Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 10
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BAKAR GUGUWA BAKAR GUGUWA SHEHU USMAN MUHAMMAD 1 2 BAKAR GUGUWA BAQAR GUGUWA uhairu yana tafe akan ingarman dokinsa cikin sassarfa da hanzari ya nufi bakin wani makeken lambu ma’abocin ni’ima da ‘ya ‘yan itatuwa furanni da qoramu masu gudanarwa a cikinsa. Zuhairu jarumi ne na gasken gaske wanda jarumta da bajintarsa ta shahara a dukka nin faxin alqaryun dake kusa da birnin su yana da qarfin zuciya da rashin tsoro na ban mamaki. Shi kaxai yakan fasa rundunar mahara da masu tare hanya su yi wa fatake masu tafiya a daji fashi. Al’addar zuhairu ce yakan ziyarci bakin wannan lambu ako wanne yammaci don yaga wata ‘yar sarki dake zuwa lambun tare da kuyanginta ako wacce rana. Tun daga ranar da ya fara ganinta a cikin wasu ranaku da yake yawo a wannan wajen ya ji zuciyarsa takamu da tsananin begenta irin wanda ba zai musaltu ba, sai dai baisan makomar rayuwarsa ba bisa ga qaunar da yake yiwa wannan ‘yar sarki, kasancewar, mafi girma da daraja daga cikin manyan ‘ya ‘yan sarakunan duniya. Z 3 BAKAR GUGUWA Ya yi sani da cewar ‘ya ‘yan sarakuna a wannan lokacin basa auran wanda ba xan sarki kamarsu ba, ko kuma attajiri wanda dukiyarsa ta shahara shi kuma gashi ba xan sarki ba, dan haka ya kauda kai gabarin tunkararta ya bayyana mata abinda yake zuciyarsa na daga begenta saboda girman matsayinta da ya wuce nasa, sai dai yakan ziyarci bakin wannan lambu da take zuwa akowane yammaci dan ya ganta. Da isarsa bakin wannan lambu ya sauka daga kan dokinsa ya kaishi gefe ya xaure sannan ya koma gindin wata itaciya dake fuskantar qofar lambun ya zauna ya xauko wata sarewa ta azurfa da ya gaa a wajen mahaifinsa ya soma busawa cikin nishaxi yana mai sauraron isowar wannan ‘yar sarki dan ya ganta. Yana zaune a wannan wajen har rana ta kusa faxuwa wannan ‘yar sarkin bata zo ba, ransa ya vaci saboda kewar rashin ganinta ya yi shiru yana tunani da saqe-saqe a ransa. Yana cikin wannan halin kamar daga sama sai ya ji anyi masa magana da wata irin zazzaqar murya mafi sanyi daga ababan sauraro muryar tace masa “Da kazama mai yiwa zuciyarka adalci da babu shakka da ka rabu da begen wadda bata san kana begenta ba. Da ka rabu da tunanin wadda bata san kana tunaninta da ka sauya lamarinka daga quncin qaunar wadda ba za ta so ka ba, saboda girman matsayinta da ya wuce naka”. Zuhairu ya xago kansa cikin sauri ya dubi inda ya ji muryar da ta yi masa magana amma baiga kowa ba ya duba kowane vangare na daga inda yake baiga mai maganar ba. Muryar ta sake cewa da shi “Kada ka damu ko kaji tsoro mai qaunarka ce take yin magana da kai, ko kana inkarin abinda na ambata na bayyana gare ka dan tabbatarwa”. zuhairu ya dubi 4 BAKAR GUGUWA inda ya kejin muryar yace “Idan kin kasance tare da alhairi ki bayyana gare ni don nasan wacece ke da kuma dalilin zuwanki gareni har ki kayi sani da halin da nake ciki da faxar magana mafi munin ambato idan kuma bakya tare da alhairi to kuwa ina mai neman tsari da ke da roqon ki nisanta da ni ko wacece ke”. Zuhairu ya ji anyi dariya cikin tattausar murya sannan murya tace da shi “Zan kasance alhairi gareka tunda ina tare da xunbin qaunarka a zuciyata, dan haka zan bayyana gareka nasanar da kai koni wacece da kuma abinda ya kawoni gareka kamar yadda ka ce” Tana gama faxar maganar sai yaga wani farin haske ya bayyana a gabansa daga cikin farin hasken sai ga wata mace ta bayyana kyakkyawar budurwa tana sanye da fararen tufafi hannunta riqe da wani qaramin gora abin zagayewa da guraye da kambuna irin na aikin sihiri.ta dubeshi tayi murmushi tare da juya fararen idanunta dan jan hankali. Zuhairu ya qare mata kallo sannan yace da ita “Wacece ke kuma meya kawoki gareni cikin wannan yanayi na aikin sihiri, ki sani cewar babu aminci tsakanin musulmi da duk wasu mushirikai ma’abota tsafi da sihiri, matuqar basu tuba sun bi Allah ba” Kyakkyawar budurwa nan tayi dariya sannan tace da shi “Da dai kayi sani da irin martaba da daraja da take tattare da alqaluman sihiri da kuwa ka yi biyayya ga ma’abota mallakarsu dan kazamo daga cikinsu shi ne abin tunqaho da alfaharin mu dan a yanzu duniyar ma’abota sani na alqaluman sihiri ne keda tasiri akan komai”. Ta sake yi masa murmushi irin na jan hankali sannan ta ci gaba da cewa “Suna na BUNIYATUL HAJARI BIN KAUWAS mahaifina shi ne shugaban bokaye da ma’abota 5 BAKAR GUGUWA aikin sihiri dake yammacin birnin SINAR ya rasu cikin wannan shekarar yana tsakiyar tafiya ba tare da wata rashin lafiya ko cuta ba, bayan rasuwar sane muka gaji sihiri tsafi da sihirinsa ni da yayana da ya rasu ya barmu a duniya, na gaji kashi xaya cikin xari na alqaluman sihiri mahaifina yayana kuma ya gaji kashi casa’in da tara daga ciki. Dalilin zuwa na gareka kuma shi ne na kasance mai bibiyar rayuwarka tun daga lokacin da na fara ganinka zaune a wannan wajen kana busa sarewa, tun daga wannan ranar na kan ziyarci wannan wajen dan na saurari busar sarewar da kake yi mai sanyaya zuciya har zuciyata ta kamu da tsananin begenka. Sai dai bantava bayyana gareka ka ganniba sai a yau, kuma na lura cewar zuciyarka ta kamu da qaunar wata ‘yar sarki da take zuwa wannan lambu, dan haka na baiyyana gareka dan na raba tunaninka da begen wacce bata san kana begenta ba”. zuhairu ya fusata dajin wannan maganar yace da ita. “Da kinsa yadda nake tsananin gaba da qiyayyar mushiriki ma’abocin tsafi da sihiri da ko kusa baki tunakri inda nake da buqatar na qaunace ki ba, kiyi alqawari zaki musulunta dan samun rabo da kaucewa vata na aikin sihiri da kike aikatawa, ko kuma ki nisanta da inda nake. Idan kuma ba haka ba na rantse da wanda raina yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni da azabar kaifin takobina”. Buniyatu tayi dariya sannan tace da shi “Babu qiyayya ko gaba a tsakanina da kai masoyina idan da ina gaba da kai zai zama mafi sauqi gareni na halakaka ta hanyar qarfin tsafi da sihirina” Ta xaga kurtun sihirin da yake hannunta ta girgiza shi ta soma wasu irin surutai da sambatu irina aikin sihiri nan take wuta takama daga kowace kusurwa huxu dake zagaye da 6 BAKAR GUGUWA zuhairu sannan wutar ta taso kansa gadan-gadan zata qonashi ya halaka zuhairu ya yi niyyar kaucewa amma yaji ya kasa koda motsi daga inda yake kamar wanda qasa tariqeshi wutar ta taso masa haiqam zata qoneshi ya halaka sai da ta kusa zuwa inda yake ya soma jin zafi da hucinta sannan sai yaga wutar ta mutu ta kuma vace ya dena ganinta. Buniyatu ta sake bushewa da dariya sannan tace da shi “Wannan kaxan kenan deaga tasirin tsafi da sihirin dana gada a wajen mahaifina wanda zan iya halakaka da shi idan na so. Sai dai bani da nufin cutar da kai bare aje ga batun halakaka, saboda qaunar da nake yi maka kai dai ka yi azama ga zurfafa tunani dan amincewa da qaunar mai qaunarka, zai zama mafi kyautuwa gareka ka amince da buqatata muyi aure. Wannan shi ne qudirina akanka ka yi tunani akan maganar na barka lafiya”. Tana gama faxar maganar sai yaga ta vace daga wajen da yake ya daina ganinta sannan ya ji shuru bata sake yin magana ba bare motsinta. Dan haka ya tabbatar da cewar ta tafi tabar wajen don haka ya tashi ya kama dokinsa ya hau ya nufi hanyar komawa gida. Da isar zuhairu gida ya xaure dokinsa ya tafi wajen kakansa MARWAN BIN HADIS wanda shi kaxaine ya rage masa a duniya iyayensa sun rasu tun yana qarami, a hannun kakan nasa ya taso ya zauna kusa da shi ya gaishe shi sannan ya kwashe labarin abinda ya faru gareshi tsakaninsa da wannan shu’umar mace da suka haxu da ita a fitarsa ta wannan yammaci ya sanar da shi. Dattijo marwan ya cika da mamakin wannan labarin sannan yace da zuhairu “Babu shakka duniya ta qara qazanta 7 BAKAR GUGUWA da shu’uman mutane mushirikai ma’abota tsafi da sihiri a doron qasa”. Ya tashi daga inda yake zaune ya nufi wata akwatin baqin qarfe ya xauko wani zobe na azurfa ya dawo ya bawa zuhairu sannan yace da shi “Ka sanya wannan zoben a xan yatsanka cikin yarda Allah zai zama kariya gareka daga sharrin ma’abota tsafi da sihiri babu wani aikin sihiri da zai yi tasiri akan ka kuma komai rintsi kada ka sake ka cireshi daga hannunka a duk sanda wani matsafi ya tunkareka ko mai aikin sihiri za ka ji zoben ya yi motsi a hannunka koda kuwa baka ganinsa, haka kuma idan kaji dokinka ya yi haniniya ko ka lura akwai wani abin cutarwa kusa da kai dan shi yana ganin abinda kai baka gani kuma kar ka sake ka shiga wajen da dokinka ya yi gardama shiga,haka kuma kar ka sake kaji tsoron duk abinda dokinka bai ji tsoronsa ba. Kar ka manta yawan addu’a duk inda kake dan neman tsari da kariya daga wajen Ubangiji ka kiyaye da abinda na sanar da kai”. Zubairu ya karvi zoben ya saka a hannunsa sannan ya yiwa kakansa dattijo godiya ya tashi ya tafi. ** Washe gari da yamma Zuhairu ya sake yin shiri ya kama dokinsa ya hau ya nufi hanyar wannan lambu da Gimbiya Hasima take zuwa akowane yammaci dan ya ganta. Ya ci gaba da tafiya cikin sassarfa da hanzari har ya soma hango bakin lambun da Gimbiya Hasima take zuwa kafin ya qarasa bakin lambun sai ya hangi wasu barade su kimanin arba’in sanye da kayan faxa da makamai sun zagaye wasu ‘yan mata sun kamasu sun xora akan dakansu za su tafi da su, ‘yan 8 BAKAR GUGUWA matan suna kuka da kururuwar neman taimako amma babu wani wanda zai iya taimaka musu a wajen. Zuhairu ya saki linzamin dokinsa ya qara azama dan ya isa garesu yaga abinda yake faruwa da isarsa wajen sai yaga Gimbiya Hasima ce tare da kuyanginta baradan nan suka kama za su tafi da su. Zubairu ya fusata da ganin wannan aikin zallunci ya dakawa baradan tsawa yace da su “Kai fajirai qasqantattu ma’abota zallunci da rashin imani, mai kuke nufin aikatawa ga waxannan bayin Allah da kuka kama?” Baradan nan suka juyo suka dubi zubairu da suka ga shi kaxaine tsaye akan dokinsa sai suka bushe da dariya irin ta mugunta da zallunci sannan xaya daga cikinsu ya bashi amsa da cewar “Babu shakka ajalinka ya kusanto da kai wannan wajen, har kake tambayar abinda muke nufin aikatawa ga waxannan ‘yan mata bari mu sanar da kai dan ya zama guzurinka na tafiya barzahu, zamu tafi da su ya zuwa ga shugabanmu domin su zama bayin mu masu yi mana hidima da biya mana buqata duk sanda muka ga dama idan mun gaji da su ko kuma an samu xaya daga cikinsu ta samu ciki, sai mu sare kanta dan shayar da jininta ga ababan bautarmu, wannan shi ne makomarsu da abinda zamu aikata garesu idan mun tafi da su”. Zuhairu ya fusata da jin wannan maganar yace da su “Kaicon rayuwarku da abinda kuke aikatawa mafi munin makoma na zallunci da rashin imani kuma idan wannan shi ne qudirinku a rayuwa to kuwa zan halakaku da shafe ruhinku daga doron qasa dan kawar da wannan zallunci”. Baradan nan suka sake bushewa da dariya sannan xaya daga cikinsu ya fita gaban zuhairu ya tsaya yana sanye da sulke 9 BAKAR GUGUWA da kayan faxa hannunsa riqe da baqar takobi ya yi huci ya xaga takobin sama cikin qaraji ya taso kan zuhairu. Zuhairu ya zare takobinsa ya tare shi suka haxu ta kubbansu suka yi karciya tartsatsin wuta ya tashi sama zuhairu ya sake kai masa sara bardan ya goce kaifin takobinsa ya tafi ya zuwa wuyan dokinsa nan take ya sare wuyan dokin suka tafi suka faxi qasa gaba xaya. Barden nan ya miqe a fusace kafin ya yi wani yunquri zuhairu ya cimmasa ya sanya takobinsa ya yi masa saran karan tsaye nan take ya tsarga shi gida biyu duk da sulken qarfen da yake jikinsa ya zube qasa matacce bai ko shura ba. Wani daga cikin radan mai qarfin zuciya ya sake zaburowa cikin qaraji fusata zuhairu ya tareshi da zamiya ta salon iya faxa irin na zaratan sadaukai ya kai masa wani gawurtaccen sara da qarfin qarar da ruhi, bardan nan ya sanya garkuwarsa ya kare, garkuwa ta kece gida biyu saboda tsananin qafin saran, qafafun dokin barden na gaba suka durqushe dokin ya yi haniniya wadda ta haxu da hucin saran da zuhairu ya sake kaiwa bardan ya sameshi a tirken wuya nan take ya sare masa kai ya faxi qasa matacce. Da ganin haka sai ragowar baradan suka fusata suka sauke su Gimbiya Hasima da kuyanginta daga kan dakansu suka zare makamai suka tasar ma zuhairu baki xaya cikin qaraji da gunjin fusata. Shima ya karkata garesu ya taho suka haxu yana mai kai sara a tsakaninsu irin na qara da abokan gaba, baradan nan suka zagaye shi ta ko ina suka yi masa qawanya amma duk inda zuhairu ya keta sai dai kaga yana saransu suna zuba qasa matattu, haske takobinsa ya koma jajawur saboda jinin azzaluman baradan nan. Gaba xaya wajan 10 BAKAR GUGUWA ya yamutse aka shiga artabu da baqin gumurzu wanda ya kawo salwantar rayuka barada masu dama. Da baradan suka ga haka sai wasu daga cikinsu suka razana suka koma arcewa suna gudu dan su tsira da rayukansu saboda azaba masu qarar kwana suka ja daga aka ci gaba da kafsawa har sai da zuhairu ya qara da su baki xaya. Bayan zuhairu ya gama da waxannan azzaluman baradan ya tsaya akansu yaga babu sauran wani mai numfashi a cikinsu, sannan ya juya ga su Gimbiya Hasima ya hangeta tsaye a gefe daga ita sai doguwar riga a jikinta babu mayafi ya yi sauri ya sauko daga kan dokinsa ya xauki mayafinta dake yashe a qasa ya tafi inda take ya miqa mata. Gimbiya Hasima tasa hannu ta karvi mayafinta ta rufe jikinta da shi, bata ko yiwa zuhairu magana ba bare godiya abisa taimakon da ya yi masu, sai ma ta kauda kai gabarin duban inda yake ta tafi ta kama dokinta ta hau sauran kuyangunta suma suka kama na su dawakan suka hau, ta kaxa linzamin dokinta suka kama hanyar komawa birnin Bahazum ba tare da ta sake duban inda yake ba bare tayi masa godiya. Wannan lamari ya qara karya zuciyar zuhairu game da begen da yake yiwa Gimbiya Hasima ya duba duk irin taimakon da ya yi mata bata ko yi masa magana ba bare godiya. A tunaninsa saboda girman matsayinta da ganin shi ba xan sarki bane yasa bata ko yi masa magana ba. Ya bisu da kallo har suka vace sannan ya kaxa kansa ya juya ya kama dokinsa ya hau, ya saki linzamin dokin ya fara tafiya. Kafin ya yi nisa da wajen sai ya ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi da ban firgici tamkar faxuwar aradu ta gauraye wajen, sararin samaniya ya yi duhu mafi tsanani daga yankin kudu take qasa 11 BAKAR GUGUWA ta soma girgiza tana raurawa kamar zata tsage. Zuhairu da dokinsa su afka ciki, can daga nesa wata baqar guguwa tare da iska mai tsananin qarfi suka keto daga vangaren yamma, guguwar tana tafe feshin wuta yana zuba daga cikinta, ta tafi wajan da ya halaka azzaluman baradan nan ta wuce ta kansu gaba xaya gawarwakin baradan suka kama da wuta suka qone qurmus hadda sauran dawakansu da suke da rai duk suka hallaka. Zuhairu yaja linzamin dokinsa ya tsaya yana duban wannan abin al’ajabin da yake faruwa, ya ji zoben dake yatsansa ya yi motsi alamar wani ma’abocin aikin sihiri ne ya kusanceshi, ya duba kusa da shi baiga kowa ba, kuma baiji dokinsa ya yi haniniya ba. Ya dubi cikin baqar guguwar nan na irin abinda yake faruwa, nan take ya tabbatar cewa wannan ba komai bane face aikin tsafi da sihiri irin na ma’abota shirka. Wa’iyazubillah yace a ransa yana mai neman tsari da wannan lamari. Sannan sai yaga wannan baqar guguwar ta taso ta nufo inda yake tsaye tana ci gaba da feshin wuta duk abinda ta wuce takansa tun daga itatuwa har ciyayi sai kaga ya kama da wuta ya qone qurmus. Da farko zuhairu ya ji tsoro ya razana amma sai qarfin zuciya da jarumta suka dawo masa saboda ganin dokinsa bai razana ba. Ya ci gaba da addu’a yana mai neman tsari da wannan aikin sihiri, guguwar tana zuwa kusa da shi sai yaga ta ratse tabi gefe bata bi ta inda yake ba ta nuasa tayi gabas. Zuhairu ya bita da kallo har ta vace daga ganinsa sannan ya saki linzamin dokinsa ya ci gaba da tafiya. Akan hanyarsa ta komawa gida kafin ya isa garinsu yarinqa ganin gawarwakin baradan nan da suka arce suka gudu 12 BAKAR GUGUWA sanda yake fafatawa da su, baqar guguwar nan ta biyosu ta halakasu baki xaya daga su har dawakansu sun qone qurmus zuhairu ya sake cika da matuqar mamaki tare da neman tsari da irin wannan aikin sihiri. Ya wuce ya ci gaba da tafiya yana tunani da saqe-saqe a ransa, babu shakka duk abinda ya faru na wannan aikin sihiri yana da nasaba da Gimbiya Hasima sai dai bai yi sani da dalilin faruwar hakan ba. Gashi dai duk baradan da suka kama su Gimbiya Hasima da kuyanginta da nufin cutar da su sun hallaka hatta gawarwakin wanda ya halaka duk sun qone qurmus. Shi kaxai ne da ya yi nufin taimakonta bai halaka ba. Yasan sarki shanban bin Yasar musulmi ne kuma mai ilimin addini ba zai yuwu ace daga shi ne yake aikata irin wannan shirka da sihiri ba. Yana cikin tafiya yana wannan tunanin a ransa, kafin ya isa garinsu sai ya hangi wani mahayi tafe akan doki ya fito daga garinsu zai kama hanyar tafiya birnin Bahazum ya iso inda yake sai zuhairu yaga ashe abokinsa ne Muzaffar dake tafiya birnin Bahazum dan yin fatauci suka haxu suka gaisa zuhairu ya yi nufin sanar da shi abinda ya faru garehi, ko zai samu wani labari game da Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasir da ya ke zuwa birnin Bahazum da mahaifinta yake sarauta yawan fatauci. Zuhairu yace da shi “Ya kautu gara na sanar da kai abinda yake faruwa gareni game da begen gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasir da kake zuwa birnin Bahazum da mahaifinta yake sarauta dan yin fatauci wata qila za ka yi sani da abinda zaka labarta mun game da ita”. Ya kwashe labarin dukkanin abinda ya faru gareshi ya sanar da shi yana mai faxin “Abinda ya bani mamaki shi ne 13 BAKAR GUGUWA duk irin taimakon da na yi mata bata ko yimin godiya ba kasancewarta mafi girman daraja daga ‘ya ‘yan manya sarakunan duniya ni kuma gani ba xan sarki ba kuma ba xan attajiri ba dan haka zuciyata ta karaya ga ambaton qaunarta gareta. A bayan tafiyarta kuma nga wani abin mamki da ban al’ajabi wata baqar guguwa irinta aikin sihiri dake ci da wuta duk ta halaka dukkanin baradan nan da suka tare Gimbiya Hasima da nufin cutar da ita. Babu shakka duk abinda ya faru yana da nasaba da ita, ina labarin wannan lamarin. Muzaffar ya dubi zuhairu da duba irin mamki da al’ajabi sannan ya ce da shi “Kaicon rashin sani dake sanya zuciya afkawa a begen wandda ajali yakan kusanta ga duk wanda ya ambata yana qaunarta, na san baka da masaniyar abinda yake faruwa game da Gimbiya Hasima shi yasa har ka ambata kana qaunarta amman labari ya ishe duk wanda yake da masaniya maganar cewar wani hamshaqin matsafi ne daga cikin manya matsafa ma’abota aikin sihiri dake yamma cin birnin Sinar yake qaunarta. Kuma ya sha alwashin auranta kota wane irin hali dan haka yake halaka duk wanda yace yana qaunart, duk da ita tace bazata auri mushiriki ma’bocn tsafi da sihiri ba ‘ya ‘yan sarakuna da dama tre da manya attajirai masu yawa sun hallaka kn neman aurenta kuma wannan mtsafin shi ne ya halakar da su”. A yanzu Gimbiya Hasima ta zama tamkar hanyar kuantar ajali ga duk wanda yce yana qaunarta hasalima babu wani namiji da ya isa ya tunkareta bare ya yi mata magana matuqar ba mahaifinta ba idan ba haka ba wannan matsafin sa ya halakashi, shi yasa zaka ga a duk inda za ta je babu wani 14 BAKAR GUGUWA namiji mai yi mata rakiya daga cikin baradan mahaifinta daga ita sai kuyangunta mata take tafiya kuma duk abinda ya faru akan wannan baradan na aikin sihiri suka halaka wannan matsafine ya halakasu kaima saboda niyar taimaka mata ka yi shi yasa baka halaka ba. Wannan shi ne dalilin da yasa gimbiya Hasima bata yi maka magana ba bare godiya a sandaka taimaketa babu shakka data buxe baki ta yi maka godiya da kuwa wannan shu’umin matsafin ya halakar da kai don haka kayi hattara. Zuhairu ya cika da matuqar mamaki nain labarn abinda yake faruwa da Gimbiya Hasima tare da gasgata mganar muzaffa ya sana da shi. Saboda abinda ya gani da idanunsa sai dai lamarin baisa zuciyarsa ta karaya ga barin qaunar ta ba sai ma ya ji ya qara begenta a ransa ya kuma xauki alqawarin taimaka mata ya rabata da wannan shu’umin matsafin iyacin iyawarsa. Ya dubi muzaffar yace da shi “Idan har abinda ka ambata ya tabbata gaskiya babu shakka na xauki alqawarin kasancewa wanda zai raba tsakanin Gimbiya Hasima da wannan shu’umin matsafin ko wanene shi, za sadaukar da rayuwata dan na taimaka mata takuvuta daga makircin wannan matsafin matuqar ina raye”. Muzaffar ya sake dubansa cikin mamaki yace da shi “Kaicon zuciyar da ta makance akan soyayya har take naman kai ruhi da gangar jikinta ga halaka. Ka sani cewa rayukan mazaje da dama sun salwanta akan qanarta kamar yadda kai ma za ka halaka matuqar baka nisanta zuciyarka da begenta ba, menene dogaronka na tunkarar hamshaqin matafi da ya halaka manya jarumai ‘ya ‘yan sarakuna da attajirai masu ji da kansu akan Gimbiya Hasima”. 15 BAKAR GUGUWA Zuhairu yace da shi “Kai dai bari ga ambaton irin wannan zance kada imaninka y raunana cewa ni na dogara da Allah ubangijin musulunci, gareshi nake neman taimko kuma na yi imani da cewa shi mairinjayene akan akan kowane irin qarfin tsafi da sihir dan haka bazan tava zama mai rauni ba akan shakkar wani mutum ma’abocin tsafi da sihiri kuma da sannu zan zama mai cimma nasara akan abinda na xauki alqawari akansa cikin yarda Allah” Yana gama faxar maganar ya yiwa muzaffar sallama ya kaxa linzamin dokinsa ya wuce. Muzaffar ya bishi da kallo har ya vace sannan shima ya saki linzamin dokinsa ya ci gaba da tafiya ya zuwa inda ya nufa. Da zuhairu ya isa gida bai sanar da kakansa marwan abinda ya faru gareshi a wannan ranar ba, dan gudun kada yace yarabu da Gimbiya Hasima saboda wannan shu’umin matsafin ya bar maganr a ransa tare da xaukar alqawarin cewa idan har ya koma bakin wannan lambun da Gimbiya Hasima tak zuwa idan ya ganta zai tunkareta ya sanar da ita yana qaunarta ko dan yaga wannan shu’umin matsafin da aka basa labarinsa. ** Bayan wasu kwanaki da faruwa wannan lamarin zuhairu ya sake yin shiri ya nufi bakin wannn lambu da Gimbiya Husaima take zuwa da isarsa wajen ya tadda Gimbiya Hasima bata qaraso ba, ya sauka daga kan dokinsa ya xaure shi, sannan ya

Chapter 1 of 10