Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels +++++++++++++ZUBAR DA JINI ++++++++++++++ 1 PART A LBR ++++++++++++++HABIBULLAH KBR Gaisuwa ta musamman ga ýar uwar mu wato ummu jawaheer sannan ina tayata murnar auren da tayi sannan allah ya bada zaman lafiya Jin jina Ga dukkan makaranta wadanda suke bibiyarmu tun daga farkon littafi kuma suke yi mana comment wadanda bansan adadinsu ba Mun gode allah ya bar zumunci A wani zamani can baya mai tsawo daya shude alokacin da duniya take cikin kuncin rayuwa Saboda gaba daya mutane da dabbobi kai hatta sarakuna basu da kwanciyar hankali sakamakon yawan yawan zubar da jinin da akeyi a fadin duniya Saboda ako da yaushe cikin farautar rayuwar juna ake Wanda yafika karfi ya kashe ka ya kwashe dukiyar daka tara A wannan zamani mafi yawan mutane jarumai ne kuma matsafa Domin su kare kansu daga farmakin abokan gaba Babu abinda mutane sukafi so awannan zamani sama da suga jini ya gauraya da kasa yana gudu akanta Namiji kuwa idan bai kasance gawurtaccen mayaki ba bai isa ya auri mace kyakykyawa ba Face wani yazo har inda yake ya kasheshi ya kwaceta Kai yaran da suke wannan zamanin a haka suke tasowa Sai kaga an haifi jarirai guda biyu amma da zarar sun fara wayo sai kaga suna yunkurin kashe junansu Mutane basu da burin da yafi suga jini yana gudu acikin kwata kamar ruwa Duk sarkin kuwa da yake da bukatar shakatawa sai kaga ya hada Rundunar yaki sun farwa wata kasar wacce suka fita karfi da yawan mayaka Su yaketa sannan su kamo bayi su dawo dasu birninsu Hakika duk inda lalacewa da rashin imani yakai to wannan zamani ya wuce haka Acikin wannan zamani ne akayi wata babbar masarauta mai dumbin tarihi Wacce ta shahara a yawan mayaka da kuma girman kasa Kuma ubangiji ya azurtasu da tarin arzikin kasa mai dumbin yawa Ana kiran wannan birni da suna madaril adfam Birnin madaril adfam ya shahara wajen kasuwanci da saye da sayarwA Kasancewar shine kadai birnin da zakaje kayi zamanka lafiya ba tareda fargabar 'yan harin sumame ba Saboda tsananin zaman lafiyar da akeyi a birnin Ba komai ne ya janyo haka ba face kasancewar sarkin garin adalin gaske ana kiransa da suna fadarul munnar Kuma fasa taro tunda yake a tarihin jarumtakarsa ba'a taba yankarsa ba afilin daga Sannan kuma ya tsani zalunci bashi da burin da yafi yaga Ya kawar da zaluncin da yake faruwa acikin duniya amma ya kasa har ya zamana girma ya fara kamashi kuma gashi bashi da da ko guda daya wanda sai gaji karagarsa idan ya mutu Don haka wata rana ya tambayi wani amintaccen bokansa kan yadda zai yi duk bukatunsa su biya Koda jin bukatun sarki fadarul munnar sai bokan ya bushe da dariya sannan Yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa bukatunka duka zasu biya Amma ina mai tabbatar maka da cewa ba kaine zaka kawar da zaluncin da akeyi acikin duniyar nan ba Sai dai tsatsonka bincike ya nuna cewa matarka tana dauke da juna biyu Nan bada dadewa ba zata haifi 'ya'ya guda biyu to wadannan 'yA'yan ne zasu cika maka burinka Daga wannan rana sarki fadarul munnar ya zauna jiran ranar haihuwar matarsa wacce ake kira da gimbiya nursiba zata haihu Ana cikin wannan hali ne wata rana kwatasam sai nakuda ta kama nursiba Ta haifi ýan tagwaye guda biyu mace da namiji kyawawan gaske Awannan lokaci sarki fadarul munnar yayi farincikin da bai taba yin kamarsa a tarihin rayuwarsa Domin saida akayi sati biyu ana shagalin bikin murnar haihuwarsu Kuma tun aranar da aka haifesu aka soma tsumasu da tsumin tsafi mai matukar karfi don ya zame masu rigakafi Dukiya kuwa yayita rabar da ita ga talakawa bai san iya adadinta ba Tun a sannan suka dauki soyayyar duniya suka dorawa wadannan jarirai nasu Sannan suka rada musu suna walisa da walisu dadin dadawa wadannan jarirai suna matukar kama da iyayen nasu guda biyu kamar an tsaga kara A duk sanda sarki zaije zaman fada taredasu yake zuwa akafadarsa Wani lokacin ma sai kaga ya goya daya abayansa daya kuma ya rukeshi a hannu Lokacin da walisa da walisu suka cika shekara biyar sai aka fara koyar dasu ilimin bokanci da kuma salon yaki Kasancewar su yarane masu hazaka da kaifin kwakwalwa sai kaga duk abinda aka koya musu sun dauka tamkar zanen dutse Kai saida takai ta kawo shi kansa wanda yake koyar dasu dabarun yaki sun fishi iyawa Sannan aka mikasu hannun sarkin yakin birnin wanda ake kira da huram Shi kansa sarkin yaki huram yana matukar mamakin irin kaifin kashin wadannan yara dana kwakwalwarsu Domin a lokacin ma kowanne daya daga cikinsu yana iya yin aikin da karti ashirin sukeyi Kuma ba tareda sun jigata ba. Abangaren mutanen gari kuwa Babu abinda yake burgesu gasu walisa face yadda suka hade kansu kuma suke da matukar tausayi Sabanin ragowar yaran zamanin Tun a wadannan shekarun mutanen birnin suka tabbatar da cewa Nanda wani lokaci zasu zama gwarazan zamani wadanda za'a kara dasu a fannin jarumtaka Shi kansa sarkin yaki huram watarana da suka kebanta da sarki fadarul munnar acikin turakarsa Ya fada masa cewa Zaifi kyau shi da kansa ya horar da su walisa da hannunsa Domin sai sunfi samun cikakken horon yaki a gurinsa Da jin haka sai sarki fadarul munnar yayi murmushi sannan yace Nasan da haka amma ka sani inaso ne sai kashinsu yayi kwari sannan zan fara horar dasu da kaina Wannan dalilin ne yasa na fara mikasu gurin matemakinka sannan suka dawo gurinka To kaga idan suka zo hannuna salo na daban zan koya musu Sirrikan tsafi kuwa a gurin babban bokan birnin suke samu wanda ake kira da suna makassar Boka makassar ya kasance hatsabibin boka wanda duk nahiyar babu kamarsa Shine yake koyar dasu ilimin bokanci da sirrikansa Bayan sun cika shekara goma sha biyar sai labarin jarumtakarsu ya shiga ko ina acikin duniya kasashe da dama suka kara shakkar tunkarar birnin madaril adfam da yaki Komai karfin dakaru idan su walisa suka tunkaresu sai sun tarwatsasu Sannan su kama sarkin su su mikashi wajen mahaifinsu Atakaice dai sai da suka zama guguwar annoba ko ina ka shiga labarinsu akayi A ka idar birnin madaril adfam mace batayin mulki saidai namiji Amma hakan baisa sarki fadarul munnar yana nuna banbanci ba atsakanin 'yaýansa Wannan dalilin ne yasa suka shaku da junansu ko kadan basa taba rabuwa da juna Ana cikin wannan hali ne wata rana aka wayi gari babu yarima walisu acikin birnin Wannan al'amari ne yayi matukar razana sarki fadarul munnar da gimbiya walisa da mahaifiyarsu Babu inda ba jeba acikin birnin da makotansa ko za'a ga yarima walisu amma sama da kasa ba'a ganshi ko an sami labarin wanda ya ganshi ba Wannan al'amari ba karamin tayar da hankalin mutanen birnin madaril adfam yayi ba Domin tunda ya taso a rayuwarsa bai taba zuwa wani gurinba face da izinin iyayensa ba Babu wanda hankalinsa ya tashi fiye dana kowa face 'yar uwarsa gimbiya walisa Domin tasan ita bata da ikon mulkar birnin madaril adfam sai shi Tunda ita mace ce don haka shi kadaine yake da ikon gadon karagar birninsu Sai da aka kwana biyu ana binkice a cikin nahiyar kuma aka baza hotunansa Sannan aka saka kudi mai tsoka kan cewa duk wanda ya fadi inda yake za'a bashi su Amma duk da haka ba'a sami wani gamsashshen labari ba Shi kansa boka makassar babu irin binciken da bayyi ba don gano inda yarima walisu yake amma ya kasa Wannan dalilin ne yasa aka tara manyan bokayen da suke nahiyar guri guda domin su hada karfi da karfe su gano inda yake Wannan taron kuwa anyi shi ne a fadar sarki fadarul munnar Bayan kowa ya gama hallara sai sarki fadarul munnar ya tashi ya fara jawabi kamar haka Yaku manyan dirakun wannan nahiya dukkanku kunsan babban bala'in daya taso mini acikin wadannan kwanaki Na batan magaji na wannan birnin wato dana walisu Babu irin binciken da bamuyi ba domin gano inda yake amma mun kasa sani Adalilin hakane yasa na taraku gaba daya domin yin shi wannan aikin Inada tabbacin cewa idan kuka hada karfi da karfe zaku samo mana mafita akan wannan al'amari Idan kuwa har kukayi wannan aiki zan baku dukiya mai dumbin yawa Domin kowa acikin ku akwai irin baiwar da yake da ita Da wannan kalami nake umartarku daku fara yin wannan gagarin aiki Yana gama fadar haka yayi shiru da bakinsa ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya Nantake duk bokayen suka dukufa suka fara bincike mai zurfi Saida kowannensu ya jike sharkaf da gumi kamar an watsa musu ruwa Jikinsu kuwa ya soma rawar dari, idanunsu sukayi jazur Fadar kuwa tayi tsit kamar babu mai rai acikinta har suka shafe dakiku masu yawa Sannan dukkansu suka dago da kansu jikinsu a sanyaye Suka dubi mai gidansu boka makassar Shi kuma ya kalli sarki fadarul munnar jikinsa duk yayi sanyi sannan yace Ya shugabana dole saidai kayi hakuri da danka yarima walisu Domin yanzu haka bama musan inda yake ba Saidai bincike ya nuna mana cewa yana raye acikin duniya Yanzu haka ruhin wani hatsabibin boka ne ya shigeshi wanda ya shafe shekaru masu daruruwa da mutuwa Shidai wannan boka tunda aka halicci duniya ba'ataba samun Shu'umin matsafi ba kamarsa domin yana iya yin tsafin da zai janyo hallakar birane da dama a cikin abinda bai wuce dakika guda ba Kuma yana iya samar da hasken rana acikin tsakiyar dare Kuma tunda yafara sabgar tsafinsa bai taba taka kasa ba ko kwanciya da zama akanta ba Sai dai akan iska Kuma duk inda yake da burin zuwa saidai kawai kaga ya bayyana agurin koda kuwa tafiyar takai tsawon tafiyar shekara dubu Ana kiransa da suna sahibul ukub Azamaninsa saida takai ga cewa mafi yawan kasahen duniya da sarakuna shi suke bautawa amatsayin abin bautarsu Saidai wasu kebantattun mutane mabiya wani addini wadanda basu da yawa acikin duniya Babban burinsa a duniya shine ganin ya mayar da ita ta koma rayuwar ZUBAR DA JINI Sannan yaga teku ta rine da jinin bil'adama Kuma ta dole ya dinga tilastawa mutane suna yakar masoyansu suna kashesu da hannayensu Ko kuma ya da da mahaifinsa Ko dan uwa da dan uwa, ko miji da mata Yace dole sai wani ya kashe daya sannan ya shanye jinin Shi kuwa ya zauna yayita kyalkyala dariya Bisa dole wannan mummunar dabi'a ta dinga shiga cikin zukatan mutane Har ya zamana cewa suma babu abinda suke sha'awa sama da suga jini yana yawo akan turbaya Alokacin da giyar zalunci take dibarsa ne yaga mabiya wannan addinin marasa yawa sune kadai suka ki karbar wannan mummunar al'ada tasa kuma suka ki su bauta masa Sai ya fara shirin yakarsu, watarana sai yayi karo da wani babban malaminsu kuma jarumin gaske ana kiransa da suna hasanul basari bin maharaz Suka fafata dashi daga baya ya hallaka shi boka sahibul ukuba din Tun daga wannan lokaci aka huta da bakin zaluncin sa Amma kuma duk da haka mutane suna kwaikwayon Irin rashin imaninsa, har zuwa wannan zamanin da muke ciki Shi kuwa ruhin boka sahibul ukuba tun daga sanda ya mutu ya koma kan wani tsauni ya zauna Cikin wani kasurgumin daji Mai cike da bakaken aljanu marasa imani ya cigaba da zama acan Domin tun sanda yake raye ya taba yin binciken cewa Bayan mutuwar sa da shekaru masu yawa za'a haifi wasu Tagwayen jarirai masu matukar jarumtaka wadanda zasuyi shura acikin duniya To duk sanda wadannan jarumai suka bayyana ruhinsa zai iya shiga jikin daya daga cikinsu ya cigaba da gudanar da rayuwarsa da mulkinsa na zalunci Ya shugabana to kaji labarin wannan hatsabibin kuma takadirin boka Yanzu haka ruhinsa yana jikin danka yarima walisu don haka komai zaiyi ba'a cikin hayyacinsa zaiyi ba dalilin dayasa yaki shiga jikin walisa shine ita ya kasance macece shi kuma kaga namijine Yanzu idan duniya zata taru babu wanda zai iya sanin inda walisu yake Kuma babu wanda ya isa ya iya tunkararsa da yaki face ya sami nasara akansa Kuma daga yanzu duniya zata shiga cikin tashin hankali fiye da wanda take ciki yanzu ZUBAR DA JINI zai kara yawaita a duniya kasa zata rine da jinin bil'adama Ya shugabana ka sani cewa dukda walisu ya kasance dane shi a gurinka Idan ta raya masa zai iya zuwa nan fadarka ya kasheka ya kawo karshen mulkinka Koda boka makassar yazo nan a zancensa sai sarki fadarul munnar yayi tagumi yana nazari na dan tsawon lokaci Sannan ya dago kai ya dubeshi yace Lallai akwai gagarumin tashin hankali agaba wanda zai haddasa zubar da jini A duniya kuma bai kamata a ku tsaya mu zuba ido wannan abu ya faru ba Dolene mu mike tsaye muyi maganin wannan bala'in domin zai addabi duniya ne baki dayanta Idan har mukayi sakaci da wannan al'amari zaizo daga baya muma ya addabe mu Shin yanzu amatsayin ku na manyan bokaye ta wacce hanya kuke ganin zamu tunkari wannan bala'i? Kodajin wannan tambaya sai boka makassar ya girgida kansa Kamar ba zai ce komaiba daga can kuma yace Hanya dayace kawai zamubi domin mu hana wannan bala'in tasiri Hanyar kuwa itace dolene mu tashi 'yar uwarsa gimbiya walisa tayi kyakykyawan shiri ta fita farautarsa itama Domin bincike ya nuna cewa duk duniya itace zata iya tunkararsa da yaki kasancewar karfin damtsensu daya ma'ana ita dashi kar ta san kar ne Banbancin su kawai shine karfin sihiri Domin hana shi ai watar da zaluncinsa har zuwa sanda zai sami lafiya ya rabu da wannan matsalar fatalwa Ya shugabana ka sani cewa bamu da wani zabi face yin hakan A koda yaushe zai dinga farwa manyan birane da kanana yana kashe mutane Maza da mata yara da tsofaffi kuma babu yarda zasu iya dashi domin karfinsa na musamman ne Koda duniya zasu taru basu isa su iya hanashi aiwatar da abinda yayi niyya ba Saidai kasancewar gimbiya walisa zata hanashi yin tasiri Babu wanda yasan inda zai fara zuwa kamar yadda babu wanda yasan inda yake a halin yanzu Dajin haka sai sarki fadarul munnar ya girgiza kansa yayi shiru kamar an aiko masa da sakon mutuwa kwallar bakin ciki ta zubo daga idanunsa sannan yace Lallai duk mai rai zai dinga ganin kazantar duniya kala kala tareda abubuwan al'ajabi Wannan wanne irin tashin hankali ne Wai ace dan uwa zai fita duniya takanas domin farautar dan uwansa Lallai mai rai baya rabuwa da ganin abubuwan al'ajabi Wannan al'amari ba karami bane Don haka yanzu yanzu za'a kirawo gimbiya walisa domin tasan wannan al'amari kuma tayi shiri Yana gama fadar haka sai ya kira sarkin gida ya tura shi yaje turakar gimbiya walisa ya kirawota Da isowarta Sarki ya kwashe labarin duk abinda ya faru da kuma hukuncin da suka yanke ya fada mata Koda gama jin wannan al'amari saita faa she da kuka sannan ta fice daga cikin fadar ta nufi turakar mahaifiyarsu ta kwashe labarin komai ta fada mata Dajin wannan mummunan labari sai nan take gimbiya nursiba Ta fadi kasa sumammiya ME ZAI FARU NAN GABA SHIN WALISA ZATA AMINCE DA WANNAN TAFIYAR? MU HADU A KASHI NA GABA DAGA HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++ZUBAR DA JINI +++++++++++++1 PART B LBR +++++++++++++++HABIBULLAH KBR Take gimbiya walisa ta rusa uban ihu karar ihun nata ne Ya amsa kuwwa har zuwa can cikin fada cikin sauri sarki fadarul munnar Ya falfalo da azababben gudu cikin turakar Da zuwa sai ya debi ruwa ya yayyafawa gimbiya nursiba Take kuwa ta farfado daga suman da tayi tanamai ajiyar dogon numfashi Ta kalli sarki fadarul munnar tace Shin da gaske ne yanzu shi kenan na rabu da dana walisu? Kan sarki fadarul munnar a kasa yace kwarai kuwa abinda walisa ta fada miki gaskiyane Babu yadda zamu iya akan wannan al'amari face mu hakura mu tura 'yar uwarsa Ta bishi cikin duniya domin nemansa ta wannan hanyace kadai zamu iya samu mu dawo da dan mu zuwa garemu Idan ba haka ba kuwa mu dashi har abada domin bazai taba yarda cewa Mu iyayensa ne ba kuma duk sanda ta raya masa zai iya dawowa nan birnin mu ya yake mu Kuma bamu da abinda zamu iya yi masa awannan lokaci Koda jin haka sai nan take hankalin gimbiya walisa ya tashi tashiga tunani a cikin zuciyarta Bata san sanda zancen zuci ya fito fili ba tace Yanzu shikenan ni da dan uwana mun zama abokan gaba da samu dinga farautar juna ? Shakka babu dolene ki aikata haka domin ceton miliyoyin rayuka daga hallaka Idan kuwa kika ki to tabbas zanyi nadamar haihuwarki Domin burina kawai shine ganin an sami zaman lafiya a duniya an daina ZUBAR DA JININ da akeyi Ina mai umartarki da ki kasance cikin shirin wannan tafiya kisa aranki cewa zaki ceto dubban rayuka ne daga hallaka Yana gama fadin haka sai ya juya ya nufi hanyar zuwa fada yanayi mata nuni data biyo bayansa Nantake kuwa ya bishi abaya har suka isa cikin fada duk inda suka gifta dakarune suke rissinawa suna gaishesu Da isowarsu cikin fada sai suka sami guri suka zauna Sarki fadarul munnar yayi gyaran murya sannan yace Yaku wadannan bokaye duk naji irin bayanin da kukayi Kuma na gamsu dashi sosai amma inaso idan akwai wani taimako da zaku iya yiwa walisa to inaso kuyi matashi yanzu Koda sukaji abinda sarki fadarul munnar ya fada sai duk suka tsaya suna nazari Daga can sai dukkansu suka hadu waje daya suka tattara hannayensu Suna masu karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya Saiga wani irin karanin dutse ya bayyana a tsakiyar hannunsu Shidai wannan dutse girmansa baifi tafin hannu ba Sannan wani irin shudin haske yana tashi daga jikinsa Boka makassar ya tashi da kafafunsa yazo gaban gimbiya walisa ya mika Mata wannan dutse sannan yace wannan dutsen zai taimaka miki sosai acikin wannan tafiya Duk sanda kikaga wannan shudin haske ya juye zuwa ja To tabbas akwai wani bala'i da yake shirin faruwa a wannan yankin A yanzu kuma kinga babu bala'in daya fi na dan uwanki a wannan duniya Karki kuskura ki rabu da wannan dutse koda yaushe ya kasance ajikinki Koda kuwa barci zakiyi domin yana daga cikin abubuwan da zasu taimaka miki Cikin sauri takarbi wannan dutse ta sakashi acikin aljihu ta ajiye Sannan sarki fadarul munnar ya debi dukiya mai yawa ya baiwa wadannan bokaye Ya sallame su suka kama hanya suka tafi kowa ya shiga sabgarsa Kai tsaye sarki fadarul munnar da gimbiya walisa suka koma cikin gidan sarauta hanyar da zata kaika dakin sarki Koda suka kusa zuwa kofar dakin sai suka yi arba da gimbiya nursiba Atsaye a bakin kofar idanunta cike da kwalla Take tazo ta rungume walisa sannan tace Zanyi kewarki yake 'yata zanso ki dawo wannan birni namu a raye Daga wannan farautar mutuwar da zaki fita Kodajin haka sai walisa ta janye jikinta daga na mahaifiyarta tace Haba ummi na bai kamata ki fidda rai dani ba ki sa aranki cewa dole zan dawo wannan birni Kuma inayi miki alkawarin bazan dawo ba sai tareda dan uwana yarima walisu Domin shine babban burin mahaifina tunda shine yake da gadonsa bani ba Dajin haka sai kwalla ta zubowa sarki fadarul munnar Take yaji tausayin gimbiya walisa ya kamashi don haka sai Kawai ya bude kofar turakarsa ya shiga Ashe suma sun kula da wannan hawayen daya zubo daga idonsa Cikin sauri suka biyoshi abaya sannan walisa tace Ya abbana kayi hakuri idan maganar dana fada ta bata maka rai Ka sani cewa ban fada bane domin nufin cutar dakai ba Cikin murmushi ya dubeta yace. Yake 'yata ko kadan baki bata mini raiba saidai tausayi Da kika bani na ganin cewa baki da gadon karagata Nima bani da yadda zanyi akan haka domin haka ka'idar mulkin birnin mu yake Da ace ki namiji ce to da tabbas kece zaki gaji kujerar mulki na Yana gama fadar haka sai yaje ya dauko wata akwati acan kasan gadonsa Ya budeta sai gashi ya zaro wani irin bakin sulke mai kaurin gaske Tareda wata iriyar takobi itama baka kamar yadda sulken yake Ya taho zuwaga walisa ya mika mata wadannan kayan sannan yace Ga wadannan kaysn ki rikesu a hannunki zasuyi miki amfani sosai acikin wannan tafiya Nima na gajesu ne awajen mahaifina kuma nima yanzu na mallaka miki su Daga yau har zuwa sanda zaki dawo Nantake walisa ta karbi wadannan kayan ta saka ajikinta Sannan ta nade gashinta guri daya ta saukeshi ya zuba akan kafadunta Ta juyo ta rungume mahaifiyarta Nan dai sukayi bankwana da juna ta juya ta fice daga cikin turakar tana waiwayen mahaifiyarta Shikuwa sarki fadarul munnar sai ya biyota abaya yana rakata Sannan yana kara karfafa mata gwuiwa akan aikin dake gabanta

Chapter 1 of 17