Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kallo ya rakata har sai da ta shiga sannan ya nufi sofa ya zauna ya na jiran ta sai da ya yi ten minutes cib ko zaune a haka kafin ya jiyo wani dadaden qamshi ya fara tashi cikin parlourn har wani dan lumshe idanu ya yi dan bai taba jin qamshi mai dadi irin wannan ba slowly ya juyo da kallon shi saitin corridor nan ya gan ta ta na tafiya a hankali cike da nitsuwa , ta na sanye da wata Abaya navy blue mai mugun kyau , ta sha ruwan stone launin gold ma su mugun kyau , ta gyara gashin ta , ya zubo mata har saman shoulder ta yafa veil din abayar white color ta na rike da wata yar karamar bag a hannunta , fuskar ta cike da annashuwa tun da ta fito ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , wannan shi ne first time da ya gan ta cikin Abaya kuma gaskiya ta yi mugun kamata a haka har ta karaso gaban shi ta na yi mishi magana amma sam bai ji ta ba tuni ya tafi duniyar shi murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta kai hannun ta saitin face din shi ta kyasta mishi yatsu a dan razane ya dawo cikin hayacinsa ya na fadin " me ya faru ? " cikin zolaya ta ce mishi " irin wannan kallon haka ai sai ka saka min evil eye " bai ce mata komai ba ya mike tsaye ya na fadin " i'm sorry , ban taba ganin ki ba ne cikin irin wannan kayan " daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " sun yi min kyau ? " slowly ya gyada mata kai allamun Eh wata yar karamar dariya ta yi kafin ta yi mishi godiya ta na fadin " yanzu ina za mu je ? " a takaice ya ce mata " shan ice cream , amma ke a ki biya " ba ta ce mishi komai ba ta kai hannu ta dauki wayar ta , ta bude bag din ta ta saka kafin ta juya ta fara takawa ta na fadin " let's go ! " ba musu ya bi bayanta su ka fito , kai tsaye building din su ka baro , su na tafe ta na zuba mishi hira , shi dai kawai ya na kallon ta ya na jin abun da ta ke fada mishi , yau bakin nata ya ki rufuwa kamar parrot a haka har su ka karaso chop din , su ka sayi ice cream din , ta sayowa Safna ita ma , amma dan jaraba shi Kim biyu ya ce ya na so daya ta chocolate daya kuma vanilla babu yadda Esra ta iya haka ta saya mishi biyun , ta biya kudin kafin su juya su nufi hanyar gida tafiyar su ke yi su na shan ice cream din su har su ka iso greenwich street ba tare da ta lura ba , shi kuma a ganin shi ta nan zai fi sauri su koma gida ne shi ya sa ya biyo ta nan hanyar babu kowa , ko lamps ma daya daya ne ke kunne , kamar an yi busa a wajen su na tsaka da tafiyar su kawai su ka ga wasu samari uku sun sha gaban su , da ga ganin su ka San ba mutanan kirki ba ne , har wani warin taba su ke yi dum Esra ta ji zuciyarta ta buga har ta saki bowl din ice cream din ta ba shiri , da sauri ta yi bayan Kim ta buya cikin nitsuwa Kim ya ce musu " Guys , what are you doing here ? " wanda ke tsakiya ne ya ce mishi " ni ke tambaya a nan , where is my money ? ka ce min two weeks , yau har one month shi ne ka sauya wajen zama dan kar na kama ka , yau sai ka ban kudi na " cikin sigar rarrashi Kim ya ce mishi " I'm sorry Pablo , i don't have money now , ka ba ni one week wlh zan kai maka kudin ka har gida " ko sannu Pablo bai ce mishi ba ya juya ya kalli saurayin da ke daman shi , da kai ya yi mishi allamun ya caje shi ba musu ya karaso ya kai hannu ya fara caje Kim da sauri Esra ta dan ja da baya ta na sakin kara da sauri Kim ya juya ce mata " please calm down " kafin ya juya ya kalli Pablo ya ce mishi " please , ka ba ni one week zan ba ka kudin ka " ya na gama fadar haka kawai ya ji saurayin nan ya kai hannu saman dick din shi a dubu dari Kim ya sa hannu ya ture shi ya na dan zaro idanu kallon Pablo saurayin nan ya yi ya na fadin " Boss , babu ko sisin kwabo a tare da shi " cike da bacin Pablo ya kai dunkule hannu ya kai wa Kim bugu a face har sai da Kim ya dan rinsina kamar zai fadi amma ya dago ya na dan ja da baya ya ce " please Pablo , i promise zan biya ka kudin ka , ka ban one week , in na wuce ka kashe ni in ka na so " ko sannu Pablo bai ce mishi ba ya kai hannu ya damko kwalar rigar shi , ya daga hannu a dunkule zai sake kai mishi wani bugun da sauri Esra ta shiga tsakiyar su ta datse idanun ta da karfi ta na jiran saukar naushin a face din ta Pablo na ganin ta ya tsaya Cak , wani makirin murmushi ya saki ya na kallon ta Kim na ganin irin kallon da ya ke yi wa Esra ya san ba al'heri ba ne , da sauri ya sa hannu ya buge hannun da ya rike kwalar shi da shi , ya riko hannun Esra ya meda ta bayan shi ya na kallon Pablo cikin ido Wani dan karamin murmushi Pablo ya saki kafin ya ce " ai ga kudina nan a bayan ka , ka ban ita kawai mu tafi " Dum Esra ta ji gaban ta ya fadi , nan take idanunta su ka ciko da ruwa , kawai sai kara kankame Kim ta yi ta baya ta na girgiza kanta a hankali a sanyaye Kim ya ce mishi " No Pablo , please and please na ce zan biya ka kudin ka " murya kassa kassa Esra ta ce mishi " nawa ne kudin zan biya shi " murya kassa kassa shi ma ya ce " ki na ji ? zan kirga zuwa uku , ki juya ki bar wajen nan da gudu " da sauri ta ce mishi " No , ba zan iya tafiya na barka ba , ka fada m....... " ba ta kai karshen maganar ta ba Pablo ya katse ta da cewa " kai , wai maganar me ku ke yi kassa kassa haka ? " Kim bai amsa mishi tambayar shi ba kawai ya shiga girkawa da ga uku , a rube su Pablo su ka tsaya su na kallon shi sai da ya ida girkon shi kawai ya ji Esra ba ta motsa ba , cikin rada ya ce mata " ki bar wajen nan na ce miki ! " ya na gama rufe bakinshi ta sake shi ta juya ta kwassa da gudu Pablo na ganin ta fara gudu ya dan zaro idanu kafin ya kwassa da gudu shi ma ya yi bayan ta da sauri Kim ya bi bayan shi ya na fadin " No Pablo , please ka kyale ta ! " ya na haka kawai ya ji an riko hannayanshi ta baya an tsayar da shi dai'dai lokacin da Pablo ya cin ma Esra ya damko ta ta kugu wata razananiyar kara ta saki ta na neman kwatar kan ta har sai da ta saki bag din hannun ta [28/02 à 10:22] đŸĒˇđŸŠˇ: Assalamu alaykum Barkanmu da warhaka yakk Allah ya sadamu da alkhairin dake cikin wannan ranar Ta Juma'a yamana kariya daga dukkan sharri 😊😊😊 In sha Allah gobe za mu shiga watan Azumi mai Albarka 😊 zan so na nemi gafarar baki daya , wanda na batawa ba tare da sani na ba ku yahe min 😊 yau dai kun gani har pages 3 na yi posting 😂 na bankwana ne , da ga yau zan tsayar da posting sai bayan sallat , 😂 da ga nan kuma sai dai na ce mu hadu a paid group d'ina , đŸĨąđŸĨąđŸĨąđŸĨą da farko na saka kudin littafin a kan 500 ne , so saboda abun da ke faruwa kwana biyun nan na ce zan sauko da shi kan 400 ko kuma 300 har yanzu ban yanke shawara ba đŸĨąđŸĨąđŸĨą 😂😂😂😂 sai mun hadu a paid group din , ni da ga nan na yi tafiyata amma in sha Allah bayan sallat zan fara posting din Free book d'ina , ma su jiran RETURN OF EXILED PRINCE 😂😂😂 a ci gaba da jira to 😊😊😊 Na gode sosai da irin kulawar da ke samu da ga gare ku Sisters , Allah ya bar zumunci duk me son yin magana da ni ga number ta nan +22798999753 I LOVE YOU SO MUCHHHHH 🩷🩷🩷 sign : MEERAH đŸĒģ💜 .......... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12