ba a ka fara , in dai wannan satar ta ci gaba ina ga Dukan mu sai dai mu nemi wani wajen aikin daban "
" Arthur , one milliard fa ka ce ? " Cherry ta fada
a hankali ya gyada mata kai ya na fadin " Abun da ya fi Hakan ma , kin san fa PDG din companyn nan sam bai damu da abun da ke faruwa cikin ta ba , karewar zancen , big bro din shi ke kula da gidan nan , da sauran companyn shi "
" Wait , ka na Nufin Sir Kevin ba shi ne mamallakin Companyn nan ba " Esra ta fada cike da rudu har da dan zaro idanu
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
__________________
💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITING BY : Princess Meerah 🎀💋
THE WRITER'S OF
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
PAGE 3 & 4 💦🔥
Har hada baki Arthur da Cherry su ka yi su na ce mata " wai ke dama a tunanin ki shi ne mai wajen ? "
a hankali ta gyada musu kai ta na fadin " Ni na zata shi ne mai wajen , saboda shi ke kula da komai tun lokacin da na fara aiki a wajen nan , kuma ban taba jin wani ya ce akwai wanda ke sama da sir Kevin "
dan tabe baki Cherry ta yi kafin ta ce " tabb ki na cikin Duhu ko "
Arthur ne ya katse ta da cewa " Wannan companyn da ki ke gani , ni da kai na ban taba ganin mai ita ba , Abu guda na sani , sir Kevin big brother din shi ne , Da farko Companyn ta mahaifinsu ce , amma ya kamu da ciwon zuciya a tunanin shi mutuwa zai shi ya sa ya mallakawa yaron shi na biyu duk wata company da ya mallaka , shi kuma ya ba wa Sir Kevin ragamar kula da su baki daya "
" me ya sa ba zai kula da kayan shi ba , tunda mahaifin nasu bai mutu ba , ya meda mishi companyn shi in ba zai kula da su ba "
" Ni ma haka na gani , yanzu ga shi bai ma san abun da ke faruwa cikin companyn shi ba " Cherry ta fada ta na komawa geffen Arthur ta zauna
ta na zama ya ce mata " ba mamaki sir Kevin da kan shi ke satar kudin , ko ni na ji an ce mahaifin mu ya ba wa little brother di na duk abun da ya mallaka , ba zan hakura da sauki ba "
hararrar wassa Esra ta yi mishi kafin ta ce " kai dai Arthur , a dinga fadin gaskia , Sir Kevin ta ya zai iya satar kudin dan uwan shi "
mikewa tsaye Arthur ya yi ya na fadin " Humm a na ki tunanin ko , amma ai mu na tare da ke , za ki gani " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya fice Office din
da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan ita ma Cherry ta mike ta na fadin " ya ne yau za mu je shan coffee ne ? "
" No gaskiya yau ba zan samu dama ba , may be tomorrow " Esra ta fada ta na dan marairaice fuska
wani cool murmushi Cherry ta saki kafin ta gyada mata kai a hankali ta sa kafa ita ma ta fice office din , su ka bar Esra ita daya cikin office din
su na fita ta fido laptop din ta da ga cikin bag din ta , ta fara aikin ta
a haka ta ci gaba da aikin ta ita daya cikin nitsuwa har wajen karfe 6 na yamma sannan ta baro building din
a hankali ta ke Tafiyar ta saman Titi , ta na taku cike da nitsuwa ta na kallon gaban ta
kamar da ga sama kawai ta ji an kwace mata bag din ta ta baya
dum ta ji gaban ta ya fadi , a razane ta juya ta na shirin ta saki kara
ta na ganin shi ta rufe bakin ta , ta na dan lumshe idanun ta , ta sake bude su
ko sannu bai ce mata ba ya bude bag din ta ya na leko ya ce " where is my chocolate ? "
" ka ga malam ka ban jaka ta , ni ba wani chocolate da gare ni " ta fada ta na mika mishi hannun ta allamun ya bata jakar ta
a hankali ya juya ya fara takawa ya na rike da bag din ta ta
da sauri ta bi bayan shi ta sha gaban shi ta marairaice fuska ta ce " please ka ban jaka ta , mu tafi zan saya ma "
tsaya wa ya yi ya na kallon ta na dan lokaci kafin ya ce " Mu tafi yanzu "
" shikenan ban jaka ta , sai mu tafi "
ba musu ya mika mata jakar ta ,
da sauri ta sa hannu ta karba ta na sauke ajiyar zuciya sannan ta ce " yanzu idan na saya maka chocolate din shikenan mun rabu ? "
a hankali ya gyada mata kai allamun eh
wani dogon nunfashi ta ja kafin ta ce " shikenan mu tafi " ta fada ta na fara takawa ta bi ta geffen shi ta wuce
a hankali ya juya shi ma ya bi bayan ta
a tare su ka yi tafiyar su ba wanda ke ce ma wani ufan har su ka iso cikin wani dan market ya na biye da bayan ta
su na shiga ta nufi kai tsaye wajen Fridge , ta bude ta dauko Chocolate har biyar sannan ta rufe ta dawo ta nufi reception ta biya kudin su ka fito market din
su na fitowa ta mika mishi chocolate Hudu ta rige gudar
kallon chocolate din ya yi kafin ya ce " Dayar fa ? "
hararrar shi ta yi ta na fadin " tawa ce , ka karba mana "
a hankali ya girgiza mata kai ya na fadin " no , ni wacen na ke so " ya fada ya na nuna dayar da ke cikin hannun ta guda
kallon shi ta yi baki sake cikin zuciyar ta ta ce " amma wlh ya raina min hankali "
ba ta gama fadar haka ba kawai ta ji ya kwace mata chocolate din
a razane ta dawo cikin hayacin ta na shirin yi mishi magana ta ga ya fara takawa ya yi gaba
dan karamin tsaki ta ja kafin ta fara takawa ita ma a hankali har ta kamo shi
har ya bude Chocolate din ya fara ci
cikin konciyar hankali ya ke cin chocolate din nan , har wani lumshe idanu ya ke yi , da allamun ya na son chocolate sosai
kawai sai ji ta yi ta tsargu da kallon shi , ba karamin burge ta ya yi ba har sai da ta saki wani cool murmushi ba ta sani ba
ta na a haka kawai ta jiyo Muryar shi ya na fadin " daina kallo na haka kar ki cinye ni "
da sauri ta kauda kan ta gefe ta na fadin " ni ba kai na ke kallo ba "
" uhm uhm to me ki ke kallo ? " ya tambaye ta dai'dai ya kai chocolate din shi a baki
" ni chocolate di na na ke kallo , wannan na ke so amma ka kwace min ita " ta fada ta na dan turo baki , ita wai ta ba kallo ba
a hankali ya tsaya da ya tafiyar shi , cak ta tsaya ita ma kamar ya riko ta
slowly ya juyo ya kale ta ya ce " shikenan karbi kayan ki " ya fada ya na mika mata ledar chocolate din dan ya cinye
kallon ledar ta yi kafin ta saki wani dan karamin murmushi mai sauti ta ce " amma ka raina min hankali ko ? bayan ka cinye , rike ba na so " ta kai karshen ta na fara takawa
da sauri ya ce mata " ji mana yan mata "
cak ta tsaya da tafiyar ta , ta juyo a hankali ta na matse gera
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " please ko za ki kara min wata , ba ta ishe ni ba " ya kai karshen ya na dan marairaice muryar shi
yanayin da ya yi mata maganar ba karamin tada mata gashin jikin ta ya yi ba , nan take ta ji zuciyar ta ta fara duka uku uku kawai ta tsare shi da ido , su ka yi ido hudu babu ko kiftawa
a hankali ya daga mata gera allamun minene
da sauri ta janye idanun ta , ta na girgiza mishi kai kafin ta mike mishi sauran chocolate din hannun ta
wani cool murmushi ya saki kafin ya tako a hankali ya tsaya gaban ta , ya kai hannu ya karbi chocolate din ya na fadin " Thanks " da ga haka ya juya ya fara takawa
tsaya wa ta yi ta na bin shi da kallo , sam bai yi kama da wadanan bata garin ba , da ga yanayin da ya ke maganar shi ma , cike ta ke da nitsuwa ga kaifin harshe duk yadda a ka yi wannan ba bata gari ba ne akwai dai wata a kassa
sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon shi kafin ta juya ita ma ta fara takawa ta nufi apartments din ta , ba ta dauki five minutes ta iso
building din ya na da girma sosai , a killa zai kai hawa 40 , a kowane hawa kuma part 5 a dakwai , duk da Parlour guda , Bedrooms biyu , toilet guda sai kitchen kuma dukkan su design guda gare su kuma piece of furnitures din iri daya ne har colors din
ta na shigowa building din kai tsaye lift ta nufa , ta shiga ta Haye Floor na 10
ko da ta fito lift din wani dogon corridor ne da ga dama zuwa hagu , mai dauke da doors har biyar
kofar lift din kuma ta na fuskantar kofar wani daki , an rubuta ROOM 52 da manyan harufa mai launin White
hannun damar ta ta yi ta nufi Door ta Biyu an Rubuta ROOM 51 a sama ita ma
ta na isa ta kai hannu cikin bag din ta ta ciro key , ta saka kofar ta bude sannan ta zame key din ta tura kofar ta shiga ta na sallama , sai da ta shiga sannan ta juya ta rufe kofar
sannan ta juya ta karaso cikin parlourn
ba laifi wajen a gyare ya ke masha Allah , duk furnitures din white and green color ne , da wata yar karamar Tv plasma din ta
parlourn gaskia ba shi da laifi ya na da dan girma komai na ciki White and green colors ne a geffen dama akwai wata yar karamar table allamun dining table ce mai chair biyu bayan ta kuma kitchen ce , har da fridge
geffen Hagu kuma wani corridor ne na hango , akwai wasu door din bedroom biyu a ciki su na fuskantar juna sai guda a tsakiyar su wadda ina kyautata zaton toilet ce
a hankali ta karaso cikin parlourn ta na sallama , sannan ta ajiye Bag din ta saman table din tsakiya ta nufi corridor
ta shiga bedroom din da ke saman damar ta , ta tura kofar ta shiga ta na sallama
bedroom din ya na da dan girma
saman damar ta wani Desk ne da chair kamar dan office , da wasu takardu a sama
gaban shi kadan akwai wani dressing mirror , dauke da lotion perfume da sauran su
a geffen hagu kuma Wani closet ne White color na kayan ta me door hudu
a cen cikin dakin geffen hagu akwai bed din ta game da bango , shi ma white color har bedsheet din shi white color ce , da bedside drawer din ta , ta daura wata bedside lamp da alarm clock
ta na shigowa ta warware veil din kan ta , ta yi baya da kan ta , ta girgiza shi a hankali
nan take jelar gashin kan ta , ta zubo mata , ta na da gashi gaskia , smooth da shi brown color kamar na turawa
ajiye veil din ta ta yi saman bed din ta , sannan ta nufi closet din kayan ta , ta bude na karshe
underwear ne cike a wajen , da pant da bra har da wasu towel white , pink , green colors
hannu ta kai ta dauki Towel Fari sannan ta juya ta fice dakin
kofar toilet ta nufa ta bude ta shiga sannan ta turo kofar ta rufe
After some minutes ta fito Daure da Towel a kirjin ta , kai tsaye bedroom din ta ta nufa ta shiga
ta na shiga ta nufi closet din ta , ta bude door ta uku , ta fido Wasu kayan barcin ta wando da T-shirt pink color
ta saka kayan ta , sannan ta dauki Hijabin ta pink color shi ma , ta dauki Daddumar ta
ta nufi dan carpet din da ke gaban gadon ta ta shinfida sannan ta saka hijabin ta , ta tada sallar ta
bayan ta Kamala ta tashi ta fida Hijabin ta , ta nufi Dressing mirror din ta , ta dauki lotion din ta ta fara shafawa , sannan ta feshe jikin ta da perfume
sannan ta nufi kofar fita dakin ta fito parlour
ta na fitowa ta nufi doguwar Sofa ta zauna sannan ta janyo table din tsakiya gaban ta , ta dauki Jakar ta , ta fara fido abun da ke ciki daya bayan daya
ta na a haka wata kyakyawar budurwa ta bude kofar gidan ta shigo ta na Sallama
Budurwar kyakyawa ce gaskia , a shekaru za ta kai 22 to 23 years , Skin din ta chocolate ce mai mugun kyau , da ga kan ta ka ga jinin Hausa fulani
ta na sanye da Wando palazzo black color da t-shirt Orange , da wani Veil shi ma orange ta yi Rowling din shi a kai , ta na rataye da wata yar karamar bag a bayan ta , ta karaso cikin parlourn ta na kokarin cire bag din
dago kai Esra ta yi ta na kallon ta , ta amsa mata sallamar ta sannan ta daura da cewa " Safna , yau kuma sai yanzu ki ka dawo "
ajiye bag din ta Safna ta yi saman sofa geffen Esra sannan ta zauna ta na fadin " Kin dai gani wlh duk na gaji jiki na har ciwo ya ke min "
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta juya kan ta , ta ci gaba da fido abun da ke cikin Bag din ta
mikewa tsaye Safna ta yi ta dauki bag din ta , ta na fadin " na shiga wanka " ta fada ta na fara takawa ta nufi corridor
da to kawai Esra ta amsa mata ba tare da ta dago kai ba
ta na tsaka da fido kayan bag din ta , ta fido wani dan karamin abu baki kamar USB stick haka
dago USB din ta yi ta kawo ta saitin fuskar ta , ta na bin ta da kallo
" wannan kuma da ga ina ? " ta fada dan ita a sanin ta ba ta da USB key
sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon USB din nan kafin ta janye ta da ga gaban face din ta , ta dauki bag din ta ta fara meda duk kayan da fido ban da wayar ta , da laptop
sai da ta Kamala meda wa sannan ta dauko laptop din ta , ta daura saman cinyoyin ta , ta kunna ta , sannan ta saka USB key din a ciki ta fara latsawa
ta dauki wajen good Five minutes a haka kafin ta mike tsaye a dubu dari ta na rike da laptop din ta , ta na zaro idanu ta ce " oh my God , ya Allah me na ke shirin gani haka "
ni dai ban san me ta ke kallo ba , wasu rubutu ga su nan irin statistics haka , ita kadai ta san abun da ta ke gani
slowly ta koma ta zauna ta rufe laptop din ta ta zame USB din ta meda cikin bag din ta , sannan ta dauke ta , ta koma bedroom din ta , ta ajiye saman table din office din ta , sannan ta juya ta fito dai'dai lokacin da Safna ta fito da ga cikin toilet ita ma ta na sanye da bathrobe white color
ko sannu ba ta ce mata ta sa kai ta fito corridor din ta koma parlour
Safna kuma ta shiga bedroom din ta
jim kadan ta fito Sanye da kayan barcin ta ita ma amma nata navy blue ne kuma wandon ta iya cinya ne kawai
ta na fitowa ta nufi parlour ita ma ta zauna geffen Esra ta ce mata " wai ba ki gyara komai ba yunwa na ke ji "
dan karamin murmushi Esra ta yi kafin ta ce " kin gan ni nan , ko kitchen din ma ban shiga ba , bare na yi tunanin gyara wani abu , ni na zata za ki biyo mata da take away da ga Restaurant din ku "
dan karamin tsaki Safna ta yi kafin ta kauda kan ta , ta ce " wane restaurant , yau bayan wuya ba abun da na sha , dan jaraba ni su ka bari serving yau , Wlh ba zan yarda ba , ni fa a matsayin Chef na nemi aiki cikin restaurant din , amma wai su ka ba ni receptionist"
yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " To tashi mu koma Nigeria mana "
dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " wa ? ni ? ai ni da Nigeria sai dai Ziyara , Ziyarar ma , sai da babban dalili "
💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞
__________________
💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞
( A HEART TOUCHING LOVE STORY )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💋
GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول!
BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM
PAGE 5 & 6 💦🔥
Dariya sosai Esra ta yi , wai Ziyarar ma sai da babban dalili kenan sai in parents din ta sun mutu ko kuwa ?
hararrar wassa Safna ta yi mata ta na fadin " matsala ta da ke kenan ba a iya hira da ke "
tsagaita dariyar ta Esra ta yi kafin ta ce " Oya shikenan na daina "
" ko ke fa , amma ba ki tambaye ni abun da ya faru restaurant ba yau "
daga mata gera guda Esra ta yi ta na fadin " Oya fadi ina jin ki ! "
gyara zaman ta Safna ta yi , ta juyo su na fuskantar juna ta ce " Shugaba ku na ONE WORLD TRADE CENTER , ya je sun yi wani meeting da wasu mutane a restaurant din mu , ni da kaina na yi serving din su , sai wajen karfe 4 na yamma su ka tashi "
dan tabe baki Esra ta yi ta na fadin " no really , kenan Saurin da na ga ya na yi da safe cen za shi ? "
daga kafadun ta Safna ta yi ta na cewa " na san ba , amma kin san abun da ya fi ba ni mamaki ? "
girgiza mata kai Esra ta yi allamun a'a
" wani hadaden saurayi ne na gani a tare da su , Esra ina fada miki , duk zaman da na yi a New York , ban taba gani Saurayi hadade irin shi "
katse Esra ta yi ta na tsaki sannan ta ce " Shi ne abun mamakin ? " ta kai karshen ta na kauda kai
cike da zumudi Safna ta ce mata " Ki tsaya ki saurare ni mana "
juyo da kan ta Esra ta yi kafin ta ce " to shikenan ina jin ki "
" yawwa ! ni fa ba haduwar saurayin nan na ke fada miki ba , idan ki ka gan shi ba zai wuce 30 years ba , amma duk mutanan da su ka halarci Meeting din da Boss su ke kiran shi , har shi kan shi shugaban ku , a sani na Kevin Brian shi ne Boss din ku , ko kuma akwai na sama da shi ? "
" haka na ji su na cewa amma wlh ban sani , Fada min ya kamanin shi su ke ? "
yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta ce " Gaskia a jiki dai ya hadu ga tsayi ga fafadan kirji kamar mai dambe , sai dai ya na sanye da face mask ban samu na ga fuskar shi ba , idanun shi kadai na gani , ya na da dara daren sexy eyes , Sai dai kwayar cikin su ban sani ba in blue ce ko green dan da ga nesa na gan shi kuma ya sunkuyar da kan shi , amma dai between Blue or green ce gaskia , ni sai da na ji Muryar shi ma na kara tabbatar wa da shi ne boss din su , kar ki so ki ji Muryar shi kamar a na busa sarewa dan dadi , kuma cikin nitsuwa ya ke magana kamar an yi mishi dole , kai gayen nan duniya ne kawai wannan ina ga shi ne Mister US baki daya ma "
Dariya sosai Esra ta yi har da lumshe idanun ta , ta na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12