Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rike da hannunta ba musu ta bi bayan shi ta na murmushi cikin zuciyar ta ta na fadin " za ka gani , in sha Allah sai ka bude baki ka roke ni na zama abokiyar ka " a hankali su ke tafiyar su cikin park din kamar wasu masoya a haka su ka fara hango wasu samari guda uku zaune saman wani bancin , biyu na rike guitar dayan kuma ya na rike da saxophone su na kidan su cikin konciyar hankali , kuma gaskiya sun iya [28/02 à 08:19] 🪷🩷: 💞 🔥 TRUE LOVE 🔥 💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 29 & 30 💙💦} a hankali ya juya ya ce mata " mu tafi ko gani " ba musu ta bi bayan shi su ka iso wajen musician din nan , su ka tsaya kawai su na kallon su haka su ma samarin ba su daina kidin nasu ba , har sai da su ka kammala su na kammala wa ko Kim ya shiga yi musu tapi , da sauri ita ma Esra ta shiga yi musu tapi ta na wata yar karamar dariya da ga haka Kim ya ba su hannu daya bayan daya su ka gaisa sannan Kim ya ce musu " gaskiya , song don nan ya yi min dadi sosai " a tare su uku su ka yi dariya kafin su yi mishi godiya " please , ko za ka ara min guitar din ka ? ina so na gwada ni ma " " why not " wanda ke rike da guitar guda ya fada ya na mika mishi guitar din hannun shi wani kyawatencen murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya karbi guitar din , sannan ya zauna geffen shi da sauri Esra ta ce mishi " Kim , ka ga ka ba shi abun shi , yaushe ka iya wassan guitar ? " bai ce mata komai ba ya fara buga guitar din sai da ta dan zaro idanu jin yadda ya ke buga ta cike da kwarewa , har su kan su musician din sai da kidin ya burge su shi kuma sai ya dan yi nisa da kidin sannan ya bude baki cike da nitsuwa ya fara rera waka ya na fadin " LOOKING ME LIKE I'M CRAZY , WHEN I SHOT MY FEELINGS OUT LOOKING ME LIKE I'M DIFFERENT , STILL YOU STAY CAUSE YOU FEEL SOMETHING REAL IT'S SO LOST IN MY MOMENT , DOESN'T MEAN I DON'T NEED YOU , I , I........ FELL IN LOVE WITH THE COLORS , THEY KINDA TELL ME WHAT I'M THINKING FELL IN LOVE WITH THE WAY WE ARE , AND THE WAY WE LOSE IT SOMETHING DIFFERENT ABOUT US , AND THE REASON WHY WE STAY , STAY...... WE FLY AROUND LIKE PAPER PLANES THEY NEVER KNOW WHERE WE WILL FALL NOBODY CAN SEE US STILL THEY WANNA TEAR US APART , THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT THE WAY WE ARE , ARE , ARE......... OOHHHHHH , OOH , OOH......... THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT US OOHHHH , OOH , OOHHH........ THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT US " Ita dai Esra ta tsaya cak ta na kallon shi , ta na sauraron zazzakar Muryar shi ya na wakar shi cike da nitsuwa ba ita ba har su musician din sai da ya burge su slowly ya daina kidan bayan ya gama rera wakar shi , har ya daina kafin ya dago kai slowly , idanun shi ba su sauka ko ina ba sai cikin na Esra ta na ganin ya tsaya ta saki wani cool murmushi ta na yi mishi tapi a tare su ma samarin nan uku su ka shiga yi mishi tapi kafin wanda ya ba shi guitar din ya ce " guy , wakar nan ta hadu gaskiya " wani dan karamin murmushi Kim ya yi kafin ya mika mishi guitar din shi ya na fadin " na gode " a hankali ya kai hannu ya karba , mikewa tsaye Kim ya yi kafin ya koma geffen Esra ya tsaya ya riko hannunta , ya na kallon musician din nan ya ce musu " mun gode sosai " wanda ke rike da Saxophone din ne ya amsa mishi da cewa " ba komai , we are HAPPY to see mun saka couple din ku farin ciki " dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon shi jin ya ce wai couple har ya bude baki zai yi magana Esra ta riga shi cewa " Thanks a lot " ta na gama fadar haka ta juya ta kalli Kim ta ce mishi " let's go now " ba musu ya bi bayan ta su ka bar wajen ya na tunanin abun da saurayin nan ya ce wai couple , yanzu a haka sun yi kama da couple ? shi ko bai san tun lokacin da su ka shigo park din kowa kallon couple ya ke yi musu musaman hannun ta da ya ke rike da sai da su ka yi dan nisa sannan ta ce mishi " Kim , babu toilet a cikin park din nan ? " ba tare da ya juyo ba ya ce mata " akwai , ki na son shiga ne ? " " Eh " ta fada a takaice bai ce mata komai ba su ka ci gaba da takawa har su ka karaso wajen toilet sai da su ka iso sannan ya saki hannunta ya na nuna mata kofar wata toilet ya ce " cen ne toilet din Mata " okay kawai ta fada mishi kafin ta taka ta shiga toilet din ya na ganin ta shiga ya juya ya nufi wata katuwar bishiya da ya hango ta na fuskantar toilets din , ya jingina bayan shi jikin bishiyar ya lumshe idanunshi , ya tafi duniyar tunanin shi ya na a haka ya jiyo Muryar Esra ta na fadin " Kim , na ga jakata please " slowly ya bude idanun shi kafin ya juyo ya kalle ta ya mika mata bag din hannu ta kai ta karba ta na yi mishi godiya , bai ce mata komai ya juya ya lumshe idanunshi hannu ta kai cikin bag din ta fiddo wata yar karamar leda , sannan ta ajiye bag din gaban ta bude ledar ta yi ta fiddo wata ledar amma kamar sallaya ta ke a hankali ta daga kai ta kalli sama , kafin ta juya ta shinfida Sallayar , ta na fuskantar gabas , ta haye sama ta juyawa Kim baya sannan ta kai hannu ta warware veil din ta , nan take jelar gashin ta , ta warware ta zubo mata har tsakiyar baya slowly Kim ya bude idanun shi wai ya ga me ta ke yi , nan idanun shi su ka sauko saman gadon bayan ta da jelar gashin ta ita kuma bude veil din ta ta yi nan ga ashe babba ne sosai kawai ta na ninke shi ne meda ta yi ta yi Rowling din shi a kai , ya zubo mata har wajen guiwa cikin nitsuwa ta tada sallar ta shi dai Kim ya tsaya ya tsare ta da ido ya na kallon yadda ta ke sallar sai da ta yi sujada ta farko sannan ya ce mata " minene ki ke yi haka ? " kawai sai ya ga ko juyowa ba ta yi bare ta amsa mishi , hakan ya sa ya ja bakin shi ya yi shiru , ya zauna a kassan bishiyar ya na kallon ta kawai sai ya ji wani bakon yanayi cikin zuciyarshi , ya ji wata nitsuwa ta shigo lokaci guda ita kuma cikin nitsuwa ta yi sallar ta , bayan ta gama ta zauna ta na addu'o'in ta ta shafa kafin ta juyo a hankali ta shafa mishi shi ma ya na ganin haka ya ce mata " wai me ki ke yi tun dazu na miki magana kin kyale ni " wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Sallat ce na yi " cikin rudu ya ce " Sallat ? minene sallat ? " " ta na daya da ga cikin kinshigin addini na , sallat ita ce abu me mahimanci ciki addinina , ta ita ce kawai a ke iya gane musulmi " " kamar dai irin sallar da a ke yi church ? " girgiza mishi kai ta yi a hankali ta na fadin " a'a , ka na dai gani yadda na yi yanzu , haka nan su ke yi a church ? " slowly ya girgiza mata kai allamun a'a sai da ta saki murmushi sannan ta ce " to ka gani , ka ga ko na fada maka ba ganewa za ka yi ba dan haka tashi mu tafi " cikin nitsuwa ya ce mata " wata rana za ki fada min ? dan ina son na san yadda addininki ya ke " wani kyawatencen murmushi ta saki abun da ta ke so ya samu , cikin sanyin murya ta ce mishi " yau daddare idan ka je , zan yi maka bayani " okay kawai ya fada mata kafin ya mike tsaye , ya na fadin su tashi su koma gida ba musu ta tashi ta nade sallayar ta , su ka bar wajen a tare su ka baro park din sai da ya raka ta har building din su , sannan su ka yi sallama , shi ya juya ya bar wajen ita kuma ta shiga ciki , da allamun ta mance da sallamar ta da kevin ya yi ko da ta koma apartment din su bayan ta ajiye bag din ta , kai tsaye toilet ta wuce ta yi wanka , ta fito ta shirya cikin kananan kaya kawai ta haye gado ko two minutes ba ta yi ba barci ya yi gaba da ita _________________________________________________________ ▪BROOKLYN ▪DISTRICT OF WILLIAMSBURG A zaune duk mutanan gidan su ke a saman dining table su na cin abincin su cikin konciyar hankali , amma Ayden ya na zaune ya na rike da wata jarida ya na karantawa , ya rufe fuskar shi da ita ba na iya ganin komai sai hannayan shi da ke rike da jaridar cen sai Brian ya ce mishi " Ayden , ka ajiye jaridar nan ka ci abincinka tun bai yi sanyi ba " ya fada cike da kula ba tare da ya ajiye jaridar ba Ayden ya ce mishi " i'm full Dad , mun biya restaurant ni da Adrian kafin ya sauke ni " " okay , " Brian ta fada a takaice kafin ya juya ya ci gaba da cin abincin shi su na a haka su ka jiyo Muryar Ayden ya na fadin " Kevin , na ji an ce ka sallami wata da ga cikin ma-aikatan mu na one world trade center " ba tare da ya kalle shi ba Kevin ya ce mishi " Yes , haka ne " " zan iya sannin dalilin ka na sallamar ta ? ko wani laifi ta yi maka ? " cikin ko in kula Kevin ya ce mishi " no , kawai na gaji da aikin ta ne , kullum late ta ke zuwa shi ya sa na sauwake mata aikin " dan jinkirtawa Ayden ya yi kafin ya ce " dan ta na zuwa late kawai sai ka sallame ta , ba ka san abun da ke tsayar da ita ba , kuma ai ni ban ba ka izinin sallamar ta ba " shiru Kevin ya yi bai ce mishi komai ba ko dago kai ma bai yi ba ya na cin abincin shi a hankali Ayden ya mike tsaye ya na rike da jaridar ya ce " next time idan za ka sallami wani ma-aikacin ka fara ba ni hujjojin sallamar tashi kafin ka sallame shi , ba zan lamunci ka na sallamar ma-aikatana ba haka kawai babu dalili , kar ka manta kai ma zan iya sallamar ka idan har na ga dama " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi stair ya haye gaskiya maganar shi ta yi matukar sosawa Kevin rai , sai da ya ji ya fara takawa sannan ya dago kai a hankali ya bi shi da kallo har sai da ya haye stair sannan ya kai hannu ya dauki glass din ruwan geffen shi ya juya ya tilla shi a glass din bayan shi ya na huci kamar zaki cikin sanyin murya Brian ya ce mishi " Kevin , ai ba karya ya yi ba , why za ka dinga sallamar ma su yi mishi aiki ? at least ka fara sanar mishi , ka yanzu ya karbi kayan shi , zan so ka hakura ka bar mishi ya kula da abu ne " Cikin bacin rai Kevin ya juyo ya wurga ma Brian wani mugun kallo kamar ba shi ne mahaifin shi ba " dama na sani ka fi son shi fiye da mu , mu ne fa yaran ka ba shi " Kevin ya fadawa Brian da sauri Emilie ta ce mishi " Kevin , wannan zancen bai tasso ba na Daddy ya fi son shi fiye da mu , na sani tun ya na karami ka ke mugun kishin shi har zuwa yanzu , please ka danne zuciyarka , tsawan shekaru 20 ya na tare da mu amma har yanzu ka kassa kabar shi a matsayin dan uwanka " ta karashe maganar cikin dan rauni wata boyayyar ajiyar zuciya Kevin ya sauke kafin ya ce mata " ranar da ya bar duniyar nan a ranar zan karbe shi a matsayin dan uwana " ya na gama fadar haka ya mike ya nufi stair ya haye da kallo Brian da Emilie su ka raka shi har sai da ya Haye sannan Emilie ta kalli Brian , ta na marairaice fuska ta ce " Daddy , why Kevin ba ya son Ayden ? brother din mu ne fa , amma duk duniya shi ya tsana " " na sani Emilie , Ba ba ya son shi ba ne kawai hanyar da ya shigo ahalin mu ne ba ya so , tabbas na san abun da momyn ki ta yi bai dace ba , kuma har yanzu ina jin zafin hakan , amma ba laifin Ayden ba ne abun da ta yi , shi kan shi na san ba zai so ya shigo duniya ta hanyar cin amana , amma babu yadda mu ka iya " " yanzu kennan Daddy kai ma ba ka son Ayden ? " ta fada idanun ta na cikowa da ruwa wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya kai hannun saman face din , murya a sanyaye ya ce mata " ko kusa , yadda na ke son ku haka na ke son shi har cikin zuciyata " wani dan karamin murmushi Emilie ta sakin mishi ba tare da ta ce komai ba su na a haka Ayden ya fara sauko stair , ya na sanye da wasu Tracksuit purple , da sneakers farare , ya saka wata face mask white ita ma , da wata coat black color sam ba na iya ganin face din shi bai bi ta kan su ba ya nufi kofar fita gidan ya fice abun shi [28/02 à 10:12] 🪷🩷: 💞 🔥 TRUE LOVE 🔥 💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 31 & 32 💫💛} da kallo Emilie da Brian su ka raka shi har sai da ya fice sannan Brain ya yi wata yar karamar dariya ya ce " ke dai wannan dan uwan naki ya na son face mask " ita ma dariya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba 💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛 ▪ESRA ❤🌼 zaune ta ke cikin parlourn apartment din su , ta yi zugum waje guda ta na tunanin yanzu ya za ta yi tunda ba ta da aiki ta ya za ta ci gaba da zama a New York , ba za ta iya daurawa Safna nauyin ta ba , in ba ta koma Nigeria ba , to dole ta nemi aiki ko da na server ne ta na cikin duniyar tunaninta ta ji a na yi musu knocking a hankali ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar ko tambaya ba ta yi ba kawai ta bude kofar ta na budewa idanunta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar sanye da wani wandon jeans dai'dai guyiwa white color da wata shirt white , gashin nan nashi a gyare yau ya yi wani smooth a konce gefe guda ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta na shirin magana ta jito wayar ta ta na ringing a hankali ta juya ta na fadin " bismillah , come in " ba musu ya shigo ya meda kofar ya rufe Esra kuma ta nufi wayar ta ta dauka ta na kallon Screen din wayar ta ga sabuwar number ce kuma ta New York ce cikin rudu ta dago ta kalli Kim da ke tsaye ya na kallon ta kamar shi ne ya kira ta a hankali ta dawo da kallon kan wayar kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ba tare da ta ce komai ba kawai sai ya jiyo Muryar Adrian ya na fadin " please ina son magana da Miss Esra Yahaya " " ita ce " ta fada a sanyaye murya cike da tsoro cike da fara'a ta jiyo Muryar Adrian na ce mata " Good , Miss Esra my name is Adrian Manager of Ayden Brian , PDG of ONE WORLD TRADE CENTER , na san dazu da safe sir Kevin ya je ya ce miki ya sallame ki haka ne ? " a hankali ta zauna saman sofar kamar za ta yi kuka ta ce " Eh haka ne , please sir ku yi hakuri , in sha Allah zan gyara ko ma minene matsa...... " da sauri Adrian ya katse ta da cewa " I'm sorry Miss Esra Sir Kevin bai isar da sakon ba yadda ya dace , ba sallamar ki a ka yi ba , Sir Ayden ne ya ba ki promotion na zama P.A din shi " cikin rudu ta ce " P.A ? " " Yeah P.A , hakan na nufin za ki samu karin Albashi , sannan kuma promotion din ta na tare da gida da mota duk na P.A din shi , in har kin amince ki zo company karfe 7 da rabi dai'dai dan sa hannu a cikin sabon contract din , da ga nan ki fara aikin ki , Hope za ki zo , Na gode " ya na gama fadar haka ya katse kiran slowly Esra ta sauko da wayar ta na kurawa gaban ta kallon ta kassa wani motsi ganin ba ta ce komai ba ya sa Kim matsowa ya na fadin " Miss Chocolate , what happened ? " ya na rufe bakin shi ya ji ta saki wata yar karamar kara ta tashi da sauri ta na tsale ta na kara kamar wata yar karamar yarinya dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon ta cike da rudu ya ke fadin " Miss Chocolate are you okay ? what happened ? " ba ta ba shi amsar tambayar shi kawai ta nufe shi ta riko hannayanshi ta fara jujuwa da shi ta na dariya shi dai kawai ya biye mata sai tambayar ta ya ke amma ta ki amsa mishi kawai ya ja bakin shi ya yi shiru sai da ta gama juyin nata sannan ta shiga yi wa Allah godiya ta na karanto addu'a ta na shafawa kafin ta kalli Kim ta ce " ka san wani abu ? " " ta ya zan sani bayan tun dazu ina tambayar ki kin kyale ki ne " ya kai karshen ya na kauda kai wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " i'm sorry , farin ciki ne ya hana na ji ka , yanzu Manager din shugaban companyn mu ya kira ni , ya ce an ba ni promotion din zama P.A din Shugaban mu , hakan na nufin za su min karin Albashi " dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon ta baki sake ya ce mata " P.A fa ? " da sauri ta gyada mishi kai ta na murmushi ta ce " hakan na nufin za mu samu kudin sayan Chocolate ko yaushe , kuma har gida su ka ba ni da Mota " shiru ya yi bai ce mata komai ba , ya ma rasa me zai ce mata ganin bai ce komai ba kawai sai ta daina murmushin , a sanyaye ta ce mishi " Kim , da allamun ba ka ji dadin abun da na fada maka " wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi wani dan karamin murmushin geffen fuska ya ce " Ta ya za ki ban ji dadi ba ? ni da za a dinga saya ma chocolate kullum , congratulations I'm really happy for you " ya qarashe maganar ya na mika mata hannu ba musu ta riko hannunshi su ka gaisa ta na sakin wani kyawatencen murmushi da ga haka ta ce mishi " okay , yau me za mu girka kuma ? " dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " ina ga kamata ya yi mu fita mu yi celebrated wannan news , ko ya ki ka gani ? " ya kai karshen ya na daga mata gera guda da sauri ta nufi Corridor ta na fadin " give me ten minutes yanzu na dawo " da

Chapter 11 of 12