sau duhu daga sallar Asuba zuwa faxuwar rana.
**
Bayan su zuhairu sun yada zango a kusa da inda suka
yaqi sansanin na biyu, suka kwana da gari ya waye suka yi
sallah Asubahi suka yi shiri suka ci gaba da tafiya. Suka sake
yin tafiya har ta kwanaki uku, sannan suka iso inda sansani na
qarshe yake wato Darul mautu wanda daga shi sai fadar
matsafi Bahalu.
Da suka isa inda wannan tsauni yake suka yada zango a
bayansa don su huce gajiya su kuma shirya sosai yadda za su
kai farmaki akan wannan sansani, da yake sun gama fahimtar
yadda za sy riqa samun nasara akan wannan barada sai suka
bari sai da tsakar dare, sannan suka tafi cikin duhun itatuwan
da ke kusa da tsaunin suka voye. Yadda baradan ba za su gansu
ba, suka soma kai farmaki akan su cikin duhun darebayan sun
kashe hasken manyan fitilun da suka haske wajen.
Su zuhairu sun samu nasara matuqa kamar yadda suka
so, sai dai an xan samu tsaiko da turjiya daga sansanin baradan
inda suka jajirce da nuna juriyarsu ta qoqarin da tabbatar da
tsaro da kiyayewa akan fadar matsafi Bahalu, suka kuma
120
BAKAR GUGUWA
fahimci daga inda ake kai hari akan su duk da tsananin duhun
dare, don haka suka tasarma wajen da su zuhairu suke voye
cikin duhun itatuwa da nufin hallaka su abinda ya haifar da
artabu da arangama mai matuqar muni, har mutum biyar daga
cikin jaruman da suke tare da su zuhairu suka hallaka ita kuma
Buniyatu da wasu jaruman su shida suka samu munanan
raunuka.
An yi xauki-ba-daxi, artabu da baqin gumurzu mai
tsanani a tsakaninsu kafin zuhairu ya samu nasarar kaiwa inda
wannan gunki da suke bauta a gare shi yake ya sare kansa da
takobinsa. Wanda sare kan gunkin ne ya kawo qarshen turnuqu
da baqin gumurzun da ake kwafsawa a tsakaninsu. Gangar
jikin gunki ta kama da wuta, tsaunin da ke wajen ya yi qara da
rugugi mai tsananin qarfi ya fashe. Tartsatsin wuta ya yi tsiri
ya tashi sama ya riqa watsuwa a jikin baradan da ke wajen
suna kamawa da wuta, suna qonewa, suna hallaka. Baradan
suka yi matuqar firgita da razana mara misaltuwa saboda ganin
abinda yake faruwa, suka yi nufin su arce don tsira daga
hallaka sai dai babu wanda ya samu damar kuvuta daga cikinsu
har sai da feshin wutar nan ya riske su,ya qarar da su baki xaya
suka qone qurmus. Ba a kawo qarshen wannan arangama ba
har sai da kusan asubahi bayan ketowar alfirjir.
Su zuhairu suka yi godiya ga Allah bisa ga nasarar da
suka samu na karya wannan rundunar baradan. Suke nemi
ruwa suka gabatar da sallah Asubahi, sannan suka xauki
gawarwakin ‘yan uwansu da suka hallaka suka yi musu sallah
suka binne su. Wanda suka samu raunuka aka yi musu magani,
suka matsa kusa da wani rafi suka yada zango a wajen, daga
inda suke suna hangen Darul sabar inda matsafi Bahalu yake
121
BAKAR GUGUWA
an zagaye ta da manya katangu masu matuqar tsawo da kauri.
Akwai qofa ta baqin qarfe da ke farko a kulle daga vangaren
da suke.
Da gari ya gama wayewa sosai rana ta fito sai zuhairu
ya dubi Buniyatu da sauran jaruman da suke tare da su yace da
su.
“Tunda Allah ya nufe mu da samun nasarar isowa inda
wannan fada take, sai ku tsaya anan gaba xayanku ku jirani a
wannan waje,ni kuma zan je na shiga fadar don yaqar matsafi
Bahalu na kuvutar da Gimbiya Hasima daga hannunsa, ku ci
gaba da yi mini addu’a don fatan samun nasara, tare da jinyar
wanda suka samu rauni har zuwa sanda zan dawo, idan na
samu nasara akan wannan shu’umin matsafi cikin yarda Allah”.
Buniyatu da sauran jaruman da suke tare da zuhairu
suka amince da wannan shawarar tasa. Da su zauna a bakin
wannan rafi su jira shi har ya dawo, suka yi masa addu’a ta
fatan samun nasara, sannan zuhairu ya tashi ya kama hanyar
tafiya ya tunkari inda wannan fada take.
Da isarsa inda qofar fadar take ta farko ya dubeta da
kyau. Ya ga an yi ta ne da xanyan baqin qarfe, yadda babu
wani abin hallita daga jinsi mutum ko aljani da zai iya karya
qofar ya shiga cikin fadar komai qarfinsa na jarumta da
sadaukantaka. Ya sa hannu ya fiddo da mukullin da Boka
Afrahu ya basa daga xamararsa ya saka a jikin qofar ya murxa
a hankali. Qofar ta xan yi qara a hankali, sannan ta soma ja da
baya tana buxewa da kanta. Zuhairu ya zare makulllin daga
jikin qofar ya maida xamararsa sanda qofar ta gama buxewa da
kanta, sannan ya zare takobinsa ya ja daga bai yi gaggawar
shiga qofar ba, kamar yadda aka aka umarce shi. Ya yi saurare
122
BAKAR GUGUWA
don ganin abinda zai fito daga cikinta ya gama da shi kafin ya
kai ga shiga ciki.
Huci ya fara ji irin na tahowar iska da ke cuxanye da
mutsanancin zafi kamar tiriri ya bugo daga cikin qofar sannan
sai ga wani qaton baqin maciji mai matuqar girma da kauri ya
fito daga cikin qofar a fusace, ya fasa kai girmansa ya zarce na
macijiyar da suka hallaka a cikin ruwan kogin da suka wuce
kafin su shiga lardin Ashtar. Zuhairu ya yi sauri ya sanya
takobinsa cikin azama da zafin nama ya sare kan baqin macijin
tun kafin ya kai masa sara. Macijin ya yi wata tsiwa ta azabar
fitar rai ya zube qasa matacce. Wani irin baqin jini mai kauri
da yauqi ya zubo daga inda zuhairu ya sare kan macijin.
Sannan sai macijin ya riqa narkewa yana zagwanyewa har ya
zama jini gaba xaya.
Zuhairu ya sake tsayawa a wajen yana saurare.ko zai
sake ganin wani abin cutarwa ya fito daga cikinta, amma har
aka xau lokaci mai tsawo babu abinda ya sake fitowa daga
cikinta. Daga nan sai ya tafi gareta ya shiga ciki, babu abinda
ya gani a tsakanin wajen illa wata doguwar hanya ta miqe ya
zuwa qofa ta gaba. Ya bi wannan doguwar hanya da ta miqe ya
ci gaba da tafiya har ya isa inda qofa ta biyu take.
Yana isa wajen ya iske qofar a buxe kamar yadda aka
sanar da shi, tun kafin zuwansa. Yana iya hangen abinda yake
cikin qofar daga inda yake akwai wasu bishiyu na ‘ya ‘yan
itatuwa masu zaqi na marmari tare da furani masu matuqar
qayatarwa ga wasu fararan tsuntsaye suna shawagi a sararin
subahana tare da sauka daga wannan bishiya ya zuwa waccan
bishiya. Ya hangi wani xawisu yana tafe a qasa daga cikin
qofar ya taho zai fito waje ya zuwa inda zuhairu yake.
123
BAKAR GUGUWA
Zuhairu ya yi sauri ya lave daga gefe inda xawisun ba
zai ganshi ba. Ya xara hannunsa akan takobinsa har zuwa
lokacin da xawusun ya iso gare shi. Yana fitowa daga cikin
qofar sai zuhairu ya xaga takobinsa ya sari xawisun ya raba
kan shi gida biyu. Gashin jikin xawisun ya fatattake ya tashi
sama, tamkar auduga a cikin iska, wani abinda ya bawa zuhairu
mamaki da al’ajabi shi ne; duk inda gashin xawisun ya zuba a
qasa sai ka ga qasar wajen ta kama da wuta ta qone qurmus ta
yi baqi, saboda musiba.
“Wa’iyazubillahi” Ya ce a zuciyarsa don neman tsari da
wannan masiba sannan ya wuce ya zuwa inda qofar take.
Bayan ya iso gare ta ya maida takobinsa ya kama qofar
ya rufe kamar yadda aka umarce shi. Sannan ya sanya mukulin
da aka ba shi ya murxa a hankali qofar ta buxe da kanta.
Zuhairu ya zare makullin ya maida a xamararsa, sannan ya
shiga cikin qofar ta biyu. Da shigarsa sai ya ga babu wannan
bishiyu, tsuntsaye da furanin da yake hange tun da farkon kafin
ya shigo. Sai dai wata doguwar hanya da ta nufi inda qofar
qarshe take makamanciyar wadda ya wuce a baya. Ya bi
hanyar ya ci gaba da tafiya har ya isa ga qofar ta uku.
Yana zuwa wajen da qofar take ya tadda ita a kulle.
Jikinta jajawur tamkar qarfen da aka ciro daga wutar maqera.
Tiriri da huci mai tsananin zafi yana ketowa daga jikin yana
bugun jikin duk wanda ya tunkari inda take. Zuhairu ya matsa
a hankali ya isa ga qofar ya fiddo mukulli da aka bashi ya saka
a hankali ya murxa qofar ta buxe da kanta ya zare mukullinsa
ya ja daga yana mai saurare da ganin abinda zai fito daga
cikinsa.
124
BAKAR GUGUWA
Wuta ce ta fara tasowa daga cikin qofar ta yo wajen
tiririnta da zafinta tamkar zai narkar da jikin zuhairu ya kama
da wuta ya hallaka. Zuhairu ya yi sauri ya duba gefensa akwai
mulmulallun farin dutse kamar yadda aka sanar da shi, ya xaga
takobinsa ya sari farin dutsen ya raba shi biyu, nan take wutar
ta mutu tun kafin ta qaraso inda yake, hayaqi ya turnuqe bakin
qofar har sai da ya daina ganin komai.
Bayan lafawar hayaqin sai ya ga qofar ta zama tamkar
qofofin da ya wuce a baya. Ya bi ta cikin qofar ya shiga
harabar fadar anan ne ya ga wajen na da matuqar faxi da girma.
An qawata fadar da ado mai kyau na ginin qananan duwatsu
abin yiwa ado da jauhari, ga furani da qoramu masu gudanawa
a tsakiyar wajen tamkar wani lambun shawatawa.
DARUL SABAR
Zuhairu ya qarewa wajen kallo da ganin yadda aka
qawata ginin fadar irin na fadar manya sarakunan duniya da
suka shahara a fagen tarin dukiya wadata tamkar wanda ya
gina fadar baya tunanin zai mutu ya barta.
“Babu shakka wanda ya gina wannan fada ya shiryawa
zaman duniya da tunanin dauwama a cikinta abadan ba zai
hallaka ba” Zuhairu ya ce a ransa sannan ya wuce ya ci gaba da
tafiya ya zuwa cikinta.
Kafin ya isa inda fadar take sai ya ji qaqqarfar iska da
ke cuxanye da baqar guguwa ta taso ta tunkaro inda yake. Aka
125
BAKAR GUGUWA
yi tsawa da rugugin aradu mai matuqar qarfi gaba xaya fadar ta
gauraye da duhu mai tsanani, mafi munin gani daga yankin
duhun dare. Zuhairu ya ja daga cikin shirin artabu da arangama
yana duban wannan baqar guguwa don ya san wanda yake tafe
gare shi a cikinta. Baqar guguwar ta qaraso gaban shi ta tsaya
sannan sai ta soma lafawa a hankali, daga cikinta sai ga matsafi
Bahalu ya bayyana gaban zuhairu.
Haqiqa yana tare da tsananin damuwa da vacin rai mara
misaltuwa hannunsa na hagu yana riqe da gorarsa na sihiri na
dama kuma riqe da sandarsa ta tsafi. Ya dubi zuhairu cikin
tsananin fushi da fusata yace da shi.
“Makoma ta munana gareka cikin wa’adin shigowarka
fadata. Duk da ban yi zato ga faruwar hakan ba, amma tunda
har ka shigo cikinta to kuwa ya inganta na tabbatar da hallaka a
kanka, ba za ka samu nasarar abinda ya kawo ka ba, bare ka
fita daga cikinta duk da ka samu nasara a kan sansanoni
ma’abota tsaro ga wannan fada da ka hallaka a baya kafin ka
kawo gare ta, hakan bai tabbatar da sahihancin samun nasara
akai na ba, kuma na rantse da girman darajar mahaifina da
abinda ya mallaka na daga alqaluman sihiri da tsafi sai na
hallaka ka da kisa mafi muni da qasqanci sababin shigowarka
wannan fada” Zuhairu ya dube shi da duba irin na qasqanci ya
maida masa raddi da cewa.
“Kai da bari ga ambato abinda ba shi da amfani ambato
a gareka. Don kuwa kai ne makoma ta munana gareka da za ka
hallaka cikin shirka da kafirci tunda har ma’abota tsaro da bada
kariya da kake alfahari da su suka gaza bada kariya da
kiyayewa akan wannan fada na shigo cikinta. Wadda ka yi
imani da cewa babu wani mahaluki da ya isa ya shigo cikinta
126
BAKAR GUGUWA
har abada. To kuwa lokaci ya qure a gareka rayuwa ta munana
akan ka, ajali ya kusanto ka cikin wa’adinka na barin duniya,
yau ne ranar da za ka yi nadamar halittarka a doron qasa da
wanzuwarka cikin abinda kake aikatawa na shirka da sihiri.
Yau ne ranar da za ka tabbatar da cewa akwai ubangijin
gaskiya mai rinjaye akan kowanne aikin sihiri da kake ainkarin
tabbatarsa”.
Ya zare takobinsa cikin kabbara da maxaukakiyar
murya mai qarfi ya taso kan matsafi Bahalu da nufin cim masa
ya keta shi gida biyu ya hallaka. Matsafi Bahalu ya nuna shi da
sandar tsafinsa ya soma karanto xalasimai na aikin sihiri da
nufin aikata wani abu da zai hallaka zuhairu da shi. Amma ga
mamakinsa sai ya ga dukkanin xalasiman da ya mallaka na
aikin sihiri sun lalace duk abinda ya yi nufin aikatawa akan
zuhairu ya kasa tasiri akansa. Shi kuwa zuhairu da ya ga haka
sai ya tuna da maganar da tsohuwa Diyanuwa ta sanar da shi na
cewa; idan har ya samu nasarar shiga fadar matsafi Bahalu shi
kenan babu wani aikin sihiri da zai qara tasiri akansa. Don
haka ya qara himmatuwa da qarfin zuciyarsa ya tasar ma
matsafi Bahalu don ya hallaka shi.
Matsafi Bahalu ya jefar da sabdarsa ta tsafi da kurtun
sihirinsa da suke hannunsa saboda rashin muhimmanci da
amfaninsu a wannan lokaci. Ya zaro wata baqar takobinsa da
ke xaure a xamararsa ya yi qaraji da kururuwa irin ta fusatuwa
ya taso kan zuhairu suka haxu a tsakanin filin wajen suka
kaiwa juna sara,kaifin takubbansu ya haxu a sararin samaniya
hakan ya haifar da wata tsiwa mai tada tsigar jiki, tare da
tartsatsin wuta da ya watsu a sararin samaniya suka ci gaba da
127
BAKAR GUGUWA
kaiwa juna sara cikin mugun nufi na hallaka abokin gaba,
amma har suka rabu babu wanda ya samu nasara akan wani.
Suka sake zaburowa suka kaiwa juna sara. Zuhairu ya
shammace shi ya kai masa wata irin suka da tsinin takobinsa ya
same shi a kafaxa. Bahalu ya yi qaraji da kururuwa saboda
azaba ya zabura ya maida martani akan zuhairu da kai masa
wani gawurtaccen sara. Ya samu sulken yaqin da yake jikinsa
har sai da sulken ya kece gida biyu. Suka sake yunqurawa suka
kai xauki kan juna, kaifin takubbansu ya sake haxuwa kan iska.
Suka ci gaba da sokekeniya da bugaiya irin ta zaratan sadaukai.
Kowannensu na neman makasa da hanyar samun nasara akan
abokin karawarsa. Haka suka yi ta gabza artabu xauki-ba-daxi
da kafsawa a tsakaninsu, amma babu wanda ya samu nasara
akan wani har sai da kaifin takubbansu ya dakushe, hasken su
ya dusashe. Saboda yawan haxuwa da suke yi yayin kaiwa juna
sara.
Suka watsar da takubban suka farma juna da bugu da
hannu. Aka soma ‘yar damtse,kowannensu na kai duka da
dukkanin qarfinsa. Nan fa aka soma sabon timiri da timimiya
irin ta manya jarumai da suke ji da kan su, tun daga farkon
harabar fadar har sai da suka dangata da qarshenta suka sake
dawowa inda suke kafsawa tun da farko. Suka yi tirjiya irin ta
matuqar buguwa da jin jiki gaba xayansu. Matsafi Bahalu a
sake fusata da ganin ya kasa samun nasara akan zuhairu tunda
suka soma kafsawa. Ya yunqura ya kai masa sura ya xaga shi
sama ya juya shi zai cake kansa a qasa, kamar yadda ake cake
tsinin mashi ya karya masa wuya, ya hallaka shi zuhairu ya
juye cikin azama da zafin nama ya dire da qafafunsa.
128
BAKAR GUGUWA
Suka sake zuburowa suka riqe hannun juna aka yi ‘yar
gwajin qwanji babu wanda ya murxe wani daga cikinsu.
Zuhairu ya shammace shi ya yi masa karo da kai a tsakiyar
fuska kuvus! Matsafi Bahalu ya yi baya taga-taga kamar zai
faxi ya turje bai faxi ba. Zuhairu ya sake narka masa bugu a
tsakiyar qirji, Bahalu ya tafi da baya ya faxi a zaune. Hannunsa
ya kai kan takobinsa ya yi sauri ya xaukota ya taso kan zuhairu
a fusace ya kai masa sara da ita. Zuhairu goce ya sake kai masa
sara da ita zuhairu ya sake gocewa sannan ya riqe hannun
matsafi Bahalu da yake riqe da takobin ya juya tsinin takobin a
saitin qirjin matsafi Bahalu ya danna tsinin takobin da qarfi ya
shiga ciki har sai da tsinin takobin ya nutse.
Matsafi Bahalu ya yi qaraji da kururuwa mai tsanani
qarfi saboda azaba. Ya sa hannunsa ya ture zuhairu daga
jikinsa ya tafi ya faxi qasa. Shi kuma ya zare tsinin takobin
daga qirjinsa jini ya yi tsartuwa sama. Ya xaga takobin cikin
qaraji da kururuwa ya tasarma zuhairu zai kai masa sara da ita.
Zuhairu ya hangi tasa takobin yashe a qasa kusa da shi
ya sa hannu ya xauka ya kare saran da ya kawo masa. Sannan
ya sanya qafarsa ya tokare havar matsafi Bahalu da ita, matsafi
Bahalu ya yi baya taga-taga kamar zai faxi. Zuhairu ya miqe
cikin azama da zafin nama ya xaga takobinsa ya kaiwa matsafi
Bahalu sara da dukkanin qarfinsa ya same shi a tirken dokin
wuyansa, kan matsafi Bahalu ya yi tsalle sama ya rabu da
gangar jikinsa saboda qarfin saran da zuhairu ya yi masa,kuma
kafin gangar jikin ta faxi qasa itama zuhairu ya sanya
takobinsa ya tsinka shi kashi biyu. Cikin zafin nama da
gwanintar sara irin na hamshaqin sadauki. Kowanne vangare
ya faxi qasa gefe daga sassan jikin matsafi Bahalu, daga nan
129
BAKAR GUGUWA
tasa ta qare, ya hallaka bai ko shura ba. Zuhairu ya yi sujjada
don nuna godiya ga Allah da ya bashi nasarar hallaka wannan
shu’umin matsafin.
Duk abinda yake faruwa tsakanin matsafi Bahalu da
zuhairu Gimbiya Hasima da sauran dukkanin ‘yan matan da ke
cikin fadar sun fito waje suna ganin wannan artabu da baqin
gumurzu da suke yi a tsakaninsu. Da suka ga zuhairu ya samu
nasara akan matsafi Bahalu ya hallaka shi sai suka yi matuqar
murna da farin ciki, don sun san cewa ranar kuvutarsu ce da
komawarsu hannun iyayensu ce ta zo. Suka taho da farin ciki
Gimbiya Hasima ta tsaya a gaban zuhairu tana duban sa cikin
matuqar farin ciki na ganin ya kawo qarshen mawuyacin halin
da rayuwarta ta kasance a ciki ya hallaka matsafi Bahalu. Ta yi
godiya ga Allah tare da jin begen zuhairu da qaunarsa ya qaru
a zuciyarta.
Shi ma zuhairu ya dubeta cikin farin cikin sake ganinta,
sannan ya yi murmushi na tabbatar mata da alqawarin da ya
xauka na kawo qarshen matsafi Bahalu da irin mayuwancin
halin da ya sanya rayuwarta a ciki. Bayan sun nutsu zuhairu ya
tambaye ta waxannan ‘yan mata da yake gani tare da ita su
wanene su? Gimbiya Hasima ta amsa masa da cewa, “suma
waxannan mallaka fada ne ya xauko su daga hannun iyayensu
ya kawo su ya ajiye su a matsayin kuyangi da masu yi masa
hidima kamar yadda itama matsafi Bahalu ya xaukota”.
Daga nan ya sake tambayarsu a ina rijiya take don ya je
gareta ya xebo ruwan cikinta ya yi amfani da shi don karya
aikin sihirin da yake jikinsa. Gaba xaya ‘yan matan da suke
fadar babu wadda ta san inda rijiyar take sai sanawiyatu Assad
wadda aka fara kawowa cikin fadar, don haka ta yi masa rakiya
130
BAKAR GUGUWA
har inda rijiyar take a cikin tsakiyar fadar zuhairu yana zuwa ya
ga rijiyar ba ta da tsananin zurfi cikinta yana kusa-kusa. Ya
kama gavar rijiyar ya taka ya shiga cikinta. Ya sanya sulkarsa
na xibar ruwa ya xebo ruwan da yake cikin rijiyar ya fito.
Bayan ya fito ya kafa kai yana shan ruwan da ya xebo a
cikin rijiyar. Nan take sai aikin sihirin da yake jikinsa ya karye.
Kamaninsa suka sauya daga siffar dattijo mai tarin shekaru ya
zuwa siffar matashin jarumi, kuma sadauki gaba xaya ‘yan
mata dake tare da Gimbiya Hasima suka cika da matuqar
mamaki wannan lamari.
Zuhairu ya sake yin godiya ga Allah sannan ya maida
sauran ruwan a xamararsa ya xaure don kaiwa tsohuwa
Diyanuwa kamar yadda suka yi alqawari. Daga nan ya
shaidawa Gimbiya Hasima da sauran ‘yan mata da suke tare da
ita cewa ba shi kaxai ba ne yana tare da abokan tafiya da suka
taho tare, don su taimaka masa ya baro su a wajen fadar. Don
haka suka kama hanyar ficewa daga fadar don su koma inda ya
baro su Buniyatu da sauran jaruman da suka taho tare da su.
Da fitar su zuhairu daga cikin fadar suka xan yi nisa
kafin su kai ga inda abokan tafiyarsa suke sai suka ji wata irin
tsawa da rugugi mai tsananin qarfi a bayansu. Suka juya don su
ga abinda yake faruwa sai suka ga wannan fada tana girgiza da
raurawa tana rushewa da kanta har ta gama ragargajewa.
Sannan dukkanin wajen ya kama da wuta fadar ta qone qurmus
da suka gama ganin abinda ya faru sai suka ci gaba da tafiya
har suka isa inda su Buniyatu da sauran abokan tafiyarsa suke.
Buniyatu da sauran jaruman da zuhairu ya bari a wajen
suka yi matuqar murna da farin cikin ganin zuhairu ya dawo
lafiya,tare da samun nasarar kuvutar da Gimbiya Hasima da
131
BAKAR GUGUWA
sauran dukkanin matan da ya tarar a cikin fadar da kuma
samun nasara karya sihirin da yake tare da shi. Ya dawo
siffarsa ta asali daga siffar tsoho da matsafi Bahalu ya mayar
da shi. Bayan sun nutsu zuhairu ya kwashe labarin dukanin
abinda ya faru tsakaninsa da matsafi Bahalu ya sanar da su da
kuma labarin ‘yan matan da ya tarar a fadar tare da Gimbiya
Hasima, kamar yadda ta sanar da shi suka sake yin godiya ga
Allah bisa wanna nasara da suka samu sannan suka zauna a
wannan wajen don su qara huce gajiya kafin gari ya waye su ci
gaba da tafiya su kama hanyar komawa gida.
**
Da gari ya waye bayan su zuhairu sun yi sallar Asunahi
suka yi shiri, suka kama hanyar komawa gida suka shafe tafiya
har ta tsawon kwanaki a cikin lardin Ashtar suna keta tsaunuka
da kwazazzabai sallah da cin abinci ne kawai yake tsayar da su,
har suka iso bakin kogin nan da suka qetaro kafin su iso
wannan lardi. Da yake babu jirgin ruwa a wajen sai da suka sa
ke yin tafiyar kwanaki biyar a gefen kogin kafin su qure
tsayinsa su zagayo inda suka bar dawakansu.
Da suka iso wannan waje sai suka yada zango suka
kwana don su huce gajiya, da gari ya waye suka sake yin shiri
suka kama dawakansu suka hau don ci gaba da tafiya Gimbiya
Hasima da sauran ‘yan matan da aka xauko daga fadar matsafi
Bahalu suka hau dawakan jaruman da suka hallaka a cikin
lardin Ashtar da yake suna da yawa wasu ‘yan matan sai suka
hau doki xaya su biyu. Aka ci gaba da tafiya.
Bayan tafiyar wasu kwanaki suka iso dajin sa tsohuwa
Diyanuwa take zaune. Suka isa bukkar ta take suka sauka daga
kan dawakansu.Tsohuwa Diyanuwa ta fito daga cikin bukkar
132
BAKAR GUGUWA
tana dogarawa da sandarta. Ta tare su cikin murna da farin ciki
na dawowarsu cikin fatan samun nasara. Buniyatu ta tafi tare
da rungumeta cikin murna, sannan ta shaida mata sun samu
nasarar abinda suka tafi aikatawa a fadar matsafi Bahalu.
Tsohuwa Diyanuwa ta sake yin murna da farin ciki. Sannan
zuhairu ya kwanto salkar ruwan rijiyar wubaisa da ya xebo a
fadar matsafi Bahalu ya miqawa Buniyatu don ta bata ta wanke
idanunta da shi ta samu waraka daga aikin sihirin da yake tare
da ita, kamar yadda suka yi mata alqawari kafin su tafi.
Buniyatu ta karvi salkar ruwan ta bawa tsohuwa
Diyanuwa ta wanke idanunta da shi. Nan take aikin sihirin da
yake tare da ita ya karye, idanunta suka buxe. Ta samu waraka
daga halin makantar da take ciki tsawon lokaci. Ta dubi jikarta
Buniyatu da sauran jama’ar da ke wajen ta sake yin murna da
farin ciki daga nan su zuhairu suka yada zango a wanan wajen
suka kwana kafin gari ya waye su ci gaba da tafiya.
Da gari ya waye suka tashi gaba xaya har tsohuwa
Diyanuwa suka ci gaba da tafiya ya zuwa birnin Bahazum.
Kuma cikin hukunci Ubangiji ba su sake haxuwa da wani abin
cutarwa ba, ko kuma wanda zai vata musu lokaci, sallah da cin
abinci ne kawai yake tsayar da su, ko kuma idan sun yi
matuqar gajiya su yada zango don su kwana. Haka suka shafe
kwanakin da za su kai su birnin Bahazum.
A ranar da suka isa birnin tun suna bayan gari sarki
shaiban ya samu labarin dawowarsu kuma ga yadda aka shaida
masa da alamun samun nasara a tare da su. Don haka shi da
kansa da tawagar manya gari da ke fadarsa suka hau dawakai
suka fito bayan gari don taryarsu. Da isowarsu zuhairu tun
daga nesa sarki shaiban ya hangi ‘yarsa Gimbiya Hasima a
133
BAKAR GUGUWA
cikin ayarin ‘yan mata da suke tafe da su. Ya sauko daga kan
dokinsa ita ma Gimbiya Hasima tana qarasowa wajen ta sauka
daga kan nata dokin ta tafi ga mahaifinta sarki shaiban suka
rungume juna cikin tsananin murna da farin ciki mara
musaltuwa suna masu godiya ga Allah da ya sake haxa
fuskokinsu.
Bayan sun nutsu suka rankaya gaba xayansu suka tafi
fadar sarki shaiban. Labari ya ishe jama’ar gari na dawowar
Gimbiya Hasima suka fito suka tare su cikin murna da farin
ciki har zuwa fada. Da suka isa fada ne zuhairu ya kwashe
labarin abinda ya faru daga tafiyarsu har ya zuwa dawowarsu
ya sanar da sarki shaiban da sauran jama’ar birnin. Sarki ya
sake yin godiya ga Allah abisa wannan nasara da suka samu na
kuvutar da ‘yarsa daga hannun shu’umin matsafi Bahalu
sannan suka yi jimamin rashin jaruman da suka hallaka a hanya
ya yin wannan tafiya. Sarki ya sa aka bawa iyalinsu da sauran
dangin wanda suka rasu dukiya mai tarin yawa, don kula da
rayuwarsu kada su shiga mayuwancin hali na rashin ‘yan
uwansu. Suma sauran jarumai da aka dawo tare da su ba su
hallaka ba aka ba su kyautar dukiya mai tarin yawa.
Bayan an gama da wannan sarki shaiban ya tambayi
Buniyatu abinda take so na ladan aikinta na taimakon Zuhairu
da ta yi. Aka samu wannan nasara ta kuvutar da Gimbiya
Hasima, Buniyatu ta dubi sarki shaiban cikin girmamawa tace
da shi. “Allah ya baka nasara ni babu abinda nake so na daga
dukiya a matsayin lada aikin da na yi duk abinda na aikata na
yi ne saboda Allah burina kawai zuhairu ya amince ya aureni
saboda shi ne abinda nake muradi” Da faxar wannan maganar
134
BAKAR GUGUWA
ta ta tun kafin zuhairu ya ce wani abu Gimbiya Hasima ta yi
sauri ta amsa da cewa.
“Idan dan wannan ne qudurinki babu shakka zuhairu zai
aureki ki zama matarsa” Shi