mahaifin ki akan kud'i ba sai bayan na baki magani dan da nasan haka yake wallahi bazan bayar ba. sai an biya ni in ba haka ba nakai k'ara wajan y'an sanda suzo su karb'ar min ta dole." Mik'ewa tsaye tayi Khalil ya bata sandar ta ta kalle shi tace, "Za'a biya ka kud'in ka in Allah ya yarda, kar ka sake kuma ka sake zagin iyaye na in ba haka ba zan nuna maka bani da mutunci nima."
"Ai nasan ki waye bai san sanfurin rashin mutuncin ki ba?, duk zafin kan ki na fiki wallahi dan na dame ki na shanye tuni. Kud'i ne dole a biya; ki daina in Allah ya yarda ai dole ne ma ki biya ni in ba haka ba kuka ga hauka keda iyayen naki." Banza tayi masa ta kalli Khalil zuciyar ta nayi mata ciwo tace, "muje Khalil."
Ba musu yayi gaba tana jin sa yana ta yi mata ihu bata juya ba tana tafiya bata kallon gaban ta bata san tazo kan titi ba sai horn d'in mota taji mai k'arfi hakan ya saka ta tsayawa cak ta runtse idsnun ta. Motar ta tab'a ta hakan ya saka ta fad'uwa sandinan suka zube katin maganin da yake hannun ta shima ya fad'i. Da sauri Khalil yazo wajan ta yana k'ok'arin d'aga ta yace, "Sannu Anty baki ji ciwo ba?."
K'ok'arin mik'ewa take taji kwarjini ya mamaye wajan lokaci guda, sanyin khamshi da zazzafan izza da k'asaita ta bayyana a wanan mai d'auke tsantsar nutsuwa da kamewa. Tsayuwar mutum da inuwar sa take ji a kanta hakan ya saka ta d'ago kai ta kalle shi idanun su suka had'u dana juya ta wara idanu tana k'are masa kallo shima kallon idanun ta yake dan iya shi kawai yake gani ta rufe sauran da face mask.
Saurin janye idanun ta taji jin wani abu kamr shocking da kwarjini yana ratsa cikin jijiyoyin idanun ta, jikin ta yayi sanyi lokaci guda taji baza ta tab'a iya jure cigaba da kallon sa ba ta dole ta janye idanun ta. A b'angaren sa shima hakan take zagayayyun idanun ta da ya kalla na wasu mintina sun masa kama da wanda ya sani amma kansa ya kasa tuna a inda ya san su hakan ya sama shi zuba mata ido yana so ya tuna.
"Kai dan Allah shine ka buge min Antyna bayan wani ya kad'e ta ta karye ya daina zuwa ya duba ta ta koma wayo da sanda, yanzu ma fa wajan mai magani muka je dan bamu dankud'i shine har da zagin Baban mu yace bazai bada maganin ba" Khalil ya fad'a kamar zaiyi kuka yana kallon Asad da yake tsaye a kanta har lokacin.
K'okarin mik'ewa take yi Khalil yana so ya rik'e ta amma ta kasa Asad da ya gama sauraron abinda Khalil yace ya dawo da kallon sa gare ta yaga tana kiciniyar tashi amma ta kasa, a hankali ya tsuguna a gaban ta khamshin turaren sa ya sake kawo mata ziyara cikin hancin ta ta runtse idanu gaban ta na fad'uwa ya kama kafad'un ta duka biyun ya mik'ar da ita tsaye, Khalil ya bata sandinan ta ta tsaya cak har lokacin kala baice ba.
"Na d'auka iya mugunta da rashin sanin darajar d'an adam ka sani ashe ka iya taimako....?. A waccan ranar ka mare ni na k'yale ban tanka ba sabida akwai abinda nake jin tsoro a gidan bawai dan ina jin tsoron ka ba. Kana da kud'i ko mulki duka basa gabana indai mutum ya tab'a ni nima sai na tab'a shi dan bai fini daraja ba, mutum shi nima mutum ce. Sa'ar ka guda ni nasan darajar d'an adam da babu abinda zai hana na wanke maka taka fuskar da mari kamar yadda ka mari tawa, banbanci na dakai kenan na fika tarbiyya da sanin ya kamata, amma koda nan gaba kasan irin matan da zaka dinga wulak'antawa domin ni da kake gani na nafi k'arfi suya sai dai babbaka" ta k'arasa fad'a tana kallon gefe domin bazata iya jure kallon saba shima yana kallon ta cike da mamakin kalaman ta.
Baki yake so ya bud'e yayi magana amma ya kasa cewa komai sai kallon ta kawai da yake yi tana zazzaga masa rashin kunya yana jin ta yana kuma kallon ta, sai da ta kai aya sannan ya kalli Khalil yace, "a ina kuke?" Ya fad'a cikin muryar sa mai taushi da ratsa zuciya. Gabanta taji ya fad'i jin kamar ba waccan muryar bace.
Muryar Khalil taji yace, "A unguwar Katsalle muke." Kallon ta yayi sai ya kalli Khalil yace, "Muje."
"Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni Rauda na shiga motar wanda bai san darajar d'an adam ba sai kansa kawai ya sani Allah ya kiyaye ni. kaje can ka k'arata kai kad'ai tunda ku y'ay'an manya da y'ay'an masu mulki baku san kowa ba sai y'an uwan ku masu mulki. Dan kana d'an sarkin garin nan baka isa ka saka ni nayi abinda banyi niya ba, bada hak'uri ya gagare ka akan buge ni d'in da kayi a yanzu me zai kaini shiga motar ka?" Rauda ta fad'a cikin masifa lokacin hijjabin ta yake ja baya har tabon sallar dake goshin ta ya bayyana.
A wannan lokacin suka tsallaka bai juya ya kalle ta ba bai kuma bar wajan ba amma kalaman ta sun tabbatar masa ta tab'a had'uwa da Aliyu ne yadda ta zayyano abinda ya faru yasan tabbas Aliyu ta gani take tunanin shine, katin maganin ya gani a k'asa ya d'auka yana kalla kafin ya juya sai yaga har sun b'ace masa, numfashi ya sauke ya shiga mota zuciyar sa na bugawa, kallo inda suka bi yake yi zuciyar sa na fizgar sa zuwa wani tunani daban ya runtse ido ya kunna motar ya buɗe idon sa ya ja ya bar wajan.
*tofa fan's an gamu fa.*🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*013.*
Rai a b'ace Rauda ta shiga gida Khalil ya taimaka mata ta ajjiye sandar hannun ta ta zauna a kan farar kujerar da take tsakar gida shi kuma ya zauna a k'asa. Yanayin ta Umma ta kalla tasan an tab'o ta kuma tasan bazai wuce akan maganin ba hakan ya saka tace, "ko baki ce ba nasan ya hana ki maganin ne shiyasa kike kunbura fuska, sai kiyi hak'uri." Rauda tace, "daga neman taimako Umma sai ya zage ni? Har yana cewa da yasan halin Baba tun farko bazai bada bashi ba."
Umma ta murmusa tace, "ban ga laifin sa ba Rauda; yanzu kafin wannan kud'ad'e masu tarin yawa su fito daga hannun baban ki a shekara goma a fama. Yayi k'ok'ari fa da ya baki ma dan ba kowa ne zai bada magani mai tsada kamar naki ba, Allah yasa baki masa rashin kunya ba dan ya taimaka miki." Shiru tayi bata amsa ba Baba da yaji komai ya shigo yana fad'in,
"In ma tayi masa rashin kunyar ita ta jiyo ai ita k'afar zata damu da ciwo sabida rashin magani bani ba." Shiru sukayi dukkan su kafin Khalil yace, "Umma wani kyakykyawa kamar balarabe ya kusa kad'e Anty yanzu har sai da ta fad'i k'asa." Umma tace, "Kuma dai?."
"Amma ai bata ji ciwo ba ai. Umma ta yi masa rashin kunya yace muzo ya kawo mu gida tak'i kuma baki ga motar ba babba" ya fad'a yana fad'ad'a hannayen sa alamun girma.
Baba da yake alwala a durk'ushe furzar da ruwan bakin sa yace, "A koda yaushe ke ai bak'in halin ki yake ja miki alkhairi yake tsallake ki ya koma kan wanin ki. inda kin shiga motar da bai siya miki maganin ba." Umma tace, "Rauda akan me zaki masa rashin kunya? Meyasa ke baka jin kunyar yiwa babba rashin kunya ne?." Rauda tace, "Umma nifa ba rashin kunya nayi masa ba na fad'a masa abinda yake raina ne. shine wanda nace miki ya mare ni lokacin da na raka su Habiba gidan sarki shine na amayar masa da abinda yake zuciya ta a lokacin ban samu dama ba ina jin tsoron doki ya hana ni mayar masa."
Umma ta wara idanu tace, "D'an sarkin Katagum guda masu ji da kud'i da mulki kika yiwa rashin kunya Rauda?, Yaron da an masa shaida bashi da kirki ina ke ina shi?, in ya saka aka yi miki wani abun fa?." Rauda ta turo baki gaba tace, "To Umma dan yana d'an sarki sai yayi min abinda yaga dama na k'yale shi? Bafa haifata yayi ba da zai fad'a min magana na tsaya ina kallon sa, wallahi saina rama dan mutum ne shi nima mutum ce."
"Sannu y'ar gidan dangote, nace sannu y'ar gidan shugaban masu kud'in duniya. Wato in ana neman talaka mai fad'in rai wanda aka fad'a a hadisi aka same ki Rauda an shafa Fatiha. Tunda bake ban tab'a ganin yarinya mai karanbani da nuna isa kamar y'ar wani ko y'ar wata sai ke da kanki yake rawa. D'an sarki guda kika yiwa rashin kunya, bakya jin tsoron wani abun ya same ki ke ga fitsararriya mai ji da fitsara. Har yace miki kizo ki shiga mota ya kawo ki kika ki sabida girman kai yayi miki yawa. To Allah ya isa abinda yayi niyar baki in ya kawo ki kika yi mana bak'in ciki da yau nasan kaji zamu ci mu kwanta, sakamakon rashin kunya duk abinda ya saka aka yi miki ke kika ja kar sunan Adamu ya fito a gaban sunan ki" Baba ya fad'a yana buge rigar sa ya fita.
Umma ta girgiza kai tace, "Wai Allah ya isa, Malam har ya saka a ran sa ma za'a bashi wani abun bama illar shiga motar tasa yake hangowa ba kawai a bashi kud'i koma me yayi miki in kin shiga motar ke kika jiyo. Kai Allah ya kyauta" Umma ta fad'a tana murmushin takaici kafin ta kalli Rauda tace, "Kinga Rauda na raba ki da y'ay'an masu kud'in nan babu ruwan ki dasu in ba so kike ki jawo mana matsala muna zaune lafiya ba. Ina ke ina yi masa rashin kunya? In yaso a batar dake yana da damar yin hakan babu wanda yasan shine yayi, ki dawo hankalin ki dan Allah bana son wannan fitsarar taki." Rauda bata ce komai ba tayi shiru k'afar ta na ciwo rashin shan maganin da batayi ba.
*☆☆☆*
Tun a mota yake tunani har ya isa guest house d'in mai martaba ya shiga kamar yadda ya saba shi kad'ai ya zauna a akan kujera yana sauke ajiyar zuciya. kallon katin yake yana kallon sunan ta kamar a jikin sunan yana so ya gano wani abun. _Sa'ar ka guda nasan darajar d'an adam da babu abinda zai hana ban wanke maka taka fuskar da mari kamar yadda ka mari tawa._ kalaman ta suka fad'o masa a rai ya runtse ido jin abinda bai tab'a ji ba yana kawo barazana ga kunnen sa.
"Ta tab'a had'uwa da Aliyu" ya furta a hankali idanun sa har lokacin a kulle zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri. "Wacece ita?" Ya tambayi kansa yana dafe kansa da duka hannayen sa idanun ta da goshin ta na sake dawowa masa cikin kansa da idanun sa a hankali.
Sake kallon katin yake maganar Khalil na sake dawo masa zuciyar sa ya kai idanun sa sunan asibitin da aka rubuta mata maganin. Mik'ewa zaune yayi sosai mamaki ya kama shi ya wara idanun sa ganin sunan asibitin su ne ya tafi k'aramin tunani kafin ya d'auko waya daga aljihun sa da azama.
Sai da ya danna number Dr Yasir ta shiga sai kuma yaji haushi ma akan me ma ya saka shi ya kira Dr, "Assalamu Alaikum, Ranka ya dad'e" muryar Dr ta katse tunani ya kalli wayar kamar bazai yi magana ba sai yace, "ehemmm Hydar" sai kuma yayi shiru jin hakan Dr yace, "Jikin sa ana samun ci gaba saura kiris ma ya farfad'o domin ana samun cigaba fiye da baya."
"About yarinyar da ya buge fa?." Gaban Dr ya Fad'i jin abinda yace yayi shiru Asad yace, "tana ina?."
Dr yace, "Prince Mama ta saka an sallame ta tun kwanakin baya." Asad yayi shiru cike da mamaki yasan tsaf Mama zata aikata abinda yafi haka ma hakan ya saka shi yin shirun kafin yace, "meye sunan ta?." A sama Dr yaji maganar hakan ya saka shi yin shiru kafin yace, "na manta ne prince abubuwan da yawa marasa lafiyar da yawa babu lallai na rik'e." Shiru dukka sukayi kafin Dr yace, "Na tuna, sunan ta Rauda sunan mahaifin ne dai na manta."
Asad baice komai ba ya yanke wayar ya sake kallon katin yaga sunan da ya fad'a masa ya ajjiye katin a gefe yana kallo, _Mama meyasa?, ga yarinya yanzu a cikin yanayi mara dad'i, babu kud'in magani gashi har tana yawo da sanda a silar Hydar._ ya fad'a a zuciyar sa yana sauke numfashi shi jikin sa duka babu dad'i.
Kiran magrib ya tashe shi yayi alwala ya fita masallacin estate d'in yayi sallah sannan ya dawo ya d'auki motar sa zuwa gida. Wajan Mama ya wuce kai tsaye bai same ta a falo ba ya shiga d'akin da Hydar yake a nan ya ganta a zaune kusa dashi kamar koda yaushe. Da sallama ya shiga ta kalle shi ta d'auke kai ya tsaya a kan Hydar yana kallon sa. Har zai mata magana sai kuma ya fasa ya d'auke kansa itama kuma bata ce masa komai ba. Ganin bata kallon sa ya saka yace, "Mama ko meyasa aka sallami yarinyar da Hydar ya buge daga asibiti?" Ya fad'a a tausahe kamar ko yaushe. Kallon sa tayi ta harde hannun ta a k'irji tana kallon sa alamun bazata yi magana ba kenan.
"Na saka an sallame ta d'in sabida bata dace da zaman wannan asibitin ba akwai abinda za'a yi min ne?. kuma ahir naji kaje wajan ta da niyar wani abun, shima Hydar nice na dakatar dashi kar ka jawo abinda raina zai b'aci a kanta iya abinda aka yi mata a asibiti ya ishe ta" ta fad'a a kausashe tana kallon sa. Ajiyar zuciya yayi yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ban fad'a dan ranki ya b'aci ba." Kai ta kawar gefe tayi masa alama da ya bata waje ya kuwa fita kamar yadda tace.
Masallaci ya fara wucewa yayi sallah kafin ya nufi d'akin sa jikin sa duk babu dad'i, zuciyar sa na bugawa sosai yana jin bak'on abu yana zaga jikin sa kamar yadda jini yake zaga jijiyoyin jikin sa. Yana tsallaka k'ofar d'akin yaji kansa yayi mugun sarawa ya tsaya cak yana bin wajan da kallo amma baiga komai ba ya runtse idanun sa.
"Lafiya?" Aliyu ya fad'a daga bayan sa ganin yanayin sa duk ya canja. K'arasowa Aliyu yayi yana kallon sa yace, "baka da lafiya?." Asad ya cize bakin sa ya kalle shi yace, "Kaina" abinda yace kenan ya shiga ciki shima yabi bayan sa.
Suhail da yake lab'e a bayan babban gate d'in da ya raba apartment d'in su da gidan ya fito yana murmushi ya bar wajan da sauri ya fiddo waya daga aljinun sa ya danna kira ana d'auka yace, "An zuba masa kuma tabbas ya taka yanayin sa ma ya canja." Waziri yace, "Good boy." Daga haka ya yanke wayar yayi saurin barin gidan gabad'aya.
Shigar Asad falo keda wuya kansa yayi mugun nauyi ya rasa me yake masa dad'i bai san lokacin da yayi saurin dafa bango ba yana furta, "Ya salam!." Ganin hakan ya saka Aliyu ya rik'o hannun sa yace, "you're not okay deaf, zauna" ya fad'a yana jan sa kan kujera ya zaunar dashi yana juya kansa. Yadda kansa yake mugun ciwo da sarawa fita yayi daga hankalin sa idanun sa suka firfito waje ya saka hannayen sa biyu ya dafe kansa yana ji kamar ana saka guduma ana dukan kansa.
Aliyu ganin abin yayi yawa sai hankalin sa ya tashi ya zauna kusa dashi ya rik'e kan nasa jin yadda jijiyoyin kan nasa suke bugawa a guje sune ya sake tayar da hankalin sa yace, "oh my God wannan wanne irin ciwo ne?." Da sauri ya lalubo waya ya kira Dr Yasir amma bai same shi ba ya tashi tsaye ya kira number Mama ya sanar da ita halin da ake ciki.
A gigice Mama ta tawo apartment d'in nasu gab da zata shiga Hafiz ya tsaya a gaban ta yace,"Mama kar ki wuce nan wajan." Hararar sa tayi kafin tace wani abu yace, "Wani abu aka zuba masa ya wuce ta wajan, kalli kiga" ya fad'a yana nuna mata wani bak'in ruwa a wajan ga garin magani a cikin sa har yellow yake yi.
Kallon wajan take gaban ta na fad'uwa da sauri ta k'arasa ta kunna hasken wayar ta ta sake haska wajan ta kalli Hafiz tace, "Waye ya shigo nan b'angaren?." Hafiz yace, "ban sani ba Mama."
"Kuna ina! Kuzo nan" ta fad'a cikin d'aga murya sosai masu tsaron wajan suka k'araso a guje suka zube kafin suyi magana tace, "Kafin Asad ya shigo wajan nan waye ya shigo?." Jikin d'aya yana rawa yace, "Ranki ya dad'e Suhail ne ya shigo."
"Suhail again" ta fad'a tana dafe kanta kafin ta juya da sauri ta nufi falon Asad d'in, bata sake bi ta kan maganin dake wajan ba ta tsallaka ta shiga ta same shi a zaune hannu sa duka biyu a kan sa jikin na rawa sosai. Da sauri ta k'araso ta rik'e shi ta d'ora hannun ta a akan sa tace, "Aliyu kayi wani abun please." Aliyu yace, "Mama na kira Dr yana hanyar zuwa yanzu."
"Sannu Asad" ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon sa.
Ya canja lokaci d'aya jijiyoyin kansa sun fito radau jikin sa na rawa sai juya kai yake alamun yana cikin azabar ciwo, hankalin Mama ya sake tashi ganin numfashin sa yana k'ok'arin tsayawa ta kalli Aliyu da yake a tsaye hannun sa rik'e da waya shima duk ya rud'e. Shigowar Dr Yasir ya saka Mama kallon sa tana fad'in, "yi sauri kazo ka duba shi." A guje ya k'araso ya tab'a kan Asad jin yadda yake bugawa sai da ya d'auke hannun sa da sauri.
Hannun sa har rawa yake ya saka masa ruwa ya kuma yi masa allura ya fara auna bp sa, abinda ya bashi mamaki komai normal yake dan yadda yaji kansa yana bugawa ya d'auka ko jinin sane yayi k'asa hakan ya saka ya kalli Mama itama shi take kallo duk rauni ya bayyana a tare da ita kamar zatayi kuka. Hannu Asad ya saka ya cire ruwan da yake shiga jijiyoyin sa sabida ji yake kamar azaba tana shiga cikin jikin sa. "A'a Asad ya zaka cire?" Mama ta fad'a tana kallon sa hankali a tashe.
Juya kan nasa yake yi cikin tsawa Mama tace, "Dr kana ganin abinda yake yi ka tsaya kana kallon sa!?." A firgice ya kalle ta yace, "Ranki ya dad'e na rasa gane kan matsalar, bara nayi masa allurar bacci" ya fad'a da gaggawa yana yi masa allurar bacci amma ko gezau baiyi ba.
Aliyu yace, "Dr muje asibiti kamar zai fi." Hafiz yace, "No prince zaman sa a nan yafi safe, dan Allah Yasir kayi iya k'ok'arin ka a samu yayi bacci." Gabad'aya sun rud'a Dr ya rasa ma abinda zaiyi yayi masa allurar bacci baya son sake yi masa wata dan tabbas zai zama cikin risk domin abubuwan zasu yi masa yawa a blood d'in sa. "Prince in aka sake masa another injection abubuwan zasu yi masa yawa" ya fad'a yana kallon Aliyu.
"Kayi masa mana, ko meye kayi masa abinda zai bar wannan condition d'in!" Mama ta fad'a a fusace tana kallon sa dan hankalin ta a tashe yake, bai san sanda ya balle kan allurar ya ja a sirinji ya dannawa Asad a jijiyoyin jikin sa. Lumshe idanu Asad ya fara yi har lokacin yana rik'e da kansa idanun sun k'i rufewa yadda ake so.
Abin mamaki da al'ajabi Dr ya tsaya yana kallon ganin har lokacin bacci bai d'auke sa ba sai kansa ya kulle ya rasa abinda zai bashi kuma nan gaba. Domin allurar da yayi masa bata second biyar a jikin mutun bata saka shi bacci ba. Hafiz da yake tsaye ya lura da yanayin Dr hakan ya saka ya k'arasa wajan fridge da sauri ya d'auko ruwa ya bawa Mama yace, "Mama ki masa tofi ya sha zai fi samun sauk'i." Ba musu ta karb'a ta fara tofa masa duk ayar da tazo bakin ta kafin ta bashi yasha ta shafa masa ragowar a fuskar sa. Komawa gefe Dr yayi yana kallon ikon Allah har lokacin bacci bai d'auke Asad ba kuma kansa bai daina ciwo ba.
"Hafiz kama shi mu kai shi d'aki ya kwanta" Aliyu ya fad'a yana kallon Hafiz. Tare suka d'aga shi aka kai shi kan gado ya kwanta har lokacin hannun sa na dafe da kansa idanun sa kuma a bud'e. Mama na zaune a gefen sa hannun ta guda d'aya ta rik'e nasa tana tofa masa addu'a a hankali, sun kwashe sama da mintina arba'in a wajan kafin bacci ya d'auke shi.
Ajiyar zuciya Mama tayi ganin yayi bacci ta kalle su da suke tsaye har lokacin bata ce komai ba ta mik'e aka ja masa k'ofar aka fita ta kalli Dr hakan ya saka shi yace, "Ga magani na koma na d'auko masa in ya farka sai ya sha. Nayi mamakin ciwon nan nasa ban tab'a karo da ciwon kai irin wannan ba gaskiya" ya fad'a yana ajjiye maganin akan table.
Bata ce komai ba ta fita da sauri ta dinga kiran masu tsaron wajan suka k'araso a guje suka zube ta kalle su tace, "Daga yau ban amince a sake barin kowa ya shigo wajan nan ba, ko waye ko wace ban amince ba in kuma aka sab'a abinda na fad'a....." Bata k'arasa ba ta girgiza yatsan ta guda kafin ta bar wajan da sauri.
Tana shiga b'angaren ta d'akin da Hydar yake ta shiga yana kwance inda yake ta fita ta koma d'akin ta. Waya ta d'auka hannu na rawa ta zauna jikin ta duk yayi sanyi ta nemi number mahaifin ta ta kira shi. yanke kiran aka yi hakan ya bata tabbacin zai kira ta kenan bata ajjiye wayar ba kuwa kiran ya shigo, da sallama ta d'auka muryar ta na rawa sosai kafin tace, "Barka da dare Abbie." Jin maganar ta a haka ya saka yace, "Ban saba jin rauni a muryar Rabi'atu ba, me ya haifar da hakan?."
Kuka ta fara yi mara sauti kafin tace, "Abie suna neman su kashe min Hydar da Asad. Hydar na kwance har yanzu baya motsawa ga Asad can yanzu na baro wajan sa kansa na ciwo dak'yar aka samu yayi bacci. Ban san me suke nema a wajan su ba so suke suga bayan su."
Abie ya murmusa yace, "Babban kuskuren mijin ki da ya furta zai sauka daga kan kujerar sa ya bawa Asad wannan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 24