Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 10
cikinsa a sanda matsafi Bahalu ya bayyana. Sannan kuma sun sake ganin fitowar baqar guguwar daga cikin kogon dutsen ta tashi sama. Daga nan sai suka ji wannan tsawa mai tsananin qarfi da ruggugi na fashewar dutsen har sai da suka razana suka ja baya, saboda jin wannan qarar, sannan sai suka ga dutsen da zuhairu ya shiga cikinsa ya dagargaje ya fashe. Hankalin Buniyatu da na sauran jaruman ya yi matuqar tashi, suka razana matuqa da ganin fashewar dutsen da zuhairu yake ciki, Buniyatu ta tashi cikin kixima da ruxani ta nufi wajen da dutsen yake, amma hucin wutar da ya gauraye wajen ya bugi jikinta tsananin zafi ya sa ta kasa qarasawa inda wutar take. Dole ta juyo ta dawo da baya, ta fashe da kuka dan razana da tunanin zuhairu ya hallaka. Suma sauran jaruman da suke 105 BAKAR GUGUWA tare da ita jikinsu ya yi sanyi, saboda ganin abinda ya faru babu wanda bai yi zaton zuhairu ya hallaka ba daga cikinsu. Suna tsaye cikin wannan hali na fargaba da jimami sai suka hangi zuhairu ya keto ta cikin duhun hayaqin da ya lulluve wajen. Sai dai ga alama ya yi matuqar jigata saboda ganin yadda yake tafiya a galabaice. Nan take fargabarsu ta koma farin ciki suka yiwa Allah godiya da ya sa zuhairu bai hallaka ba, wasu daga cikin jaruman suka tafi gare shi suka taro shi, suka qaraso da shi inda suke tsaye suna jiransa. Suka kai shi gindin wata inuwa mai sanyi, suka zaunar da shi dan ya samu nutsuwa ya huta. Bayan zuhairu ya huta, ya shaida musu ya samu nasarar abinda ya shigar da shi kogon dutsen ya basu labarin abinda ya faru tsakaninsu da boka Afrahu har ya mallaka masa mukullin da zai buxe waxannan qofofi da kuma bayyanar matsafi Bahalu ya hallaka Boka Afrahu, da abinda ya faru tsakaninsa ya yi nufin hallaka shi, su Buniyatu da sauran jaruman da suke tare da shi suka yi farin cikin samun nasara tare da yin godiya ga Allah da ya kuvutar da zuhairu daga mugun nufin matsafi Bahalu bai hallaka ba. Da yake yamma ta qarato rana ta kusa faxuwa sai suka samu waje suka yada zango dan su kwana anan kafin gari ya waye su ci gaba da tafiya. ** Da gari ya waye su zuhairu suka yi sallar asubahi, suka yi addu’ar sannan suka tashi suka kama hanya, suka ci gaba da tafiya kafin rana ta xaga sama sosai suka isa lardin Ashtar da shigarsu cikin lardin suka ji yanayin wajen ya sauya gaba xaya dajin ya yi duhu wani farin hayaqi ya gauraye ko ina, iska mai 106 BAKAR GUGUWA tsananin zafi dake busar da maqoshi tana busawa daga ko ina suna qara shiga cikin lardin zafin da suke ji na daxa qaruwa. Haka suka wanzu suna tafiya har rana ta kusa faxuwa suka yada zango a lokacin zuhairu ya basu shawarar yadda za su bi wajen yaqar waxannan sadaukan. Jaruman suka amince da shawarar da zuhairu ya kawo akan yadda za su yaqi baradan da ke bayan tsauni. Sannan masu harbi da kibiya da masu majaujawa suka je suke voya a cikin duhun itatuwa kamar yadda zuhairu ya umarce su. Su kuma su zuhairu,Buniyatu da sauran jarumai masu faxa da mashi da takubba suka tafi suka tunkari inda rundunar baradan suke. Da zagayawarsu bayan wannan tsauni sai suka hangi dandazon baradan nan sun jeru sahu-sahu, sun yi sujjada gaban wani gunki da ke kusa da tsaunin. Wasu kuma daga cikinsu suna tsaye dan lura da duk abinda zai tunkaro wannan waje daga kowanne vangare da ganin su zuhairu sun tunkaro inda suke sai xaya daga cikin baradan nan ya daka musu tsawa da maxaukakiyar murya yace da su. “Kai waxannan al’umma fanxararru, hallaka ta tabbata a gareku bisa ga shigowar ku lardin Ashtar da zuwan ku wannan waje da sanin ku ko kuma bisa ga rashin sani na kuskure. Haqiqa makoma ta munana gareku cikin qasqanci da zama ababan shayar da jinin ku ga abin bautarmu dan girmamawa” Zuhairu ya maida masa da raddi da cewa “Kaicon mai ambato da abinda yake ambatawa cikin zantukansa marasa tasiri, ka sani cewa ba ka da ikon tabbatar da hallaka akan mu har sai wanda ya halicce mu ya tabbatar da hakan a garemu. Kuma mun yi imani da shi tare da neman taimakonsa don mu 107 BAKAR GUGUWA karya rundunar mushirikai ma’abota bautawa gumaka wanin Allah ba Allah da ya halice su ba. Don haka ina mai yin ishara a gare ku da cewa; hallaka ce ta gabata gare ku da kawo qarshen shirka da baxala da kuke aikatawa a bayan qasa”. Mai maganar nan na farko ya fusata da jin abinda zuhairu ya ambata ya sake yin magana cikin tsawa yace da shi “Kai dattijo gajiyaye ma’abocin rauni da gazawa ka bari matasa masu sauran jini a jikinsu su yi magana ba kai dattijo ba wanda ba shi da tasiri aikata komai na jarumta. Kuma na rantse da girman daraja gunki da nake bauta a gare shi sai na hallaka ka don na tabbatar da girmansa da kuke qasqantarwa” Ya fidda wata irin baqar takobi daga xamararsa ya tasama zuhairu a fusace da nufin hallaka shi. Shi ma zuhairu ya fidda tasa takobin ya tare shi suka yi haxuwa irin ta karon battar qarfe, tare da kaiwa juna sara, irin na hallaka abokin karawa. Kaifin takobbinsu ya haxu a sararin samaniya da qarfi barden nan ya ji tamkar sun haxa qaifin takobi da matashin jarumi sadauki, savanin dattajo mai raunin da tarin shekaru da yake kallon zuhairu, suka rabu babu wanda ya samu wani. Suka sake zaburowa sukai sara ga juna zuairu ya goce kaifin takobin barden ya wuce, kafin ya juyo ya sanya tasa takobin cikin gwanintar sara da zafin nama ya sare kan barden ya yi tsalle sama gangar jikin ta faxi qasa daga nan tasa ta qare bai ko shura ba. Da ganin haka sai ragowar baradan da ke tare da shi suka yi qaraji da kururuwa mai qarfi suna ambatan wasu kalamai da su zuhairu ba sa jin abinda suke cewa. Nan take sauran baradan da ke cikin halin yin sujjada gaban gunki suka xago cikin sauri, sannan suka riqa zare makamansu suna 108 BAKAR GUGUWA tasowa kan su zuhairu da sauran jarumai da suke tare da shi, suka ja daga cikin shirin artabu da waxannan baradan duk da cewa idan suka farmusu wani ma ba zai ga koda gawarwakin su zuhairu ba, saboda tsananin yawansu. Kafin su isa gare su sauran jarumai da suke tare da su zuhairu suka soma sakar musu ruwan kibau da jifa da majaujawa, daga cikin duhun itatuwan da suke voye. Baradan nan suka riqa zuba qasa matattu tamkar yayyafi. Duk wanda ya zaburo kan su zuhairu sai ka ga ya faxi qasa matacce ba tare da san abinda ya hallaka shi ba. Sai dai masu harbi da kibiyar da jifa da majaujawa suka ci qarfin rundunar baradan, sannan su zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka farma rundunar baradan da sara. A ka yi arangama da qazamar haxuwa. Nan take waje ya yamutse, qura ta turnuqe ta tokare sararin samaniya. Qarar haxuwar takubba ta cika wajen, kururuwar mazaje ta yawaita. Zuhairu na kai sara cikin baradan yana halaka su yana qara dannawa cikinsu. Duk inda ya sa gaba a tsakanin baradan sai dai ka ga wajen ya zame masa hanyar wucewa. Haka kuma komai yawan baradan da suka taso kansa sai ya qarar da su gaba xaya, da kaifin takobinsa. Haka ya yi ta keta dandazon baradan nan har sai da ya isa inda wannan gunki da suke bauta a gare shi yake, ya xaga takobinsa ya yi kabbara ya sari kan gunki da dukkanin qarfinsa, ya raba shi da gangar jikinsa. Da sare kan gunki sai suka ji wata irin qara mai tsananin qarfi ta gauraye wajen, gangar jikin gunki ta kama da wuta. Tsaunin da ke kusa da su ya soma girgiza yana tsatstsagewa. Da ganin haka sai baradan da ke bauta ga wannan gunki suka firgita, hankalinsu ya tashi suka gigita, tsaunin da 109 BAKAR GUGUWA suke samun abinci da abin sha daga gare shi ya tarwatse ya fashe. Nan take suka soma watsar da makaman da yake hannunsu suna fantsama cikin daji a firgice. Su zuhairu da sauran masu harbi da kibiya da jifa da majaujawa suka ci gaba da hallaka su suna yi musu kisan qare dangi, har sai da suka ragargaza rundunar baradan suka tarwatsa su, da yawa daga cikin baradan sun hallaka. Wasu kuma suka fantsama cikin daji suka arce a firgice dan su tsira daga hallaka da guguwar ajali da ta turnuqe a tsakanin sannaninsu. Bayan su zuhairu sun gama da baradan da suka rage ba su samu damar arcewa aga wajen ba. Suka qarar da su baki xaya, sauran jaruman da suka voye a cikin duhun itatuwa suka taho suka haxu da su zuhairu. Suka dubi baradan da suka hallaka da irin yawansu suka yi godiya ga Allah da ya ba su nasara akan wannan rundunar mushirikai, suka ga bayansu don su yi imani da cewa ba qarfi da dabarunsu ce ta sa suka samu nasara akan su ba, illa taimako daga Allah. Bayan sun nutsu qurar yaqi ta lafa, sai suka hangi wani kogi a kusa da inda suke tsaye, Ruwa yana gudana a cikin kogin garai-garai fari tas da shi. Da yake su zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi, suna tare da qishir ruwa ga kuma gajiya ta artabu da gumurzu da suka yi da waxannan barada. Don haka suka tunkari wannan kogin da nufin zuwa gare shi su sha ruwa.suna isa inda kogin yake suka fara xiban ruwan za su sha. Buniyatu da ke tare da su da ta ga abinda suke shirin aikatawa ta yi musu magana cikin tsawatarwa ta ce da su. “Kada wanda ya sake ya sha wannan ruwa daga cikin ku, saboda musifa dake tare da shi” Jaruman nan suka dakata 110 BAKAR GUGUWA gabarin shan ruwan suna masu saurarenta da jin abinda ta ambata gare su, Buniyatu ta ci gaba da cewa. “Babu shakka duk wanda ya sha wannan ruwa daga cikin ku to kuwa zai hallaka saboda akwai guba irin ta aikin sihiri a cikinsa. Su kan su baradan da ke zaune a bakin wannan tsaunin ma’abota tsaro ga fadar matsafi Bahalu ba sa shan wannan ruwan kogi sukan sha ruwa ne da yake zubowa daga saman wannan tsauni da yake kusa da su, sai dai idan wani daga cikin su ya yi laifi akan yi masa azaba da wannan ruwa a ba shi ya sha don ya hallaka. Da suka ji wannan bayani na Buniyatu sai suka haqura da shan ruwa. Suka tashi suka bar bakin kogin, suka xauki makamansu da sauran kayayyakin su,suka ci gaba da tafiya duk da tsananin qishirwa da take tare da su, suna masu neman inda za su samu ruwan da za su sha. Kafin su isa sansanin baradan ma’abota tsaron da ke gaba. ** Al’amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya bar zuhairu a cikin kogon dutsen Boka Afrahu a sanda kogon dutsen yake shirin fashewa ya tarwatse. Ya koma fadarsa cikin yaqinin cewa zuhairu ya halaka a cikin kogon dutsen. Don ya yi imani cewa babu yadda za’a yi ya kuvuta ya fita daga cikin kogon dutsen ba tare da ya hallaka ba. Kuma bai sake komawa takan jaruman da ke tafe tare da zuhairu ba, don ya san ba su da tasirin aikata komai akansa, kuma ya san za su hallaka ne a cikin wannan daji saboda ba su da damar shigowa lardin Ashtar ko kuma su koma inda suka fito, don haka ya maida hankalinsa ga sauraren haxewar taurarin nan na aikin sihiri da 111 BAKAR GUGUWA za su tabbatar da mallakar Gimbiya Hasima a gare shi, ya samu damar kusantar ta. Bayan kwanaki uku yana zaune a fadarsa, sai ya ga fadar ta yi duhu, duhun da ke bayyanar da isowar saqo a gare shi cikin alqaluman sihirinsa. Ya ji an yi ambato a gare shi da wata firgitacciyar murya mai nuna gajiyawa. Muryar mai maganar tana raurawa aka ce da shi. “DARUL UKUB ta karye, sansanin ma’abota tsaro na farko ga wannan fada mai daraja, wasu jama’a da ba a san maqasudin abinda ya kawo su ba, ko kuma aka haqiqance qarfin tasirin abin bautarsu, sun farmaki sansanin cikin wata sa’a daga cikin sa’o’in da mazauna sansanin suke gudanar da ibadarsu. An samu tsaiko da tagaiyara baradan ma’abota tsaro da ke zaune a wannan sansani. Wanda hakan ya jawo mummunan yanayi na salwantar rayukan baradan cikin qasqanci. Da yawa daga cikin su sun hallaka, gunkin da suke bauta a gare shi ya kama da wuta ya qone qurmus. Tsaunin da suke samun abinci daga gare shi ya tarwatse ya fashe, hakan tasa sauran baradan suka razana suka fantsama cikin daji akan samu nasara akan su aka karya sansanin su Darul Uqub ta faxi”. Da jin wannan saqon sai ran matsafi Bahalu ya vaci, zuciyarsa ta harzuqa ya fusata da fushi mara musaltuwa ya tashi cikin sauri ya tafi ga kaskon bincikensa na alqaluman sihiri don neman sani ga wanda suka aikata wannan al’amari akan sansanin baradansa. Bayan ya zana qasa ya share da yin sauran siddabarunsa cikin alqaluman sihiri. Bayanai suka bayyana gare shi cewa, zuhairu da ya bari a cikin kogon dutsen boka Afrahu bai hallaka ba. Kuma shi da sauran jaruman da suke tafe tare da shi 112 BAKAR GUGUWA ne suka shigo lardin Ashtar suka farmaki sansanin ma’abota tsaro na farko, suka samu nasara akan su suka karya Darul Uqub. Kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa sansani na biyu don kai hari akansa. Ya yi matuqar mamaki da ganin yadda suka samu nasara akan wannan sansani duk da tsananin yawan baradan da ke cikinsa. Wanda ya dogara a gare su don bada kariya da kiyayewa daga masu kawo hari akan fadarsa. Hankalin matsafi Bahalu ya tashi zuciyarsa ta tunzura, ya tashi cikin sauri dan tafiya ga sauran sansanin ma’abota tsaro guda biyu da suke rage, don ya sanar da su abinda ya faru ga sansani na farko, ya kuma qara karsashi a gare su akan su qara tsaurara tsaro da kiyayewa, su kuma hallaka duk jama’ar da suka ga sun tunkaro fadarsa ba tare da neman sanin ko su wanene ba. Da isarsa sansanin ma’abota tsaro na farko Darul maut ya yi shela da maxaukakiyar murya mai matuqa qarfi da hauhawa. Ta bakin gunki da suke bauta a gare shi cikin alqaluman sihirinsa. Baradan da suke cikin wannan sansani suka yi saurare ga abinda muryar take ambatawa. Bayan sun gama jin wannan shela gaba ki xaya suka faxi gaban wannna gunki suka yi sujjada a gare shi don girmamawa. Sannan suka tashi cikin sauri suka himmatu ga aikata abinda aka umarce su da aikatawa, suka qara tsaurara tsaro da kariya ga wannnan sansani na su. Shugaba daga cikinsu ya qara musu karsashi na qarfin zuciya, don tunkarar duk abinda ya kusanci wannan sansani na su suga qarshensa su hallaka shi. Daga nan matsafi Bahalu ya wuce ya zuwa sansani na biyu, wato Darul musiba. Ya yi shela makamanciyat wadda ya yi a sansani na farko. Cikin murya mai hauhuawa ta bakin 113 BAKAR GUGUWA gunki da suke bautawa su ma waxannan baradan suka shiga shiri kamar yadda sansani barada na farko suka yi. Matsafi Bahalu bai baro waxannan sansanin barada guda biyu da suke bada kariya akan fadarsa da kuma yin shirin tunkarar duk wanda ya ce zai farmaki sansanonin baradan su ga bayansa, sannan ya koma fadarsa ya zauna cikin yin imani da cewa abinda ya aikata zai zama kariya gare shi akan duk wanda ya ke son zuwa fadarsa dan yin yaqi da shi. ** Su kuwa su zuhairu da sauran jaruman da suka rage tafe tare da su, bayan da suka bar wajen da suka yaqi sansanin na farko suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daji suna masu neman inda za su samu ruwan da za su sha. Suka yi tafiya ta tsayin yini guda ba su samu inda ruwa yake ba, qishirwa ta tsananta gare su ga zafi da xumamar yanayi na daxa qaruwa don haka suka yi matuqar jigata da yawansu suka galabaita. Ba su samu inda ruwa yake ba sai da rana ta kusa faxuwa, sannan suka riski bakin wata qorama a tsakanin wasu kwazazzabai, ruwa yana gudanawa a cikinta, suka yi matuqar farin ciki da ganin wannan ruwa suka isa ga qoramar su ka sha, suka yi hani’an sanna suka yi alwala su ka yi sallah magariba. Suka xebi wanda za su yi guzuri da shi idan sun ci gaba da tafiya. Da yake dare ya yi ga kuma gajiya sai suka yada zango a bakin wannan qorama dan su kwana kafin gari ya waye su ci gaba da tafiya zuwa sansani na gaba. Da gari ya waye suka tashi suka yi sallah tare da addu’a ta neman samun nasara, sannan suka kama hanya suka ci gaba da tafiya ba su isa inda sansani na biyu yake ba sai da kusan faxuwar rana. Tun daga nesa suka hangi qaton tsaunin nan na 114 BAKAR GUGUWA biyu inda sansanin baradan yake a bayansa, a jikin tsaunin an yi rubutu kamar haka. “Wannan shi ne DARUL MUSUBA, sansanin ma’abota tsaro da bada kariya ga fadar DARUL SABAR na biyu hallaka ta tabbata ga wanda ya kusanci wannan sansani bisa ga rashin sani ko kuma don nuna tijara da jin kai”. Da suka isa inda wannan tsauni yake sai suka dakata suka sauka a bayanhsa bayan sun huta sun samu nutsuwa sai zuhairu ya tashi ya tafi don ya leqa bayan wannan tsauni a voye, ya ga yadda jama’ar da ke cikin sansanin suke saboda su san ta inda ya dace su farmake su don samun nasara akan su cikin salon yaqi. Da zuhairu ya zagaya inda zai iya hangen sansanin baradan, sai ya voya cikin duhun itatuwa yadda ba za su iya ganinsa ba. Ya hangi baradan cikin shirin yaqi ba kamar yadda suka tadda sansani na farko cikin shagaltuwa da bautar gunki ba, an zagaye wajen da tsaro yadda babu wanda zai iya keta wajen ya shiga ba tare da sun gan shi ba. Wasu daga cikin baradan suna kaiwa da komowa a kewayen sansanin xauke da miyagun makamai. Suna duba da binciken duk abinda ba su yarda da shi ba, don bada kariya da tsaurara tsaro da kiyayewa. Zuhairu ya qare musu kallo tare da wassafa yadda za su kai hari akan wannan sansani, don samun nasara akan baradan. Daga nan ya tashi ya koma bayan tsaunin inda sauran abokan tafiyarsa suke. Yana isa gare su ya kwashe labarin duk abinda ya gani ya sanar da su, sannan ya qara da cewa. “Haqiqa suna da labarin karyewar runduna ta farko da hallaar sansanin baradan da ke cikin ta. Don haka suka kasance cikin tsaurara tsaro da kiyayyewa kada abinda ya faru da 115 BAKAR GUGUWA sansani na farko ya faru da su. Saboda haka ba za mu tunkare su kai tsaye ba, don yin yaqi da su saboda suna xauke da manya makamai a tare da su, za mu yi amfani da hikimar yaqi ta voye. Za mu farmake su cikin wannan dare kafin gari ya waye mu qarar da su cikin yarda Allah. Yadda zamu samu nasara aikata hakan kuwa shi ne, za mu tafi cikin duhun itatuwan da ke kusa da sansanin gaba xayan mu mu vuya, kwararrun masu harbi da kibiya da jifa da majaujawa za su yi ta kai hari akan baradan suna hallaka su kamar yadda muka yi a sansani na farko. Ni kuma zan bi duhun dare na shiga cikin sansanin na je na sare kan wannan gunki da suke bauta a gare shi, idan na samu nasara aikata haka tsaunin da suke zaune kusa da shi zai fashe ya tarwatse kamar yadda tsauni na farko ya yi idan hakan ta faru baradan za su razana zuciyarsu ta karaya da ganin abin bautarsu ya hallaka. Za su tarwatse su fantsama cikin daji mu kuma sai mu yi amfani da wannan damar mu ci gaba da saransy muna hallaka su har mu ga qarshen su, mu karya sansanin na su kamar yadda muka karya sansani na farko”. Da zuhairu ya gama yi musu wannan bayani sai suka tashi suka yi shiri. Bayan sun yi sallah magariba da isha’i suka tafi can cikin duhun itatuwa da ke kusa da sansanin suka voye. Can daga nesa suka hangi baradan nan sun kunna wasu manyan fitilu na itace masu matuqar haske. Haskensu ya haskake da’irar wajen baki xaya tamkar rana zuhairu ya umarci masu jifa da majaujawa su fara jifa kan manya fitilun su kashe su. Jaruman nan suka aikata abinda ya umarce su nan take dukkanin fitilun suka mutu duhu mai tsanani ya gauraye wajen. 116 BAKAR GUGUWA Baradan da ke tsaron wajen suka ta so cikin sauri don sake kunna fitilun zuhairu ya sake bada umarnin akai farmaki akan su. Masu harbi da kibiya suka soma sakar musu ruwan kibau. Wanda kibiyar ta fara samu ya yi qaraji da kururuwa mai tsananin qarfi saboda shigar kibiyar cikin kwayar idanunsa na hagu. Ya faxi qasa yana wannan qaraji saboda azaba. Kafin ransa ya fita, sauran baradan suka tafi gare shi don kai masa xauki su ga abinda ya faru gareshi, kafin su kai kan shi wasu zafafan kibiyoyn suka keto duhun dare suka fantsama a tsakaninsu suka hallaka su. Wasu baradan suka sake tasowa masu jifa da majaujawa suka farmake su suka hallaka su. Da ganin haka sai sansanin baradan gaba xaya suka tunkaro wannan waje don yaqar abinda yake hallaka ‘yan uwansu, suka taso cikin qaraji da kururuwa irin ta fusatuwa. Jarumai da suke tare da su zuhairu suka ci gaba da sakar musu ruwan kibau da jifa da majaujawa suna hallaka su. Nan take waejen ya hargitse qura ta turnuqe ta qara wanzar da duhu cikin duhun dare zuhairu ya fito daga inda yake lave ya shiga cikin sansanin baradan ya hau su da sara, waje ya sake rincavewa,yanayi ya tsananta ga wannan barada suka shiga halin kixima da ruxani saboda rashin sanin taqamaimai abinda yake hallaka su cikin daren. Su da kansu suka riqa kai sara ga kawunansu suna hallaka junansu cikin duhun dare saboda firgici da ruxewa kafin wani lokaci baradan nan sun yi raga-raga da junansu suka karya rundunarsu da kansu. Zuhairu ya ci gaba da keta tsakiyarsu yana kai sara a tsakaninsu dama da hagu, cikin tsananin jarumta da qarfin zuciya, yana hallaka su da haka har ya isa inda wannan gunki 117 BAKAR GUGUWA da suke bautawa yake. Yana zuwa wajen ya xaga takobinsa tare da kabbara cikin maxaukakiyar murya mai qarfi ya sari wuyan gunkin da dukkanin qarfinsa kaifin takobinsa ya sare kan gunkin ya faxi qasa. Da sare kan wannan gunki sai suka ji wata irin qara mai tsananin qarfi da ban firgici ta gauraye wajen tsaunin da ke bayan gunkin shi ma ya yi qara ya fashe ya tarwatse, qasa ta ci gaba da girgiza da raurawa mai qarfi kamar za ta tsage jama’ar dake wajen su nutse a cikinta su hallaka, gangar jikin gunkin ta kama da wuta, hasken wutar da haske ko’ina baradan suka ga abinda yake faruwa a tsakaninsu. Da ganin gunkin da suke bautawa ya kama da wuta, sannan sansanin da suke samun abinci daga gare shi ya fashe ya tarwatse, sai baradan nan suka sake firgita da razana da abinda yake faruwa, zuciyarsu ta karaya suka ga tamkar ranar hallakace da azaba mai tsanani za ta wanzu a gare su cikin wannan dare. Nan take suka zubar da makaman da ke hannunsu cikin tsaro, suka fantsama cikin dajin a firgice don su tsira daga hallaka. Su zuhairu da sauran jarumai da ke tare da shi suka tare su suka ci gaba da hallaka su kafin su kai ga arcewa. Suka hallaka da yawa daga cikin su sai ‘yan qalilan daga cikin su ne suka samu nasarar arcewa suka shiga cikin daji ba su hallaka ba. Da su zuhairu suka ga sun karya rundunar baradan sai suka yi matuqar farin ciki da samun nasara akan sansani na biyu, tare da yin godiya ga Allah abisa wannan nasara da suka samu. Daga nan suka koma inda suka fara sauka da farko don su huce gajiya su kwana anan kafin gari ya waye su ci gaba da 118 BAKAR GUGUWA tafiya ya zuwa sansani na uku, kuma na qarshe. Wanda daga shi sai fadar Darul sabar inda matsafi Bahalu yake zaune. ** Can kuma a Darul sabar fadar matsafi Bahalu a cikin wannan dare mummunan labari ya isa gare shi na karyewar sansani na biyu na ma’abota tsaro da bada kariya ga fadarsa. Ya gari da idanunsa cikin alqaluman sihiri, yadda sansanin baradan suka tarwatse suka bazama cikin daji a firgice. Dan su tsira daga hallaka da musiba da ta afka musu cikin sulusin dare wadda ba su san mafarin ta ba, da yawa daga cikin baradan sun hallaka. Gunkin da suke bautawa a gare shi ya kama da wuta ya qone qurmus. Tsaunin da baradan suke samun abinci da abin sha daga gare shi wanda alqaluman sihirinsa suke tare da shi don tabbatar da kafuwar sansanin shi ma ya fashe ya tarwatse. An samu matuqar damuwa da vacin rai mara musaltuwa tattare da matsafi Bahalu game da abinda yake faruwa na karyewar sansanonin baradan sa ma’abota tsaro ga fadarsa da yadda sua zama marasa tasirin bada kariya a gare shi kamar yadda ya ta’allaqa dogaronsa gare su, sai dai wannan bai sa zuciyarsa ta sake karaya ba, ko kuma ya zama izina a gare shi da cewa hallaka na qara kusantar shi cikin kowacce sa’a idan har su zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka samu nasarar shigowa fadarsa suka iso gare shi. Don ya yarda da kansa da kuma alqaluman sihiri da ya mallaka, kuma bayanai cikin bincikensa ba su tabbatar masa da cewa hallakarsa tana tare da xaya daga cikin waxannan jama’a ba, sannan ya yi imani da cewa shi mai samun nasara ne akan su, da ma duk 119 BAKAR GUGUWA wanda yake yin jayayya da shi ko kuma zai tunkari fadarsa da nufin yaqi da shi a faxin duniya. Haka ya kasance cikin wannan yaqini da ke zuciyarsa saboda tsananin shirka da vata irin na ma’abota aikin sihiri da tsafi. Allah ka tsare mu da wannan al’amari, Ameen. Can kuwa a birnin BAHAZUM sarki shaiban ya sanya malamai suna ta addu’a don neman samun nasara ga su zuhairu akan wannan shu’umin matsafi su kuvutar da ‘yarsa Gimbiya Hasima daga hannunsa. A kullum aka yi saukar Alqur’ani mai girma kamar

Chapter 8 of 10