Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mu , kuma kin ba ni shikenan , why za ki takura min ? " wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ni kai na ban san abun da ya sa na takura maka haka ba " " to ki rabu da ni mana " ya fada ya na kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo wata sabuwar tabar da sauri ta kai hannu ta buge tabar ta na fadin " Please , stop , ka san irin illar da abun nan za ta yi maka ba , tun safe ka na sha " " breakfast ne na ke " ya fada ya na sake kai hannu ya fiddo sabuwar tabar yanzu ma hannu ta kai ta buge ta na fadin " mu je na saya maka breakfast to " " da kuma tabar da ki ka buge min " ya fada ya na kai bayan trush ya fiddo wasu sneakers purple ma su kyau , ya saka a kafafun shi kafin ya mike tsaye wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " na yarda , amma bisa sharadi guda " daga mata gera guda ya yi ya na fadin " wane sharedi kuma ? " " can i be your friend ? " ta qarashe maganar ta na mika mishi hannu kallon hannun nata ya yi na dan lokaci kafin ya girgiza mata kai a hankali ya ce " kin taba ganin duhu da Haske sun hadu a waje guda ? ni kamar duhu na ke , ke kuma haske , ba za mu taba kasancewa a tare ba , haka tsarin rayuwa ya ke " " to ka ba ni dama , na mamaye duhun rayuwar ka da haskena , ka ba ni dama na sauya wannan tsarin , kai ma ka na da izinin samun abokin da zai taya ka kuka , wanda zai taya ka dariya , wanda zai sauya maka rayuwa , ka ba ni damar kasancewa wannan abokin " sai da ya kare mata kallo da kyau kafin ya ce mata " shikenan , na yarda mu zama abokai just for two weeks , cikin satin nan biyu in har ki ka yi nassarar sauya min rayuwa , abotar mu za ta kasance ta har abada " wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " Eh , na yarda just two weeks , zan sa ka daina shan wine da taba , zan gwada maka colors din rayuwa , idan ban yi nassara ba zan kyale ka har abada " " All right ! " ya fada ya na riko hannunta su ka yi musbaha wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan , my new friend , mu je na saya maka breakfast , ina da sauran lokaci kafin karfe 8 ta yi ni ma zan samu na yi breakfast " bai ce mata komai ba ya janye hannun shi ya fara takawa zai bar wajen da sauri ta bi bayan shi ta na sakin murmushi su ka bar wajen , sai tafiyar shi ya ke cike da nitsuwa , ya na kallon gaban shi ita dai Esra sai satar kallon shi ta ke ta wutsiyar ido a haka har su ka karaso restaurant din da Safna ke aiki , cike da mamaki ta shiga restaurant din ta na tunanin yadda a ka yi ya san wajen nan amma ba ta ce mishi komai ba , su ka shiga restaurant din , su ka zauna saman chair sai da su ka zauna sannan Esra ta fara bin wajen da kallo , ta ga su kadai ne babu kowa a wajen , sai servers din da ke kula da wajen a ta mike ta na fadin " bara na yi mana order " gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta fara takawa ta nufi reception ta na barin wajen ko Adrian ya shigo restaurant din , ya na sanye da wasu suit bakake , hannayanshi rike da wasu paper da laptop , ya na taku cike da nitsuwa tun da ya shigo Kim ya tsare shi da ido babu ko kiftawa , har ya nufi VIP space ya zauna , ya bude takardun shi ya fara aikin shi a hankali ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ya kauda kan shi , dai'dai lokacin da Esra ta dawo wajen ta zauna saman chair din ta , ta na fadin " hope ka na shan coffee ? " " Coffeeeeee ? , na yi miki kama da me shan coffee ? may be ice tea zan iya sha , amma ban da coffee gaskiya " ya kai karshen ya na kauda kai wata yar karamar dariya ta yi , ta na shirin magana idanun ta su ka sauka saman Adrian da ke zaune bayan Kim , a VIP space nan take yanayin face din ta ya sauya , ta karewa Adrian kallo da kyau , nan take kalaman Safna su ka dawo mata a kai na wani da ke zuwa ko wace safiyar monday restaurant din amma ya a ka yi , yau Friday ba monday ba da sauri ta kai hannu cikin bag din ta ta fiddo wayar ta ta saita Kim akwai ta danna ta yi mishi pic , ga shi ko shi ma ita ya ke kallo pic din sai ya yi kyau gwanin burgewa wani dan karamin tsaki ta yi ta na fadin " Kim , yi gefe guda please " ba musu ya yi gefe kafin ya juya ya ga abun da ta ke son gani a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ga Ta na yi wa Adrian Pic cikin rudu ya ce mata " celebrity ne ? why ki ke yi mishi pic ? " ba ta ce mishi komai ba ta sauko wayar ta , ta meda cikin bag din ta , dai'dai lokacin da Server ya iso wajen rike da tray din order da Esra ta yi , ya shirya musu abincin saman table din su sannan ya juya ya bar wajen ya na barin Wajen Kim ya kai hannu ya dauki Fork ya fara cin toast din da a ka shirya da Eggs , ita dai Mug din coffeen kawai ta dauka ta fara sha ta na kallon shi ya na cin abincin cike da nitsuwa , ga shi ko yadda ya ke aiki fork din sai ka rantse da Allah shi ne jikan Sarauniyar UK Elizabeth amma ita duk da idanun ta na saman shi , hankalin ta na kan Adrian , shi ko bai ma san abun da ke faruwa ba , sai aikin shi ya ke cikin konciyar hankali a haka har Kim ya kammala breakfast din , ya sha ruwa ya na yi mata magana amma ba ta ji shi ba a hankali ya kai hannu ya kyasta mata yatsu saitin face din ta a razane ta dawo cikin hayacinta ta kalle shi ta na fadin " What ? me ya faru ? " " za ki yi late wajen aikin ki " ya fada dan ya na son ya dan tsoratar da ita a razane ko ga dauki bag din ta ta mike ta na fadin " wayyooo ni Esra na shiga uku wajen Sir Kevin , na tafi " " wait , bari na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye ina ko sauraron shi ba ta yi ba ta nufi kofar fita , Kim kuma , a hankali ya juya ya kalli Adrian kafin ya juya ya bi bayan Esra su ka bar wajen su na barin wajen ko Safna ta shigo sanye da uniform din ta bangaran Esra kuwa , tafiya ta ke da sauri da sauri , Kim na biye da bayanta ya na kiran sunanta amma ba ta tsaya sai da ta karaso one world trade center sannan ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ta tsaya a hankali ta juyo ta kalli Kim da ke tsaye bayan ta ta ce mishi " na tafi sai mun hadu an jima " gyada mata kai kawai ya yi kafin ta juya ta shiga hall din ta na shiga ko Motar Kevin ta yi parking bakin hall din ya fito sanye da wasu suit purple ma su mugun kyau , ya na sanye da glass a idanun shi kamar an kira sunan shi kawai ya juya ya kalli saitin da Kim ke tsaye nan take su ka yi ido hudu , Kim na ganin hakan ya juya cikin nitsuwa ya bar wajen da kallo Kevin ya raka shi har sai da ya kurewa ganin shi sannan ya juya ya shiga Building din โ–ชADRIAN sai da ya yi wajen good 30 minutes bayan fitar su Esra kafin ya jiyo Muryar Ayden ya na fadin " har yanzu ba ka gama ba mu tafi ? " wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya dago kai ya kalli Ayden ya na tsaye gaban table din , ya na sanye da wasu Tracksuit white color ma su mugun kyau , rigar na da hula ya saka wasu sneakers green kalar gashin kan shi , amma ba ka iya ganin face din shi dan ya saka Face mask , da wasu glass kamar medical glass , amma su na dan duhu kadan ba ka iya ganin idanun shi " tun dazu kai na ke jira , ya ? a kawo maka coffee ? " Adrian ya fada girgiza mishi kai Ayden ya yi a hankali ya na fadin " No , idan ka gama tashi mu tafi kawai " " okay mu tafi " ya fada ya na tattare papers dinshi , waje guda sannan ya mikawa Ayden laptop din shi ba musu Ayden ya karbi laptop din , su ka fara takawa a tare su ka bar wajen har su karaso wajen Table din da su Esra su ka zauna kawai sai ya ji ya taka wata paper cak ya tsaya ya na kallon paper din kassan kafar shi a hankali ya sunkuya ya dauki paper din ya na kallon ta kafin ya kalli table din da su Esra su ka zauna , har yanzu ba a gyara table din kawai sai ya yi tunanin ko na wanda ya zauna a wajen ne da sauri ya taro Ayden da ya nufi kofar fita ya na fadin " Ayden wait two minutes please " a hankali Ayden ya juya , ya gyada mishi kai allamun okay wani dan karamin murmushi Adrian ya yi kafin ya nufi reception ya na fadin " excuse me , wanda su ka zauna a cen sun manta wannan , da allamun kuma ya na da mahimanci " wani cool murmushi Safna ta sakin mishi kafin ta ce " okay , na gode , za mu yi kiran su mu mayar musu " " okay " Adrian ta fada , ya na shirin dago paper din na hannun shi su ka kubce da sauri ya sunkuyo ya dauki takardun shi kafin ya mikawa Safna paper din da ya tsinta kafin ya juya ya bi bayan Ayden su ka bar wajen kallon paper din da kyau Safna ta yi , cen kassa a geffen dama ta ga an rubuta ONE WORLD TRADE CENTER , allamun da ga companyn su Esra paper din ha fito a hankali ta juya ta kalli dayar receptionist , cikin sanyin murya ta ce mata " Please duba min cikin register First client din mu na yau , minene sunan shi " ba musu ta duba register din gaban ta kafin ta ce " Esra yahaya , around 7h20 su ka shigo wajen nan " " okay , na gode " Safna ta fada ta na murmushi kafin ta ninke paper din ta saka cikin bag din ta bangaran Adrian kuwa ya na fitowa ya tardo Ayden zaune cikin wata dankareriar mota fara kal ta ji da gani , irin motar da sai wane jikan wane ke iya shigar ta ba banza bare ba , dan tayoyin ta ma sun isa daukar ido kai tsaye wajen driver ya nufa ya shiga dan ya San halin abokin nashi , ba ya son tukin mota , idan kuma ya ce zai yi tukin to tabbas mutuwa zai tunkara dan ba karamin gudu ya ke ba kamar zai tashi sama tada motar Adrian ya yi ya na fadin " ina za mu je ? " cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " One world trade center , ina son na yi wa kevin magana a kan tafiyar da za mu yi Washington dan ganin sabon building din da mu ke shirin budewa a cen , ina son mu ware Space din restaurant , at least ina son mu yi two type na restaurant a ciki " wani dan karamin murmushin geffen fuska Adrian ya yi kafin ya ce " wai me ya sa harkar abinci ke burge ka ? ka na fa cikin Top ten din billionaire din United State of America baki daya " " na sani , kawai restaurant din ne ke burge ni , yau Friday , ina fatan ka sa a shirya abincin da a ke aikawa gidan marayu ? " " yeah , ban manta ba , ai ko wace Friday abu na farko da ka ke fara tambaya shi ne Adrian ka sa a shirya abincin da za a kai gidan Marayu ? Adrian ka sa an shirya kayan da za a kai gidan marayu ? Adrian ka tura kudin da na ce ka tura gidan marayu ? wadanan tambayoyin kamar a bakin ka a ka yi su , but ina jin dadin hakan gaskiya , kar ka damu na yi duk wani abun da ka ce " " okay " Ayden ya fada a takaice da ga haka ba wanda ya sake ce ma wani ufan har su ka karaso wajen wani traffic light a hankali Adrian ya yi parking din motar , ya na jiran a ba su izinin wucewa a hankali ya juyo ya kalli Ayden , ya ga ya lumshe idanunshi ya tafi duniyar tunanin shi wani cool murmushi Adrian ya saki kafin ya juya ya ce " me ka ke ji in ka na tare da ita ? " kai tsaye Ayden ya ce mishi " peace " a takaice da allamun ba ya cikin hayacin shi murmushi mai dan sauti Adrian ya yi kafin ya ce " ka yi a hankali , kar plan din ka ya juye maka " shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba , da allamun ya lula duniyar tunanin shi bai ma san abun da ya ke ba a haka har traffic light din ya nuna green , Adrian ya ja motar su ka bar wajen [17/02 ร  14:02] ๐Ÿชท๐Ÿฉท: ๐Ÿ’ž SOYAYYAR GASKIYA ๐Ÿ’ž __________________ ๐Ÿ’ž๐Ÿ”ฅ TRUE LOVE ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ž ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH ๐Ÿ’‹ GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ุฑุจูŠ ุฃุฒุญ ุงู„ุฃู„ู… ุงู„ุฐูŠ ูŠุนุชุตุฑ ู‚ู„ุจูŠ! ุญุฑุฑ ู„ุณุงู†ูŠ ูˆุฎู„ุตู‡ ู…ู† ูƒู„ ุบู…ูˆุถุŒ ุญุชู‰ ูŠูู‡ู… ุงู„ู†ุงุณ ู…ุง ุฃู‚ูˆู„! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM ๏ฝ›P A G E 13 & 14 ๐Ÿ•Šโค๏ฝ a haka har su ka karaso one world trade center , sai da Adrian ya yi parking din motar a parking space sannan ya tabo Ayden cikin sanyin murya ya ce mishi " ta hanyar sirri yanzu ma za ka shiga ko kuwa ? " slowly Ayden ya ware idanunshi , ya sa hannu ya bude kofar motar ya na fadin " no , mu je kawai , two minutes sun isa " ya kai karshen ya na sauka ya nufi hanyar shiga building din cikin nitsuwa Adrian ya kashe motar ya sauko ya bi bayan Ayden ______________________________________ โ–ชESRA ๐Ÿ‘‘ da sauriยฒ ta ke tafiya ko kallon gaban ta ba ta yi , idanun ta cike da ruwa , fuskar ta a marairaice kamar za ta yi kuka , kamar za ta yi kuka ta ke fadin " shikenan ta kare min , in ban samo takardar nan ba wlh mutuwa zan yi " ta na gama fadar haka kawai ta ji ta bugi kirjin mutun da karfi , fuuuuu ta yi baya za ta fadi ta na sakin wata yar karamar kara ta datse idanunta da karfi cikin zafin nama Ayden ya kai hannu ya damko kugun ta ya taro ta ba ta kai kassa ba da sauri ta kai hannu ta riko damtsen shi da kyau ta cak ya tsaya ya na kallon face din ta , ta wani lumshe idanunta ta na cije lips din ta na kassa gwanin burgewa lokaci guda ta tafi da imanin sa , dan ba karamar fadawa ya yi ba su na a haka Adrian ya karaso wajen , ya na ganin yanayin da abokin shi ke ciki ya ida isowa da sauri ya na fadin " Ayden , are you okay ? " a dubu dari Esra ta ware idanunta jin an ce Ayden , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi duk da ya na sanye da glass ba ta iya ganin su lokaci guda idanun su su ka sarkafe cikin na juna , shi kuwa Adrian sai pic ya ke musu dan ba karamin kyau su ka yi ba kamar irin masoyan nan na cikin film haka ma duk wanda ke cikin hall din cak ya tsaya ya na kallon su dai ba su ma san abun da ke faruwa a zagaye da su ba wata boyayyar Ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya mike a hankali ya gyara tsayuwar shi ya tallabo ta ta mike tsaye su na mikewa tsaye ko Kebin ya iso wajen ya na fadin " Ayden , me ya faru ? " ya kai karshen ya na tsayawa geffen Ayden ya na ganin Esra ya saki wani dan karamin tsaki ya na fadin " Miss Esra , you again ? what are you doing here ? " lokaci guda Kuka ya kubce mata , ta bude baki har wata yar kerma ta ke ta na shirin magana Ayden ya daga mata hannu allamun ta yi shiru ba musu ta yi shiru ta na sunkuyar da kai hawaye na zubo mata bibiyu cikin sanyin murya Kevin ya ce " Ayden , Adrian , ku tafi office di na ina zuwa , Miss Esra , koma office din ki " tun bai rufe bakin shi ba Esra ta raba ta geffen Ayden ta bar wajen da gudu ta na kuka sai da ta bar wajen sannan Ayden ya juyo ya kalli Kevin ya ce " me ya faru ne ? " wank dan karamin tsaki Kevin ya yi ya na fadin " nothing , kawai ba ta meda hankali kan aikin ta , shi ne na yi mata magana , mu tafi " " no , in mun je gida mun yin maganar , akwai inda zan je yanzu , Adrian mu tafi " ya kai karshen ya na fara takawa ya fice wajen Adrian na biye da bayan shi shi ma Kevin bayan su ya bi ya bar wajen dama fito ya ke son yi bangaran su Ayden kuwa , ya na isa wajen motar su ya shiga wajen driver , tun kafin Adrian ya iso ya tada motar da sauri Adrian ya nufe shi ya na fadin " Ayden please sauko zan yi driving , ban shirya mutuwa ba please " " za ka shiga ko na tafi ? " ya fada cikin wani yanayi kamar ran shi a bace ya ke da sauri Adrian ya zagayo geffen me zaman banza ya shiga ya zauna ya na zama Ayden ya tada motar ya bar wajen a 360 kamar zai tashi sama , ga shi kuma ya danne horn , ya ki saki da sauri motoci ke rabewa gefe su na ba su waje har police din da ke kula da traffic su ka yi kokarin tsayar da shi amma ya ki tsayawa sai da ya yi ten minutes ya na irin wannan tukin kafin ya ja wani mugun burki sai da kan shi ya bugi steering motar , shi ma Adrian kan shi ya bugu a gaban motar slowly su ka dago kawunan su a tare , sannan Adrian ya ce " you're mad ? kashe ni ka ke son yi ko kuwa ? " a sanyaye Ayden ya ce mishi " i'm sorry , idanu na ne su ka rufe " wani dan karamin tsaki Adrian ya ja kafin ya ce " sauko na mayar da mu gida , ni yunwa ma na ke ji " cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " mu fara biyawa gidan marayu , kuma gidan ka za mu tafi ba zan koma ya yanzu ba " " okay , yadda ka ke so haka za a yi " Adrian ya fada ya na bude kofar geffen shi ya sauko Ayden kuma maimakon ya sauko kawai sai ya matsa ya koma wajen mai zaman banza dan ba ya da ra'ayin saukowa ya shiga yin wani zagaye shi dai Adrian ba abun da ya ce ya shiga wajen driver ya tada motar ya reversing din ta , ya kama hanyar gidan marayu cikin abun da bai fi five minutes ba su ka iso kar ku so ku ga yadda yaran ke farin ciki ganin Ayden da Adrian , sun samu kyakyawan tarba , ga yaran turawa ko da mugun shiga rai ji na yi kamar na sace guda na gudu haka zalika Ayden ya ji wani mugun sanyi a ranshi ganin yaran nan , duk ya na sanye da face mask amma sai da ya yaran nan su ka gane shi , kenan sun san me kula da su Ayden kuma bai yi mamakin yadda a ka yi yaran su ka gane shi ba , sai da ya yi musu wassa kamar wani familyn su sannan ya yi musu albishir zai mayar da su makaranta baki daya kuma shi zai dauki nauyin karatun su ba yaran ba har mai kula da gidan marayu sai da ta yi farin ciki kamar ta yi kuka , ta na yi wa Ayden godiya duk da ba ta san ko wanene ba , ita dai kawai ta san kowace Friday ya na kawowa yaran abincin da kaya wani lokaci har kudi ya ke turawa a kai su shopping , amma ba ta taba sanin wanene Ayden ba sai da su ka yi wajen one hour a gidan marayu kafin su baro shi , su ka nufi gidan Adrian na san kuma ku na son ki san dalilin shi na kula da yaran nan kamar yan uwan shi , nan gaba kadan za ku sani amma ba yanzu wajen ba ku dai ku ci gaba da bibiyar labarin dan yanzu a ka fara kamar kullum ku na tare da alkalamin MEERAH โœŒ๐Ÿ’•๐Ÿ•Š [18/02 ร  11:55] ๐Ÿชท๐Ÿฉท: ๐Ÿ’ž๐Ÿ”ฅ TRUE LOVE ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ž

Chapter 5 of 12