwa ga halaka tun kafin lokacin ka ya cika Ka sani tunda nakeyin bauta ga uban gidana mai girman daraja sahibul ukub Ba'a taba samun mahalukin daya tsira daga hannuna ba…. Kafin ya gama fadin abinda yakeson fada fada sai hassanul basari ya saka masa tsawa yace Kai karya kakeyi ni nayi maka alkawarin daga kai har uban gidanka Saina rabaku da wannan duniyar gaba dayanta. Yana gama fadin haka ya zare takobinsa ya falfala da azababben gudu Zuwa kan dodon koda yazo daidai inda yake sai nantake ya daka Tsalle ya dirga akan cinyar dodon tareda kai masa wani mummunan sara Koda takobin ta sauka ajikinsa sai yaji kamar ya sari dutse Kafin shima yayi wani yunkuri tuni dodon ya cilloshi daga kan cinyar tasa sannan yasa kafa da nufin takeshi Cikin bakin zafin nama ya daka tsalle ya kaucewa harin dodon Koda kafar dodon ta sauka akan kasa sai gashi ta haddasa wani wawakeken rami Zurfin gaba dubu don saida kusan kaurinsa ya nutse acikin ramin Take suka hargitsa wannan filin domin wani irin azababben bakin gumurzu suka dinga yi Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda sadauki hasanul basari yake iya kaucewa munanan hare haren dodon ba tareda ya sami nasararvkoda taba fatar jikinsa Su kuwa su gimbiya bahjaht da sauran kuyanginta kamewa sukayi kyam kamar gumaka suna kallon wannan bakin gumurzun Musamman ma ita gimbiya bahjaht don ita ba yakin take kalloba Tsananin kyawun sadauki hasanul basari take kallo domin awannan lokaci sai taji ta raina nata kyawun, har ta tambayi kanta tace to wai shin inda ace shi mace ne to wanne irin kyawu zaiyi? Tabbas inda ace mace ne shi saidai akirashi da sarauniyar kyawawan duniya, kodayin wannan tunani sai nantake taji ta kamu da tsananin soyayyarsa Har tana fada acikin zuciyarta cewa, tabbas kota halin kaka sai na mallaki wannan jarumi amatsayin abokin rayuwa ta Kawai sai kuma wata zuciyar tace da ita Kul ! Kada ki kuskura kice zakiyi haka domin zaki zubar da darajar ki ne a'idon duniya wata kilama yaki amincewa dake Haka dai ta dinga tunani kala kala, Can kuwa al'amarinsu sadauki hasanul basari koda yaga sun dauki lokaci mai dan tsawo suna fafata yaki da wannan dodo Kuma yana ta bata masa lokaci, sai kawai ransa ya baci Ya kara harzuka fiyeda ko yaushe, ya canja salon fada Ya dinga hadawa da tsalle tsalle yana hawa jikin dodon kamar kadangare Shi kuwa dodon saiya dinga kawo masa duka da hannayensa Amma kafin hannayen su sauka ajikinsa tuni ya daka tsalle yabar gurin ya kara hawa sama Saidai kaga idan hannuwan suka sauka aduk gurin da sadauki hasanul basari ya bari da zarar hannun dodon ya sauka agurin sai kaga wajen ya dare jini yayi tsartuwa Wannan itace damar daya dinga samu, don kafin ajima da fara haka har jikin dodon yayi jina jina da jini, kuma kuzarinsa na dada raguwar saboda jinin da yake zuba ajikinsa, Ana cikin wannan hali ne kawai sai hassanul basari ya daka wani mahaukacin tsalle kamar daga jikin baka aka harbashi Sai gashi ya sauka akan kafadun dodon sannan ya kara daka wani tsallen akaro na biyu ya dira akan wuyansa Kawai sai yasa hannuwansa guda biyu ya kama kan dodon da dukkan karfinsa ya murde masa wuya Take kuwa dodon yayi wani irin mahaukacin ruri na fitar rai sannan kuma sai nantake ya tarwatse ya bace bat aka daina ganinsa sai ganin sadauki hasanul basari kawai saujayi akan iska yana saukowa kasa Kamar tsuntsu mai fuka fukai, Kodaya gama saukowa kasa bisa turba sai kawai suka hada idanu da gimbiya bahjaht Take anan kowa yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske kamar zata faso kirjinsu ta fito waje SHIN MENENE TSAKANIN GIMBIYA BAHJAHT DA KUMA SADAUKI HASANUL BASARI? SHIN HASSANUL BASARI ZAI KARBI SOYAYYAR GIMBIYA BAHJAHT? WANENE YA TURO WANNAN DODO ZUWA BIRNIN FASAWANA KUMA ME YAZO YI? DON SANIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI MU HADU A KASHI NA GABA DON JIN KARASHEN WANNAN KAYATACCEN LABARI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN+++++++++ZUBAR DA JINI ++++++++++3 PART C LBR +++++++++++++++habibullah KBR Nanfa suka kurawa junansu idanu kamar gumaka ko kifta idanunsu basa iya yi Sai daga baya hassanul basari yayi sauri ya kawar da fuskarsa ga barin kallonta Adaidai wannan lokacin ne mahaifinta sarki mayasin ya karaso gurin bayansa tare da dakaru kimanin dubu biyu a bayansa Dukkansu sunyi shigar yaki mai bantsoro Kai kayi zaton duniyar zasu yaka Sun fito domin suga abin da yake faruwa, Tun daga nesa ya dinga hango irin kallon da gimbiya bahjhat da hassanun basari suke yiwa junansu, Harma ya lura da jarumi hassanul basari ya kawar da fuskarsa ga barin kallonta amma ita har yanzu hankalinta yana kansa Don haka koda ya iso inda suke kawai saiya shiga tsakaninsu da dokinsa sannan yaja linzamin dokinsa ya tsaya Koda jarumi hassanul yayi arba da sarki agabansa sai kawai ya rissina agabansa domin girmamawa Ita kuwa har sannan bata lura da abinda yake faruwa saboda gaba daya ruhinta ya fita daga jikinta Har saida sarki mayasin ya dora hannunsa akan fuskarsa Sannan ta farfado daga duniyar data shiga don haka Koda tayi arba da mahaifinta agabanta sai taji kunya ta kama ta don haka sai kawai tayi murmushi Sannan ta kalli hasanun basari tace ina yakai wannan jarumi ina matukar godiya agareka bisa wannan taimako da kayi mana Don ba don kaiba da tuni mun dade da zama shekakku Dajin wannan batu sai hassanul basari ya mayar mata da martanin murmushi Shikuwa sarki mayasin sai ya hade fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa Kawai sai ya yiwa hassanul basari godiya bisa taimakon da yayiwa ýarsa Sannan itama ya umarceta data kama hanya ta tafi gida Take kuwa aka kawo mata ingarman doki ta hau suka jera da mahaifinta Har sun danyi nisa sai kawai taja linzamin dokinta ta juyo suka hada idanu da hassanul basari Take sukayiwa junansu wani irin tattausan murmushi Kuma duk wannan abu daya faru sarki mayasin ya gani Don haka sai yaji kamar ya kwallara ihu saboda bakin ciki Ahaka dai har suka isa cikin gidan sarauta kowa ya koma cikin bagarensa Adaidai wannan lokacin ne wata kuyanga ta kawo mata kwanukan abinci da kuma na abubuwan sha Ta ajiye mata su ta kama hanya ta fice Ba tareda bata lokaci ba ta taso ta zauna akan kujerar da take fuskantar teburin ta mika hannunta cikin kwanon abincin Kwatsam sai taga fuskar hassanul basari aciki yana yi mata murmushi Nantake ta mike tsaye zumbur cikin razani ta dan ja baya Sai asannan ne ta gane cewa bashi baneba gizo kawai yakeyi mata Amma duk da haka sai ta kasa cin abincin domin duk sanda ta kai hannun shi take gani Nantake tace acikin zuciyarta wai shin menene yake shirin faruwa dani ne Domin ban taba shiga cikin irin wannan yanayi ba ABINDA BATA SANI BA SHINE SOYAYYA CE TA SHIGA CIKIN ZUCIYARTA Ahaka dai ta samu tayi barci amma duk da haka acikin mafarkin nata babu abinda take gani face shi Har gari ya waye ++++++++++++++++++++++++++++ Shi kuwa sadauki hasanul basari tunda suka rabu da gimbiya bahjaht Sai yaji gaba daya yanayin sa ya sauya domin in banda tunanin ta babu abinda yakeyi Ahakane yana cikin tafiya acikin daji kawai sai ya iso bakin wata korama wacce ruwa yake gudana acikinta Take ya karasa bakin koramar ya sunkuya da nufin ya sha ruwan cikinta Kwatsam sai ya hango surar jikin gimbiya bahjaht aciki tana sanye da wasu korayen tufafi tana yi masa wani irin tattausan murmushi Koda ganin wannan al'amari sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske Yace tabbas a wannan lokaci bazan yaudari kaina ba domin ko shakka banayi soyayyar gimbiya bahjaht ta shiga zuciyata Kuma dolene nayi kokarin cire soyayyarta daga cikin zuciyata tunda aurena da ita bazai taba yiwuwa ba tunda ita bata kasance musulma ba Haka dai yayi ta sake sake acikin zuciyarsa har ya isa can sansaninsu Da zuwansa sai ya iske ýan kabilarsu sun fito sun tsaya suna jiran dawowarsa gaba daya sun kagu da dawowarsa saboda sunsan dole akwai wani abin daya hanashi dawowa akan lokaci Koda sukaga dawowarsa sai duk suka kamu da farinciki suka taho suka tarbeshi Take ya kwashe labarin komai ya shaida musu abindaya faru Bayannan ya dauko kudadan su gaba daya ya raba musu Awannan rana dai duk kokarin da jarumi hassanul basari yayi d0n ya cire tunanin gimbiya bahjhat daga zuciyarsa saida yayi amma ya kasa Domin duk sanda ya rufe idanunsa babu abinda yake gani face fuskar gimbiya bahjhat Wannan al'amari ba karamin firgitashi yayi ba. Ahaka ya kwana har gari ya waye Koda gari ya waye yayinda jarumi hassanul basari ya fito daga cikin dakin da yake kwana Kawai sai sukayi kichibus da wani kanin mahaifinsa mai suna hubairu Koda suka hadu dashi sai ya kalli idanun jarumi hassanul basari yaga alamun baiyi barci ba awannan daren Koda ganin haka sai ya kirashi gurinda yake ya tambayeshi kan ya fada masa gaskiyar abindaya faru acikin birnin Take kuwa ya kwashe labarin komai ya fada masa kodajin wannan labari Sai fuskar hubairu ta cika da murmushi sannan yace dashi Yakai dana kada ka damu da wannan al'amari shawarar da zan baka itace duk sanda kuka hadu da gimbiya bahjhat to ka baiyana mata sirrin da yake cikin zuciyarka Ni kuma nayi imani da cewa ba zata ki amsa maka ba domin kai na daban ne Bayan haka kuma wata kila ta sanadiyar haka ta karbi musulunci Kaga idan haka ta faru kamar ka jefi tsuntsu biyu da dutse daya ne Don haka ka shirya haduwa da ita ako wanne lokaci kar kaji kunyar fada mata sirrin da yake zuciyarka Da gama fadin haka saiya wuce yabar hassanul basari atsaye kyam domin jin maganar yake kamar tatsuniya Acan gidan sarautar sarki mayasan kuwa bayan daya shige cikin turakarsa Sai ya kasa zaune ko tsaye sakamakon fargabar data cika zuciyarsa Domin babu shakka abinda yake gudu shine yake neman faruwa Domin ya kula da irin kallon da bahjaht da hassanul basari suka dinga yiwa junansu Lallai kallone mai cike da alamun soyayya kuma tabbas Idan har baiyi da gaske ba to yana daf da rasa ýarsa jar abada Domin idan yayi sake soyayyarsa ta shiga zuciyar ta to shi kansa bai isa ya iya sarrafata ba Saboda aurenta da hassanul basari bazai taba yiwuwa ba face ta karbi addininsa na musulunci Shi kuwa bazai taba bari hakan ta faru ba domin zai zama abin yi masa gori acikin ýan uwansa sarakai Kuma da hakan ta faru gwanda ya rasa ýar tasa gaba daya Koda yaga zuciyarsa bata sami nutsuwa ba Sai kawai ya tashi da kafafunsa ya nufi can bangaren da take Koda zuwansa sai kawai ya danna kansa cikin dakin kai tsaye ba tare da neman izini ba Da da shigarsa cikin dakin sai kawai yayi arba da ita a zaune agaban kwanukan abincin da aka kawo mata Ta zauna tayi tagumi kawai tana kallon abincin ba tareda tayi koda loma daya ba Tana kallon abincin kawai tana murmushi kamar tana tattaunawa da wani, Koda ganin wannan al'amari sai kawai ya girgiza kansa kuma yaki yayi mata magana Sannan ya juya ya fice daga cikin turakar tata ya kama hanyar komawa tasa turakar Ita kuwa gimbiya bahjhat gari na wayewa saita tashi Ta kira wani amintaccen badakarenta mai suna uzumnal Shidai uzumnal yakasance amintaccen ta ne kuma abokintane domin tare suka taso Kuma sun shaku dashi sosai don haka babu wanda ta yarda dashi aduk cikin hadimanta kamar sa Saboda haka ne ma duk wasu aiyukan sirri take nemansa idan tanaso tayi su daidai Da zuwansa sai ya tsugunna har kasa ya gaisheta sannan yace Ya shugaba ta me kike da bukatar nayi miki yanzu take na aiwatar Dajin wannan batu sai tayi murmushi sannan tace dashi Inaso ne kayi mini rakiya zuwa can sansanin kabilar banu sudes Domin na gano saurayin daya ceci rayuwata kuma nayi masa godiya Dajin haka sai ya dago kansa arazane yace ya shugabata Wannan aiki da kike shirin yi ganganci ne babba arayuwarki ina mai rokonki da ki hakura da zuwa wannan guri Domin idan har mahaifinki ya gano cewa kinje wannan guri to babu shakka kasheni zaiyi Ina rokonki da darajar iyayenki daki hakura da wannan tafiya Kodajin wannan batu sai take ta daka masa tsawa akaron farko na rayuwarta sannan tace Shin kasan irin halinda ni zan shiga idan har na rasa hassanul basari? Dolene kayi mini wannan aiki, kuma ina mai tabbatar maka da cewa koda asirinmu ya tonu to bazan bari mahaifina ya cutar dakai ba Saidai duk irin hukuncin da zaiyi maka ni yayi mini shi, saboda haka saika shirya ka jira fatowata awajen gidan sarauta Dajin haka sai nantake ya tashi ya fice daga cikin turakar tata Sannan ita kuma ta tashi ta kewaye tayi wanka ta fito sannan ta caba ado na gani na fada Tana gamawa saita fito ta nufi hanyar fita daga gidan sarautar Duk inda ta gifta sai dai kaga dakaru suna gaisheta sannan kuma kaga sun kura mata idanu suna mamakin fitarta a daidai wannan lokaci don basu taba ganin ta fita a wannan lokaci ba Har gimbiya bahjhat ta fice sai kawai tayi wani dan tunani saita juyo Ta dawo wajen shugaban masu gadin tace dashi Kada wanda ya kuskura ya sanar da mahaifina wannan fitar tawa Duk wanda kuwa ya kuskura ya sanar dashi wannan sirri sai na sa an kasheshi Tana gama fadin haka sai ta fice daga cikin gidan ta nufi bayan gari inda zata hadu da hadiminta uzumnal………… . Adaidai wannan lokaci ne wani hadimi ya shigo cikin turakar sarkin kasuwa yimana Ya rissina yace ya shugabana lokacin gudanar da wannan gagarumar gasa yayi Dajin wannan batu sai sarkin kasuwa yayi murmushi sannan ya dubi Walisa yace To kinji lokaci yayi kamar yadda na fada miki cewa da zarar lokaci yayi zamu katse wannan labari mu tafi kallon wannan gasar jarumta Sai bayan mun dawo zamu cigaba da wannan labari Dajin haka sai walisa tayi murmushi sannan tace kada ka damu ni zan jira daga nan har a kammala wannan gasa Yana gama fadin haka saiya tashi ya shiga bangarensa yayi shiri Ya fito sannan su walisa suka tashi suka biyoshi abaya Amma saida walisa ta dauko bakin kyalle ta sake rufe fuskar ta dashi saboda tabbatar da tsaro Da fitowarsu daga cikin gidan sai sukaga awannan ranar birnin ya cika ya batse fiye da ko yaushe Da jaruman gasa da kuma baki maza da mata daga sassa daban daban Ahaka dai suka dinga ratsawa ta cikin mutane har suka isa filin Da kyar suka samu aka budawa walisa hanya ta shiga cikin filin ta zauna Shikuwa sarkin kasuwa yimana saiya wuce izuwa cikin Wata katuwar rumfa wacce take can karshen filin gasar Akasanta an jera kujeru na alfarma wadanda manyan mutane zasu zauna acikinsu Acikin jerun kujerun kuwa an ware wata guda daya wacce tafi kowacce girma da kawatuwa Kuma ita kadaice babu kowa akanta sai kuma wacce sarkin kasuwa ya zauna akanta amma ragowar duk an zauna akansu Akasan filin gasar kuwa mutanene birjik suketa tururuwar shigowa domin kallon wannan gasa Wasu kuma da suka zo da wuri sun sami kujeru sun zazzauna Wadanda kuwa suka makara sai kan katangu suka dinga hawa don kallon gasar Domin sunsan cewa dolene kowa ya morewa idonsa kallo Ana cikin hakane sai aka fara jiyo sautin bugun ganguna da busar sarewa suna tashi daga can hanyar tahowa daga gidan sarauta Nanfa kallo ya koma can hanyar da wannan sauti yake tahowa Daga can kuma sai ga dakaru masu dumbun yawa suna tahowa daga ta wannan hanyar Rike da makaman yaki masu matukar ban tsoro, suka firfito suka kewaye gaba daya hanyar da sarki aryan zai wuce Awannan lokaci gaba daya jaruman gasa sun gama hallara afilin jira kawai suke sarki ya fito afara wannan gasa Duk wanda ka kalla acikinsu kasan dolene ya kasance jarumin gaske Bayan lokaci kadan sai ga sarki aryan ya taho cikin shigar kayan sarauta masu kyawun gaske, da tsada Kalar kayan da yasa kuwa sun kasance shudin launi mai haske Kuma kayan sun matse jikinsa ta yadda suka nuna tsantsar kyawun surar jikinsa da kuma murdewar jikinsa Ya sanya wata hula akansa wacce aka kerata da zallan zinare Kuma anyi mata alamar hannun mutum rike da takobi a samanta A jikin kugunsa kuwa ya daura wata takobi wacce aka kera kubenta da zallan dutsen lu'u lu'u Tun daga nesa haskenta ya dinga dallarewa mutane ido Koda mutane sukayi arba dashi cikin wannan kyakykyawar shiga sai suka rude da ihu suna koda shi tareda yi masa kirari Har sai da yaje kan kujerarsa ya zauna sannan akayi tsit ana jiran jawabinsa Bayan kowa ya gama bada hankalinsa sai kawai ya mike ya fara bayani kamar haka Yaku mutanen wannan birni namu mai tarin albarka da kuma wadanda sukazo daga wasu kasashen Domin shiga ko kallon wannan gagarumar gasar jarumtaka inayi muku barka da zuwa wannan birni namu Sannan bayan haka kowa ya sani nima ina daga cikin jaruman wannan gasa Don haka banida ikon gabatar da jawabi a wannan lokaci sai munji abinda alkalan gasa suka yanke game da wannan gasa Saboda haka yanzu sai mu saurari bayani daga bakinsu Yana gama fadin haka sai ya sami guri ya zauna akan karagarsa Sannan alkalin gasa shima ya mike tsaye ya fara nasa jawabin da cewa Ina yiwa jaruman gasa barka da zuwa wannan gasa mai albarka Bayan haka kamar yadda kuka sani wannan gasa anayintane da zallan karfin damtse Ba'a yadda wani yayi amfani da sihirin tsafi ba acikinta Duk wanda aka kama kuwa za'a ci shi tara mai yawan gaske Acikin wannan gasa ni kaina inajin akwai wani babban abin al'ajabin da zai faru Domin naga yadda jaruman gasa suka cika wannan fili da kuma ýan kallo wadanda ba'a taba samun masu yawansu ba Duk jarumin daya lashe wannan gasa sarki yayi masa alkawarin zai bashi dukiya mai tarin yawa sannan zai bashi kambun wannan gasar da hannunsa Saboda haka ina mai shawartar jarumai dasu kara zage damtse domin ganin sun sami nasara akansa Ita dai wannan gasa zamu kasata kaso uku ne ayau zamu gudanar da zagayen farko Wadanda suka haye shi to sune zasu zo kuma su hadu a zagaye na biyu Sannan duk wanda ya zama zakaran gwajin dafi acikin su To shine wanda zai kara da mai girma sarki aryan a rana ta uku SHIN YAYA WANNAN GASA ZATA KASANCE? WANENE ZAI LASHE WANNAN GASA? WANNE IRIN ABIN AL'AJABI NE ZAI FARU ACIKINTA ? INA LABARIN JARUMI WALISU DAN UWAN JARUMA WALISA? DON SAMUN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU. HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEM+++++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++++++++ 4 PART A LBR ++++++++++++++HABIBULLAH KBR Acikinsu ne zamu fitar da zakaran wannan gasa saboda haka yanzu muna da bukatar jaruman gasa gaba daya su hallara acikin fili Bayan haka kuma a wannan karon ba'a yarda kowa yayi amfani da makaminsa ba Amma zamu bashi irin makamin da ya iya amfani dashi Yana gama fadin haka take yasa aka budewa jaruman gasa hanya suka shiga tsakiyar fili suka yi layi sahu sahu Sannan wasu dakaru suka shigo da makaman yaki masu yawa kala daban daban suka ajiye Bayan nan aka umarci kowa da yaje ya dauki kalar makamin da ya iya amfani dashi ba Take kuwa koya yaje ya dauki kalar nasa na ainihin kuwa ya ajiyeshi agefe Hikimar yin haka itace anaso kowa yayi amfani da zallan karfin damtsensa da iya yakinsa ne Don ba'aso wani yayi wani sihirin ajikin makaminsa Koda suka gama karbar makaman yaki sai take shugaban alkalan gasar ya fito ta daga katon bututu yace A ka'idar wannan gasar da muka tsara awannan shekara Ba'a yarda wani ya kashe wani ba acikin zagayen farko ba Amma zaka iya yi masa dukan da zaiji jiki matukar dai bazai mutu.ba Koda gama fadin haka sai ya juya ya kalli wani katon badakare wanda ke ruke da katuwar guduma ahannunsa ya tsaya agaban wata ganga Take kuwa badakaren ya daga wannan gudumar ya buga ajikin gangar alamar a fara gasa Nan da nan kuwa jaruman suka ja baya tareda zare makamansu Dukda yawansu kuwa saida filin ya cinyesu domin babban filine kuma an tanaje shi ne kawai saboda wannan gasar Sannan suka afkawa junansu da yaki cikin wani irin azababben salo Wohoho nanfa mutane suka rude da ihu gami da shewa Sakamakon ganin irin wannan bakin artabu da akeyi Wanda ana iya kiransa da turnuku fadan iblisai babu abinda idanu suke gani face Yadda mazaje suke bangazar kirazan juna duk wanda aka fishi karfi saidai kaga kafin aje ko'ina an zubar dashi kasa Saidai dakaru su zo su daukeshi daga cikin filin don kada a hallakashi Karafkiyar karafa tareda ihun mazaje suka cika dodon kunnuwa Jini ya dinga fantsama ako'ina kananan jarumai kuwa suka fara nadamar kawo kansu wannan fili Su kuwa ýan kallo in banda ihu babu abinda sukeyi Kafin cikar dakiku masu yawa anzubar da sama da rabin jaruman Hakika komai rashin imanin mutum saiya tausayawa kananun jaruman gasar Su kuwa mutanen da suke gurin kawai ihu suke suna dada koda jaruman su Acan bangaren sarki aryan kuwa kawai ya zauna ne yana murmushi Sannan yana karewa jaruman gasar kallo yana nazarin salon fadan kowanne daga cikinsu A sannan ne ya fahimci cewa lallai acikin wannan shekarar sai ya kara zage damtse acikin gasar domin tunda aka fara gudanar da

Chapter 6 of 17