Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasa kwanciya tunda a gaban ta akayi ba kuma ta tab'a ganin hatsari a zahiri ba sai a kan wannan. Baba ya jima da fita ya dawo Umma tace, "Malam an same ta?." Baba yace, "ban samu komai, inda aka buge ta d'in tabbas ga jini nan har yanzu yana wajan amma babu wanda yazo ya bada sanarwa koda y'an uwan ta zasu neme ta." Umma ta dafe kanta tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu a ina zamu same ta gashi har dare yayi?." Baba yace, "ki kwantar da hankalin ki ko waye ya buge ta zai nemi dangin ta ai kodan kula da lafiyar ta, kiyi hak'uri." "Ka gani ko?, kaga illar tallan da suke fita ko? Yanzu da basu je tallan ba da babu abinda ya same ta." "Tsautsayi ne ko tana gida sai ya same ta" ya fad'a yana fita daga gidan gabad'aya. Umma kasa magana tayi sai tagumi da tayi kawai zuciyar ta na k'una da zafi domin bata san halin da y'ar tata mai tausayin ta take ciki ba. *◇◇◇* Lokacin da Hydar ya shiga gida b'angaren mahaifiyar sa ya wuce a nan ya same ta a zaune ita da Asad ta saka shi a gaba tana ta jero masa tambayoyi amma guda d'aya ya gaza bata amsa, yadda ya shigo ya saka ta bishi da kallo tace, "Hydar lafiya?." Kusa da Asad ya zauna yayi shiru kafin ya kalle ta yace, "Accident nayi." Suhaima tace, "Accident a ina?." Kafin yayi magana Mama tace, "Babu abinda ya same ka?." "Babu Mama, but na buge wata yarinya yanzu haka ta asibiti unconsciously." "Da ranta dai ko?" Suhaima ta tambaya tana kallon sa. Kai ya d'aga alamun eh Mama tace, "A ina take yarinyar?." "I don't know, but zata tsallaka titi ne kawai sun fito daga kasuwa, I think tana sai da abinci ne." "Mtswww, to meye na damuwa? Ba ka kaita asibiti ba?" Ta fad'a tana kallon sa ganin yadda ya wani damu akan y'ar talakawa. Hydar yace, "Ranki ya dad'e Dr ya tabbatar min in abinda akayi bai yi ba sai an kaita Cairo an yi gyaran a can, taji ciwo sosai a k'afar ta kuma nine sila dole na damu." Mama ta tab'e baki tace, "Is okay tunda dai kai lafiya kake, kaje ka huta." Jikin sa a sanyaye ya mik'e sai a sannan Asad yace, "Sorry Bro." Kai ya girgiza kawai ya fita daga apartment d'in. "See him akan wata yarinya yar talakawa yake wannan damuwar, I hate dis" ta fad'a tana bin sa da kallo tana yatsine fuska kafin ta dawo da kallon ta ga Asad da yake kallon ta tace, "Dis time bazan d'aga maka k'afa ba Asad dole kaje ka nemo auren Jidda itace zab'ina a wajan ka sai kuma ka aure ta." Kai ya girgiza baice komai ba dan bai san me zaice mata ba. Baiyi magana ba Suhaima taji wayar ta na k'ara ta mik'e ta fita daga falon gabad'aya ta nufi can k'arshen gidan ta hango wanda ya kira ta a tsaye yana jiran ta, "Hello Suhail, I hope lafiya kake nema na haka?" Ta fad'a tana kallon sa. Kallon ta yayi yace, "lafiya lau Auta, akwai wani abu da nake so na baki ne ban sani ba ko zaki karb'a." "Meye shi?." "Magani ne nake so ki bawa Asad ya sha ba tare da ya sani ba." Wara idanu tayi tana k'are masa kallo mai cike da harara da mamaki ganin hakan ya saka shi yin murmushi yace, "bazan cutar da Asad ba kin sani, tunda kika ga na kawo masa kin san naji wata magana ne da take shirin faruwa." Hannu ta d'aga masa tace, "Bana daga cikin wad'annan shirmen naku kai ka sani, baza kuma ka hani wani abu kace na bawa Asad ba tare da ya sani ba, baza ka had'a kai dani a cutar dashi ba." Ya matso kusa da ita yace, "ba cutar dashi zanyi ba Suhaima, ke kin san baza'a tab'a had'a kai dani a cutar da Asad ba because he's my favorite cousin and he's my friend, wannan maganin da zan baki in ya sha zai karya dukkan abinda za'a aiko masa dashi, u know rayuwar Asad tana cikin hatsari a yanzu, kowa neman ganin bayan sa yake ki taimaka ki karb'a ki taimaki Yayan ki." Suhaima tayi masa kallon up and down tace, "Kai meyasa baza ka bashi ba?, kamar kai ma ya amince da kai ko?." "Eh ya amince dashi, amma kin fini kusa dashi kece zakiyi ba tare da kowa yasan hakan ba, sharaɗin maganin ba'a so wanda zai sha yasan an zuba. help us please in wani abu ya same shi dukkan mu ya sama." Numfashi ta fesar tana kallon sa a kaikaice zuciyar ta cike da tunani kala-kala. "Please Suhaima" ya fad'a yana sake marairaicewa yana kallon ta. "Sorry I can't" tana fad'ar hakan ta juya ta bar wajan ya bita da kallo yana cize bakin sa ji yake kamar ya jawo ta ya shak'e mata wuya yayi k'wafa ya juya ya bar wajan zuciyar sa cike da k'unar rashin samun nasara. Direct apartment d'in su Asad Suhaima ta wuce tana zuwa ta tarar dashi a zaune shida Hafiz ta shiga da sallama ta kalle shi tace, "Yaya ka amince da Suhail or not?." Hafiz yace, "what happened?." "He called me yanzu yana fad'a min akwai maganin da zai bani na bawa Bro deaf yasha wai zai protecting d'in sa daga abinda za'a aiko masa dashi, ban amince dashi ba gaskiya." "U see na fad'awa Asad Suhail ba abin yadda bane amma always sai yace min shi ya amince dashi, yanzu kin karb'i maganin?." "No, I'm not." "Ki kira shi yanzu ki karb'a sai ki zubar dashi in ba haka ba tabbas zai bayar a zuba masa ne, daga yau ko me zai baki akan Asad ki karb'a." Asad yace, "kar ki karb'a." Da mamaki ta kalle shi tace, "Why?." Idanun sa ya zuba mata akan fuskar ta yace, "abinda nace kenan" yana fad'a ya tashi ya shiga d'aki ta bishi da kallo. Hafiz ya kalle ta yace, "ban san me yake damun Asad ba akan Suhail, ya kasa gane inda ya dosa har yanzu but muje mu sanar da Mama ita kad'ai ce zatayi maganin abin." Kai ta d'aga alamun haka ne suka fita a tare zuwa wajan Mama. Asad lokacin da ya shiga d'aki zagaye kawai yake yi a cikin d'akin gabad'aya ya rasa tunanin me zaiyi cikin kwanakin mugayen mafarkai yake da mutane kala-kala suna k'ok'arin cutar dashi, dalilin da ya sanya gabad'aya baya sha'awar yin sarautar ko kad'an amma Mama ta dage shi bai ga abin so a cikin ta ba. Kan gadon sa ya kallah a gyare yake tsaf dan Suhaima ce kad'ai take shiga d'akin sa ta gyara sai Mama bayan su wani dogari ko baiwa basa zuwa cikin d'akin dan umarnin Mama ne. Tunda ya kwanta jiya a kansa yake jin kansa yayi masa mugun nauyi ga wasu abu kamar allura da yake ji yana sukar sa gabad'aya kansa ya kulle ya ma rasa tunanin me zaiyi. Ji yayi gidan gabad'aya yayi masa zafi ya d'auki makullin mota ya fita daga d'akin. Washe gari. Bayan gari yayi haske sosai Hydar ya d'auki mota ya tafi asibitin da Rauda take ya nufi office d'in Dr da sallama, yana ganin sa ya mik'e tsaye yana fad'in, "Barka da zuwa prince." "Ya jikin ta?." "Da sauk'i, mun samo dangin ta ma suna wajan ta a yanzu." "Good a cigaba da kula da ita ayi mata komai, but bana so suna na ya fito a maganar ka samu wani sunan but banda nawa." "Okay Prince in sha Allah." "Let's go" tare suka fito suka shiga d'akin da take nan suka samu Mama da Baba da kuma Inna suna zaune a kusa da ita. Da sallama suka shiga suka amsa Hydar ya kalle su dukkan su kana ganin su kasan talakawa ne duk da duk wanda yake k'ark'arin masarauta talaka ne amma nasu talaucin ya fito yace, "Ya mai jikin?, nine wanda na buge." Ganin babban mutum mai kalama da kwarjini kamar Hydar sai Baba aka gyara tsayuwa aka ce, "Jiki gashi nan dai har yanzu bata farka ba, sai dai fatan Allah ya bata lafiya." Kusa da gadon nata Hydar ya k'arasa yana kallon ta ya kalle su yace, "zata ji sauk'i, Dr zai mata komai babu damuwa." "Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Umma ta fad'a tana kallon sa. Kai kawai ya d'aga baice komai ba ya fita daga d'akin daman burin sa a samo dangin ta. Gida ya koma ya shirya zai tafi aiki kasnacewar Friday ce, bayan ya gama ya shiga wajan Mama ta kalle shi tun kafin yayi magana tace, "Ina kaje d'azu?." Da girmamawa yace, "naje wajan wacce na buge ne." "Kaje kayi mata me? Ba ka bada komai Dr zai mata meye naka na zuwa inda take?." Shiru yayi Bai amsa mata ba tace, "Sunan ta Rauda iyayen ta talakawa ne suna zaune a unguwa Katsalle tana saida abinci a kasuwa meye naka da zaka dinga zuwa inda take?, wannan ba kalar wacce zaka je dubawa bace Hydar, zubar da kima ne a ganka a wajanta!, Tunda ka bar komai hannun Dr kar ka sake waiwayon ta kayi mata iya k'ok'arin ka." Kallon mahaifiyar tasa yake da zallar mamaki jin har ta binciko komai a kanta daga jiya zuwa yau kuma wai ya daina zuwa inda take tsakani da Allah ai babu adalci a cikin abinda tace shi kuma bazai iya ba, baice komai ba sai daga baya yace, "In kin min izini zan fita." Ta kalle shi da hannu tayi masa alama haka ya fice taja dogon tsaki tana fad'in, "meye nasa na damuwa akan wata banza y'ar talakawa oho?, har na tsani yarinyar" ta fad'a tana yarfe hannun ta tana tab'e bakin ta. *GRA.* Su biyu ne kacal a zaune a falon Sadiya da y'ar ta Jidda suna zaune suna tattaunawa kamar koda yaushe Jidda tace, "Mum u mean zan mallaki Asad matsayin miji na?." Sadiya ta murmusa tace, "of course Jidda, nan kusa bada jimawa ba zaki zama mallakin sa." "Wow!" ta furta tana juya idanun ta cikin jin dad'in abinda Mum d'in tace. Murmushi mahaifiyar tata tayi tana kallon ta tace, "Wannan kyauwu naki Jidda ai sai sarki, d'an sarki, jikin sarki ne zai d'auka." "But Mum kina ganin zaiamince?, kin san halin sa fa kamar ba mutum ba." "Babu abinda zai hana ya amince, yana jin maganar Maman sa fiye da tunanin ki, ko wuta ta nuna masa tace ya shiga zai iya shiga kuma ke kin san yadda take jin maganata ko ta iyayen ta bata ji, duk yadda zanyi sai nayi wajan ganin kin shiga cikin gidan nan matsayin matar sa. Wallahi zan iya k'arar da komai nawa wajan ganin hakan ya tabbata." Jidda bata ce komai ba Mum ta kuma cewa, "da sannu zan kwace duk wani jin kai da take ji dashi ya dawo hannun ki, da idanun ta zata kasa sarrafa d'an ta sai abinda muka ce shi zaiyi, tana muryar d'an ta zai zama sarki ne ni kuma ina murnar zaki mallaki sarki, zata kasance mahaifiya a gare shi zaki kasance mata a gare shi, duk wani sirrkan sa zai dawo tafin hannun mu daga nan Rabi'atu ta gama yawo." Murmushi Jidda tayi kyawun ta ya sake bayyana kana kallon ta kasan asalin iyayen ta ba hausawa bane tace, "Mum tana son Asad sosai fa, kina ganin zata bada wata dama kuwa?." "Nice damar ai Jidda sai abinda nace mata ke kin sani, duk wannan zafin kan da take ji dashi sai na sauke mata. Kin san wahalar da nasha kafin na mallake ta kuwa...? Na kashe kud'i ban san adadin su ba wallahi. Akwai tarin abubuwan da tayi min a baya na tabbata ita ta manta amma ni ban manta ba, kwantan b'auna kawai nake mata so nake ki mallaki Asad a nan zata gane wacec Sadiya." "Mum indai mallakar Asad ne lokaci ya kusa ai, ina so ma naje gidan na gaida ta." "Hakan yana da kyau Jidda, kije gobe ki wuni a can ki samu ku keb'e keda Asad duk da baya magana kiyi k'ok'arin ganin kunyi magana dashi." Shiru Jidda tayi Mum tace, "zan baki turare ki shafa a jikin ki duk wanda ya shak'i shi sai ya rikice Jidda." Dariya tayi tace, "da alama kin gama shirin ki Mum." "Murucin kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya, lamarin Rabi'atu ba abu bane mai sauk'i ta wuce inda kike tunani. Kar take kallon kowa kanta na mugun ja sai da dabara da wayo zaka gano lagwon ta." Bata ce komai ba ta cigaba da danna wayar ta amma zuciyar ta cike take da farin cikin zata zama mata ga Asad kyakykyawa, mai aji, mai nutsuwa, mai kud'i, mai ilimi kuma sarki d'an sarki. *◇◇◇* K'asa-k'asa take magana kai da kaji kasan duk abinda ake fad'a babu gaskiya a cikin sa tana fad'in, "ka tabbatar Suhail ya saka layar a k'asan kafitar sa?." Daga can b'angaren yace, "na tabbatar domin inda bai saka ba Suhail bazai min k'arya ba." "Amma kasan ni bana son long process nafi son ayi abu a gama kawai a wuce wajen." "Ki kwantar da hankalin ki zancen da nake miki ma mai martaba ya jinkirta bayar da kujerar zuwa nan da wani lokaci." "Kai kamar baka san halin sa ba?, kwantan b'auna zai mana lokaci d'aya sai dai mu wayi gari muji ana bugawa Asad tambari, nifa in ba gani nayi an kawar da Asad ba hankali na bazai kwanta ba." "Ki kwantar da hankalin ki in abun bai yu ba a wannan karon zamu nemi master planer......." "Master planer!? Wacece Master planer?" Ta fad'a da mamaki tana jiran amasa. Murmushi yayi mai sauti yace, "Zaki Santa in lokacin hakan yayi, ita take tsara komai kuma yake tafiya yadda ya kamata, in abu ya gagare ni ita nake nema, ta wuce duk tunanin ki ta dame ki ta shanye a hatsabibanci, ta wuce tunanin ki da hankalin ki, in kika ji shirin ta sai kin san naki ba komai bane ba." Hajiya tace, "wacece ita?, a ina take?, meye alaqar mu da ita...?." Waziri yayi murmushi yace, "kamar yadda na fad'a miki zaki santa in lokacin yazo amma banda yanzu, ki cigaba da zuba idanu tabbas a kwanakin nan za'a wayi gari ace azo a fitar da gawar Asad, ki rubuta ki ajjiye na tabbatar da wannan" yana gama fad'ar hakan ya yanke wayar ba tare da ya jira yaji me zata ce ba tabi wayar da kallo zuciyar ta na hasaso mata Master planer amma ta kasa gane wacece................. *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *007.* Bayan sallar juma'a aka samu kiran gaggawa daga mai martaba duka iyalan gidan hatta matan da suke gidan mazajen su sai da aka kira su aka taru a fadar cikin gida duk wani da ya kasan jini a gidan sai da aka kira shi. Dukkan su suna zaune ana sauraren abinda mai martaba zaice kowa yayi mamakin kiran. A kamalance da k'asaita da zallar nutsuwa da hikima ya fara fad'in, "kamar yarda na saka a kira ku nasan da yawan ku kuna tunanin lafiya akayi kiran gaggawa haka kasancewar bai tab'a faruwa ba. Ba wani abun bane an kira ku ne akan murabus da nace zanyi a d'ora Asad." Kallon kallo aka shiga yi dukka mutanen wajan gaban su na fad'uwa matuk'a burin kowa yaji k'arshen maganar. "Babu batun ta a yanzu mu janye, amma nan da wasu kwanaki maganar zata dawo matuk'ar ina raye kuma abinda nace baza'a canja shi ba, in kunga abinda na fad'a bai faru ba ku tabbatar k'asa ta rufe fuska ta." Shiru fadar take ko masu kirari babu kasancewar magana ce ta cikin gida su kad'ai babu damar magana kuma sai ya bada dama. Fuskokin mutanen dake wajan zaka kalla zaka hango zallan farin ciki akan abinda yace, fuskar Mama ce kawai a d'aure cikin akasin farin ciki amma bata ce komai ba. "Bana son na sake jin wata magana akan wannan na yiwa tufkar hanci, in lokaci yayi komai zai bayyana amma banda yanzu." Nan ma shiru suka kuma yi kafin yace, "Akwai wanda yake da magana a cikin kuz?." Shiru akayi babu wanda yace komai sai daga baya babar y'a kaf gidan mai Maimuna wacce taci sunan mahaifiyar mai martaba ake kiran ta da Mummy tace, "Allah yaja da zamanin mahaifin mu, Allah ya kare mahaifin mu a duk inda yake. Hukuncin mai martaba shine hukunci a ko wanne lokaci, babu mai magana a cikin mu." Kai ya girgiza kafin yace, "Kowa zai iya tafiya." Kai k'asa sukayi da kansu a tare dukkan su suka furta, "A tashi lafiya." Dukkan su suka fita kowa ya nufi b'angaren sa zuciyar kowa fari kar sab'anin Mama da take cikin mayuwacin hali. Tunda ta shiga b'angaren ta take zagaye hankalin ta a tashe ta matuk'a ta kasa zama sai kai kawo take, ta d'auki waya hannu na rawa ta kira Sadiya tana d'auka tace, "Sadiya akwai matsala babba." Daga can b'angaren tace, "Ranki ya dad'e me ya faru?." "Mai martaba ya janye batun murabus d'in sa haka kawai babu wani dalili." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Ranki ya dad'e munyi sake gaskiya, duk yadda akayi wani abun aka yiwa mai martaba kuma ya shiga jikin sa. In fulani zata tuna akwai wanda zasu shiga su fita wajan ganin an tarwatsa mana abinda muka saka a gaba." "Shiyasa nace miki ina buk'atar zuwa Kano, dole ne na shiga garin Kano a kwanakin nan, babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da mulkin Asad, babu shi ko waye" tana fad'a ta yanke wayar hannun ta na rawa ta kira Asad. Yana zaune yaga kiran ta daman yasan sai Mama ta neme shi ya d'auki wayar baiyi magana ba ya sauke daga kunnen sa ya tashi ya tafi b'angaren nata, can ciki ya shiga inda ya kasance babu mai shiga sai su yana shiga kafin ma yayi magana tace, "a tafiyar da kuka yi dashi me kuka tattauna har ya canja shawara lokaci guda?." Ya d'ago ido kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin hakan sai ranta ya sake ya b'aci tace, "bazan lamunci wannan shirun naka ba Asad! Ka fad'a min kaine kace masa baka ra'ayi?." Kai ya girgiza alamun a'a kafin yace, "wallahil azim Mama bamuyi magana irin wannan dashi ba, ki amince dani bazan yi k'arya dan na kare kaina ba" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'asa. remote ta d'auka tayi jifa dashi ya tarwatse a wajan tana wuci tace, "koma dai meye Asad baka isa kak'i karb'ar mulkin nan ba indai ina da rai, Asad kaine zaka mulki garin nan babu wanda ya isa ya shiga tsakanin ku da mulkin nan, dole ka cika min burin." tana fad'in hakan ta wuce zuwa d'akin ta tana fad'in, "A shirya min tafiya gobe zan wuce Kano." Kai ya girgiza sai da ta shiga ciki sannan ya juya ya fita zuciyar sa gabad'aya babu dad'i ko kad'an. A falon Hajiya iyalan ta zagaye suke da ita maza da mata y'ay'an ta kowa ka kalla zaka hango zallar farin ciki a tare dashi barin ma ita da take ta murmushi ita kad'ai alamun hak'ar ta ta cimma ruwa. Wayar ta da taji tana k'ara ya sakata ta mik'e ta shiga d'aki ta barsu a wajan ta amsa wayar tace, "Abu kamar wasa yana ta zama gaske, sai ga mai martaba da kansa ya janye batun nan." Waziri yace, "Na sha fad'a miki ki kwantar da hankalin ki komai fa a hannun mu yake amma duk sai ki bi damu kan ki." Murmushi tayi mai sauti tace, "yanzu meye abu na gaba?." "Master planer tace mu had'u dake waje d'aya zamu tattauna." "Yaushe zaka shigo to?." "Zan shigo zuwa dare." Murmushi tayi tace, "Allah ya kai mu" tana fad'ar hakan ta yanke wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane. *◇* Amaryar Sarki Hajiya Rukayya wacce ake kira da Ammi a gidan itama tana zaune da nata iyalan babban d'an ta namiji mai suna Nazif a shekaru bazai wuce shekara sha hud'u ba ya kalle ta yace, "Ammi ni na rasa ganewa kamar kina goyan bayan sarautar Asad?." Murmushi tayi ta kalle su dukkan su tace, "To meye nawa da zanki goyan baya Nazif? Kai dai a musulunce baka kai minzalin jan ragamar al'umma ba to meye abin tayar da jijiyoyin wuya akan hakan?." Babbar y'ar ta mace mai suna Zainab wacce ake kira Yaya Zainab tace, "kin huta Ammi, koma waye zai mulki garin nan mudai burin mu ya kasance alkahiri a gare mu da kuma garin." Wacce take bin ta tace, "Shine kawai fatan mu amma ni banga abin tayar da hankali a lamarin nan ba. Asad kuma kaf gidan nan babu mai kirkin sa kawai shi rashin maganar sa ce illa amma kowa yasan halin sa ga san y'an uwan sa baya lakari da yanayin gidan namu kowa na sa ne. Duk da Mama bata son yana sauraren mu amma shi ko a jikin sa, ga ilimi da kud'i a hannun sa." Ammi tace, "Allah ya kyauta" duk suka amsa da amin suka cigaba da hirar su gabad'aya maganar mulkin katagum bata gaban su su kam. Hydar da Aliyu da kuma Asad ne a zaune a b'angaren su babu wanda yake yiwa d'an uwan sa magana dukkan su waya ce a hannun su suna dannawa hankalin su a kwance, waya Hydar ya d'auka ya kira Dr ya sake tambayar sa jikin Rauda ya tabbatar masa da komai daidai. Asad ya dafe kansa da yake mugun ciwo yana yatsine fuskar sa. Hydar ya kalle shi yace, "Deaf ya dai?." Yatsine fuska yayi yace, "nothing" yana fad'a kawai ya tashi ya shiga d'akin sa ya kulle k'ofar ya zaga baya ya bud'e varanda yana kallon harabar gidan ana ta hidima da shige da fice. Allah ya sani baya k'aunar mulkin da ake son k'ak'aba masa ga jifa da yake sha tun daga fara maganar sarautar nan yake ganin mutane da yawa wanda baiyi tunani ba a mafarkin sa ina ga an bashi sarautar?. Burin sa kasancewa a madina ba'a Nigeria ba a can yake burin yin aiki kuma burin sa ya cika amma Mama ta hana. Lumshe idanun sa yayi mafarkin da yayi a jiya ya dawo masa kansa ya wara idanun sa yana k'ok'arin tuno fuskar yarinyar da ya gani ta taimake sa a mafarkin amma ya kasa, furzar da iska yake yi jikin sa na kyarma hankalin sa ya tashi ji yake gidan gabad'aya yana juya masa sam baya son zama a cikin sa, duk yadda yaso daurewa kasawa yayi ya fito ya d'auki makullin mota ya fita har lokacin Hydar da Ali suna zaune. Hydar ma fita yayi aka bar Aliyu a zaune yana ganin fitar su ya mik'e ya shiga d'akin Asad yana k'arewa d'akin kallo kamar yana neman wani abun a ciki. Babba ne d'akin sosai komai fari ne a d'akin hatta tiles d'in d'akin fari ne labulaye carpet komai fari ne a d'akin, fari kuma tass babu alamun daud'a a tare da ko ina sai khamshi da yake yi. tab'e

Chapter 6 of 24