Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na Dubata" Da kai ta amsa min kafin tace"Allah yasa" Bamu cigaba da Hira ba na mike na koma kitchen na dora ma Ya Ishaq ruwan tea bayan ya tafasa na juye mai a falas ba komai na cefane har kwai ya kare wani sauran dankali ne bashi da yawa na fere na soyamai sai namai miyar albasa,na tattara komai na kai Shashensa na shiryamai afalonsa na fice Ganin Hafsa ta karbi gyaran gidan ni kuma sai na kwashi wankin yaran da suka taru naje bayan  inda tankin ruwa da famfo yake yi na Fara wanki Uniform na fara wanke musu da Hafsah ta gama sai tazo ta sameni tana tayani sama sama muna Hira,Saboda yanayina Allah yasa bani kuma da yawan mgana sosai Muna cikin wankin Ya Ishaq ya Leko dauke da Ahmad a Hannunsa yana fadin"Sai ku bar Cikin gida ba kowa sannan ku bar yaro shi kadai adaki..? Wannan wani irin rashin Hankali ne..? Da Sauri na tsame Hannuna a ruwan Sabulu na karisa wajensa na karbi Ahmad ya juya batare da yayi min mgana ba sai nabi bayansa muna zuwa Falo ya tssya ya juyo yana kallona Lokaci daya yana fadin"Ga cefane nan..Ki lallaba kinsan ina da Hidima yanzu haka wajen Milyan daya zan yi ma Anty Binta ciko na Hidiman bikin nan sannan ba Lalle na kara miki wani cefane ba sai karshen wata" Da kai na amsa mai kafin a Sannu nace"Angode Allah ya saka da alheri" Ko amsa ni bai yi ba yayi gaba daidai Lokacin da wayarsa tayi kara kafin ya shiga ya Daga wayar kasa kasa yayi mganarsa ban ji ba. Zama nayi na bama Ahmad Nono na maidasa baya na kwantar Domin bazai yarda na ijiyesa ba. Na dauki Ledojin na shiga da su Kitchen Katan din Bobo ne sai na maltina sai Biskit kwali biyu sai Na ruwa faro sai kwai da doya sai Dankalin Turawa sai kayan miya,na Zazzage komai na jera a muhallinsa Sannan na koma muka cigaba da wanki ni da Hafsah duka sai da muka wanke har da nawa muna bayan Ya Ishaq ya fice daga gidan bamu sani ba fitowa kawai nayi naga bayanan sannan ba Motarsa nasan bazai wuce gidan Mama ba..ga Hafsah zata tafi bani ko da naira Biyar balle na bata na Mota. Ina so na bata wani abu ta kaima Tamadina bani da komai sai na Dibar mata Sabulin wanka da na wanki muna da Sauran su bai kare ba, nace ta kai mata,mganar kudin mota kuma tace min kada na Damu goggo ta bata 3k da zata taho zasu isheta ta koma Gida ina ji ina gani Hafsah ta tafi ni na rakata har kofar gida muna Daga ma juna Hannu. Na dawo cikin gida Nepa sun kawo wuta na zauna na fara gugan kayan Su Amir saboda sai yammah zasu dawo,haka ma Ya ishaq sai da yammah sai nayi Tunanin sai da yamah nayi girkin ni kuma Daman cikina ya cushe hafsah kad'ai taci taliyan nan na Safe ni kuma sai na barta sai an juma. Ban tashi Daga wajen nan ba sai da na goge rabi da kwatan kayan nan tas sai wad'anda basu bushe ba kawai Sallah kawai ke tadani sai bayan Sallar la'asar na tashi daga wajen shima Saboda girki ne. Sai alokacin nayi wanka na saka wata bubar doguwar rigar wata atamfa da Yaya Asiya ta dinka mana mu hudu har da ita. Na shiga kitchen na fara Tunanin me zan sarrafa sai kawai nace bari nayi jallop din shinkafa tunda ina da Sauran kayan lambu sai na Hada da su,Naso na hada ko lemu ne to bani da kankana ba aya ba abarba ba Sinadrin hadawa kayan zobo kuma Daman Badariya ke siyon irin wad'anan abubuwan duk Ya Ishaq baya siyan su sai abunda ya zama Dole. Sai da na gama komai naje nayi sallar mangariba Allah ya taimake ni Ahmad yau barci ya yini yi bai yi rigima ba Tunda naji su Anum shuru nayi Tunanin Babansu ya Dauko su suna gidan Mama. Shiyasa na idar da sallah sai na fara jera ma kowanne kayan sa a dirowansa ina Dakin wayata na kara ammh ban ji ba sai chan sama sama naji karan a cikin kaina. Na daukota na Duba Goggon Karofi ce Ina hada Hausa Ina karantawa wanda bai da wahala sosai in dai kamar na sune ko mgana wacce ba'a rubuta tayi tsawo ba. Ina Daukan kiran na sakata a speaker Hafsah ce muka gaisa tace ta Sauka lafiya taje wajen Tamadina taji sauki tana ta godiya Daganan ta bama Goggo muka gaisa ta yi tamin nasiha daman ita nata kenan Fadi take yi "Fa'iza ki yi hakuri kin ji ko..?Allah bai manta dake ba..In sha Allahu zaki ci Ribar wannan biyayyar taki" Shuru nayi ban ce komai ba ta yi ta bani Misalai da matan da suka yi Biyayya agidan aure sannan suka Rabuta ranar Lahira hawaye suka kawo Cikin idanuwana ina tuna Baba a mganarta shima duka kalamansa ne..daga karshe tace min"Naji Isahaq zai kara aure ko..?to sai kin kara Hakuri Fa'iza daman abunda Saudatu take nema ne ya samu ki koma gefe ki rumgumi ya'yanki Allah yayi albarka Allah ya baki Dangana" Ina share hawayena nace"Ameen Goggo ammh dai zaki zo ko..? Goggo tace"To sai nagani in zan samu zuwa ammh yara zasu zo su zauna Dake" Daga haka mukayi sallama na koma na cigaba da aikina naki bari Tunanin auran nan ya shiga zuciyata. Tun ina saka ran dawowar su da wuri har na sare gani  har Tara tayi nayi sallar isha'i nayi ma Ahmad wanka har yayi barci nima wanka na Sake yi na saka Riga da wando masu taushi na barci Diyar Goggon karofi Anty Nasara ta kawo min su Tsaraban Umra. Ina zaune afalo ni kad'ai kamar mayya naji Hayaniyar yaran da shigowar su dukkansu jikina suka fado suna murna nima na rike su ina Mirmishi Tun kafin nayi mgan Amun tace"Umma Gidan Mama fa Daada ya kaimu" To daman yana da inda yafi gidan Maman ne..? Suka fara gwadamin Tsaraban Kayan lashe lashen da ya siya musu sai ga shi ya shigo yana shigowa da sallama bai ko bari na amsa ba ya fara fada yana fadin"Don iskanci kina ji ina ta Hon bazaki iya fitowa ki budemin get ba..? Ni wlh har ga Allah ban ji ba cikin sanyina nace"Ban ban ji ba wlh..kayi hakuri" Tsaki kawai yaja ya wuce Shashensa yana fadin"duk kin ji..ai ba hayaniya a inda kike balle ki fake da Lalurarki" Ina jinsa ban ce komai  ba sai ma kirkiri mirmishi Saboda yaran kada su Fahimci wani abu,ni ke kokarin kauce ma wasu abubuwan ammh yadda Ya ishaq baya jin kunyar tozartani gaban ya'yana in da ina Biyesa da tuni yaran tun tashi da shi a ransu,sai dai in dai suna wajen da ya fara fadansa zan yi saurin ba shi hakuri na nuna komai ba komai ba ne. Kayan makarantan su nace suje su cire kafin su ci abinci sukace min sun sha tea agidan Mama. Suna shigewa d'aki ni kuma nabi Ya Ishaq Shashensa kada yace ya dawo nayi banza dashi daman na hada mai abincin sa tuni na kai mai shashensa. Koda na shiga yana Cire kayan jikinsa sallamanta ma aciki ya amsa min na Rankwafa ina mai Sannu da zuwa ya amsa sau d'aya ya dauke kai ya Tura kofar Tiolet ya shige ni kuma sai na karisa cikin bedroom din na Tattara kayan daya cire na ninke mai na bude Wardrope dinsa na sakamai na gyara mai Dakin Dazu daman saboda bai bar key din bane shiyasa. Ina Dakin ya fito yana Digan ruwa da Sauri na Dauko mai Towel na basa ya amsa yana Goge jikinsa Lokaci d'aya yana kallon kayan jikina ni kuma ban ma Lura ba wardrope dinsa na Bude ina Fadin"Jallbiya zan dauko maka..? Kai tsaye yace"Bar shi kawai" Ban damu ba na rufe na koma gefe na Tsaya kaina na kasa kamar Daga sama naji yace"Ina kika samu wad'anan kayan barcin kuma..? Shuru nayi kafin nace"Anty..Na..Nasara ta kawo min Tsaraban Um umra." Tabe baki yayi kafin yace"Shi yasa da zata baki sai da ta zabo kalan da zai yi daidai da yanayin ki.. Green wannan kayan ba su yi ba ammh ke kin ga abun sawa da sunan ki yi ma mijinki kwalliya dashi.." Sai naji na muzanta duk da ya saba kusheni ammh na yau sai yafi Dafani barin ma da ya kara fadin"Kwata kwata na rasa wani abu ne zaki saka ya Dace dake Fa'iza..Alhamdulillah da Allah ya bani Zeey yarinyar mayar dressing ne komai tasa ajikinta sai kin ga kamar don ita aka Hallici kayan zata zo kuga juna don Allah in kun had'u ki fara D'aukan gyara daga kanta" Kaina sai da ya yi Dum jikina sai yayi min ba Dadi ammh ban nuna ba kayan jikina na kallah har ga Allah  ni ban ga Aibun su ba kore ai kalan yan aljannah ne sai dai daman shi tozarcin sa ba inda baya tashi. Da naga zai saka kaya sai na fice abuna na zauna afalo ina jiransa haka ya fito yazo ya zauna ya fara cin abinci sai da ya gama sannan na kwashe komai na kai kitchen na koma nayi mai sai da Safe naga yana waya da Hannu kawai yayi alamun naje ni kuma na fice na koma Dakin yarana na iske Amir na koyama Anun aikin da aka bata a makaranta Musty har yayi barci na gyaramai kwanciya na mai addu'a na koma cikin su Anum na zauna ina ganin abunda suke yi ina mirmishi sai da suka gama na saka Amir yaje yayi fitsari shi da Anum suka kwanta muka karanta addu'an barci atare suka Shafa na gyara musu kwanciya  na rage musu fanka na kashe musu wutar Dakin na fita zuwa D'akina na gyarama Ahmad kwanciya nima na kwanta agefensa ina addu'an barci. Karfe uku na dare yau na tashi nayi Nafilfiluna sannan na fita naje na tashi su Amir,sai ga Baban su ya fito suka tafi masallaci ni kuma muka yi tamu ni da Anum agida. Kamar yadda n Saba kafin bakwai din Safe sun shirya cikin kayan makarantar su Ahmad na bayana sai rigima yake yi,Ba ya ishaq zai kai su ba Haruna mai adaidaita ne wanda ya saba kai su  baban nasu yau zai koma Abuja. Shashen shi suka je suka mai sallama sannan suka fito ni na saka Hijabi na rakasu har waje muka gaisa da Haruna sannan suka shiga suka wuce ina Dawowa a gurguje na had'a ma Ya Ishaq abun karinsa buredi da kwai na Soyamai sai ruwan tea na kai mai Shashensa ya fito cikin shirin Tafiya sanye da Suit bakake ya tsuke kamar ba shi ba har da wani damfararen bakin glass na ba mutumci. Yana zaune yana karyawa ina Gabansa Ahmad na Hannuna ina Lallashinsa sai da ya gama sannan ya mike yana fadin"Fa'iza zan tafi kuma kila sai satin biki zan shigo.karbi ki ga." Kudi ya miko min yan Dubu na saka Hannun na karba ina godiya Karamar Jakarsa ya Dauka na mike ina Sabe da Ahmad zan karb'a da Sauri yace"Kada ki damu da wannan..Ki kularmin da yarana in akwai wani abu ki kirani a waya..koda yake nasan zaki kira indai kina da bukatar wani abun" Nidai ina biye dashi har Haraban gidan Ahmad ya karba yayi masa sumba kafin ya miko min shi Sai da ya shiga mota sannan ya Leko yana fadin"Anty Binta zata aiko miki da kayan fitan biki da wasu kaya da ta matsa sai na siya miki in ma da wani abu zaki ji wajen su Mama na tafi..Ban da yawo..Fa'iza gidan Mama da Gidan Anty binta kad'ai kike da izinin zuwa ki Kiyaye" Daga haka ya rufe motarsa lokaci daya yana fadin"Ki budemin get" Haka na tafi zugwi zugwai ga goyo a bayana,na saka karfina na bude mai get ya fice na bisa da Allah ya kiyaye hanya na maida get din na Rufe ina Haki sai da na koma falo sannan na Kirga kudi Naira dubu biyar itama nasan Saboda matsalan yara ne daman duk sati in yazo haka ya ke bar min. Kuma kafin ya Dawo ta kare ko Kudin motar da nake zuwa gidan Mama ko Anty Binta sannan ga Dawaniyar yara yau Anun tace bata da pensil gobe Amir yace zai siya Drowing duk anan kudin ke tafiya. Tunda ya tafi sai na maida Hankalina wajen kula da ya'yana Kwana Hudu Tsakani da Tafiyar Ya Ishaq Anty Binta ta kirani a waya mu hadu agidan Mama ranar jumma'a da Safe bayan su Anum sun tafi makaranta na shirya na tafi bayan nace ma Haruna gidan Mama zai kawo su Anum in ya Dauko su daga makaranta. Naje na iske gida cike da kawayen Mama ana ganin kayan lefen da za"a tafi dasu Abuja agobe. Akwatuna goma shake da kayan alfarma ni ko Aleda Anty Binta ta bani nawa Less d'aya atamfa biyu sai takalmi sai Hijabi na karba da Hannun Biyu ammh sai Mama ta harareni tana fadin"Naga kin karba a wulakance kin raina ne..? Kaina na kasa na kasa mgana Hajiya Barira aminiyar Mama tace"To ina Laifi wannan kayan Hajiya Saudatu..?ai wlh naga kokarin Ishaq ma matar farko ai ba kowa ke wani wahalar da kai akan su ba" Mama ta tabe baki kafin tace"Matar ma irin wannan abar ba.." Suka kwashe da Dariya suna nuna ni, Anty Binta ta kyabe fuska tana Fadin"In ma ta raina ita ta sani..Kila wad'anan take kalla ai inda suka dace za'a kai su Yarinya ba inda basu dace ba" Ni dai kazil ban ce ba Saboda suna so naji cin mutumcin su da karfi suke mganar su,Haka suka sallameni na kwashi kayana zuwa Dakin Badariya bata nan tana makaranta. Ba domin nace Haruna ya wuto da su Anun nan ba da gida zan koma saboda su yasa na jira sai da suka Dawo nazo musu da kaya suka sauya ni nayi girki daman indai nazo to kamar jaka haka take komawa agidan Mama. Sai La'asar na koma gida ni da ya'yana da kayan da Anty Binta ta bani duka an dinka su daman,Washegari kuma Badariya tazo take gayamin an tafi kai lefe har da Hajiyar Dala da Anty Binta da Hajiya Barira kawayen Mama. Sai fada take wai ba su sanar da Goggon karofi ba araina nace ita din banza ai in dai su Hajiyar Dala na waje kowa ma bai da kima a wajen Mama. *Littafin KANA NAKA Book 2,3paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.* *Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223* *Janafty* *KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Book 1* *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *GADALIN MATA AKWAI*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*. *TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *NATION WIDE DELIVERY*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* 🙏.             *🅿️07* Bayan ta gama fad'an rashin gayama Goggon karofi sai ta koma fad'an kayan da aka bani bayan tace na dauko mata ta gani Badariya karama ce acikin ya'yan mama ammh da ace itace Babba da abubuwa da dama sun gyaru tana da kyakyawan zuciya da Hali mai kyau. Ina kallonta ta d'aga kayan a rene tana tabe baki kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza abunda suka baki kenan acikin Uban kayan akwati goma da suka tafi kaiwa Abuja..? Duk da ba duka naji mganar ta ba,ammh na dauki wasu,Sannan ina Bin bakin wanda na saba mgana dashi na kan Fahimci abunda yace ko da ban ji ba. Ban ce mata komai ba sai ma wani mirmishin takaici da nayi,na sani ko Lokacin aurena ya ishaq bai min lefe ba ballatana yanzu ba da bani zai aura ba,Daman a wanchan Lokacin Baba ne ya matsa masa akan sai yayin lefe ba Sadaka ya aura masa ni ba, awanchan Lokacin Mama ta shiga mganar tayi ruwa tayi tsaki akan ita da kanta zata had'amin lefe nagani na Fad'a da ya kara tambayata sai tace tuni ta bama ya ishaq ya kaimun kaya ahalin kaya ko kala goma basu kai ba sannan saukakku dai ba masu tsada ba daman tun a baya na fada muku Baba shi ba magidanci ba ne mai bin diddigin abunda ke faruwa a cikin gidansa ba shiyasa wani Lokacin Mama kan yi nasara a kansa da kuma kila an yi masa surkullen mutanen yamai. Ni ban damu ba saboda ba kayan ba ne a gabana, ko su bani ko kar su bani bazai kankare yadda bani da Daraja a idanuwan ya ishaq da su kansu ba. Har ta gama fadan ta ban bude baki nayi mata mgana ba to me zan ce..?duk abunda zan ce alokacin bashi da amfani Saboda ajiyan agaban Mutane Anty Binta ta kara maimaita Dakyar ta lallaahi Ya ishaq ya amince ya siyamin ma kala ukun da aka bani Domin da farko cewa yayi bazai siya ba Saboda ko ya siya zai yi asara ne ban san Darajan su ba sai da tayi ta basa baki sannan ya amince to saboda mene zan damu..? Awannan gabar da auran mu ya zama jingina ba lalle ne Hakkokina su rataya a wuyansa ba ni ba Dolen sa ba ne yanzu Saboda haka raina ya daina Damuwa kan duk Tozarcin da zai aikata agareni. Kuma na kudiri araina bazan saka kayan sa ba,Akallah dai zan fara Dogara ga kaina ko Saboda ya'yana na fara Tunanin zamana ahaka bazai yuyumin ba in ya'yansa Dolensa ne,ni na tashi adolensa bazan bar gidansa yanzu ba Saboda lokaci bai yi ba ya'ya na suna Bukata ta, sosai in na tafi na bar su basu da wanda zai kula da su da Tarbiyan su ina tsoron su tashi Cikin maraicin uwa kamar yadda muma muka tashi cikin wannan maraicin muna da uwa a raye ammh kamar bataa raye ne a wajenmu. Tattara komai nayi na tusa cikin Wardrope d'ina ban kuma yarda nayi mganar da kowa ba Daman Ya Asiya ce kadai take kirana kan Sha'anin Bikin Yaya mariya ko sau d'aya bata kirani ba ita ta na da Zafi ne Ko zuwa tayi had'uwa goma sai sun yi Cacan baki da Anty binta gata irin tanada Sauri Saurin mgana ne kafin Anty Binta ta fadi daya ta maida mata Biyar Shiyasa bata cika zuwa katsina ba sai da Dalili mai girma waya kuma bamu cika mgana ba Saboda abu kad'an zataji ranta ke baci kuma bata da Hakuri ko kada'n. Biki nata karatowa barayin su Mama suna ta shirin su gayya Mama tayi bani da Gayya ba Domin tace sai yanzu ta san Ishaq zai yi aure ni ina gida bansan halin da suke ciki ba,bani cikin kwanciyar Hankali Saboda ina ta mafarkin Tamadina sai na tsorta kada tazo ta mutu itama bamu gana ba sai na fara Tunanin ya kamata naje na gaisheta na Dubata Saboda mahaifiyata ce in na rasata a wannan gabar sai nafi kowa kuka Saboda dani kad'ai ne bata gana ba. Na fara Tunanin Tafiya sai dai matsaalan kudi ne Dubu daya da Dari Biyar suka Ragemin a hannuna cikin Dubu biyar din da Ya Ishaq ya barmun da zai tafi sannan Tunda ya tafi ko sau daya bai kirani yaji Halin da muke ciki ni da yara ba nima kuma ban kirasa ba Sai dai na riga na kuduru niyyar zuwa gaida Tamadina Cikin Satin nan da zai shiga kafin Lokacin Bikin yazo. Na shirya tafiya ta Ranar asabar in su Amir sun tafi Hadda,Shiyasa Ranar jumma'a da Daddare na yi ma Ya Ishaq flashing Saboda wayata ba kati na ma manta Rabon da na saka mata kati ba na kira daman sai dai mai son mgana dani ya kirani bansan adadin Flashing din da nayi masa bai kira ba sai chan naga kiransa na dauka jikina na rawa na saka ta a amsa kuwwa na kara kunne tun kafin nayi mgana ya Dakamin Tsawar da sai da tasa na razana Cikin Fadansa yace"Haba don Allah wai meye haka Fa'iza..? Sai flashing kike yi min tunda kika ga ban kira ba ai kinsan ina wani abu mai muhimmanci ne ko ina tare da wani mutum mai muhimmanci ke duk abunda kika fara Hankali bai isa ya baki ki bar shi haka ba..? Sai naji kwallh ta ciko cikin kwarmin Idanuwa na cikin rawan zuciya da na Murya nace"Kayi..ka..yi hakuri..Ban..Sani ba ne.." Karamin tsaki yaja kafin yace"Zan kiraki in na koma gida ina tare da Zeey ne.." Daga haka ya katse wayarsa ina jin muryanta kafin ya katse tana fadin"Honey kai da waye kake ta Ihu haka..?kamar a kusa da wayar tayi mganar shiyasa na ji ta. Ban ji me yace mata ba ya katse kiran sai na Sulale gefen gadona na fashe da kuka Allah yasa yaran duk sun kwanta har ta Ahmad yayi barci kuka nayi wanda naji ya isheni nasan bani da wata Daraja a idanuwan Ishaq ammh ban dauka har agaban wacce zai aura ma bani Daraja ba ,Sai na fara tunanin wani irin karb'a amaryan sa zatayi min in muka fara Had'uwa sannan me ya fada mata akaina..? Wata zuciya ta amsamin ya fad'amata ke bakomai bace face bebiya mummuna baka mara gata sannan mara ilimin zamani wacce bata da komai atare da ita tuna haka yasa kuka na ya karu bansan tsawon Lokacin da na Dauka ina kukana ba sai da nagaji sannan na tashi na Shiga Tiolet na wanke fuska ta na fito na k'i yi barci ina jiran kiransa na riga na sakama raina Gobe zan je na Duba Tamadina kuma ba yadda zan iya tafiya batare da izininsa ba.. Bai kira ba sai wajen sha d'aya da Rabi na Dare sannan ya kirani ina D'auka fada ya hauni da shi wai ni bai san me nake yi ba sannan bani da Hankali komai ba cikin lissafi nake yi ba ni dai Hakuri nayi ta basa sai da ya sha iska ya gama wulakacin nasa sannan yace"Ina yara na..? Ina fatan suna nan cikin koshin lafiya ko..? Nayi saurin amsa mai da suna lafiya jin nayi shuru yasa yace"Fa'iza fadi abunda yasa kika addabeni da Flashing ina da shiga office da Safe zan kwanta akan Lokaci" Cikin yanayin mganata nace"Da dama..Ina so ne gobe naje Dutsenmah na Duba Tamadina" Cewa yayi bai ji ba na sake bud'e muryanta na kara gayamai sai kawai yace"wacece haka..? Ban yi mamaki sanin Waye Ya ishaq kai tsaye nace"Babarmu.." Karamin Tsaki yaja kafin yace"Daman nasan bana ganin kiranki sai wata Bukatarki ta taso miki Fa'iza baki da wani Amfani sai kina da bukatar wani abu..me akayi da kike son ki tafi..? Kai tsaye nace"Tayi rashin lafiya ne ni kad'ai ne ban je na Dubata ba" Kyafci yayi kafin yace"Kada nace bazaki je ba kice na hanaki ganin mahaifiyarki Allah ya kiyaye hanya..Sai dai kada ki kuskura ki tafin min da yara na gidan da ba wanda yasan su, salon suje suna Rab'e rab'e ke kanki ai araben zaki je Ahmad na amince kawai ki tafi dashi Shima Saboda yana shan Nono ne" Ban damu ba nace"Eh daman suna Hadda haruna in ya Dauko su in ban dawo ba gidan mama zan ce ya kai su" Da Sauri ya tasomin yana fadin"Au Dare ma zaki kai?ko nufin ki Daman chan zaki kwana..? Cikin daburcewa nace"A"a..Dama..Dama ina so na Biya Karofi na gaida Goggo ne" Kai tsaye cikin D'agawar Harshe yace"Ban amince ba..Ban kuma baki izinina ba..Dutsemah kadai zaki je shima Dubiya ce in kika Kai dare Fa'iza wlh sai ranki ya baci..Wato ki je a had'u ayi ta gulmana ana zagina nan Goggon karofi ta kirani tana min Fad'a duk akan ki wai in nayi aure  kada na wulakantaki to in tana ganin ban taimake ki ba meyasa sanda Baba ya nuna zai Aura min ke bata famsheni ta aura miki Isa ba..?karewar tana kaunarki da Tausayin ba..bana son Rainin wayau kada ki sake naji kin taka Karofi in kuma naji wlh tallahi kin ji Rantsuwan musulmi Fa'iza zaki ga Other

Chapter 8 of 25