Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
tunda kin yi zavi da kasancewa cikin wannan hali tare da jama’ar da ki ke tare da su, to ku yi sauraren da zuwan musibar sa za ku riskeku ta kai ku ga halaka, ita ce za ta zama hanyar salwantar rayuwarku ba za 90 BAKAR GUGUWA ku tava kuvuta daga gareta ku qetare wannan kogi da ku ke ciki ba”. Yana gama ambato wannan maganar ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da zallunci sannan ya vace cikin baqar guguwar da ya bayyana a cikinta ya bar wajen, daga nan sai suka sake jin wata tsawa da rugugi mai ban firgici ya gauraye wajen can daga gabansu sai suka hangi ruwan kogin nan ya dare gida biyu ya yi tsiri sama,tsayinsa zai iya shan kan jirgin ruwan da suke ciki ya nutse da su su halaka, sannan sai wata iska mai qarfi ta soma tura jirgin ruwan yana tunkarar inda ruwan kogin nan ya dare gida biyu za ta dulmiyar dasu su halaka, su zuhairu suka ci gaba da addu’a don neman kiyayewar ubangiji ya kuvutar da su daga wannan musiba da suke ciki. Jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya yana qara tunkarar inda ruwan kogin ya dare gida biyu zai dulmiyar da su su halaka. Shin me zai faru? BAQAR GUGUWA 3 irgin ruwan yaci gaba da tafiya da su zuhairu har ya isa da su inda ruwan kogin ya dare gida biyu ya yi tsiri sama, suka ji an kece da dariya irin ta mugunta da zalunci cikin muryar matsafi Bahalu. J 91 BAKAR GUGUWA Kuma sun tabbatar dacewa shi ne yake yin dariyar duk da cewa basa ganinsa,suka ci gaba da addu’a dan neman kiyayewar ubangiji ya kuvutar da su daga wannan masufa da suke ciki, suna zuwa tsakiyar inda ruwan kogin ya dare gida biyu, sai suka sake jin wani rugugi mai matuqar ban firgici da hauhawa, iska mai qarfi ta sake juya ruwan kogin igiyar ruwa ta murxa, ruwan ya sake yin tsiri sama tare da ambaliya ya dawo akan jirgin ruwan da su zuhairu suke ciki, nan take jirgin ruwan ya yi wata irin qara mai tsananin qarfi ya ragargaje ya fashe qarar fashewarsa tamkar fashewar dutsen da aka jefa da majaujawar wuta. Su zuhairu Baniyatu da sauran jaruman da suke tare da su, suka gantsama cikin ruwan kogin suka nutse a cikinsa sakamakon fashewar da jirgin ruwan ya y, igiyar ruwa ta ci gaba da juyawa da su tana dulmiyar da su qasa tamkar sun halaka baki xaya, matsafi Bahalu ya sake bushewa da dariya daga inda yake tsaye, yana ganin abinda ya faru ga su zuhairu, sannan ya juya ya kama hanyar komawa fadarsa cikin farin cikin ya halaka su zuhairu saboda abinda ya aikata akan su na aikin sihiri. Su kuwa su zuhairu da suka faxa cikin kogin iskar nan mai qarfi ta ci gaba da juyawa da su a cikin ruwan tana dulmiyar da su qasa, sannan ta xaga sy sama har sai da suka yi matuqar jigata, suka fita daga haiyancinsu. Da yake Allah bai qaddara za su hallaka gaba xaya ba, sai igiyar ruwa ta tura su bakin gavar kogin ta watsar da su a gefe bisa rairayi. Suka tashi da qyar suka qarasa fita, daga inda ruwan kogin yake qarasowa idan ya yi ambaliya. 92 BAKAR GUGUWA Bayan sun gama fita daga cikin ruwan suka duba suka ga mutum bakwai ne daga cikinsu suka halaka a cikin wannan ruwa da suka faxa. Adadin yawansu ya zama saura mutum talatin da biyu suka rage daga cikin mutum arba’in da biyu da suka taho tun da farko. Suka yi godiya ga Allah da ya kuvutar da su ba su halaka gaba xaya ba. Tare da addu’a ta neman gafara da rahamar Ubangiji ga waxanda suka halaka. Da yake sunyi matuqar jigata gaba xaya basu bar bakin kogin ba sai da suka huta sosai suka samu nutsuwa. Bayan sun nutsu Baniyatu ta dubi zuhairu tace da shi “Ya inganta mu qara godiya ga Allah da ya bamu nasarar qetare wannan kogin muka iso wannan waje kuma daga nan zuwa lardin Ashtar tafiyar kwanaki biyu ce zamu fara tarar da sansani na farko daga cikin sansanonin baradan dake tsaron wannan fada sai dai kafin mu isa inda wannan sansani yake ya kyautu mu fara neman hanyar da zamu buxe qofofin da ke kulle da fadar idan mun isa inda take, kamar yadda tsohuwa Diyanuna ta umarcemu. Saboda idan bamusan yadda za mu buxe qofofin shiga fadar ba, koda mun yi nasarar yaqar waxannan sansanonin barada mun halakasu mun isa inda fadar take ba zamu samu damar shiga cikinta ba shi ke nan duk wahalar da muka yi ta tashi a banza kenan”. Zuhairu ya yi shuru yana sauraronta da ta gama bayaninta ya yi tambaya a gareta da cewa “To yanzu menene shawararki cikin wannan lamari?” Buniyatu ta sake cewa da shi “Shawarata shi ne na yi sani da labarin wani boka mai suna Afrahu dake zaune a tsaunin wannan kogin da sansanin barada ma’abota tsaro na farko a cikin wannan kogin dutse, idan mun isa gare shi zai sanar da mu yadda za mu buxe qofofin dake 93 BAKAR GUGUWA kulle a fadar sabat idanmun isa gaeta” Zuhairu ya sake duban Baniyatu cikin mamaki yace da ita. “Wane ne kuma Boka Afrahu da za mu tafi gare shi don ya sanar damu yadda za mu shiga fadar, kuma mene ne alaqarsa da fadar da yake da masaniyar yadda za mu shiga cikinta bayan kin ce bayanai sun tabbatar da cewa babu wani mahaluki da yake da masaniyar sirrin fadar, bare yasan yadda za’a shiga shiga cikinta, sannan ki sani cewa yarda da maganar Boka kuskure matuqar abinda ya faxa ya zama bincike ne na cikin alqaluman sihiri da tsafi”. Buniyatu tace da shi “Ai ba za mu je gareshi bane don ya yi mana bincike alqaluman tsafi da sihirinsa ba, sai don kasancewar shi wanda yake da masaniya cikin dukkanin hanyar ta shiga fada, saboda asali ita wannan fadar ba mahaifina bane kaxai ya ginata, sun ginata ne tare da wasu mashahuran bokaye da alqaluman sihiri su biyar, kuma sun ginata da nufin su shiga ciki gaba xaya su zama manya bokayen duniya da za su riqa bada umarni ga qananun bokaye dake cikin wannan lardin kamar yadda suka ga manya sarakunan musulmai suna yi, idan sun kafa daular musulunci ga sauran sarakuna mabiyansu. Bayan sun gama gina fadar ne mahaifinmu ya hillace su ya halaka bokayen guda huxu daga cikinsu, ta hanyar qarfin tsafi da sihirinsa dan ya mallaki fadar shi kaxai. Sauran boka xaya ne yarage daga cikin bokayen mahaifina bai halakashi ba, wato wannan boka Afaraha da zamu tafi gareshi a yanzu, shima ya gane cewa mahaifinmu yana shirin halaka shi ne kamar yadda ya halaka sauran bokayen dan haka ya yi gudun hijira daga wannan da’ira tasu ya koma cikin wani kogon dutse 94 BAKAR GUGUWA a cikin wannan daji ya zauna a cikinsa dan ya tsira daga hallaka. Mahaifinmu ya yi ta neman inda ya shiga a cikin faxin duniya dan ya bishi ya halaka shi kafin ya tare a wannan fada, saboda gudun kada a samu sauran wanda yasan sirrin fadar a haxa baki da shi dan kawo hari a gareshi, da kuma sanin shu’umancin wannan boka kada wata rana ya dawo gareshi dan yi ramuwa, amma yarasa inda ya shiga cikin alqalaman sihirinsa saboda kasancewarsa qwarare kuma masani cikin alqaluman sihiri na bada kariya ga wani voyayyen al’amari, dan Boka Afrahu shi ne ya samar da wannan qofofi guda uku dake kulle da fadar da kuma duk wannan tsaro dake cikinta, sai dai a yanzu ya zama nakasashe wani sashe daga jikinsa ya dena amfani sakamakon jifansa da alqaluman sihiri da mahaifinmu ya yi a sanda yake qoqarin halakashi kafin ya yi hijira ya dawo wannan waje,kuma mahaifinmu bai samu nasara gano inda yake ba cikin bincikensa sai bayan shekara biyu bayanai suka bayyana a gareshi, kuma a ranar da ya gama shiri da nufin tafiya wannan kogon dutse halaka Boka Afrahu sai ajali ya gabata gareshi ya halaka. Dan haka zamu tafi ga wannan Boka dan ya sanar da kai yadda za ka samu nasarar shiga fadar, idan mun isa inda kogon dutsen yake kai kaxai za ka shiga cikinsa, kuma zan sanar da kai yadda za ka shiga da abinda zaka sanar da Boka Afrahu dan ya amince ya sanar da kai sirrin buxe qofofin shiga fadar, bisa ga sharaxi kanaso ka halaka mahaifinmu ne saboda ba shi da labarin rasuwarsa”. Data gama yi masa wannan bayyani sai zuhairu ya amince da shawararta. Daga nan suka tashi tare da sauran 95 BAKAR GUGUWA jaruman da suke tare da su suka ci gaba da tafiya, da yake tafiyar qafa ce ba akan dawakai ba, kuma ga ramuka da kwazazzabai da suke ratsawa ta tsakaninsu basu isa inda wannan kogon dutsen da Boka Afrahu yake cikinsa ba sai da suka yi tafiya kwana uku. ** Shi kuwa matsafi Bahalu bayan da ya koma fadarsa cikin murna da farin ciki na zato cewa su zuhairu da jaruman da suke tare da shi sun halaka a cikin wannan kogin da ya baro su, ya koma aikansa na saurara bayyanar haxewar taurarin nan na aikin sihiri su zama xaya, dan samun damar mallaka Gimbiya Hasima ta zama matarsa kamar yadda ya yi imani da tabbatar hakan, yakan ziyarci xakin da take ciki a kowace rana dan yaganta ya ji sanyi a ransa, kuma a kullum qaunarta da muradinta na qara qaruwa a cikin zuciyarsa, sai dai bashi da ikon kusantarta da nufin biyan buqatarsa da ita, saboda alqaluman sihiri da ya yi imani da su basu bashi damar tabatar da hakan ba. Bayan kwanaki biyu sai ya ji zuciyarsa tana mai muradin sanin yadda su zuhairu suka halaka dan fanin qarshen su da yadda suka kasance a bayan halakarsu kamar yadda yake zato, ya tafi ga kaskon nan na lu’u-lu’u dake xauke da farin rairayi a cikinsa ya yi ane akan farin rairayin ya share sannan ya rufe idanunsa ya soma karanta waxansu xalasumai na cikin sihiri bayan ya gama ya buxe idanunsa bayanai suka bayyana a gare shi cikin wani mummunan lamari mai matuqar ban mamaki da tu’ajjabi a gareshi da ya sashi fargaba da razani ganin cewa zuhairu da sauran jarumai da suke tare da shi basu 96 BAKAR GUGUWA hallaka a cikin wannan ruwan kogin gaba xaya ba wasu daga cikin sune suka halaka. Nan take kammaninsa suka sauya daga yanayin farin ciki ya zuwa baqin ciki, zuciyarsa ta yi masa qunci ya sake share rairayin yayi wani rubutun akansa dan neman sanin halin da suke ciki a yanzu, bayanai suka sake bayyana a gareshi dake sanar da shi cewa, su zuhairu da sauran jaruman da suka rage basu halaka ba, suna cikin dajin dake tsakanin lardin Ashtar da ruwan da suka nutse a cikinsa yake zaton sun halaka kuma suna kan hanyar sune ta zuwa cikin wani kogon dutse inda wani boka masanin sirrin buxe qofofin shigowa fadarsa ta Darul sabar da ke kulle yake zaune, dan neman sani daga gareshi ya sanar da su yadda za su shiga fadar. Matsafi Bahalu ya sake yin matuqar mamaki da ganin cewa akwai wani biladama masanin sirrin wannan fada a duniya ba tare da ya san da shi ba. Don haka ya quduri aniyar zuwa ya halaka wannan boka kafin su zuhairu sukai gare shi ya sanar da su sirrin shiga fadarsa. Duk da yana ji a ransa cewa su ba masu samun nasara bane akan sa koda ya sanar da su sirrin shigowa fadar. Saboda sansanonin ma;abota tsaro da bada kariya da yake tare da su kafin su kai ga isowa inda fadar take. Nan da nan ya tashi ya yi shirinsa na kayan aikin Bokanci da sihiri ya fita daga fadar ya kama hanyar tafiya kogon dutsen da Boka Afrahu yake zaune a cikinsa. Dan ya halaka shi kafin ya kai ga sanar da zuhairu sirrin shiga fadarsa. ** Su kuwa su zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi, bayan da suka isa bakin wannan kogon dutsen da boka Afrahu yake zaune a cikinsa. Suka ja linzamin dawakansu suka 97 BAKAR GUGUWA tsaya. Buniyatu ta dubi zuhairu tace da shi “Wannan shi ne kogon dutsen da boka Afrahu yake zaune a ciki, kuma kai kaxai za ka shiga cikinsa, don neman ya sanar da kai sirrin shiga fadar ta Absar da muka zo nema a gare shi. Saboda idan muka shiga tare da ni zai ganeni ya shaida cewa ni ‘yar gidan Boka Kauwas ce, wanda ya aikata wannan aikin sihiri na naqasar da jikinsa ya yi akansa, kuma ya nemi halaka shi kafin ya yi gudun hijira daga da’irar da suke zaune gaba xaya. Ba zai tava yadda da ni ba, kuma ba zai tava yadda da abinda zan ambata a gare shi ba. Don haka sai dai ka shiga kai kaxai, kuma zan sanar da kai yadda za ka shiga wannan kogon dutsen”. Ta ciro wani zobe na azurfa daga hannunta ta miqa masa sannan tace da shi “Ka sanya wannan zobe a xan yatsanka dan ba za ka iya shiga cikin kogon dutsen ba, sai kana tare da wannan zoben idan ka shiga cikin kogon dutsen za ka riski Boka Afrahu zaune akan wata karaga ta zinare ya harxe qafaffunsa. Gaba xaya jikinsa ya naqasa tun daga kafaxarsa har ya zuwa qafarsa, babu abinda yake iya motsawa bare ya yi amfani da shi. Hannnayansa sun shanye, kan sa ne kawai yake iya waiwaiyawa baya, ko kuma ya buxe baki ya yi magana, haka kuma yana iya hangen duk abinda zai shigo cikin kogon dutsen koda kuwa aljani ne”. Idan ka tunkari inda yake za ka ji ya daka maka tsawa, ko kuma ya yi maka magana. Kada ka sake ka amsa masa har sai ka isa inda yake zaune. Ka durqusa a gabansa ka shafi dogon farin gemunsa, sannan ka cire wannan zobe da na baka ka sanya a xan yatsansa ka kama hannunsa na dama ka saka masa zoben ana sa xan yatsan, za ka ga ya dubi zoben sannan 98 BAKAR GUGUWA ya sake dubanka kada dai ka sake ka yi magana sai ka ci gaba da saurare dan jin abinda zai ambata a gareka”. “Idan ya nemi sanin sunanka ka sanar da shi sunanka na gaskiya, amma ka shaida masa mai wannan zobe shi ne mahaifinka, kuma ya turoka garesa ne dan ka taimaka masa ya samu waraka daga halin naqasa da yake ciki kuma kai ma ka samu waraka daga aikin sihirin da yake tare dea kai. Ka faxi buqatar ka ta son ya sanar da kai sirrin buxe qofofin da ke zagaye da fadar Darul sabar dan ka samu nasara shiga cikinta ka halaka wanda ya mallaketa, ka kuma xebo ruwan da ke cikin rijiyar tsakiyar fadar dan ka kawo masa, wanda shi ne za a yi amfani da shi dan karya aikin sihirin da yake tare da shi da kuma wanda yake tare da kai”. “Idan ya ji wannan bayani da za ka yi masa na tabbatar zai yi matuqar farin ciki sosai. Zai kuma sanar da kai sirrin yadda za ka shiga wannan fada. Sai dai duk abinda ya uwarce ka ko ya sharxanta ma kafin ya sanar da kai yadda za ka shiga fadar, kada ka yi masa musu ko jayayya ka ce ka amince dan ya sanar da kai” Da ta gama masa wannan bayani, sai zuhairu ya karvi zoben ya sanya a xan yatsansa. Sannan ya kama hanya ya tunkari qofar shiga wannan kogon dutsen. Ya shiga cikinsa da shigarsa ya ga kogon dutsen yana da girma da faxi, ya ci gaba da tafiya har ya isa wani waje mai kama da fada an qwawata shi da abubuwan qawa da ado mai tsari. Can daga gefe ya hangi Boka Afrahu zaune akan karagar zinare kamar yadda Buniyatu ta sanar da shi, sai ya ji an daka masa tsawa da maxaukakiyar murya mai matuqar razanarwa da ban firgici aka ce da shi. 99 BAKAR GUGUWA “Wanene kai kuma me ya kawo ka cikin wannan kogon dutsen? Halaka za ta tabbata a gareka idan ba ka yi gaggawar amsa tambayar da mai ambato ya yi gareka ba” Zuhairu bai yi magana ba, kamar yadda Buniyatu ta uwarce shi, haka zalika bai ga mai yin magana a gare shi ba. Dan ya haqiqance ba wannan boka da ke zaune akan karaga da ke gabansa ne ya yi magana ba, aka sake daka masa tsawa da murya wadda tafi ta farko hauhawa, tare da maimaita abinda aka faxa da farko, a wannan karo ma zuhairu bai yi magana ba, ya ci gaba da tunkarar inda mutumin yake zaune har ya isa gare shi. Ya durqusa a gabansa ya shafi dogon farin gemunsa sannan ya cire zoben nan na azurfa da Buniuatu ta bashi ya kama hannunsa na dama ya saka masa zoben a xan ysatansa sannan ya ci gaba da saurare don jin abinda zai ambata a gareshi. Boka Afrahu ya dubi zoben sannan ya dubi zuhairu yace da shi “Wanene kai da ka mallaki zoben HINAS na babban aminina. Kuma me ya kawo ka gareni har ka sanya zoben a hannuna?” zuhairu ya ce da shi “Sunana zuhairu, kuma me wannan zoben shi ne mahaifina, ya turo ni gareka ne don na taimaka maka ka samu waraka daga halin da kake ciki na naqasa irin ta aikin sihiri” Ya kwashe labarin abinda ya kawo shi gare shi ya sanar da shi, kamar yadda Buniyatu ta tsara masa. Sannan ya shaida masa buqatarsa ta san ya sanar da shi sirrin buxe qofofin da ke fadar Darul sabar dan ya samu nasarar shiga cikinta da xebo masa ruwan da ke cikin rijiyar tsakiyar fadar wanda da shi ne za a karya aikin shirin da ke jikinsa. Da boka Afrahu ya ji wannan bayani sai ya yi murmushi na nuna farin cikinsa har haqoransa suka bayyana sannan ya 100 BAKAR GUGUWA dubi zuhairu yace da shi “Abota da aminci sun tabbata tsakanina da Boka Gulaisu mahaifinka da ya turoka dan ka taimaka a gareni na fita daga wannan halin da nake ciki, babu shakka zan sanar da kai sirrin yadda za ka buxe qofofin da ke fadar sabar ka shiga cikinta da zarar ka isa inda take dan kuwa nine na samar da qofofin da tsaron da ke tare da su, dan haka sirrin buxe qofar yana tare da ni, kuma na daxe ina neman wanda zan sanar da shi wannan sirri ko dan xaukar fansar abin da Boka kauwas ya aikata na cin amana da nufin halaka ni bayan mun gama ginin wannan fada” “Da farko kafin ka isa inda fadar take za ka fara tarar da sansanonin ma’abota tsaro har guda uku da ke gadin fadar. Kowanne sansani suna da tsananin yawan da ba za ka iya yaqi da su ba, bare ka samu nasara akan su, hikimar da za ka yi shi ne ka duba bakin tsaunin da baradan suke zaune za ka ga gunki da suke bauta a gare shi, ka sanya takobinka ka sare kan gunki shi kenan za ku samu nasara akan baradan duk da tsananin yawa da qarfin tasirin tsafi da sihirinsu. “Idan har ka samu nasarar hallaka waxannan barada ka isa inda fadar take kada ka ce za ka tunkari qofar kai tsaye ka ce za ka buxeta. Zan mallaka maka wani makulli da za ka buxe qofofin da shi, gaba xaya duk qofar da ka sa makullin a jikinta qofar za ta buxe da kanta, sai dai kada ka yi saurin shigarta har sai ka jira kaga abinda zai fito daga cikinta. Idan na cutarwa ne ka sanya takobinka ka halaka shi, idan kuma abin tsoratarwa ne kada ka razana ka bi ta cikinta ka wuce”. “Qofa ta biyu ita ce BUWAS za ka tadda ita a buxe kada ka sake ka shiga cikinta har sai ka jawo qofar ka sanya mukulin da zan baka ka kulleta, sannan za ka ga qofar ta sake 101 BAKAR GUGUWA buxewa da kanta, ba sai ka sake buxewa ba sai ka bi ta cikinta ka wuce ka tafi ya zuwa qofa ta gaba” “Qofa ta qarshe ita ce JAHABU idan ka isa inda ta ke za ka tadda tana ci da wuta, babu damar ka isa gareta ka sanya mukullin ka buxe, ka duba daga gefen qofar vangaran dama za ka ga wani mulmulallan farin dutse ka sanya takobinka ka sari dutse za ka ga wutar da ta ke ci a jikin qofar ta mutu, daga nan sai ka isa gareta ka sanya mukullin ka buxeta ka shiga cikin fadar. “Idan ka samu nasarar tsallake waxannan siraxi ka shiga cikin fadar, shi kenan ka gama da duk wani aikin sihiri da siddabaru da ke bada kariya ga wanda yake zaune a fadar, kuma babu wani aikin na alqaluman sihiri da zai sake tasiri akan ka, sai ka yi qoqarin yaqar shi wannan shu’umin matsafi maci amana a gare ni ka halaka shi, idan ka samu nasara a kansa sai ka xebo ruwan da ke cikin rijiyar tsakiyar fadar ka sha, dan karya aikin sihirin da ke tare da kai, sannan ka xauko wanda za ka kawo a gareni ka taho da shi ka dawo. Sai dai kafin na baka wannan mukulli zan kafa maka wasu sharuxxa da nake so ka kiyaye, ka kuma amince da su” “Da farko idan ka samu nasara hallaka wannan matsafi da ke fadar kada ka sake ka ce za ka tava komai a cikin fadar, kada kuma ka sake ka ce za ka fitar da wata daga cikin kuyangi mata da za ka tarar a cikin fadar. Idan ka yi nufin aikata xaya daga cikin abinda na haneka babu shakka fadar za ta nutse da kai ka halaka, kuma kada ka sake ka ce za ka bawa wani mukullin wannan fada, ka dawo da shi gareni kamar yadda na baka da kaina”. 102 BAKAR GUGUWA Zuhairu yace ya amince da wannan sharaxi da ya kafa masa, sannan Boka Afrahu yace da shi tafi ga waccan kwatarniya da ke ajiye, za ka tadda ita a cike da ruwa duk abinda ka ga ruwan yanayi kada ka tsorata ka sa hannu ka laluba za ka ji mukullan waxannan qofofi a cikin ruwan sai ka xauko ka tafi ya zuwa wannan fada ka aikata abinda na umarce ka da sannu za ka kasance ma’abocin samun nasara matuqar ka kiyaye da abinda na sanar da kai” Zuhairu ya yi masa godiya bayan da ya gama yi masa wannan bayani, sannan ya tashi ya nufi inda wannan kwatarniya take girke a qarshan kogon dutsen ya tadda ruwan da yake cikinta yana tafarfasa, tirir na tashi sama. Ya kai hannu zai laluba cikin ruwan ya xauko makullin, akwai wani qaramin zobe na baqin qarfe a qaramin yatsansa ya suvuce ya faxa cikin ruwan da ke cikin kwatarniyar nan take zoben ya narke saboda musiba. Zuhairu bai razana ba duk da ganin abinda ya faru ya sanya hannunsa a cikin ruwan dan ya xauko mukullin maimakon ya ji tsananin zafi a cikin ruwan ga mamakinsa sai ya ji ruwan ya yi matuqar sanyi, tamkar ba shi ne yake tafasa da tiriri ba, ya laluba a hankali ya ji ya tava mukullin a qasan ruwan ya sa hannu ya xauko sannan ya juyo ya sake yin godiya ga Boka Afrahu ya kama hanyar fita daga kogon dutsen don komawa ga su Buniyatu da ke waje. Kafin zuhairu ya kai ga fita daga kogon dutsen sai ya ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi da amo mai hauhuawa ta gauraye cikin kogon dutsen. Ruguginta tamkar zai tsaga dutsen ya fashe,ya juyo dan ya ga abinda yake faruwa sai ya hangi wata irin iska mai qarfi da ke cuxanye da baqar guguwa ta keto cikin kogon dutsen ta lulluve inda boka Afrahu yake zaune 103 BAKAR GUGUWA akan karagarsa wajen ya yi duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare. Nan take zuhairu ya fahimci cewa matsafi Bahalu ne ya bayyana a cikin kogon dutsen dan ya hana Boka Afrahu ya sanar da su sirrin shiga fadarsa da suka tunkari zuwa gareta. Sai dai kuma ya zama makarare dan tuni ya sanar da su abinda suke son sani daga gare shi. Baqar guguwar tana gama sauka a cikin kogon dutsen sai ga matsafi Bahalu ya bayyana ta cikinta ya xaga sandar tsafi da ke hannunsa cikin tsananin fushi da fusatuwa ya makawa boka Afrahu a tsakiyar kansa, Boka Afrahu ya yi wata kaxaitacciyar qara irin ta azabar fitar rai, kansa ya fashe, qwaqwalwarsa ta fantsama a jikin bango, kogon dutsen nan take ya zube qasa matacce bai ko shura ba, gawarsa ta kama da wuta ta qone qurmusu. Bayan matsafi Bahalu ya halaka wannan boka ya juyo ga zuhairu a fusace yace da shi. “Na yi sani da zuwanku wannan waje da abinda ya kawo ka, kuma kamar yadda na sanar da kai a farko marra cewa ba za ka tava samun nasara a kaina ba, komai bibiyar bokaye da masana alqaluman sihiri dan ka samu nasarar zuwa fadata, kuma kamar yadda na hallaka wannan boka da ku ka zo gare shi dan neman sani, haka kai ma zaka hallaka a cikin wannan kogon dutsen ba za ka fita daga cikinsa ba”. Yana gama faxar wannan magana ya xaga sandar tsafin da ke hannunsa ya daki bangon kogon dutsen da ita. Nan take kogon dutsen ya soma girgiza da raurauwa yana tsatstsagewa tamkar zai fashe ya hallaka duk abinda yake cikinsa. Qasa ta soma zabtarowa tana zubowa daga saman kogon dutsen ta ko’ina alamar kogon dutsen ne zai fashe, Matsafi Bahalu ya yi 104 BAKAR GUGUWA sauri ya vace cikin alqaluman sihirinsa, baqar guguwar nan da ke cuxanye da qaqqarfar iska suka keta bangon kogon kogon dutsen suka fice matsafi Bahalu ya tafi ya bar zuhairu a cikinsa. Kogon dutsen ya ci gaba da girgiza yana tsatstsagewa da zabtarowa yana zubowa qasa. Zuhairu ya juya cikin hanzari da azama ya kama hanyar fita daga cikinsa. Yana gudu kogon dutsen na ci gaba da zabtarowa daidai sanda ya kawo qofar fita daga cikinsa sai kogon dutsen ya yi wata irin qara mai tsananin qarfi ya fashe, qarar fashewarsa tamkar faxuwar aradu iska ta yi sama da zuhairu ta jefar da shi can a gefen wajen da kogon dutsen ya fashe tare da wata wuta da ba a san mafarinta ba tare da qura fashewar suka turnuqe suka tashi sama. Buniyatu da sauran jaruman da suke tsaye abakin kogon dutsen suna jiran fitowar zuhairu sun ga zuwan baqar guguwar nan ta keta kogon dutsen ta shiga

Chapter 7 of 10