Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko dan ki dinga saya min chocolate " ya kai karshen ya na kai chocolate din shi a baki wata yar karamar dariya Esra ta yi dan maganar shi gaskiya ta ba ta dariya wai zai zama abokin ta ko dan ta dinga saya mishi chocolate [24/02 à 09:13] 🪷🩷: 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 21 & 22 🕊❤} sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce mishi " kenan saboda chocolate din ne za ka zama friend din na ? " cikin ko in kula ya ce mata " yeah , rayuwar yanzu babu wanda ke zaune da kai da zuciya guda sai in ya na son wani abu wajen ka , kowa abun da zai gyara shi ya ke dubawa , ni ban san me ya sa ki ke son zama friend's di ta dan ba ni da komai kuma ba za ki samu komai ba sai problems , amma ni zan zama friend's din ki dan ki dinga saya min chocolate , kin ga advantage di na na ke dubawa " wani dan karamin murmushi geffen fuska Esra ta saki kafin ta ce mishi " abun da ke fada gaskiya , kowa advantage din kan shi ya ke dubawa , but ba zan ga laifin ka ba ko da a ce ka yi anfani da ni dan samun abun da ke so , asali ma zan ji dadin ta sanadiya ta ka samu abun da ka ke har ka yi farinciki , na san ko ba komai wata rana in ka tuno da abun nan za ka tuno da ni " shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali ya na a haka kawai ya ga wata ball ta buge shi a kafa slowly ya dago kai ya ga wani dan yaro ya nufo shi ya na dariya allamun tashi ce sai da ya karaso gaban Kim ya tsaya ya na fadin " please Sir ko za ka iya ban ball di ta ? " ba musu Kim ya kai hannu a hankali ya dauki ball din kafin ya ce mishi " zan iya yin wassa da kai ? " wani kyawatencen murmushi yaron nan ya saki kafin ya gyada mishi kai da sauri ya kai hannu ya karbi ball din ya na fadin " Oya , let's go and play " ba musu Kim ya tashi ya bi bayan yaron nan , kafin ya iso wajen yaron ya ida chocolate din hannun shi ya tilla leda , ya kai hannu ya meda gashin gaban goshin shi baya ita dai Esra ba ta ce komai ba ta na kallon shi har su ka fara wassa da yaron nan gwanin burgewa kamar uba da yaron shi , ga shi ko yaron sai dariya ya ke ya na biyewa Kim , lokaci guda su ka yi mugun burge ta wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta kai hannu cikin bag din ta , ta fiddo wayar ta , ta yi musu wata yar karamar video ta yi musu pics har uku kafin ta meda wayar cikin bag din ta ta dauki chocolate din da ta ajiye wa Kim ta meda su cikin ledar sannan ta ajiye ta mike a hankali ba tare da ta ce komai ba ta fara takawa ta nufi hanyar fita garden din ta na sakin murmushi Kim kuwa bai ma san abun da ke faruwa ba ya na wassan shi kamar wani karamin yaro sai da iyayen yaron su ka kira shi za su bar wajen sannan su ka daina , Ya na juyawa ya ga babu kowa saman bancin su sai ledar chocolate din da ta ajiye mishi a hankali ya tako ya dauki ledar kafin ya fice Garden din shi ma _________________________________________________________ ▪BROOKLYN ▪DISTRICT OF WILLIAMSBURG wani kyawatencen parlour ne mai mugun girma , ya kyawatu iya kyawatuwa komai na cikin shi White and black colors ne , duk walls din wajen na zallar glass ne , ka na iya hangen garin , da allamun samun building ne dan ka na ganin garin da wasu buildings ta ko ina a bangaran dama , parlourn kyawace ya ke da wata doguwar sofa White color irin wannan ma su disign din L , sai wasu kananan pillow a saman ta white colors suma a dayan geffen ta akwai wasu Sofas one seater biyu duk black color da ga tsakiya kuma an shinfida wani kyawatencen carpet round , Black color mai ratsin white , an daura wata kyakyawar table ta zallar glass white color da ga sama da ga saman ta kuma akwai wasu magazine wajen uku ko hudu haka ajiye , geffen su kuma remote ne biyu sai dan decoration na flowers ma su kyau wall din da ke fuskantar Sofar ya na rufe da wasu curtains farare kal , an rufe wall din da su da ga gaban wall din akwai wata yar table an daura wata makekiyar Tv plasma a sama wall din da ke fuskantar wadanan sofas one seaters guda biyu kuma , da ga gaban shi kadan akwai wata doguwar dining table ta zallar glass black color zagaye da wasu slipcover chair guda goma sha biyu su ma duk black colors ne , saman table din gaban ko wace chair akwai wani dan karamin tablecloth white color kamar handkerchief haka da ga saman shi akwai wani plate white color a juye , sai spoon da fork da eating knife a geffen dama geffen hagu kuma glass ne guda biyu kamar irin na shan wine haka , guda babban guda karami dan nesa da dining table din na hango wata kyawatenciyar kitchen cike da kayan girki na zamani , kuma duk abun da ke ciki white color ne a nan ba a saka black ba a bangaran hagu kuma na hango wani dan madaidaicin office , da wani closet cike de books kamar library da ga gaban Closet din akwai wani carpet white color mai dan girma , ya fi na parlour girma da ga saman shi an daura wasu Armchair guda biyu white color su na fuskantar junan su da ga tsakiya kuma wata yar table kamar ta ice haka bayan wannan closet din kuma na hango wani Stair na zallar glass , sai abun ya yi kamar saman closet din nan stair din ya ke takaitaciyar description din wajen kenan amma a zahari abun ya fi haka dan in na ce na ci gaba da description din sai mun kammala book din ma ba page din nan ba , abun dai Masha Allah kawai za a ce dan ka na ganin wajen nan ka san ba na kananan mutane ba ne , amma bari mu koma cikin labarin mu a zaune na hango Kevin saman chair a dining table da allamun diner ya ke yi ya na sanye da wasu pajama farare kal fuskar nan tashi a daure kamar hadari a geffen daman shi na hango wani kyakyawan bature fari kal da shi , ya na kama da Kevin , sai dai ya tsufa sosai dan zai kai 55 years , kun san yadda farar fata ta ke ba ka da resistance , da ka fara Tsufa ta ke jemewa , ga shi kuma duk gashin kan shi fari ne , amma ba shi da gemu ko kadan ya na sanye da wasu Suit navy blue ma su kyau tsadadu da ga gani da allamun wannan shi ne mahaifin su Ayden wato Brian a haka na hango wata kyakyawar budurwa ta na fuskantar Kevin , fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito , cikakiyar baturiya a shekaru ba za ta wuce 20 to 21 years ba ta na kama tak tak da Kevin kamar an tsaga kara sai dai color din idanun ta Hazel ne mai mugun kyau ta na da gashi sosai har tsakiyar bayan ta kuma mai laushi russet color da shi mai daukar hankali ta na sanye da wani mini skert pink ko ida rufe mata guyiwa bai yi ba , da wata yar karamar T-shirt dai'dai cibi Red color , amma gaskiya ba ta da shape kun san turawan ban ba wani shape ne da su ba , dama dama breast din ta ya dan tasso kuma ba ramamiya ba ce sosai kowane ya na cin abincin shi cikin konciyar hankali babu me cewa ufan a hankali Kevin ya kai hannu ya dauki glass din ruwan da ke geffen shi na hagu ya kai a baki ya surbi kadan kafin ya ajiye ya juyo ya kalli Brian ya ce " Daddy , gaskiya ya kamata ka yi wa Ayden magana , na daina wannan shiriritar da ya ke , ya dawo mu kula da companyn mu , mu na samun matsala kwana biyun nan , a na yi mana satar makudan kudade Daddy , ba zan iya kula da komai ba ni kadai " a hankali shi ma Brian ya kai hannu ya dauki glass din ruwa ya kai bakin shi ya surbi kadan kafin ya ajiye ya kalli Kevin ya ce mishi " kai ma ka sani , bayan restaurant din shi ba abun da ke cikin zuciyar shi , ko ya dawo ba zai maida hankali ya kula da companyn kamar yadda ya ke kula da restaurant din shi ba " " but Daddy , i've my own life , ba iya ci gaba da kula da companyn nan ba , ni ma ina dreams , ina da aikin da na ke so na yi , please ku yi mishi magana mana , duk abun da ya ke ku/ku ke goya mishi baya ya na yi , da tun farko kun bar shi ya kula da companyn da ba za mu fuskanci wannan matsalar ba , ni ban ma san abun da ya sa momy ta bar mishi companyn ta ba " ba tare da ta dago kai ba budurwar nan ta ce " Saboda ya fi ka kaifin basira , ya fi ka ilimi , ya fi ka tunani , ya fi ka sanin ya kamata , ya fi ka sanin harkar kasuwanci , ya fi ka zuciya , ya fi ka kula da tattali , na ci gaba ko ya isa haka ? " gaskiya maganar ta ba karamin batawa Kevin rai ta yi , cikin bacin rai ya dago hannu zai wanka mata mari cak Brian ya taro hannun ya na fadin " Kevin , are you mad ? marin ta za ka yi ? " da karfi Kevin ya kauce hannun shi kafin ya koma ya zauna ita ko ko a jikin ta dan ko dago kai ba ta yi da allamun ta san Brian ba zai bari ya mare ta ba cike da bacin rai Kevin ya ce " Daddy ka na fa jin abun da ta ke fada " dawo da kallon shi Brian ya yi kan budurwar nan ya ce " Emilie , why za ki fada mishi hakan ? " " ai gaskiya ce na fada " ta fada ta na kai abincin ta a baki " da ke da wancen sakaren zan yi maganin ku , sannan Daddy ka ce mishi ya shirya ya koma companyn in ya wuce one week gaskiya ni bari zan yi , i'm tired " Fadin Kevin slowly Emilie ta dago kai ta kalle shi a sanyaye ta ce mishi " don't worry , na ji ya ce monday zai koma " a tare Kevin da Brian da su ka zaro idanu har su na hada baki su na cewa " da gaske ki ke ? " a hankali ta gyada musu kai ta na fadin " i'm serious , na ji shi ya na waya da Adrian ya ce wai ya sa a gyara office din shi , monday zai kama aikin shi " wani kyawatencen murmushi Brian ya saki ya na fadin " to ka gani , ka na nan ka cika mu da surutu , ka ji monday zai karbi companyn shi , idan ka so za ka iya tafiyar ka " shiru Kevin ya yi bai ce mishi komai ba sai ma hannu da ya kai ya dauki ruwan shi ya kai a baki ya sha kadan kafin ya sauko ya ci gaba da cin abincin shi da allamun ya yi sumar zaune ko kuma wani makamancin hakan su na zaune a haka Ayden ya fara sauko stair a tare duk su ka kai kallon su wajen stair din sanye ya ke cikin wasu Tracksuit farare kal kamar madara , ya saka wasu sneakers farare kal su ma a kafafun shi ba na iya ganin face din shi saboda ya saka hular rigar ya kuma saka face mask baki , ya na takowa Hannayanshi cikin aljihun rigar shi , kai a sunkuye a haka ya gama sauko stair din ya nufi hanyar fita gidan da sauri Brian ya taro shi da cewa " Ayden ba za ka yi diner ba ? " a hankali ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " No , ni da Adrian za mu fita may be idan na dawo zan yi " bai gama rufe bakinshi ba Kevin ya ce " kullum ka fita , kullum ka fita , wai ina ka ke tafiya ? , a sani na ba kai ke dahuwa cikin Restaurant din ka ba , ba kuma company ka ke zuwa ba , kawai ku na cikin gari kai da wancen sakaran ku na yawo " maganar shi ta so ta sosawa Ayden rai gaskiya , duk duniya ba abun da ya tsana kamar a ci mutuncin wani na kusa da shi , wannan abun ya na bata mishi sosai wani dogon nunfashi ya ja kafin ya daga kafa a hankali ya taka ya fice gidan ya na fita Brian ya ce ma Kevin " kai dai ba ka iya fadin al'heri da bakin nan naka , ga shi yanzu ka bata mishi rai " " ai gaskiya ce na fada , tun baya kai ne da ba ka tsawatar mishi , ni ban ma san abun da ya ke cikin familyn mu ba " da sauri Emilie ta dago kai ta ce mishi " no , our family , shi ma ya na cikin familyn mu , ka daina mayar da shi bare , little brother din ka ne " cike da bacin rai Kevin ya ce " no , ni ba brother di na ne ba , kawai yaron da momy ne ta samu wajen cin amanar Daddy da ta yi " " Kevin ! " Brian ya fada da dan karfi ya na zaro idanu dan maganar Kevin ta bata mishi rai shi kuwa Kevin ko a jikin sa sai ma cewa ya yi " why za ka daga min murya ? ai ba karya na yi ba , ba banza ta mallaka mishi duk companyn ta ba saboda na uban shi ne , da a ce ba ta ci amanar ka ba da ba zai zo duniyar nan ba " a hankali Brian ya kai hannu ya dafe saitin zuciya shi ya na yamutse fuska ya na kallon Kevin cike da takaici Emilie na ganin haka ta zaro idanu ta na fadin " Daddy , are you okay ? " murya a disashe ya ce mata " ban ruwa " ba musu ta dauki ruwa ta mike ta kai mishi a baki ya sha sannan ta sauko shi ta koma ta zauna wani dan karamin tsaki Kevin ya yi kafin ya ce " I'm sorry maganar ce ta fito haka kawai , amma ba haka na ke tunani ba , i'm so sorry " MY BOOK IS ₦500 VIA 8081129487 Khadija Sabi'u Monie point bank 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 23 & 24 🕊❤} Da Brian da Emilie duk babu wanda ya ce mishi ufan , amma har cikin zuciyoyinsu sun ji zafin maganar shi duk abun nan da Kevin ya fada a kunnen Ayden , dan ya na tsaye bakin kofar da ga baya , bai tafi ba , abun da Kevin ya fada ya kara tabbatar mishi da abun zuciyar shi ke fada mishi na Kevin ya tsane shi , kawai ya na nuna mishi soyayya ne a fili , abun nan ba karamin zafi ya yi mishi ba dan har hawaye sai da ya zubar amma da ido guda a hankali ya kai hannu ya goge sannan ya bar wajen ya yi tafiya shi 🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼 ▪MISALIN KARFE 8 NA DARE ▪ESRA ❤🕊 Zaune ta ke cikin parlourn apartment din su ta na sanye da wasu kananan kaya blue ma su mugun kyau , sun yi mugun kama ta ko kamar a jikin ta a ka yi su ta na zaune ta na latsa laptop din ta cikin konciyar hankali , Safna kuma ta na cikin bedroom din ta ta na barci dan tun safe ta ke jin jikin ta ba dadi ta na a haka ta ji an bubuga musu kofa a sanyaye slowly Esra ta dago kai ta kalli saitin kofar , kafin ta rufe laptop din ta , ta ajiye saman table ta mike a hankali ta nufi kofar ,l ko tsoro babu ta bude kofar ta na budewa idanun ta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar fuska a marairaice , ya na sanye da kayan shi na safe idanun shi na sauka saman ta ya ji zuciyar shi ta yi wata muguwar bugawa ya rasa dalili , har wani dan zaro idanu ya yi kadan ya na kallon ta kamar bai san ta ba ita kuma ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " na zata ba za ka zo ba " shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na kallon ta babu ko kiftawa ta na ganin haka ta juya ta na fadin " tun da ba za ka ce komai ba shigo , na shirya maka duk abun da za ka bukata a kitchen " ba musu ya biyo bayan ta ya shigo gidan kafin ya tura kofar ya rufe ya na ida shigowa ya gan ta zaune saman sofa ta na rike da laptop din ta kawai sai ya yi tsaye ya tsare ta da ido babu ko kiftawa ita kuwa duk hankalin ta na kan aikin ta , ta ma manta da shi lokaci guda kawai ta ji duk ta tsargu kamar a na kallon ta wani cool murmushi ta saki kafin ta dago kai ta kalle shi , cikin zolaya ta ce " Ba ni za ka girka ba , ga kitchen din cen , akwai aikin da na ke yanzu idan na ida zan zo na taya ka " a hankali ya gyada mata kai kafin ya juya ya nufi Kitchen da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta juya ta ci gaba da aikin ta Kim kuwa ya na shiga kitchen din ya tsaya ya na kallon ingredients din da ta jera mishi saman counter a hankali ya juya ya nufi fridge ya bude ya fara bin abun da ke ciki da kallo cen ya hango fish , Potato , carrot , peas , cikin irin ledodin nan na deep freeze bai tsaya bata lokaci ba ya kai hannu ya dauki Fish , potato da carrot , ya dawo ya ajiye saman counter , sannan ya juya ya dauki green pepper , da chilli pepper sannan ya rufe fridge din a hankali ya nufi Oven ya bude ya fiddo tray din ciki ya ajiye saman counter , kafin ya juya ya fara bude closet na sama daya bayan daya da allamun ya na neman wani abu sai da ya bude closet na biyu sannan ya ga wasu kwalaben spices , hannu ya kai ya dauki thyme , rosemary , garlic powder , onion powder ya juyo ya ajiye geffen tray din oven sannan juya ya bude closet na gaba ya fiddo Aluminum, ya juya ya ciro ya shinfida saman tray din oven bayan ya shinfida ya juya ya nufi mixer din da ya hango dayan geffen , ya bude ya fiddo bowl din , ya zuba green pepper , chilli pepper Thyme, rosemary garlic da onion , ya zuba salt da black pepper , ya zuba oil ya koma ya yi mixing din su ya yi marinade sannan ya fiddo bowl din ya dawo ya wajen counter din ya ajiye ya kai hannu ya dauki fish da potato da carrot ya Zube su saman tray din oven

Chapter 8 of 12