Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka saboda haka Itama Yaya Asiya badai a ganta da kama mara kyau ba. Ni dai ko da yaushe cikin Tsumma da Ragga In Baba ya gani yayi mgana Mama ta lawayance zance ni kuma bana iya karyatata agabansa,bazan taba mantawa da wata sallah ba,Sallah da na fara yinta a gidan Baban katsina Lokacin na kwashe wajen wata Tara a katsina,kuma tunda nazo ko Karofi kafata bata kara takawa ba Ga Hajiya na raina in Baba zai tafi gaisheta sai naji kamar na bisa,tunda duk karshen wata yake zuwa wani Lokacin shi da Mama suke zuwa wani lokacin shi kadai da Direba ko shi da Jamal. Hajiya na rai na ita da su Yaya Asiya musamman Hasfatu kewar Tamadina kuwa har na cire sa araina tunda ba samun ganinta zan yi ba Tun bayan dawowata Ko mutum daya Daga karofi bai leko mu ba na dai ga Hajiyar Dala da suka taba zuwa Bikin Dangin mijinta ta sauka anan kawaye ne ita da Mama sai muguntar su tazo daya sai dai ita tafi mama ji da kai da nuna ita din watace. Sallar azumi ne Dama da azumi duk na Rame na kara lalacewa,Ni bansan gayu ba, bansan komai mai kyau ba ni na dauka abu mai kyau a wajen mata masu kyau ake samun sa,Wani Riga da Sikat na saka cikin kwancen kayan ya'yan kawayen Da mama ke bani ne wuyan zamemin yake haka ma Sikat din yayi min yawa sai da na saka Tsumma na Taresa ajikina Hijabi ne kadai Sabo Shima Anty Mahma ce ta dinkamin domin jiya gidanta na wuni na tayata soyan Nama da aikin cinci Sai Dare ita da mijinta suka maidoni gida ita ta na da kyauta in nayi mata wahala tana min alheri takalmin kafata na Roba ne shima din Na jamal ne da ya daina amfani da shi na Dauka Da farko Mama bata so aje dani Sallar idi ba,Sai Baba yace dani za'a tafi Ya Ishaq ya dawo agida yayi azuminsa Shi na lura kamar baya ma san kallo na shiyasa ban cika giftawa ta gabansa ba. Lokacin da na fito Kofar gida Baba ya ganni sai da yaji kwallah ta cikamai ido,Ya kalli Badariya ta kure adaka ita da Mama,Jamal da Ya ishaq sun ci Fararan Shaddodi sai Faman sheke suke ni kuma bazar bazar kamar mahaukaciya wata yar aikin ma tafini kyan gani ni kuwa bakina kamar zai Tsage Saboda murna zan fita masallaci naga jama'a Tun kafin Baba yayi mgana Mama ta rigasa da fadin"Ke Fa'iza meyasa kika saka wadanan kayan..? Ina naki irin na Badariya..? Sai na kasa mgana Saboda ni dai bansan da wani kaya ba,ba'a bani ba ganin Baba ya saussauto yana kallonta yasa ta kara karya murya tana Fadim"Bansan meke damun Yarinyar nan  ba Abban Ishaq ko da yaushe bata da aiki sai saka Tsumman kaya nama ce ta hada su in zaka Karofi ka tafi da su arabama mabukata" Ban yi mamakin kalaman Mama ba Domin tun zuwana gidan ba Dadewa,Ta daina Fada da Baba akaina sai ta koma aiki da Kissa shima shawaran wata kanwartace daga Yamai hure ita tace mata in tana so taci Ribar Rayuwa to ta daina tada Hankali ta yi amfani da kiss,kuma Tabbas kissanta tana Tasiri wajen Baba don nan take ya kalleni kafin yace"Haba Fa'iza ya zaki saka wadanan kaya..? Baki ga sauran yan'uwanki ba ne.?maza je ki sauya kaya mu tafi kada mu makara'" Da Sauri Mama tace"Zamu bata Lokaci Alhaji muje in mun dawo sai ta sauya" Sanin Halinsa na rashin bincike kan al'umura yasa tace haka,Haka muka tafi su kamar zara cikin wata ni kuma kamar yar aikin su Shikenan ko da muka Dawo Baba yayi baki yana falon waje har Dare bai kara bi ta kaina ba,Sai da Washegarin Sallah da kwana Biyu mukaje Karofi ranar dai Mama ta bani Sabon kaya na saka ta kuma ja kunnena in taji wata mgana sai na Raina kaina ni ko araina nace wazan gayamawa.?bata san ina da zurfin ciki ba ba tun yau ba,bakomai ake jinsa bakina ba. Duk da Sabon kayane ammh da na sanya kamar wata Dussa komai ba Tsari ni kaina nasan ba kyakyawa bace ban mallaki komai na mata masu sa'a da gata ba,Kusan daman Hausawa kan ce in kana da kyau ka kara da wanka to ni bani da kyau din sannan ban iya wankan ba ballatana na kara dashi,Wani Lokacin sai Dare nake samun Damar yin wankan Tunda Dakin da nake ciki akwai karamin Tiolet to iya wankan ne ko shi ba don kyau nake yi ba Komai bazar bazar ne bansan iyakarsa ba. Da mukaje karofi na hadu da su Ya Asiya har sai da sukace har baki na kara na rame sun yi tambayan Duniyan nan kan wani irin rayuwa nake yi agidan Baban katsina naki ce musu komai sai dai in kallesu ina mirmishi naji dadin ganinsu haka barin ma Hafsatu da ta zama kamar ba ita ba ta kara wayau da girma. Ina jin su a tsakaninsu suna tattauna yadda Rayuwa ta jefa su a inda suke ni dai bana ce musu komai nadai san na Tambayesu tamadina suka fadamin tana Lafiya Yaya mariya na zuwa Dubata ita da Goggon Karofi sukace In Baba ya barni gobe sai muje na ganta. Ganin Goggon Korofi yasa Mama batayi mgana ba,Baba kuma ya amince washegari chan muka wuni sai yammah muka dawo ita kanta Tamadina ta na cikin wahala gida cike da yara,wahalar tayi mata yawa sai dai ba yadda zatayi ne kwanan mu biyu muka koma Katsina,Na koma da Tausayin Hajiyar Karofi ganin jikinta duk ya kara rikicewa yanzu ma dayan barin shima ya Daina aiki Goggon Karofi da ya'yanta suna matukar kokari kan Hajiya. Haka rayuwata ta cigaba da tafiya a gidan Baban katsina duk da irin azaban da nike sha achan ban taba jin na gaza ba sai ma nake ganin Sun yi min komai tunda zan ci na sha na kuma samu wajen barci Baba na jin Takaicin rashin Karatu na ko da yaushe naje gaishe shi da Safe sai ya kalleni yace min"Fa'iza kin k'i makaranta ko..? Baki san ilimin zamani ginshiki ne ga rayuwar ya'mace ba..? Ni kuma bana iya mgana sai dai na Dukar da kaina cikin Tausasawarsa yake cigaba da Fadin"Da kin Daure Fa'iza ai kina jin mgana zaki gane komai sannan zan yi ma malaman ku bayani kamar yadda nayi ma malamanki na islamiya bayanin Laluran ki" Ina Dagowa muka Hada ido da Mama ta Sakar min harara sai jikina ya fara rawa cikin yanayin mgana ta nace"Baba shi na addinin ba Ilimi ba ne..? Sannan shi ba Ginshiki ba ne ga rayuwar mu ba..? Baba ya jinjina mganata kafin yace"Ginshiki ne Fa'iza babban ginshiki ba kuwa..Sai dai ka hada duka fufukan guda biyu sai ka samu na zaman duniya da Lahira" Alokacin sai nace ma Baba"Baba ka barni haka..na islamiyan kadai ya isheni" Zai matsamin sai Mama ta taresa tana nuna mai Tunda ban so to ya kyaleni,Shi kuma bai da Zafi sai ya Rabu dani ammh ko da yaushe kalamansa akaina na alheri ne har ya bar duniya ko kallona yayi sai yace"Fa'iza Allah yayi miki albarka In sha Allahi bazaki Taggyara ba..Ina ji ajikina kina da wata baiwar da Sanadinta zaki Daukaka watarana" In naji haka sai nayi Dariya araina Domin bana hango ma kaina hakan Na amince Baban Katsina ya karbo ni Hannun Goggo karofi ne domin ya inganta Rayuwa ta,sai dai bashi da Mafita ne Mama ta fi karfinsa ammh har yau bazan manta kokarinsa akaina ba. Shi ya fadama malaman islamiyan da nake zuwa yanayina suke bani kyakyawan horo ko an gama karatu gabadaya sai an kara min bita ni kadai,Bani da wata kawa shiyasa ni kadai nake zama iyakata da kowa Mirmishi ko Sannu nasan ana mgamata ammh da yake bana ma ji Sosai ban cika Damuwa da su ba. A farkon zuwa na gidan Mama cikin kasuwar katsina take zuwa siyayyarta ammh sai Kawarta Hajiya Barira irin masu son kudin nan ne ita ta bata shawaran ta rika zuwa kano kwantin kwari tana saro kaya alokacin Mama sai tace"Kai Barira ya yi nisa ni kinsan ban san wahala" Hajiya barira ta rika nuna mata yanayin komai tare da fadin nachan sun fi sauki sannan zata hadata da yan kasuwar chan tunda itama tana siyayya achan har sai da Maama ta amince bazan manta ba na zo kawo ma Hajiya Barira abinci na juya naji tana ce ma Mama"ko wannan bakar yarinyar kika tara sai kuje tare ta rika Daukan miki kaya" Mama ta kalleta kafin tace"Ko Hajiya barira"? Tace to zauna Daman meye amfanin irin su in ba aikin wahala ba. Da wannan shawaran Mama ta zauna tana fadama Baba ya amince tunda shi ba mutum ne mai Takura ga iyalansa ba.kuma da tace dani zata bai yi gaddama ba domin nuna mai tayi ina kokari zata nuna min komai Domin tana Tunanin nan gaba ko ban yi karatu ba zan yi kasuwanci to ai Daman haka take fadamai ko na wahalan da nake yi ne,Girki ma Baba yace nayi kankanta Mama tayi Karaf tace gwara na koya Saboda gaba gidan wani zani Daganan Baba bai kara mgana ba. Daman tun anan ni nake kaimata Dinki chan batagwara kusa da gidan Anty binta,in ba'a gama ba sai na zauna an gama Wani Lokaci anan nake wuni buhu ne shake da kaya zam Dauko akai zuwa bakin Titi na samu Daidaita sannan in na Dawo na Hau ware ma masu kayan nasu,wad'anda za'a tafi da su yamai kuma duk ni ke shirya su Mama na gefe tana lissafin komai ban isa nace nagaji ba. Ranar da muka fara zuwa kano sai da na raina kaina Wuni guda acikin kasuwa kuma bata Dauki dan dako ba ni ke daukan mata kaya akai kamar mahaukaciya ga yunwa ga kishi Takalmi a Hannu hijabi a hannu Wlh ko abinci bata siyamin ba Da muka Dawo sai da nayi rashin Lafiya Saboda na Jigata matuka alokacin Mama fada ta Dinga min akan na fara zama mai son jiki to in zam mike tun wuri gwara na mike Bani da wani amfani in ba Bauta ba. Ni ba kyau ba,Ba ilimi ba,Ba ji ba,ba komai na inganci rayuwa ba,bai kamata na rika nuna gazawata ba tabbas gaskiya ta fada ba ni da wani gata a Duniya Bautar dai da ta Fada shine ya fi dacewa da mata marasa galihu ire irena zuwa Lokacin da na shafe shekaru Shidda Cif a wajen Baban katsina bazan iya fadin irin bautar da nayi ba abu daya na sani ni Fa'iza ban sauya ba Sai dai na kara girma ammh ba Domin na sauya Daga yadda nake ba Ina nan a  mai raunannan ji,Mara gata baka Mummuna mara sa'an rayuwa in ji ya Ishaq in ya ganni yakan ce Bai taba ganin mace mara sa'a ba irina komai Total zero ne a bangarena ba wani abun so ko sha'awa tare dani nima nasan haka ko badariya dake tasowa mai kyau ce sannan yar gayu kuma yar gata ni kuwa ban ma san me ake kira da gayun ba,Ni dai kawai nayi wanka na suturta jikina mganar gyaran jiki da Tsaftan jiki ban san shi ba Ba kuma wanda ya ke zaunar dani ya koyamin Ko kitso sai ni nagaji da kaina na tsefe shi kitso kuma sai in Mama taga dama zata bani kudi naje,ayi min. Zuwa Lokacin rayuwa ta Daga,Sosai ba kamar baya ba,kawayen Mama da suka sani tun abaya in suka gani sai like sai suka rika ce ma Mama Daman wannan mummunar dangin mijin naki na nan baki aurar da ita ba.? Mama kan basu amsa da cewa wazai kwashi Baki da muni da bebanci sannan uwa uba ba ilimi sai su yi ta Dariya suna cema Mama shikenan ta samu yar aiki to ai daman ba marabata da mai aiki maraban mu daya in da Daukoni akayi da sunan aiki za'a  rika biyana albashi,Shine kawai bambamcina da mai aiki acikin wannan gidan. Su Yaya Asiya duk sun yi aure ita da Yaya Mariya Ya Asiya acikin garin kano tayi aure wani malamin makaranta ne yana da mata da yara,Mai karamin karfi ita kuma Yaya Mariya A karofi tayi aurenta wani dan kasuwa ta aura mai rufin asiri. Kusan tare akayi Bikin su sai dai na Ya Asiya aka fara yi ,Duka naje bikin su ammh na Ya Asiya sai da Goggon Karofi ta kira Baba ta mai mgana domin tasan Halin Mama munje kano mun yi kwanaki Tunda Bikin tare da manyan ya'yan Hajiyar Dala babansu ya Hada, da Asiya harta duka kudin siyayyan kayan Daki tare ya bada ammh Mama ta zuga Hajiyar Dala akan su ya'yanta suna da gata Asiya kuma ayi mata na Daidai da ita Daga karshe ma ita taci kudin domin duka Dawaniyar Yaya Asiya Baban katsina yayi mata shi,Duk ciki ita kadai ta auri mai karamin karfi gidan falo daya ne sai Dakuma nata da na uwargidan Ba Shakka Baba yayi mata kokari sosai,Bangaran Yaya mariya Goggo da Mijinta sukayi komai ita gidanta ita kadai wannan bikin ne har Tamadina tazo,na Yaya Asiya ne bata je ba, in naga yadda Rayuwar Mahaifiyarmu ta koma sai na kara tabbatarwa lalle bamu da gata gatanmu ya fadi tun Lokacin Rasuwar Baba. Da ace Hajiyar Karofi na Da lafiyanta da kila abubuwa sun sauya ammh kuma tana kwance sai dai a kwantar a tayar bama wanda ya zata kai haka araye,ana zuwa gida ana Dubata har yau tana nan jiya iyau bata ko mgana Sai wanda ya kara kunnensa yake ji me take fadi in naje Hajiya ta rika kallona kenan na rike hannunta ina Fadin"Allah zai baki lafiya Hajiya" Sai dai kaga Hawaye na Bin gefen fuskarta Hajiya na bani Tausayi sosai shekaru kusan bakwai tana jinya tana kwance waje daya,Gidan su na karofi Babban Yaron Goggo Yaya Isa ya gyara da yayi aure yake zaune da matarsa kada abar gidan ba kowa ya mutu Baba ya matsa sai ya zauna da Farko Goggon Karofi bata so hakan ba gudun Rigiman zumunci. Ya Ishaq ya dawo gida ya gama karatu har ya samu aiki a Hukumar Tattara Haraji na kasa reshen jahar katsina,Shekaru uku da suka gabata,Sai dai baya zaman gidan in ya fita tun safe sai dare in kuma ya Dawo yana Dakinsa na fada muku tun a baya shi baima son ganina shiyasa bamu cika Haduwa ba, bana zama inda nasan zai ganni Saboda yafi kowa iya kallon wulakanci da kaskanci. Akwai watarana tana cikin cikin Ranakun da bazan manta da su ba acikin kaddarorina ba,Muna gabda Riskan kaddaran auren mu ni da Ya Ishaq al'amarin ya faru watarana ya kira Mama a waya yace yana son abincin Mutum hudu abokansa zasu zo su yi Dinner anan biki sukayi na wani abokin aikinsu. Nan da nan Mama ta tasoni na shiga Kirchen daman na fada muku a bangaran girki ni Fa'iza bani da makusa,Harta Mama yanzu in ba girki na ba bata iya cin abinci,Shi ko Baba kullum Mama yake godemawa yana ganin ita ta tallafamin na iya girken girken zamani zuwa kuma Lokacin na rage wasu walwahalun,Saboda Mama ta daina aike na ta samu yaron aike bangaran kasuwancinta kuma komai ta waya ne sai dai a saka mata a mota a aiko mata dashi,sannan ta dauki masu wanki da guga da kuma mai wanke wanke na koma gyaran gida da girki. Jin baki ya ishaq zai zo da su na Zage nayi musu girki mai rai da lafiya fatan pototo,da Hanta sai white rice da Miyar kifi,Sai nayi musu lemun Abarba Sai na hada musu da na Gwangwani kafin ya kariso Mama ta sani na je na shirya komai afalon Baba,na koma kitchen na Dora abincin dare na gida har bakin suka zo ni bansani ba Na gama girkin Dare doya da Miya Mama tace ayi naje nayi sallar mangariba ina zaune saman sallaya Jamal ya shigo Dakin da nake mai karamar katifa sai tarkace yace min Ya Ishaq na kirana afalon Baba sai da gabana ya fadi ban cire Hijabin jikina ba yamin yawa yana neman gadani na nufi Falon Baba Ina shiga da sallama gabadaya zaratan mazan dake falon suka Dago suna kallona ni ban iya kallon su ba,Saboda yadda jikina ke kyarma,ina ji Ya Ishaq ya dakamin Tsawa yana Fadin in kariso,Ni dai nasan nazo gabansa na durkusa kaina na kasa ina ji yace musu"To ga wacce tayi girkin nan da kuka matsu ku ganta" Ya fada cikin sigar Dariya da karfi yayi mganar yasa naji abunda yace gabadaya shuru sukayi kafin naji sun kaure da Dariya gabadayansu sai naji na muzanta matuka muzantan da ban taba yi ba suna ta mganganu wasu ina ji wasu kuma bana ji nadai ji sanda Ya Ishaq yace"Kai ka yi mata da Hausa No Turanci..Sannan Ears." Gabadaya suka gwalalo ido kafin ya kalleni yace"Yes..sai kunyi mgana da karfi zata jiku Bebiya ce" Na kusa dani ne ya matso saitin kunnena yana Fadin"What is your Name.? Aoh Sorry ya sunanki..? Na dago idanuwana sun cika da kwallah nace"Fa'iza" Cikin yanayin mganata gabadaya sai suka sheke Da Dariya har suna Tafawa da junansu Sai naji na kara raina kaina Nasan ni ba bebiyace ba ce ina dai da Raunin ji ammh ba Kurma bace ni Mutane ne suka kara Raunana jina da kushe da Tsangwaman su akaina,Ninasan inaji sai dai sai an yi mgana da karfi Sannan mganata tana  da Tsami Tsami Kuma ina Rabe ta kamar ina in ina kuma saboda Raunin ji na ina karantar bakin mutum in yana mgana Ko Tamadina ba Kurma bace tana mgana sai dai mganata tafi nata fita sannan na fita karfin ji. Ammh yadda suke kankanba Bebanci na abun bai kai haka ba. Ban taba jin guilt irin wanda naji ba  Ranar hawaye suna bin fuskata na mike zan fita Ya Ishaq ya dakamin tsawa yana fadan sun sallameni ne..?sai na Dawo kawai na Durkusa ina jin Ya Ishaq na fadin bai taba ganin baki da muni ba sai a wajena su ma abokan irin sa ne suna ta Dariya na kamar sun ga abun dariya ajikina ko acikin Abunda suke ma Dariya aciki akwai wanda na bama kaina ba Allah ya bani ba? abun da nake sakawa araina kenan ina jin wani irin abu a kasan raina. Sun dade suna kallona suna Dariya kafin Ya Ishaq yace na kauce daga gabansa na mike idona ya rufe bana ko gani,bansani ba na ture Teburin dake gaban su jug din lemu ya fado ya zube Lemun ya fallatsa a jikin abokan nasa dashi kanshi har ga Allah ban lura ba,ba karfi ji ne dani ba shiyasa ban ji karar faduwar wani abu ba,ba ma haka ba yanayin da nake ciki gabadaya ji na sa ganina ne suka Dauke a lokaci d'aya. Na dai san kafata ta bigi wani abu ammh yanayin da nake ciki bai sa na Tsaya Dubawa ba. Sai ji kawai nayi an dawo dani baya an yarfar dani akasa ya Ishaq ya Daga Hannu ya wankeni da mari acikin kalmominsa na tsinci kalmar"Banza Jaka,Mummuna useless har na isa na wulakanta abokansa ko akwai sa,a na acikin su ne..? Ina dafe da kuncina na bisu da Kallo ya fadi gaskiya ba sa'a na acikin su kamar yadda yake kyakyawan gaye haka suke suma,jikina na rawa na fara bashi Hakuri sai yace sai na juya na basu hakuri haka na Durkushe ina basu Hakuri sai da sukace sun hakura ya bi ni da Hambari ina Rarrafe na bar Falon ranar kwana nayi ina kuka har na fara neman nayi Sabo sai na zauna nace meyasa Allah bai yo ni mai kyau kamar kowa ba..? Ko dai da gasken ne bani da Sa'a..? Washegari Da Mama taji Labari Allah ya kara tayi har da fadin da ya fada mata Tun jiya sai ta karamin da Duka. Ina Falon ina goge goge ne alokacin naji sanda Jamal yace"Kai ma Bro meyasa ka kirata cikin abokan ka.? Sai da yayi tsaki mai karfi kafin yace"Su suka matsa sai sun ga wacce tayi abincin" Daganan ban ji meya ke fad'i daga karshe ba,Saboda ya Rage murya Ranar ina aiki ina kuka abaya bana Damuwa in an kusheni ammh yanzu sai naji kamar da gaske ne ni Fa'iza bani da Sa'a Ashe abunda Ya Ishaq bai sani ba Matarsa ya Tozarta,Agaban abokansa Domin ko sati ba'ayi ba Baba ya tafi Karofi Sakamakon kiran da Goggo tayi mai kan cewa jikin Hajiyar ya tashi Abun mamaki tana ta kiran sunan sa shi da Mama da ya Ishaq suka tafi suna chan ne nima ina gida Hankalina nakan Hajiya ban san me ya faru ba, ni dai nasan sun Dawo gidan cikin Hargitsi da Rashin kwanciyar Hankali mama sai kuka take yi tana Fadin bamai hada mata zuru'a da Dangin munana da kurame. Washegari fada ita da Baba har Falo alokacin naji Baba yace"ko bayan Ransa sai auran Fa'iza da Ishaq ya kulli sai dai ta mutu" Dayake da karfi yayi mganar naji sa ni kaina sai da na gigice ana haka sai ga Ya jamal yazo yana fadin Ya Ishaq ya kwashe kayansa ya bar gida Mama ta fadi kasa Hannunta akai tana kururuwam ta shiga uku ta Lalace Haka Baba ya tsallake ya barta ban bari kowa ya ganni ba na koma Daki ina rawan jiki mai nake ji,Wai ni Ya Ishaq zai aura.? Tirkashi ni kaina na hango tashin Hankali acikin lamarin ranar har Anty Binta tazo ita da Anty Mahma da kawayen Mama na kusa,sai mganganu suke ni,ni ina Daki baji nake yi sosai ba, ranar ko girkin ban iya yi ba kuma ba wanda ya nemeni. Nima Badariya ta shigo take fadamin Wai Hajiyar Karofi tace a hada aurena da Ya Ishaq,ance Dakyar ma aka gane me take nufi Saboda Harshenta ya karye. Ba Ya Ishaq kadai Hajiyar Karofi ta cuta ba  wlh har dani ina ni ina Ya Ishaq ai tazaran ma mai yawa ne.ranar kafin Baba ya Dawo Mama da su Anty Binta suka kirani Falo suka min Fata fata zagi da gori ba wanda ba su yi min ba har da gorin mu dangin maciya Amana ne to wanda ma naji kenan wanda kuma ban ji bansa me suka fada ba,Dayake da karfi suke mganar Anty Binta ko har tana Hadamin da dunguri Mama taci kuka har ta godema Allah idanuwanta sun kala sun yi jajir Ita damuwarta Ishaq ba bawanda yasan inda ya tafi ya kuma kashe duka wayoyinsa Mama taja kunnina da cewa in Baba ya Kirani ya tambaaye ni in na amsa mganar auran nan sai na gwammace rashin amsawata Domin bata fatan Had'a zuru'a dani Har gaban Abada. *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *GADALIN MATA AKWAI*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*. *TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *NATION WIDE DELIVERY*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* 🙏. *Littafin KANA NAKA paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.* *Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223* *Janafty* *KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Book 1* *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *GADALIN MATA AKWAI*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*. *TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *NATION WIDE DELIVERY*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* 🙏. *Assalamualaikum! Phydoors* *collection (home of all you need)tazo muku da kayan gyaran girki masu inganci da Gina jiki da faranta Ran Mai gida harda Ma yaranmu domin inganta girkin uwargida

Chapter 5 of 25