Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
al’amari da ta faxa masa, daga nan suka tashi suka kama dawakansu suka hau suka ci gaba da tafiya, inda za su yi tafiyar kwanaki goma sha biyu akan hanyarsu ta zuwa lardin Ashtar kafin su isa inda tsohuwa Diyanuwa take zaune. ** Ita kuwa Gimbiya Hasima daga ranar da matsafi Bahalu ya kawota wannan fadar ta Darul sabar ta kasance cikin halin tsananin damuwa da baqin ciki mara misaltuwa, babu abinda ta rasa na daga suturu, abinci ko abin sha, a wannan fada har ma da hadimai masu yi mata hidima, sai dai ba ta iya cin abinci sosai kullum tana cikin tunani da damuwa da baqin cikin rabota da mahaifinta da matsafi Bahalu ya yi, cikin kwanaki kaxan ta rame ta yi baqi tamkar wadda ta shekara a halin rashin lafiya, ba ta da aiki sai yawaita ibada don ta riqa samun nutsuwa, tun da Gimbiya Hasima take a cikin wannan fada ba ta tava fita daga cikin xakin da matsafi Bahalu ya ajiyeta ba, duk da ya bata damar ta fita ta zagaya cikin wannan fada duk inda take so, wata rana da yamma ta yi tunani ta fita waje don ta xan zaga a harabar fadar ko ta ga wani abin nishaxi da zai xebe mata kewa. Ta tashi ta fita daga xakin ya zuwa waje ta ga an zagaye harabar fada da shuke-shuke masu matuqar qayatarwa ga furani da ‘ya ‘yan itatuwa na ababen marmari iri daban-daban ta ci gaba da tafiya a cikin harabar fadar tana zagayawa har ta iso wani xan qaramin lungu da duhun itatuwa da furanni suka 76 BAKAR GUGUWA lulluveshi tana shiga sai ta riski wata kuyanga daga cikin kuyangin dake hidima a wannan fada tana sallah, Gimbiya Hasima ta cika da matuqar mamaki don ba ta yi zaton akwai ma’abocin addinin musulunci a cikin wannan fada ba, ta tsaya daga bayanta har sai da ta idar da sallah ta zauna ta yi addu’a ta shafa, sannan Gimbiya Hasima ta matsa gareta ta yi mata sallama. Kuyangar nan ta xago kai da sauri ta dubi me yi mata sallama da ta ga Gimbiya Hasima ce ta amsa mata cikin mamaki don ba ta yi zaton cewa itama ma’abociyar addinin musulunci bace ba. Gimbiya Hasima ta zo kusa da ita ta zauna sannan ta ce da ita “Ya ke wannan baiwar Allah ina labarinki kuma me ya kawoki wannan waje na ganki a halin yin hidima qarqashin wannan shu’umin matsafi, ma’abocin shirka da sihiri bayan ke kin kasance musulma mai bauta ga Allah(SWT).” Kuyangar nan ta sunkuyar da kai hawaye ya zubo daga idanunta sannan ta xago ta dubi Gimbiya Hasina tace da ita. “Sunana SANAWIYATUL ASSAD BIN ABDULNAS mahaifina sarki ne dake sarautar birnin KUBAIRU gabas da kogin Haisa, kuma jarumi ne da ya shahara a fagen yaqi da runduna mayaqa, wanda hakan ta sa sauran sarakunan qasashen kafirai ma’abota bautar gumaka da tsafi suke matuqar shakka da tsoron kai hari akan birinsa, ya yi yaqe-yaqe da dama na jahadi dan xaukaka addinin musulunci har sai da ya kafa daular musulunci a wannan yanki, na taso cikin gata da kulawa tare da tarbiyya irin ta addinin muslunci har na kai girmana. 77 BAKAR GUGUWA “Wata rana daga cikin ranakun rayuwata wani xan sarki daga cikin ‘ya ‘yan sarakunan yamma ma’abocin bautar gumaka ya ganni ya ce yana sona ya tafi ya sanar da mahaifinsa buqatarsa ta san a nema masa aurena, da yake yana da gata a wajen mahaifinsa saboda shi kaxai ya haifa a duniya, tun a wannan rana sai mahaifinsa ya taso ‘yan aike daga fadarsa zuw fadar mahaifina akan neman aurena ga xansa ‘yan aike suka iso fadar mahaifina suka nemi iso aka basu damar su shiga bayan sun shiga suka kai gaisuwa sannan suka sanar da mahaifina saqon sarkinsu na neman aurena ga xansa. Da mahaifina ya ji bayani dake tafe da su sai ya basu amsa da cewa, su koma su sanar da sarkin su cewa babu auratayya tsakanin xansa ma’abocin bautar gumaka da ‘yarsa musulma, sai dai idan ya amince zai karvi addinin musulunci daga shi har jama’ar birninsa su daina bautar gumaka da tsafi, to kuwa zai bada aurena ga xansa. ‘Yan aike suka tashi suka kama hanya suka koma birninsu, da suka isa birnin suka sanar da sarkinsu abinda mahaifina ya ce sai ran sarki ya vaci, ya yi fushi da harzuqa mai tsanani ya xauki alqawarin sai ya yaqi mahaifina ya rushe birninmu ya xaukeni ya tafi dani fadarsa ya aurar dani ga xansa, tun daga sanan suka shiga shirin yaqi, sun kawo hari har sau uku birninmu amma ba su tava samun nasarar shiga birnin ba, bare su samu nasara abinda suke nufin aikatawa kuma a duk sanda zo sukan koma ne cikin tsananin rauni da tagayyara,yawan rundunar baradansu ya kan qaranta jarumai daga cikinsu su zama raunana, maxaukaka daga cikinsu su zama maqasqanta. 78 BAKAR GUGUWA Bayan da suka dawo daga yaqi na uku ne da suka je kai hari birninmu, wannan xan sarki ya fusata da ganin baradan mahaifinsa sun kasa samun nasara akan jama’ar birninmu ya tafi ya xauki guba ya sha ya halaka da mafi munin mutuwa saboda ni, sarkin nan ya yi matuqar baqin ciki mara misaltuwa, saboda hallakar xansa saboda ni wanda shi kaxai ya mallaka a duniya. Tun daga wannan lokaci ya sake xaukar alwashin akan sai ya halakani ya halaka mahaifina don xaukar fansar salwantar xan sa, ko ta wane irin hali don haka ya koma neman taimako daga manyan matsafa da hamshaqan bokaye don a samu wanda zai je fadar mahaifina ya halakashi ni kuma ya xaukoni ya kai masa fadarsa, amma cikin hukunci ubangiji babu wanda ya samu nasara a kaina ko kan mahaifina daga cikin jama’ar da yake turowa har zuwa sanda ya haxu da boka Kauwas, wanda shi ne mahaifin matsafi Bahalu wanda ya xaukoki ya kawki wannan wajen, shi ne ya xaukoni daga fadar mahaifina ya kawoni wannan wajen duk da bai samu nasara halaka mahaifina ba, kuma bai kaini fadar wancan sarki da ya yi alqawarin zai xaukoni ya kawo ni ba, sai ya taho dani wannna wajen ya ajiye ni. “Yadda al’amarin ya faru kuwa shi ne wata rana da yammaci muna zaune a xakina tare da sauran kuyangina muna hira, sai muka ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi daban firgici ta gauraye xakin,qarfin tsawar kamar faxuwar aradu muka razana matuqa daga ni har kuyangin da suke tare da ni muka tashi za mu fice daga xakin a firgice sai muka ga wata guguwa ta turnuqe ta rufe qofar fita daga xakin, nan take kuma ta gauraye ko ina, xakin ya yi duhu mafi tsanani daga yankin dare, sannan sai na ji an wafceni an yi sama da ni cikin iska, na 79 BAKAR GUGUWA yi qaraji da kururuwar neman taimako daga sauran kuyanfin da suke tare da ni amma babu wanda take ganina saboda tsananin duhu da ya rufe xakin kamar yadda bana ganin kowa, daga nan sai na ji kaina ya juye na fita daga hayyacina ban sake sanin abinda yake faruwa gareni ba. Sai da na dawo hayyacina sai na ganni a cikin wannan wajen da kuma wanda ya kawoni wato Boka Kauwas mahaifin matsafi Bahalu da ya xaukoki, ni ce mace ta farko da aka kawo wannan waje dukkanin sauran daga baya ne aka kawo su. Kuma duk wadda ki ka gani a cikin wannan fada ‘yar wani sarki ce ko kuma ‘yar attajiri aka xaukota daga hannun mahaifinta aka kawota nan, yau shekarata uku kenan rabona da mahaifina da sauran dangina, na yi kukan baqin ciki da takaici mara misaltuwa, har na haqura na miqa lamarina ga Allah ina mai roqon sa ya kuvutar da ni daga wannan hali da nake ciki, wannan shi ne labarina da abinda ya faru a gareni”. Da Gimbiya Hasima ta ji wannan labari nata sai ta yi matuqar tausayawa wannan kuyanga, itama ta bata nata labarin da abinda ya faru tsakaninta da matsafi Bahalu ya xaukota ya kawota wannan wajen, suka taya juna jimami tare da addu’ar Allah ya kuvutar da su daga halin da suke ciki, daga nan suka ci gaba da hira har zuwa faxuwar rana, suka yi sallar magariba sannan suka yi sallama Gimbiya Hasima ta tashi ta koma xakinta. Tun daga wannan rana Gimbiya Hasima ta kan ziyarci wannan kuyangar su yi hira, ko kuma ita kuyangar ta je xakinta da haka har suka yi matuqar shaquwa da juna. 80 BAKAR GUGUWA ** Su kuwa su zuhairu bayan da suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daji suka shafe tsawon kwanaki shida sannan suka iso inda wata bukka take ita kaxai a tsakiyar daji,Buniyatu dake gaba ta dubi zuhairu tace da shi. “Wannan shi ne bigiren da kakata tsohuwa Diyanuwa take zaune, don haka bari mu isa gareta kaga abin al’ajabi cikin hikima da baiwar da Allah ya hore mata. Kuma keta wanda ya yi magana daga cikinku ku yi saurare ku ga abinda zai faru tsakanina da ita dan ku zama shaidu da tabbatar da abinda na ambata”. Suka tunkari inda wannan bukka take, kafin su isa gareta sai suka hangi wata tsohuwa ta fito daga cikin bukkar da ta ji takun sahun tafiyar dawakansu sanye da baqaqen tufafi hannunta riqe da sanda tana dogarawa, ta tunkaro inda take jin motsin tafiyarsu ta tsaya har suka qaraso gabanta suka ja linzamin dawakansu suka tsaya, gaba xaya babu wanda ya yi magana daga cikinsu, ita kuma idanunta a rufe irin na halin makanta tace da su. “Su wanene waxannan jama’a da kuka zo gareni haqiqa na ji akwai jikata Buniyatul Hajari a tare da ku” Buniyatu ba ta yi magana ba ta karvi kwari da baka daga hannun wani jarumi daga cikin jarumai da suke tafe tare da su, ta sanya kibiya a cikin bakar ta ja ta sakar mata kibiyar a sairin qirjinta, kibiyar ta tafi gareta da qarfi kafin ta kai jikinta tsohowa Diyanuwa ta ji hucin tahowarta, ta sanya sandar dake hannunta ta kaxe kibiyar ta tafi jikin wata bishiya ta cake a jikinta, sannan ta sake yin magana ta ce da su. 81 BAKAR GUGUWA “Babu shakka wannan harbin kibiyar na jikata ne Buniyatu, marhabin da zuwanki gareni kuma ke da su wa ku ke tafe har ku adadin mutum arba’in da biyu kuma ke kaxai ce mace a cikinsu?” Su zuhairu da sauran baradan dake tare da shi suka cika da mamaki abinda ya faru tare da maganar da tsohuwa Diyanatu ta ambata, wadda babu kuskure a cikinta tamkar idanunta a buxe tana ganin adadin yawansu. Buniyatu ta amsa mata da cewa “Babu shakka ni ce jikarki Buniyatu Hajari, na ziyarceki tare da waxansu jarumai da muke tafe tare da su cikin wata buqata da ta kawomu gareki, amma ya aka yi ki ka san adadin yawan mu cewa mu arba’in da biyu ne muka zo wannan wajen kuma ni kaxaice mata a cikinsu?” Tsohuwa Diyanuwa ta yi murmushi sannan tace da ita “Jikata mantawa kika yi dani shi yasa ki ka yi min wannan tambayar amma ki sani ina da hikimar gane mace a cikin taron maza komai tsananin yawansu kuma koda ba ta yi magana ba, ta hanyar hucin numfashinta da bil adama suke yi wanda kunnena yake ji kuma na gane adadin yawanku ne tun daga takun sawun dawakanku da na ji sanda kuka tunkaro inda nake” Ta juya ta nufi wajen bukkarta tana dogara sanda tare da yi musu izinin su qaraso, su zuhairu da Buniyatu suka saki linzamin dawakansu suka qarasa bakin wannan bukka suka sauka suka xaure dawakansu, tsohuwa Diyanuwa ta gabato musu da abinci da abin sha na daga ‘ya ‘yan itatuwa suka ci suka sha har sai da ya ishe su gaba xaya duk da yawansu. Bayan sun huta sun nutsu tsohuwaDiyanuwa ta tambayesu me ke tafe da su gareta, kamar yadda Buniyatu ta fara sanar da ita da farko. Buniyatu ta kwashe labarin duk 82 BAKAR GUGUWA abinda ya faru tsakanin zuhairu da kuma yayanta matsafi Bahalu ta sanar da ita, ta kuma yi mata bayanin abinda ya kawosu gareta, don ta karanta musu wannan rubutaccen saqo na sirri da mahaifinta ya bari kafin ya rasu, saboda su sami damar zuwa wannan fada da matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima su karvota daga gareshi, su kuma xebo ruwan da yake cikin rijiyar tsakiyar fadar, don samun waraka daga aikin sihirin da aka yiwa zuhairu su kuma kawo mata don karya sihirin dake tare da ita, ta warke daga halin makantar da take ciki. Da tsohuwa Diyanatu ta ji wannan bayani sai tace da Buniyatu “Haqiqa zan taimaka muku ko don na samu waraka daga halin da nake ciki, idan kun cimma nasara, kuma bana qaunar zallunci ba kuma zan tava goyan bayan azzalumi ba a duk inda yake a faxin duniya” Ta juya ga Buniyatu tace da ita “Ina rubutaccen saqon yake?” Buniyatu ta xauko wannan fata ta miqa mata, tsohuwa Buniyatu ta karva ta warware fatar ta shafi rubutun dake jikinta da tafin hannunta, ta soma karantawa tana sanar da su ma’anar rubutun kamar haka:Darul sabar wata shahararriyar fada ce aka ginata a lardin Ashtar tsakanin wasu manya tsaunuka guda uku,tana da matuqar kariya da tsaro na xalasumai na aikin sihiri da sihiri dake zagaye da fadar, kuma kafin ku isa inda wannan fada take da zarar kun shiga lardin Ashtar za ku fara gamuwa da fitintinu iri daban-daban, na abubuwan cutarwa da za su taso gareku da nufin halakaku, sai kun yi da gaske wajen samun nasara a kan su, don shi kansa lardin Ashtar yanayinsa ya bambanta da sauran yanayin da ku ka saba ji a cikin wannan duniya, akwai 83 BAKAR GUGUWA masifu da wahalhalu masu tsanani wanda zai wahala wani bil’adama ya shiga cikinsa ya fito ba tare da ya halaka ba”. Idan kun shiga lardin Ashtar kafin ku isa inda wannan fadar take za ku fara tarar da wasu manya-manya sansanin barada kuma jarumai ma’abota aikin sihiri har guda uku, mahaifinki boka kauwas ne ya samar da wannan sansanin baradan, kuma sai da ya shage shekaru uku cur yana tattaro manya sadaukai da suka shahara a fagen jarumta, sannan ya kafa waxannan sansanonin qarqarshin alqaluman sihirinsa, don su zama masu bada kariya da tsaro ga dukkan wanda zai kawo farmaki akan fadarsa, ya sanyawa kowane sansani shugaba daga cikinsu da kuma sunan da yake kiran sansanin da shi, sansani na farko sunansa DARUL UQUB sai na biyu DARUL MUSIBA na qarshe shi ne DARUL MAUTU babu abinda waxannan baradan suke aikatawa a kowane sansani illa bauta ga wasu manya gumaka dake kusa da tsaunukan nan guda uku da suka zagaye fadar,tun daga farkon hudowar rana har faxuwarta, kuma sukan ci su sha ne daga abinci da abin sha da yake zubowa daga saman wannan tsaunukan da zarar sun fara bauta ga gumakan da suke kusa da su, wannan wata hikima ce ta zubowar abincin daga saman tsaunukan daga mahaifinku da ya tara waxannan jaruman cikin alqaluman sihirinsa don su qara qarfafa imaninsu ga gumakan da suke bautawa. Babu wata halitta mai rai da zata gifta ta wannan waje baradan basu farmaketa sun halakata ba, koda kuwa tsuntsune dake shawagi a sararin samaniya, don haka babu wani mutum da zai wuce ta wajen ba su farmakeshi da nufin halakashi ba, don haka ya zama dole kuma sai kin bi ta wannan sansanin kun halaka su sannan ku qarasa wannan fadar. 84 BAKAR GUGUWA Idan kun samu nasarar halaka waxannan baradan ku ka isa inda fadar take za ku tadda tana kewaye da manya qofofi guda uku, ban san yadda za ku iya buxe qofofin ku shiga cikin fadar ba, saboda ba a rubuta a jikin wannan saqon na sirri zuwa fadar ba, sai dai na yi sani da cewa qofofin suna tare da tsaro na xalasumai na aikin sihiri, wanda ba za ku iya tunkarar qofar kai tsaye ku buxe ku shiga cikinta ba, ku yi qoqarin neman hanyar da za ku buxe qofar da kanku, idan kun samu nasara shiga cikin fadar shi kenan babu wani aikin sihiri da zai iya tasiri a kanku, daga nan kuma ya rage tsakaninku da shi wanda yake zaune a fadar ku yaqeshi don samun nasara a kansa”. Da ta gama karanta wannan rubutaccen saqo da suka kawo mata tare da yi musu bayanin abinda saqon ya qunsa, ta qara da cewa “Kada abinda na sanar daku na daga wahalhalu da masibar dake tare da wannan tafiya da zaku yi ta sa ku karaya ko ku zama masu rauni da fargaba, ku yi imani da cewa za ku iya samun nasara akan abinda ku ka sa gaba a zuwanku, za ku ga nasara akan abinda ku ka sa gaba a zukatanku, za ku ga nasarar tana tare daku ku kai ga cimma qudirinku akan duk abinda kuka sa gaba”. Su zuhairu suka yi mata godiya a bisa wannan shawara da ta basu, da kuma karanta musu rubutaccen saqon da ta yi ta sanar da su yadda za su iya zuwa Darul sabar fadar da matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima, da yake yamma ta yi sai suka yada zango a wannan wajen suka kwana da gari ya waye suka yi shiri suka yi bankwana da tsohuwa Diyanuwa suka kama hanya suka ci gaba da tafiya, suka tunakari dajin da zai kai su lardin Ashtar inda wannan fada ta matsafi Bahalu take. ** 85 BAKAR GUGUWA Bayan su zuhairu sun bar inda tsohuwa Diyanuwa take zaune ita kaxai a cikin daji suka ci gaba da tafiya har suka shafe tsawon kwanaki takwas, sannan suka iso bakin wani qaton kogo ma’abocin girma da faxi, ruwan cikinsa na kaxawa daga gabas zuwa yamma, iska na turashi da qarfi yana ambaliya da toroqo ya yi tsiri sama, daga gefen kogin suka ga wani qaton jirgin a tsaye tamkar ana jiran isowarsu su shiga dan qetare ruwan, suka ja linzamin dawakansu suka tsaya a bakin wannan kogin Buniyatu ta dubi zuhairu tace da shi. “Wannan shi ne ruwan da zamu qetare mu shiga lardin Ashtar da mun wuce wannan kogi tafiyar kwana biyu za mu yi mu shiga cikin lardin, kuma mun yi sa’a ga jirgin ruwa a bakin kogin da zamu iya shiga cikinsa mu qetare, anan zamu bar dawakanmu har zuwa sanda zamu dawo, don dukkanin tafiyar da zamu yi a cikin lardin Ashtar zamu yi ta ne da qafafunmu” Da Buniyatu ta yi musu wannan bayani sai zuhairu da sauran baradan suka sauka daga kan dawakansu suka xaure su a bakin wani kogi,suka tunkari jirgin ruwan za su hau, sai zuhairu ya dakatar da su, ya zare takobinsa ya nufi wajen da jirgin ruwan yake don ya tabbatar da cewa babu wani abin cutarwa a cikinsa kafin su shiga yana zuwa ya shiga cikinsa tun daga farko ya fara ganin jini face-face a jikin jirgin ruwa ko ina, ya riqa tafiya a hankali yana qara shiga ciki, sai ya soma ganin qasusuwa da gawarwakin bil Adam birjik a cikin jirgin, ya ci gaba da tafiya yana dube-dube ko zai ga abin da ya halaka wannan jama’a sai ya soma jiyo wani gunji da huci tamkar na wata halitta da ke da rai a cikin qarshen jirgin ruwan. Zuhairu ya gyara riqon takobinsa ya ci gaba da tunkarar inda yake jin wannan gunji da huci don ya ga abinda yake yin 86 BAKAR GUGUWA sa, har ya isa qarshen jirgin ruwan da zuwansa sai ya tarar da wata qatuwar macijiya a nannaxe ta fasa kai tana huci, girmanta kamar wani qaramin dutse za ta iya haxiye mutum ya halaka lokaci guda a gabanta ga gawarwakin mutane nan da ta halaka take haxiya a matsayin abinci, nan take zuhairu ya fahimci macijiyar nan ce ta halaka jama’ar dake cikin jirgin ruwan gabaki xaya. Da ganin zuhairu sai macijiyar nan ta yi wani huci mai qarfi ta taso ta kawo masa sara, zuhairu ya kauce ta samu jikin itacen jirgin ruwan ya xaga takobinsa ya kai mata sara ya samu jikinta amma sai ya ji kamar ya sari dutse takobinsa ta tashi sama ba tare da ta yanki jikinta ba. Macijiyar ta sake kawo masa sara zuhairu ya goce, ta sake kai masa sara za ta haxiye shi, ya kai mata sara ya samu bakinta, macijiyar ta yi gunji da girgiza saboda azabar saran da ya yi mata, jirgin ruwan ya yi tangal-tangal kamar zai kife, sauran baradan da ke bakin kogin suka ja baya saboda jin wannan gunji shi kuwa zuhairu ya sake jan daga don tunkarar ta, da ya lura sosai sai ya ga ya ji mata rauni a inda ya sareta a baki, don haka ya qara azama da kai sara a wannan wajen don ya halakata. Macijiya ta sake taso masa a fusace tana kai masa sara da wafta za ta haxiyeshi shi kuma zuhairu ya riqa gocewa da kai mata sara cikin tsananin jarumta da qarfin zuciya, duk inda macijiya ta sara a jirgin ruwan sai ka ga itacen wajen ya fashe ko ya ragargaje. Da ragowar jaruman da suke tare da zuhairu suka hangi abinda yake faruwa sai nan da nan suka zare makamansu, gwanayen harbi kibiya suka riqa sakarwa macijiya ruwan 87 BAKAR GUGUWA kibbau daga inda sue, masu jifa da majaujawa suka riqa jifanta da wasu dunqulallun qarafa masu tsini dake huda jikinta, sauran jaruman masu faxa da takubba ko mashi suka tafi ga jirgin ruwan don kai xauki gareshi, da zuwansu suka far mata da sara da suka babu qaqqautawa, macijiya nan ta kawo wafta cikinsu ta suri xaya ta haxiye shi daga shi har takobi da sulken yaqin dake jikinsa,ta sake kawo sara ta samu mutum uku lokaci guda, iska ta kwashesu ta yi sama da su saboda qarfin saran suka zube a gefe matattu ba su ko shura ba, jikinsu ya riqa zagwanyewa yana narkewa kamar jini, saboda masifar dafin da ke jikin macijiyar. Da ragowar jaruman suka ga haka sai suka ja da baya a razane, shi kuwa zuhairu ya sake tasar mata a fusace ya kai mata wani gawurtaccen sara irin na zaratan sadaukai da dukkanin qarfinsa, ya yi sa’ar ya sameta a lokacin da take qoqarin kai masa sara, macijiyar ta yi wani irin gunji mai tsananin qarfi saboda azabar saran da ya kai mata, jini ya yi tsartuwa sama daga inda ya sari jikinta, macijiyar ta yi tsalle ta faxi cikin ruwan kogin, masu jifa da majaujawa da harbi da kibiya suka ci gaba da harbin ta har ta nutse a cikin ruwan kogin, jini ya taso sama ya gauraye ruwan kogin daga inda ta nutse. Zuhairu ya tsaya yana sauraron ko zai ga macijiyar ta sake tasowa saman ruwa daga inda ta nutse amma har aka shafe lokaci mai tsawo ba su sake ganinta ba don haka ya yi zaton ta halaka sun gama da ita, daga nan suka kwashe gawarwakin ‘yan uwansu da sauran jama’ar da macijiyar ta halaka a cikin jirgin ruwan suka fita da su suka binnesu, sannan suka share jirgin ruwan suka gyara duk abinda ya lalace a 88 BAKAR GUGUWA cikinsa, suka zuba kayansu suka hau suka xauki fila-filai da ake amfani da su wajen tuqa jirgin ruwan suka soma tuqawa suka kama hanyar da za su qetare kogin. Bayan sun yi tafiya mai nisa a cikin kogin har rana ta kusa faxuwa ba su kai qarshensa ba, can daga bayansu sai suka riqa jin wani qugi da gunji yana tunkaro inda suke, iska mai qarfi ta soma tasowa daga gabas tana kaxa ruwan, kogin ya soma tanbatsa yana ambaliya da tsiri sama, igiyar ruwa ta soma kaxawa tana girgiza jirgin da suke ciki sannan sai suka ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi da ban firgici ta sake gauraye wajen, ruwan ya sake hautsinewa yana kaxawa da qarfi tare da yin tsiri sama kamar zai sha kan jirgin ruwan ya nutsar da su su halaka, jirgin ruwan ya soma tangaxi da tangal-tangal kamar zai dulmiyar da su su halaka. Can daga bayansu sai suka hango wannan baqar guguwar ta keto ta saman ruwan kogin tare da iska mai tsananin qarfi sun tunkaro inda suke, gaba xaya wajen ya yi baqiqqirin sararin samaniya ya yi duhu mafi tsananin gani daga yankin duhun dare, suka sake jin wata tsawa mai tsananin amo da rugugi mai matuqar hauhawa da ban firgici, jirgin ruwan ya sake yin girgiza da tangal-tangal tamkar zai kife da su daga cikin baqar guguwar nan ta qaraso inda suke sai ga matsafi Bahalu ya bayyana akan iska hannunsa riqe da gorarsa na aikin sihiri tare da sandarsa ta tsafi ya dubi su zuhairu ya bushe da dariya irin wadda ya saba yi a duk sanda zai aikata wani abu na mugunta da zallunci ya ci gaba da qyalqyala dariya har zuwa wani tsawon lokaci sannan yace da su. “Halaka ta tabbata a gareku cikin wannan rana babu shakka ba za ku kuvuta daga wannan musiba da ku ke ciki ba 89 BAKAR GUGUWA har sai kun halaka, kamar yadda na sanar da ku cewa ajali zai gabata gareku cikin wannan tafiya, saboda babu wani mahaluki a faxin duniya da ya isa ratsa lardin Ashtar bare ya je inda fadata take, saboda ma’abota tsaro da bada kariya dake tare da ita”, ya dubi ‘yar uwarsa Buniyatu yace da ita. “Ke kuwa Buniyatu zan sake bada dama a gareki kafin ku riski inda za ku halaka, ki zama mai neman afuwa a gareni tare da yin rantsuwa da alqaluman sihiri masu girma akan cewa za ki rabu da begen wannan jarumin da ku ke tare da shi, tare da barin addininsu da ki ka yi imani da shi a yanzu, ni kuma na yi miki alqawarin zan kuvutar da ke daga wannan halaka da ku ke ciki na maida miki alqaluman tsafi da sihirinki da na rabaki da su, na tafi da ke fadata mu zauna tare cikin salama da tasirin aikata abinda ki ke son na daga alqaluman sihiri”. Buniyatu ta maida masa raddi da cewa “Bana buqatar taimako daga gareka ka kuvutar dani, ga Allah nake neman taimako kuma ba zan tava juya baya ga abinda na tabbata a kansa yanzu ba, na fita daga addinin musulunci ba, kuma na neman ka dawo da alqaluman sihirin da ka qwace daga gareni don a yanzu ina neman tsari da su, kuma ba ka isa ka tabbatar da hallaka akan mu ba, komai qarfin tasirin tsafi da sihirinka har ranar da ubangiji ya so tabbatar da hakan a kanmu”. Matsafi Bahalu ya fusata da jin kalamanta masu tsauri a gareshi ya dubeta yace da ita. “Ke dai kina cikin ximuwa da tavewa wadda ba za ta dawo dake kan turbar gaskiya ba, kuma

Chapter 6 of 10