Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsabar kishirwa Don haka sai ta yanke shawarar ta tsaya a wannan guri domin ta dan huta Sannan ya sha ruwan cikin koramar da ita da dokin nata kuma tayi wanka Take ta sauka daga kan dokin nata ta jashi bakin wannan koramar yasha ruwa ya koshi Sannan ta jashi ta kaishi bakin wata katuwar bishiyar kuka ta daureshii Tana gama daureshi ta juya ta kalli dajin sosai ta kare masa Kallo tana yin nazarinsa ko zata sami wani abin mai cutarwa acikinsa Bayan ta tabbata babu wani abin cutarwar da kuma bil'adama acikin dajin Sai kawai ta kwabe tufafin jikinta ta fada cikin wannan koramar Tana wanka abinta kamar a can cikin gidan sarautarsu takeyi ko kadan babu fargaba acikin zuciyarta Kai harma tana rera baitocin wasu wakoki a bakinta Koda ta shafe sa'a hudu tanayin wannan wanka sai kurum Taji koramar da take ciki ta soma girgiza ruwan ciki yana hautsinewa Kamar zaibar kan doron kasa ya tashi sama koda ta dago da kanta daga cikin koramar Sai tayi arba da wata katuwar kada Tunda tazo duniya bata taba ganin halitta mai girman wannan kadan ba Domin girman bakinta kawai yakai girman a hade manyan giwaye guda biyu Ballantana kuma girman jikinta, idan wannan kadar ta motsa jikinta Saidai kaga ruwan ya hautsine, nanfa walisa ta tambayi kanta Shin wannan dabba dama can acikin wannan koramar take rayuwa? Abinda bata sani ba shine ita wannan koramar reshece daga babban tekun duniya Kuma wannan kadar ta kasance sihirtacciyace domin bata cin naman dabbobi sai na bil'adama Shiyasa tana iya gano bil'adama indai ya shiga daya daga reshinan tekun Kuma taje ta riskeshi cikin 'yan dakiku kadan WANNE IRIN TASHIN HANKALI WALISA ZATA FUSKANTA YAYIN HADUWARTA DA WANNAN DABBA? SHIN ZATA TSIRA DA RAYUWARTANE KO KUMA MUTUWA ZATAYI A WANNAN KORAMA? MU HADU A KASHI NA GABA DAGA HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++++++++2 PART A LBR ++++++++++++++HABIBULLAH KBR 0=====[===============> Koda gama bayyanar wannan kadar sai walisa ta daka tsalle Tareda zare takobin da nufin ta fice daga cikin koramar Ba zato ba tsammani sai kawai taji wannan kadan ya kawo mata duka da jelarta Inbadon ta tsallakeba da tuni kadan ya raba ta biyu da jelarta Amma duk da haka sai da jelar kadar ya raba wata bishiya dake gefen koramar Koda ganin haka sai take walisa ta daka tsalle sama da nufin ta haye tsakiyar kan wannan kadar Take kuwa kadan ya sa jelarsa ya dokota ta fado kasa cikin ruwa Cikin sauri walisa ta dago saman ruwan ta fuskanci wannan kadar Suka ruguntsume da masifaffen fada kamar wasu manyan shedanu Nanfa suka ruda ruwan da yake cikin koramar saboda Tsananin gumurzu saidai kaga kifaye suna tasowa sama matattu Jaruma walisa ta wanzu tana mai kaiwa wannan kadar mugayen hare hare domin taga bayan ta da wuri Amma ina babu damar hakan domin itama wannan kadar Irinsu ake cewa murucin kan dutse bai fitoba sai daya shirya Duk sanda walisa ta sari ko ta yanki jikin wannan kadar saidai taga tartsatsin wuta ya tashi kamar haduwar karfe da karfe Itama kadar idan ta kawowa walisa hari da zarar ta goce duk abinda ta daka da jelarta Take yake dagargajewa Tabbas inba don walisa ta kasance mai tsananin zafin nama ba Da bata isa ta iya shafe dakiku uku ba suna fafatawa da wannan kadar ba Kai komai yawan ayarin mutane idan suka yada zango a bakin wannan koramar To ba makawa sunansu gawa domin ko daya daga cikinsu bai isa yayi rai ba Kai saida takai ta kawo matafiya sun gane wannan koramar sun daina tsayawa abakinta domin sun san sakamakon tsayawa agabar tata Koda suka shafe wasu dakikun masu yawa sai fadan nasu ya zama abin tsoron kallo Domin saida gaba daya reshinan wannan koramar suka amsa wannan fafatawa da akeyi Kai harma saida takai zuwa ga babban cibiyar wannan korama wato tekun bahar zus Sai gashi gaba daya dabbobin cikinsa sun haukace Suna neman gurin buya, kai wasuma har tsalle sukeyi suna fadowa kan doron kasa Ba tare da sun sani ba, saidai suyita kokarin komawa cikin tekun amma su kasa Ahaka har ransu ya fita, Acan bangaren su walisa kuwa lamarin yafiyin tsamari Domin dukkansu sun san cewa yau sun hadu da gamonsu Kuma a wannan yanayi kar ta san kar ce a tsakaninsu Ana cikin wannan bakin artabun ne kadar ta sammaci walisa Ta kawo mata hadiya da nufin ta tauneta gaba daya Cikin tsananin zafin nama ta daka tsalle ta kaucewa harin wannan kadar Inbadon tayi saurin kaucewa ba da tuni shi kenan an gama da shafinta Amma duk da haka saida kadar ta doketa da kafarta ta gaba Take tayi sama ta fice daga cikin koramar ta gwaru da wani katon dutse Wanda yasa har jini ya fita daga cikin hancinta ta fara ganin taurarin wuya acikin idanunta Cikin tsananin juriya ta mike tsaye rukeda takobinta a hannunta Tana jiran karasowar kadar domin alokacin itama kokarin fitowa daga cikin koramar take Sai bayan ta gama fitowa ne walisa ta karewa wannan kadar kallo sosai Sannan ta gane lallai wannan ba irin kadar da ta saba gani bace Ita gaba daya jikin wani irin santsine dashi kamar an shafa masa Kubewa sannan kuma yana da tsananin daukar ido, A tsakiyar gadon bayanta kuwa akwai wani dan karamin kaho Tana cikin wannan nazarin ne kawai taga kadar ya kawo mata wani irin harin bazato Cikin zafin nama ta daka tsalle cikin shammace ta dira A gadon bayan wannan kadar kuma ta kama wannan kahon ta rukeshi da hannunta guda daya Nan fa wannan kadar ta haukace ta fara kokarin wullo ta daga gadon bayanta, itakuwa sai taki yarda ta fado kasan Ta ci gaba da ruke wanna kahon, Wohoho hakika idan kaji ance ga ki gudu to sa gudu ne baizoba Sai gashi da wuya tayi wuya kadar ta dinga zuwa tana gwara jikinta da jikin bishiyoyi Suna karyewa da faduwa kasa, Ganin wannan al'amarine yasa walisa ta fahimci cewa tabbas Ruwa baya tsami banza dole akwai dalilin dayasa kadar bata son a ruke wannan kahon na bayanta Gama wannan tunani keda wuya sai ta tattara karfinta Guri guda ta daga takobinta sama ta sara a tsakiyar wannan kahon Take kuwa kahon ya rabe gida biyu kamar an tsaga lemo Faruwar hakan keda wuya sai kadar tayi wani irin gurnani mara dadin saurare Jini yayi fitar burgu daga jikin wannan kahon ya kwarara Zuwa cikin wannan koramar yana gudu kamar ruwan famfo Take ta fara mirgine mirgine tana tumurmushe abubuwan da suke cikin dajin Aciki harda dokin da walisa take hawa koda walisa ta ga abinda yake faruwa saita daka tsalle ta sauka daga kan kadar Ta sauka can gefe guda tana kallonta tun tanayin motsi har ranta ya gama fita daga jikinta Bayan kadar ta mutune sai walisa ta dawo bakin koramar ta sake shiga cikinta ta wanke jinin daya bata mata jikin nata Tana cikin wanke jinin da yake jikintane kawai sai taji wata irin guguwar iska mai karfin gaske ta wuce Ta saman kanta cikin sauri ta dago da kanta sama take tayi arba da dan uwanta Walisu da wasu irin manyan fuka fukai a cikin sararin samaniya yana zabga gudu kamar tauraruwa mai wutsiya Ya nufi bangaren gabas, domin shi baima kula da Ita ba Koda ganin wannan al'amari sai tayi sauri ta fito daga cikin koramar ta debi kayanta da makamanta ta sanya ajikinta Sannan ta falfala da azababben gudu ta nufi bangaren da shi walisun yabi Domin itama ta tabbatar da cewa zaijene domin ya aikata ta'addanci Nanfa ta dinga tsala azababbben gudu acikin dajin Kai saboda ma karfin gudun har tashi sama zakaga tanayi Tana tsallake kananan bishiyoyi da ramuka sai a sannan nema ta kula da cewa Ta ma fi dokin nata karfin gudu saboda cikin lokuta kadan ta dinga Shafe tafiya mai nisan gaske gaba daya cikin zuciyarta Tana tunanine akan inane jarumi walisu sai nufa domin tayi gaggawar dakatar dashi ga barin yin wannan mummunan aikin da yakeyi Kai wani lokacinma idan bishiyoyi suka tare mata hanya Sai dai kawai kaga ta daga tsalle sama tana kama reshinan Bishiyoyin tana tsalle akansu kai sai kayi zaton cewa ita ba mutum bace Gwaggwon biri ce ahaka ta dinga wucewa ta dajijjika masu yawa Idan kuwa tazo gaban ruwa da zarar ta karanta wadansu Dalasiman tsafi saidai kaga tana tafiya a saman ruwan kamar akan doron kasa takeyi Saida ta shafe sa'o'i tana gudu sannan ta iso bakin wani babban birni Da ganinsa saita cika da tsananin mamaki sakamakon ganin garin da tayi cikin nutsuwa babu alamar ana tashin hankali acikinsa Take ta tambayi zuciyarta cewa Anya kuwa yarima walisu yazo wannan birnin kuwa ? Ko dai canja hanya yayi ya tafi wani bangaren daban? Amsoshin data kasa baiwa kanta amsarsu kenan don haka Kawai sai ta yanke shawarar shiga cikin birnin koda kuwa baya ciki Da gama wannan tunani kawai saita rikide ta koma saurayin mafarauci Dauke da mataccen murgujejen zaki akafadarsa Kai da ka ganta a wannan lokaci ba zaka taba tunanin ba mace baceba Saboda komai na siffar jikinta ya rikide ya zama na maza Take ta nufi wannan babban birni wanda tun daga nesa ta fara Hango dakarun cikinsa dauke da miyagun makamai sai zare idanu sukeyi kamar saci babu kai da ganinsu kasan babu sauran tausayi acikin zukatansu Kowannensu ya bada hankalinsa wajen kallon kan hanya Domin su ga wanda zai shiga cikin birnin ahankali walisa taci Gaba da tafiya tana kara kusantar wadannan dakarun Kuma ko kadan babu tsoro acikin zuciyarta a haka harta karasa wajen masu tsaron kofar Daya daga cikinsu wanda ya kasance murgujejen gaske Mai kirar mutanen farko ya dakawa saurayin mafaraucin tsawa Yace kai kuma wanene kuma daga ina kake inason ka fada mini Iyakar gaskiya idan ba haka kuwa yanzu nasa takobina na raba Jijiyoyin da suke jikin wuyanka biyu domin tasha jinin jikinka ta kuma barwa kasa ragowar ta shanye Kodajin haka sai saurayin mafaraucin ya russinar da kansa Yace ka gafarceni ya kalmaru nine jamwar daga marugayi sarkin mafarauta na wannan birnin namu mai albarka Abinda yasa baka san da fita ta ba shine Ka sani cewa ni bata wannan kofar da kuke gadinta na fitaba Na fitane ta wata kofar daban akan hanyata ne na hadu da wannan murgujejen zakin Inda muka kasa tseren gudu dashi har saida muka iso wajen kusa da wannan kofar da kuke tsaronta Sannan na samu na iya cimmasa na kamashi Muka fafata yaki dashi daga baya na sami nasara akansa Dajin wannan bayani sai sarkin kofa yayi shiru yana dan nazari Yana cikin yin tunanine sai wani badakare dake bayansa Ya matso gabansa yace ya shugabana tabbas wannan shine jamwar daga marugayi sarkin mafarauta Don haka inaganin abindaya fada gaskiyane badon komaiba sai don ya zo da hujja Ga zakin nan a kafadarsa, dajin haka sai sarkin kofa yayi murmushi Ya kalle badakaren yace waya fada maka kowa abin yarda ne? Idan har sun fafata yaki da wannan murgujejen zaki dolene Za'a sami tabo ajikinsa don haka ba zan yarda dashi ba har sai na duba na gani Yana gama fadar haka sai ya yafito jamwar da hannu Yana mai yi masa nuni da yazo inda yake Cikin sauri kuwa ya matso gabansa ya tsaya Sarkin kofa ya kalli fuskar sa ya kare mata kallo sannan ya kalli kan damtsen sa da kan wuyansa Kawai Saiyaga yankan farce harma yankan ya danyi zurfi da ganin haka Sai sarkin kofa yayi murmushi yace to yanzu zaka iya shiga cikin birnin nan Amma ka sani idan nayi bukatar ganinka zan nemeka Da gama fadar haka sai ya umarci dakarun dake bayansa da su bude kofa Take kuwa suka cika umarnin shugaban nasu, cikin girmamawa jamwar yace nagode Ya kama hanya ya shiga cikin birnin mai suna teheran Da shigarsa cikin birnin sai ya kama hanyar da zata kaishi cikin gari Bayan ya danyi nisa da barin kofar birnin yadda masu tsaron kofa Ba zasu ganshi ba sai ya sake rikidewa daga wannan siffar Zuwa ta dan yaro dan kimanin shekaru goma sha biyu Matalauci wanda ko kaya masu kyau babu ajikinsa kuma a hannunsa ruke yake da kokon bara Take ya kama hanyar shiga cikin gari ya dinga bibiyar guraren da mutane Suke yanayin bara acikin barar tasa yana hada mutane da darajar abin bautarsu kan su taimaka da abin da zaici Amma sai yaga duk wanda ya kalleshi saiya kyalkyale da dariya Sannan su koreshi daga inda suke wannan halayya tasu Ba karamin bashi mamaki tayi ba yace acikin zuciyarsa Wai dama haka ala'dar gaba daya mutanen duniya take babu wanda yakeda tausayin nakasashshe? Abin da bata saniba shine duk duk mutanen wannan zamani haka suke Itama abinda yasa bata san da hakaba shine mahaifinsu Ya hana aikata wannan dabi'a acikin birninsu tun kafin a haifesu Wannan dalilin ne yasa ake zaman lafiya acikin birninsu har mutane suke sha'awar rayuwa acikinsa Yana cikin wannan tunanin ne ta iso bakin wani gidan abinci Wanda ya cika da mutane maza da mata kowa yana ciye ciyensa Da zuwa gurin saiya fara yi musu bara kan su taimaka masa da abinda zaici koda kuwa loma dayane Yana cikin yin barar ne kawai wani murgujejen kato ya dauke abinci ya taho gurin da yake Hannunsa ruke da kwanon abinci Da zuwa gurinda yake saiya kalleshi kamar yana jin tausayinsa Yace kai yaro yanzu yaushe rabonka da cin abinci? Cikin karamar murya irin ta yara yace Rabona da cin abinci tun jiya da rana ina mai rokonka daka Taimaka mini da wannan abincin don kaima wataran ubangiji ya taimakeka Dajin haka sai saurayin ya murtuke fuska take ya saki kwanon abincin agabanta Ya zube sannan yasa kafa ya tattakashi yace Lallai ma yaran nan kai da ganin irin siffata nayi maka kama data masu tausayi? To ka sani ko zaka mutu bazan taba taimaka maka da abinci ba Yana gama fadar haka yasa hannu ya zabga masa mari Ganin abindaya faru ga wannan almajiri sai ya baiwa mutanen da suke cikin wannan rumfar dariya har suna yabon wannan saurayin akan abin da yayiwa almajirin Almajirin ya tashi fuskarsa na zubar da hawaye ya tafi daga wannan rumfar ya kara nausawa cikin gari Koda ya bar jikin wannan rumfar ya kara shiga tsakiyar kasuwa Kawai sai yayi arba da dakarun sarki kalkus suna tafiya acikin tsakiyar kasuwar Adadinsu yakai dubu uku kuma sarki kalkus dinne akan gaba Har sun dan gifta ta inda almajirin yake sai kawai akaga sarki kalkus Ya ja linzamin dokinsa sannan ta dawo daidai inda wannan almajirin yake Ya kare masa kallo sama da kasa sannan ya bushe da dariya yace Wai dama har yanzu akwai irin wadannan kaskantattun mutanen acikin wannan duniya? Gaskiya da ace ban fito farautar boka sahibul ukub ba to da sai na sa an kama mini kai An kaika masarautata domin ka dinga debe mini kewa saboda Babu abinda nakeson gani a rayuwata kamar makaskantan mutane irinka Duk ragowar dakarun da suke bayansa sai suma suka bushe da dariya Sannan sarki kalkus ya kada linzamin dokinsa ya kara gaba dakarun sa na biye dashi Ana cikin wannan yanayi ne kawai sai ya jiyo sautin wani yaro yana tsallara ihun neman taimako inda wani gabjejen kato Ya sakashi agaba yana zabga masa wata katuwar bulala Wacce ko doki idan aka dakeshi da ita sai yaji zafin dukan Idan wajen ya kumbura sai kaga ya debo gishiri yana shafawa akan shatar bulalar Yaron sai rusa ihu yake kamar ransa zai fita amma duk da haka An rasa mutum daya wanda zaije ya ceci wannan yaron Kowa idan yazo sai kaga ya kauda kansa ya kara gaba Abinsa domin sam wannan abu ba komai baneba su awajensu Domin sun saba ganin zaluncin daya wuce wannan har almajirin ya kauda kansa zai kara Gaba sai yaji shifa ba zai iya tafiya ya bar wannan yaron ba Cikin bakar wahala ba don haka sai ya juya ya tafi inda ake azabtar da wannnan Da isarsa sai ya fara yiwa wannan gabjejen katon magiya akan ya yi hakuri ya kyale Yaron yayi tafiyarsa amma sai yaki ya hakura daga bayama Sai ya daga bulalar da nufin shima ya hada dashi ya azabtar Koda ya daga bulalar sama da nufin zabgawa wannan almajirin sai kawai yaji an shureshi an dagashi sama sannan An dokashi da kasa saboda karfin dukan saida yaji kamar kashushuwan bayansa Sun kakkarye take ya mike tsaye tareda zare takobinsa da nufin Ya sare kan wannan almajirin Kafin ya aikata haka sai yaga wannan almajirin ya rikide daga Wannan siffar ya koma zuwa ainihin siffar jaruma walisa Koda ganin wannan abin al'ajabi sai wannan ya wullar da takobinsa Ya falfala da gudun gaske saboda firgitar da yayi da lamarinta SHIN INA YARIMA WALISU YA TAFI? KUMA ME WALISA TAKE NEMA ACIKIN WANNAN BIRNIN? ME SARKIN GARIN ZAIYI MATA SABODA TA WULAKANTA DAN CIKIN BIRNINSA AMATSAYINTA NA BAKUWA ? SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT++++++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++++++2 PART B LBR +++++++++++++++HABIBULLAH KBR Jaruma walisa ta sanya hannayenta ta tashi wannan yaron tsaye Sannan ta nuna inda tabban bulalar jikinsa yake Take ya daina jin radadin bulalar jikin nasa Ya dago da kansa ya kalleta yace Yake wannan ma'abociyar taimako ina matukar godiya agareki Bisa kulawar da kika bani kuma ina addu'a agareki ubangiji ya baki nasara kan dukkan abubuwan da kika sanya agabanki Dajin haka sai tayi murmushi agareshi sannan tace Kaikuwa wanne irin laifi ka aikata masa wanda yasa yaketa faman azabtar dakai? Dajin wannan tambaya sai yaron yace ni kaina bansan laifin da nayi masa ba Saidai kawai nasan al'adar duk wani wanda yakeji da karfi A wannan nahiyar idan yana da bukatar yin nishadi sai Kawai ya kama wanda yafi karfi yayita zaluntarsa su kuma mutane Idan suna ganin haka sai suyita jin dadi Koda jin bayanin da wannan yaron yayi mata sai kawai Tausayinsa ya kamata kuma taji ta tsani zama acikin birnin Don haka sai ta debo dinare dari ta baiwa wannan yaron Sannan tace ga wannan sai kaje dashi ka baiwa iyayenka Ni kuma zan kama hanya domin na bar wannan birnin in kara Gaba saboda ba zan iya zama a garinda mutane da dabbobi basu da banbanci ba Yaron ya kalleta yace yake wannan jaruma shin waike wacece Kuma menene ya kawoki wannan birni namu saboda naga alamun kamar ke bakuwace Dajin wannan tambaya sai tayi murmushi sannan tace Nice gimbiya walisa ta birnin madaril adfam Kuma ba komai ne ya raboni da gidaba face neman dan uwana yarima walisu Wanda ruhin wani takadirin boka ya shiga jikinsa yake sarrafashi Tana gama fadin haka saita juya zata tafi kawai sai taji an ruko Gefen rigarta koda ta juya bayanta sai kawai taga wannan yaron Ya mike tsaye siffar jikinsa shima tana rikidewa zuwa ta saurayi Kakkarfa sannu ahankali sai gashi ya koma siffar dan uwanta Yarima walisu amma kuma sai taga gaba daya ya sauya daga yadda ta sanshi Ga wasu irin manyan fuka fukai ajikinsa launin fatar kirjinsa kuwa Itama ya sauya gaba daya gashi ya lullubeshi sai kace tsuntsu Hannunsa na dama kuwa ruke yake da wata iriyar zabgegiyar sarkar tsafi Cikin sauri walisa ta dubeshi tace Ka ganeni kuwa nice ýar uwarka walisa yanzu haka mahaifinmu ne ya turo ni nemanka Take ta kai hannu da nufin ta rungumeshi Koda hannuwanta suka sauka akan fatar jikinsa sai taji Wani irin zafi mai radadi yaratsa jikinta kamar wacce ta kama garwashin wuta Cikin sauri ta cikashi tareda ja da baya taku uku tana mai fuskantarsa Shi kuwa sai kawai ya kyalkyale da dariyar mugunta Wacce tasa taji kamar gabaki daya kunnuwanta zasu fashe Harsaida tasa hannayenta ta toshe kunnuwanta dasu Kasar gurin kuwa ta fara girgiza kamar za'ayi girgizar kasa Saida yayi dariyarsa ta isheshi sannan kuma yaci kunu tareda murtuke fuska Sannan ya daka mata tsawa yace Ke karamar yarinya karya kikeyi baki isa ki raina mini Hankali ba domin duk duniya bani da ýan uwa ni kadaine Sannan inaso ki sani ina sane dake tun sanda kika biyo bayana Kina nemana saidai duk wannan abinda kikeyi kina yaudarar kanki ne Ina mai tabbatar miki cewa duk duniya babu wanda ya isa Ya hanani aiwatar da abinda nayi niya balle ke karamar yarinya Ni kadai fasa tarone don haka babu yadda za'ayi mutum daya ta iya hanani cika burina Inaso ki sani cewa inda ina da burin kasheki to babu makawa yanzu take Zan hallakaki sannan na tafi can birnin ku na hallaka mahaifinku To amma bakune agabana ba nafiso sai na gama razana mahaifinki Sannan zanje shima nayi masa irin kisan da nake bukatar yi masa To a lokacin ne duniya zasu tabbatar da cewa Boka sahibul ukub ya dawo sannan kowa ya dawo ya cigaba Da bauta mini kamar yadda akeyi abaya Koda yazo daidai nan azancensa sai itama ta bushe da dariya Sannan tace karyarka tasha karya baka isa ka aikata abinda kakeso ba A wannan duniyar sa'arka dayace shine nayiwa mahaifina Alakawarin zand dawo masa da kai a raye amma badon hakaba Kasheka kawai zanyi Koda gama fadin haka saita zare takobinta ta daka tsalle sama Da nufin tayi masa fashin albasa, koda takobin ta sauka Ajikinsa sai wata kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe tareda tartsatsin wuta Cikin bakin zafin nama ta sake daka tsalle sama ta dinga jera masa Kutufo da naushi akan fuska saboda karfin dukan saida taji Kafafun nata da hannuwanta suna radadi amma duk da haka sai taga ko motsi baiyiba daga inda yake A ka'ida idan tayi irin wannan dukan ko bishiya ta daka Sai bishiyar ta fadi komai girmanta da kuma nutsewar da tayi acikin kasa Sai kaga ta bubbugo daga cikin kasa har jijiyoyinta Sun zube akasa ba'a taba samun akasi ba, don haka saita kamu da tsananin mamaki akan

Chapter 3 of 17