Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dauki marinade din na ya zuba a sama ya juya ta shiga cikin kowane , sannan ya dauki tray din ya juya ya saka cikin oven din ya riga ya kunna ya yi zafi sannan ya rufe ya dawo ya tattare ledodin ya zubar a trash ya wanke bowl din mixer din ya mayar ya na juyowa ya ga Esra tsaye bayan shi ta na sakin wani kyawatencen murmushi ba karamar razana ya yi ba dan har wani dan baya ya yi wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za mu yi yanzu ? " a hankali ya karaso gaban counter din ya tsaya ya na fadin " oven nawa gare ku ? " " biyu ne " ta fada ta na karasowa geffen shi ta tsaya " okay , ki na da puff pastry ? Apple , cinnamon , cane sugar , lemon " cikin rudu ta ce mishi " me kuma za ka yi da su ? " sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Apple pie , ko ba ki so ? " dan zaro idanu ta yi ta na fadin " no , da gaske , shi ne favorite dessert di na " slowly ya juyo ya kalle ta sai sakin murmushi ta ke , shi kan shi bai san lokacin da ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na ce mata " ni ma haka " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta juya ta nufi fridge ta fiddo mishi duk abubuwan da ya zano mata ta dawo ta ajiye gaban shi ta na fadin " amma fa ban da mold din yi pie " " no wonder , wadda za mu yi ba ta bukatar mold , it's simple and delicious , cikin 30 minutes za ki iya yin ta " gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta ce " okay prof , bismillah ina kallon ka " wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " yawwa student , yanzu kawo min tray din gudan oven din , sannan ki kunna shi saman 180° " " Yes Chef " ta fada cikin zolaya kafin ta juya ta nufi dayan oven din maganar ta gaskiya ta ba ta shi dariya har wani murmushi ya ke saki shi kadai fiddo tray din ta yi ta kunna oven din kafin ta juya ta ajiye mishi gaban shi ta na ajiye wa ya juya ya nufi gas cooker dama pan din na ajiye a sama , kawai sai ya kunna , ya dawo ya dauki Apples din ya yanka su kana kana sannan ya zuba cikin pan din da ta riga ta yi zafi , ya zuba cane Sugar din da cinnamon da juice din lemon kadan , ya jujuya su , su ka shiga cikin juna har apples din su ka fara yin laushi ya na ganin hakan ya kashe ya dauko pan din ya juyo da ita ya ajiye saman counter sannan ya juyo ya kalli Esra ya ce " ina fatan ki na ganin abun da na ke ? " " ni fa kaina 10000GB ne , duk na yi recording abun da ka ke yi " wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya juya ya dauki puff pastry din nan , ya shinfida saman tray din oven , sannan ya dauki knife ya raba shi gida 8 da ga haka ya dauki spoon ya fara debo apples din ya zuba saman parts 4 , sannan ya dauko wadancen da bai zuba ba a kai ya rufe su da su , ya dauki fork ya danne bakunan su daya bayan daya dan kar su bude ya na gamawa ya matsa gefe ya kalli Esra ya ce " za ki iya sakawa a oven " dan zaro idanu ta yi ta na fadin " ban gane ba , har mun ida ? " gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba " mun yi sauri fa " ta fada ta na daukar tray din ta saka a oven ta rufe kafin ta dawo geffen shi ta tsaya ta na fadin " minti nawa zai yi a ciki ? " " juste 20 minutes " ya fada ya na kai hannu ya dauki spoon ya debo apples ya kawo saitin bakin Esra allamun ta ci wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta bude baki a hankali ta karba ta na kallon shi gaskiya ba karamin dadi abun ya yi mata ba har wani dan lumshe idanu ta ke yi sai da ta gama cinyewa sannan ta kalle shi ta ce " gaskiya ya yi dadi , har na matsu ya gama " wani cool murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ke ce mutum ta farko da ta ci abun da na girka kuma ya ce ya yi dadi " " hmmmm , yanzu mintina nawa za mu jira ? " " just 20 minutes " ya fada a takaice wani dogon nunfashi ta ja ta na saukewa a hankali kafin ta ce " Yanzu me za mu yi ? " sai da ya dan jinkirta kafin ya ce mata " Watch cartoon " dan zaro idanu ta yi a hankali ta na fadin " cartoon ? da wannan shekarun naka ? " " yeah , har yanzu ni baby ne " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kai hannu ta ja mishi kumatun shi na dama ta na fadin " yeah , you are a big baby " shi kan shi maganar ta sai da ta ba shi dariya , har sai da wadanan fararen hakwaren nashi su ka fito a hankali ta janye hannunta ta na kallon face din shi gwanin burgewa tun da ta ke ba ta taba ganin murmushi mai kyau irin nashi ba wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta na fadin " mu je na saka maka , Big baby kawai " ba musu ya bi bayanta su ka koma parlourn , su ka zauna sannan ta kunna mishi Tv , ta ba shi remote din sannan ta dauki laptop din ta ta ci gaba da aikin ta cikin nitsuwa Kim ya fara sauya chanel din har ya samu chanel din da su ka saka cartoon kamar wani karamin yaro ya tsaya ya na kallo amma ta wutsiyar ido Esra ya ke kallo ya na a haka kawai ya fara jiyo Muryar ta sama sama kamar ta rero waka shi ko karatun Qur'ani ne ta , ta na karanto suratul Mariam cike da nitsuwa ga Muryar a sanyaye mai dadin sauraro duk da bai san abun da ta ke fada ba amma ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi , irin sanyin da bai taba ji ba a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juyo ya kalle ta da kyau ya ce mata " wace waka ce wannan ki ke ? " wani cool murmushi ta saki kafin ta dasa Aya ta dago kai ta kalle shi ta ce " ba waka ba ce " " to minene ? ni ban taba jin wannan abun ba " " dama ta ya za a yi ka ji shi , kai da ba musulmi ba kuma babu musulmai a kusa da kai , ka san minene religion ko ? " " Eh na sani , amma ban taba yarda da su ba saboda duk makaryata ne , sai su yi ta maganar abubuwa da ba gaskiya ba su na karbar kudaden mutane " " wannan church ne su ke yin hakan , akwai mosque a garin nan zan so ka je ko so guda ne , za ka gane abun da ya ke gaskiya da abun da ya ke karya , amma zan so ka san addini na ba karya ba ne , sai wanda Allah ya so ke samun damar kasancewa musulmi " cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " wanene wannan Allah , kenan in bai so mutun ba ba zai iya zama musulmi ba ? , kenan ni ba ya so na ? " " Allah shi ne ubangijin da mu ke bautawa , shi shi kadai ya ke , babu wani abun bautawa bayan shi , shi ya hallice samai da kassai sannan ya hallice mu dan mu bauta mishi , cikin addini na shan wine haramun ne , shi ya sa na ke son ka daina , bayan hakan babbar illa ce ga rayuwar ka ma " bai ce mata komai ba ya mike a hankali ya nufi kitchen Esra kuwa tambayar shi ba karamin dadi su ka yi mata ba tun da har zai iya tambaya wanene Allah hakan na nufin ta fara jan hankalin shi zuwa ga musulumci , in har Kim ya koma musulmi to tabbas abun alfahari ne wajen ta ta na kallon shi har ya shiga kitchen din ya bude oven kai tsaye kawai ya kai hannu zai dauki tray din a dubu dari ya janye hannun ya na ja da baya shi duk ya mance da zafi abun gare shi da sauri Esra ta ajiye laptop din ta ta tasso ta nufe shi ta na fadin " Oh my God , Kim kai ma ina hankalinka za ka sa hannu kai tsaye babu mitten " " mantawa na yi " ya fada ya na matsowa wajen washbasin ya kunna fanfon ya zuba ma hannun shi ruwan sanyi kafin ya janye cike da kula Esra ta ce mishi " mu je na shafawa maka pommade kar wajen ya ja ruwa ya zame maka matsala " potholder ya dauka ba tare da ya ce mata komai ba ya saka , sannan ya fiddo tray din ya ajiye saman counter ya na ajiye wa wani qamshi mai dadi ya fara tashi a wajen ko ni sai da na hadiye yawu a hankali ya juya ya nufi gudan oven din ya bude ya fiddo tray din ya ajiye geffen dayan sannan ya fidda gloves din ya ajiye gefe ita dai Esra ta zama yar kallo a nan ta na hadiyar yawu shi kuma plates biyu ya dauko , dan madaidaita , ya dauki spoon da fork ya fara dauke Apple pie din nan daya bayan daya ya jera saman dayan plate sannan ya fara kwassar fish din nan da potato da carrot ya Zube duk saman dayan plate , sannan ya dauki tray din ya kai wajen washbasin ya ajiye MY BOOK IS ₦500 VIA 8081129487 Khadija Sabi'u Monie point bank 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 25 & 26 🕊❤} bayan ya ajiye ya dawo ya tsaya geffen ta ya ce " here is , ga shi na kammala " da murmushi a face din ta ta ce " gaskiya da ga gani zai yi dadi , Yanzu ka iya girki haka ka ke neman bata wa kan ka lokaci wajen yin security a nightclub , why ba za ka nemi aiki ba a wani restaurant ba ? " " na nema , amma duk restaurant din da na je sai su ce na gwada musu takardun karatu na ko certificate din kwarewa ta a girki , ni kuma ko primary school ban yi ba , shi ya sa na hakura na daina nema " har cikin zuciyar ta ta rasa dalilin da ya sa ta ke mugun jin tausayin Kim , he look so innocent , amma rayuwar shi ta na neman ta ruguje haka , gaskiya ya kamata ta gyara mishi rayuwa ko da shi ne abu na karshe da za ta yi a ta/ta rayuwar wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce kai hannu ta dauki plate din Apple pie ta na fadin " okay , let's go and eat " ta kai karshen ta na fara takawa ta nufi parlour ba musu ya dauki dayan plate din ya bi bayan ta su ka nufi yar dining table din su ta ajiye a sama sannan ta zauna saman chair guda ta na ce mishi ya zauna ajiye plate din kawai ya yi kafin ya dan ja da baya ya na ce mata " no , lokacin hawa aikina ta kusa , tafiya zan yi " marairaice fuska ta yi ta na mikewa tsaye har ta bude baki kawai ta ga ya juya ya fara takawa zai fice da sauri ta ce mishi " Kim , ka tsaya na zuba maka cikin box kar ka tafi da yunwa " ko juyowa bai yi ba ya sa kafa ya fice ya janyo mata kofar ita dai da kallo ta raka shi har sai da fita sannan ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta koma zauna ta so ya tsaya su ci abincin tare ko da pie din ce tun da ita ce favorite dessert din shi , amma yanzu ya tafi a hankali ta kai hannu kai tsaye ko spoon ba ta saka ba ta dauki Apple pie din nan guda ta kai a baki ta na bismillah sannan ta fara ci a hankali ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya kafin ta lumshe idanunta a hankali , gaskiya taste din da yi mata mugun dadi , ita ba ta ma taba cin Pie din da ta yi mata dadi irin wannan ba , ga shi abun so easy amma taste din duniya ne guda , gaskiya Kim ya iya girki cikin kankanan lokaci ya shirya wannan abun ina ga an ba shi isashen lokaci abun da zai yi sai ya fi hakan sai da ta gama cinye sannan ta tashi a hankali ta nufi corridor ta shiga a hankali ta kai hannu ta tura kofar bedroom din Safna ta na sallama kassa kassa a konce Safna ta ke saman bed din ta , ta na rufe da duvet ta na ganin Esra ta dago kai a hankali ta na amsa mata sallamar ta a hankali Esra ta karaso cikin dakin ta zauna bakin gadon ta na fadin " ya jikin naki ? " wata yar karamar ajiyar zuciya Safna ta sauke kafin ta ce " da sauki , amma yunwa na ke ji , tun dazu na ke jin wani qamshi na tashi ban san da ga ina ya ke ba , please gyara min wani abu na ci " wani dan karamin murmushi Esra ta saki kafin ta ce " tashi mu je ki ci , shi ya sa ma na zo na kira mu je mu ci abinci " ta na gama fadar haka ta mike ta nufi kofar fita a hankali Safna ta janye duvet din jikin ta , ta mike zaune ta sauko da kafafun ta kassa ta mike tsaye ta fara takawa a sanyaye ta fito dakin ta na fitowa ta isko Esra zaune saman yar dining table din su dan zaro idanu ta yi ta na kallon abincin da ke sama ta karaso wajen ta janyo dayan chair din ta zauna ta na fadin " Esra , ina ki ka samo wannan abincin ? " wani dan karamin murmushin geffen fuska Esra ta yi kafin ta ce " kamar ya ? ni na shirya " a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " fadi gaskiya , na san kin iya girki amma ba ki taba girka irin wannan abincin ba , asali ma ban taba ganin ki gyara fish ba , ko dai sayo wa ki ka yi ? " wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " kin yi gaskiya , ina saurayin nan da mu ka taimaka a garden ranar nan ? " a hankali Safna ta gyada mata kai allamun ta gane shi " To shi ne ya zo ya girka mana , kuma da yay duk karfe 8 zai zo mu yi girki tare " dan tabe baki Safna ta yi ta na kai fork din da ta debo fish da potato a ciki ta kai baki sai da ta gama ta hadiye sannan ta kalli Esra ta ce " Yanzu saurayin nan ya yi wannan girkin ? " gyada mata kai Esra ta yi ta na fadin " ni kaina na yi mamakin yadda a ka yi ya iya girki haka , kuma wlh ko one hour bai yi ba " " gaskiya ya fi shirmen da ki ke girka mana " ta qarashe maganar ta na wata yar karamar dariya , kamar ba ita ba ce dunkule kamar an aiko mata mutuwa ita ma Esra wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mata " wannan karan zan yarda da ba ki yi karya ba , amma ai koya min zai yi nan gaba kadan sai na fi shi kwarewa " ita dai Safna ba ta ce mata komai ba ta na cin abincin kawai ba karamin dadi ya yi mata ba Esra na ganin ta yi shiru ta gane ta tafi , hakan ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru ta ci gaba da cin abincin sai da su ka cinye komai har Apple pie din ba su rage ba sannan su ka tashi su ka gyara wajen Safna kuwa har ta dan ji karfin jikin ta bayan sun gyara table din su ka wanke plates din a tare sannan Esra ta dawo parlour ta zauna Safna kuma ta koma bedroom din ta , ciki ya cika sai barci _________________________________________ ▪AYDEN 🦋 💙 konce ya ke saman wata doguwar sofa fara kal , ya daura hannun shi guda saman cikin shi , gudan kuma saman idanun shi , wa ya sani ya na farke ko barci ya ke ya na a haka Adrian ya shigo parlourn da ga shi sai short da singlet fuskar shi da damuwa a kai ya nufi wajen kafafun Ayden ha na zauna murya a sanyaye ya ce " Ayden , ba ka ce komai ba dangane da paper din nan ba ? " shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai amma ya na jin shi dan ba barci ya ke ba a hankali Adrian ya kai hannu ya buge shi a cinya ya na fadin " bro , da kai na ke magana please ka ce wani abu mana "

Chapter 9 of 12