na sa kafa ta fice office din
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
__________________
💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : Meerah 🎀💋
THE WRITER'S OF
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 9 & 10 💦 🔥}
a haka Esra ta ci gaba da aikin ta ita kadai cikin Office din , sai da ta share wajen good one hour a haka kafin ta ja wani dan karamin tsaki ta kai hannu cikin bag din ta ta fido wayar ta , ta saka karatun kur'ani ta aiki ta na saurare
_________________________________
▪BROOKLYN
wata kyawatencen balcony ne Fari kal , ya sha tiles farare kal ma su mugun kyau da haske
ga wata katuwar Swimming pool , ruwan cikin ta sky blue ne saboda tiles din da ke cikin pool din blue ne sai ruwan su ka dauki launin tiles din
pool din zagaye ta ke da wasu umbrella irin na bakin beach haka
kassan kowace akwai wasu chair guda biyu dogaye kamar na icce , da ga tsakiya su akwai wata yar karamar table ta glass saman kowace akwai Towel farare guda biyu ajiye
bayan wadanan chair din dan nesa kadan akwai wani kyawatencen parlour wall din da ke fuskantar pool din duk da glass ne an rufe shi da wasu curtain farare kal
parlourn ya kawatu da duk kayan more rayuwa , ilahirin abun da ke cikin parlourn Milk color amma bari mu koma cikin labarin mu dan tukunna ba mu isa parlourn ba
duk balconyn zagaye ya ke da glass ka na iya ganin duk yanayin garin
wani kyakyawan Saurayi ne zaune saman daya da ga chair din bakin pool
saurayin kyakyawa ne , a shekaru zai kai 32-34 years , fari ne kal cikaken bature gaba da baya , ya na da wani kontancen gashi color din shi baki kirin ne amma harshen su duk blue ne , ya konta min a baya gwanin burgewa sai wasu da su ka zubo mishi gaban goshi
ya na da kananan idanu farare kal kwayar cikin su kuma Ash ce , ya na da dogon hanci da dan karamin baki lips din shi kuma pink color ne ya na da wani piercing a kunnen shi da na dama
ya zaune saman chair din ya mike kafafun shi da ga shi sai short , a hannun shi na dama akwai wani Tattoo kamar flowers haka
ya na rike da wani magazine ya na karantawa cikin konciyar hankali
ya na a haka wani server ya shigo wajen ya na sanye da wasu Suit bakake hannun shi rike da tray dauke da glass biyu ya juice da wani dan plate na fruits
kai tsaye wajen wannan saurayin ya nufa ya kai hannu ya dauki glasses din nan ya ajiye saman table din geffen shi da plate din fruits din sannan ya mike ya koma dayan geffen saurayin ya ce " sir , ku na bukatar wani abu ? "
a hankali Saurayin nan ya girgiza mishi kai ya na murmushi ya ce "No , za ka iya tafiya na gode "
gyada mishi kai kawai server din nan ya yi kafin ya juya ya bar wajen
wani dan karamin tsaki saurayin nan ya yi kafin ya ce " wai kai malam ba za ka fito ba , ka yi wajen two minutes a ciki fa " ya fada da turanci
ya na gama fadar haka wani saurayin ya fito da ga cikin pool din ya juyawa saurayin da ke zaune baya , Babu riga a jikin shi , gashin kan shi kawai a ke iya gani ya zubo mishi har baya keya ya konta mishi luf amma light green ne , amma da ga gani ba karamin namiji ba ne dan damtsen shi a murde ya ke kamar dan dambe ,
a hankali na jiyo Muryar shi ya na fadin " lafiya ka fiddo ni ? " cike da nitsuwa ga murya ta shi a sanyaye kamar an busa sarewa
" Ayden wai yaushe za ka daina harkar restaurant ka kama companyn ka , ka fi kowa sanin satar da Kevin ke yi maka amma ka yi shiru "
ko sannu Ayden bai ce mishi ba ya koma cikin ruwan
wani dogon nunfashi saurayin nan ya ja ya na cewa " oh ni Adrian , ba da kai na ke magana ba ? "
Ayden ya na jin shi amma ya share ya ci gaba da yawon shi cikin ruwan
wani dan karamin tsaki Adrian ya ja ya na fadin " shikenan amma kar ka ce ban fada maka ba " ya na gama fadar haka ya kai hannu ya dauki glass din juice ya kai baki ya surba Kafin ya mayar ya ajiye
sai da ya yi wajen two minutes a haka kafin ya sake fitowa da ga cikin ruwan , yanzu ma ya juyawa Adrian baya
a hankali ya kai hannu ya yi baya da gashin kan shi da ya jike
cikin nitsuwa ya ce " Guy , don't worry , na kusa gamawa da Maganar Kevin , kawai ina son na gama da Business din restaurant din nan ne , da kai na zan koma Companyn , yanzu ka yi kawai abun da na saka ka "
sai da Adrian ya dan jinkirta kafin ya ce " na shirya ground plan din companyn , sign din ka kawai na ke jira "
" okay " ya fada a takaice kafin ya yi kassa ya koma cikin ruwan
wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya ci gaba da karatun shi
▪ESRA 💕
Zaune ta ke cikin parlourn su , ta na sanye da wani dan karamin wando dai'dai cinya , da wata t-shirt white color mai kyau
ta mike kafafunta saman sofar , ta daura laptop a sama ta na latsawa cikin konciyar hankali
ta na a haka Safna ta turo kofar part din ta shigo ta na sallama , ta na sanye da uniform din restaurant din su
amsa mata sallamar ta Esra ta yi ta na fadin " sai yanzu ki ka dawo ? "
da murmushi a face din ta Safna ta karaso cikin parlourn ta ajiye bag din ta saman table sannan ta zauna ta na fadin " kin dai gani "
" okay , je ki yi wanka , na shirya mana diner " Esra ta fada ba tare da ta kalle ta ba
wata yar karamar dariya Safna ta yi har da tapi ta na fadin " iyeeeee , wai Esra da gaske kin shirya mana diner ? lafiya ? ko dai tsintuwa ki ka yi ? "
wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " ba abun da na yi kawai dai na dawo ne ina jin yunwa shi ya sa na shirya mana "
" okay bari na je na yi wanka " ta fada ta na kokarin tashi
da sauri Esra ta tsayar da ita ta na fadin " please , zauna ina son na yi miki wata tambaya "
ba musu Safna ta koma ta zauna ta na fadin " wace tambaya kuma ? "
a hankali Esra ta rufe laptop din ta sannan ta sauko da kafafun ta kassa ta zauna bakin sofar ta na fadin " dama a kan restaurant din ku ne , na ce kin taba ganin mamallakin wajen ? "
a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " no gaskiya ban taba ganin shi ba , but ba restaurant guda ba ne , restaurant din shi su na da yawa gaskiya , wanda na ke aiki ciki karami ne ma sosai , na so ki ga restaurant din shi na Washington , sai ki rantse da glass a ka yi shi , musaman sai manyan ministers da yan kasuwa ke shiga restaurant din , shi ma sai sun yi booking one week before , ba karamin mutum ne ba wlh "
cikin nitsuwa Esra ta ce mata " but , ko so guda bai taba zuwa restaurant din ya duba ba ? "
girgiza mata kai Safna ta yi ta na fadin " no gaskiya , ko so guda ban taba ganin shi ba , ni ko sunan shi ma ban sani ba wlh , kawai dai in mu na meeting ne manager din mu na maganar shi amma bai taba fadin sunan shi ba "
" okay , na gode " Esra ta fada kafin ta bude laptop din ta ta ci gaba da aikin ta
ita dai Safna ta tsaya ta kurawa waje guda ido kamar mai tunanin wani abu
cen sai ta ce wa Esra " Esra , kin san wani abu ? akwai wani mutum da ke yawan zuwa restaurant din duk Monday , kullum shi ne first client din mu , kuma kullum in ya zo coffee ne kadai ya ke sha ya yi tafiyar shi "
a Hankali Esra ta dago kai ta kalle ta ta ce " ki na iya gane shi idan kin gan shi ? may be shi ne mai restaurant din ba ki taba sani ba "
" Eh zan iya gane shi , sosai ma , kin ga ko wlh kullum in ya zo da laptop a hannun shi ya na typing , sai wajen karfe 9 sannan ya ke barin restaurant din , watarana su biyu ma su ke zuwa , amma gudan ban taba ganin face din shi ba gaskiya "
" okay , yanzu je ki yi wanka mun yi maganar da ga baya "
da to kawai Safna ta amsa mata kafin ta tashi ta dauki bag din ta , ta nufi corridor ta shiga bedroom din ta , ta bar Esra nan zaune ita kadai ta na aikin ta
____________________________________
▪LAGOS ( NIGERIA )
wani kyakyawan matashi ne zaune saman chair , tsakiyar wani kyawatencen garden
matashin kyakyawa ne ba laifi , a shekaru ba zai wuce 36 years ba , skin din shi chocolate ce , da ga gan shi ka ga cikaken bahaushe gaba da baya
ya na sanye da wasu suit khaki , ma su mugun kyau sun zauna mishi a jiki
ya na rike da wayar shi ya na latsawa ya na sakin murmushi
ya na a haka wani kyakyawan dattijo ya iso wajen ya na sallama , ya na sanye da wata jallabiya white color mai dogayen hannu , fuskar shi babu yabo babu fallasa , a shekaru zai kai 60 haka , amma da ga ganin yanayin jikin shi ya na samun hutu dan har ya fi saurayin da ke zaune haske , ga shi kuma bai tare kyasumba ba sai ka yi tunanin kamar dan shekara 40 ne
a hankali matashin nan ya dago kai ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya mike tsaye ya na mika mishi hannu ya na fadin " Barka da fitowa uncle "
wani dan karamin murmushi mutumin nan ya yi , ya na mika mishi hannu su ka yi musbaha
sannan ya zauna saman dayan chair da ke geffen ta matashin nan
sai da ya zauna sannan ya ce " Irfan , sai yau ka tuno da ni ko ? "
komawa Irfan ya yi ya zauna ya na dan sunkuyar da kai ya ce " a'a wlh uncle , kun san yanayin aiki ne , ko wannan zuwan na tsaye ne komawa zan yi dan gobe zan koma London "
" Masha Allah , Allah ya taimaka , Allah ya kara daukaka "
" Ameen ya rabbi , na gode uncle " Irfan ya fada cike da girmamawa
wani kyawatencen murmushi mutumin nan ya saki kafin ya ce " ya ka baro mahaifin naka , da momyn ka da sauran yan uwan ka ? da fatan ka baro su lafiya ? "
" Alhamdoulilah uncle , su na nan lafya , sun ma ce na gaishe ku idan na zo "
gyada kan shi mutumin nan ya yi a hankali ya na fadin " Masha Allah , ba zan tsayar da kai ba , dama ni na yi wa mahaifinka magana ya turo ka , mu yi magana , ina fatan za ka saurare ni da kunnen basira "
cikin girmamawa Irfan ya ce " uncle ba sai kun yi min maganar ba , na riga da na san komai dan Daddy ya fada min , kuma ina goyen bayan ku dari bisa dari , in sha Allah ba za mu ba ku kunya ba , zai kara dankon zumuntar da ke tsakanin familyn mu , ni dai ta bangare na ba ni da matsala , kawai fata na Allah ya tabbatar mana da al'heri "
Hamdala mutumin nan ya yi ya na fadin " Alhamdoulilah , Alhamdoulilah , ka san ni da mahaifin ka tare mu ka taso , tun muna yara , a tare mu ka yi wassan kassa , a tare mu ka yi karatu , aiki ne kawai ya raba mu , tun muna matasa mu ka yanke wannan shawarar , ina fatan hakan zai zama karin dorewar abotar mu , mu zama family guda ta hanyar ku "
wata yar karamar dariya Irfan ya yi kafin ya ce " uncle , ai mu dama family guda ne , kar ka manta a nan na taso , ina tune lokacin da na ke wassa saman cinyoyin ku , in sha Allah za mu cika muku burin ku , albarkar ku kawai mu ke nema da addu'ar ku "
" Albarka kullum cikin saka muku ita mu ke yarona "
" na gode Uncle , i'm sorry amma tafiya zan yi , akwai inda a ke jira na "
wani kyawatencen murmushi Mutumin nan ya saki kafin ya ce " no , kar ka damu , amma ka yi hakuri tukunna ba ta dawo ba , amma zan turawa Daddyn number din ta ya ba ka ko da gaisuwa ce kafin lokacin ya zo "
" kar ku damu uncle , na gode sosai " ya kai karshen ya na mikewa tsaye
a hankali shi ma mutumin nan ya mike tsaye su ka yi musbaha , da ga nan su ka yi sallama Irfan ya bar wajen , shi kuma ya koma ya zauna ya fiddo wayar shi ya fara latsawa
ya yi wajen ten minutes a haka kafin wata kyakyawar mace ta shigo garden din rike da wani tray dauke da wasu glass biyu na juice
matar kyakyawar gaske ce , a shekaru za ta kai 45 to 50 years , kallo daya za ka yi mata ka san mahaifiyar Esra ce dan su na kama sosai , kawai Esra za ta gwada mata haske , amma da ga ganin yanayin jikinta ka san ta na samun huta , da kuma kula
ta na sanye da wata Abaya red color mai kyau , da wani Hijab fari da kadan ya wuce kirji , fuskar ta dauke da wani cool murmushi , ta na tafiya cike da nitsuwa
a haka har ta karaso wajen dattijon nan ta zauna saman chair din da Irfan ya tashi ta ajiye tray din a kassa dan babu table a wajen
cikin sanyin murya ta ce wa dattijon nan " Engineer , har Irfan ya tafi ne ? ni da na kawo muku juice "
[16/02 à 09:38] 🪷🩷: __________________
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH 💋
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 11 & 12 🕊❤}
wata yar karamar dariya Engineer ya yi kafin ya ce " No , ya ce wai ya na da aiki , may be next week ya dawo dan gobe zai koma London "
gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta kai hannu ta dauki glass din juice ta mika mishi
hannu ya kai ya karba ya na yi mata godiya
ba ta ce mishi komai ta kai hannu ta dauki gudan ta fara sha cikin nitsuwa
cen sai ta ce mishi " ka na ganin wannan shawarar da ka yanke me bulle wa ce ? "
cikin rudu ya ce mata " kamar ya me bullewa ? ban gane ba "
" ka fi kowa sanin halin yarinyar ka , idan ka ce za ka matsa mata da maganar ba za ta taba amincewa ba , ni ma ina son ta yi aure but ya kamata mu ba ta damar zabar wanda ta ke so ba mu cilas ta mata ba , a cikin 21st century mu ke , an daina wannan hadin auren da a ke "
" ni dama na san ba za ki taba amincewa da wannan maganar ba Aysha , amma in ba haka ba ba za ta taba yarda ta yi aure ba , ki na gani US ta gudu dan kawai kar mu yi mata maganar , amma ina jiran ta dawo auren Yasmina , ba zan bari ta koma ba "
wani dogon nunfashi Aysha ta ja kafin ta ce " ka yi dai tunani mai kyau , ba dan ka na son abotar ku da Wadi ta daukaka za ka hukuntar da yarinyar mu , kuma ba na tunanin za ta amince da auren nan , ni dai zan so ka zauna ka kara tunani , rayuwar ta ce baki daya ka ke shirin yin wassa da ita "
shiru Engineer ya yi bai ce mata komai ba ya na ci gaba da latsa wayar shi , shi dai a wannan maganar ba gudu ba ja da baya duk abun da a ka yi sai ya yi auren Esra da Irfan dan shi ne babban burin shi a rayu
________________________________________
▪US ( NEW YORK CITY )
▪GREENWICH STREET
a hankali ta ke tafiya cike da san'da kamar barauniya , ta na sanye da wata gown white color mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta Purple a kai , ta na rataye da bag din ta kamar kullum
tafiya ta ke ta na waiwaye kar a je akwai gangs din da su ka fito a wannan lokacin
cikin sa'a ko ba ta hadu da kowa ba har ta karaso wajen wannan kangon da Kim ke rama
ta na shigowa ko ta hango shi cen zaune saman wasu box , ya na sanye da wani short white color da shirt Red color babu takalmi a kafafun shi , ya na rike da taba ya na sha cikin konciyar hankali
a hankali ta karaso wajen ta na yi mishi sallama duk da ta san ba zai iya amsa mata ba
ko sannu bai ce mata ba ya ci gaba da shan tabar shi
a sanyaye ta ce mishi " Hi , Good morning "
" Hi ! " ya fada a takaice ya na kai tabar a baki ya kara sha
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " Kim , tun da safe ka na shan taba ? ka yi breakfast ko ? "
a hankali ta saki tabar ya sa kafa ya murje ta , ko zafin wutar bai ji ba , Esra kuwa har wani dan lumshe idanu ta yi ji ta yi kamar ita ta taka wutar
shi kuwa ko ajikin shi kamar ba wuta ba ce ya taka
a sanyaye ya ce mata " wai me ki ke yi a nan ? a sani na chocolate ne ya hada
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 12