Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fadin " Ni dai na san akwai Miss US , amma ban taba jin Mister US ba sai yau " hararrar ta da kyau Safna ta yi kafin ta ce " ke wlh dan ba ki gan shi ba ne , amma Allah ya sa su dawo restaurant din sai na dauki pics din shi dan ki gani " tsagaita dariyar ta Esra ta yi ta na fadin " hum na ji dai malama , yanzu tashi gyara mana wani abu mu Ci yunwa na ke ji " hararrar wassa Safna ta yi mata kafin ta ce " kin yi sa'a ni ma ina jin yunwa ba dan haka ba sai dai ki sha ruwa " ta kai karshen dai'dai lokacin da ta shiga kitchen din yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta dauki wayar ta saman table ta na daukar wayar ba abun da ya fado mata a rai sai Kim , kawai sai ta saki wani cool murmushi cikin zuciyar ta ta ce " ko ba komai ya Hadu gaskiya " ta na tuno yadda ta gan shi ya na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali , duk yadda a ka yi wannan akwai wani boyayen Al'amari a tare da shi ta yi nisa cikin duniyar tunanin ta , ta jiyo Muryar Safna ta na cewa " ke malama tun dazu a na kiran ki a waya ba ki jine ? " a dan razane ta dawo cikin hayacin ta dago wayar ta ta na kallon screen din wani cool murmushi ta saki kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na fadin " Amarsu ta ango , lfy a ka kira ni warhaka ? " wata yar karamar dariya na fara jiyowa kafin na jiyo Muryar wata macen da ga jin ta ta budurwa Ce ta na fadin " Za ki fara ko ? ni yanzu fada min yaushe za ki zo kin san fa jiya a ka kawo lefe amma ko kira na ba ki yi ba " a kai karshen cikin shagwaba yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " Sorry sister na , ya ki ke ya su momy duk da ma mun yi waya da ita da safe " " Fine ! kowa ya na nan lafya , yanzu fada min yaushe za ki zo ne ? " " kawai dan ki tambaye ni yaushe zan zo , auren da ko rana ba saka ba " Esra ta fada ta na mikewa tsaye ta fara takawa ta nufi corridor a daya bangaran kuma a ka ce mata " Hum wa ya fada miki , ai jiya a ka saka rana , Farko ga watan March " " wow ki ce nan da two months " ta fada dai'dai lokacin da ta ke shiga cikin dakin ta " eh , nan da kwana 52 bai kai two months ba " yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " to sannu malama har kin kirga ko kwana nawa ne " " eh mana dole na kirga kwana nawa su ka yi mana saura ni da Habibi kafin mu zama Mr & Mrs Raouf " ta kai karshen ta na yar karamar dariya dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " ke ki ka san wani Habibi , kin ga sai an jima ni Sallat zan yi , sai da Safe " ta na gama fadar haka ta sauko wayar ta katse kiran ta nufi closet din ta , ta bude ta dauki wani Hijab White color ta saka , har kassa sannan ta dauki Sallayar ta shinfida , ta Haye ta tada sallar ta cikin konciyar hankali ___________________________________________ WASHE GARI ▪GREENWICH STREET a hankali ta ke tafiya saman titin , ta na sanye wando palazzo pink color da Shirt White color , ta yi Rowling veil din ta a kai shi ma White color , ta na rike da bag din ta , ta na tafe ta na juyawa kar a je yau ma akwai baratin nan da su ka tare ta a haka har ta karaso wannan kwangon da ta ga Kim ya shiga a jiya ta na shiga ta hango shi cen zaune saman wasu case , ya hada bayan shi da bango ya lumshe idanun shi , ya na sanye cikin wando Crazy jeans black color , da wata T-shirt white color gaskia wannan bai min kama da dan shaye² ba , dubi yadda ya ke a wanke tsab tsab Masha Allah akwai dai wata a kassa a hankali ta karaso gaban shi ta na Sallama duk da ta san abu me wuya ne a ce zai amsa mata ko motsi ma bai yi ba , amma ya san da ita dan tun lokacin da ta yo kwanar ya jiyo qamshin turaren ta Murya cen kassan makoshi ta ce mishi " Kim ? " ta fada ta na dan lekon Face din shi ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce mata " What are you doing here ? " ya fada cikin sanyin murya da sauri ta yi baya kadan , ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta " Kim , wine ka sha amma ko ? " ta fada dan ta jiyo warin ta cikin breath din shi gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba " Why ? " ta fada mishi cikin sanyin murya wani dan karamin murmushi Geffen fuska ya yi kafin ya ce mata " ke ni fa dan iska ne , shan wine karamin abu ne waje na , wai me ya kawo ki nan ma please let me " cikin Sigar rarrashi ta ce mishi " please ka daina , wlh za ta iya maka illa ba kadan ba " irin wannan murmushin Takaici ya yi kafin ya ce " please ki daina nuna kin damu da ni , ba ki san ni ba , ba ki san ko wanene ni ba , ki na ganin wajen da na ke zaune , kullum cikin tsangwamar mutane na ke , su na zagi na , Kalle ki , ki kale ni rayuwar mu ba daya ba ce , dan haka ki daina kula ni please ba na bukatar kindness din ki , ki tafi ki kyale ni " " tabass ban san ka ba , ba ka san ni ba , amma ai ka taimake ni duk da ba ka san ni ba , ka ga ko dan hakan zan iya nuna damuwa gare ka , ni gaskiya ce na fada maka , shan wine babu kyau , ta na iya janyo maka cancer , sannan cikin adinin mu , shan wine Haramun ne " ta fada dan ita sam ta manta da shi ba musulmi ba ne murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Ke ki ka san wani addini , Ni ba ni da wani Aboki duniyar nan kamar Wine , duk lokacin da na sha ta na kan ji damuwa ta ta fi , na kan ji na daina kewar ta , please and please let me ki na damu na " tsaya wa ta yi ta na kallon shi ba tare da ta ce komai ba tabass akwai wani boyayen al'amari tare da shi , amma minene wannan abun ? ita ta ma rasa dalilin ya sa ta damu da shi lokaci guda haka , musaman dan ta gan shi yau ta fito tun karfe 7 ga shi kuma ya ce ta kyale shi , ko bude idanu bai yi ba bare ya kale ta a haka dai jiki a mace ta juya ta fara takawa ta bar wajen ya na jin ta fara takawa ya bude idanun Slowly sun yi jazir ko , lalle ya na cikin maye wani dishi dishi ma ya ke gani , amma a haka ya raka ta da kallo har sai da ta bar wajen , sannan ya meda idanun shi ya lumshe a hankali ta ke Tafiyar ta duk ta yi nisa duniyar tunanin ta ba ta fi ten minutes ba ta iso hall din ONE WORLD TRADE CENTER sai a lokacin ta dawo cikin hayacin ta , ta na shirin shiga ko ta ga Kevin ya fito da ga cikin building din , ya na sanye da Suit sky blue ma su mugun kyau , ya na sanye da bakaken glass a idanun shi , ya na takawa cike da kwarjini a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ci gaba da takawar ta kai a sunkuye yau duk jikin ta a mace ya ke har ta kai bakin kofar ta jiyo Muryar Kevin ya na kiran ta dum ta ji Gaban ta ya fadi har sai da ta karanto kalmar shahada a haka ta juya ta nufe shi ya na tsaye bakin motar shi , driver ya bude mishi kofar kai a sunkuye ta ce mishi " Good morning Sir " a hankali ya sa hannu ya sauke glass din shi ya zuba mata idanu babu ko kiftawa nan take ta ji duk ta tsargu , slowly ta dago da kan ta , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi da sauri ta meda kan ta ta sunkuyar ta na sunkuyar da shi , shi kuma ya meda glass din shi ya ce mata " lafiya yau ki ka zo da wuri ? " ba tare da ta dago kai ba ta ce " nothing Sir " gyada kan shi ya yi a hankali kafin ya ce " no wonder , Hope za a ci gaba da zuwa a cikin lokaci " ya na gama fadar haka ya juya ya shiga cikin motar shi ya na shiga ita ma ta juya ta nufi building din ta shiga dai'dai lokacin da motar su ta bar wajen da mugun gudu kai tsaye lift ta shiga ta nufi floor na 97 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : Meerah 🎀💋 THE WRITER'S OF TAURIN ZUCIYA EXILED PRINCE HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM P A G E 7 & 8 💦 🔥 kofar Lift na budewa ta daga kafa ta fara takawa ta nufi office din ta , ta na isa ta kai hannu saman finger print , nan take kofar ta yi wata yar kara ta bude kan ta , a hankali Esra ta shiga ta na sallama cen kassan makoshi , office din ta ta nufa , ta ajiye bah din ta a saman desk din , sannan ta zagaya ta zauna saman chair din ta ta na zama ko Cherry ta turo kofar ta shigo office din da murmushi a fuskar ta ta ce " Hi Esra , How are you ? " murmushi kadan ita ma Esra ta yi mata kafin ta ce " Fine Cherry " karasowa cikin office din Cherry ta yi ta nufi daya da ga cikin chair din da ke gaban desk din ta janyo ta zauna ta na kallon Esra ta ce " ya a ka yi ki ka riga ni zuwa yau ? " murmushi mai dan sauti Esra ta yi kafin ta ce " ai dama kullum sai na riga ki zuwa " wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na shirin magana Arthur ya shigo office din ya na fadin " wai da gaske Esra ce a karfe 8 dai'dai ? " hararrar wassa Esra ta yi mishi ta na fadin " wai kowa cikin companyn nan ido ya saka min " karasowa ya yi cikin office din ya ja chair din da ke geffen ta Cherry ya zauna ya na fadin " Ni ban sani ba , amma ni da Cherry dai mun sa miki ido " ya na gama fadar haka Cherry ta mika mishi hannu ta na fadin " ka gani ai , karfe 8 saura mintina biyu , ban kudi na " cikin rudu Esra ta ce mata " Wane kudi kuma ? " " oh bet mu ka yi , na ce mata yau ma sai kin late , ita kuma ta ce ba za ki yi ba " Fadin Arthur ya na fidda 100 Dollar ya ajiye saman hannun Cherry wani dan karamin murmushi Esra ta yi ta na kallon su ta ce " yanzu tsakani da Allah bet ku ke yi a kai na ? " " may be ba mu kadai ba ne , ko kuwa Arthur ? " Cherry ta fada ta na dawo da kallon ta kan Arthur wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan yanzu Esra minene ki ke son gwada mana , yi sauri kar Sir Kevin ya dawo ya tardo mu nan " gyada mishi kai ta yi kafin ta kai hannu ta janyo jakar ta , ta bude ta ciro laptop din ta , da wannan USB key din , bude laptop din ta ta yi , ta kunna ta , sannan ta saka wannan USB key din ta shiga latsawa na dan lokaci kafin ta juyawa su Arthur laptop din a hankali Arthur ya kai hannu ya janyo laptop din gaban su shi da Cherry su na kallon screen din can kuma sai Cherry ta daura hannun saman bakin ta , ta na zaro idanu ta ce " Oh My God , Esra ina ki ka samo wannan abun ? " " yadda ku ka gan ta haka na gan ta ni ma , abun ya yi matukar ban mamaki " Fadin Esra ta na gama rufe bakin ta Arthur ya ce " Esra , ba fa karamin abu ba ne a nan " ya fada ya na latsa laptop din wata ajiyar zuciya Esra ta fada kafin ta ce " ni kai na na yi mamakin ina na gamo da wannan abun wlh " katse ta Cherry ta yi da cewa " Duk wasu kudi da a ke fitarwa da ga account din company , duk relieve din shekarar nan su na a ciki , Idan har da gaske ne hakan na nufi abun da a ka sata cikin companyn nan sun kai wajan one Hundred Milliards of American dollars kuma duk da sunnan Sir Kevin " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan Arthur " kenan Sir Kevin shi ke satar kudin companyn nan ? " Arthur ta fada ya na dago kai ya kali Esra kada mishi kafadu ta yi allamun ita ma ba ta sani ba da sauri Cherry ta ce " Tabass shi ne , a na satar irin wadanan makudan kudaden kuma ya yi shiru bai sa an fara investigation a kai ba , ku ma kun san da wata a kassa " gyada mata kai Arthur ya yi ya na cewa " ni ma abun nan ya tsaya min , ya san satar da a ke yi kuma bai sa an fara investigation a gano waye ke satar ba , shi ya ke aikata satar shi , shi ya sa ya ja baki ya yi shiru , sai dai ya yi ta sallamar ma'aikatan da ba su ji ba , ba su gani ba " ya kai karshen ya na dan tsaki " yanzu Esra ya ki ke so mu yi , dan gaskiya ba zan iya yin shiru ba , Idan ya ci gaba mu ma za mu rasa hanyar cin abincin mu , duk gidan mu fa da aikin ga nawa su ka dogara , idan ya kore ni akwai matsala fa ! " fadin Cherry cikin nuna damuwa Dan jinkirtawa Esra ta yi kafin ta ce " ni ma abun da ya sa na kawo muku ky gani kenan , saboda abun da ha ke ba dai'dai ba ne , Arthur ka ce ai companyn ba tashi ba ce ? " ta fada ta na kallon Arthur gyada mata kai ya yi kafin ya ce " eh ba tashi ba , ta little brother din shi ce " " Fine , shi ya kamata mu kai wa wannan abun ya gani " cikin nitsuwa Arthur ya katse ta da cewa " ki bar ma wannan tunanin , it's not sure ya yarda da mu , kuma wannan ba zai isa ba , dole mu samo File din in har ta cikin laptop ne zai iya cewa karya mu ke yi wa dan uwan shi " cikin rudu Cherry ta ce " wai wanene mai companyn nan , ni fa shekara uku yanzu ina aiki a ciki , ba dan jiya ka ce min ba sir Kevin ne ba PDG da ba zan taba sani ba " wata yar karamar ajiyar zuciya Arthur ya sauke , Kafin ya jingina bayan shi a jikin chair din ya ce " Ayden Brian , shi ne PDG din wannan company , asalin wannan companyn ta mahaifiyar su ce , ya na da shekara 20 ta rasu , duk wani abu da ta mallaka ta saka shi a sunnan Ayden Brian har da companyn nan , a lokacin ya na cikin kuruciyar shi ne ya sa mahaifin su yanke shawarar ba wa Kevin companyn dan ya kula da su , dan Ayden ya samu damar kamala karatun shi , bayan ya Kamala karatun shi ne ya shiga harkar restoration , yanzu haka maganar da na ke miki ya na da restaurant a ko ina cikin New York , Washington , New jersey da canada , ya fi meda hankali a kan Restoration din , da a ce ya meda hankali a kan Companyn nan , da zai gano irin satar da dan uwan shi ke yi mishi , ni dai ko so guda ban taba ganin shi cikin companyn da sunnan ya zo aiki , shi ya sa kowa ke ganin cewa Kevin shi ne PDG " ya kai karshen ya na jan nunfashi " kenan Restaurant din , da Safna ke aiki a ciki nashi ne ? " Esra ta tambayi kan ta cikin zuciyar ta ta na a haka kawai ta ji Muryar Cherry ta na fadin " Yanzu ya za mu yi mu samu file din , ya kuma za mu yi mu samo Ayden Brian yadda za mu gwada mishi tun kafin lokaci ya kure mana " " File din na san ba zai wuce cikin Office din Kevin ba , maganar Ayden kuma gaskiya abu me wuya ne samo shi " Arthur ya fada ya na gama rufe bakin shi ya jiyo Muryar Esra ta na cewa " ni zan Samo muku Ayden , ku yi kokarin samo mana File din nan t ........ " ba ta kai karshen maganar ta ba Arthur ta katse ta da cewa " ke malama shiga office din Sir Kevin ba karamin abu ba ne , A floor na 101 ya ke , kuma Security system din shi ya fi na kowane office , musaman scanner din na kwayar idon shi ce ba na hannun ba , sannan akwai wani password wanda Kevin ne kadai ya san shi , Idan ka yi kokarin saka password din da ba shi ba har sai uku , nan take machine din will send an electric shock before you even move, you will be electrocuted to death, on top of that, when Kevin closes his office with his magnetic card, there is a laser beam system which is triggered, the only way to deactivate it is with this magnetic card , so forget even the idea it's dead " " kun gani ko , dan ba shi da gaskiya ne ya sa wannan uban security , da a ce ya na da gaskiya password din ma kadai zai isa " Cherry ta fada cike da bacin rai a hankali Esra ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " yanzu babu wata hanya da za a shiga office din nashi ? " da sauri Cherry ta ce " System of climatisation " cikin rudu Arthur da Esra su ka maimaita abun da ta ce da sauri Cherry ta mike ta nufi bayan desk din Esra , ta na nuna mata wani air conditionner ta ce musu " duk yadda a ka yi akwai ac a office din shi , why ba za mu yi anfani da hakan ba wajen shiga office din nashi ? " " ki na da hankali kuwa ? dubi girman building din nan , kafin ma mu samo na office din shi zafi ya kashe mu , ko kuma mu bace " Fadin Arthur cikin nitsuwa Esra ta ce musu " ku na ji ko , ku bari idan mun sauka mu tafi apartments di na , ko kuma mu tafi shan coffee a cen mu yi maganar mu cikin konciyar hankali " a hankali Cherry ta dawo wajen Chair din ta ta zauna ta na fadin " okay hakan ma zai fi , kun san akwai camera cikin office may be maganar nan da mu ka yi ma sun jiyo mu " a tare Arthur da Esra su ke hada baki su na cewa " da gaske ki ke ? " su ka fada su na zaro idanu da ga gani sun tsorata wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na fadin " na so kun ga kawunan ku , wai da gaske ki ke ? , matsorata kawai " ta kai karshen ta na sakin wata dariyar a tare Arthur da Esra su ka ja tsaki su na cewa " Allah ya shirya ki wlh " cikin dariyar ta ta , ta ke fadin " da gaske na ke akwai cameras , sai dai ban sani ba in akwai cikin office din mu ba " mikewa tsaye Arthur ya yi ya na fadin " ni na tafi Abu na tun da haka ne " wata yar karamar dariya Esra ta yi ta na fadin " kenan da gaske ta ba ka tsoro ? " " kin san an ce hanyar lafiya a bi ta da shekara , gwara na tafi kamar yadda na shigo , sai mun hadu an jima " ya na gama fadar haka ya kafa ya fice ya na fita Cherry ta kalli Esra ta ce " yau ba ki hadu da dan iskan ki ba ? " ta kai karshen ta na daga mata gera tsuke fuska Esra ta yi ta na fadin " kin ga malama tashi fice min da ga nan " wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na kokarin tashi ta ce " da ga tambaya ? , ni ma na tafi tun da haka ne ". " ai dama ban kira ki ba " Esra ta fada ta na kai kallon ta kan laptop din ta " okay , see you later " Cherry ta fada ta

Chapter 3 of 12