Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dawo Nigeria ai yana magana a can fa in ba karatun alkur'ani ba to yana masallacin madina yana limanci." Murmushi yayi mai cike da izza kana yace, "Sai yanzu nake ganin ganganci da nayi wajan furtawa y'an uwana Asad zan barwa mulkin Katagum, tabbas nayi kuskure a wannan b'angaren dana bar abin a zuciyata sai dai aji na aiwatar hakan zaifi." Wambai yace, "Allah yaja da ranka abinda aka riga aka furta ya wuce, sai dai dole mu dage da taya Asad da addu'a dan wannan maganar da mai martaba ya furta wasu suna nan da ita suke kwana suke tashi burin su bai wuce su samu hanyar da zasu kawar dashi ba dan cikar burin su." Mai martaba yace, "Nasan da wanann, makusanta na sune suke wannan k'ok'arin na san da hakan. Amma in Allah ya amince babu abinda zai faru sai alkhairi. Dan ma Asad d'in ba baya bane wajan addini da yanzu sun haukata shi. Allah zai kiyaye." "Da izinin Allah." Daga haka suka canja hirar zuwa wata daban. A guje ta shiga cikin babban falon jikin ta na rawa sosai ta zube a gaban wata babbar mace mai ji da jiki mara haske sosai tana fad'in, "Allah ya ja zamanin uwar gidan mai martaba, Allah ya ja zamanin ki, Allah ya ja da ranki ya saka ki fi haka, Allah ya albarkace ki da iyalan ki. Ranki ya dad'e" ta fad'a tana mata jinjina hannun ta na k'asa. Kallon ta tayi daga inda take zaune tace, "Ramma lafiya?." "Ranki ya dad'e yarima mai jiran gado na gani........" "Duk sanda na sake jin kin kira shi da wannan suna sai na saka an k'ona bakin ki" ta dakatar da ita a fusace. "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake, nabi Allah na biki ki yafe ni." Tsaki ta ja sannan tace, "Ina jin ki." "Asad na gani a k'aramar fada shi da mai martaba sunyi ganawar sirri." "Ganawar sirri?" Ta fad'a tana mik'ewa zaune sosai tana kallon ta. "Na tabbatar ranki ya dad'e, domin daga shi sai wambai a ciki ko dogarai babu, kuma ya jima a ciki kafin ya fito." Jinjina kai take yi kafin ta mata alamu da hannu taje ta mik'e tana godiya ta fita. Tashi tayi tsam ta shiga cikin d'akin ta ta d'auki waya ta kira number Waziri. Duka biyu aka d'auki wayar yana d'auka tace, "Kana da masaniyar ganawar sirri da mai martaba yayi da Asad?." Daga can b'angaren yace, "Bani da masaniya, meya faru?. Waye ya kawo miki wannan labarin?." "Na tab'a kawo maka mara tushe ne?." "Baki tab'a ba." "Nifa kwata-kwata bana son mulki yaje hannun jinin Rabi'atu, tana yi mana kallo y'ay'an talakawa dan kawai ta kasance jinin sarauta, da zarar d'an ta ya zama sarki tabbas mun shiga uku zaman gidan nan sai ya gagare mu, dole nida kai mu san abin yi domin kuwa Asad ne kawai burin ta shima mai martabar shine burin sa ya zama dole muyi maganin sa." Dariya wanda ta kira da Waziri yayi yace, "Ina raye, ina numfashi, ina da wayo, ina ji, ina gani, ina da lafiya, wani bai isa ya mulki masarautar katagum ba face ni. Nine na dace kuma nine zan yi, babu wanda ya cancanta sama dani. Rabi'atun banza da wofi balle wasu y'ay'an ta?, ki bar ni dasu zaki ga yadda zan b'ullowa lamarin matuk'ar ina raye karagar nan tafi k'arfin ta!?." "Haka kake cewa koda yaushe amma ka kasa yin komai, da zafi-zafi ake dukan k'arfe amma kana barin sa yana wucewa, tun kafin mai martaba ya furta maganar murabus kake fad'ar haka yau gashi har ya riga ya furta ya kuma ambaci sunan Asad, da zarar an tabbatarwa da Asad mulki nida kai dole mu bi babu yadda zamuyi. A daina d'aukar lokaci in za'a yi kawai ayi bana son a dinga mayar da hannun agogo baya." Daga can b'angaren yace, "ki bani lokaci Asad bai isa yayi mulki ina da rai ba, yaron akwai tsari a jikin sa sosai dama kad'an nake so na samu nayi masa shigar sauri, zamu gani za kuma muji, kema kuma zaki gani" yana fad'a ya yanke wayar tabi wayar da kallo tana sauke numfashi zuciyar ta tana tafasa cike da bak'in ciki da b'acin rai. A shirye take da ta salwantar da duk abinda ta mallaka wajan ganin jinin Rabi'atu bai mulki katagum ba, zata iya salwantar da rai da lafiyar wani domin burin ta ya cika. *☆☆☆* K'aramin gida ne kana kallon sa kaga gidan talakawa wanda basu dashi yanayin sa da komai nasa ya nuna zallar talakawa ne suke rayuwa a cikin sa, ko a yanayin unguwar kasan ta masu k'aramin k'arfi ce amma tana da babbar hanya wanda mota zata zo har k'ofar gida. Daga cikin gidan tsakar gida ne mara girma duk turb'awa ko arzuki siminti babu sai d'akuna a tsakar gidan guda uku sai d'akin girki da kuma band'aki. "Rauda! Rauda!! Rauda!!" Gajeren Dattijo mai duhun fata da farar furfura ya ke fad'a yana shigowa gidan. Maimakon mutum d'aya ta fito kamar yadda yake fad'a sai mata uku suka lek'o, biyu daga d'aki d'aya guda d'aya kuma daga wani d'akin daban. A hankali ta tako ta k'araso inda yake ta durk'usa tace, "Baba gani." Kallon ta yake cikin harara yace, "uban me ya hana ki fita wajan waccan yaron mai mota da yake son ki?." Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa ganin hakan ya saka shi ya fusata yace, "ba magana nake miki ba?." D'ago idanu tayi ta kalle shi kafin tayi magana yace, "ke ba kyau ba amma ki dinga wulak'anta manyan mutane masu kud'i irin wad'an nan? Dan kin samu zasu d'auki irin ki....? a ka'ida a mai aikin gidan sa zaki je amma yayi miki adalci yana so ya d'auke ki matsayin mata kike ja masa aji, ina aji a wajan talaka..? Nace miki ina aji a wajan talaka...?." A hankali tace, "Baba kayi hak'uri." "To tashi kije ki ku tattauna bana son jan magana." Bata musa ba ta mik'e taja mayafin ta a kan igiyar shanyar da take tsakar gidan ta saka takalmi ta fita. D'akin da mata biyu suka lek'o ya kalla sai suka koma ya ja tsaki yace, "haka dai, ke munafuka y'ar ki ma munafuka." Rauda lokacin da ta fita ta tarar da wanda zuciyar ta ta bata tabbacin ganin sa a tsaye a jikin motar sa yana facing gidan su. Yana hango ta ya saki murmushi sab'anin ita da face d'in ta take a cushe ba walwala ko kad'an ta k'araso tace, "Ina wuni." Sai da yayi murmushi sannan yace, "lafiya lau Rauda, ya gida da mutanen gidan?." "Lafiya." "Kiyi hak'uri na saka Baba ya fito dake." Bata bashi amsa ba daman yasan hakan yayi murmushi yace, "Ina son ki Rauda, Ina burin ranar da zaki ce min kema kina sona" Bata ce komai ba ta kalle shi tace, "Sai anjima." Har zata juya yace, "minti d'aya Rauda." Cak ta tsaya ya zagaya mota ya d'auko leda k'arama ya dawo ya mik'a mata yace, "ga tsaraba babu yawa." Kallon ledar tayi ta kalle shi tace, "na gode" daga haka ta juya ta shiga gida ko waiwayen sa batayi ba. A kan idanun Baba komai ya faru tana shiga soron gidan ya yi mata dak'uwa yace, "uban me yasa baki karb'a ba?." Kamar zatayi kuka tace, "Umma ta hana ni." "Keda Umman ba nine a gaba da ku ba? Dallah malama koma ki karb'o, ka ganar min yarinya y'ar bak'in ciki." Idanun ta yayi rau-rau zatayi kuka tana kallon sa yace, "in baki koma ba sai na fyad'a ki da k'asa, ka jimin yarinya mai bak'in ciki, zaki koma ko sai na b'alla ki?." Juyawa tayi hawaye na zubo mata ta kalli inda motar take taga babu shi alamun ya tafi ta sauke numfashi ta juyo ta dawo ta kalli Baban tace, "Ya tafi." Harara ya banka mata ya ja tsaki yace, "a nonon uwar ki kika tsotsi bak'in ciki dan ni kam ba haka halina yake ba, na rantse da Allah duk ranar da kika sake aikata wannan kuskuren sai ranki ya b'aci. Banza mummanar banza da wofi, ke ba kyau sai tsinanan bak'in ciki da mugun hali. Duk wanda ya kwashe ki matsayin mata ya shiga uku." Shiru tayi kanta na k'asa yace, "wuce muje ki d'auki d'anwake ki tafi bakin kasuwa rana tana yi." Babu yadda ta iya haka ta shiga cikin gidan yana bayan ta ya wuce cikin madafar da kansa ya had'o mata kayan abincin ya fito dasu yace, "D'auki maza ki wuce kar lokaci ya k'ure, kuma wallahi kika dawo kika ce min baki siyar ba duk inda zaki nemo kud'i sai kin nemo kin kawo min, domin ke bak'in halin ki har akan kayan sana'a ta yake." Umman ta da ta fito daga d'aki tace, "Malam dan girman Allah ka daina d'orawa yaran nan tallah, yaran nan sun girma sun kai munzalin aure maimakon ka tura su makaranta sai ka dinga basu talla.....? Nace maka ni ka barni zan siyar maka a gida amma kak'i, gani kake kamar baza'a siya ba, tura yara talla kamar su Rauda ba komai zai jawo ba sai lalacewar rayuwar su." Da kallo yake binta har ta kai k'arshe yace, "to uwar iyayi ita y'ar uwar ki bata yi magana ba sai ke?, yaran nan dai nine na tsuguna na haifi kayana ba wani ya haifar min ba, kema da kike tutuyar y'ar kice nine nayi miki cikin ta ko? To ki saka min matsaya a lamarina da y'ay'ana na amince da tarbiyayyar dana yi musu, in ma bak'in ciki kike dan ina samun arzuki da talla sai dai ki mutu." Shiru tayi Rauda ta sunkuya ta d'auki kular da yake mai marik'i ce kuma bata da girma can ta kalli mahaifiyar ta ta da mahaifin ta tace, "Sai na dawo." "Allah ya kiyaye" Umma ta furta a sanyaye tana kallon ta ta fita daga gidan jikinta a sanyaye......... *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *002.* Bayan fitar Rauda Umma ta kalli Baba ta girgiza kai tace, "Dan Allah Malam ka daina d'orawa y'ay'an ka talla ka bar mu mu matan ka mu dinga siyar maka kome kake so a gida, tura yaran nan tallah babu abinda zai haifar sai d'a mara ido." "Kedai kiyi masa amma ni kam gwara a d'ora musu tallan, yadda za'ayi rububin siya a wajan su mu baza'a yi a wajan mu ba. sune y'an mata wani saurayin ko dan su kula shi ma ya siya a wajan su" wacce take fitowa daga d'aya d'akin ta fad'a tana kallon Umma. Baba yace, "bar ta Asabe ita ai baza ta tab'a ganewa ba shiyasa, indai akace an tab'a mata Rauda shikenan babu zaman lafiya, ko da yake tun lokacin yayyen Raudan ake fama da ita y'ar bak'in ciki ce bata so taga nayi arzuk'i." Murmushi Umma tayi ta kalle su cikin takaici tace, "Amma bakwa gudun wani abun ya faru dasu ta silar tallan da ake basu?, kun manta y'ay'a mata ne dukkan su sun kai munzalin aure?." Baba ya nuna ta da yatsa yace, "Kinga Binta bana son mugun fata a kan yarana, ina yi musu addu'a ba dare babu rana Allah zai kare min su duk inda suke, kar na sake jin kin furta wata magana mara dad'i a kan su in ba so kike ranki ha b'aci ba." Umma bata kuma cewa komai ba ta koma d'akin ta. Tana jiyo shi yana fad'in, "kuma wallahi kika cigaba da hure mata kunne akan yaron nan Anas da yake son ta take k'in sauraron sa ki kiyayi hukuncin da zan miki, ban tab'a ganin uwa y'ar bak'in ciki kamar ki ba. Ace y'ar ki ta samu mai kud'i amma ki dinga bari tana wulaƙanta shi....? ita ba y'ar kowa ba ba kuma jikar kowa ba, gata ita ba kyau ba balle ace shi ya gano ya nace amma ki dinga hure mata kunne." Tana jin sa tayi shiru ta zauna a kan ledar da take shinfid'e a d'akin tana girgiza kai. Lamarin sa kullum sake gaba yake duk da girman da yake cimma masa, indai akan kud'i ne ba sani ba sabo, ko meye zaiyi indai akace kud'i zance ya k'are, tun lokacin baya haka yake gashi shekaru har sunyi nisa halayyar sa tana nan. Malam Adam haifaffan garin azare ne mazaunin unguwar Katsalle, y'an uwan sa da kowa nasan y'an Azare ne a nan aka haife su a nan kuma suka tashi suke kuma zaune. Yana da mata guda biyu Asabe da Binta y'ay'a kuma yana da goma takwas mata biyu maza, Asabe tana da guda shida biyar mata namiji d'aya, Umma kuma uku mata d'aya namiji shine auta a gidan gabad'aya. Suna zaman lafiya babu laifi wata ran ka gansu kamar y'an uwa wata rana kuma da kaga yanayin su kasan kishiyoyin juna ne. An aurar da mata biyar uku suka rage a gidan, Rauda wacce ta kasance itace babba wanda suka rage a d'akin su sai k'anwar ta Ummulkhairi sai k'anin ta Khalil. D'aya d'akin kuma sa'ar Rauda mai suna Rahma sai k'anin ta Garzali. Talakawa ne gidan wani lokacin abincin da zasu ci gagarar su yake sai dai kowa ya san abinda zai ci shida y'ay'an sa, mai gidan Allah ya d'ora masa san abin duniya baya jin kunyar rok'o haka baya jin kunyar cewa a bashi, koda sirikan sa ne mazajen y'ay'an sa indai Allah ya had'a su koda a hanya ne da wahala su rabu bai tambayi wani abun ba duk da suma ba masu kud'i bane ba. Tun y'ay'an nasa mata suna nuna rashin jin dad'in hakan da yake yiwa mazajen su har suka gaji domin ba zai daina ba. Tunda su Rauda suka kammala secondary school suka sauke a islmaiyya ya ajjiye batun karatu daman dak'yar aka k'arasa shi, dak'yar da sid'in goshi da ya hana su cigaba da karatu yace bashi hali suka koma islmaiyya suna hadda shima dan kyauta ce wani d'an siyaya ya d'auki nayi. Shekarar farko aka kori Rahma ita kuma Rauda ta cigaba da yin haddar ta tana sake sanin littafan addini dan Allah ya bata kaifin basira. Bayan ta kammala hadda a cikin shekara d'aya ta dawo gida sosai ta samu ilimi ta k'aru ta kuma san abubuwa da yawa a fanin addini, burin ta ta zama y'ar jarida amma kuma Baba ya daqile wannan burin nata domin yace bashi da halin da zai kaita jami'a dole ta jinginar da burin ta badan taso ba. Daga nan ya fara dafa musu abinci yana d'ora musu talla su shiga kasuwa su siyar su kawo masa kud'in ya d'aga pillow ya ajjiye dan babu wanda zai ci kud'in koda abinci ne babu a gidan sai dai a hak'ura. Dangin sa babu wanda bai masa fad'a akan basu tallan nan da yake yi ba amma ya shafawa idanun sa toka yace shifa ya haife su baiga wanda zai dakatar dashi da neman kud'in sa ba dole aka hak'ura aka k'yale shi. Babban yayan Umma babban malami ne a garin kowa ya sanshi har shi sai da ya yiwa Baba magana a kai amma ya nuna shifa y'ay'an sane yana da iko dasu dole aka zuba masa idanu. Masifar son kud'in sa ya amince ya ajjiye kud'in kar ya ci kar iyalan sa su ci amma zai ajjiye yayi ta kallon kud'in yana jin dad'i a fad'ar sa yace kallon kud'in ma rahama ne, da kansa yake girka musu abinci suna shiga kasuwa suna siyarwa gudun ma kar matan nasa su b'ata masa rai akan hakan shiyasa yake zagewa ya hura wuta ya dafa. Rauda yarinya ce y'ar shekara ashirin da hud'u bata da wadaccen kyau haka baza'a ce mata mummuna ba ba laifi dai zata shiga kadaran kadahan, tana da farin jinin samari sabida ilimin addinin ta kowa abinda yake kwad'ayi kenan a tare da ita amma bata sauraron su burin ta karatun jarida ne amma mahaifin ta ya hana shiyasa bata kula su musamman masu kud'i Umman ta takan ce mata kar ta d'ora buri a zuciyar ta domin duniyar ta koma kwarya tabi kwarya. Rauda wayayyiya ce in suna hira da Umma baza kace babar ta bace hira suke sosai suyi shawara kamar yaya da k'anwar ta. Sam Rauda bata da duhun kai in taga abu bata sani ba zata tambayi wanda ya sani ya fad'a mata sabida gaba hakan ya saka take a waye in taci kwalliya ka ganta baza kace yar Malam Adamu bace ba. Tana da kirki da girmama na gaba amma fa bata da kunya in aka tab'a ta, bata bari ko waye yayi mata sai ta mayar musamman a tab'a mata iyaye bata jure wannan. Duk girman mutum in ya latsa ta bazata bar masa ba sai ta mayar a cewar in babba bai ja girman sa ba dan k'arami yabi ta kan girman nasa ba wani abun bane, Allah bai halicce ta da tsoro ba ko Baba ne yayi wani abun ba daidai ba zata same shi ta fad'a masa sai dai yayi mata fad'an ya gama tunda ta fad'a shinkenan, halitta d'aya take tsoro a duniya shine doki. Anas ya jima yana bibiyar Rauda amma bata sauraron sa bai gaji ba duk sati sai yazo k'ofar gidan su koda bai ganta ba zai gama zaman sa ya tafi sabida Allah ya d'ora masa k'aunar ta, nutsuwar ta da ilimin ta yana daga cikin abinda yake sake jawo hankalin sa zuwa gare ta, kowa yana kaf unguwar itace mai haddar alkur'ani sau da dama y'an matan unguwar wajan ta suke zuwa tayi musu k'ari abinda yake sake burge Anas kenan da ita. In Baba yana nan ne yake tilasta mata zuwa wajan sa kawai dai ya bata wani abun ya kwace ya ajjiye gobe ma in ya dawo ya sake turata shine burin sa kawai. *☆☆☆* Aliyu tunda ya bar cikin gidan sarauta ya nufi wani plat house mai kyau da ya tsaru da falayoyi da fitala masu kyaun gaske, yana zaune a falon yayi shiru yana aikin jan tsaki ba komai ne yake k'ona masa rai ba sai zancen mahaifiyar sa akan Asad, pillow da yake ajjiye a kan kujara ya d'auka ya cillar cikin fushi yana jan numfashi zuciyar sa na mugun tafasa sabida bala'in b'acin rai da bak'in ciki. Cize lips d'in sa yayi ya koma ya jingina da kujera yana jin d'aci yana tasowa daga cikin zuciyar sa har kan harshen sa yana jin sa. "meyasa komai sai Asad?, meyasa ni ba'a maganar zan yi sarauta sai shi?!" Ya fad'a da k'arfi yana d'aukar remote yayi jifa dashi ya daki bango ya tarwatse a wajan. "Ya dai prince lafiya?" Wani matashi wanda bazai wuce sa'an sa ba ya fad'a yana shigowa falon yana bin sa da kallo, bai magana ba sai sake runtse idanun sa da yayi matashin ya zauna a kujerar da take kallon sa ganin yanayin da yake ciki ya saka yace, "Prince yane?." Nan ma bai masa magana ba bai kuma d'ago ba ganin hakan sai ya ja bakin sa ya tsuke baice komai ba sai da ya ga dama sannan ya d'ago ya sauke numfashi yana kallon sa shima yana kallon sa. "Sarkin mu na gobe, kaine yarima mai jiran gado, masarautar katagum taka ce, kai sarki, mahaifin ka sarki, kakan ka sarki, mahaifin mahaifiyar ka sarki. Allah ya ja zamanin Aliyu gadanga k'usar yak'i, daga kan ka an gama sarauta, kaine zakayi ko basa so sai ka hau karagar mulkin katagum." Lumshe idanu yayi jin kirarin da yake masa bai san lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba ya kalle shi sai kuwa ya sunkuyar da kai yace, "Duk mai shirin bamu matsala akan hawa karagar mu zamuyi maganin sa ko waye, kar yarima ya damu muna tare dashi za kuma mu bashi goyan baya duk wahala duk dad'i, ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai Aliyu ya gaji katagum koda Za'a rasa rai." Jin hakan sai Aliyu ya bud'e bakin sa a hankali yace, "Asad." "Shi d'in wa? Ana zancen mutanen k'arfafa wa yake zancen rago Asad?, mulki naka ne sai dai Asad ya duk'a a gaban ka ya kwashi gaisuwa, shi waye da zamu duk'a masa?, wane mutum balle aljan?. Mulki na k'arfafa ne ba irin Asad ragwaye ba, mulki na madu dakakkiyar zuciya ne ba irin Asad maau rauni ba. Allah ya ja zamanin yarima bai kamata Asad ya dinga damun ka ba domin ta ko ina kaine a sama bashi ba, waye zai d'auki mulki ya bawa kurma...?" wanda yake amsa sunan Hashim yake fad'a yana kallon sa cikin girmama irin wacce ake yiwa sarakai. Murmushin jin dad'i Aliyu yake yi duk duniya babu abinda yake k'auna sama da hawa karagar mulkin gidan su, babu abinda yake so sama yaga manya da yara suna duk'awa suna gaishe shi duk tsufan su haka duk yarintar su, yana so yaji ana buga masa tambari ana buga masa bindiga ana bud'e masa lema ana binsa a guje ana yi masa fifita. Asad yana neman zama cikas a cikin lamarin sa, burin sa da yake mafarki kullum Asad yana k'ok'arin ganin ya tafi a banza ba tare da ya tabbata basketball, sake kallon Hashim yayi har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya d'auki wani pack a gefen sa ya bud'e ya d'auki kwayar da take bugar dashi yasha ya kora da ruwa yana sauke ajiyar zuciya. Murmushi Hashim yayi ya mik'e ya fita dan yasan ba kasafai yake son magana ba shi kuma ya lumshe idanun sa zuciyar sa na kawo masa abubuwan da ya kamata yayi a kan Asad. *ASAD.* A zaune yake a k'aramin falo ya hard'e yatsun sa waje d'aya yana kallon wani wajan daban idanun sa a kulle kamar mai tunani, wanda yake zaune kusa dashi kallon sa kawai yake yi kafin yace, "Asad hak'uri zaka yi fa babu yadda zakayi." Numfashi ya sauke ya buɗe idanun sa ya kalle shi kamar zai magana sai ya fasa ya koma ya jingina da kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa. "Kai kad'ai ne ka dace da sarautar garin nan ka fi kowa ilimi da girmama talakawa, kai kad'ai ne kaf gidan nan baka yiwa bawa tsawa sai dai murmushi koda bakayi magana ba, kai kad'ai ne zaka cigaba da gunadar da mulki kamar mai martaba, matuk'ar sarautar nan ta bar hannun ka sarautar garin ta lalace gabad'aya" wanda yake zaune kusa dashi ya fad'a yana kallon sa. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe ya kalle shi a hankali ya furta, "ni kuma bana so, why sai ni?." Jin yadda yayi maganar ya saka Suhail yayi murmushi yace, "kamar ba yanzu na gama fad'a maka qualities d'in ka ba?, bazan b'oye maka ba ko mahaifi na da yake k'ani a wajan mai martaba matuk'ar ya karb'i sarautar nan sai ya lalata komai, domin kansu kawai suke hange ba talakawan su ba, kaine ka dace dole ka hak'ura." Jijiyoyin kansa ya dafe yana murza wajan a hankali zuciyar sa na kawo masa abubuwa da yawa. _Meyasa ma suke zancen shine zaiyi sarki bayan mahaifin sa na raye kuma yana kan mulkin?._ ya tambaya a zuciyar sa yana so ya furta a bakin sa amma baya tunanin zai iya hakan ya saka shi ya sake yin ajiyar zuciya baice komai ba. Mik'ewa Suhail yayi ya k'arasa wajan fridge ya d'auko fresh milk ya had'o da glass cup ya dawo kusa dashi ya zuba masa madarar ya mik'a masa yace, "karb'i ka sha zaka ji dad'i a zuciyar ka." Bai motsa ba kuma bai karb'a ba

Chapter 2 of 24