Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : Princess Meerah 🎀💋 THE WRITER'S OF TAURIN ZUCIYA EXILED PRINCE HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) * Wannan gajeran labari ne , labarin soyayya tsakanin Fari da Baki , Soyayya tsakanin abun da ba za su taba kasancewa a waje guda ba , ga cin amana , na jinin ka ma ba zai kyale ka ba , wannan labarin da ga karkashin zuciya ta ya fito , duk wanda ya sauya min ko da kalma daya cikin abun da na rubuta ban yahe mishi ba , sannan duk wata kalma da na fada ba dai'dai ba ko na yi kuskure to ku yahe min , Duk kuma wanda ya fadi wata mumunar kalma a kai na , to shi da Allah * GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {PAGE 1 & 2 💦🔥 } ▪UNITED STATE OF AMERICA ( U.S.A ) ▪NEW YORK STATE ▪GREENWICH STREET Wata kyakyawar Budurwa ce ke tafe a saman titin waya a kunne Ta na sanye cikin Wando palazzo Black colour da Shirt Navy blue , ta yi Rowling wani veil navy blue a kan ta , ta na rataye da wata yar bag Black ita ma , hannun ta na dama ta rike da wani cup na coffee dayan kuma ta na rike da wayar ta a kunne Budurwa kyakyawar gaske ce , amma kallo daya za ka yi mata ka san ba jinin turawa ba ce , a shekaru za ta kai 22 years Skin din ta fara ce kal amma ba kamar na turawa ba , ta na da dara daren idanun ma su daukar hankali , farare kal kwayar cikin su kuma Black ce , Black din ya ciza sosai har wani kyali ya ke yi eyelashes din ta dogaye da su kuma baki kirin , ta na da dogon hanci kamar pencil , design din lips din ta gwanin burgewa , pink colour da su ga bala'in laushi , sun sha lips balm , ta saka wasu medical glasses a idanun ta Ta na da shape kamar na coca cola , hips da breast din ta cike su ke bam dai'dai shekarun ta , ta hadu iya haduwa kamar ita ta yi kan ta Masha Allah Wani cool murmushi ta saki cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ta ce " Momy , ki bari har na samu hutu , in sha Allah ina nan zuwa , kin San ba yadda za a yi auren Yasmine ba na nan " ta fada da haoussa , hakan na nufin ita bahaoushiya ce ? Ta dan dauki lokaci kafin ta saki yar karamar dariya ta ce " Momy , aure fa lokaci ne , in sha Allah in na wa lokacin ya zo zan yi , amma gaskiya ban da ra'ayin aure a yanzu " ta kai karshen dai'dai ta sha wata kwana Kawai sai jin ta ta yi ta bugi mutun har sai da cup din hannun ta ya kubce mata ya fadi kassa cikin sa'a bai bata mata kaya ba Da sauri ta dago kai ta ja da baya Wasu samari ne tsaye a gaban ta , sam ba su yi kama da mutanan kirki ba Kare musu kallo da kyau ta yi kafin ta ce " momy ina kiran ki " da ga haka ta sauko da wayar ta , ta kashe kiran sannan ta ce da samarin nan " How can i help you ? " Wanda ta yi karo da shi ne ya mika ma ta hannu cikin tsawa ya ce " Give me your phone " " why ? " ta fada mishi cikin ko in kula Wata yar karamar dariya ya yi kafin ya fido gun a bayan shi ya saita kan ta , da sauri ya na fadin " give your phone , give your phone " Dayan saurayin ne ya katse shi da cewa " and her bag " Wata yar kara budurwar nan ta yi kafin ta mika mishi wayar ta da sauri hannun ta har kerma ya ke yi ta fido jakar ta , ta mika musu ta na fadin " please let me , ga su nan na ba ku " Su na karba su ka yi kwanar da ta fito da gudu Su na barin wajen ta daura hannayan ta saman kai nan take idanun ta su ka kawo ruwa ta na fadin " wayooo Allah na shiga uku na , ina zan sa kai na yau ni Esra , duk keys din apartments di na su na a ciki ya zan yi da raina ni " Sai sambatun ta ta ke yi ita kadai dan hanyar babu kowa saman ta Kamar da ga sama ta jiyo Muryar mutun a bayan ta ya na fadin " Miss wannan na ki ne ? " A dubu dari ta juyo ta na kare mishi kallo Saurayin ya hadu ba laifi gaskiya , a shekaru zai kai 33 years Fari kal da shi kamar ka taba jini ya fito , ya na da sexy eyes farare kal kamar madara , kwayar cikin su kuma light Green ce , da dan karamin bakin shi , lips din shi kuma duk pink color ne , gashin kansa Darck black curly ne amma bai tara suma sosai ba , ta zubo mishi gaban goshi kadan ta rufe idanun shi , ya na saka wani earring a kunnen shi na dama ga wani saje baki kirin konce a fuskar shi , ya na da tsayi ga kuma murdaden jiki sosai allamun ya na yawwan motsa jiki Ya na sanye cikin wando Crazy jeans blue color , sai yar singlet fara wadanan karfafun damtsen na shi duk a waje su ke , kafafun shi su na cikin wasu sneakers ma su mugun kyau farare , A hankali ta sauko da kallon ta kan abun hannun shi , ta na ganin bag din ta da phone din ta ta saki wani kyawatencen murmushi Da sauri ta kai hannu ta kwace su , ta na fadin " eh , nawa ne , na gode sosai , na dauka na rasa su kennan har abada " Hannayan shi ya saka cikin aljihun shi kafin ya ce " sai a bani ladan aiki na ko , ko 100$ ce za ta ishe ni " ya kai karshen ya na fudo hannun shi ya kai bayan keyar shi Kare mishi kallo ta yi da ga sama har kassa kafin ta ja wani dan siririn tsaki ta juya ta ci gaba da tafiyar ta , ta rataya bag din ta Ta na shirin mayar da phone din ta cikin bag din ta , ta ji an zabce mata ita A dubu dari ta dago kai ta na fadin " waye ne ? " , nan ta ga saurayin nan ne , ya na zabtar wayar ta ya yi gaba ya yi wata yar kwana da ke gaban su kadan Da sauri bi bayan shi ta na fadin " kai malam ban waya ta " dai'dai lokacin da ta yi kwanar ita ma Cak ta tsaya ba shiri , ashe ba kwana ba ce , irin dan kwangon nan ne da turawa ke yi dan ajiye trash bin Cen ta hango shi zaune saman wasu kwali , ya na rike da wayar ta ya na jujuya ta , hannu gudan kuma ya na rike da taba ya na busawa ( YANZU DA YIN KWANAR SHI HAR YA SAMU DAMAR KUNNA TABA ? 🤔🤔🤔 ) A hankali ta karaso gaban shi ta na sa hannu ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta dan wajen ya na mugun wari , ga kuma na tabar da ya kunna , amma shi sam bai damu ba ya saba da wannan warin Gaban shi ta karaso ta mika mishi hannun ta , ta na fadin " give my phone please , wlh na yi late a wajen aiki " Ba tare da ya dago kai ya kale ta ba ya ce " cewa na yi ki ba ni ladan aiki na amma ki ka ki , kin san idan na sayar da wayar nan za ta fi 100$ ? " Da sauri ta ce mishi " eh na sani , ka yi hakuri ban rike da kudi amma gobe zan kawo maka please ban waya ta " A hankali ya kai tabar shi baki ya ja kafin ya sauke ta ya busa hayakin a saitin ta Da sauri ta kauda kai gefe ta na dan lumshe idanun ta " What's your name ? " ya fada ya na meda tabar shi baki Dan tsaki ta ja kafin ta ce " don Allah ka ban waya ta " " who is Allah ? Ni ban san shi , dan haka in ki na son wayar ki , ki amsa min tambayoyi na " ya fada ya na kunna wayar ta ya kali screen din , hoton ta ne ke sama , ta na sanye cikin wata gown pink colour , zaune cikin wani garden ta saki murmushi gwanin burgewa Da sauri ta ce mishi " Esra Yahaya " A hankali ya gyada kan shi kafin ya ce " okay , my name is Kim , are you married ? " " no " ta fada a takaice " okay zan ba ki wayar ki , but promise me za ki kawo min Chocolate gobe , ko ba ki zo ba ni zan tarda ki gida " ya fada ya na mika mata wayar ta Maganar shi ba karamin mamaki ya ba ta ba , ba ta san lokacin da ta ce mishi " me kuma za ka yi da chocolate kai da ke shan taba , na dauka kudin sayan tabar ka ke so " Slowly ya sunkuyar da kan shi ya ce " Kudin sayan tabar ba za su yi min wuya ba , kawai chocolate din na ke so " Kare mishi kallo da kyau ta yi kafin ta kai hannu ta karbi wayar ta juya ta fara takawa za ta bar wajen Ya na jin ta fara takawa ya dago kai slowly ya na kallon yadda ta ke tafiya cike da nitsuwa Sai da ta kusa fita wajen ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Ki daina biyowa hanyar nan , akwai gangster sosai a wannan lokacin , ba ki ga babu kowa saman hanyar ba " Dan karamin murmushi ta yi mishi kafin ta ce " na gode , gobe zan kawo maka chocolate din ka " da ga haka ta juya ta fice wajen Har ta bar wajen bai janye kallon shi ba , sai da ya dauki lokaci kafin , ya sa hannu cikin gashin shi duk ya cakuda , ya sa hannu cikin aljihu ya ciro kwalin tabar shi ya ciro guda ya kunna ya ci gaba da aikin shi Esra kuma ta na barin wajen ta fara tafiya da sauri sauri ba ta dauki 6 minutes ta iso bakin wani tanpasheshen building duk na zallar glass ▪ONE WORLD TRADE CENTER ya na da ga cikin jerin manyan building goma na cikin New York , ya na dauke da hawa dari da hudu , wannan ginin sai da ya dauki wajen shekara 7 a na yin shi , sannan an kashe mishi makudan kudade wanda za su kai 3,9 milliards na dollars Da sauri ta shiga cikin building din ta na duba watch din hannun ta Kawai sai jin ta ta yi ta bugi kirjin mutun , har sai da bag din ta , har takardun da mutuman ke rike da su ka zube Ba tare da ta dago kai ba ta ga wanene gaban ta ba ta duka da sauri ta dauki jakar ta , ta rataya sannan ta fara tatare takardun shi ta na fadin " yi hakuri don Allah , wlh sauri na ke tun Sir Kevin bai gan ni ba , na....... " kut maganar ta yanke sakamakon dago kan ta da ta yi ta ga wanene ke gaban ta Tsaye ya ke cak cike da kwarjini ya na sanye cikin Suit farare kal gwanin burgewa Cikeken bature ne fari kal da shi kamar ka taba jini na hito , ya na da dan tsayi amma ba sosai ba , da murdaden jiki , ya na da kananan idanu farare kal kwayar cikin su kuma black ce , ya na da dogon hanci , da jajayen lips shape din su kamar heart , bai wani tara gashin kai ba shi ba baki ba , shi ba brown ba , sumar shi a konce ta ke lufff gwanin burgewa , gayen ya hadu sosai amma fuskar nan ta shi a daure ta ke tamau kamar hadari Murya na kerma Esra ta shiga fadin " So.......sorry sir " ta kai karshen ta na mika mishi takardun shi da ta su ka fadi Hannun ya sa ya karbi takardun shi ya na tsare ta da wadanan kananan idanun shi Ya na karba ta yi sauri ta raba ta geffen shi ta wuce Ba ta yi wani taku biyu ya kira sunan ta cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa da izza , cak ta tsaya ta lumshe idanun ta na karanto duk wata adu'ar tsari da ta fado mata a zuciya A hankali ya daga kafa ya dawo gaban ta ya tsaya ya na ci gaba da kallon ta Sai da ya dauki wajen good ten minutes a haka kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce " open your eyes " Dum ta ji gaban ta ya fadi , zuciyar ta ta shiga duka uku uku , a hankali ta fara bude idanun ta , sai cikin na shi , da sauri ta sunkuyar da kan ta , dan ba za ta iya jure kallon cikin idanun shi ba A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce mata " me ya tseda ki , yanzu karo na hudu ki na zuwa a makare cikin satin nan , apartments din ki fa just behind ya ke , ba zai wuce ki dauki 15 minutes cikin kin jima kafin ki zo , amma kullum sai kin yi late " Wasu yawu ta hadiye kafin ta bude baki lips din ta har kerma su ke yi wajen cewa " I'm so sorry , wlh wasu........ " A hankali ya katse ta ta hanyar daga mata hannu ya daura da cewa " ki bi a hankali Miss Esra , in har ki na son aikin ki , dole ki kiyaye nan gaba ba zan iya daukar wannan late ba " " nagode Sir in sha Allah zan kiyaye " ta fada cikin girmamawa Sai da ya tsaya kallon ta da ga sama har kassa sannan ya raba ta geffen ta ya fice abun shi Ya na fitowa sai saman wata dankareriar mota baka kirin har wani kyali ta ke yi kamar mirror , kudin motar nan kadai ya isa mutun ya yi lafiyayen gida har ma ya ja jari Da sauri driver din shi ya bude mishi kofar baya , ya na shiga ya meda kofar ya rufe ya koma wajen shi da sauri ya tada motar su ka bar wajen da gudu Da kallo Esra ta raka shi sai da ya bar wajen sannan ta sauke nanauyar ajiyar zuciya har sai da ta dan lumshe idanun ta ta na dafe saitin zuciyar ta ta na fadin " Allah na gode maka " da ga haka ta daga kafa ta nufi lift kai tsaye hawa na 97 ta nufa dan ta na cikin manya manyan ma su aiki a wajen Sai da ta dauki wajen 2 minutes kafin lift din ya bude ta fito Wajen cike da ya ke da mutane sai zirga zirga su ke yi , kowane rike da file a hannun shi sai sauri su ke yi Da sauri ta nufi wani dan madaidaicin office na glass Ta na isa ta daura hannun ta saman finger print nan take door din ta bude kan ta Har ta daga kafa za ta shiga , ta jiyo Muryar wata yan mata a bayan ta ta na kiran sunan ta Slowly ta juya ta na ganin yarinyar ta saki wani cool murmushi sannan ta shiga cikin office din , ta na shiga ita ma yarinyar nan ta shigo Yarinyar cikakiyar baturiya ce a shekaru za ta kai 24 haka , ta na sanye cikin wata gown dai'dai guyiwa navy blue , ba laifi ta hadu Sai da Esra ta nufi desk din ta , ta zauna saman chair sannan ta ce " Hi ! " ajiye bag din ta ta yi saman desk sannan ta juyo ta kali baturiyar nan ta ce " Good morning Cherry " Gyada kan ta Cherry ta yi sannan ta ce " lafiya ki ka yi late haka , ko dai har yanzu ba su gyara Lift din building din ku ba , ya kamata ki sauya apartments gaskiya Esra " Dan karamin murmushi Esra ta yi ta na zama saman chair din ta , ta ce mata " Cherry in na sauya na tafi ina , kar ki manta ba ni daya ba na ke zaune ciki ba , Sun gyara lift din tun shekaran jiya , Wlh tsotsayi ne ya kai bin GREENWICH STREET a tunani zan fi sauri , kawai na hadu da wasu yan iska su ka kwace min Bag di ta da waya ta " " No , har yanzu a na yaayin wannan abun ? To ya a ka yi ki ka karbo su ? " Dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " Wani dan iskan kamar su ya amso min su , shi ma da kyair ya ban wayar cewa ya yi sai na ba shi wani abu , ni kuma babu cash a jiki na " Yar karamar dariya Cherry ta yi sannan ta ce " Esra akwai ki da abun da dariya , wai wani dan iskan kamar su , inda dan iskan ne ba zai medo miki kayan ki ba sai dai ya yi gaba da su , kin san dama raba sata ga barawo........ " Ba ta karasa maganar ta ba wani bature ya turo kofar office din Esra ya shigo ya na sanye cikin Suit Bakake Ya na shigowa ya nufi wata yar sofa da ke fuskantar Desk din Esra Wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " Miss Esra yau ma late , hope dai ba ki hadu da wannan mai fuskar shanu ba , dan fa yau a sama ya ke " Yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " ni ko na hadu da shi , har mu ka buge juna , ai shi dama kullum sama ya ke " Wannan karan a tare duka su ka yi dariya sannan baturen ban ya daura da cewa " Amma kin yi sa'a fa , yanzu haka abun da na ji ya sallami ma'aika ta har biyu ba su ji ba , ba su gani ba " Dan zaro idanu Cherry ta yi ta na komawa geffen shi ta zauna ta ce " please da gaske ka ke Arthur ? " Gyada mata kai ya yi ya na fadin " da gaske na ke , yanzu haka ma sun bar building din " " Toooo , lafiya ya sallame su haka kawai " Esra ta fada cike da tsoro cikin zuciyar ta Mikewa tsaye Arthur ya yi , ya dawo bakin kofar office din ya dan soko kai , ya leka ya ga ba kowa sannan ya koma ya rufe kofar , ya rage sautin Muryar shi ya ce " ni ma ban sani ba amma na ji an ce wai , ana fitar da kudi da ga cikin account din companyn , last relieve ma babu one Milliard , kuma ba yanzu

Chapter 1 of 12