Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 10
qawatawa da kayan ado nau’i daban-daban, suka zauna suka yi hira irin ta masoya aka kawo masa abin sha na ‘ya ‘yan itatuwa na marmari dangin su tufa,inibi da kayan ciye-ciye na karama masoyi zuhairu ya ci ya sha daga abinda aka kawo masa sannan suka yi sallama a bayan gama hirarsu ya tashi ya kama dokinsa ya hau ya kama hanyar komawa gida. Tun daga wannan lokacin zuhairu ya ci gaba da ziyartar Gimbiya Hasima cikin wannan lambu da take zuwa a kowane yammaci suna hira, wani lokacin kuma ya kan tafi har birnin Bahazum fadar mahaifinta ya ziyarceta a can su yi hirarsu irin 31 BAKAR GUGUWA ta ma’abota begen juna. Sannan zuhairu ya sanar da kakansa marwan dukkanin abinda yake faruwa game da soyayyarsa da Gimbiya Hasima da yadda mahaifinta ya karveshi da martaba hakan yasa dattajo marwan ya yi mamaki da wannan lamari sannan ya gargaxeshi cewa ya guji shiga abinda bai shafeshi ba, matuqar ba taimako zai yi akan xan uwansa musulmi ba, sannan kada ya sake ya cire zoben da ke yatsansa ko kuma ya taka sahun wani matsafi da ya taso masa da nufin halakashi a duk inda yake, idan ya kiyaye wannan sharaxi babu shakka zai samu nasara akan kowane irin shu’umin matsafi komai tasirin tsafi da sihirinsa. ** Al’amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya koma bagirensa da suke zaune tare da ‘yar uwarsa Buniyatu a cikin wasu manya tsaunika da suke nesa da Birnin Bahazum sai da I sukan yi tafiya cikin alqaluman sihirin rage nisan tafiya su je birnin cikin qanqanin lokaci, kuma idan suka je yankin da birnin yake sukan shafe kwanaki masu yawa wani lokacin ma har watanni kafin su sake komawa bigirensu. A sanda matsafi Bahalu ya fara qaunar Gimbiya Hasima ya kan zauna kusa da birnin Bahazum cikin halin vata na alqaluma sihiri yana lura da duk wanda zai ce yana qaunarta ya halakashi, kamar yadda ya halaka ‘ya ‘yan sarakuna da dama. Bayan matsafi Bahalu ya yi jinyar raunin da zuhairu ya ji masa a hannu tsawon kwanaki masu yawa har ya warke, sannan sai ya sake yin shiri dan komawa birnin Bahazum da nufin halaka zuhairu yana mai fusatuwa da abinda ya aikata gareshi. Ya tafi ga taskarsa ta ajiyar kayan sihiri da tsafi da ya gada a wajen mahaifinsa ya buxe ya xauko wani kurtun sihirin 32 BAKAR GUGUWA daga cikin taskar ya maida taskar ya rufe ya koma gaban wani farin dutse mai haske dake tsakiyar xakin ya faxi ya yi sujjada, sannan ya xaga kurtun sihirin ya girgiza shi yana mai surutai da sambatu irin na aikin sihiri wani farin hayaqi ya soma fita daga cikin kurtun zuwa jikin dutsen, nan take sai ga zanen siffar zuhairu ya bayyana a jikin farin dutsen tamkar madubi. Matsafi Bahalu ya nuna wannan surar ta zuhairu da ta bayyana a jikin dutsen da tafin hannunsa yana mai ci gaba da ambaton wasu kalamai irin na aikin sihiri da nufin neman sa’a a kansa ya halakashi idan ya sake komawa gareshi. Yana cikin wannan hali na aikin sihiri sai ga ‘yar uwarsa Buniya ta shigo cikin kogon dutsen, ta dubi jikin farin dutsen nan dake gaban matsafi Bahalu, sai ta ga zanen surar masoyinta zuhairu tamkar a jikin madubi nan take farin ciki ya lulluveta ta gabata gareshi tana mai yin yabo da begen wannan surar. Da jin abinda take cewa sai Bahalu ya dakata da abinda yake yi ya juyo ya yi mata magana da cewar “Shin ko kin yi sani da wannan jarumi da kike yabo da ambaton kyawun surarsa” Bunayatu ta amsawa yayanta matsafi Bahalu da cewar “Babu shakka na yi sani da wannan jarumin sunansa zuhairu bin safwan yana zaune a birnin samaras dake qarqashin masarautar birnin Bahazum, na kasance mai bibiyar rayuwarsa cikin bege tun daga ranar da na fara ganinsa, cikin wasu ranaku da na ziyarci yankin birnin Bahazum, shi ne wanda zuciyata take bege da mafi kyawun ambato dan kasancewa tare dani, shi ne wanda na kyautata rantsuwa ta akan alqawarin aurensa duk da ya nuna rashin amincewarsa akan muradina”. Matsafi Bahalu yace da ita “Ni kuma na kasance mai nuna tsananin gaba da qiyayyata gareshi sababin abinda ya 33 BAKAR GUGUWA aikata a kaina, ya kasance mai qaunar wata ‘yar sarki da nake so da muradin aurenta, na kuma yi alqawarin halaka duk wanda yace yana qaunarta don ta zama mallakina duk da ta ce ba za auri ma’abocin tsafi da sihiri irina ba. Shi ne mutum na farko da ya tava xaga makami a kaina da nufin yin gogayya dani har ya fidda jini daga jikina. Shi ne wanda ya fasa xaya daga cikin kurtun sihirin da na gada a wajen mahaifina har qarfin tsafi da sihirina ya raunana. Wannan shi ne dalilin da ya sa na xauki alqawarin halakashi dan yin ramuwa akansa bisa ga abinda ya aikata a kaina a duk sanda na sake komawa birnin Bahazum”. Buniyatu ta ce da shi. “Ina mai neman afuwa gareka kada ka halaka masoyina bisa ga abinda ya faru, cewa ni na kasance mai yawan bege da qaunarsa gwargwadon bugawa zuciya da fitar numfashi,kuma zai zama abin kaico gareni da wanzuwa cikin qunci da baqin ciki idan na rasa wannan jarumi ban ma san yadda makomar rayuwata za ta kasance ba” Bahalu yace da ita “A rayuwata bana afuwa kuma bana fasa xaukar fansa, ba zan saurara ga duk wanda ya xaga makami gareni ba da nufin halakashi har sai da naga bayansa, kuma bani da kaico akan kowane irin hali da rayuwarki za ta kasance idan na halaka wannan jarumin. Bakin alqalami ya riga ya bushe gareki don na yi rantsuwa da ababen bautata tare da yin yanka garesu akan hakan ba zan fasa abinda na yi niyya ba, sai ki yi haquri”. Buniyatu ta fusata da jin maganarsa tace da shi “Idan kuwa har ka halaka masoyina kamar yadda ka ambata na rantse da duk abinda nake yin rantsuwa da shi, sai na je na halaka 34 BAKAR GUGUWA Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasar da kake son ka halaka masoyina saboda ita”. Tana gama faxar maganar ta tashi cikin fushi ta fice daga kogon dutse ta barshi, Bahalu bai damu da maganarta ba,ya ci gaba da abinda yake yi na aikin sihiri dan neman nasara akan zuhairu ya halakashi duk da cewar yasan Buniyatu zata iya aikata abinda ta ambata akan Gimbiya Hasima. ** Bayan fitar Buniyatu daga kogon dutsen ta fita ta zauna ta rasa abinda yake yi mata daxi a duniya ta shiga tunanin maganganun da yayanta ya amabata na cewa sai ya halaka masoyinta zuhairu, damuwa ta yi mata yawa har ta rasa abinda yake mata daxi, ta san cewa tunda yayanta ya yi nufin halakashi to kuwa babu shakka rayuwarsa tana cikin hatsari, ta ji ta kamu da kewar son ganinsa nan take ta tashi ta kama hanyar tafiya birnin samaras dan ta ga zuhairu duk da tayi alqawarin cewa ba za ta sake zuwa gare shi ba har sai ranar da za ta tabbatar da cikar burinta na aurensa ko da bai amince ba. Ta yi tafiya mai nisa a cikin alqaluman sihirin rage nisan tafiya har ta iso birnin samaras da tsakiyar dare gari ya yi shiru babu motsin kowa ta nufi gidansu zuhairu kai tsaye ta shiga ta wuce har xakinsa ta sameshi a kwance yana barci akan gadonsa ta tsaya a gabansa tana dubansa cikin bege da qauna har tsawo wani lokaci shauqin sonsa ya qara ratsa mata zuciyarta anan ta sake xaukar alqawarin cewa ba za ta bari yayanta ya halaka masoyinta zuhairu ba matuqar tana raye,idan kuwa ya samu nasara halakashi ba da saninta ba, ko kuma ya yi masa aikin sihiri na cutarwa to kuwa ta yi alqawarin sai ta halaka Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban dan ta rama. Bayan 35 BAKAR GUGUWA ta gama wannan tunanin na ta ne ta kai hannun za ta shafi jikin zuhairu saboda shauqin qaunar sa dake qara ratsa zuciyarta. Kafin hannunta ya kai jikinsa sai zoben da ke xan yatsan zuhaiu ya yi motsi da qarfi zuhairu ya farka daga baccin da yake yi saboda motsin zoben ya yi alamar wani matsafine ko ma’abocin aikin sihiri ya kusanceshi ya duba ko ina a cikin xakin bai ji motsin komai ba,bare ya ga wani abu ya yi shiru yana saurare jikinsa ya bashi cewa akwai wanda ya shigo cikin xakin duk da baya ganin komai, dan ya sa cewa babu yadda za a yi zobensa ya yi motsi ba tare da wani ma’abocin aikin sihiri ya kusanceshi ba. Ya tashi zaune ya yi addu’a sannan ya tafi ya xauko takobinsa dake rataye a jikin bango da Buniyatu ta ga haka sai ta ja da baya sannan ta juya ta fice daga xakin cikin aikin sihiri yadda ba zai ji takun sawunta ba bare ya ganta. Bayan fitar Buniyatu sai zuhairu ya ji kamar motsi a waje ya buxe qofar xakinsa cikin sauri ya fito ya duba baiga kowa ba ya sake jin kamar takun sahu an nufi wajen da yake xaure dokinsa sannan ya ji dokin nasa ya yi haniniya alamar ya ga wani abu da shi zuhairu baya gani, ya zare takobinsa a hankali ya nufi wajen cikin nutsuwa yana mai lura da taka tsantsan dan gudun kada wani abu na cutarwa ya afko masa cikin duhun dare ya cutar da shi. Kafin ya isa wajen sai ya ji anyi masa magana da murya qasa-qasa aka ce da shi. “Kada ka wahalar da kanka zuhairu ka koma ka ci gaba da baccinka cikin aminci da salama mai qaunarka ce ta kawo maka ziyara cikin wannan dare, kuma ban zo da nufin cutarwa gareka ba” Zuhairu ya shaida murya Buniyatu ce duk da baya ganinta ya amsa mata da cewa. 36 BAKAR GUGUWA “Ba zan gaza ga sanar da ke abinda na sanar dake a baya ba cewa ki nisanta dani ko kuma na salwantar da ruhinki da kisa mafi muni ta hanyar kaifin takobina,qiyayyarki gareni tana daxa hauhawa tsawon rayuwarta kuma ba za ki tava zama mai daraja a gareni ba har sai ranar da kika rabu da hanyar vata ta aikin tsafi da sihiri, ki ka dawo hanyar gaskiya ta bin tafarkin addinin muslunci” Buniyatu ta bayyana gareshi wani farin haske ya zagey kewayen inda take tsaye yadda zai iya ganin fuskarta duk da tsananin duhun dare ta dubeshi tana mai tausasa murya tace da shi “Ni kuma ka ga qauna da begenka ne ya ke daxa hauhawa cikin zuciyarta a koda yaushe ba zan daina qaunarka ba har zuwa ranar da zan cimma qudirina cewa ni na kasance mai sauraron bayyanar wasu bayanai cikin alqaluman sihirina da za su bani damar mallakarka ka zama miji a gareni ta kowane irin hali,dan haka ba zan daina qaunarka ba kamar yadda ba zan rabu da abinda na gada a wajen mahaifina ba na sirrin tsafi da sihiri. Zuhairu ya ce da ita “Ke dai kina cikin ruxani da vata mabayyani, kasancewarki mai yin imani da bayyanar wasu bayanai na alqaluman sihiri akan cikar qudirinki, kuma cikin yarda Allah ba za ki tava cimma qudirin naki ba, cewa ni na kasance mai dogaro dashi akan ya kiyayeni daga duk wani sharri ma’abota tsafi da sihiri irin ki” Buniyatu tace da shi. “Kaine rayuwar ka take cikin tasku da razani na kusantar halaka, sababin alqawarin da xan uwana ya xauka na halakaka, akan soyayyar Gimbiya Hasima dake wanzuwa a tsakaninku kalamansa sun munana akan ambato salwantar da rayuwarka cikin aikin sihirin da yake shiryawa da rayuwarka cikin aikin sihirin da yake shiryawa a yanzu dan zuwa gare ka, 37 BAKAR GUGUWA wannan ne dalilin da ya sa zuciyata ta kasa samun nutsuwa akan maganarsa kuma na shiga halin damwa da begen son ganinka don haka na taso na taho gareka cikin wannan dare na yi alqawarin bada kariya gareka akan duk wani aikin tsafi da sihirinsa, kuma idan har wani abin cutarwa na daga cikin sihirinsa ya sameka to kuwa na yi alqawarin sai na halaka Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasar da yake son cutar da rayuwarka saboda ita” Zuhairu ya fusata da jin maganarta ya maida mata da raddi da cewa. “Har ke kina da tasirin bada kariya ga wanda ya dogara ga Allah cikin lamarinsa, ke kanki ba ki da ikon kare kanki daga duk abinda Allah ya hukunta zai faru gareki,kuma ina mai gargaxinki da gargaxi mai tsauri kan cewa duk abinda ya faru ga Gimbiya Hasima na rantse da wanda raina yake hannunsa sai na halakaki daga ke har xan uwan naki na share rayuwarku daga doron qasa” Yana gama faxar maganar Buniyatu bata ko tanka masa ba, ta vace cikin alqaluman sihirinta ta fice daga gidan ta yi tafiyarta ta barshi, zuhairu ya tafi ya koma xakin sa ya yi addu’a ya kwanta yana tunanin maganar da Buniyatu ta faxa akan Gimbiya Hasima har bacci ya xauke shi. ** Tun daga wannan rana da Buniyatu ta je wajen zuhairu ta sameshi a gida da tsakiyar dare, zuhairu bai sake ganinta ta bayyana gareshi ba, kuma wani abu bai faru gareshi ba, game da yayanta akan alqawarin daya xauka. Sannan zuhairu bai sanar da Gimbiya Hasima abinda ya faru tsakaninsu da Buniyatu ba, akan alqawarin data xauka na idan wani abu na cutarwa ya same shi daga yayanta itama za ta maida martani akanta. 38 BAKAR GUGUWA Al’amarin Gimbiya Hasima kuwa ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali akan lamarin matsafi Bahalu tun tana fargaba da tsoron kada ya halaka zuhairu kamar yadda yake halaka duk wanda yace yana qaunarta,har ta daina fargabar komai saboda ganin matsafi Bahalu bai sake bayyana gareta ba tun daga ranar da suka yi artabu da zuhairu ya fasa kurtun sihirin da yake hannunsa, kuma ta daina yin munanan mafarkemafarken da take yi a kansa, tare da ganin ababen ban tsoro da firgitarwa dake sata razani a duk sanda zai bayyana a gareta. Sukan haxu da zuhairu a duk sanda ta ziyarci wannan lambu da take zuwa tare da kuyanginta su yi hira irinta ma’abota bege da qaunar juna har zuwa faxuwar rana, sannan zuhairu ya yi mata rakiya har qofar shiga birninsu daga nan ya juya ya kama hanyar komawa gida. Duk wannan abin da yake faruwa Buniyatu ta an kasance tare da zuhairu a duk inda yake saboda alqawarin da ta xauka na bada kariya gareshi don kada yayanta matsafi Bahalu ya halakashi kamar yadda ya sha alwashi, sai dai ta kan yi nesa da zuhairu yadda ya sha alwashi sai dai ta kan yi nesa da zuhairu yadda ba zai ji motsinta ba, don ta san idan ta kusanceshi zai gane cewa tana tare da shi saboda zoben da yake yatsansa. A duk sanda zuhairu suke cikin lambu suna hira tare da Gimbiya Hasima, Buniyatu ta kan ji kishi da baqin ciki kamar ta je ta halaka Gimbiya Hasima, sai dai ba ta da ikon aikata haka saboda sanin cewa idan ta halakata babu shakka sai yayanta ya halaka zuhairu, don haka ta kan yi nisa da bakin lambun dan kada ta ji ko ta ga wani abinda suke yi na soyayya da begen juna. 39 BAKAR GUGUWA Wata rana daga cikin irin waxannan ranaku na rayuwarsu, Gimbiya Hasima tare da zuhairu suna zaune cikin lambu suna hira, kuyanginta sun basu waje suna zantawa irin ta ma’abota begen juna, Gimbiya Hasima ta cava ado da kayan ado mafi daraja da ‘ya ‘yan sarakuna suke sanyawa suna zaune akan wasu kujeru na alfarma dake tsakanin wasu filawoyi da furanni masu qayatarwa da kyan tsari, qamshin turare wuta ya gauraye wajen mafi daxin qamshi daga turaren almiski. Buniyatu da ta kasance mai bibiyar zuhairu a duk inda yake, ta yi nisa da bakin lambun ya zuwa cikin wasu duwatsu dake bayan lambun dan kada ta riski hirar da suke yi ta masoyi saboda kishi. Gimbiya Hasima ta dubi zoben nan dake xan yatsan zuhairu sannan tace da shi “Na daxe ina muradin mallakar zoben nan na azurfa dake hannunka, tun daga lokacin da na fara ganinsa tare da kai, sai dai ban yi sani ba ko cewa ba irin zoben da za ka bada kyautarsa gareni bane, kasancewar ko yana tare da wani sirri na daga rayuwarka a tare da shi”. Zuhairu ya murza zoben sannan yace da ita “Haqiqa wannan zobene mai daraja a gareni, kuma yana tare da wani sirri da ya shafi rayuwata don haka ba zan iya bada kyautarsa gareki ba, kamar yadda wanda ya mallaka shi gareni ya umarceni cewa kada na sake na rabu da shi a duk inda nake cikin kowane irin hali” Gimbiya Hasima tace da shi “Za ka iya bani shi na gani don na qarewa irin qirarsa kallo, idan na koma birnin Bahazum na sanya qwararun maqera su qera min irinsa”. “Zan iya baki ki gani” In ji zuhairu ya cire zoben daga xan yatsansa ya miqe mata, Gimbiya Hasima ta karva ta qarewa zoben kallo na irin kyawun qirar da aka yi masa, sannan sai ta sanya a xan yatsanta dan ta gwada zoben ya yi 40 BAKAR GUGUWA mata kyau matuqa kamar saboda ita aka qerashi, shi kansa zuhairu sai da ya yi bege ga kyawun zoben a jikin xan yatsanta, ya ji ba don wasiyar da aka yi masa ba cewa kada ya sake ya rabu da zoben da kuwa ya bar mata zoben ta sanya a hannunta. Suna cikin wannan hali ne kafin Gimbiya Hasima ta cire zoben daga hannunta ta baiwa zuhairu sai suka ji wata irin qara mai tsanani qarfi da rugigi mai ban firgici kamar faxowar aradu ta cika wajen, qasar ta riqa girgiza tana raurawa kamar za ta tsage su rufta cikinta, wani baqin gajimare ya taho daga gabas ya lulluve sararin samaniya tamkar hadari, gaba xaya wajen ya yi duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare, rugugin da suke ji ya ci gaba da hauhawa yana qara kusanto inda suke har sai da suka daina jin komai sai shi, tamkar qoqon kawunansu zai fashe saboda tsananinsa. Kuyangin Gimbiya Hasima suka razana suka ruga inda su zuhairu suke cikin firgici ita kanta Gimbiya Hasoma sai da ta tsorata ta shiga halin ruxani da kixima, saboda ta san cewa matsafi Bahalu ne zai bayyana, cikin wannan hali mafi munin yanayi daga alamomin bayyanarsa. Shi kuwa zuhairu duk da ganin abinda yake faruwa bai razana ba, sai ya miqe tsaye yana duba wannan yanayi cikin tsananin jarumta da qarfin zuciya kuma ya san wannan ba komai bane face aikin sihiri da tsafi irin na ma’abota shirka da tavewa, wa iyazy billahi ya ce a ransa, yana mai hasashen cewa matsafi Bahalu ne zai sake bayyana garesu. Bayan wani lokaci sai suka hangi baqar guguwar nan ta danno daga vangaren yamma, tare da iska mai tsananin qarfin feshin wuta yana tartsatsi da zubowa daga cikin baqar guguwar kamar dai yadda matsafi Bahalu yake yi idan zai bayyana. 41 BAKAR GUGUWA Guguwar ta ci gaba da tahowa har sai da ta iso gaban zuhairu sannan ta tsaya aka sake yin tsawa da rugugin aradu mai tsananin qarfi da ya zarce wanda suka ji da farko, wani farin haske ya keto daga cikin baqar guguwar daga cikin hasken sai ga matsafi Bahalu ya bayyana sanye da kaya irin na mashahuran matsafa ma’abota aikin sihiri, hannunsa na hagu yana riqe da wani kurtun sihirin bayan wanda zuhairu ya fasa a wancan haxuwar da suka yi sanda suke fafatawa a tsakaninsu. Matsafi Bahalu ya dubi zuhairu cikin tsananin fushi da fusatuwa yace da shi “Kaicon ranar dana-sani marar amfani gareka, da za ka hallaka sababin bijirewa umarni da gargaxin da na yi gareka, akan ka rabu da Gimbiya Hasima amma ka qi ji. Yau ne ranar da zan tabbatar da isa da qarfin ikona a kanka. Yau ne ranar da za ka tabbatar da tasirin tsafu da sihiri da kake inkarinsa ya zarce tasirin duk wani abin dogaronka. Yau ne ranar da za ka halaka da salwantar ruhinka daga doron qasa ta hanyar kisa mafi muni da uquba mai tsanani kafin fitar ranka. Kuma yau ne ranar da na jima ina sauraron zuwanta da alamomi za su bayyana gareni na mallaki Gimbiya Hasima ta zama matata, idan na hallakaka zan xauketa na tai da ita DAHRUL SABAR dake lardin ASHTAR mu zauna tare da ita har abada, fada ce da mahaifina yasa aka gina masa a wannan lardi da babu wani mahaluki da ya isa zuwa inda take ya shiga cikinta idan ba mamallakinta ba, kuma shima kafin ya kai ga tarewa a cikinta ya rasu, don haka ni ne zan tare a cikinta tare da Gimbiya Hasima”. Zuhairu ya amsa da cewar “Kada ka zama mai alfahari da bayyana abinda ba za ka iya aikatawa ba, cewa kai ka kasance mai yawan alwashi da yawan rantse-rantse ga abinda 42 BAKAR GUGUWA ka ke hasashen samu nasara a kansa, kuma tun wancan lokacin har ya zuwa yanzu ababen bautarka tun wancan lokacin har ya zuwa yanzu ababen bautarka da ka ke yin rantsuwa da su sun kasa baka nasara bisa ga tasirin tsafi da sihirinka”. Bahalu ya fusata da jin maganarsa ya yi qaraji da gunji dake tattare da aikin sihiri gabaki xaya wajen ya yi amsa kuwa da amo mai hauhawa, ya zaro wasu kibiyoyi irin na aikin sihiri ya jefa zuhairu da su, kafin kibiyoyin sukai kansa sai wani farin haske ya ratso ya shiga tsakaninsu daga cikin farin hasken sai ga Buniyatu ta bayyana a gaban zuhairu ta sanya wata garkuwa ta kaxe kibiyoyin suka zube qasa, wajen da kibiyoyin suka faxi ya kama da wuta qasar wajen ta qone ta yi baqi. Bahalu ya fusata da ganin abinda ya faru ya dakawa Buniyatu tsawa yace da ita “Me ya sa ki ka kare abinda na aikata cikin alqaluman sihirina da nufin halaka wannan jarumi, ki sani cewa ba zan fasa abinda na yi niyyar aikatawa ba, na halaka wannan mutum ko ta wanne irin hali” Buniyatu ta ce da shi “Na yi rantsuwa da duk abinda nake yin rantsuwa da shi ba zan bari ka halaka masoyina ba, idan kuwa wani abu na cutarwa ya sameshi daga gareka to kuwa sai na halaka Gimbiya Hasima wadda ka ke son hallakashi saboda ita”. Matsafi Bahalu yace da ita “Idan kin zama mai bada kariya a gareshi to kuwa ba za ki iya kuvutar da shi daga abinda na yi niyyar aikatawa a kansa ba, na yi rantsuwa da tasirin tsafi da sihiri na tare da yanka ga ababen bauta ta na kuma nemi sa’a daga garesu ina mai fatan samun nasara a kansa”. Ya sake turawa zuhairu wani aikin sihirin wuta ta yi kansa za ta kama jikinsa ya qone, Buniyatu ta yi nata surkulen ta tare wutar, nan take wutar ta mutu kafin ta kai kan zuhairu. 43 BAKAR GUGUWA Ya sake jifansa da wani irin mashi na aikin sihiri ja jawur dashi kamar qarfen da aka curoshi daga wutar maqera, Buniyatu ta tura wasa iska mai tsananin qarfi ta ture mashin ya tafi ya faxa cikin wata qorama dake gudanawa a tsakiyar lambun, ruwan cikin qoramar ya kama tafasa saboda masifa nan take launin ruwan ya sauya ya koma ja jawur kamar jini. Matsafi Bahalu ya sake fusata da fushi mai tsanani ya yi qaraji da kururuwa mai matuqar qarfi ya daki qasa da sandar tsafin dake hannunsa, iska da baqat guguwa suka turnuqe suka rufe wajen har sai da su zuhairu suka daina ganin junansu ya biyo ta cikin duhun baqar guguwar da nufin halaka zuhairu, Buniyatu ta tura wani farin haske cikin qabar guguwar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana tana ganinshi, ya xaga sandarsa ta tsafi dake hannunsa zai makawa zuhairu Buniyatu ta sanya hannunta ta kaxe sandar bai same shi ba. Bahalu ya sake fusata ya kai mata sura cikin sa’a ya fizge kurtun sihirin da yake hannunta, wanda a tare da shi ne duk wani abu da ta gada na daga alqaluman sihiri yake ciki, Buniyatu ta yi qaraji da kururuwa mai tsananin qarfi, saboda suvucewar kurtun sihirin daga hannunta zuwa hannun matsafi Bahalu. 44 BAKAR GUGUWA BAKAR GUGUWA 2 afin matsafi Bahalu ya bar wajen Buniyatu ta tasar masa da nufin karve kurtun sihirinta daga hannunsa, ta kai masa sura za ta fizge kurtun sihirin shi kuma ya sanya sandar tsafi dake hannunsa ya maketa. Buniyatu ta yi qaraji ta tafi ta bugu da jikin wata itaciya dake tsakiyar lambun nan take ta zube qasa sumammiya, jini na zuba ta hanci da bakinta. K Zuhairu ya fusata da ganin wannan al’amari ya zare takobinsa cikin kabbara ya tasarma matsafi Bahalu da nufin kai xauki gareshi ya ketashi gida biyu ya halaka,shima Bahalu ya juyo gareshi a fusace, ya tasar wa zuhairu cikin qaraji da gunji mai tsananin qarfi dake tattare da aikin sihiri gaba xaya dukkanin wajen ya yi amsa kuwwa da amo mai hauhawa da ya gauraye ko ina, suka haxu a tsakanin fusatuwar su suka kaiwa juna sara da bugu da makaman da yake hannunsu,kaifin takobin zuhairu ya haxu da sandar sihiri dake hannun matsafi Bahalu wani farin hayaqi ya tashi sama tare da tartsatsin wuta tamkar haxuwar qarfe da qarfe.zuhairu ya sake kai masa sara a fusace kafin matsafI Bahalu ya kare kaifin takobin ya sauka a jikinsa amma abin ka da shu’umin matsafi sai Bahalu ya zama hayaqi saran ya wuce ta jikinsa ba tare da ya ji masa rauni ko wata illa ba, ya sake bayyana a gabansa da saran ya wuce. 45 BAKAR GUGUWA Zuhairu ya sake maida kaifin takobin a tsakiyar kansa Bahalu ya kare saran da sandar sihirin dake hannunsa suka kaiwa juna sara irin ta neman makasar abokin karawa kaifin takobin zuhairu ya wuce ta gefen wuyan masafi Bahalu da karfi kaxan ya rage ya sare kansa daga gangar jikinsa, suka yi tirjiya irin ta arangama sannan suka sake zaburowa suka yi wata bahaguwar haxuwa irin ta zaratan sadaukai dake sanya halaka da matuqar tsoratarwa ga qananan jarumai masu raunin zuciya.makaman dake hannunsu suka haxu da qarfi har sai da dukkaninsu suka yi baya taga-taga kamar za su faxi sannan suka tirje suka tsaya. Suka sake zaburowa suka kai xauki ga juna, zuhairu ya suri matsafi Bahalu ya cirashi sama da dukkanin qarfinsa ya makashi da qasa, ya bi shi da sara cikin azama da zafin nama,kafin kaifin takobin ya sauka a kansa Bahalu ya vace, takobin ta sari qasa, ya sake bayyana a gefen zuhairu ya sake yin kansa da sara cikin fusatuwa ya riqa kai masa sara cikin jarumta da qwarewa irin ta sadaukantaka, shi kuma matsafi Bahalu ya riqa karewa da sandar sihiri dake hannunsa ko kuma ya goce, wani lokacin ya kan tsage kashi

Chapter 3 of 10