rigar ki domin on Saturday zamuyi reception ranan lahadi Kuma mazaje sun had'a Mana party a barrac. .."
Katseshi tayi tace"dakata d'an rainin wayau ya Ina tambayar ka kana min maganar rainin hankali meyasa ka rabani da me Sona?"Kara canza topic yayi da cewa"yusra lallin ki yayi kyau duk ni nine da wanan kwaliyar?"
Kara kunnata yayi ta mike tare da fashewa da kuka tace"Allah ya isa tsakanina da kai mugu kawai azzalumi"
Murmushi gefen baki yayi daya Kara me kyau yace"ki bani size din sauri nike akwai shirye-shirye"
Tace"ban badawa munafuki allah"
Yace"toh bari in Kira Abba"
Tace"takalmin 39ne gown din Kuma 20"
Yace"good girl
Tashi yayi ya zauna kusa da ita yace"baby me kike shirya min a daren mu na farko?"
Kallonshi tayi ta janye hanunta tace"sakeni munafuki kawai"
Murmushi yayi yace"ko dai abin sirri ne sai a turaka?" Ya Kare magana da kashe mata ido
Wani haushi ne ya kamata sai ta fashe da kuka tana dire-dire
Natsuwa yayi Yana kallon shagwab'ata Kamar Yar baby
Yace"
Anty shamsiya da sis khady team soja ni Kuma team lecturer Nikeππππin na gan dama in bawa soja in nagan dama lecturer
Maman Nur
Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
Dedicated to my fans
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
π‘ *N W Aπ‘*
Lightning and bringing smile to your world is our perority
*NUR WRITERS* ~it a beautiful~ ~world~
π
Ώ3β£1β£-3β£2β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yace"yus ai ba sai kin fara yau ba ki hakura gobene fa sai kiyi shagwab'a a jikina hankalin ki kwance"
Hararanshi tayi tare da mikewa tace"mugu kawai"
Hanunta ya kama ta fisge tace"karka Kara tab'ani"
Yace"kina nufin in Bari sai gobe kenan muyi Mai gaba d'aya?"
Cikin jin haushi ganin in ta b'ulo ta nan saiya fitota wani wuri"
Tace"nifa bana son iskanci fa ni ba a koya min iskanci a gidanmu ba'
Murmushi rainin hankali yayi yace"da ma koyawa mutum akeyi?ai ji mutum yake a jikin shi Amma in ke baki jin feelings kiyi hakuri zan koya Miki"
Tsaki tayi,sai ya buge Mata baki yace"karki Kara min tsaki bani son rainin "
Kara jan wani dogon tsaki tayi tana wani irin janshi tana turo baki tace"in bakaso sai ka fasa auren "
Murmushi yayi yace"baby sake Jan tsakin ta Miki kyau wallahi ni gaskiya a ta jamin kullum "
Cikin haushi ta fashe da kuka murmushi yayi a ranshi yace"duk abinda bana sonshi zanyi ta nuna Miki Ina so Wanda nike so Kuma in nuna Miki bana so"
Har zata fita a falo sai taji yace"ki shirya da yamma zamuje muyi hoto zanzo in d'auke ki zan zo da kayan da Zaki sa kuma babban hijab Zaki sa domin banason kowa ya gan lallin da akamin na amarci"
Tsaki tayi ba tare da ta amsa ba
Yace"yus in kikayi tsakin nan sai in ji kamar in rungume ki domin jin sonki Nike har zuciyata"
Har zatayi tsaki sai ta tuna faranta me take in tayi tsaki
Yace"ki shirya sai na zo"
Tace"babu inda zani"
Yace"toh zan fad'awa Abba"
Sai tace"karfe nawa"
Yace"karfe takwais Kuma bana son kiyi kwalliya domin banason kowa ya kalle mini ke,nafi son ki bini da kumburaren idonki in so samu ne ki wuni kina kuka domin idon su Kara tashi"
Bata kulashi ba ta shige ciki ya bita da kallo yana murmushi
Tana wucewa ya bar gidan
Bayan su general sun bar gidan direct gidan su Rahma sukayi inda suka aika yaro ayi musu sallama
Kawo da ya kwanta a taburma Yana jira ga yunwa domin umma share shi tayi
Yana ganin yaro ya fara kwalawa umma kira yace"sun iso maman Yan biyu"
Kafin ta fito ta bashi amsa har ya fita waje yayi musu izo da su shigo kafin ya dawo har umma ta shimfide taburma
Zama sukayi itadai tayi mamakin ganin malam haruna
Har kasa Aayan ya sunguna ya gaida umma ya kasa d'agowa ya kalleta itako sai murmushi take domin tana son mutum me kunya hakan yasa itama kunya ya kamata
Malam haruna yace"Ina fatan malam Musa yayi Miki bayanin komai?"
Kafin ta bada amsa kawo yace"ai tun safe Nike Nan na Mata bayani Kuma ta amince"
Gyran muryar malam yayi yace"nasan a ka'ida be kamata mu sameki ba Amma mun amsa gayyatar ki ne bisa bukatar ki na son ki gan angon toh sai mu ka duba Kuma muka gano kina da hakki akan yar'ki kuma Zaki so a ce kin San inda za a Kai yarki toh da farko dai nasan kin sanni Amma bari in Kara gabatar da kaina sunana malam haruna nine Wanda zai tsayawa Abubakar ki kwantar da hankalin ki yar'ki hanun ta gari zata shiga"
Umma duk sai taji nauyin su ga kunya ya lullubeta ga wani kallo da dattijo general ke mata Kuma ta yaba da tarbiyyar Aayan
Kawai sai tace"babu komai kawunta zaiyi komai Allah ya Sanya alkhairi "tana gama magana ta shige d'aki ta barsu
Duk sukayi murmushi kawo ya kallesu yace"yanzu za a d'aura?"
Hararanshi Aayan yayi kasa-kasa sai yace"eh na tuna sai gobe"
General yace"sai goben kenan mu had'u a massalacina"
Kawo yace"angama"
Tashi sukayi Aayan shima ya tashi
Sai general yace"yi zaman ka ka gana da amaryar taka baza ku rasa abin Fadi ba tunda abin ya zo ba shiri"
Zama Aayan yayi cikin jin kunya yayiwa su malam godiya
Bayan kawu ya dawo daga rakiya Aayan ya kalleshi yace"Ka maida musu kayansu da kudin da Suka kashe ko kuwa?"
Kawo ya fara in Ina Aayan yace"amsa nike jira"
Kawo yace"ai kasan asara ce a maidamusu ai su Suka ce basu son auren bamu ba dan haka komai ya Zama namu"
Aayan ya kalleshi daga sama zuwa kasa silipas ne kafanshi ga uban kaushi da pasau ga shaddan Nan yayi bakin kirin
Tsaki yayi yace"shiyasa baka cigaba duk cutar mutane da kakeyi baka arziki,yanzu dai ka maida musu kayansu domin ni ba matsiyaci bane kuma karka Bari in samu labarin baka maida musu ba"
Yace"toh yallabai Amma maganar filin tana nan ko?"
Wani kallon Aayan yayi me sai ya natsu yace"Bari in kira maka ita Ramatu bacci take zazzabi na damun ta ne"
D'akin ya shiga Kamar an koroshi umma ta harareshi
Ganin Rahma zaune ta jigina da bango tana hawaye
Hamdala yayi yace"ummana ki saka hijabi ki fito ana jiran ki"domin Rahman sunan mahaifiyarsu gareta
Umma tace"tashi kije kinji Rahmatu na"
Itadai Bata fahimci meke faruwa ba mikewa tayi jiri na d'ibarta umma ta sa Mata hijabi
Ganin tana tafiya a hankali yasa kawu cewa"ummana ko in d'auke ki ne"har ya karasa
Umma tace"ah'ah ya haka?"
Yace"wai da in taimaka mata"
Itadai umma harya isheta Allah Allah take ya bar Mata gida
Rahma na ganin uku-uku ta isa gaban Aayan ta zauna
Kawo ya zo ya zauna kusa da ita ya sata a tsakiya
Wani kallo Aayan yayi me sai kawai yace"da wai kasawa zanyi in tsare kar tace Bata sonka kasan ummana akwai kafiya"
Umma data fito d'aukar wani kwanu kawai ta gan kawu zauna
Tace" wai ya haka?"
Yace"kamar ya?"
Tace"toh ai na gan ka wani samu wuri ka zauna da sirikin ka ko da Kai za ayi zancen?"
Yace"yanzu zan tashi"
Rahma ko tunda kawo ya anbaci aure ta fara harhad'a kalaman su har da umma tace"siriki"
A fili tace"wai meke faruwa ne?"
Kawo yace"ai shine mijin da Zaki aura ki rabu da wanan d'an isakan"
Shidai Aayan beyi magana ba amma a ranshi cewa yake ita Bata gaisuwa ne watoh dan raini so take in gaisheta"
Maganar Rahma ne ya dawo dashi duniyar tunanin shi da yaji tace"aure kuma?me Kuma ya samu my Aamir kuyi hakuri wallahi ni nasan gobe my Aamir zaizo nasan yasan halina bazai tab'a yarda da wanan videon ba"
Kawo yace"wanan yariyar da bakin ciki take"shiko Aayan ranshi ne ya mugun b'aci a ranshi yace"kamar ni a ce dan rainin hankali tana maganar wani a gabana"
Umma tace"watoh Rahma ban Isa ba?bana hanaki kiran sunan shi ba?"
Ai ji sukayi ta gangara jikin Aayan summamiya
Umma tace"subhannallah"
Kawo yayi maza zai d'agota sai ya ji hanun maza ya
Please yau ku min afuwa wallahi aikine yamin yawa kwanan nan sai kuyi hakuri da inda posting zaiyi ta zuwa muku Amma zan kokarta a min uzuri please
Maman Nur
Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
Dedicated to ummu Yasmeen novel group
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
π‘ *N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR ~WRITERS* ~it a beautiful~ world~
π
Ώ3β£3β£-3β£4β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Rike me hanun yayi gam da yasa kawo sake tusa domin tusar sub'uce me yayi
Umma cikin b'acin rai domin yau kawo ya Gama ba da ita
Tace"wallahi anji kunya a ce a gaban siriki ake Banka tusa"
Yace"da kin ji rabin abinda na ji ke har kashi zakiyi "hanun maza fa naji
Umma zatayi magana sai Aayan yace"umma dan Allah in akwai socks kusa a bani"
Umma tace"me za ayi dashi"
Be tanka ta ba ya fara gyrawa Rahma hijab
Su Hassan ne Suka shigo da gudu dawowarsu daga makaranta
Zama Hassan yayi Yana cire socks hussaini ko tambaya yake akan meya same anty Rahma
Socks din da Hassan ya cire shi Aayan ya d'auka yasawa Rahma
Sai a lokacin umma ta fahimci desighn dinta ne beso a gani murmushi tayi
Yace"umma muje asibiti"
Tace"ah'ah ba sai munje ba bari in d'auko ruwan sanyi domin daga jiya zuwa yau sumanta be kirguwa Kuma ruwan sanyi nike watsa Mata"
Kawo ko a ranshi cewa yake" ki tashi Rahma filina na hanun ki "
Umma na zuwa ta watsa Mata ruwan
Wani numfashi ta ja sanan ta bude idonta
Kawo yace"sannu dan girman Allah karki Kara sumewa in ba haka ba nima zan biki yau ma a gidan ku zan kwana Kar cikin dare ki sume a rasa me taimako"
Umma tace" ikon Allah ka tafi mun gode sai goben kenan"
Aayan ya harareshi ai sai kawo yace"wallahi Allah ya dibewa yaron nan albarka yanzu Dan shiga hakkin ya kakabawa yariya sharri dake sumar da ita "
Aayan yace"me akayi Mata?
Yace"ai video akayi mata da wani gardi ni na tabbata ba ummana bace"
Aayan ko a ranshi yace"Allah yasa ba jibrin bane kodai plan din da yace kenan?"
Kuka Rahma ta fashe dashi tace"Dan Allah ka daina tsineme bashi da laifin ni na San shiga tsakanin mu dashi akayi Kuma wallahi bazan tab'a yafewa ko waye keda hanun a ciki ba"
Ji yayi gabanshi ya fadi
Mikewa yayi yace"umma ni zan tafi zan turo likita a dubata "
Yana gama magana ya ja hanun kawo suna fita yace"tafi gida ya Isa haka"
Zaiyi magana ya katseshi da cewa ka tafi ko insa a Zane ka"
Yace"tuni na Kai gida"
Jibrin ya zo ya d'auke shi suna kaiwa guest house
Ya kalli jibrin yace...
Maman Nur
Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITER ASSOCIATIONπ‘π*
π‘ *N W A* π‘
*Lightning and bringing smile to your world is my peority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
π
Ώ3β£5β£-3β£6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Kallon jibrin yayi yace"what exactly do you do da yasa aka fasa auren Rahma?"
Jibrin yayi murmushi ya tsara me kafin yace"sir it was a simple plan"
Aayan ya gyra Zama yace"Iam interested"
Jibrin cikin jin dadi ya bashi labarin komai harda nuna me video
Ji yayi jinin shi na tafiya a 360 ganin wani saman Rahma yasa ranshi mugun b'acewa
Mikewa yayi ya kaiwa jibrin wani mugun pounch kawai jini ya b'ale me
Aiko be kyalleshi ba ya dinga naushi Amma ba halin gudu
Neel down yayi,shigowar Abdul ne yasa ya kyaleshi yace"kasan abinda ka aikata kuwa?kasa mutane na Mata kallon Yar iska,you defame her above all ka kawo wani kazami ya hau jiki Rahma"
Jibrin yace"kaifa ka ce at all cost"
A fusace yace"will you shout your dirty mouth"
Abdul yace"toh me kake so yayi inda beyi haka ba da yanzu kana gadon asibiti an d'aurawa Rahma aure da wani"
Wani kallo yayiwa Abdul yace"ai da ya fad'a min dana sa abinyi"
Kallon jibrin yayi yace"yau ka koma Lagos a can zan hukunta ka"
Jibrin ya tashi ya tsara me sanan ya bar wurin
Wanene Aayan?
Major general Abubakar mohammed jabir Amma ana kiran shi da Aayan Yana domin sunan kakarshi ne dashi d'an ne ga marigayi late general Mohammed jabir da mahaifiyarshi dr Maryam su asalin Yan garin kano ne hausawa ne
Su biyu iyayen su Suka Haifa dashi da kanwarshi Amina
Aayan a kano aka haifesu inda tun Yana da karanci shekaru mahaifin shi ya turashi N D A watoh Nigeria defence academy tun yana karami yake samun horo me sanani
Aayan Yana da mugun girman Kai Kuma miskili ne na ajin farko shi a rayuwar shi ya tsani raink Amma Kuma shi Yana da rainin wayau da wuya ka gan Yana da dariya sai dai in su biyu ne da ummishi ko da babban aminin shi Abdul Wanda shima ba kullum yake ganin dariyar shi ba ga shegen miskilancin tsiya wanan dalilin na cikin abinda ya hanashi aure domin a ganin shi macece zata ce tana sonshi Amma yafi karfin yayi ta bin mace shiyasa in yayi budurwa Wanda su din ke nuna suna sanshi in sun gaji sai su rabu domin be Basu kulawa ko kiran su beyi
Tun suna kanana Suka kulla abota da abokin shi Abdullahi mansur (Abdul )Wanda tun abdul na karami yake da sha'awar aikin soja amma da yike rayuwar yanzu in Kai ba kowa bane makaranta ma gagaran talaka yakeyi domin shi Abdul iyayen shi ba masu Hali bane kuma maraya ne domin a wajen haihuwarshi mahaifiyarshi ta bar duniya ya taso ne cikin ukuba da matsifar kishiyar uwa Wanda kwata-kwata bata sonshi a gidan ta mayar dashi jaki Kuma mahaifin shi be isah yayi magana ba kasan cewar sai inda akayi dashi
Ba karamin wahala ya Sha ba gidansu Aayan kawai yake zuwa ya ji sauki a lokacin da Aayan ya tafi NDA duniya tame mugun zafi shima Aayan haka bejin dadin makaranta a daddafe yayi shekara d'aya a shekara na biyu ne ya tursasawa Abba shi ya tsayawa Abdul shima ya shigo makaranta
Kowa a makaranta yasan da abotansu duk da Aayan yayi senioring dinshi da one year
Sai dai sun mayar da hankali sosai a karatu suna abinda ya dace
Cikin ikon allah Aayan ya fara graduating inda ya fito da second lieutenant
Aayan jami'i ne Mai hazaka da sanin aikinshi shekara na zagayo Abdul yayi graduating duk a Lagos aka tura su aiki basa rabuwa da juna sai dai hallayensu ya bambanta domin shi Abdul Yana da fara'a shi Kuma Aayan babu dariya a tsarin shi
Ganin yau abdul ya Zama wani abu yasa ladidi fara shishshige me karshe ma sai ya fita harkarsu ya bar gidan mahaifinshi sai dai duk wata Yana aika musu kayan abinci ana cikin haka ne sai Allah yayiwa abbanshi rasuwa
Mutuwar ya girgiza shi domin baba ne kawai ya rageme a duniya besan Yan uwan ummashi ba kuma Yan uwan abbana shi a kauye suke"
A haka rayuwa ta cigaba da ta tafiya inda cikin ikon Allah Suka Kai wani matsayin babba a aikin soja
Sai dai kuma wata rana aka samu gawar general abban Aayan a office an bindige shi saboda ya kasance mutum ne me son gaskiya hakan yasa na gaba dashi dama kasa dashi Suka tsaneshi domin ya hanasu musgunawa talakawa kuma ya hana ayi ta kashe su
ana hakane wasu kungiyan Yan ta'ada da Suka adabi al'uma masu suna *Alkibila* Suka nimi ya had'a hanun dasu Amma yaki Kuma sai ya fara bincike akan kungiyar a b'oye har ya gano shugaban Wanda be tab'a tunanin Yana da hanun a kashe dumbin jama'a ta hanyar sa musu bomb Amma a zahiri mutane na ganin shi mutumin arziki
Wanan kungiya ya tara manyan kasa Kama daga minister senators da Yan kasuwa yan siyasa jami'an tsoro da sauransu
Tun wanan ranan Aayan ya d'aura d'anmara Kuma ya Sha al'washi sai ya kunyarta da duk wani Wanda keda hanun a kisar abbanshi sai yasa ya fuskanci hukunci Kuma sai ya tarwasa kungiyar *Al'qibila* yanzu wanan shine babban burin mazajen nan biyu Wanda yanzu Aayan ya Kai major general shikuma Abdul brigadier general
Aayan fari ne sol Yana da kwarjini sab'anin Amir dake da baby face shima Abdul farine Amma be Kai Aayan ba Domin farin Aayan har jaja yakeyi
Aayan Yana da skekara arba'in shikuma Abdul Talatin da Tara
Wanan kenan sauran bayani sai Nan gaba
*Cigaban labari*
Please ignore any errors
Maman Nur
Share
[2/20, 8:26 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITER ASSOCIATIONππ‘*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our peority*
*NUR WRITERS* ~it a beautiful~ ~world~
Dedicated to zainab Hassan Ina jin dadin comment dinki
π
Ώ3β£7β£&3β£8β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Bayan jibri ya bar gidan Abdul ya kalli Aayan yace"yanzu miye abinyi domin mu kanmu musan masu laifine mun zalunce matan nan me zamuyi dan goge lafin mu"
Aayan yace"wani laifin?ai babu ko wani laifin da nayi everything is fair in love and war,Kuma bazan Bari yar tasisiyar yariya ta raina ni ba kuma ai itama tayi laifi kuma zan hukunta ta na kiran sunan wani yaro a gabana"
Abdul yace"lallaima ka duke ta ka Hanata kuka niko kulawa zan bawa yus dina har sai ta fara Sona da kanta tunda nasan ni me laifine"
Tabe baki Aayan yayi yace"Ashe zaka jawowa kanka raini ni ba wani lallab'ata da zanyi casa juna zamuyi daga baya mu shirya most important thing na aureta"
Abdul yace"nidai ba ruwana in tayi tsami kowa nashi ta fishe shi"
Da misalin karfe 8:pm Abdul ya fita direct gidan su yusura yayi Walid ne yayi me izo daya shigo ciki gidan falon Abba ya kaishi suka gaisa
Walid ya shiga cikin dan Kiran yusura
Yusura ne zaune bakin madubi ta tsara kwaliya tayi masifar kyau fashe jikinta tayi da tulera
Tace"aini abinda baka so shi zanyi tayi Kuma wallahi babu wani hijabi da zansa haka zan bishi dan ni ba umurnin shi zanbi ba "
Gylen abayanta ta d'auka tayi rolling
Walid ne ya shigo d'akin yace"kizo Yana jiran ki"
Kallonshi tayi tace"Yaya yanzu ka kyauta kenan?a matsayinka na yayanah ka bari a ka had'a baki da kai akamin sharri?kai ka Kara d'aurewa wanan munafukin gidi ya min sharri Kaine ka ce ka ganni ina rokonshi harda auwal"
Walid yace"ke yimin shiru ya min alkawarin zai kaini kasar waje"
Yusura tace" yanzu saboda kasar waje za a had'a baki da kai a cuceni?"
Wucewa yayi ya Barta da takaici kasancewar shi Yaya a gareta babu sallama ta sameshi a falon abba
Karasawa tayi cikin hade rai ta zauna
D'angowa yayi ya kalleta dariya na niman sub'ace me ganin tayi kwaliyya watoh dan ta b'ata ranshi tayi Bata san abinda yake so ba kenan
Gimtse dariyar shi yayi yace"baby ba gaisuwa ne?"
Tace"eh babu"
Murmushi yayi yace"ai nasan kunya kikeji domin na gan kunyar a kwayar idonki yus ashe bana ce karkiyi kwalliya ba"
A fusace tace"anyi kwaliyar ubana ne kai da zaka bani umurni in bi?nifa bana son ana takurawa rayuwata dan haka karka matsa min "
Murmushi yayi yace"tashi muje"
Tashi tayi tabi bayan shi sai kunkuni take shidai murmushi yakeyi"
Ya bude mata mota
Ko kallonshi batayi ba sai latse waya take
Yace"kefa Nike jira ki shiga"
Tace"ban gama abinda nike bana in na gama zan shiga charting nike da my Umar"
Ranshi ne ya b'ace amma sai yayi controlling yace"ki shiga pleaee dare nayi"
Sai a sanan ta shiga ya ja motar tuki yake yana satar kallonta murmushi takeyi jefi-jefi
Aiko ta balai'n sosa me rai a haka suka isa studio
Da k'yar akayi hotuna uku domin yusura cewa tayi bazata tab'a shi ba kuwa haka ya kasance karshenta wani style sukayi Kuma yayi kyau
Suna Gamawa suka fito sit motar babu me magana
Yana kaiwa wani joint na sayar da nama kaza ya tsaya ba tare da yayi magana ba ya fita
Siyowa yayi Koda ya dawo waya ya gan tanayi sai murmushi takeyi beji me take cewa ba kawai ya fisge wayar a fusace ya fincikota yace"yus ni Zaki kawowa iskanci dawa kike waya?"
Tace"babu ruwanka malam ka bani wayata"
Murmushi yayi ya ajiye wayar kasa ya fara takewa har yayi rugu rugu"
Kuka ta fashe dashi tana Allah ya isah
Shiko be kulata ba saima Jan motar da yayi ya maida ta gida a kofar gida yayi parking har ta bude zata fita sai taji yace"in kika Kara taku d'aya ranki zai b'ace"
Kallonshi tayi sai tace"toh kayi hakuri"ta Kare magana tana turo baki
Lumshe ido yayi ya bude yace"yus meyasa kika Raina ni?"
Shiru tayi tana Wasa da yatsun hanunta
Hanun ya Kama Yana murzawa yace"talk to me yus"
Tace"saboda Kai munafuki ne makaryaci ka had'ani da iyayena,ka rabani da masoyina Umar ni BANA SONKA na tsane ka"ta Kare magana da fashewa da kuka Yi yayi kamar beji ta ba sai ma rungumota da yayi ya bude tab dinshi yace"yus ki zab'a nan dubai ne cikin hotels dinan guda biyu wanne kike so muyi honeymoon"
Jan Jikinta tayi domin ta Kara tabbatarwa d'an rainin hankaline har zata fita sai kuma ta kalleshi
Tace"ya Kuma maganar makaranta na tunda ka ce kano zamu koma ya zanyi?"
Be kalleta ba balle tasa ran zai bata amsa
Tace"da kaifa nikeyi domin wallahi semester d'aya ya rage min bazan Bari a cuce ni,toh nidai na fad'a ma "tana gama magana ta wuce fuuuuuuuuu kamar iska "
Murmushi yayi yace"aini a Sarina babu maganar makaranta watoh so kike in ajiye ki saboda ki samu damar kula d'an isakan nan "
Yana gama magana ya bar anguwan
B'angaren Aayan ko
Maman Nur
Share
[2/20, 8:27 PM] Maman Noorul Hudah: ππππππ
*BANA SONSHI*
ππππππ
_By maman noorul_
_Hudah__
*ππ‘NUR WRITERS ASSOCIATIONπ‘π*
*π‘N W Aπ‘*
*Lightning and bringing smile to your world is our perority*
*NUR WRITERS* ~it's a beautiful~ ~world~
Dedicated to Anty Shamsiya
π
Ώ3β£9β£-4β£0β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
B'angaren Aayan ko bayan Abdul ya fita yaji duk hankalinshi ya koma wurin Rahma
Tashi yayi ya shirya cikin blue jeans da farin polo
Makulli ya d'auka sai gidansu Rahma a kofar gidan ya paka mota
Ya shiga da sallama umma ne zaune a kofar d'aki tana d'ura sobo a gora
Karasawa yayi har kasa ya sunguna ko iya kallonta beyi ba kunya yake ji
Tashi tayi tace"Bari in kirata"be amsa ba ya bar kofar d'akin
Hassan ne ya fito ya rungumeshi Yana dariya HUSSANI ko kallonshi yakeyi Amma beyi magana ba
Umma na shiga ta tarar da Rahma zaune yau ba laifi jikin da sauki
Tace"kije yana waje yana jira ga makullin d'akin hamza ki bude"
Tashi tayi ta saka hijabi ta amsa makullin domin Bata son fad'an umma
Fitowa tayi taje ta bude d'akin hamza ta Shiga ta zauna
Shiko ranshi ya mugun b'ace domin yi tayi kamar bata ganshi ba balle ta gaishe shi har tace"ya shiga hakan ya b'ata me rai
Amma sai ya basar ya shiga ciki
Zaune ya ganta bakin katifa
Kin Zama yayi Yana jira tace"ya zauna"itako ta basar dashi kamar bata San ya shigo ba
A ranshi ko cewa"yake oh ni take son in fara Mata magana?Ashe zamu dawwama a nan kenan"
Itako lumshe ido tayi a haka har sukayi minti talatin Kuma yana tsaye
Jin shiru yasata cewa"tunda baka da abin fadi zanje in kwanta bacci nikeji"mikewa tayi zata tafi ya jawota har ta fad'a kirjin shi rungumeta yayi Gam sai ajiyar zuciya yake saukewa kokuwan kwace kanta takeyi Amma ta kasa
Yar Kara ta sake tace"live me you are hurting me "sai a sanan ya dawo hankalinshi ya saketa cikin jin kunya yace"in zakiyi tafiya kiyi ta kallon gaban ki bawai kiyi ta rungume mutane da sunan Zaki fadi ba"
Cikin mamakin shi tace"excuse me malam kaifa ka jawo ni ka rungume bani na rungume ka b..."
Katseta yayi da cewa"oh nayi laifi dana taroki Zaki fadi?"
Tsaki tayi tace"I don't have your time bacci nikeji"
Yace"ai baki Isa ba zama zakiyi sai na ce ki wuce"
Tace"malam karka manta nan gidan mu ne I call the shut here"
Zama yayi ya hade kafa yace"ki tsaya kiji jibi zamu tafi so Ina son in kind'aya Miki sharudda ne na farko kisa socks in za a zo d'aukan ki muje mota na kawo Miki hijabi"
Tace"toh yau na gan ubana Kai wani irin mugune ni nace Ina sonka ne balle ka wani kindaya min sharudda?"toh in ma mafalki kake ka bude idon ka domin ni Rahma"ta nuna kan bazan tab'a sonka ba"
Tana Gama magana ta wuce ciki
Shiko yace" ashe haka ta raina ni?toh zanyi maganin ta"
Tana shiga ciki umma tace"ya na gan kin dawo?ke Rahma haka akeyi kin barshi maza ga abinci ki Kai masa ki ciro sobo a fridge ki Kai