fito
Rahma na ganin yusura ta
Maman Nur
Share
[2/20, 8:34 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
Karku manta Shirin *KALUBALE* yau ta gayyato Mana babba bakuwa watoh billynAbdul inda zamu tautauna akan UWA TA GARI game tambaya ko Kari haske akan wani abin da ya shige me duhu game da wanan topic din zai iya turomin tambayar.in baki karanta na jiya ba ki nimi ki karanta domin jiya an tautauna ne akan KAYAN Mata inda bakuwar tamu ta bamu wasu sirrika
π
Ώ7β£9β£-8β£0β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Rungumeta Rahma tayi tana dariya tace"wow yusura kin Yi kyau me kike ci haka"
Yusura da Bata jin karfin jiki da k'yar tace"kema kinyi kyau sosai Rahma"
Rahma ta kalleta tace"meke damun ki haka Kamar baki da lafiya Kuma na ji jikin ki da zafi"
Yusura tace"zazzbi nayi"
Aayan ya kalli Abdul sai kawai ya Susa Kai
Aayan a ranshi yace"kenan ni Wawa ne dana kyale Rahma but babu komai"
Rahma cikin tausayawa ta fara yiwa yusura Sannu
Rahma tace"iam so happy yau zan gan ummina naji kewarta"
Yusura tayi murmushi tace"mother inlaw ki ce fa"
Rahma tace"ni uwa na d'auketa kullum sai ta Kira tace a bani waya mu gaisa Kuma tace in an min laifi in fad'a Mata yanzu ma na Tara karar da zan Kai mata"ta Kare magana da murgud'awa Aayan baki
Murmushi yayi yace"yariyar nan kin raina ni fa zan seta ki"
Yusura tace"aini Nima tana Kira malama bake kadai take so ba"
Sai yamma ligis suka isa kano
Kano
Suna kaiwa tun a mota Amina ta fito ta tarbesu tana murna
Rahma tace"Amina baki da mutunci ko flashing?"
Amina tayi murmushi tace"ai Bari nayi ku ci amarci "
Yusura tace"hmm Aiko an barki a baya aure dadi gareshi"
Amina tace"ba sai kin min gori ba Nima N
nan da lokaci kad'an zan Shiga tsahun ku "
Rahma tace"Amma baki da kunya fa sai na fad'awa soja"
Amina zatayi magana Suka ji ummi tace"baxaku shigo bane a waje zaku tsaya?
Murmushi Rahma tayi ta karasa da gudu ta rungume ummi tace"ummi nayi kewar ki"
Tureta yusura tayi tace"Nima ki Bari inji d'inmin ummi mu"
Murmushi tayi ta hadesu ta rungume tace"welcome my dotas "dan tuni su Abdul suka shige ciki"
Suna shiga ummi tace"kuje d'aki kuyi wanka ku fito ku ci abinci"
Bayan sun haura sama ne ummi ta kalli Abdul tace"son ya aikine?"
Shagwab'a fuska yayi yace"ummi sai yanzu kika ganni ke yaranki kika sani"
Murmushi tayi ta kalli Aayan dake latse waya tace"Aayan dama Ina son magana da Kai tambaya zan maka,ya akayi ka auri Rahma?"
Mamaki tambayar ta bashi yace"ban fahimta ba"
Tace"domin na samu labarin wani taso ta aura ba Kai ba Yan gidan angone Suka fasa saboda dalilin wani video ko miye ni banma fahimci zamcen ba?"
Gaban shine ya fadi yace"ummi waye ya baki wanan labarin?"
Murmushi tayi tace"
Maman Nur
Share
[2/20, 8:34 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ8β£1β£-8β£2β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Murmushi tayi tace"ai abin duniya baya b'oyuwa har gida aka biyoni aka fad'a min,nidai so Nike in fada maka ka rike matar ka hanun biyu biyu karka bari wata magana yasa ka canza Mata"
Shiru yayi Yana tunanin ya fad'a Mata ne ko ya Bari
Abdul ne yayi gyran murya yace"Aayan mun aikata babban kuskure dole mu gyra kafin mu bar kasar nan"
Ummi tace"me kukayi? Ku fad'a min"
Aayan da kanshi ya kwashe komai ya fad'a Mata be b'oye Mata ba ya kare da cewa laifina ne dana bi wanan hanyar dan auren Rahma gashi nasa mutane na Mata kalon Yar iska"
Kuka da Rahma ta fashe da shine yasasu mikewa
Ummi ta karasa da sauri tace"daughter meya faru?"
Cikin kuka tace"ummi wallahi ban tab'a yin iskanci ba ki yarda dani"rungumeta ummi tayi tace"na yarda dake daughter
Yusura ta murgud'awa Abdul baki tace"ummi su suka had'a komai wallahi"
Ummi ta kallesu rai b'ace tace"toh zuwa Niger ya Kama ku domin sai kunje kun gyra abinda kuka b'ata wanan ai zalunci ne waye yace muku ana niman aure kan aure?maza ku tafi wajen iyayensu ku fad'a musu gaskiya"
Aayan yace"ummi ai mun gama magana da ita ta hakura Kuma gobe fa zamu koma Lagos yaushe har zamu Minna mu dawo?"
Ummi tace"I don't care how nidai kawai ku tafi ku bani wuri "
Abdul yace"ai ummi na fad'a me yaje kawai zan jirashi a Nan"
Aayan ya kalleshi ya harareshi kafin yace"ai tare zamu tunda kai ma kayi karyan"
Abdul yace"aini ba a sa date ba kuma babu Wanda nasa yayi kissing dinta ni da kaina nayi ......"
Sake baki ummi tayi tana kallonsu tace"toh gaku Yan duniya ko maza ku tafi ku ban wuri" tana Gama magana ta haura ta barsu
Yusura ta murgud'awa Abdul baki
Nuna kanshi yayi yace dani kike gyda me kai tayi tana dariya
Murmushi yayi yace"zan Kama ki ne"
Aayan ko karasawa yayi inda Rahma ke tsaye tana kuka rungumeta yayi yace"iam sorry please forgive me "
Kokarin raba jikinta take da nashi
Yace"no wallahi yanzu zan tafi Minna har gidansu d'an iskanan zanje in sanar da mahaifiyarshi ba haka kike ba"
Tureshi tayi ta mike ta haura,kallon Abdul yayi yace"toh malam kiss din ya isa haka ka zo mu kama hanya"
Hararan shi yayi yace"haka kawai ka hana mutum jin dadi saboda girma Kai duk shi ya janyo yau bazan kwanta kusa da Matata ba "
Yusra ta ruga da gudu,har suka fitoh Abdul na mita
Sai cewa yake ni yanzu na ajiye iyali zan daina biye maka tunda baka jin shawara gashi yanzu haka kawai ka mayar dani gwaro ni da Nike so jin d'inmi matana gaskiya ka zalunceni tun farko sanda nace maka kaje ka fad'a Mata kaki yanzu gashi k ....."
Tari ya farayi Aayan yayi murmushi ya Mika me goran bottle water
Yace"in kana surutu kayi ta had'iye miyau"
Tsaki yayi ya kwace goran ruwan"
Aiko cikin tsakiyar dare Sosai Suka Isa Minna garin Minna
Direct guest house sukayi a falo Abdul ya kwanta a kujera Yana tsaki jefi-jefi
Waya ya d'auka yayi dialling number yusura domin ya bata d'ayan wayarshi
Ga mamakin shi sai yaji ta d'auka gyra kwanciya yayi cikin jin dadi
Yace
Maman Nur
Share
[2/20, 8:34 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah_
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ8β£3β£-8β£4β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yace"baby baki yi bacci ba?"
Yusura ta turo baki kamar Yana ganinta tace"ah'ah"
Yace"meyasa?"
Tace"banji baccin ne tun d'azun sai juyi nikeyi"
Murmushi yayi yace"kin ji kewa na ne?"
Tace"Allah ya kiyaye In ji kewar ka"
Yace"toh shikenan sai da safe daga yau mun b'ata"ai Bata San lokacin da tace"Dan Allah Kar ka kashe bazan iya bacci ba"
Murmushi yayi yace"baby kin iya gulma"cigaba sukayi da wayar sun dade sunayi kafin yaji shiru bacci yayi awon gaba da ita
Murmushi yayi ya kashe wayar
B'angaren Rahma ko duk yau sai taji ba dadi Wanda Bata San dalili ba
Wayar da ya bata ne yayi Kara kamar Wanda ke jira tayi saurin d'aukawa tayi sallama
Beyi magana ba sai hello take taji shiru
Gajiya tayi ta gyra kwanciya domin tasan Yana jinta a haka itama bacci ya d'auketa
Washe gari da asuba suka farka sai gidan su Rahma
Ba Karamin mamaki umma tayi na ganin su ba ga kuma fargaba kardai laifi Rahma tayi ne"
Bayan sun gaisheta cikin ladabi ta shimfid'a musu taburma Suka zauna
Shiru dai babu me magana cikin su
Umma tace"lafiya dai ko?"
Aayan yayi gyran murya yace"umma niman gafara muka zo "
Tace"na me fa?"
Cikin jin kunya yayi Mata bayani ran umma ya mugun b'aci harta kasa b'oyewa Abdul ya bata hakuri yace"kiyi hakuri muma bamu da masaniya jibrin yayi haka"
Kafin tayi magana sai ga mummy tayi sallama da mamaki umma ta kalleta tace"lafiya yau a gidana ko? zuwa kikayi ki Tara min jama'a?
Mummy tace"ah'ah ganin ki na zo yi kuma zuwa nayi mu sasanta"
Ita da kanta ta d'auko kujera da ta hango ta zauna
Umma tace"Ina jinki"
Kallon Aayan tayi sai ta gan yayi Mata kwarjini Bata San sanda tace"sanunku bayin Allah ba"
Abdul ya amsa,kallo umma tayi tace"kiyi hakuri na zo ne mu sasanta Kuma in fad'a Miki na amince Amir ya auri Rahma"
Ai Aayan ji yayi zuciyarshi ya mugun bugawa ya kalleta
Umma tayi Yar dariya tace"hajiya Maryam kiyi hakuri Rahma tayi aure ga mijinta nan da yike bata da hakkin ku kuna fasawa washe gari allah yayi Mata canji da abinda ya fi al'khari Amma meya faru ne haka yau kikeson Rahma?"
Kuka mummy ta fashe dashi tace"na cuci d'an na na shiga uku na lalace hafsat kin cuceni dakika ingizani nasa aka fasa bikin nan Allah ya isa tsakanina dake" umma ta lallasheta cikin kuka ta Basu labari
Umma da ta tausaya Mata tace"kiyi tame addu'a inshaallahu zai dawo dai-dai "
Mummy tace"inayi kullum inayi"har kofar gida umma ta rakata bayan Aayan ya fad'a Mata Rahma Bata aikata abinda ta zarge ta dashi ba
Bayan ta wuce umma ta dawo zaciyar ta fes
Harsu Aayan sun tashi zasu wuce sai ga kawu ya shigo be lura dasu Aayan ba ya fara kwallo da abubuwan cikin gidan
Yace"
Maman nur
Share
[2/20, 8:35 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ8β£5β£-8β£6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Da mamaki duk suka kalleshi Aayan ya nade hannuwanshi yana kallonshi
Har kawu ya d'ago kai zai fara zazzagewa umma rashin mutunci sai idonshi ya sauka kan Aayan ai zubewa kasa yayi yana kwasar gaisuwa
Kallon da Aayan ke mishine yasa shi kallon umma yace"maman Yan biyu meyasa kike ajiye Kaya a hanya irin wanan in badan na masar ba ai sai mutum yaji ciwo ko?Amma Bari inje zan dawo yanzu Ina zuwa"
Umma tace"ka fasa rashin mutuncin da ka Saba ne?"
Yace"Kai maman yan biyu kiji tsoron Allah yanzu sharri Zaki min?yaushe rashin mutunci ya taba shiga tsakanina dake?"Yana magana ne Yana tafiya har ya bar gidan yana fita kofar gida ya ruga da gudu Dan bazai manta kashedi da Aayan yayi me ba akan umma bayan ya bashi filin da yame alkawarin ya gargade shi akan ya fita harkan umma ya daina takura mata
Aayan ya sunguna har kasa yace"umma ku fara shiri gobe zansa a zo a d'auke ku a maidaku kano
Umma tace"Nan ma yayi,mun gode"
Abdul yace"umma ki dubi Girman Allah ki bari akwai gida a can kano din"
Zatayi magana Aayan ya katseta yana rokonta da k'yar suka shawo kanta ta amince inda Suka ce muhimman kayanta zata kwashi akwai komai a can
Godiya ta musu tare da fatan samun nasara a tafiyar su
Sun ji dadin addu'a ta daga gidan sukayi gidan su yusura Suka Fadi laufinsu
Sosai Abba ya ji ba dadi Amma yasawa zuciyar shi hakuri domin aikin gama ya riga ya gama addu'a yayi musu na samun nasara a tafiyar su
Bayan sun bar gidan makaranta su Hamza sukayi bayan sun cika me booth da kayan provision
Bayani sukayi me domin be san su ba Sosai ya ji dadi
Aayan yace"yaushe zaku gama waec?"
Yace"jibi zamu gama"
Yace"ok jibin in kun Gama sai ku tafi kano in result dinka ya fito ka kaiwa jibrin zan me bayani
Cikin sanyi jiki yace"toh Kai Ina zaka?"
Yace"tafiya zanyi zanje peace keeping "
Yace"toh Allah ya Kare"
Shafa kanshi Aayan yayi yace"take good care of your sister"
Yace"I promise"
Daga makaranta suka d'au hanyar kano
Sai da misalin karfe hud'u Suka Isa garin kano
Yusura najin muryar Abdul yana magana da maigadi dariya ya sub'uce Mata
Rahma ko bugun zuciyarta karuwa yayi
Da sallama suka Shiga falon inda ummi ta kallesu tace"Ina fatan dai kun gyra kuskuren ku?"
Aayan yace"
Maman Nur
Share
[2/20, 8:35 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ8β£7β£-8β£8β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Aayan yace"eh ummi sai ka ce ba ya'yan ki ba kinsa Mana zafi"
Murmushi tayi tace"ai gaskiya ne"
Tashi tayi domin Basu wuri tunda tasan da safe zasu wuce kowa ya gana da matarsa
Abdul na ganin ta shige ya tashi ya koma inda yusura ke zaune ya koma kujeran da yusura ke zauna
Yace"babu sannu da zuwa balle a bani ruwa?"
Murmushi tayi tace"toh bari in d'auko"
Tashi yayi yace"muje d'akina kawai akwai sa'idawa a nan wurin
Murmushi tayi ta mike ta bi bayan shi
Aayan ko satar kallon Rahma yayi sai ya gan ta basar Kuma in ba ya fara Mata magana ba bazata yi me ba
Mikewa yayi yaje inda take yace"hi"
Tace"hello"
Yace"babu gaisuwa?"
Tace"welcome"
Yace"follow me"
Da dai kamar bazata bishi ba sai Kuma ta mike ta bi bayan shi
Tana kaiwa d'aki tace"uhrmmm gani"
Murmushi yayi ya karasa inda take yana kallonta yace"sunana ba urhmm ba yau dai sai kin Kira sunana"
Tace"aini ban sani ba"
Yace"karya kikeyi"
Rufe fuska Rahma tayi tace"kunya nikeji"
Rungumeta yayi ta baya yana shinshina kamshin wuyanta yace"Rahma ki ce kina Sona ko zan samu kwanciya hankali please"
Shiru tayi,yace"please I want to know my stand in your life"
Hawaye ne ya shiga gangaro Mata
Yace"subhannallah kiyi hakuri tunda baki so"yana gama magana ya koma gado ya kwanta
Tsayawa tayi tana kukan da babu dalili shiko kwanciyar shi yayi domin ta fara b'ata me rai
Kasa wucewa tayi sai ma Zama da tayi a kasar tiles ta jigina da bango
Duk wani abinda takeyi yana kallonta amma sai yayi Kamar me bacci har baccin gaske ya d'auke shi
Bayan awa biyu ya farka a zaune ya ganta ko motsawa batayi ba sai ma bacci da takeyi karasawa yayi ya gyra matasuman kanta da ya barbaze a fuskarta sanan ya shiga bayi domin d'auro alwala
Cikin dare ko babu inda beyi ba dan ta furta me kalman so amma taki harya gaji ya kyaleta
Washe gari
Da asuba sun gama shiri yusura sai kuka take
Rahma dai ji tayi bata da lafiya rokosu sukayi zuwa d'akin ummi tayi musu addu'a tare da musu nasiha sanan tace"matarsu su rakasu
Abdul ya makakle yusura sai shagwab'a takeyi shiko Aayan fushi yake da Rahma dan haka be jirata ba ya shige mota ya zauna
Kawai sai ta fashe da kuka ganin ya kulle motar jiran Abdul kawai yake su wuce
Kukanta ne yasa shi bude motar a fusace yace"toh miye in kika yi hakuri yanzu zan bar Miki garin tunda kin tsane ni karki damu zan bar Miki gidan yanzu"
Karfin kukanta ne ya Karo ranshi na Kuna yace"please ki koma ciki Kar ummi ta fito ta d'au wani abu nayi Miki "
Kafin tayi magana Abdul ya karaso da yusura bayan ya gama lallashinta Shiga motar yayi driver ya jasu
Abdul na d'agawa yusura hanun suna barin gidan Rahma ta zube a kasa da guiwowinta ta saki kuka .
Yusura tace hakuri zakiyi haka aikin nasu yake"
Amina ce ta fito ta jasu zuwa ciki kowa yayi d'akin mijin shi ya kwanta rai babu dadi"
Rahma da ta dunkule rike da rigar Aayan tana shishinawa tana kuka
Cikin takaici tace"
Maman Nur
Share
[2/20, 8:35 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ8β£9β£-9β£0β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Meyasa bazaka kalli kwayar idona ba ka gane Ina sonka shin SOJA kasan inda Nike jin ka kuwa a raina?meyasa bazaka gane ba karka tafi ka barni kasan halin da zan shiga kuwa?
Haba SOJA a da ban tab'a tunanin zan so wani Kamar amir ba Amma bansan meyasa ba ko tunanin shi banayi why?meyasa baka bari munyi sallama ba?"
Amina ne ta shigo tace"da kin San kina sonshi kika bari ya tafi da b'acin rai?Rahma ko wani soja in zaiyi tafiya Yana son ya tafi hankali kwance da tunanin matar shi na gida tana me addu'a shin kin San irin abubuwa da sukeyi dan su Kare mutane?meyasa kika me haka wallahi Yaya bai tab'a soyayya ba da a ce ya tab'ayi nasan da zai gan tsansan soyyayar shi a kwayar idonki,keda ya kamata ki koya me soyyaya inda zaije fa ko ya kashe ne ko a kashe shi kika San ko bazai dawo ba?meyasa kikayi wasa da damarki?"
Kukan Rahma ne ya karu,Sosai take kuka tana yiwa mijinta addu'a sai cewa"take Allah ya tsare ya Kare min Kai mijina na tuba"
Amina tace"Bari in Kira Miki shi nasan basuyi nisa ba in basu fita garin kano ba ya fadamin inda suke in kaiki"
Cikin kuka Rahma tace"yauwa Kira shi"
Dialling numbershi akayi bugu uku ya d'auka
Rahma tace"sojana ina kuke?"
Amma Kash matsala network ya hana Aayan ya ji magana sai hello yake cewa karshe ma wayarshi ya d'auke service baki d'aya
Kallon Abdul yayi yace"babu network ga Amina na kirana"
Abdul yace"ga nawa wayar ka kira"
Tsaki yayi bayan ya amshi wayar yace"ga wayar ka Mara amfani tunda Kai cajin waya wahala take baka"
Abdul yace"mantawa Nike in saka Kuma jiya yusura kwana tayi tana kallo dashi"
Cikin ikon Allah Suka Isa Lagos lafiya direct office sukaje
Suka fara shirya tsarin tafiyarsu Sai kusan cikin dare Suka koma gida inda washe gari da asuba suka Kama hanyar cerelion
Kwata-kwata basu samu sunyi waya da gida ba duk inda suka so Yin haka abin ya fassakara domin suna kaiwa aka turasu inda zasu Kai agaji domin Yan ta'ada sun hana mutane sakat sai dai fa wani ikon Allah rabasu akayi biyu Abdul na jagoran wasu team Aayan ma da nashi team din Wanda duk aikin Yan kungiyar Al'qibila ne dan akai Aayan wuri me had'arin gaske shiko zuciya d'aya ya tafi inda shi Wanda aka bawa kwangila kashe shi a daji ya gama shirya komai domin a ganin uche Aayan shike hanashi cigaba
Babu b'ata lokaci kowa ya jagoranci team dinshi
Rahma ko kwana tayi tana kuka ko abinci taki ci ummi tayi lallashi ta gaji sai bata baki takeyi ganin irin kukan da Rahma takeyi domin zuciyarta nauyi take yasa yusura fashewa da kuka a ganin yusura mutuwa zasuyi shiyasa Rahma ke kuka
Ummi dake rike da waya a hanun tana trying layin su amma baya shiga
Zama tayi tace".....
Yana da kyau kayi Abu a lokacin shi domin ba kowa yake samun dama na biyu a rayuwa ba Rahma kinyi kuskure gaskiya
Maman Nur
Share
[2/20, 8:36 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ9β£1β£-9β£2β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ummi tace"toh ni ya kuke so in Yi ne kunsa ni a gaba Kuna min kuka wanan wani irin bala'i ne ku tuna fa d'ana ne Nima ji nike Kamar in Yi kuka,shifa auren soja yana bukatar mutum ya Zama jaruma nima haka na kasance har Allah yayiwa abban ku rasuwa"
Yusura tayi shiru zuwa yanzu Rahma ta daina kuka zuciyarta zafi yake Mata"
Ummi tace"Rahma zo ki kwanta kina bukatar bacci"
Babu musu ta kwanta a gado ummi na shafa kanta,lumshe ido tayi
Bayan minti ashirin ummi ta tashi zata bar d'akin Rahma ta rike Mata hanun
Ummi ta juya ta kalleta
Ba tare da ta bude ido ba tace"ummi kwana nawa zasuyi a can?"
Ummi tace"sati biyu"
Ai tashi tayi tace"sati biyu? gaskiya tayi yawa "
Ummi a ranta tace"toh in tasan Basu da ranan dawowa fa?"
Rahma tace"yau sun kwana d'aya kenan ko?saura kwana goma Sha uku"har lissafi take da yatsun ta"
Ummi jikin ta yayi mugun sanyi cikin sanyi jiki tace"kwanta kiyi bacci"
Tace"umma bazan Yi bacci ba addu'a zanyi me kema ummi je kiyime kinsan ke mahaifiyarshi ne karki damu dani ummi banSan meyasa nike jin ba dadi ba gabana fadiwa yakeyi,ummi bana son komai ya samu soja"
Ummi tace"karki damu babu abinda zai sameshi inshaallah"
Barin d'akin ummi tayi ta leka d'akin Abdul hango yusura tayi tana bacci
Hamdala tayi a ranta sai dai fa bacci yusura ya fara bata tsoro
Abu dai Kamar Wasa yau kwanan su goma Sha uku Amma ko waya babu Kuma ankira be shiga domin daji suke
Rahma ne zaune dasu Amina sai murmushi takeyi tace"Amina kin iya kitso?"
Amina tace"ah'ah "
Tace"lalli fa?"
Amina tace"ban iya ba toh Mai zai hana muje saloon "
Rahma tace"babu inda zani in Kigan na fita gidan nan toh soja ya dawo na nimi izinin shi yace min bayason yawo Kuma ni bana son in b'ata me rai
Yusura ta mike taje zubar da miyau a waje ta dawo ta zauna
Amina tace"wai lafiyar ki kuwa tashin ki fa yafi goma"
Rahma ta kalleta sai Amina tace"yusura kamar fa cikine dake"
Zaro ido tayi sai Kuma murmushi ya sub'uce Mata tace"da gaske?"
Amina tace"it obvious"
Rahma ta fashe da kuka Mai cin rai
Amina tace"lafiya?"
Rahma tace"na aikata babban kuskure a rayuwa yau gashi yusura nada ciki ko ba komai ta wani fanni Abdul na tare da ita nifa?
Yusura tace"Rahma wai wani laifi kikayi ne domin kukan tayi yawa"
Cikin kuka Rahma ta Bata labarin komai ta Kare da cewa a daren da zai tafi babu irin rokona da beyi ba akan in bashi hakkinshi har kuka ya min yanzu yusura in wani abu ya faru ya zanyi wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba"
Yusura tace"inshaallah gobene zasu dawo"
Rahma tace"eh shiyasa nike son in gyra kaina wallahi in na tuna abinda ya Shiga tsakanin mu kafi n ya tafi sai inji zuciyata na zafi "
Ummi dake labe tana jinsu ta koma ciki tana dana sainin fad'awa Rahma zai dawo gobe"
Amina tace"please ku tashi muje gidan umma zaku ji dadi"
Yusura tace"wata umm?"
Amina tace"umma Rahma sun dawo kano da Zama Yaya ya basu gida"
Rahma tace yaushe?"
Amin tace"yau kwanan su goma Sha biyu da dawowa ban dai fada muku bane tunda na gan kowa na cikin damuwa"
Rahma tace"ni bazani ba sai ya dawo muje tare yace Kar inje yawo"
Washe gari tunda Rahma ta tashi sallah asuba bata koma bacci ba kicin taje ta had'a girki ta gyra part dinshi sai kamshi yakeyi cikin kayan lafen da aka kawo musu kwana biyar da suka wuce ta bude akwatin ta ciro wani dinkeken material tasa
Yusura ce ta leko d'akin tace"wow mashaallah kinyi kyau"
Tace"hmm ai da nayi kitso da lallai dana fi yin kyau"
Yusura tace"gaskiya ne ai ke kika ki zuwa ni ba gashi naje nayi ba yau nasan Abdul bazai bari in huta ba domin yasan dinkina ya warke wallahi Rahma abinfa da zafi"
Rahma dake gyra d'aurin d'an kwalinta tace"niko yau ko mutuwa zanyi sai na mallakawa mijina kaina yayi inda yaso "
Yusura tace"kayan lafe mu sunyi kyau Kuma komai iri d'aya"
Rahma tace"ai addu'a kawai zamuyi musu domin sunyi kokari"
Sauka sukayi Rahma ta zauna ummi sai kallonsu takeyi tana rasa daga inda zata fara domin Rahma sai kallon agogo take jefi-jefi tana saki sai tace" ummi har yanzu shiru"
Ai ranan anyi drama domin wuni Rahma tayi tana jiran Aayan amma shiru tana ganin magrib nayi ta fashe da kuka da tun tafiyar Aayan batayi irinshi ba
Lallashi Amina keyi ummi ko ta wuce ciki domin ta gaji
Yusura ko ta koma cikin d'aki ta bude shafin bacci
Amina ne ta taimakawa Rahma ta kaita part din Aayan domin jiri take ji
Da k'yar tayi sallah tana idarwa ta koma ta kwanta rungume da hoton Aayan
Kiran umma tayi Suka gaisa umma tace"Rahma ki godewa Allah da ya baki Miji irin Abubakar kin gan irin gidan da muke kuwa? duk harda hamza mun dawo"
Rahma ta fashe da kuka tace" ya tafi ummi be dawo ba wallahi ya tafi umma zan mutu ki Kira ki bashi hakuri"
Umma tace"Yi hakuri zai dawo kin ji?"
Katse wayar tayi domin bata jin zata iya dogon magana
________________
Abu dai kamar Wasa yau
watan su hud'u ba labari duk Wanda ya gan Rahma sai ya tausaya Mata Bata cin abinci kiriki domin kullum da azumi take tashi in kuma lokacin bude baki yayi be wuci ta Sha tea ba
Ummi ne zaune a falo tasa su gaba sai sun cinye abincin plate dinsu sai fada takeyi
Tace"ke yusura ko baki ci Dan kanki ba ai Zaki ci Dan abinda ke cikin ki haba kasheni zakuyi toh wallahi bazan iya ba yau zaku tafi gidan umman ku
Rahma dake kuka sosai tace"ummi wallahi azumi nikeyi"
Ummi tace"yau sai kin karyashi ai bana Wasa dake"
Rahma ta b'are baki tana kuka tace"wallahi baki Sona ummi in soja ya dawo sai na fad'a me ya tafi dani"
Dariyar dole ne ya sub'ucewa ummi sai Kuma ta hade rai
Yusura ta kwabe fuska tace"ni na koshi"
Ummi