Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Asiya tace"Ko kefa Fa'i ki rika shiga Mutane don.Allah..Yafi ki yi ta zama agida ke kad'ai kamar mayya..Mutane Rahma ne sannan Makoci yafi dan'uwaka tunda sai wani abu ya sameka kafin wani naka yazo ya kawo maka Dauki makocinka yazo ya taimake ka" Cike da gansuwa da mganarta nace"Hakane" Domin ya faru akaran kaina kuma nagani,Tare muka kwana agado daya yaran mu na tsakiyar mu mun dad'e bamu yi barci ba Duk Mganar Yaya Asiya na Hakuri ne da kuma hakuri da yadda zamantakewar aure tazo min kafin mu kwanta sai da tace min"Fa'iza gaskiya ya kamata ki fara wata sana'ar ai zama haka bazai haifar miki da komai ba sai takaici Daman mun yi mgana da Mariya zamu tarfa miki jari tunda kina sha'awar Korin ko shi zaki jaraba ki gani ko za'a dace..? Nayi shuru ban ce mata komai ba sai ta kyaleni sai da Safe bayan mun karya tayi shirin tafiya ta karamin mganar cikin yanayin mganata nace"Yaya Asiya bazai bar ni na rika zuwa kasuwa ba" Tayi shuru kafin chan tace"Kuma da wannan don wannan..To shikenan  dai zamu tattauna muga wata sana'ar zaki fara wacce bazata kawo miki matsala da mijin ki ba" Da haka muka rabu da ita har waje na rakata,ina ta mata godiya tazo min da caryfish da yawa,tace na rika miya da shi sannan da Bushasshan kifin da tazo da shi zata kaima Tamadina da su Goggo ta D'ibarmin na karba ina jin hawaye suna kawomin cikin Idanuwana kalli yadda yan'uwana suka zame min garkuwa ammh ahaka su Mama ke min kallo kaskastttaciya mara gata. Na bata sakon gaisuwa wajen Tamadina tace min insha Allahu zata sanar da ita Sannan nace agaida su Goggo da kowa da kowa ammh na kasa cewa ta gaida min Yaya mariya ina Tsanaanin jin kunyarta sannan ina Tunanin ta Rufamin asiri bata bayyana ma kowa abunda ya faru ba. Sai naji ta burgeni ta zama yar'uwa mai Rufa ma yar'uwata asiri. **** Sai Ranar Litini da yammah Jamal ya Dawo min da su Amir,sun zo da kaya niki niki da jakunkuna mai Dauke da Hoton Zainab da Ya ishaq da kyakyawan D'an su kamar balarabe sannan kaladan ma ta Hoton yaron Dauke da sunan Lawal Ishaq kabir karofi(FARHAN) yaci kayan alfarma kamar asace sa a gudu in ka gansa kamar d'an larabawa,Dole yayi kyau daga uwarsa har ubansa masu kyau ne masha Allah. Sun taho da kayan fulawa da yawa da Soyayyan Naman kaza,Samosa,Meatpie,Sprilroll,Cake,Da sauran sai lemukan gwangwani jaka shake da kaya Sannan sun taho da Sabbin kaya yan kanti a bakin Amir naji yace Antyn su ta basu sabbin kaya. Su Anum yan Abuja sai tsallen murna take tana ta bani Labarin abunda ya gudana achan Jamal na zaune kan kujera mai zaman mutum d'aya yana Latsa wayarsa shi haka yake bai cika Hayaniya ba cikin Daga murya ya Dago yana fadin"Anun shut up.." Da Sauri tayi tsit har tana saka Hannunta a baki ta kama tasan Halinsa baya musu da wasa Musty ya kwace motar wasan da ke Hannun Anum,Domin har da tarkacen kayan wasa suka shigo da su. Ta mika hannu itama ta kwace sai ya kwabe fuska zai saki kuka da Sauri ta dora Hannu saman bakinta tana fadin"Shiii up.." Dagani Har Jamal sai da muka yi Dariya Amir kuma mai hankali kayan su da suka watsar a Tsakar Dakin yake tattara zuwa Dakinsu ina kaunar yaron har acikin raina Saboda akwai Boyayyen Dabi'un da ya Dauko nawa. Jamal na je na kawo ma ruwa ya Dago yana fadin"matar yaya anya ruwan nan zai shiga kuwa..? Ba waku ne..? Nayi dariya daman nasan Halinsa kafin nace"Tuwon Masara nake yi miyar Kubewa D'anya zaka ci..? Da Sauri ya mike yana fadin"Tuwo fa..Am ok." Na wuce sai da Safe..My childreen Good Night' Anum da Musty suka bisa da Bye bye uncle ni kuma ina yar Dariya nace ya gaida su mama yace zasu ji,nayi mamakin yadda nake yawan ganinsa a gida lokaci bayan Lokaci,sai washegari da ya shigo anguwan ya kara shigowa na tambayesa ashe yana garin.?sai yace min ya koma makaranta wlh yajin aiki aka shiga shiyasa ya Dawo shekaran jiya. Nasha Labarai wajen yara musamman ma Anum Amir bai da surutu Musty kuma mganar ba wani kwari tayi ba rabi gwaranci ne,Anum sai fadamin take Umma jaririn Anty mai kyau ne muma yaushe zaki haifo mana Jariri mai kyau..? Sai na kalleta nayi dariya naja kumatunta kafin nace"In sha Allahu zan haifo muku jariri mai kyau Anum" Ta Dameni sai faman tambayana takr yaushe da nagaji nace mata watarana sai ta fara murna na kalleta ina jinjina yarinta yara dai basu da matsalan komai a duniya. Nasan ko kayan da Anum suka Dawo dashi Darajan su Anum naci ba Domin haka ba nasan ko abunda ba'a so ba wanda zai kawomin Naci kayan fulawan da suka zo da shi kazan dai su na saka ma fridge da safe ina saka musu cikin kwandon abimcinsu in zasu tafi makaranta da Lemuka daman kwanakin baya ruwa nake saka musu pure water da ya kare sai dai na d'ura musu na Famfo a Gorinan na su tunda bana da shi ban kuma da hanyar samu. Ashe gayya ne guda akayi aka tafi Abuja Badariya taje ita da Halisa Anty Mahma da Anty Binta sai Hajiyar Dala da manyan ya'yanta guda Biyu,duk sai da Badariyan tazo ta ke fadamin. Ranar da tazo gidana ta kwana Tunda basa zuwa makaranta suna yajin aiki kwananta ta uku mama ta matsa mata sai da ta koma gida ita kuma tana som zama saboda tana koyon girke girke a wajena Ammh Mama bata kaunar wani nata ya rabeni ballatana in tasan nata d'in yana so na ko Fad'an da take yi da Goggo saboda ni ne da ace Goggo bata kaunar mu kamar Yadda Hajiyar Dala ba ruwan ta damu da zaman Lafiya za su yi ammh Saboda ni ta yanke alaqa da Goggo sai wanda ya zama Dolen Dolen an had'a Dangi bata da yadda zatayi. Ana haka ba Dad'ewa Yara suka yi Hutun makaranta suna gida sai na koma koyar da su na addnini a gida na Bokon kuma ban yi musu wasa ba nakan matsa musu su Dauko Littafansu Amir dake gaba dasu ya Rika Duba musu,nasan zafin rashin Ilimin boko tunda har da shi yasa na zama Bora agidan mijina tunda ko nasan zafin kaskasci bazan so wani daga cikin ya'yana ya Dan'dana abunda nayi shekaru ina Fuskarta ba. Hutun yaran a gida ya taimakamin sosai na rage damuwa sannan walwalata ta Dawo har na fara maida jikina,sun gama cinye Hutun su suka koma makaranta a satin aka fara musu mganar kudin makaranta da Sabbin Littafai Anun kuma jakar makarantar ta mutu tana bukatar Chanji,sannan sabon Registration ne zata shiga primary 1 da suka fad'amin nace su bari in Uncle Jamal yazo su fad'amai Saboda ni bani da mafita. Shi kuma kamar yasan ana jiransa sai ya Dauke kafa agidan ni dai fatana da addu'a ta kada su koresu daga makarantar karatun su ya tsaya,Ranar jumma'a sukace duk wanda bai biya ba kada ya zo ina jin haka sai na sakama kaina gwarin gwiwa na Fahimci an kawo gabar da ni ce uwar ya'yana kuma nice Ubansu Ranar Monday nace su shirya tare zamu je makarantar suna ta Murna,na yi wanka na saka kaya na mai kyau da Hijabi na shirya Ahmad na kulle gida nabi Haruna muka je makarantar ban taba zuwa ba Ya Ishaq ke zuwa ko Jamal in wani abu ya taso. Yaran suka rakani har Office din mai makarantar Mace ce ina ta Fargaban ance da Turanci ake mgana ni kuma ban iya ba,Muna shiga Matar ta Dago fara kyakyawan gaske,na samu karfin gwiwa jin ta min mgana da Hausa ganina da su Amir yasa tace"Umman su ce ko..? Na gyada mata kai ina mirmishi sai tace na zauna su kuma ta kada su aji suka tafi suna lekena. Bayan mun gaisa cikin yanayin mganata nayi mata bayanin komai nace su yi hakuri babansu baya nan ne ammh in ya Dawo zai biya. Sai tace bakomai tasan ba su da matsala da yaranmu nan tace zasu yi ma Anum Rigistration su bata Uniform din Primary section sai su had'a cikin Bill din kudin makaranta nace ba Damuwa muka rabu cikin mutumci a raina nace ashe ba ko'ina ne ake mgana da Turanci ba in ko Hakane nima zan iya shiga ko'ina da yarena na Hausa kuma nayi mgana a Fahimceni. Haruna ya tafi bakin sana'arsa abun hawa na hau zuwa gida,Daman shi kudin da goggo ta bani da na wajen Yaya Isa na had'a na bashi na wata daya yanzu yana bin na wajen wata uku zuwa Hudu shuru Ya Ishaq bai basa kuma ko zuwansa na karshe bai tsaya ba ya tafi ma ban sani ba ballatana ma ya bani yace na basa ni fa na fara Tunanin tashi Tsaye kawai na nema ma kaina mafita na gama Fahimtar Sabon Iyalin da Ya Ishaq ya Had'a ya zabe su sama da ni da ya'yana ko da yake ai ni ya Dade da Zabar Zainab a kaina ya'yansa ne na Fara Gane ya fara mantawa da matsayin su a wajensu. Sai a satin da naje makarantar ta su Jamal yazo gidan Anum sarkin karad'i ita ta fadamai an ce su biya kudin makaranta,To kwana biyu tsakani suka zo Da shedar an biya komai Anun an bata sabbin kayan makaranta da Text books,ranar kuma da Daddare shi Jamal din ya kawo musu littafan Rubutu da Sabbin Safuna da takalma ganin ba Jaka sai nake gayamai ta Anum ta lalace yace duka kudin da Ya Ishaq ya Turomai sun kare ammh zai yi ma mama mgana kamar nace ya bar shi ba sai yayi mata ba sai na kasa mai mgana. Ni nasan za'a rina aiko da yaje yayi mata mgana fad'a ta kama yi tana fadin ina fakewa da ya'ya ina mai da D'anta bawa,ba domin Mama tasan ba'a sauya ma Tuwo suna ba da Tuni ta Hana Yaya Ishaq Dawainiyar ya'yansa to tasan dai ya'ya nasa ne sannan yana son su bazai iya kyalesu ba duk da Yaya Ishaq bashi da Kirki a wajena bazan yi mai karyan baya kula da Laluran ya'yansa ba wani Lokacin har da Muguntan Mama aciki gani take ina Fakewa da Guzuma ina Harbin karkasa. Jakar da kuma taki bada kud'i a siyan ma Anum kenan Jamal yazo yana fadin da ya ke shi Santsi daya ne baya munafunci kaf abunda Mama ta fad'a ya fadamin sannan ya kara da cewa bai da kudi da ya siya ma Anum din Sabuwar jaka nace kada ya Damu ai na Gode da kokarinsa. Dakyar na Lallashi Anum ta rika tafiya da Tsohuwar jakarta ni kaina naga duk ta mutu ta yayyage ammh ya na iya..?Tunda ba ni da wata mafitan sai dai ina jiran mafitan da na Roki Allah ya samar min kuma ina ji ajikina ya amsa duka addu'o'i na.    Yau ta kama alhamis ne tun bayan tafiyar yara makaranta da suka maido wuta na fara guga sallar azahar kadai ya tadani sai rigiman Ahmad na shiga Kitchen na Damamai kuni na basa yasha sai ya fara harkan gabansa yana ta wasa da yar motan wasan yara na Mutsy da suka taho da shi Daga Abuja. Hankalina ya tafi kan gugan da nake yi ban ji sallama ba,Kuma ko ma anyi in ba an matso kusa dani ba ne bana jin sallamr sai da naji an tabani na Juyo da Sauri har na Tsorata sai naga Tamadina da abokiyar zamanta Maman Isuhu suke kiranta. Ai basan Lokacin da na watsar da gugan gabana ba na Daka Tsalle na Rumgume Tamadina ina murnar ganinta Cikin yanayin mganarta na Rikeni tana fadin"Faaa...Izzzaa..' Sakin ta nayi na koma ina Dariya ina musu barka da zuwa,Ahmad ne motarsa ta makale jikin kujera sai ya fara kuka,Tamadina tayi Saurin zuwa ta Dauke sa,Ni kuma na kashe Soket din gugan da nake yi jikina na rawa Farinciki kamar ya sumar dani na nufi kitchen na Dauko musu ruwa na kawo musu ina gaishe su. Sun sha ruwan Tamadina kuma wanda ta rage ta bama Ahmad kamar ya ganeta ya ko lafe a jikinta shi da ya ke da kiwuya. Kafin ma na tambayesu daga Ina Mamar Isuhu ta ke shaidamin Matar yaron Uwargidan su ce ta haihu aiki akayi mata tana Asibitin katsina shine suka zo Dubata Tamadina tace su Biyo su yi sallah kafin su tafi. Aiko naji Dadi,Dakina na kai su suka shiga bayi domin alwala ni kuma na fada Kitchen na fara kokarin sama musu abinci Jallop din Shinkafa na Dafa musu da bushasshan kifin da Yaya Asiya ta kawomin ina ta lallabawa Sauran sa kenan nayi takaicin rashin kudi ko Lemu ban da shi ballatana na siya musu kuma bani da kayan had'a Lemu ko daya ballatana na Had'a musu. Har Daki na kai musu na iske sun Idar da Salla,Ahmad na kan jikim Tamadina yana ta wasan sa ta kalleni cikin mganarta tace"Suuuu...Saurrraaan...yarrran fa..? Nace"Suna makaranta Tamadina sai yammah zasu dawo" Ta gyada min kai Allah Sarki Uwa,uwa ce ko da akan bola take kwana,ita fa uwa ta gwammace tayi ma Abun da ta haifa ko da bazai rama mata wannan alherin ba. Gyad'a Soyayyiya da Masara gashashiya ta kawo ma su Amir da gurjiya dafaffiya Maman Isuhu na Dariya tace abakin asibiti ta siya Masaran nan da gurjiya. Ta turamin gabana tace na bama Yara sai hawaye suka kawomin cikin Idona na fara godiya Ahmad dai sai bare mai gurjiya take yi tana bashi yana Mamula da Hakoran sa guda Hudu Biyu a gaba biyu a kasa da suka fitomai. Falo na koma har sai da suka gama cin abimcin,Sannan na koma naga suna shirin tafiya sai naji kamar kar su tafi ammh ba Dama Hijabi na Dauka muka fito ina Tunanin me nake da shi da zan basu..? Na duba gabas da yammah ba ni da komai ballatana na basu haka muka tafi waje da su,ni nace su zo na kai su makota na da muke mutumci su gaisa. Sa'adatu kadai muka samu Habiba bata nan taje gidan su daman yar katsina ce acikin gari. Sa'adatu tana ganin Tamadina tace min"ga maman ku ko..? Na gyada mata kai ta gaishe su cikin Ladabi daga jin yanayin mganar Tamadina basai ta nemi karin bayani ba tasan inda na gado Lalurata kenan. Ita ta fitar dani kunya ta basu siga da yawa cikin wacce take saidawa bani da bakin da zan gode ma Sa'adatun tamin komai shiyasa mata mu daina kuskure domin mazajen mu sun hanamu huld'a da makotanmu sai mu Biye musu mu sani Annabi ma yayi Mgamar Hakkin makota sannan mutane Rahma ne duk yadda mutum yake shiga Jama'a yana da Bambamci da wanda ba ya shiga mutane sosai. Har bakin Titi na rakasu suka samu Motar Dutsemah,Kunya naji da zasu tafi ban basu ko kudi ba Ahmad har da rigiman Tafiyar Tamadina nace Yaro yasan kakarsa. Sai da suka wuce sannan na koma gida Ranar cikin Annushuwa na yini kamar an mun bushara da gidan Aljanmah sai dai ina ta kallon Tamadina ta kara ramewa nima tana ta kallona duk sanda na kalleta sai mun Had'a ido,Ina Kaunar Uwata a yadda take domin bani da makwafinta in kuma na rasata har Abada nayi maraici gaba da baya. Haka kurum in na Tuna da kallon sai naji jikina yayi sanyi a raina nace kodai kallon karshe take yi mim..? Tuna haka yasa sai da gabana ya amsa da Sauri nace a fili"A'a ba haka ba ne Insha Allahu ba yanzu zaki barmu ba Tamadina." Da su Amir suka Dawo na basu tsaraban Tamadina suna ta murna sukace min waya siya musu ina Mirmishi nace"Kakar ku" Sai Anum tace"Mama..? Sai na kallesu nace'A'a mahaifiyata..Sunan ta Tamadina" Anum tace"Umma bamu santa ba meyasa ba ma zuwa wajenta..? Sai na kasa mgana nayi gefe da kaina araina ina auna yadda Ya Ishaq ya Rusamin rayuwata gabad'aya ace ya'yana ma basu san wacce ta Haifeni ba ? sai kirjina ya karayin nauyi da Dubara na share hawayena na Lallab'e su da cewa zan kaisu su ganta Amir dai zai iya ganeta shima ba lalle ba. A fili na furta"Na ga ta kaina ni Fa'iza wannan wata irin rayuwa nake yi haka..? *FA'IZA NA GODIYA TACE KU YI HAKURI KOWANI TSANANI SAUKI NA WAJEN ALLAH TACE MADALLA DA KU MADALLAH DA MASOYAN JANAFTY* *Janafty* *KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866 Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN 😳 Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700👌👌 MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866 IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE 😀           *🅿️14* Tsakanin zuwan Tamadina da saukan su Ya ishaq da amaryan sa Zainab garin katsina kwana biyu ne,Ni bani da labarin suna tafe,Sai da yammah da suka iso gidan nagan su,Ashe wai Mama aka kawo ma Farhan ta gani shine suka zo gayya guda bayan kanwarta zuzu har da wata yarinya mai yi mata reno,sai Iyayanta Guda biyu,ban taba ganin inda iyaye ke rako ya'yansu ganin Dangin miji ba sai akan Amaryan Yaya ishaq na fara gani sai abun bai wani bani mamaki ba ya'yan yan boko ne da suka mallaki dukkan wani kawan duniya. Shashen sa suka yada Zango dukkansu ni dai iyakata nayi D'awaniya da su kamar yadda na saba na abinci da shimfidar fuska wacce Hausawa sukace ta fi na tabarma. Har shashen nasa na shiga suna ciki ita da kanwarta mai renon ne ke falo tana Fama da Farhan Yaya Ishaq kuma suna shigowa ya fice bansan ina zashi ba daga gani dai fitace mai muhimmanci. Hannun mai renon sa na karb'esa ina kallon yaron yayi wani girma kamar dan wata biyar,Tsarki ya tabbata ga Allah nace acikin raina,Saboda ashe a Hoto ban ga komai na kyau da zatin yaron ba sai da na gansa a hannuna Jajir da shi kamar ka taba jininsa ya fito yafi kama da Yaya Ishaq sai dai Hancinsa irin na mamansa ne har da Idanuwan ma kuka yake ta yi yarinyar ta kasa lallashinsa na kalleta Lokaci daya ina fadin"me yasa ya ke kuka..? Kamar zatayi kuka tace"Ni ma ban sani ba kuma ba yunwa yake ji ba yanzu na basa madaran sa" Rikesa nayi a jikina ina kara Tattaba jikinsa naji zafi kad'an alamun yana Tare da zazzabi sai na kalleta lokaci daya ina fadin"Kamar da zazzabi a jikinsa bari nayi mai wanka sai a bashi mgani" Kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa ni kuma na fice da shi zuciya ta daya,Daman su Amir na makaranta basu dawo ba,kitchen na shiga na saka Ruwan zafi bayan na goyasa luf kuwa yayi shuru ruwan na zafi na juye a baho na shiga Dakina nayi mai wanka tas da ruwa masu dimi ina cikin yi mai wankan na fahimci Cibiyarsa ne ta dan kumbura ina da wani mgani da Goggo ta bani Tun Ahmad na karami da cibiyarsa ta fara kumbura ina fara shafamai ta koma ta daina ciwo kuma ta Daina kumburin,sai na Dauko daman ban cika banzarta da irin wadanan kayan ba tunda ina da yara na mulke mai Cibiyar da shi cikin kayan Ahmad da suka yi mai kad'an na saka mai riga da wando,na goyasa ram a bayana ba jimawa sai barci ya kwashe sa da shi a bayana na cigaba da Hidima ta Ahmad daman yayi barci ne yana tashi ya kafa rigiman sai na Sauke Farhan dake bayana na goyasa. Ina Dariya shima na Sunkucesa na Saba a kafad'ana ina fadin"Haba babban mutum ka girma ka bar ma kaninka bambon mana" Kuka ya fara min na fita da shi Falo na Zubomai abinci na zauna ina basa Shidda Saura sai ga yaran sun Dawo daga makaranta suna ganin goyo a baya suka fara tambayana Umma wa kika goya kamar ma Anum taji Labari. Ina mirmishi nace"Sabon jaririn Anty ne" Anum ta daka tsalle tana lekonsa ta bayana kafin tace"Umma waya zo da shi..? Sai nace"Tare da Daadan ku suka zo da Antyn ku" Anum ta fara tsalle tana oyoyo oyoyo Daada Musty na tayata Amir dai Dakin su ya shige ya Sauya kaya gudu ta kwaasa zuwa shashen baban nasu nace mata ya fita ta bari ta sauya kaya taci abinci in suka yi sallah sai ta shiga ta gaida Antyn nasu bata da yadda zatayi hakanan ta Hakura ni suka bari da kwashe takalma da jakunkunar su da suka watsar a tsakar Falon. Anum dakina ta Shige Saboda na maidata da ita da kayanta tare dani,ina shigowa na iske ta watso kayanta kan gado da karfi nace"Anum ba na hanaki watso kaya ba..? Cikin rigima tace"To umma ban ga wanda zan saka ba ne" Riga da sikat na Dauko mata na bata ina Fadin"Duk na goge fa kayan nan ammh ji yadda kika wargazasu Anum" Ganin ban ji dadi ba yasa tace"Kiyi hakuri Umma" Kanta na shafa ina fadin"Bakomai yar Umma muje aci abinnci" Musty kuma Amir ya cire mai kayan makarantar ya sakamai, na gida suka fito falo na zubo musu abinci Farar shinkafa da miya,Sa'adatu ta aiko min da Kayan Miya itama daga gidansu aka aiko mata dashi kamar babanta aikin gwari yake yi. Dukkansu waje daya na Hada musu kamar yadda na saba sun fara ci,Anum da Musty suka fara rigima kamar kullum nace su bari suka ki sai na kalle su ina fadin"Anum zan mai da ke cin abinci ke kad'ai tunda bakya jin mgana" Jin haka yasa Da sauri Amir yace"Umma ki yi hakuri Musty ke Tsokananrta ki barta mu rika ci tare" Sai na gyada kai ina fadin"Musty kana son Bulala ne..? Na fada ina nuna masa hannun alamun duka kafada ya makale dariya nayi kafin nace"To ka daina tsonakar Yaya Anum in baka son duka" Da sauri ya gyada min kai Lokaci daya yana fadin"To umma" Cikin Salom mganarsa ,cin abinci suka cigaba da yi a natse ni kuma Farhan dake baya na ne ya motsa sai na mike ina Jijjigasa Daidai da Bude kofar falo da Shigowar Yaya Ishaq bayansa Jamal ne da manyan Ledoji,Nasan har ga Allah bai kalleni ba,ballatana ma yasan wanda na Goya Sannu da zuwan ma da nayi mai ban ji ya amsa ba Jamal ne yake kokarin Sauke Lodijin hannunsa a falon da Sauri ya Juyo yana fadin"Jamal bani Lodojin Hannunka" Yafada daidai da yaran zasu tashi suna kiran Daada da karfi nace su koma su gama cin abincin su duk da ban kallesa ba nasan sai alokacin ya bini da kallo ni kuma sai na Dauke kaina ba domin ina jin Haushin sa ba sai domin nasan ba ni da wata Daraja a wajensa shiyasa nima na koyi kama kaina. Jin abunda nace ne yasa ya kalli yaran yana fadin"Ku gama cin abincin ok.? Atare suka gyada mai kai Jamal ya mika masa ledojin hannunsa ya shige Bangaransa sai da ya shige na Dawo da kallona wajen Jamal wanda ya zauna saman kujera su Amir na gaishesa ya amsa yana fadin"My Childreen how far" Amir ne ya amsa mai da We are fine Uncle"Dariya yayi yana fadin"Daddy na ya fi kowa gane karatu a makaranta ko Amir..? Anum ta tura baki tana fadin"Nifa Uncle" Kallonta yayi kafin yace"Mommy nama tana ganewa itama" Jin haka yasa ta washe baki Musty kuma ya tayata,Sai alokacin ya Dago muka gaisa,cikin yanayin mganata nace"Ya su Mama..?Daga ina haka da yammah nan..? Yana sauke ajiyar zuciya na gajiya yace"Wlh Dad din Anty Zainab muka kai Masauki  sannan muka je Restaurant  muka yi oder abinci muka Biya gidan Mama muka kai mata kinsan Mom din Anty Zainab din wajen Mama ta sauka" Na jinjina kai ban yi mgana ba ya cigaba da fadin"Shine duk najini a gajiye me kuka dafa ne..? Kai tsaye nace"Farar shinkafa da miya

Chapter 16 of 25