fashe da kuka shi yana na Sarari ni ina na zucci.
Mama ta kama kunnuwana ta murde tana fadin"Ni zaki hada ma gulma da munafunci har Goggon karofi ta taka har gidana taci min mutumci don Ubanki..?ai nayi miki komai Tunda na rike ki kuma sannan daga karshe Mijina ya aura miki D'ana kika shiga Cikin zuru'ata duk da bana so..Shegiya mai bakar aniya,Wlh fa'iza na tsaneki na tsani na bude ido na ganki a matsayin surukata"
Anty Binta ta karbe da Fadin"kuma ban da Ishaq din uban waye zai aureta ya zauna da ita ahaka..?
Mama tace'Ki barta zan yi mganinta Tunda bata san mutumci ba"
Haka suka gama zage zagen su,suna yi suna Dungurina suna murdemun kunni sannan suka saka kafa sukayi tafiyar su haka na zauna na Rumgume D'ana ina kuka shima yana kuka har sai yaushe ne zan daina Fuskartar wannan Tozarcin..?
Ba mai Lallashina na gama kukana na Share hawayena,Ashe ban tsira ba Sati biyu da Tafiyar su Ishaq,sai gashi ya Diro ranar asabar da yammah,Abunda yayi min yasa na Fahimci daman saboda yaci min Mutumci ya Dawo.
Har Bangaransa ya kirani na Duka gabansa shima ya ci min mutumci,har yana fadin ba Domin mugun kalaman bakin Baba akansa ba wlh da sai ya Sakeni sai naje Goggon ta auramin Isa ko Yusuf cikin manyan ya"yanta sannan ya kara jamin kunne akan yaya mariya da gaske yake yi kada ta kara zuwarmai gida in kuma wlh tallahi ya kara ganinta sai ya wulakantata.
Na Dago kaina cikin Hawaye muryata ta shake cikin wani yanayi nace"Kayi hakuri..Ba..zan iya fada mata ta daina zuwa ba ne"
Sai kawai na Fashe da kuka Tsawa ya Dakamin yana fadin"To ni zan gayamata in muka hadu Tunda gidan nan nawa ne ina da iko da shi kada na kara ganinta acikin su..In kina Tunanin yar'uwan ki ce in kun had'u wani waje sai ku gaisa ammh ba"a gidana ba kin ji maa na gayamiki"
Sai na kasa mgana kaina na kasa na Share majina kafin nace"Kayi hakuri don Allah.."
Mikewa yayi a fusace yana fadin"Ke dai kika sani kin dai ji abunda na gaya miki..daman abunda ya kawoni kenan Har ga Allah bana son zama agidan nan chan yafiye min kwanciyar Hankali ki kula Fa'iza kada a kara kirana afadamin an hada baki dake an tozarta uwata in hakan ta kara Faruwa zan manta kalaman Baba da komai kema na wulakanta Rayuwarki wlh"
Daman Tozarta ne yazo yi kuma yayi washegari tun Safe ya Dauki hanya,ko sallama bai min ba sai zuciyata ta kara Kek'ashewa na kara Fahimtar cewa ni din ba kowa bace a zuciya Ishaq da duka ahalinsa akwai yuyuwar na nemi abunda zan tsaya da kakafuna ko Saboda gaba da kuma ya'yana domin na Lura hankalinsa yayi gaba daidai da su Yaran ya daina Damuwa da su Sosai.
Tun tafiyar nan da yayi sai da yafi wata bai zo ya ganmu ba,Kudin Hannuna duka ya kare bamai lekomu dagamu sai Allah,kayan abincin mu sai ya kare mun fara shiga yanayi sannan ake aiko mana da Cefane wani Lokacin Direban gidan Anty Binta ko Badariya,a wannan gabar sai da yayi wata biyu da kwanaki sannan yazo ya ganmu shima din sallama suka zo yi Zasu tafi Umra shi da Zeey da iyayanta gabadaya har da ita Zeey din suka zo sallama kwana D'aya suka yi suka koma gidan Mama kuma suka Sauka sai da Safe suka zo min sallama,nayi masa korafin Haruna ya fara mganar rashin biyansa akan Lokaci sai ya fara masifan bazai iya ba gaskiya shi bashi da kudi kuma haka ya tafi bai bani ko sisi ba,Daganan na kuduri niyar bazan kara mai mganar ba Zan neman ma kaina mafita,Bani da wata mafita alokacin sai na maida lamurana wajen Ubangiji na rokensa yaga Halin da nike ciki da ni da ya'yana ya Gaggauta sama min mafitan da zan kula da kaina da ya'yana.
*Janafty*
*KANA NAKA..!*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'A SKWATO__SAKINA HASSAN 08066726866
INA MATA Y'AN KWALISA MASU SON GYARAN JIKI MACCE DA TASAN KANTA KULLUM CIKIN GYARA TAKE
INA MATA MASU FAMA DA RAMA KU KINSA KAYA BASU KAMA JIKIN KI 😫
INA MATAR DA ADDA JIKI BAKI DA HIP BAKIDA BAYA IN KINYI DRESS BAYANKI A SHAFE
INA WADDA KE FAMA DA ZUBEWA NONO KU KE BAKI JIN DADIN GANIN SU KAMAR SILIFAS
KINYI TA GYARAN BRST HAR KIN GAJI HJY TA GYARAN BRST WAHALA GARESHI DUK WADDA TACE MIKI GA MAGANIN BRST DA SHA ZAIYI TO KARYA TAFADA MIKI GYARAN BRST YANA SON JUREWA DA DAGEWA IN KIN FARA BA'A TSAYAWA INSHA ALLAH SAI KIGA SUN ZAMA NORMAL
MUNA DA INGANTATA ZUMA BRST DA MUNKA SARRAFA DA KAYAN ORGANIC HERBAL SU MACA DASU AGUAJE WADDA INDAI KIN RIKE TA INSHA ALLAH ZAKI GA SUN CIKO SUNYI KOSHI RUBA 2 KU 3 SUN ISA YAZAMA MIKI YADDA KK SO 4K
MUNA DA GARIN HIP DA BRST YAKE GYARA DA GYARAN JIKI DA KARIN NIIMA YAKE YI 4K
MUNA DA INGANTATA ZUMA TA HIP ITA MA MUN SARRAFA TA DA KNGAN TATUN KAYAN ORGANIC HERBAL DA KE FIDDA MIKI HIP 6K
MUNA DA ZUMA KIBA WADDA ZAKIYI FRESH DA BULBUL ITAMA RUBA 2 KU 3 ZATA YIMIKI YADDA KK SO 2K
MUNA DA GARIN GYARAN BRST DA KARIN NIIMA SHIMA GUDA 2 KU 3 ZAKI SHA 2K
GASKIYA DA AMANA ITACE NASARAR.MU
MUNA AIKA KAYA KU INA CIKIN YARDA DA AMINCI
MMN MUJAHID __SAKINA HASSAN MUNA SOKOTO DA KEBBI 08066726866
*🅿️10*
*Wacece ZAINAB...?*
Cikakken sunanta shine Zainab Lawal bako asalin duka iyayanta uwa da uba Fulani ne gaba da baya,Mahaifiyarta Hajiya Halima bata yi karatun boko ba Saboda yar asalin rugar Njob'oli ne fulani Jahar yola,Shi ma Dr.Lawal din, Mahaifinsa ya'yan maza suke da Mahaifiyar Hajiya Halima auran zumunci ne iyayansu suka kulla a tsskanin ya'yan nasu.
Shi Dr.Lawal a cikin garin Yola ya girma kuma nan aka haifesa saboda Mahaifinsa ya baro cikin Ruga saboda neman ilimi kuma ya samu Dalilin da yasa bai koma cikin ruga ba kenan sai dai Lokaci bayan Lokaci yana zuwa Dubasu,Sannan shima matarsa Daga Rugar aka aura masa shiyasa shima Alhaji Lawal aka ki bari ya bar gida.
Alhaji Lawal bako yayi karatun Boko har matakin Phd dinsa ya fara aiki da Hukumar Tattara haraji ta kasa reshen Jahar Yola,kuma achan ya fara zama bayan an aura masa Halima,Da farko yaso ya Bijirema auran ne,ganin kamarsa mai ilimi dan gayu a had'asa da yar Rugar da batasan komai ba Sai dai ya sauya shawara lokacin dayaje yaga Halima sai yaji zai iya auranta Saboda Tana da kyau Farace doguwar Bafullatana,ga gashi har gadon baya Hancinta har baka kyau kamar ita tayi kanta sai yaji alfahari ya karun masa Saboda Shi yana son abu mai kyau wanda zai zame masa abun Alfahari watarana.
Bayan auran su a yola suka fara zama,Ya na son Halima sosai,Saboda kyanta da sanyin Halinta,sannan Bafullata ne irin sa,Abu daya ne yayi mata cikas rashin ilimin Boko na addinin ma ba sosai take da shi ba Saboda ko acikin Rugar ba kmar yanzu da gwamnati ke basu tallafe tallafe domin inganta ilimi a rugga ba,
Yaso ya barta tayi karatu ammh Saboda Tsananin kishinsa yasa bai barta ba,kuma taso tayi karatun tunda ta dawo cikin gari da zama,ammh ya hanata saboda Yana da Tsananin kishi,bazai jure ganin ta a makaranta tana gwagwamarya cikin maza ba,Sai ya hanata ya nuna mata ilimi mace shine zaman gidan mijinta ta kula da ya'yanta dalilin haka yasa sai ta hakura iyayan su kuma Ilimin bai Dame su ba damuwa suka yi da karatun ba.
Dr.Lawal bako dan boko ne sosai Domin Rayuwar boko yake yi a gidansa shi ya tsara hakan tun farkon zaman auransa da Halima,Ya'yan su biyu ya tsara zasu haifa Saboda a cewarsa bazai zo ya haihu da yawa ba ya kasa Rike ya'yansa ba,Sai dai Kana naka Allah ya riga ya gama nasa Sai da Halima tayi haihuwa Uku suna yin wabi sannan ta Haifi zainab ta Tsaya Tsakaninta da kanwarta Zeenat suna kiranta Zuzu Shekara Biyar ne daga kanta kuma sai ta Haifi namiji sai dai ko arba'in din sa batayi ba ya koma ga Allah Daganan suka tsaida Haihuwa a cewar Alhaji Lawal bako Kada ta kara Haihuwa kyanta da Nagartatan su Lalace ita kuma bata da yadda zatayi bata iya masa gaddama rayuwarta da ita kanta sai abunda ya tsara mata.
Duka ya'yan nasa yadda yaso haka ya tarbiyarta dasu,Halima bata isa ta nuna wani iko kan ya'yanta ba tun suna kanana sai abunda Baban yace shi zasu aiwatar sannan baya shawara da ita gani yake bata san ne take yi ba Tunda bata da Ilimin Zaman duniya.
Zainab da kanwarta Zuzu sun taso cikin Sangarta da Sakewa da kuma Tsananin gata,ba kwaba ba kyara ba Gyara haka suka taso a gaban iyayansu koda sun yi wani abun mara kyau in uwar zata kwaba musu sai Uban ya hana sai ya rika nuna su kadai ne ya"yan su in basu ji dasu ba da waye zasu ji..?Dole ne su ji da su tunda basu da kamar su,In tace hakan bai kamata ba sai yace duk wanda kika ga bai sakar ma ya'yan sa Gata ba bai da shi ne sannan bai san Darajan ya'yan ba ne.
Daga karshe sai ta koma bangaran yaran sai ta Fahimci suma sun fi jin mganar Uban su fiye da ita tun suna yara sun Fahimci mahaifiyarsu kamar Hoto take sai Uban yayi shawara da su,ammh ita bai neme ta ba ko wani abu yace in suka ce Daddy mommy fa..?Sai yace su kyaleta kawai mommy bata san komai a wannan zamanin ba to har suka girma da wannan Tunanin aransu Daddyn su shine nasu uwar su kuma ta nan a matsayin Mahaifiyar su ammh bata da wani Say a gidan da Rayuwar su gabadaya.
Sun taso da Yare guda biyu a bakin su Turanci da Fullanci saboda Daga Uban har uwar basu yarda Yaren su ba In dai suna gida daga Fillaci sai Turanci suke yi Hausa kuma sai dai a waje ko a makaranta,Sannan in sukaje ziyara chan Rugga basa wani yare sai Fillanci sai yaren ya zauna Sosai a bakinsu..
Zainab da Zuzu kyakyawan yan mata ne na gani na fada kamar su, sukayi kan su Saboda kyau da zati to bangaran Uwa da uba duk kyawawa shiyasa suke jajir kamar a taba jini ya fito sannan sun tashi cikin gata da jin Dadi,Zainab ta gama junior secondary dinta suka koma Abuja da zama anan ta ida karatunta ta fada Universty of Abuja ta karanta Chemisty,Gatan duniya ba wanda basu samu ba komai suke nema kafin su yi mgana sun same shi Tun suna kanana komai yan aiki ke yi musu shiyasa su Rayuwar Hutu suka sani da jin Dadin.
Dr.Lawal bako Rauninsa Daya ne ya'yansa yana tsananin kaunar su,Zai iya batawa da duk wanda ya nemi ya tabasu sannan zai iya karta ma kowa rashin mutumci a kan wadanan ya"yan nasa,Yana nuna musu kauna a fili har tana wuce misali Hajiya Halima da suke kira Mommy ko tayi mai mgana sai yace me ta sani kan wannan zamanin tayi mai shuru kawai shiyasa ita nata ido ne sai dai tana addu'an Allah yasa kada su zame mai Raunin da zai zame masa Lalura watarana.
Ishaq kabir karofi ba Zainab ya fara sani ba,Dr.Lawal bako ya fara sani Lokacin da aka mai karin girma da sauyin wajen aiki ya koma Abuja shine ke rike da babban Ofishin su na Abuja,Haka kurum Ishaq yaji Dr.Lawal na Burgesa saboda he is Educated and Innocent,sannan jajirtattace ne kan aikinsa,Shi kuma Ishaq yana da Ladabi da Biyayya ga manyan sa shiyasa suka Saba da Dr.Lawal,Kuma karin ma abun yana ganinsa Farin namiji gaye kyakyawa mai ilimi da sanin ya kamata Dr.Lawal na son harka da mutane masu kyau da wad'anda suka san abunda suke yi,Dalilin Sabawar su yasa Ishaq bai iya kiran sunansa Sai dai yace Daddy kafin shekaru su ja su san komai na juna har gida Daddy kan gayyace sa gidaansa yaje yaci abinci anan yaga Zainab ya nuna yana sonta lokacin tana shekarar karshe a jami'a tana masters d'inta lokacin daya ganta yaji aransa mafarkin daya Dade yana yi ne Allah zai tabbatar masa bai nemi zainab kai Tsaye ba sai da ya fara Tuntubar Daddy shi kuma yace ya bashi lokaci ya kara Bincika Ishaq din kuma ya Samu komai yadda ya sanar da shi Cikin Lokaci ya amince batare da Shawara da Hajiya Halima ba Ya'yansa kawai yayi shawara da su,Daman kuma achan Rugga an saka ido kan rashin auran su zainab din,Shi daman baya so ya aurar da su in da zasu sha wahala ne ya fi son ya aurar da su inda yake da Mgana a wajen zai iya kula da ya'yansa ya kuma Tofa komai a lokacin da yaso a kan Rayuwar ya'yansa.
Zainab bata isa tace taki Ishaq ba ganin Farko da tayi mai taji ya shiga ranta suka fara soyayya sai dai da Farko taso ta Damu da taji yana da mata sai ya nuna mata kada ta Damu Fa'iza ba komai bace a rayuwarsa face Uwar ya'yansa ita ce First love dinsa da ta fadama Dr.Lawal Dariya yayi yaji Dadin da yarsa zata kasance Zara Cikin wata Hajiya Halima nata sai dai ido kawai har gwara ma Zuzu bata kai zainab rawan kai da Daukan duka Hallayar mahaifinsa nasu ba ita ta kan tsawarta mata taji,Ita ma tana nan tana karatu a Nile University of Abuja,zainab kuma tana gama karatu tayi Services a wani kamfani karafuna bayan ta gama kuma suka Riketa aiki a wajen,Batare da Ishaq din ya sani ba kuma Lokacin har an yi mgana ta iyaye lokaci kawai za'a sanya har zuwa Lokacin da akayi auran Ishaq bai fahimci bai da wani iko akan Zainab ba sai abunda Mahaifinta yace da shi ta ke amfani.
Shi ya gina auransa kan Soyayya da kyau nasaba kudi da nagartan ilimin zamani,ita kuma ta auresa ne Saboda kyansa da kudinsa sannan saboda Mahaifinta,shi kuma Dr.Lawal bako ya amince da auran ne saboda yana Tunanin Daga Ishaq har Zainab suna karkarshinsa ne zai iya yanke kowani irin Hukunci kan yarsa batare da ya D'aga ido yayi mgana ba.
Muje zuwa..!
****
*Katsina..*
Bayan wata daya.
Mutanen Umra sun dawo an kawo Tsarabobi kala kala nima Badariya ta kawo ma su Amir nasu,abakin ta nake jin Tsaraban ma aiko da shi sukayi ta Abuja suka sauka,Ya Ishaq din kuma bai zo ba,an kawo ma yaran Jallabiya Amir da Musty,Anum kuma Riga da wando,Ahmad kuma kaya riga da wando masu kyau da yarari,Sai Dabino da ruwan zamzam na amsa nayi godiya Daman ni ban saka aka ba ballata don ba'a bani ba na Damu Badariya ta fadamin har Hajiyar Dala an aika mata Da Tsaraba to daman ai ya kamata a aika mata ta chanchanta.
Damuwa ta daya ne yanzu yadda komai ya ke kara lalacewa,Ni ba na jin kaina sai ya'yana sune a gaba,Ko Haruna ni da kaina na shirya na shiga har gidansa Daman makota muke bamu da nisa,Na taba shiga sau biyu tun Fara kai su Amir makaranta,Sunan matarsa Sa'adatu,dayake bana harka da kowa sau daya ta taba shigomin gidan daganan bata kara ba Ishaq bayan Yan'uwana da Dangina har da Mutane ma ya rabani da su Ahalin kuma an ce Mutane Rahma ne.
Naje na same sa na bashi Hakuri akan rashin Biyan sa kudin sa wajen wata uku sai ya nuna min bakomai an zama D'aya tunda Hakkin makota ya hadamu matarsa Sa'adatu ta karbe ni Hannun Bibbiyu,Na isketa tana ta Saida Saide kayan miya da su maggi da gishiri kayan dai kulle kulle na gida na mata sai kuma zuwa ake yi ana siya sai abunda ya bani sha'awa naji Dama ni ce ban iya shuru ba har sai da nayi mata mgana nace dama nice ita ina son nima na Fara sana'ar cikin gida na mata, bata ji ba sai da na kara maimaita mata sannan taji ni Dariya tayi kafin tace"Haba Hajiya kamar ki ina ke ina wata sana'a..?kuna da Rufin asirin ku..Sana"a ai sai irin mu matan talakawa mu samu na Rufa ma kanmu asiri damu da mazajen mu"
Naji mamakin mganarta ni kuma sai nace mata"ai sana'a bata ga Talaka bata ga mai kudi..Muna yin sana'a ne Domin dogaro da kanmu da kuma ya'yanmu sannan ita mace da neman na kanta a kasanta saboda kada gazawa ya zame mata nakasu watarana"
Sai ta jinjina kai kafin tace"Kuma hakane Hajiya"
Ina kallonta kai tsaye nace"Ba sunana Hajiya ba..Sunana Fa'iza ko ki kirani maman Amir"
Daganan tayi dariya muka cigaba da Hira sama sama,Ban jima ba na koma gida tundaga Lokacin araina na saka ma raina bazan zauna na mutu ni kad'ai acikin wannan gidan da bama ceto sai Allah ba nima zan rika fita na shiga jama'a domin su din Rahma ne.
Muna cikin Haka aka kore su Amir daga makaranta suna dawowa suka fadamin suna zuwa aka koresu kudin makaranta acikin makarantar suka zauna har sai da aka tashi Haruna yaje ya Daukosu hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi na so na kira Ya Ishaq na fadamai sai kuma bani da kati ko na flashing kuma bani da ko asi a hannuna sai na koma na Rumgume hannunawana kawai na rasa mafita,kawai sai nace su dakata da zuwa makarantar sai an biya a baya duk Lalacewa yana biyan musu kudin makaranta akan Lokaci basai ta kai ga an koresu ba,ganin sun kwarari sati a agida ba bokon ba islamiyan sai dai nayi musu na Islamiyan agida,Sai suka fara Damuwa suna ta tambaya na Umma meyasa muka Daina zuwa makaranta..?Anum da Musty kenan Amir shi yafi su wayau da sanin me ake ciki,gabadaya na rasa mafita Kwana takwas da Faruwar haka Ranar da yammah sai ga Jamal yazo shima k'wallo suka zo yi anguwan ya shigo gidan ya iske su a bakin Anum yaji basa zuwa makaranta da ya ce meyasa yau basu je ba..?Shine daya tambayeni nace an koresu ne basu biyu kudin makaranta ba yana ta mamaki ya tambayeni ko na fadama Ya Ishaq sai nace mai A'a.
A gabana ya Daga waya ya Kirasa yana fadamai abunda ke faruwa duk da bana jin me yake fada nasan Fada yake yi kuma duk a kaina,Sai da suka gama mgana yace min Ya Ishaq yayi fada kan meyasa ban kirasa na fadamai ba..?
Har Jamal din na fadin"Anty Fa'iza kema da kin kirasa kin fadamai Halin da ake ciki.."
Kallonsa kawai nayi ban yi mgana me zan ce..?ko na fadamai ba ganewa zai yi ba shurun yafi alheri.
Labari har kunnen Mama da Anty Binta na kuma san nasha Zagi da cin mutumci washegari Jamal din yazo ya Dauke su ya kaisu makarantar ya biya komai,Sannan da yammah ya kawo min 20k a bama Haruna kafin ya Dawo na karba nayi godiya da Safe kuma da kaina na shiga na kai mai yana ta godiya nima inayi sai naga ai ni ce da Godiya domin ni yake yi ma alfarma.
Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa masu jin dadi suna ji masu jin akasin haka ma sun cigaba da ji,Har azumi ya karato Ya Ishaq bai waiwayo mu ba abun na bani mamaki ace in shi ya manta damu su Mama ai basu manta yana da mata da ya'ya ba ammh sai naga suma basu damu ba kamar hakan ma yafi ye musu,Kayan abinci ko wani sako sai dai ta Hannun Mama ko Anty Binta batagwara,Ni bani da wata Daraja ko kima sai ta zaman ya'yansa kamar yadda yace din.
Tuni yara har sun saba tafiya makaranta ba biskit ba Lemo saboda babu Daga shinkafa sai taliya ake kawo min sai man girki da kayan maggi,duk abunda bazai zama Dole ba ba'a kawo mana shi,Nama ko mun manta rabon mu da shi,ni bana ma jin kaina yaran nake ji sun gaji da Rigima sun Hakura tunda babu sannan Tun suna Zencen Daada har suka hakura suka Dangana ni ce karfin gwiwan su shiyasa bana yarda na Sare ko Raunina ya bayyana agabansu
Ahaka muka fara azumin watan Ramadana,Har kuma muka fara shi muka sauke Ya ishaq bai zo ba,kuma bai taba nema na ba,Ni ma sai na kama kaina sai dai da watan nan mai albarka ban yi barci ba nayi addu'an Allah ya sama min mafita domin ya'yana domin goben su,Kayan sallar yara Sai ana gobe sallah Jamal ya kawo musu Amir da Musty shadda guda biyu sai yan kanti kowanne D'aya d'aya Ahmad ma shadda guda daya sai sauran yan kanti Anum kuma Atamfa da leshi dinkakku sai Doguwar riga guda daya,sai takalma su sai nawa kala daya jal na wata Bakar atamfa,ko araina ban ji zan sakaba sai dai in na zauna ba kaya ammh in dai suturan Ya ishaq ne na hakura da su har abada Tsoffin dai zan cigaba da sawa Tunda bani da zabi ammh bayan ya jingine aure na dashi na cire ma raina kara Daura wani abu daya fito daga Hannunsa..
Ganin yadda ya kwarari wata Hudu bai zo ya ganmu ba nasan da gaske yake yi ya zabi Zainab a kaina sai ban ji komai ba sai dai naji Bakinciki har da ya'yan sa suma ya jingine su..?
Ban damu ba ni kawai Fafutaka nake yi har akayi azumi akaga gama bamu ci ko tsokar nama ba ballatana su Dankali da kwai sai tsurar abinci kawai nice nake Sarrafa nau'in abincin Tunda Allah yasa na iya sai Wahalan bata mana yawa sosai ba.
Naman Sa da naman kaza Jamal ya kawo min ranar idi da Safe na gyara na soya su Anum nata murna zasu ci Nama sai da nayi musu kwallah ina Tunanin tun yanzu kenan to nan gaba bansan wani Hali ni da ya'yana zamu shiga in dai na zauna ahaka ba,
Allah Sarki Goggo washegarin Sallah sai ga Hafsatu ta aiko da sakon Nama da Cincin da Cake,Naman soyayye da Danye,Sannan da sakon Hijabi Sabo da Anty mariya ta dinkamin da takalmi na karba na rumgume kayan ina kwallah Allah Sarki yan'uwana basu manta dani ba duk da ni ma ban manta da su ba yanayi ne yasa nayi nesa da su ba acikin son raina ba
Ta fadamin daga gidan Tamadina take jiya taje chan ta kwana ta kai mata kaya daga kano Anty Asiya ta aiko dashi sai naman sallah Daga Goggo sai na wajen Ya mariya naji dadin jin Tamadina tana lafiya,Naji takaici bani da abunda zan daga na bama mahaifiyata nima nema nake yi.
Zuwan Hafsah ne ya Debemin kewa Dani da yara Ranar sallah ta uku gidan Mama muka yini sai Dare Ya Ishaq ya sauka shi da Zainab,Anty Binta da Mama suka rasa ina zasu saka su saboda murna mun gaisa da ita sai mamakin ganin chanzawarta nake yi ta zama wata katuwa ta kara gogewa shima gogan ya Sauya kamar ba shi ba har da Tumbi ya sauke.
Darajan zainab yasa da ni da yara da Hafsah ya kwaso mu muka koma gida,Wannan karon ma Shashen sa ta sauka kuma ni na rika wahala da ita da shi,Dalilinta yasa yayo mana Cafane mai rai da lafiya Saboda sai abun take so ake ci acikin gidan,Da kuma zabinta ake amfani..
Hafsah ita kanta da take yarinya sai da ta ga abun bai dace ba ranar da zasu fita yace na shiga na gyara Bangaransa nasa,Suna fita ta kalleni kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza bayan Girkin da kike musu har da gyaran inda suka kwana kamar wata yar aiki..?
Ban ce mata komai ba sai ma Dariya kawai da nayi to ai batayi karya ba kamar yar aiki nake agidan nan,Sati Daya suka yi mana suka koma inda suka fito,Hafsah dai ana jibi Tafiyarsu ta koma Karofi Saboda an koma makaranta..
Bayan tafiyar su muka koma Gidan Jiya kamar yadda muka Saba dai,Allah ya taimake ni Matar Ya Isa wajen Goggo ta haihu,yan biyu Dalilin dayasa Mama tace na shirya aje suna Dani,Murna kamar an biyamun aikin Hajji,Dukkamu muka tafi har da Anty Mahma da Halisa da yara,Nima tare da su Amir muka tafi chan na hadu da Ya Mariya,Yaya asiya dai bata samu zuwa ba,naji dadin zuwana karofi Allah yasa kuma Lokacin Tamadina tazo gida na kai mata su Amir ta gansu sai mamakin girman su take yi shi da Anum,Koda wani Lokaci in naga Tamadina sai na tuna da Dan'uwan ta da akace sun hada Uba,Wanda tunda mahaifiyarsa da Danginsa suka tafi dashi ba"a kara jin Labarinsu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 25