Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 10
biyu saran ya wuce, ta jikinsa ko kuma ya vace ya zama iska. Haka suka yi ta fafatawa da arangama a tsakaninsu har sai da kaifin takobin zuhairu ya dakushe haskenta ya dusashe, saboda yawan kai sara da haxuwar da take yi da sandar sihiri da take hannun matsafi Bahalu. Da Bahalu ya ga lamarin ya ta’azzara a gareshi zuhairu ya tsananta masa da kai sara yana shirin halakashi,sai ya yi wani irin qaraji da kururuwa mai ban firgici dake tattare da aikin sihiri wata baqar guguwa ta turniqe a tsakaninsu sannan ya nunashi da sandar sihiri dake hannunsa 46 BAKAR GUGUWA yana ambaton wasu xalasimai na aikin sihiri, wata irin iska mai tsananin qarfi ta yi sama da zuhairu ta makashi da qasa, zuhairu ya yunqura ya tashi matsafi Bahalu ya sake nunashi da sandar sihirin iska ta sake yin sama da shi ta makashi da jikin bishiyar dake tsakiyar lambun ya bugu da buguwa mai tsanani har takobin da take hannunsa ta suvuce ta faxi qasa. Haka matsafi Bahalu ya ci gaba da nuna zuhairu da sandar sihirinsa iska mai qarfi tana wujijjigashi tana maka shi da itatuwan da ke cikin lambun har sai da zuhairu ya yi matuqar jigata, ya faxi qasa jini na zuba ta hanci da bakinsa, matsafi Bahalu ya dubeshi ya bushe da dariya sannan yace “Ahir xinka da yin jayayya da hamshaqin matsafi da ya buwayi cikin lamarinsa kamanta Bahalu nake bin kauwas cikamakin ma’abota sani na ilimin bokanci da sihiri da ke raye a doron qasa ka sani cewa na yi yanka ga ababen bautata don neman nasara a kanka kuma ina da tabbacin samun nasara akan naka,babu shakka ka cika namiji ma’abocin jarumta da sadaukantaka don duk a cikin masoyan Gimbiya Hasima da na halaka babu wanda ya kai ka jarumta da qarfin zuciya sai dai wannan rana ita ce sa’arka ta qarshe a rayuwar duniya da zan halakaka kamar yadda na xauki alqawarin halaka duk wanda ya ambata yana qaunar Gimbiya Hasima. Ya xaga sandar sihirin dakehannunsa zai daki zuhairu da ita a tsakiyar kansa ya halakashi Gimbiya Hasima da ke tsaye tana gani abinda yake faruwa ta yi qaraji da kururuwar irin na firgita da ganin matsafi Bahalu zai halaka zuhairu a sannan Buniyatu ta farfaxo daga suman da ta yi ta hangi abin da yake shirin faruwa yayanta matsafi Bahalu ya xaga sandar sihirinsa zai daki zuhairu da ita,ya halaka nan take ta miqe 47 BAKAR GUGUWA cikin sauri ta shiga tsakaninsu ta kare zuhairu kafin ya dakeshi da sandar tana mai faxin cewa. “Kar ka halaka abin begena dan kuwa ba zan iya rayuwa a duniya ba tare da shi ba, idan kuma ka ce sai ka halakashi to kuwa sai dai ka halakamu gaba xaya ni da shi” Matsafi Bahalu ya fasa dukan zuhairu da sandar sihirin ya dubi ‘yar uwarsa Buniyatu yace da ita. “Tunda kin zavi kare abin begenki akan zama da ni xan uwanki to kuwa zan barki tare da shi ba zan halakashi ba, duk da nayi rantsuwa da ababen bautata akan aikata hakan, sai dai ki sani daga yau babu ke babu sake aikata wani aikin sihiri tunda na qwace kurtun sihirin dake hannunki, kuma ba zan sake maida shi gareki ba har abada.za ki ci gaba da zama da a wannan birnin tare da wanda kika zava fiye da ni xan uwanki na jini, ni kuma zan xauki Gimbiya Hasima na tafi da ita Darul sabar fadar da mahaifinmu ya gina kafin tare a cikinta ya rasu, mu zauna a can tare da ita. Kuma abadan ba za ki iya riskar inda wannan fadar take ba, bare ki dawo gareni har qarshen rayuwarki, saboda ba kya tare da duk wasu xalasimai na aikin sihiri da za ki iya amfani da su don zuwa wannan fadar”. Yana gama faxar maganar ya juya ga zuhairu ya nunashi da sandar sihirin da take hannunsa ya soma karanta waxansu xalasimai na aikin sihiri wani farin haske ya fita daga jikin sandar ya shiga jikinsa,nan take zuhairu ya soma tsuma da maqyarqyata irin ta rawar sanyi har sai da ya durqushe a qasa, sannan sai kamaninsa suka soma sauyawa daga siffarsa ta saurayi maji qarfi zuwa siffar dattijo mai tarin shekaru ma’abocin rauni, gaba xaya gashin jikinsa ya koma fari fat irin 48 BAKAR GUGUWA na furfura tamkar dattijo da ya haura shekaru tamanin a duniya daga nan ya faxi qasa a sume. Buniyatu da Gimbiya Hasima suka qwala wata razananniyar qara saboda ganin abinda ya faru akan zuhairu,matsafi Bahalu ya bushe da dariya irin ta mugunta da zalunci sannan ya dubi Buniyatu yace da ita “Wannan shi ne yadda abin begen naki zai kasance har qarshen rayuwarsa kuma haka za ki kasance da shi cikin wannan siffa ta dattijantaka abadan ba zai dawo siffarsa ta asali ba ko matuqar bani ne na karya wannan aikin sihirin ba ko kuma aka bashi ruwan dake cikin rijiyar BASRA dake tsakiyar fadar Darul sabar da zan tafi da Gimbiya Hasima, kuma babu wani mahaluki da ya isa shiga cikinta komai qarfin tsafi da sihirinsa idan bani da na mallaketa ba ko kuma wanda na yiwa izinin ya shigeta”. Ya sake qyaqyacewa da dariya sannan ya daki qasa da sandar sihirinsa iska mai qarfi ta keto daga bayansa tare da baqar guguwa suka haxu suka turnuqe wajen suka yi tsiri sama, matsafi Bahalu ya bi ta cikin baqar guguwar ya vace,sannan ya biyo ta inda Gimbiya Hasima take a tsaye cikin kuyanginta ya sureta ya yi sama da ita. Gimbiya Hasima ta yi qaraji da kururuwa mai tsananin qarfi sanda matsafi Bahalu ya sureta ta cikin baqar guguwar nan ya tashi sama da ita,Buniyatu da sauran kuyanginta suna ganin sanda guguwar ta yi sama da Gimbiya Hasima tana qaraji da kururuwar neman taimako, tun suna ganinta da hangenta da jin qarajinta har ta vace cikin baqar guguwar nan matsafi Bahalu ya tafi da ita. 49 BAKAR GUGUWA Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai wajen ya washe duhun da ya lulluve sararin samaniyar ya yaye suka daina jin qaraji da rugugin da suke ji tun farko. Buniyatu ta dubi zuhairu ta ganshi cikin halin suma ta tafi gareshi cikin sauri ta xago kansa tana girgizashi taga babu alama motsi a tare da shi, hankalinta ya qara tashi ta tashi cikin sauri ta tafi bakin kogin dake gudana a tsakiyar lambun ta xebo ruwa ta dawo ta zauna ta riqa shafa masa ruwan tana girgizashi cikin kuka, sai da ta xauki lokaci mai tsawo zuhairu yana cikin wannan hali sannan ya farfaxo daga suman da ya yi. Da farfaxowar zuhairu ya tashi zaune a firgice ya duba bai ga matsafi Bahalu da suka fafatawa a kusa da shi ba, ya dubi jikinsa ya ga yadda kamanninsa suka koma irin na tsoho tamkar dattijon da ya shafe shekaru casa’in a duniya, ya sake duban inda kuyangin Gimbiya Hasima suke tsaye bai ganta a cikinsu ba, hankalinsa ya yi matuqar tashi, duk da irin halin da yake ciki na komawar kamaninsa irin na tsufa, babu abinda ya fara tambaya sai ina Gimbiya Hasima. Xaya daga cikin kuyangin nan ta amsa masa da cewa wannan shu’umin matsafin ya xauketa, ya tafi da ita. Zuhairu ya miqe tsaye cikin qaraji duk da siffa irin ta tsufa da kamanninsa suka koma yana jin qarfin jikinsa kamar yadda ya ke ji tun da farko. Kafin matsafi Bahalu ya yi masa wannan aikin sihiri a jikinsa, ya xauki takobinsa ya tasarwa Buniyatu cikin fushi da hatzuqa yana mai faxin cewa “Sanar da ni inda yayanki matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima, idan kuma ki ka bijerewa ambatona na rantse da sarkin da raina yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni da qasqanci, kafin na kai ga gano inda yayan naki yake na tafi gareshi shima 50 BAKAR GUGUWA na halakashi akan xaukar Gimbiya Hasima da ya yi” Buniyatu ta amsa masa da cewa “Ya abin begena zuhairu ka yarda dani da abinda zan ambata gareka, xan uwana Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima Darul sabar dake lardin Ashtar fadace da mahaifinmu ya gina kafin ya kai ga tarewa a cikinta wa’adinsa ya gabata ya halaka. Ni kaina ban tava zuwa inda lardin Ashtar take ba, bare na gano inda fadar take”. Zuhairu ya sake fusatuwa da jin maganar ta ya fizgota ya cirata sama ya makata da qasa, ya xora kaifin takobinsa akan wuyanta ya ce da ita “Ki sanar dani gaskiyar lamarin inda yayanki ya tafi da Gimbiya Hasima idan kuwa ba haka ba na shayar da ruhinki xacin mutuwa da azabar kaifin takobina” Buniyatu ta sake cewa da shi. “Ai abinda na saranr da kai shi ne gaskiya cikin wannan lamarin, idan kuma ba ka gasgata ni ba, kana inkarin abinda na ambata to9 ka halakani kamar yadda ka ambata, kuma ba zan yi kaico ba, ko kuma nadama akan haka saboda wanda nake begene ya halakani, wanda na sadaukar da rayuwata dan na taimaka masa, wanda na guji xan uwana na jini na dawo gareshi na zavi kasancewa da shi, wanda na rasa duk wani gatana da tasirin tsafi da sihiri da na gada a wajen mahaifina saboda shi, wanda nake burin taimaka masa cikin kowane irin hali matuqar ina da damar aikata hakan”. Jikin zuhairu ya yi sanyi zuciyarsa ta karaya da jin kalaman da ta ambata ya cire kaifin takobinsa daga kan wuyanta ya saketa, Buniyatu ta miqe tsaye ta dubeshi suka fusanci juna sannan tace da shi “Ya wanda nake bege da dukkanin ruhina baki xaya na rantse da duk abinda nake yin rantsuwa da shi cewar zai taimaka maka ka kuvutar da 51 BAKAR GUGUWA Gimbiya Hasima daga hannun xan uwana da ya xauketa dan na tabbatar maka da irin begen da nake yi maka ya zarce yadda nake son komai a duniya” Zuhairu yace da ita. “Ba zan amince da maganarki ba, har sai kin yarda za ki yi imani da Allah ki karvi addinin musulunci, ki daina bautar gumaka da tsafi ki rabu da duk wata shirka da sihiri da kike aikatawa”. Buniyatu tace da shi “Na amince zan karvi addinin musulunci idan har za ka yarda dani na zama abar gasgatawa a gareka, maganar aikin sihiri kuwa a yanzu bani da ikon aikatawa tun da xan uwana ya qwace kurtun sihirin da yake hannuna wanda a cikinsa ne alqaluman sihirin da zan iya amfani da su don yin wani aikin sihiri suke ciki, kuma a yanzu ya yi fushi dani saboda ina qoqarin baka kariya daga abinda yake son aikatawa a gareka, ya kuma yi alqawarin ba zai sake maidashi a gareni ba har abada”. Da ta gama masa bayani zuhairu ya sata ta yi kalmar shahada ta shiga addinin musulunci tare da sanar da ita abinda ya wajjaba akan kowane musulmi, daga nan ya tambaye ta cewa “Yanzu ta wace hanya zamu iya riskar inda matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima dan na kuvutar da ita daga hannunsa”. Buniyatu ta amsa masa da cewa “Ban san inda fadar take ba, a faxin duniya amma na yi sani da wani rubutaccen saqo na sirri da mahaifinmu ya bari, wanda ke qunshe da tarihin yadda aka gina fadar da dukkanin sirrinta sai dai a yanzu rubutaccen saqon baya tare da ni yana cikin kogon dutsen da muke zaune tare da xan uwana da mahaifinmu kafin ya rasu” Zuhiaru ya sake tambayarta “A ina wannan kogon dutsen yake?” 52 BAKAR GUGUWA Buniyatu tace da shi “Yana can kusa da birnin kisira tsakanin wasu manyan tsaunuka a gavar kogin bahar sugaira, tafiyar kwanaki biyu muke yi a cikin alqaluman sihiri na rage nisan tafiya, kafin mu isa wannan kogon dutsen amman a yanzu sai mun yi tafiyar kwanaki arba’in saboda bada alqaluman sihiri zamu yi tafiyar ba”. Zuhairu yace “Na xauki alqawarin sai na kuvutar da Gimbiya Hasima daga hannun matsafi Bahalu da ya tafi da ita ta kowane irin hali matuqar zan yi sani da inda wannan fada take a faxin duniya, don haka mu tafi ya zuwa birnin Bahazum fadar sarki shaiban mahaifin Gimbiya Hasima na sanar da shi abinda ya faru gareta, sannan mu wuce alqaryarmu na sanar da kakana abinda ya faru gareni daga nan na yi shiri don tafiya wannan fada”. daga nan ya juya ga kuyangin Gimbiya Hasima ya umarcesu da su kama dawakansu su hau don komawa gidansu sanar da sarki abinda ya faru, kuyangin suka kama dawakansu suka hau ita kuma Buniyatu ta hau dokin Gimbiya Hasima zuhairu ya hau nasa dokin suka kama hanyar komawa birnin Bahazum. ** Da isar su Birnin Bahazum suka wuce fadar sarki shaiban don su sanar da shi abinda ya faru ga ‘yarsa Gimbiya Hasima, suna zuwa qofar fadar kuyangin suka shiga ciki zuhairu da Buniyatu suka dakata daga waje don neman iso kafin a basu damar su shiga ciki. Da shigar kuyangin cikin fadar suka tarar da sarki shaiban a zaune cikin fadawa ana fadanci sarki shaiban ya yi duba ya zuwa kuyangin bai ga ‘yarsa Gimbiya Hasima ba, kuma yanayin kuyangin suna cikin wani hali na firgici da ruxani, nan take hankalinsa ya tashi ya ji 53 BAKAR GUGUWA jikinsa cewa wani abu ne ya tokare shi ya miqe cikin sauri daga kan kujerar sarauta da yake zaune yana mai tambayarsu cewa ina Gimbiya Hasima take. Kuyangin nan suka fashe da kuka sannan xaya daga cikinsu ta amsa da cewar wannan shu’umin matsafin ya xauketa ya tafi da ita… Tun kafin ta qarasa maganar sarki shaiban ya faxi qasa sumamme saboda jin mummunar labarin abinda ya faru akan ‘yarsa jama’a da ke fadar suka taso kan sarki shaiban don kai masa xauki, aka riqa shafa masa ruwa da yi masa addu’a sai da aka xauki lokaci mai tsawo sannan ya farfaxo daga suman da ya yi. Bayan sarki shaiban ya dawo hayyacinsa ya nemi yadda al’amarin ya faru, kuyangar nan ta kwashe labarin yadda matsafi Bahalu ya xauke Gimbiya Hasima ya tafi da ita da abinda ya faru tsakaninsa da zuhairu ya maida shi shi siffa irin ta tsoho cikin alqaluman sihirinsa ta sanar da sarki. Sarki shaiban ya tambaya “Yanzu ina zuhairun yake?” Kuyangar nan ta amsa da cewa “Yana qofar fada don neman iso a gareka kafin ya shigo” Nan take sarki ya umarci wani bafade da cewa aje a kira zuhairu ace masa ya shigo. Bafade ya tashi cikin sauri ya fita don cika umarnin sarki, ya je ya sanar da zuhairu cewa sarki yace ya shigo. Zuhairu ya biyo bayan bafade suka shigo tare da Buniyatu. Da shigowar zuhairu cikin fadar, sarki shaiban ya dube shi cikin matuqar mamaki da tu’ajibin ganin yadda kamaninsa suka jirkita daga siffar matashin jarumi, sadauki ya zuwa siffar dattijo mai tarin shekaru, kamar yadda kuyangar nan ta sanar da shi, gaba xaya duk wani gashi dake jikinsa ya zama fari fat irin na furfura ta tsufa. Zuhairu ya faxi gaban sarki ya kai 54 BAKAR GUGUWA gaisuwa cikin murya mai rauni irin ta dattijontaka, sarki shaiban ya amsa masa sannan ya sake tambayarsa abinda ya faru, zuhairu ya sake sanar da shi kamar yadda kuyangar nan ta sanar da shi da farko daga nan ya qara da cewa. “Ya kai wannan sarki mai tarin daraja da martaba ta hasken addinin musulunci da adalci ga jama’ar ka, ka sani cewa na xauki alqawarin sai na kuvutar da Gimbiya Hasima daga hannun wannan matsafin cikin yarda Allah, zan bi shi duk inda ya shiga a faxin duniya na karvota daga gare shi” Ya juya ga Buniyatu ya gabatar da ita ga sarki shaiban yace da shi “Wannan ita ce Buniyatul Hajari bin kauwas ‘yar uwace a wajen matsafi Bahalu sai dai a yanzu ta karvi addinin musulunci, kuma ta yi sani da yadda za mu samu nasarar riska inda wannan shu’umin matsafin yake da yadda zamu samu nasara a kansa, ta kuma yi alqawarin za ta taimaka min na cika alqawarin da na xauka cikin yardar Allah” Sarki shaiban ya yi shiru hawaye na zuba daga idanunsa sannan ya xago kansa ya dubi zuhairu yace da shi “To zuhairu na amince da wannan shawara da ka yanke, sannan zan haxaka da jarumai da za yi maka rakiya, zan kuma ba ka duk abinda kake buqata daga gareni na guzuri yayin wannan tafiyar. Ni kuma zan sanya malamai su ci gaba da yi muku addu’a tare da fatan Allah ya baka nasara ka kuvutar da ita daga hannun wannan shu’umin matsafin da ya xauketa” Zuhairu ya yi godiya ga sarki bisa ga amincewar da ya yi akan shawarar sa, sannan suka yi sallama ya tafi ya fice daga fadar da Buniyatu suka kama hanyar tafiya alqaryarsu. Sanda suka isa garinsu babu wanda ya gane zuhairu daga cikin jama’ar da suka san shi, saboda sauyawar da 55 BAKAR GUGUWA kamaninsa suka yi ya zuwa siffar tsoho suka wuce har suka isa gidansu suka shiga shi da Buniyatu suka tadda kakansa dattijo marwan zaune a tsakiyar gidan kan buzu yana jan tasbaha. Shi kansa kakansa marwan bai gane zuhairu ba, saboda sauyawar kamaninsa da suka yi zuwa siffar tsoho, ya riqa dubansa cikin mamaki ganin wani dattijo sa’an shekarunsa akan dokin jikansa zuhairu tare da Buniyatu wadda suka shigo gidan tare da ita, har ya sauka daga kan dokinsa ya qaraso gareshi. Da zuhairu ya ga yana yi masa duban rashin sani bai gane shi ba sai ya yi masa magana ya ce da shi “Ya kakana marwan ni ne jikanka zuhairu na kasance cikin wannan hali da kake ganina, kuma hakan ta faru ne sakamakon aikin sihiri da matsafi Bahalu ya aikata a kaina” ya kwashe labarin abinda ya faru tsakaninsu ya sanar da shi, har ya zuwa yadda ya samu nasara akan sa ya maidashi irin wannan siffa ta dattijo da yake a yanzu. Dattijo marwan ya cika da matuqar mamaki da al’ajabi wannan al’amari da ya faru gareshi, sannan ya dubi zuhairu ya ce da shi “Haqiqa ka aikata babban kuskure na mantawa da abinda na umarceka, ka sani cewa na haneka da cire zoben da na baka daga xan yatsanka, kuma na sanar da kai cewa ka riqa lura komai rintsi kada ka sake ka taka sawun duk wani ma’abocin tsafi da sihiri da kuke artabu da shi yayin kafsawa. Idan da ka kiyaye wannan sharaxi da na sanar da kai na yi imanin da cewa ba zai tava samun nasara akan ka ba, cikin yarda Allah sai dai a yanzu bakin alqalami ya bushe a gareka tunda har wannan lamarin ya faru, kuma ita Gimbiya Hasima da wannan zobe yake hannunta na yi imani da cewa ba zai nasarar kusantar ta ba matuqar zoben yana tare da ita” Zuhairu 56 BAKAR GUGUWA ya yi shiru yana mai nadamar abinda ya faru na yin mantuwa ga abinda kakansa ya sanad ra shi sai dai ya yi matuqar farin ciki da ya ji cewa matsafi Bahalu ba zai samu nasarar kusantar Gimbiya Hasima ba, matuqar zoben yana tare da ita. Kakansa marwan ya ce da shi “Yanzu mene ne qudirinka game da abinda ya faru?” Zuhairu ya amsa da cewa “Qudurina shi ne zan bi wannan shu’umin matsafi duk inda ya shiga a faxin duniya, don na kuvutar da Gimbiya Hasima daga hannunsa” Ya nuna Buniyatu ya ci gaba da cewa “Wannan qanwace a wajen matsafi Bahalu kuma ta yi sani da yadda zamu samu nasarar zuwa inda ya tafi da Gimbiya Hasima don kuvutar da ita, da kuma yadda za a karya wannan sihiri dake tare da ni, ta kuma yi alqawarin za ta taimaka mini akan haka”. Dattijo marwan ya amince da shawarar da zuhairu ya yanke, sannan aka bawa Buniyatu masauki inda za ta zauna kafin zuhairu ya gama shirinsa na tafiya. ** Al’amarin Gimbiya Hasima kuwa bayan da matsafi Bahalu ya xauketa cikin baqar guguwar nan ya yi sama da ita, tun tana hangen kuyanginta da sauran jama’ar dake cikin lambun da ya xauketa tana qaraji da kururuwar neman taimako har ta daina hangensu saboda nisa da suka yi da wajen sannan matsafi Bahalu ya huro wani farin hayaqi daga bakinsa ya bugi fuskarta nan take idanunta suka daina ganin komai barci mai nauyi ya xauketa, ta fita hayyacinta daga nan ba ta sake sanin abinda yake faruwa a gareta ba. Matsafi Bahalu ya ci gaba da tafiya da ita cikin alqaluman sihirin rage nisan tafiya, sai da ya shafe tsawon kwanaki goma yana tafiya tare da yada zango ya huta sannan 57 BAKAR GUGUWA ya isa lardin Ashtar inda wannan fada ta Darul sabar take, ya wuce cikin fadar dake tsakanin wasu manya tsaunuka guda biyu a tsakiyar dajin. Fadace da aka ginata da qananan duwatsu abin yiwa ado da jauhari an zagayeta da manyan katangu masu matuqar girma da tsayi tare da kariya ta alqaluman sihiri da babu wani mahaluki da ya isa shiga cikinta matuqar ba da izinin wanda ya mallaketa ba, akwai itatuwa da furani masu matuqar kyau da suka qayata wajen tamkar lambu, ga rafuka da qoramu masu gudanawa a tsakiyar wajen kana zuwa inda fadar take za ka tabbatar da cewa ka zo wata qasaitacciyar fada, irin ta manyan sarakuna da suka shahara a fagen tarin dukiya da qarfin iko. A ciin fadar akwai hadimai mata kyawawa wanda dukkaninsu an xaukosu ne daga hannun iyayensu aka kawo su wannan fada aka ajiyesu don yin hidima ga wanda ya mallaketa, kuma da ywansu ‘ya ‘yan sarakuna ne da manyan attajirai, sai dai daga cikinsu babu wadda matsafi Bahalu yake ganin ta dace ya zauna da ita a matsayin matarsa sai Gimbiya Hasima, don haka dukkanin matan da ya tara a fadar suka zama kuyangi don yin hidima a gareta. Matsafi Bahalu yana shiga cikin fadar ya wuce da Gimbiya Hasima wani xaki mafi kyawun ado daga cikin xakunan dake fadar, an qawatashi da kayan alatu na zinare da azurfa masu kyan gaske, ya sauketa akan wani faffaxan gado irin na alfarma da aka yi shi da zinare. Sannan ya nuna ta da sandar sihirin da take hannunsa, haske ya fito daga cikin sandar ya shiga jikinta, nan take ta farka daga nannauyan barcin da take yi cikin aikin sihiri har na tsawon kwanaki goma. 58 BAKAR GUGUWA Da farkawarta ta ganta kwance akan wannan gado cikin xakin da ba ta tava shigarsa ba, sannan ta ga matsafi Bahalu tsaye a kusa da ita yana dubanta, nan take ta tashi cikin tsoro da razani ta dubi matsafi Bahalu tace da shi. “Wacce qaddara ce ta sa na ganni cikin wannan hali da nake ganin kaina a yanzu…?” Matsafi Bahalu yace da ita “qarfin iko da isata ne cikin alqaluman sihiri ya sa na xaukoki na kawki wannan fada tawa, kamar yadda na sha sanar da ke cewa hakan za ta kasance a gareki wata rana daga ranakun rayuwarki”. Gimbiya Hasima ta fashe da kuka sannan tace da shi “Kaicon rayuwata da ganin wannan halin baqin ciki da ka sanyani a ciki, me ya sa za ka rabani da ‘yan uwana ka kawoni wannan wajen me ya sa kake son cutar da rayuwata don biyan buqatar zuciyarka? Me ya sa zaka nisantani da duniyar musulunci ka kawoni gareka cikin halin da kake ciki shirka da bautar gumaka da tsafi, ka sani cewa la’anar Allah ta tabbata a gareka bisa ga abinda kake aikatawa na shirka da sihiri” Bahalu ya bushe da dariya irin ta manyan azzalumai sannan yace da ita “Ai ban xauko ki na kawki wannan gurin ba sai dan ina begenki da muradin kasancewa tare da ke a matsayin matata kuma uwar ‘ya ‘yana da nake fatan su gajeni a fagen tsafi da sihiri, za ki kasance a qarqashin ikona kuma mai yin biyayya a gareni har qarshen rayuwarki” Gimbiya Hasima ta ce da shi “Allah ya yi mini tsari da dukkanin sharri da mugun nufinka a kaina, ya kuma kuvutar da ni deaga wannan hali don shi mai qarfin iko da isa ne cikin buwayarsa akan kowane tasirin tsafi da sihiri da kake taqama da shi, kuma qiyayyata na 59 BAKAR GUGUWA tare da kai har qarshen rayuwarta ba zan tava qaunarka ba, bare na yi biyayya a gareka”. Bahalu ya sake bushewa da dariya sannan yace da ita “Ai lamarina ya yi nisa a gareki daga fita daga wannan fada, kuma bakin alqalami ya riga ya bushe tunda har na riga na kawoki cikinta, ki sani cewa babu wani mahaluki da ya isa shigowa wannan lardi komai jarumta da sadaukantakarsa bare ya kuvutar da ke daga hannuna” Ya tafi jikin wata qaramar qofa dake saman xakin ya buxeta sararin samaniya ya bayyana, a lokacin da dare ne kuma babu hasken farin wata sai tsananin duhu sanna akwai wasu taurari masu matuqar haske guda biyu daga daidai qofar da ya buxe, ya dubi Gimbiya Hasima ya ci gaba da cewa. “Ki yi duba ya zuwa waxannan taurarin guda biyu dake sararin samaniya, sune taurarin da na daxe ina jiran bayyanarsu, don samun nasarar xaukoki daga birninku na kawoki wannan fada, kuma da suka bayyana na samu nasara aikata hakan, saboda haka ki ci gaba da duba ya zuwa wannan taurari tsawon kowane dare, a duk sanda kika ga wanna taurarin sun taho sun haxe da juna to wannan rana ce da take bayyana kasancewarki matata da tabbatar aure a tsakaninmu,kamar yadda bayyanar taurarin ta tabbatar da samun nasarar xaukoki daga birni ku. Ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da zallunci kamar yadda ya saba sannan ya juya ya fice daga xakin ya barta. Gimbiya Hasima ta sake fashewa da kuka saboda baqin ciki da takaicin halin da matsafi Bahalu ya sanya rayuwarta a ciki, ta daxe tana wannan kuka don tausayawa kanta har kusan asubahi, sannan ta haqura ta ga zoben nan na zuhairu yana tare da ita ba ta jefar da shi ba, ta xaukeshi ta saka a xan yatsanta ta 60 BAKAR GUGUWA sumbaci zoben sannan ta xaga hannunta sama ta yi addu’a don neman Allah ya kuvutar da ita daga hannun wannan shu’umin matsafin da ya xaukota daga birninsu ya rabota da ‘yan uwanta ya kawota wanann wajen. ** Shi kuwa zuhairu cikin kwanaki biyar ya gama shirinsa na tafiya lardin Ashtar don ‘yanto Gimbiya Hasima daga hannun matsafi Bahalu tare da neman makarin aikin sihirin da Bahalu ya yi masa ya maida siffarsa irin ta tsoho mai tarin shekaru. A ranar da zuhairu zai tafi ya fito cikin shiri na sulken yaqi ya yiwa dokinsa xamara da shiri na sosai, haka itama Buniyatu an bata doki tare da sauran kayan yaqi daga fadar sarki shaiban, ta gama nata shirin cikin sulken yaqi ta fito idan ka ganta za ka yi zaton wani hamshaqin jarumi ne sadauki da ya shahara a fagen fama ba mace ba ce, kafin su tafi suka yi bankwana da dattijo

Chapter 4 of 10