babu copy din ta ....... "
cikin nitsuwa Ayden ya katse shi da cewa " no wonder , ka ban tsoro ni , na ma zata wani abu a ka yi "
" Ayden , in ban ga relieve din nan ba ba za mu san kudin da Kevin ya fitar ba last month , duk investigation din mu zai zama kamar banza "
wani dogon nunfashi Ayden ya ja ya na gyara zaman shi saman chair din ya ce " don't worry , za mu San abun yi , kai dai kawai ka bi tsarin plan di na "
wata yar karamar ajiyar zuciya Adrian ya sauke kafin ya zagayo ya zauna saman chair din geffen ta Ayden kafin ya ce " Bro , tun wuri ya kamata ka san abun yi dangane da Kevin , ko wane month ribar companyn ka kassa ta ke , in a ka ci gaba a haka sai mun yi bankruptcy , hakan na nufin sai ka rufe companyn , na san kuma ba haka ka ke so ba "
shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba amma ya jin abun da ya ke cewa , har cikin ran shi ya na jin zafin satar nan da Kevin ke yi , ya na neman ya kashe mishi company shi kuma ba zai iya jure hakan ba saboda companyn amana ce momyn su ta bar mishi , duk abun da ya samu companyn shi ne mai laifi dan bai tsaya ya kula da ita ba yadda ya dace
ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Adrian ya na fadin " ya kamata ka koma ka ci gaba da kula da companyn ka , please my Bro "
a sanyaye Ayden ya ce mishi " Monday , ka sa a gyara Office di na monday zan koma "
wani kyawatencen murmushi Adrian ya saki ya wata yar karamar dariya ya na fadin " Yes , Yes , Yes , da gaske za ka koma ? i'm really happy , finally tsawan shekaru za ka kama business din ka "
" amma a tare za mu koma "
cike da fara'a Adrian ya ce mishi " no wonder , ni dama a shirye na ke , kai kadai na ke jira , za ka gani yadda business din zai kara habbaka , na san saboda Kevin ba da zuciya daya ya ke kula da shi ba shi ya sa mu ke yin kassa "
shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba da allamun ya tafi duniyar tunanin shi
shi kuwa Adrian sai zuba mishi surutu ya ke bai san da cewa abokin nashi ya yi nisa duniyar tunanin shi ba
sai da ya share wajen good ten minutes a haka kafin ya lura abokin nashi ba ya ma sauraron shi
hannu ya kai ya buge shi a cinya ya na fadin " kai tunanin me ka ke tun dazu ina yi maka magana ka kyale ni ? "
wata boyayyar ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya bude baki a hankali ya ce " Adrian , i think i'm falling in love "
dan zaro idanu Adrian ya yi ya na kallon shi , a rude ya bude baki ya ce " love , Ayden ka na jin abun da ka ke cewa ? Love fa ? da wa ? ban taba ganin ka ba da mace ? ta ya z...... " kut maganar ta yanke bai kai karshen ta ba
sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Ayden , ko dai yarinyar da ka taro jiya ka fara so ? "
" Esra , sunan ta Esra " Ayden ya fada ba tare da ya bude idanun shi ba
A hankali Adrian ya maimaita sunan kassa kassa , Tabbas ya jiyo lokacin da Kevin ya kira sunan Esra , kenan Ayden ya kamu da son ta lokaci guda haka ? in na gane saboda ita ne zai koma companyn Monday ?
" Ayden , da gaske ka kamu da son ta " Adrian ya fada murya cen kassan makoshi
a hankali Ayden ya gyada mishi kai allamun Eh sannan ya ce " lokacin da idanuna su ka sauka cikin nata , ji na yi kamar na bar wannan duniyar , wani sabon feeling na ji a zuciya ta wanda ban taba jin irin shi ba , for the first time in my life na samu nitsuwa cikin idanun wata macen bayan na momy , Adrian please help me na cire wannan abun da ga cikin zuciya ta dan bai kamace ni ba "
a rude Adrian ya ce mishi " why ? kamar ya ka fitar da shi ? "
" Adrian , ba na jin zan iya jure rashin wani wanda na ke so cikin rayuwa ta , gwara na cire wannan abun tun ban yi nisa ba "
da sauri Adrian ya girgiza mishi kai ya na fadin " No , No Ayden , you too have the right to love, you have the right to happiness if you really love this girl, live your life with her, forget the past, live the present with a thousand and one colors so that your future will be more than perfect, with her , ni fa abokin ka ne tun mu na 4 years , tun bayan rasuwar momy tsawan shekaru yanzu ban taba ganin ka ka yi murmushi ba "
cikin nitsuwa Ayden ya sauko da kafafun shi kassa ba tare da ya bude idanun shi ba ya mike tsaye ya fara takawa zai bar wajen ido a rufe dan ba ya tunanin zai ci gaba da wannan hirar
da kallo Adrian ya raka shi har sai da ya bar wajen sannan ya saki wani cool murmushi ya ce " in har da gaske ka na son yarinyar nan na yi maka alkawari sai na sa ta zama mallakin ka , Esra ...... Sunan ya hadu haka ita ma ta hadu gaskiya , ban ga laifin ka ba dan ka kamu da son ta "
ya na gama fadar haka ya mike a hankali ya bi bayan Ayden ya bar wajen , wannan abun ya ban mamaki gaskiya , ya a ka yi Ayden ya kamu da son Esra haka , Wannan shi ne love at the first sight , yanzu ya za ta kasance in Ayden ya koma companyn
🤣🤣 Ga Kuma Kim shi ma , da alamun Esra ta kamu da son shi ba ta sani ba , ni dai zan ga ya game din zai kasance su uku 🤣🤣🤣
[21/02 à 09:45] 🪷🩷: 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
__________________
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : MEERAH 💋
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
{P A G E 19 & 20 🕊❤}
________________________________________
▪ESRA ❤💫
zaune su ke cikin restaurant ita da Cherry da Arthur , Arthur na rike da wata paper ya na karantawa Cherry da Esra sun tsare shi da ido
sai da ya share two minutes a haka kafin ya ajiye takardar saman table din su , ya na kallon Esra ya ce " ina ki ka samu paper din nan ? "
cikin nitsuwa Esra ta ce mishi " Yesterday na zo restaurant din nan yin breakfast , to wajen fiddo kudin biyan na san na yarda wata paper ta file din da za mu yi meeting a kai har sir Kevin ya yi min magana a kai , to bayan na koma gida Safna ta kawo min paper din ta na fadin restaurant din su na bar paper din "
" but wannan ba ita ce paper din ba , ina ki ka samu wannan ? " Cherry ta fada ta na kai hannu ta dauki paper din
Esra ba ta ce mata komai ba ta dauki wayarta da ke ajiye a gefe , ta fara latsawa na dan lokaci kafin ta juya ta na nuna musu pic din Adrian da ta dauka jiya ta na ce musu " lokacin da na shigo restaurant din wannan mutun ya shigo , ku na gani da paper a gaban shi ya na aiki , to wannan paper din tashi ce , kuma jiya bayan na baro taron meeting din na hadu da shi cikin hall din Building din tare da Ayden Brian , mamallakin companyn "
dan zaro idanu Arthur ya yi ya na fadin " no , da gaske ? Ayden ya zo companyn mu jiya ? "
" Eh , ya zo , har ma mu ka yi karo da juna "
da sauri Cherry ta katse ta da cewa " wait , kenan shi ne saurayin da a ka ce ya taro ki ? "
" yeah , shi ne " Esra ta fada a sanyaye
cikin nitsuwa Arthur ya ce " kin ga face din shi ? ki na iya gane shi kenan ? "
a hankali Esra ta girgiza mishi kai ta na fadin " no , ban ga face din shi ba saboda ya na sanye da face mask , amma ina iya gane saurayin da ke tare da shi na ji sir Kevin ya kira shi da Adrian "
" ta baci , da a ce kin ga face din shi da za mu iya gano inda ya ke har mu yi mishi maganar abun da ke faruwa " fadin Arthur
ya na gama rufe bakin shi Esra ta ce " no , yanzu ma ba ta baci ba , wannan paper din za ta yi mana anfani dan kara karfafa hujjojin mu wajen shi , abu guda mu ke bukata kawai file din office din sir Kevin "
Cherry : " to yanzu ya za mu yi mu samo file din , kin dai ji uban security din da ke office din Sir Kevin "
Arthur : " idea din ku za mu bi , ta shiga ta System of climatisation "
Esra : " kai fa ka ce it's not a good idea , za mu iya bacewa ko zafi ya kashe mu "
wani dogon nunfashi ya ja kafin ya ce " That's why mu na bukatar ground plan din building din , cikin sa'a ko na samo daya da ga cikin architects din da su ka gina building din , but ya ce zai dauki two or three days kafin ya samo mana ground plan din "
a tare Esra da Cherry su ka washe baki su na dan zaro idanu kafin su dago hannu su yi tapi , sannan Esra ta ce " Fine , yanzu plan din mu zai fara , sai mun kawo karshen wannan azzalumin mai fuskar shanu " ta fada cikin bacin rai da allamun har yanzu ta na jin haushin fadan da ya yi mata gaban mutane
a tare Cherry da Arthur su ka yi dariya dan sun gane abun da ke cikin zuciyar ta
har Cherry ta bude baki za ta yi magana Wayar Arthur ta fara ringing , a hankali ya kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo wayar ya na kallon screen din
a hankali ya mike tsaye ya na fadin " girls ina ga zan tafi , akwai in da a ke jira na "
" okay , see you next time " Esra da Cherry su ka fada a tare
bai ce musu komai ba ya fara takawa ya bar wajen ya fice restaurant din ya bar su nan
" ya kamata ni ma na tafi " Cherry ta fada
a hankali Esra ta kai hannu ta tattare kayan ta , ta dauki bag din ta ta na fadin " mu tafi " ta qarashe maganar ta na mikewa tsaye
a hankali ita ma Cherry ta mike su ka baro restaurant din
su na fitowa su ka yi hannun riga , Esra ta yi dama , Cherry ta yi hagu
a hankali ta ke tafiyar ta cikin nitsuwa har ta karaso greenwich street
dan ta na mugun son ganin Kim , dan tun lokacin da ya baro apartments din su ta ke son ganin shi ta ga in ya na cikin koshin lafiya
kai tsaye Dan kangon ban da ya ke zama ta nufa ta na sallama a hankali duk da ta san ba za a amsa mata ba
cen ta hango shi zaune ya na sanye da wani crazy jeans blue , da t-shirt white color ya saka wasu Thong farare a kafafun shi , yatsun kafar shi sun fito dogaye da su farare kal gwanin burgewa
ya tirje wannan gashin kan nashi har ya rufe mishi idanu , ya na rike da sigari da hannu guda , gudan kuma ya na rike da gongwanin maltina ya na sha ya na busa sigarin shi
cikin nitsuwa Esra ta karaso gaban shi ta tsaya ta na fadin " Kim , please ba na ce ka daina shan wannan abun ba " ta kai karshen ta na kai hannu ta buge tabar da maltinar
a dubu dari ya dago kai , ba karamar razana Esra ta yi ba har wani baya ta yi ta na dafe saitin zuciyar ta bare ko idanun shi sun yi jazir
cikin bacin rai ya bude baki ya ce mata " why ? me ma ki ke yi a nan ? wai ba za ki iya ba ni lafiya ba ? me na yi miki ki ke son takurawa rayuwa ta ? "
ita dai ta tsaya ta na kallon yadda ya ke yi mata magana cike da bacin rai da allamun a buge ya ke
wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke ta matso a sanyaye ta ce mishi " Kim , please calm down "
da sauri ya katse ta da cewa " stop ! ba na bukatar kyautatawar ki , please let me , let me , babu abun da ke tsakani na da ke so let me " ya na gama fadar haka ya mike a zafafe zai bar wajen
da sauri ta riko hannunshi ta na fadin " please Kim wait , ka manta alkawari da ke tsakanin mu ? "
da karfi ya kwace hannun shi ya tura ta baya ya na fadin " forget that , i don't need you in my life , i'm happy without you " ya kai karshen ya na juyawa
da sauri Esra ta bi bayan shi ta na fadin " zan saya maka chocolate "
cak ya tsaya jin ta ce chocolate , abun da ya fi so fiye da komai a rayuwar shi
Esra na ganin ya tsaya ta saki wani cool murmushi ta karaso geffen shi ta tsaya ta na fadin " ko ba ka son chocolate din na tafi ? "
shiru ya yi bai ce mata komai ba har cikin zuciyar shi ya na son chocolate a yanzu
ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ga ta yi gaba ta na fadin " shikenan tun da ba ka so na tafi abu na "
cikin nitsuwa ya taro ta da cewa " ina so "
cak ta tsaya ta na sakin wani dan karamin murmushin geffen fuska , ta samu abun da ta ke so
slowly ta juyo ta mika mishi hannu ta na fadin " okay , let's go "
a hankali ya tako ya riko hannunta , kamar wani karamin yaro ta fara jan shi su ka bar wajen , ta na sakin wani dan karamin murmushi shi kuma ya sunkuyar da kai ya na kallon kafafun shi
kun san yadda yanayin garin US ya ke kowa harkar gaban shi ya ke hakan ya sa ba wanda ya damu su kowa na aikin shi
a haka har su ka iso wani market , sai da su ka shiga ta saki hannun shi sannan ta ce ya jira a nan
ba musu ya tsaya waje guda ya na kallon ta ta nufi fridge din wajen , ta bude ta kwashi chocolate har wajen goma sannan ta dawo ta nufi wajen biya ta , ta biya kudin
a ka saka mata chocolate din cikin leda , sannan ta dawo inda ta bar shi ko motsi bai ba
a hankali ta mika mishi hannu allamun su tafi
ba musu ya riko hannunta su ka bar wajen
sai da su ka dan yi nisa sannan ya ce mata " ban chocolate di ta "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " chocolate din ka ko tawa ? in ka na son chocolate din nan ka bi ni a hankali "
shiru ya yi bai ce mata komai ba , ya na biye da ita dan ba ya jin zai iya tafiya ba tare da ya karbi chocolate din nan ba
a haka har su ka iso wani kyawatencen garden cike da mutane musaman yara kowa na sha a nin shi su na wassa su na dariya gwanin burgewa
sai da su ka karaso wajen wani banci sannan ta saki hannun shi ta zauna ta na fadin " Oya , Sit down "
ba musu ya zauna geffen ta ba tare da ya ce komai ba
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta fiddo chocolate guda ta na fadin " zan yi maka tambaya , duk lokacin da ka ba ni amsar da na ke so zan ba chocolate guda , ka yarda ? "
slowly ya gyada mata kai allamun Eh ya yarda
" okay , First question , minene cikaken assalin ka ? "
kai tsaye ya ce mata " ba ni da "
" no , impossible a ce ba ka da assali , minene sunan momyn ka , da Daddyn ka ? "
a takaice ya ce mata " gidan marayu na girma "
nan take yanayin face din ta ya sauya , kenan maraye ne ? ta tambayi kanta
slowly ta mika mishi chocolate din
a hankali ya kai hannu ya karba , kafin ya bude ta ya fara ci cikin nitsuwa
hannu ta kai ta fiddo ta biyun ta na fadin " tun da gidan marayu ka taso hakan na nufin ba ka da yan uwa ko guda , right ? "
a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
dan lumshe idanu ta yi a hankali kafin ta ajiye mishi chocolate din geffen shi , ta kai hannu ta fiddo ta ukun ta na ce mishi " That's why ka ke shan wine saboda rage kadaicin da ka ke jin kanka , right ? "
yanzu ma gyada mata kai ya yi a hankali Allamun Eh ya na ci gaba da cin chocolate din shi
a hankali ta ajiye mishi chocolate din sannan ta fiddo ta hudu ta ce mishi " yanzu me ka ke yi da rayuwar ka ? a ina ka ke barci ? a ina ka cin abincin ? na san dai ba ka da aiki , ko kuwa ? "
ba tare da ya kalle ta ba ya ce " security a nightclub idan dare ya yi , ta haka na biya kudin apartment din da na ke zama a ciki "
cikin sanyin ta katse shi da cewa " ka na da apartment ka ke zuwa ka kwana cikin wannan kangon ? "
shiru ya yi bai ce mata komai ba
shiru ta yi ta na jiran amsar shi amma bai ce mata komai ba
sai da ya gama shan chocolate din ya kai hannu ya dauki guda cikin wadda ta ajiye mishi gefe ya bude ya fara ci
ta na ganin ta tuno ashe ba ta ajiye mishi chocolate din ba
da sauri ta ajiye chocolate din hannun ta , ta dauko wata ta na fadin " ba ka ban amsar tambaya ta ba "
sai da ya hadiye chocolate din bakin shi sannan ya ce mata " saboda na fi jin dadin zama ni kadai , babu wanda zai takura min , amma ga shi yanzu ki na son ki takura min "
wani cool murmushi ta saki kafin ta ajiye mishi chocolate din ta dauki wata ta na fadin " ban takura maka ba , kawai ina son na gyara maka rayuwa ne , ba dan ka na maraye ba za ka meda kanka mara gata , tabbas ban san ka ba kuma ba ka san ni ba amma zuciya ta ba za ta lamince ganin ka cikin wannan halin da ka ke jefa kanka , wine da taba babbar illa ce ga rayuwar ka "
" akwai ma su shan taba da wine dayawa a garin nan , why sai ni za ki taimakawa ? "
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " ai kai ma ka taba taimaka min lokacin da samarin nan su ka sace min bag di ta , ka ga ko dan hakan zan iya taimaka maka , yanzu fada min minene favorite habit din ka , wanda in ka na yin shi ka na jin duk damuwar ka tafi gushe har ka daina tunanin shan wine ? "
sai da ya dauki wajen two minutes bai ce mata komai ba kafin ya bude baki ya ce mata " cooking "
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ajiye mishi chocolate din ta kai hannu ta dauki guda ta ce mishi " Fine , da ga yau duk wajen karfe 8 na dare ka tardo apartment di na , za mu yi girki a tare dan ni ma na iya girki sosai "
a hankali ya dago kai ya kalle ta ya ce " specially with chocolate ? "
gyada mishi kai ta yi ta na fadin " yeah , with chocolate , za ka dinga zuwa ? "
slowly ya gyada mata kai allamun Eh
" Fine , ka ga in ka daina tunanin wine , za ka daina shan ta , in kuma ka daina za ka ga komai na rayuwar ka ya sauya "
" why ki ka damu da ni haka bayan ba mu hada komai da ke ba ? "
wani dan karamin murmushin geffen fuska ta yi mishi kafin ta ce " ni ma ban sani ba , kawai zuciya ta ce ta ke ce min na taimaka maka , kuma ni ina bin duk abun da zuciya ta ke fada min "
" a ka je duk abun da na fada miki yanzu karya ne , a ka je yadda ki ke tunani ba haka na ke ba , wannan rayuwar tawa duk basaja ce "
a sanyaye ta ce mishi " Idan har duk abun da ka fada min karya ne , ba zan ji komai ba saboda kai abokina ne , kuma tsakanin abokai sai dai wassa da dariya ba fada ba "
" abokai ? we are friends ? "
gyada mishi kai ta yi ta na fadin " yeah we are friends , ko ba ka son zama abokina ? "
" ina so ,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12