Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tace'ina ruwana karki ci Mana in baki ci ba in cikin ya zube kin huta"ai fara ci tayi tace"ummi ina ci cikin bazai zube bako?" Kallon Rahma tayi domin harga Allah ta tausayawa Rahma tace"ke Kuma in baki ci ba in ya dawo zansa ya maidaki gida in aura me wata ai kinsan Yana jin maganata " Rahma ta fara dire dire tana bata hakuri duk inda ummi taso taci abinci dayawa kadan taci tana Gamawa ta koma dogon kujera ta kwanta Yusura ta mike da d'an cikinta da ya fara fitowa ta koma d'aki Bacci Rahma beyi minti goma ba sai ta fara mafalki Mikewa tayi a razane da kalmar inalillahir wa Ina ilahihi raji'un, addu'oi takeyi sosai Ummi tace"lafiya?" Mikewa tayi ta ruga a guje ta shige d'aki ta rufe toilet taje ta d'auro alwala ta dawo ta shimfid'e sallaya ta tada sallah nafila Ummi yau da fadiwar gaba ta tashi B'angaren su Aayan ko Maman nur [2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *BANA SONSHI* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah__ *πŸ‘„πŸ’‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπŸ’‘πŸ’‹* *πŸ’‘N W AπŸ’‘* *Lightning and bringing smile to your world is our perority* *NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~ πŸ…Ώ9⃣3⃣-9⃣4⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim B'angaren su Aayan ko a hankali yake zubewa kasa bayan uche ya halbe shi a wuri biyu kirji da gefen cikinshi Wanda sanda ya bari sun gama da Yan ta'ada ya cika burin shi Kara me yayi a kirji,sanan ya bar wurin zuwa mota domin d'auko bomb dan ma Kar a gane kashe shi akayi baya Mason ayi bincike balle a gane kashe shi akayi Koda ya dawo be Lura da ko gawan na wurin ko bayanan ba daga nisa ya wurga bumb din wurin ya tashi boom sanan ya bar wurin Abdul ko sati d'aya kenan da Suka gama jiran Aayan yakeyi Komawa su uche sukayi sai dai babu Aayan Abdul da jikinshi rawa yakeyi ya tambaya Amma sai uche ya fashe da kuka yace"those terrorist don kill oga Aayan" Cikin tashin hankali Abdul yace"how?" Ya shake wuyar uche yace"tell me how?" Uche ya fara kuka yace"na only 3of us come back some are in the hospital some don die" Abdul ya saki kuka kamar yaro Da k'yar ya bari washe gari aka koma dajin anyi niman duniya babu Aayan in takaice muku sati biyu akayi ba a ganshi ba sai dai Abdul ya gan agogon hanun shi ya d'auka ya rungume Yana kuka kamar yaro mamaki yakeyi ya akayi hakan ta faru shidai yasan suna sa bullet proof to kodai bomb ne ya tashi dashi? Shima hanunshi katon bandage ne domin shima an halbeshi fuskar Nan duk ciwo _____________ Tundaga wanan ranan da Rahma tayi mafalki ta fara rashin lafiya sosai ga rashin cin abinci kullum kuka ummi dai damuwa ce sosai a ranta yusura ta tausaya mata Kuma taki zuwa wajen umma ko asibiti kin zuwa tayi sai dai a Kira Dr ya zo gidan Yau ummi ta Kira umma tace"ta zo gidan ta duba Rahma"dama ummi na son ganinta kunya ne kawai da kawaici Tace"inshaallah gobe zan zo" Washe gari ko ta zo da safe,Nan fa suke ta bawa Rahma baki Amma kukan Rahma karuwa yake inta tuna mafalkin da tayi Ummi tace"ikon Allah Rahma dama haka kike da kafiya wanan wani irin zuciya ce ni da nike mahaifiyar shi na danne zuciyata " Amina ta rungume Rahma tace"karki damu Yaya zai dawo" Cikin kuka da maganarta da bai fita tace"ai dama nasan zai dawo mafalki ba gaskiya bane,bama zai tafi ya barni ban fad'a me Ina sonshi ba,umma be tab'a cin girkina ba,ummi sati d'aya fa mukayi dashi hiran kirki be tab'a Shiga tsakanin mu ba,ummmi ni"ta nuna kanta babu abind....."kuka ne sosai ya ci karfinta da k'yar numfashinta ke fita A lokaci d'aya yusura da Amina harda umma suka fashe da kuka domin babu Wanda zai gan Rahma beyi Mata kuka ba shekaran jiya sanda Amina ta taimaka Mata tayi wanka tun ranan Kuma batayi ba Ummi tace"ikon Allah kema umma yara kuka zakiyi dana sani da ban kira ki ba" Umma ta fita ta Kira Wanda ta Saba kira a Lagos abokin aikinsu ta tambayeshi ko akwai labari Nan fa yace Mata sun dawo Amma ya b'oye Mata Aayan ya mutu Cikin jin dadi ta koma tace"Rahma an ce sun dawo gobe zasu zo kano " Rahma ta mike ta shige toilet tana cewa"umma dan Allah ki Kira me kitso da lalli a min" Umma tace"alhmdullilah " Yusura ta fara Jan cikinta tace"Nima zanyi lallin " Amina ta harareta tace"ke baki tausayin kanki?" Tace"eh din Ina ruwanki" Umma tace"ni zan tafi gida" Umma tace"habadai ai Nan Zaki kwana mu fara Shirin tarban shi ki Kira gida kawai Rahma ta fito jallabiya kawai tasa tace"umma ni nayi kicin zan had'a abubuwa Da k'yar ma take tafiya domin bata jin dadin jikinta Aiko gidan busy yayi sosai kowa da abinda yakeyi Rahma ko tana trying number Aayan Amma be shiga Murmushi tayi tace"nasan surprised kake son yimin sallamar me lalli da kitso ne yasa ta mikewa taje ta bude lalli Mai kyau akayi musu da kitso Washe gari tun asuba ta farka tayi girki tayi wanka ta saka d'ikin Riga da skirt Umma sai fad'a takeyi Mata wai ta daina zumud'i ko kunyar ummi bata ji?" Rahma tace"ummi uwace a gareni ba suruka ba" Zama tayi a falo tayi d'aurin Zahra buhari tayi kyau Amina na tayi Mata hoto Agogo take kallo jefi-jefi yusura sai sherri take Mata Ummi tace"madam ai ba da asuba zasu dawo ba kamar an korosu sai zuwa yamma" Murmushi tayi tace"toh ummi Amma ai ya kamata muje Lagos mu tarbesu a airport" Umma tace"eh hakane amma ance Abdul yace mu jira a gida" Kafin karfe hud'u wanka Rahma uku tana canja Kaya abinma haushi yake bawa umma da mamaki" Misalin karfe 6:30 sai ga motar sojoji sun shigo gidan Rahma na jin mota ta fita da gudu sai kawai ta gansu dayawa cikin unifoam ummi ta fito da yusura ummi na ganinsu dayawa tasan akwai matsala addu'a kawai takeyi a ranta Abdul ne ya fito daga mota Ai da gudu yusura ta karasa ta rungumeshi tana kuka Yanayin shi yasa tace"lafiya dai ko'?domin kuka yakeyi" Be iya kallon umma ba Rahma ko sai leken n Motar takeyi ta gan inda Aayan zai fito murmushi takeyi Ganin dai be fito ba ta karasa ta fara duba motorcin amma ba Wanda ya rage a ciki Karasawa gaban Abdul tayi tace"Abdul Ina soja?" Be iya kallonta ba sai ma cewa da yayi yace"ki je ciki" Murmushi tayi tace"har yanzu fushin yake kenan?' Yace"Rahma please je ciki saman drawer shi akwai wani files d'auko min" Tace"toh shi Ina yake" Yace"je dai ki d'auko please" Tace"toh" Shigewa tayi Abdul ya saci kallon ummi sai ya ganta a kasa kamar stature Karasawa yayi yace"ummi sai hakuri addu'a yake bukata umma dai har yanzu bata fahimci komai ba Amina tace"me kake nufi" Yace"Amina Allah yayiwa Aayan rasuwa" Dai-dai fitowar Rahma nuna Abdul tayi da yatsa Tace"karya kakeyi ni nasan mijina be mutu ba " Yace"Rahma addu'an mu yake bukata domin bomb ne ya tashi dashi agogon shine kawai na sinta gashi Nan ya Mika Mata " Karb'a tayi tana juyawa,murmushi Rahma tayi wurgi da agogon tace"wanan ba agogonshi bane wallahi Yace"Rahma agogon shine tare muka siya fa" Tace"in ka ce yana da irinshi na yarda Amma ba nashi bane wanan domin screen din nashi zaka ganshi a jike a hannuna ya fadi a ruwa na bashi hakuri nace ya Kai gyra sai yace min haka zai ta sawa tunda Rahmar sa ce ta b'ata,nidai dan Allah ka kirashi nasan Wasa yakeyi ka ce me ya dawo wallahi na tuba na shiryu ya dawo Kar laifina ya shafi ummi ka gan ta ko?" Yusura ta rungumeta tace"Rahma kiyi me addu'a Allah ya jikanshi A fusace tace"yusura zamu b'ata fa akan me zakiyiwa mijina fatan mutuwa eh nidai wallahi bazan bar nan wurin ba sai kun fito min da mijina azzalumai me yayi muku kuka kaishi daji?" Sosai Rahma ke surutu kamar zararriya,shiko Abdul ya zube kasa yana kuka kamar ba namiji ba ko da mahaifinshi ya mutu beyi irin kukan Nan ba Umma ne ta karasa ta wankawa Rahma Mari ta girgizata tace"muje ciki haukan ya isa haka " Ga mamakinta sai taji Rahma ta zube jikinta bata numfashi Suko sojojin fito da akwatin shi sukayi suna tsara me da duk wani abinda Suka Saba Umma tace" Maman Nur Share [2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *BANA SONSHI* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah__ *πŸ‘„πŸ’‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπŸ’‘πŸ’‹* *πŸ’‘N W AπŸ’‘* *Lightning and bringing smile to your world is our perority* *NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~ πŸ…Ώ9⃣5⃣-9⃣6⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim Umma tace"subhannallah ke Rahma bude idonki" Yusura sai kuka takeyi umma tace"ya Allah ka kawo Mana a gaji domin ummi ganin Rahma ta sume yasata d'auka wuta itama" Abdul cikin tashin hankali yace"ummi dan girman Allah ki Bude ido karki tafi ki barni dan Allah karki maidani maraya a Karo na biyu"ji yake da a ce zab'i aka bashi da zaice shi a d'auki ranshi a bar Aayan " Kowa a wurin jikin shi yayi Sanyi taimakawa ummi akayi zuwa ciki Amina na kuka tana Kiran sunanta Abdul ya Kira likita Ba a dade ba aka ceto rayuwar ummi Sai dai fa likita ta dade akan Rahma amma Bata farfado ba sai dai suna jin bugun zuciyarta kad'an-kad'an Nan fa suka gane tana raye" Ledar ruwa Suka Samata sanan tace" a fita a barta ta huta Umma tace Ina nan ba inda zani Umma dai sai addu'a takeyi itako yusura zazzabi ne ya Mata mugun kamu cikin kankanin lokaci labarin mutuwar Aayan ya zagaye ko-ina har gidan tv ana nunawa Abban yusura yaji mutuwar sosai hakan yasa yace"shima zaije kano gaisuwa rasuwar Mami ta nace sa taje yace"ta shirya Sai yamma ummi ta samu kanta tana bude ido daga baccin da take Wanda allurar bacci akayi mata ta kalle Amina tace"Rahma Bata mutu ba ko?" Amina ta fashe da kuka tace"ummi wallahi in kika gan Rahma sai kin tausaya Mata ta rame tayi bak'i ga bakinta ya bubushe" Ummi tace"tana Ina" Tace"tana d'akinta ai" Ummi tace kaini" Ummi na Shiga ta hangota kwance bata hayyacinta Amma hawaye na bin kuncinta Ummi ta karasa ta kwanta a gefenta ta rungumeta Cikin kuka tace"Rahma kiyi hakuri Wanda yafi mu sonsa ya amshi abinsa karki damu zan baki farin ciki" Kuka ummi keyi tana shafa mata baya Umma ta kasa rike kukanta sai kawai ta fashe da kuka fita kawai tayi ta koma falo tana amsar gaisuwa Yusura ko kwanciya tayi domin kwata-kwata jikinta na rawa saboda tashin hankali Abu kamar Wasa sai bayan kwana uku Rahma ta bude idonta Kallon d'akin tayi sai ta gan d'akinsu na nada Tsaki tayi ta mike da k'yar jikinta na rawa ta bar d'akin Domin babu kowa duk suna falo ana karb'an gaisuwa Part dinshi taje jikinta har rawa yakeyi ta kulle Murmushi tayi ta karasa wajen wani katon hotonshi a bango Hawa bedside tayi ta ciro ta rungume tana sauke ajiyar zuciya tace"ka gan na gudu ko?ai kasan bazan barka ba ko a baya akasi aka samu" Kallon hoton tayi tace"lah sojana Yana da dogon hanci" Sai Kuma ta ajiye hoton ta zauna a kasa ta saki wani kuka Tace"meyasa baka bani dama ta biyu ba?haba mijina nasan zaka dawo Bugun kofa da aka fara Yi ne yasa Rahma saurun kwantawa Ummi tace"ki bude please daughter kin ji?" Amina tace"Bari inje in d'auko key" Zuwa tayi ta d'auko key sai dai sunyi su bude Amma Taki buduwa saboda Bata zare key din ba" Rokonta sukeyi Amma Taki budewa Umma tace"mu koma indai Rahma ne bazata bude ba" Ummi tace"tana da kafiya ne akan komai" Abdul ko Sosai yake bincike akan Al'kibila domin yana son cika burin abokinshi be ma lura da Cikin jikin yusura ba Bayan kwana uku akayi sadakar uku Abba yusura ya zo abin mamaki harda Amir Wanda ya dannawa Aneesa saki uku domin rashin kunya tayiwa mummy Kuma da yarda Allah da addo'i asiri ya karya a ranan yayi ta kuka Yana cewa"a dawo me da Rahman shi "da k'yar mummy ta lallashi yayi shiru ta fahimtar dashi kaddarar su ce a haka tana Cikin magana aka hasko mutuwar Aayan a tv shine yazo gaisuwa tare da mummy mutuwan ya dameta Mami ko tunda ta gan Abdul domin Basu tab'a ganin juna ba sai ta gan yayi Mata Kama da Yar uwarta Aisha in badan gidan rasuwa bane da babu abinda zai hana ta tambayeshi Bayan kwana biyar kowa ya watse aka bar umma da Rahma da hakuri Rahma zuwa yanzu sai ta wuni Batayi magana ba saidai hawaye yayi ta bin kuncinta Ummi kullum Cikin bata hakuri takeyi domin tafi tausayinta da Abdul fiye da kanta Abdul ne a d'aki Yana bada order a Kama Samira domin bincike ya nuna tana Cikin kungiyar Al'qibila dumu-dumu cewa yayi ayi ta Bata horo Mai tsanani harsai ta bayyana su waye ke ciki Yusura ne ta shigo d'akin da sallama tace"ga juice nan ka Sha tun safe kana ta aiki" Da hannu ya Mata alama da ta ajiye ya cigaba da danne-danne laptop Kuka ta fashe dashi da yasa ya d'ago ya kalleta sai ya ganta da ciki Da mamaki ya kalleta yace"yus me kikasa a ciki?" Juya me baya tayi tace"sai yanzu ka gani?" Mikewa yayi Yana murmushi me had'e da hawaye ya jawota jikinshi Yi hakuri kema kinsan kwana biyun nan bana Cikin hankalina yusura na rasa aboki da babu kamarshi Aayan shine sanadin shiga soja na Aayan be tab'a bari nayi kukan maraici ba "yana magana ne yana hawaye Yusura ta d'aga kafa saboda ta kamo tsayinshi a goge me hawaye tace"addu'a samun Rahama ubangiji zamu Yi me,ni Rahma ma tafi damuna domin kwata-kwata yanzu Bata magana balle asa ran zata ci abinci" Abdul yace"na rasa ya zanyi da ita " Yusura tace"ni a ganina in ta gama takaba ka aureta ko zata samu saukin abinda takeji" Ture yusura yayi ya koma ya zauna yace"ban tab'a tunanin baki da hankali ba sai yau " Cikin kuka zatayi magana yace"get out" Hayaniyan da Suka jine a waje yasa duk yan gidan fita Rahma ne ke kokuwa da sojojin gidan ta shake d'aya wai dole sai ya fito Mata da mijinta a cewarta duka sojoji munafukai ne meyasa za a Kai Mata miji inda za a kashe shi " .ummi tace"ke sakeshi kan ranki ya b'ace nida Nike mahaifiyarshi na hakura sai ke ne bazaki hakura ba shin in badan abinki wake fad'a da ikon Allah Abdul yaje ya jawota da karfin tsiya Cikin kuka tace"da a ce mijina ya mutu da gaske da nasan yanzu zuciyata Bata bugawa Amma wanan bugun zuciyar nashi ne shi kadai Kuma nasan duk inda yake yanzu yana bukatar addu'a ta " Ummi taje ta Kama hanunta suka shige ciki duk inda ta so ta fahimtar da ita Aayan fa ya mutu bazai dawo ba abin ya fassakara Bayan wasu watanin abubuwa da dama sun faru ciki harda Gama takabar Rahma sai dai rayuwar Rahma babu canji sai ma gaba da yakeyi ance ta koma wajen umma taki Kuma da an masa Mata sai ta kulle kanta a d'aki Abdul da yusura sun koma Lagos bakin aikinshi inda Samira da taji horo ta bayyana hide out dinsu da cewa su Suka sa uche ya kashe Aayan Abdul ya had'a komai domin zuwa Abuja kuma yasa uche a tafiyar Wanda besan an gane shi ya kashe Aayan ba Suna zuwa suka bawa wurin wuta domin duk suna ciki suna meeting inda zasu ceto Samira Daga sama aka bude musu wuta gaba d'ayansu sun mutu Sanda suka Gama Abdul ya halbi uche caka-caka sukayi me sanan Suka d'auki gawan Suka koma dashi Suka ce Yan ta'adar ne Suka kashe shi inda Suka tarar da Samira ta mutu a inda aka ajiyeta Wanda duk plan din Abdul ne shi yasa a halbeta Amma abin sai ya nuna Kamar ita ta halbi kanta _______ B'angaren su ummi ko Maman nur [2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *BANA SONSHI* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah__ *πŸ‘„πŸ’‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπŸ’‘πŸ’‹* *πŸ’‘N W AπŸ’‘* *Lightning and bringing smile to your world is our perority* *NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~ πŸ…Ώ9⃣7⃣-9⃣8⃣ Ummi ta gama yanke shawaran aure za ayiwa Rahma kila in ta auri amir tunda sun tab'a soyyaya ya dawo da ita inda take a da domin in ba haka akayi ba bazata tab'a samun natsuwa ba ta gaji da ganinta haka " Zaune suke a falo Amina sai Yi Mata magana take Amma da Kai take amsawa da Amina ta isheta da surutu sai tayi tsaki ta kwanta a kujera ta jawo pillow tasa a kunni Ummine ta sauko cikin Shirin fita anguwa ta kalleta tace"gidan umman ku zani ko Zaki je?" Girgiza Mata Kai tayi ummi tace"toh ki tabbatar kin ci abinci Ta amsa da Kai ummi dama ta Saba tafiyarta tayi Bayan sun gaisa da umma ta kawo Mata ruwa da abinci Hamza ya gaisheta Tace"Ina Yan biyu?" Umma tace"sun tafi makaranta " Ummi tace"magana ne ko in ce shawaran na zo muyi Alan Rahma ni a ganina me zai hana ayi Mata aure?ta auri amir tunda ta soshi a baya nasan hakan zai taimaka" Umma tace"babu komai hajiya duk inda kika gan ya dace shekaran jiya ko mummy shi ta kirani a waya tana niman auren Rahma nace mata su bani lokaci " Ummi tace"yauwa alhamdullilah sai kawai a aura me ita zata ji dadi nasan bazata wulakanta ba da naso Abdul ne ya aureta amma Kuma sai na duba tsakaninta da yusura za a iya samun matsala" Umma tace"gaskiya da wanan" Ummi ne ta amshi number mummy ta kirata tace"sun amince ranan murna a gun mummy Kamar ta zuba ruwa ta Sha "Kiran amir tayi a waya tace"ya dawo gida akwai goodnews" Amir dake lecturing yayi saurin barin ajin ya koma gida Ummi na komawa gida ta Kira Abdul tame bayani shima yayi na'am da shawara nan fa aka fara shiri auren Cikin kankanin lokaci aka Saida Rana Yau ummi take son sanar da Rahma amma tana d'an shakka Amina tace"ummi ki fad'a mata kawai Ummi tace"je ki kirata" Zuwa Amina tayi sai gashi sun dawo tare a kasar tiles ta zauna tana rike kirji Ummi tace"meke damun kirjin?" Tace"zafi nikeji" Ummi tace"ba dole ba mutum yasa Abu a rai Rahma tun da wuri ki dawo daga rayuwar da kika saka kanki bayi bane Ina fad'a Miki,Kuma Ina son sanar dake ranan juma'a za a d'aura Miki aure da amir" Ji tayi zuciyarta ta buga ta rike kirji tace"ummi bana so wallahi bazan aurenshi ba ni haka zan Kare rayuwata ba aure ku barni" Ummi tace"toh baki Isa ba ya ishe ki haka haba ke meyasa kina da kafiya ne an ce kiyi hakuri kin ki ki hakura wanan ai aikin banza ne" Cikin kuka tace"nidai bazan aureshi na fadi zuciyata" Ummi tace"saboda ban Isa dake bako?" Rahma tace"ummi soja fa zai dawo na fad'a miki kuma zaiyi fushi a bar maganan kawai" Ummi tace"Anki a bari" Kawai sai Suka ji tayi wani ihu ta rike kirji Ummi ta taso ta riketa da kanta ta d'auko kayan aikinta ta duba ta Magani ta rubuta tace"Amina je ki siyo" Amina ta fita da sauri ummi tace"Rahma kashe kanki zakiyi?toh in baki sani ba in fad'a Miki zuciyarki na gab da bugawa Tun daga wanan ranan ba a Kara yiwa Rahma maganar auren ba sai dai an cigaba da shiri Yau dai tana zaune wayarta yayi Kara ta d'aga Amir ne Sallama yayi yace"ko amaryata ta tashi lafiya?" Rahma tace"look amir nasan munyi soyyaya a baya Kuma na soka but bekai rabin soyyaya da nikewa soja ba dan girman Allah kayi hakuri ka nimi wata ni soja Nike jira" Amir yayi dariya yace"zamu gani na Miki alkawarin sai kin dawo kina Sona kamar da" Tsaki tayi ta Katse Kiran tun daga wanan ranan ta ajiye wayar a gefe Ashe kullum amir na Mata text Bata sani ba __________ A yau ta kama al-hamis su yusura da Abdul sun dawo cikin yusura yayi girma Kamar zata haifeshi yau da k'yar take tafiya Abdul na shigowa yace"honey Ina kike" Ummi ta sauka tana dariya sai ta ji Kamar Aayan ne domin haka yake kiranta karasawa Abdul yayi Yana mata shagwab'a ta ture shi tace"ya'ta zo Nan Ashe har yanzu kina fama?" Yusura ta rufe ido tana murmushi Abdul yace"ai na dawo da ita kenan sai ta haihu" Gobe da yamma zan koma bayan an d'aura aure Ummi tace"Allah ya kaimu" Rahma dai Bata San meke faruwa ba ta dai gan ana ta zir-zirga Kuma Bata damu ta tambaya ba Washe gari ta tashi da farin cikin da ta dade batayi ba Ummi ta leko ta ganta zaune a d'akinta tana cin water melon Ummi ta bata tsumin da take Bata kullum tace"shanye shi yanzu" Amsa tayi ta shanye Ummi tace"Amina zata kawo Miki Kaya shi Zaki sa " Tace"toh" Amina ne ta shigo ta Bata Rahma tayi wanka tayi kwaliya kayan ya karbeta danma ta rame Zama tayi bakin madubi-madubi tana fesa Tulare Bayan an sauko daga massalaci aka taru a kofar gidan ummi domin kawu cewa yayi ba ruwanshi Mutane ne cike kofar gidan ana jiran ango domin ya makara go slow ya rike su Basu suka iso ba sai misalin 3:29 Zama akayi har malami zai fara d'auran aure sai ga motorci sojoji sun Yi horn me gadi ya leka sai ya dawo ya bude bayan ya fadawa sauran abokan aikinsu kowa ya kimtsa Nan fa suka Zama abin kallo domin masu gudu nayi wasu ma na zaune wurin d'auri aure Suka mike Abdul ma mikewa yayi yayi da Wanda Suka zo d'aurin aure Suka natsu Bayan anbude gate Wanda motar ya shigo wani ya zaga ya bude me kofa Wanda ya fito ne yasa Abdul yin wani yin tsalle taku biyu ya Isa gabanshi Amir ko zaro ido yayi Yace" Kuyi hakuri da rashin samu update kamar da na fad'a muku Ina da uzuri ne but inshaallahu yau na gama aikin dake gabana Manan Nur Share [2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *BANA SONSHI* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah__ *πŸ‘„πŸ’‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπŸ’‘πŸ’‹* *πŸ’‘N W AπŸ’‘* *Lightning and bringing smile to your world is our perority* *NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~ Dedicated to Na'ima Adamu maman A'A πŸ…Ώ9⃣9⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim Amir yace"not again" Wani wawan runguma Abdul yayiwa Aayan dake tsaye ya rame yayi baki da ka ganshi ka gan Wanda ya dade Yana jinya Abdul yace"Ina ka shiga Muka d'au ka mutu" Da k'yar Aayan b yace"asibiti shekaran jiya na farfado jiya da yamma na dawo Lagos aka ce ka tafi d'aurin aure but wake aure?" Abdul ya ji kirjin shi ya buga kawai sai yace"Amina " Yace"Amina Kuma me..." Katseshi Abdul yayi da cewa"je ciki Ina zuwa Abdul ya karasa wajen malamin da zai d'aura auren yace"a d'aura da Amina Kafin Amir yace"zaiyi wani abu an d'aura auren shi da Amina Shidai mamaki yake Hayaniyar jama'an waje yasa Amina saukowa tace"alhamdullila an d'aura auren Rahm..." Wanda ta gani gaban ta ne yasa ta yin shiru tace"Yaya"rungumeshi tayi tana kuka shima ya rungumeta yace"Ina honey?" Tace" tana ciki" Yace"Rahma fa?" Tace"tana Nan" Yace"aurenwa aka d'aura?" Amina ta fara in Ina"tsawa ya daka Mata yace"ki bani amsa yanzu na ji kin ce auren Rahma Jiki na rawa tace"Rahma da amir Amma wallahi Rahma Bata sonsh......."katseta yayi yace"shut up" Haurawa yayi yaje d'akin ummi,da mamaki ummi ta taso tana shafa fuskarshi tana hawaye tace"Kaine ko mafalki Nike?" Murmushi yayi yace"ummi nine ban mutu ba" Ummi tace"Ashe Rahma tayi gaskiya na shiga uku" Rungumeta yayi yace"ummi farin ciki zakiyi" Ummi dai taji dadin ganin shi Amma yanzu haukan da zaiyi in yaji da Rahma aka d'aura aure shine matsala Yace"ummi ko baki ji dadin ganina bane?" Zatayi magana sai ga Rahma ta shigo da gudu domin Amina ta fad'a mata Ta baya ta rungumeshi tana kuka tace"Ina ka shiga ne ka barni?" Dawowa gabanshi tayi ta fara shafa fuskarshi tana hawaye tace"soja is that really you? Ko mafalki nikeyi Wani kallo yake Mata sai ya gan tayi kwalliya Rungumeshi Tayi tana kuka Amma sai ya tureta ta fadi a gado Barin d'akin yayi sai binshi take a baya tana cewa"ka tsaya please na tuba mijina nasan ni Mai laifine"be kulata ba D'akin shi taje tace"soja me nayi kaki kulani ko laifi nayi in laifin ne ka yafemin na tuba Ko kallonta beyi ba saima zuwa gaban drawer da yayi ya fara dube-dube Murmushi tayi ta karasa ta kara rungumeshi a fusace ya juyo yace"wai meyasa kike damuna eh?Ina kin ji dadi na mutu ko shekara banyi ba kin komawa tsohon saurayinki har an d'aura Miki aure meyasa kike damuna?" Girgiza kai ta farayi tace" wallahi ni ban aure kowa ba na fadawa ummi Kuma ta bar zancen dan allah soja ka

Chapter 9 of 11