sai manyan ya'yan gidan maza,sai mu sai Goggo da Baba Ati kamar kaka take wajen Tamadina ita kad'ai ta rage acikin dangin mahaifinsu da na mahaifiya tunda daman auran zumunci ne tsakanin iyayan nasu..
Bayan bude taro da addu'a da yi ma Mamaciyar addu'a sai d'an nasiha garemu na hakuri da rayuwa,duk yadda tazo ma bawa sai kuma aka gangarowa mgana kan abunda ta bari na magada.mu kenan to da yake bata bar wani abu ba,sai yan kayanta da gado da Sauran tarkace nan take kuma mukace mun yafe a raba ma bakuta,suka shiga saka mana albarka Megidan su ya ce Tamadina tun iya zaman da yayi da ita, bata taba sab'a mai da gangan ba,saboda haka ya yafe mata duniya da Lahira,haka Sauran abokan zamanta suke ta fad'in alherinta suna fadi'n bata yi musu komai ba mace mai kirki da son zaman lafiya,Daga karshe Yaya mariya ta muskuta tana kallo Goggo Lokaci d'aya tana fadin"Goggo ya mganar bashi.shin ko sun san ana binta a bashi Saboda a biya a sauke mata nauyi..?
Maman isuhu ta kad'a baki tun kafin Goggo tace wani abu tace'"Allah ya jikan Tamadina ba mace bace mai cin bashi ba,ga yara nan duk sai su tsallakemu su kawo mata ajiyan kudadensu,wlh yadda suka bata haka suke karb'an su ko chanzasu batayi.bata taba cin bashi ba,macece mai godiyar Allah da Wadatar zucci"
Gabad'ayan mu dad'in wannan yabon mukaji,har sai da hakan ya nuna a saman fuskar mu,an tashi taron cike godiya da fatan Allah ya jikan Tamadina bayan Goggo ta sanar da Mutan gidan gobe zamu koma gidajenmu suka nuna alhininsu.
Bayan mutan gidan sun fice suka bar mu, mu kadai Ni ina gefe nayi tagumi bana mgana Amir ne kadai bai yi barci ba yana jikin Hafsatu,Yaya mariya ce da Yaya Asiya ke ta zencen su da Goggo da Baba Ati acikin Hiran ne Yaya Asiya tace"Baba Ati wai har yanzu ba'a samu labarin inda Dan'uwan Tamadina yake ba..?
Baba Ati ta sauke Numfashi kafin tace"Ke dai bari Asiya wlh ba'a samu ba.Kwanaki har chan karayen naje da muka kai yar gidan mallam Akilu aure chan. aka tabbatar min sun tashi sun koma cikin garin kano hannun wani Dan'uwan ita Zuwairan"
Yaya mariya tace"kuma babu lambar waya Baba Ati..?
Ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya babu..Ai tun lokacin zamanta a korafi batayi dogon Huld'a da kowa ba Zaman nasu ma da mahaifiyar Tamadina kakar ku kenan ba dadi gaskiya har da shi Mallam din saboda bata so auran ba,mahaifinta ya had'a abun akwai wanda take so shiyasa sanda aka kawota batayi huld'a da kowa ba,ko Haihuwar Usman din Rabo ne kawai da ya rantse yasa aka samar dashi.
Sai kuma mallam din yazo ya rasu.to bayan ta fita Takaba,Danginta suka zo tafiya da ita.sai ta nuna zata tafi dashi to rayuwar nan ba wanda ya damu da rikon D'an da ba nasa ba, saboda ganin Nauyi ne in ma ta barsa anan d'in shiyasa ba Gaddama akace zata iya tafiya da shi Har ga Allah na zata zata rika kawosa ko don yar'uwansa da suka Had'a uba sai kuma gashi Tunda ta saka kafa ta bar Karofi yau shekaru sama da Arba'in da Doriya bata Dawo ba.sannan shima Usman din bai nemi Dangim mahaifinsa ba har yau din nan kuwa"
Ba kuma wanda yasan inda suke ahalin yanzu"
Gabad'ayan mu muka sauke Numfashi Yaya Asiya tace"To Allah yasa yana raye"
Yaya mariya tace"In sha Allahu ma yana Raye kuma in dai da rai da rabo watarana zamu had'u da shi"
Muka amsa gabadayan mu da Allah yasa Goggo ta gyara zama tana fadin"Duk inda yake in dai jinin ku ne zai nemeku jini ai ba karya ba ne".
Muka jinjina mata kai alamun gamsuwa ni ko araina sai na samu kaina da addu'an Allah yasa yana raye domin shi kad'ai ne shakikin Tamadina anan duniya mu kuma kawun mu Namiji kwara d'aya tak da yau zamu bugi kirji muce muna da shi acikin raina ina addu'an in dai yana raye Allah ya bayyana sa da gaggawa.
Washegari da shirin tafiya muka tashi. kowa kagani da Kuzarinsa ban da ni,kwata kwata kamar an zaremin lakkan jikina,Goggo sai fad'a take min wai na kwazzabi kaina bana cin abinci Yaya mariya na wajen tace"Kuma zama da yunwa bazai taba Sauya komai ba..Tamadina ta rasu sai dai mu yi fatan Allah yasa tana kyakyawan karshe"
Sai hawaye ya kecemin suka shiga tsere bisa kumatuna, bayan mutuwar da ta dake ni,yayi sanadiyar tasomin da ciwona da daman kamar jira yake na shiga hali makamancin sa,Mun had'a duka kayanmu na yara Hafsatu ta wanke musu ta had'a musu ta musu wanka,ta shiryasu haka ma su Yaya mariya sai kuma sabon kuka ya tashi muka zauna mu hud'u muka ci kukan mu muka koshi,muka share Hawayen mu. Goggo tagaji da bamu baki ta Hakura ta koma gefe ta zuba mana ido bayan ta kira Yaya Isa tace yazo ya Dauketa ita da Hafsatu da mariya da Baba Ati, Yaya Asiya kano zata wuce nima kuma gidana zan koma.
Da azahar sai ga Hajiyar Dala,mun dauka ma bazata zo ba ne ahalin taji Rasuwar. tunda Goggo da kanta ta kira wayar ta,ta fad'a mata,Tazo tayi mana gaisuwa ta bama Yaya Asiya dubu goma Sadaka batayi awa d'aya ba,Ta ce zata tafi, nan take zencen zata karisa katsina Tare da Direba take jin Haka yasa Goggo ta kalleni tana fadin"Fa'iza tunda kun gama shiri,sai ki bi goggon taki tunda katsinar zata shiga"
Da Sauri tace"Aa ba gidan Saudatu zani fa gidan Wani abokin Major ne. mahaifiyarsa ta rasu zan biya nayi musu gaisuwa suma na wuce"
Ina jin haka nima murya a sanyaye nace"Ki bari kawai Goggo zan tafi da kaina"
Sai goggo ta jinjina kai kafin tace"Shikenan"
Daga haka tayi mana Sallama tatafi Goggo ce ta rakata har Dakunan matan gidan tayi musu gaisuwa, kafin Tafiyarta sai da ta dawo sannan Yaya Asiya ta bata kudin da Hajiyar Dala ta bata Goggo ta karb'a tana fadin"Kudin ku ne ai Asiya ba ni aka bawa ba"
Yaya Asiya tace"Goggo mu bama bukata ayi sadaka Allah ya kai Haske kabarin mahaifiyarmu"
Goggo ta amsa da Ameen itama fita tayi da kudin Dakin Maman isuhu ta shiga ta bata kudin Dakyar ta karba, Goggo tace kun yi wahala damu wajen kwana takwas ku karba ku kara Allah ya Rufa asiri .sannan ta karb'a tana sharan kwallah da kara fadin Allah ya jikan Tamadina.
Yaya Isa ya kira yace gashi nan zuwa,Shinkafa suka dafa mutam gidan suka zubo mana yaran aka zuba mawa suna ci ni dai bakina yayi nauyin bana jin Dad'in komai kaina wani Dum dum kawai yake yi duniyar ma ba daidai nake jinta ba.
Kwatsam sai gasu Sa'adatu da Habiba sun zo min gaisuwa nayi mamakin zuwan su sai da aka gama gaisawa sannan na kalle su ina fadin"A ina kukaji rasuwar sannan waya kwatanta muku gidan nan..?
Sa'adatu tace"Ai tun da naga an kwana biyu baki dawo ba nace ba Lafiya Megidan ma nata jimamin abun. yace haka kurum bazaki je ki zauna ba ko don makaranta yara da muka ga an yi kwana biyu sai yace bari yaje gidan kakaninsu su Amir yaji ko Lafiya. to chan yaji abunda ya faru wajen kanwar Baban su Amir ce domin ina ganinta tana zuwa itace ta fad'amai mahaifiyarki ta rasu sai ya Nemi ta kwantatamai gidan nan sai ta mai kwantance mun d'an sha wuya kafin mu gane,sai dai kinsan gidan mutuwa baya boyuwa balle da naga ba'a gane ba sai na rika kwantance da cewa Bebiya bata mgana sai ko gashi an kawo mu"
Na jinjina kaina,kwallah na Taruwa acikin idona makota na ne da ban had'a komai da su ba,Ammh sun nemi inda nake sun zo min gaisuwa Su mama kuwa tun ranar uku basu dawo ba,bana saka ma Yaya Ishaq a lissafi bai Dauke ni da Daraja ba,ballataana ya Dauki dangina da iyayena abun Daraja Har afili na nuna musu jin Dadi'na na nuna su ga sauran yan'uwana da Goggo suka dinga saka albarka har da gurasa Habiba tazo da shi ita kuma Sa'adatu sai ta Dafo Dambun Shinkafa da yaji Zogale Goggo ta karba ta kai ma Mutun gidan suna fad'in Allah ya bada Lada
A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana"
Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba"
Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani.
Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama"
Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata.
Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma"
Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi.
Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na ji saukin Jirin sai dai ciwon kan ne,Washegari Yaya Asiya ta koma kano Yaya mariya daman muna isowa ta wuce gidanta
Wasa wasa jikina ya ki dad'i har sai da na kara Sati a karofi Goggo na kula da ni,tare da su Amir kamar kada na koma inda na fito sai dai ba Dama ranar da nake da kwana bakwai a karofi Goggo ta saka Yaya isa ya maidani da Yammah bayan taga naji sauki,Tare da sha tara na arziki komai ta had'amin su garin kunu,garin Danwake,Wake,Tsaki,rama bushasshiya da Zogale sai Taliya yar Hausa da yara suke so sai ta saka aka Murzamin ta samin a kwali saboda kada ta karye hatta kayan maggi sai ta siyamin,da kayan miya mai yawa sannan ta saka Yaya isa ya kaini har gida ni da yara ina ta masa godiya shima da ya saukeni ya bani dubi biyar yace na rike sannan ya Jadaddamin naa kula da lafiyata na amsa mai da in sha Allahu.
Gyaran gidan na fara ko'ina duk yayi kura,Amir na tayani da kwashe kaya su Anum kuma sai dai su kara batawa,Adaran Taliya yar murji na Dafa mana na manja mai ruwa ruwa muka ci tare a faranti daya muma Santi muna gamawa bayan mun yi sallah na saka suka kwaso littafan makarantansu nace su duba tunda gobe zasu koma makaranta.
Wasahegari Laraba da wuri na shiryasu na kuma fita da su da kaina,Haruna da Sa'adatu da na leka gidan suka karamin gaisuwa da tambayan ya karfin jikina..?nace naji sauki sai hamdalar ubangiji.
Makota na dake kusa dani wad'anda ban taba ma shiga gidajen su ba sun shigo sun min gaisuwa daga suce Sa'adatu ta fad'a musu ko Habiba naji Dadi Sosai domin ba karamin masoyin ka ba ne zakayi rashin uwa yazo yace maka Allah ya kara hakuri kuma bazaka manta da wannan mutumin ba, wanda kuma bai ce maka Allah ya kara Hakuri ba,shima girman abunda ya aikata yana nan acikin ranka bazaka taba mantawa dashi ba.
Na dawo da kwana Biyu Anty Mamah tazo min gaisuwa tace ta zo sau biyu bana nan,nace mata eh nayi rashin lafiya ne tayi min gaisuwa ta kuma bani Hakurin sun yi tafiya ne chan dangin megidanta Kumo dake jahar Gombe ta jima muna ta Hira sai la'asar tatafi bayan nayi mana Danwake da manja da yaji taci ta koshi,sannan mukayi sallama washegari kuma daga makaranta Sai ga Badariya tazo min gaisuwa itama da ban hakura Mama bata nan bikin D'iyar Hajiya Barira k'awarta tatafi wajen satin ta daya Abuja aka kai Amarya, dagachan ta biya gidan su Zainab ta kwana biyu.
Sai kawai na samu kaina da cema Badariya"Sun dawo ne..?ya mai jiki..?
Badariya tace"Basu dawo ba suna chan jikin Farhan da sauki sun dai Tsaya Hutawar su kawai"
A fili nace"Allah ya dawo da su lafiya"
Daganan ban kara tofawa ba,Bata jima ba ta tafi tace saboda Mama yanzu in taga ta Dad'e sai ta fara fada, nace gaskiya kam ya kamata ta tafin kada dare yayi mata.
Mutuwar Tamadina ta Dakeni matuka,sai dai na zauna nayi Tagumi ina sharan kwallah in Amir yaga nayi Tagumi sai ya cire tagumin yana fadin"Umma ki daina tagumi ummanki zata dawo"
Sai ya bani dariya na jawosa jikina ina fadin"Aa bazata dawo ba Amir..Ai kasan mutuwa ko.?kuma a makaranta an fad'a muku duk wanda ya mutu ai baya Dawowa a rami za'a ha'ka a binnesa shikenan bazamu kara ganinsa ba"
Cikin yanayin mganar sa yace"Ita Umman ki a rami aka sakata..?
Sai na gyad'a mai kai Lokaci d'aya ina fadin"Eh mana..kowa zai mutu muma watarana zamu mutu a hak'a rami a binne mu baza'a sake ganinmu.Mu yi ma wadan'da suka rigamu mutuwa addu'a muma in mun mutu sai mu samu masu yi mana addu'a"
Ya gyad'a min kai kafin yace"To Umma zan rika yi ma umman ki addu'a"
Daman kuma ina yawan fad'a musu in sukayi sallan su rika cewa Allah ya gafartama iyayanmu da magabatanmu da yan'uwanmu,kuma suna yi,Har su Anum haka na koya musu nima in dai na yi sallah sai na Roki Allah ya jikan dukkan yan'uwa musulmai da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah yasa in tamu tazo mu samu cikawa dakyau da imani.
An yi addu'ar Arba'in Tamadina,Ni ban je ba Hakama Yaya Asiya su Goggo ne da Yaya mariya suka koma sai dai daga gida nayi mata addu'a da Sadakan Allah yakai haske kabarinta na Rokar mata salama da amimci a wajen Ubangiji a kabarinta,Ni tunda Tamadina ta rasu komai ya fita kaina naji bakowani wani abu ne zai rika batamin rai ba,Na riga nasan na rasa dukkan wani bangare na jin Dadi, Dariyata kadai ya'yana ke gan. sune kad'ai yasa har yau nake tsaye kan kafafuwana,Saboda hakane yasa na Dage da shan mgunguna saboda in nazo na kasa ko nayi Rauni ya'yana baza su iya d'aukan maraici tun suna da kananun shekaru ba. shiyasa karfina da Kuzarina duk Ta dalilinsu ne shiyasa ita uwa ya'yanta kan zama gwarin gwiwanta sau da dama.
Kwata kwata nama manta da mganar Form din da na cike na koyan sana'o'i da bada tallafi,na mikama Allah duka al'amarina,sai kwatsam Badariya tazomin da labarin an Turo mata sako Daga Kungiyar Women charity Foundation kan zasu tantancemu ranar asabar karfe goma na Safe a wata makarantar yan mata Dake cikin gari sai na rud'e na fara rawan jiki ina fadin"Bada..riya..To ni ya zan yi..?bansan ko'ina ba fa..?
Sai tayi Dariya tace"Sha kurum ki zan yi ma Mama karyan makaranta sai nazo na rakaki"
Sai da ta fad'i haka sai hankalina ya kwanta, tun daga ranar ko dayaushe addu'ata d'ayane in da alheri acikin wannan mafitan. Allah ya tabbatar min in ba alheri Allah ya musanya min da mafi alheri.
Sai naji zuciyata ta natsu da al'amarin,Ranar jumma'a Dakyar na iya barci Saboda Zullumin abunda zai faru gobe,Da sassaafe na shirya yara suka wuce Tahfeez nima ban zauna ba na shirya tara da wani abu Badariya tazo na goya Ahmad na saka Dogon hijiba na mai ruwan kasa duk yasha ruwa na rufe gida muka tafi,Ita ta biya kudin adaidaita gaskiya akwai tafiya ba kad'an ba tsakanin gidana da Makarantar mun isa goma saura Haraban makarantar cike da manyan motoci daga gani abun na manyan mata ne.
A wani babban hall na makaranta ake taruwa kai tsaye muka nufi chan mun shiga mun tarar da mata da yawa duk sunzo,muka samu waje muka zauna ina ta raba ido sai da goman tayi sannan Manya mata masu nasaba da ilimi da zati suka rika shigowa suka tsaya a gabanmu, ina ji Badariya namin Rad'a mai bakin mayafi mai jikan nan Hajiyar su Raliya ce na jinjina kaina daga gani kudi da isa sun zauna ajikinsu
A she mu Talatin suka Dauka,Bayan sun kira sunayen kowa da kowa muka mike gabad'ayamu akwai yan rakiya ire iren Badariya,Wata Hajiya ce mai glass take kiran sunaayenmu,na kasa Raunanun kunnuwa a ina jin sunana na mike bayan Badariya ta rike hannuna muka mike tare sannan ta koma ta zauna, ashe Wani kati zasu raba na na shedar Training d'in da zamu yi sannan da wasu bayanan da suka danganci abunda za'a koyar damu.
D'aya bayan d'aya aka rika kiranmu ana bamu wani karamin kati mai dan Fad'i.sannan akwai hoton kowacce ajikin katin har akazo kaina,na mike na kwanto ma Badariya Ahmad dake bayana na fita ina raba ido har gaban Babban ajin na mika hannu na karb'a ta kara kallona sama da kasa har na juya sai ta kirani da fadin sunana"Fa'iza Sidi karofi'
Sai na juyo da Sauri saboda ina gabda ita naji ta fad'i sunana yasa Hajiyar su Raliya ta D'ago tana kallona sai na rankwafa na gaisheta da girmamawa sai ta amsa itama cikin sakewa Lokaci daya tana fadin"Kece matar Brother din Badar..?
Sai na gyad'a mata kai cikin yanayi mganata nace"Eh hajiya tare..tare ma muke da ita"
Sai na juya ina nuna mata Badariya ashe har tataso dauke da Ahmad tazo wajen mu,Ta duka ta gaida Hajiyar Raliya ta amsa tana tambayanta Mama tace tana lafiya sai ta kara kallona tana fadin"Ashe tare kuka zo..?
Badariya tace"Na rakota ne Hajiya"
Kai ta jinjina tana kara kallona nasan har da mamakin ganin yanayina sai matar nan mai glass ta duko tana mata mgana naga tana nuna mata Takardan hannunta sai ta amsa tana Dubawa kafin tace"Fa'iza abu hud'u zaki koya..?kuma a ka'ida biyu ne kina ganin zaki iya..?
Da Sauri nace"Eh zan iya Hajiya.."
Sai dayan Matar tace"Hajiya kinsan dokace Biyu ne ai hudu yayi mata yawa da wanne zataji..?
Sai naga ta duka daidai kunnenta tana yi mata mgana sannan ta jinjina kai,Itama kuma Hajiyar Raliya sai tace muje mu zauna.
Komawa mukayi muka zauna ina ta Raba ido,naga mata kala kala ire irena masu fama da rayuwa da zamantakewar aure,ni dai akasan raina ina jin yakinin zan koyi duka abunda za'a koyamin Saboda shi kad'ai nake ganin gatana a wannan duniyan.
Bayan an gama bawa kowacce Katin ta, sannan suka fara mana bayanin yadda abubuwa zasu kasance zamu fara koyan abubuwan da zasu koyamana nan da sati d'aya zasu raba abun gida Biyu Mrning da Aftternoom,Da Safe za'a koyar da abubuwa Biyar da yammah ma biyar daman goma ne,Da Safe za'a koyar da girke girke da Had'a lemuka,Da yammah akwai koyan yadda ake hada halawa da dilka,Da yadda ake yinta,Da had'a Turaren wuta na Icce da Humra da su Kwallaca,sai na fara nazarin ya abubuwa na zasu kasance..?kenan sai dai na rika zuwa safe da yammah kenan..?
Sannan sun yi mana bayanin awa Bibbiyu ne da Safe tara zuwa sha Daya da Yammah D'aya na rana zuwa uku na yammah,sannan sun bamu shawaran mu natsu zamu iya duka abunda za'a koyar damu tunda na wata uku ne tsawon sati goma sha Biyu ina jin duk abunda suke fad'i Saboda da karfi suke mgana kamar su san da masu Laluran rashin karfi ji irina.
Sun tabbatar mana da cewa acikin mu za'a dibi mutane goma masu hazaka da aka ga sun chanchanta ranar da zamu gama za'a basu Jarin su a Hannunsu,sannan sun horemu da mu maida hankali komai daki Daki zasu koyamana duk abunda bamu gane ba mu yi tambaya. kada mu zama masu duhun kai,Sannan daga karshe sun ce zamu rika zuwa da Littafi da biro mu rika rubuta sunayen abubuwan da za'a koyamana saboda in mun koma gida mu yi bita,Sannan zamu rika rubuta sunanmu kullum inda muka zo da Turanci wato Attendence.
Sannan ko da wani lokaci zamu rik'a zuwa da wannan katin shine shaidar an tantance mu sai mun nunasa za'a barmu mu shiga, zuciyata na cika da Farinciki har na fara tunanin ma na iya duka abunda nasaka raina zan koya,ajikin katina an saka Abunda nake son koya kamar yadda Badariya ta Rubuta, shi zai nuna inda ya kamata na tsaya sai Sha biyu na rana aka tashi sun tabbatar mana da cewa kwararun ma'aikata ne zasu jagoranci wannan tafiya tamu mun yi godiya sosai sukace mu yi ma shugabar wannan kungiyar addu'a da fatan nasara Rayuwa, ni ko araina nace duk Sallah sai na sakata nace Allah ya yi mata gatan Duniya da lahira kamar yadda itama tayi mana gata a duniya.
Daga nan muka rabu da Badariya ta taremin adaidaita na Dawo gida zuciya ta cike da Farinciki,Sai dai na Fara Tunanin inda Zan rika kai Ahmad Saboda sun ce ban da yara saboda ba wajen da yara zasu zo ba ne,akwai abubuwan da bai kamata yara su shakesa ba yayin had'asa.
Sa'adatu ta fadomin rai nako shiga na gayamata ta tayani murna ta kuma tabbatar min na rika barin mata Ahmad zata kular min da shi sai naji Sauki na Dauki damaran maida Hankalina kan damar da Allah ya aramin,Naji dadi tun Sha daya zan dawo gida nayi ma yara girki ko na kimtsa gida da la'asar kuma in na Dawo sai naji da girkin su kafin su dawo makaranta.
Har wankin yaran sai da na kwashe na wanke na goge tare da nawa tunda zan fara fita ba lalle na rika samun Lokaci ba,Ranar Alhamis saura kwana biyu a fara koyar damu Yaya Ishaq ya dawo da Safe na sallami yara sun tafi makaranta kenan ina zaune afalo ina bama Ahmad kuninsa ya shigo ban ko ji sallamansa ba ina chan ina Lissafin duniya.
Sai da ya kariso cikin falon ya kara yin sallama sannan na jisa,na d'ago na kallesa,kamar ba shi ba ya kara Kiba har da karin Saje da gemu ga Tumbi alamun yana samun hutu da jin Dadi.
Kamar bakina na ciwo nayi mai sannu da zuwa bayan na kauda kaina.
Ahmad kuma sai ya fara dagamai hannu yana gaurancinsa.
Bakinsa na gogemai da Kyallen dake gefena shi kuma sai ya Duka ya Dagasa sama bayan ya sauke jakar Hannunsa, mikewa nayi ina kakkabe jikina zan wuce dakina araina ina fadin ka dawo adaidai kuwa.
Sai dai ban karisa ba ya D'aga murya kirani na juyo cikin mganarsa yace"Kin yi min sannu da zuwa baki dauki kayana kin kai min ciki ba.kuma zaki wuce ni kamar kin ga wani banza Fa'iza..?
Sai ban damu da kalamansa ba na koma na Dauki Jakar ya mike ina gaba yana baya ya bude shashen nasa. muka shiga a tsakiyar falon na Dire masa jakarsa na juya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 25