Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baki sam zan kara aure bane..? Yafada yana Tsareni da manyan Idanuwansa. Gabanna ya Fadi Ras! Sai na Daburce Da yanayin da yayi mganar,ba da karfi bane sai dai ai mganar auran nasa na Haddace ta akaina shiyasa nq karancin Bakinsa. Cikin Fusata yace"Wai bada ke nake mgana bane kikamin banza..? Da Sauri nace"Eh..Eh..Na sani..Mamakofar soro ta fadamin..Sannan sannan.." Daka min tsawa yayi yana Fadin"Sannan me..? Kinsan bana son wannan sanyin naki in muna mgana ko..? Mgana bata kai ta kawo ba kiyi ta uban Rabata kamar wani abun arziki zaki Fada.." Kokarim Boye Raunina nayi Cikin Dakewa nace"Anty Binta batagwara ta Fadamin wanchan satin da muka Hadu gidan Mama." Wata Uwar Harara ya jefa min kafin yace"Kin sani ammh ko Fatan Alheri bazaki min ba Fa"iza..? Kina bakinciki ne saboda zan kara aure..? Da Sauri nace"Ahah.Naga baka nan ne,Shiyasa.." Takaici ya kamasa kafin yace"Baki da waya ne..? Ko lambatace baki da ita..? Koda yake ke ai ba matar kiran jin Lafiyan miji bace za dai ki kira in wata Bukatarki ta taso miki." Ya karishe Fada yana kallona Cikin Doguwar Rigar Barcin dana sanya kadan ya Rage bai yi Dariya ba. Dariyan Takaichi wai zaki kwana da Miji ki saka wannan abu kamar kullib goro. Karamin Tsaki yaja kafin yace"Na zata kina Bakinciki ne nace kin so kanki Fa'iza Shekara Takwas nayi ina Zaune Dake ban kara aure ba..Tsakaninki ga Allah ban miki alfarma da Mutumci ba Fa"iza..? Fadamin da bakin ki na yi miki adalci ko ban yi miki ba..? Ya fada da karfi yadda Zan jisa jikina  na rawa nace"kaayi min..sosai kayi min adalci.." Naso na Daure ammh ina Raunina ya bada ni sai kuka hawaye sharr Tsayawa yayi yana kallon na kafin ya Tabe baki yace"Naji Dadi da kika Fahimci haka..Kada Goggon karofi  da yan'uwanki su tasaki suna Faman tambayanki kice musu ban yi miki adalci ba kiga yadda zamu kwashe.." Malama ki kuma cire min wannan bargon Dake jikin ki wlh matukar wajena zaki kwana na Haramta miki kara sakamin wadanan Rigunan ai ba Cinikaya zamu yi ba..Ke kinga ma sha ma Zamanki ana tabaki Ke mai cikin Haihuwa Zan D'aure nan da Wata D'aya ne kamar gobe ne.." Yafad'a Lokaci D'aya ya juya zai Fice Daga Dakin na Bisa da kallo ina D'igar kwallah duk da ba Duka mganarsa na ji ba ammh nasan yana kushe ni  ne kamar yadda ya saba. Har ya fita Daga Dakin ni kuma har na juya kawai naji dawowarsa da kara Kiran sunana da yayi da karfi. "FA'IZA..! Da Sauri na Juyo  Cikin muryata Data Fara sauyawa saboda kuka nace"Na'am..! Kallona ya tsaya yanayi lokaci d'aya yana rike da Kofar Cikin Mamaki na yace"Kuka..? Na Dake ki ne..? Da Sauri na Share hawayena ina Fadin"A"ah kamar wani abu ne ya Fadamim a ido na..!" Bai Damu ba Kafad'a ya Zakud'a kafin yace"Mama ta fada miki gidana na Abuja Zeey zata zauna..? Kai na gyada mai bai bani Damar mgana ba yacigaba da Fadin"Fa'iza kinga barin yaran nan suna bata gidan nan Duka duka yaushe muka tare acikinsa ammh kalli yadda suka maidasa..? Komai naki ba kula ba Lura..? Ko da yake ke kanki abar akula Dake ne bama ki kula da wani ba Anyway dai tunda kuka lalata gidan in ma mugunta ce ke zata ci..Sai da Safe.." Daga haka ya Sakar min kofa ya fice na Bisa da kallo hawayena  na kara cika Idanuwana ina jinsa ya Bude kofa ya shiga D'akin  yaransa ya Dade kafin naji ya Fito ya Tafi bangaransa. Kamar wacce aka Mangara kawai sai na fashe da kuka wiwi,Sai kuma nahau Rufe Bakina,lokaci D'aya da wayata Dake samam madubin dakin ta D'auki Karan neman agaji. Da Sauri na mike na nufi wayar kirar Kamfanin Itel karama Tunda Anum tataba Fasa min Sreen din Samsumg din da Ya Ishaq ya siya min bai kara siya min wata babbar wayar ba ya Had'ani da karama acewarsa ba amfanin ma Siyan min Shafa shafan tunda ba iyawa nayi ba, ta bakinsa Fa'iza ba turanci. Gabana sai da ya amsa ganin wacce ke Kirana Maman Naja ce Yaya ASIYA,Sunan d'iyarta ta fari ce wacce ta rasu Naja'atu ammh dayake sunan ya riga ya bita da Maman naja ake kiranta. *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA. SANNAN BASU DA BAURI MASU KIDIMARWA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *TUNTU'BI WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* 🙏. *Janafty* *KANA NAKA...* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Fatan alheri gareki SURAYYAH DAHIRU GWARAM,Madallah da kawar arziki irin ki da karfafa Gwiwarki,Labarin nan yazo ma masu karatu Ina miki fatan alheri a koda yaushe na gaida Uwar Dakin Sa'ada da Gudiyo,sannan na ce Madallah da Uwar Dakin Yabi*🥰             *🅿️02* Da sauri na share Hawayena nayi kokarin daidaita yanayina domin ni Fa'iza ko Uwar data Haife ni bana kaunar taga raunina ballatana yan'uwana  da kullum suke kallona abar Tausayi wacce batayi dacen Gidan aure ba acewar su. Saboda yanayin Raunin ji na, in aka kirani a waya a speaker nake saka ta wato amsa kuwwa yanzu din ma haka nayi na Daga kiran sannan na saka a speaker daidai Lokacin da naji muryan Ya Asiya na kiran sunana na amsa mata cikin dan D'aga murya. Dagachan bangaran Ya Asiya tace"Fa'iza Ashe Yaya  Ishaq zai kara aure bamu sani ba..? Fa'iza tayi wani mirmishin yak'e kafin tace"Eh Yaya Asiya zai kaara aure.." Ya Asiya tace"Shi ne baki Fadamin ba,  kuma baki fada ma Mariya ba ko..? Fa'iza tayi shuru batayi mgana ba Ya Asiya Haushi ya kamata ta fara Fada Tana Fadin"Kila ma baki sani ba..? Domin sai ma an Dauke ka da Daraja da kima ne ake sanar dakai wani abun." Da Sauri nace"Aaha nasani fa..Wlh na sani Mama ta fadamin sannan Anty Binta batagarawa itama ta fadamin." Ya Asiya Dagachan bangaran ta jimjina kai kafin tace"Shi Uban gayyar bai Samu Fada miki ba kenan..? Sai a bakin Uwarsa da yayarsa kike ji kenan..? Anya Fa'iza wannan Rayuwar zata tafi ahaka kuwa..? Shekara Takwas ai ba kwanaki Takwas bane." Fa'iza ta share hawayenta da suka zubo mata kafin tace"Ai shima ya fadamin yau daya dawo.." Ya Asiya tace"Umhh..! Saboda takaici ma ta kasa mgana,Fa'iza kuma Daman ba ma'abociya mgana bace Ya Asiya Tagaji da shurun Fa'iza yasa ta katse mganar da cewa"Goggon Karofi ke Fadamin Zai yi aure yanzu muka gama waya da ita..Ita kema Fadamin Hafsatu tazo wajen ki shekaran jiya." Fa'iza tace"Eh tazo shekaran jiya..tazo..." Sai ta saki wanchan mganar Saboda bata son tayi Tsawo ita kanta Ya Asiya ai ta sani Fa'iza bata kaunar mganar Data Danganci Ishaq da Danginsa in ma ka matsa sai ta saka maka kuka Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Yaushe ne Bikin..? Fa"iza tace"Bansani ba.." Ya Asiya tace"Allah ya kyauta zan shigo katsinar nima In nazo Duba Tamadina hala ba ma kiji bata ji Dadi ba..? Ciwon kafafu take fama dashi." Fa'iza tace"Naji Da Hafsatu tazo ta Fadamim." Ya Asiya tace"Yaushe zaki leka ki Dubata ke da ke kusa ma Fa'iza yaushe Rabon ki da Dutsenmah Tun Sanda Ta madina ta kwanta asibiti an kusa shekara fa" Fa'iza tayi shuru ta kasa mgana Saboda bata da tacewa Ishaq ne baya barinta tana son zuwa inda Mahaifiyarta take sai yace me zataje yi tana gidan wani..? Ya'yansa bazasu je gidan wani suna Rab'e Rab'e ba. Ya Asiya tayi  shuru yasa ta kyaleta sai ta shigo da mganar"Ina yaran nan..? Hala sun yi barci..? Ta amsa mata Ya Asiya tace"Shikenan Sai mun shigo zamu karisawa Tattauna ki kara Hakuri Fa'iza kowani bawa da irin tasa kaddaran..Mu Tamu kaddaran Rasuwar Baba ne itace silar Shigar mu duk Halin da muka shiga." Fa'iza tace"Haka ne Daman ai KANA NAKA  ne Allah na nashi ne..Sannan na Allah ne Daidai." Ya Asiya na jinjina kai tana Fadin"Hakane Fa'iza Allah ya mana mai kyau..Mu kwana Lafiya. Fa'iza ta rakata da Fadin ta gaida yaranta Daga haka sukayi sallama Sannan na  ijiye wayar nq koma gefen gado na zauna ina mai kura ma Madubi Ido duk da ance ba kyau kallon kai a madubi in Duhu ya shiga ammh ni sai ta samu kaina da kare ma Jikinna kallo. Tare da Fuskata ina Ayyana adadin Lokuta nawa ya Ishaq ya kalleni ya yab'a min..? Koda yaushe cikin kusheni yake yi an samu ma bayan sun fara Tara zuru'a ya Daina jifana da kalmar Mummuna ammh kalmar Baka sai dai in yan Cin mutumcinsa basa kusa ni na sani Tazaran Dake tsakanina da Ya Ishaq kamar Tazaran kasa da Sama ne ko abaya ban taba mafarkim auran miji kamarsa ba Domin ba Tsarana ba ne, sannan ba kuma Had'i shi kanshi na san ni ba irin wacce ta Dace dashi bane Mama kofar soro kullum tana Fada min hakama Anty Binta batagarawa,To ammh Ba kai kake Tsarama kanka Rayuwa ba Allah ne Kana naka ne yana nashi kuma Tsarinsa ne akan gaba. Na tabbata ba Domin kakkausan Bakin Baba kan Ya Ishaq ba, da Tuni bayan kasa ta shafe idonsa ya rabu dani  ya samu salama kamar yadda yake Fadi sai dai ina Ya Ishaq bazai iya Tsallaken mganar Baba ba Shiyasa har yanzu muke tare ina D'aukan dukkan cin kashi da Tozarcinsa Bani da wani gata nan Duniya sai Ishaq shine uwaa na shine Ubana  da Duniya ta Tamadina ga yanayin yadda Rayuwa tazo mata sauran yan'uwanna ba waje daya muka tashi ba Bayan Rasuwar mahaifinmu  Raba mu akayi ni a karofi na fara Rayuwata Kafin dalili ya yanke zamanna achan Baba Kabiru ya maido ni katsina ya Damkani Hannun Mama. Hawaye na haka suke faman zuba ban iya saka Hannuna domin na tare su  ba Saboda ko na goge su wasu ne zasu kara fitowa a irin wannam Lokacin nake samun Fitar da abunda ya dade yana Damuna,Ba bakinciki nake yi Saboda Ishaq zai kara aure ba,A'a ai daman na sani yafi shekaru yana ikararin zai auri Zab'insa Daidai da Ra'ayinsa tun kafin ma yakai haka zama a rayuwa ballatana yanzu dayake jin kansa ashi wani ne. Sai dai abu D'aya na sani zuwan Amarya nan tozarcin danake sha sai ya Ninka wanda nake sha abaya abu daya ne naake gudu wulakanci ina tsoro da firgicin Amaryan tazo tasan duka labarina tazo tana ganina a wulakance ta goraanta min Kamar yadda Shima yasha Fadi Fa'iza ba kyau ba Turanci komai nata Total zer0 ne. ammh a raina bana mai Bakinciki don zai kara aure ai yayi ma kokari da muka kwarari wad'anan shekaru bai kara ba,sai yanzu na kuma ji Dadi da matar zatayi nesa damu ko Bakomai kazantar da baka gani ba Tsabtace akasan chan raina kuma ina da kishi Domin ina son mijina so irin wanda Duk Macetagari zata nuna ma uban ya'yanta,duk da tarin Nakasun da auran mu ya kunsa, duk da ko shi din' bai taba sona ba. sai dai bazan barsa yayi wani Tasiri a kaina ba tunda inda Son ke da muhalli baza'a martabasa ba, zan iya Rantsuwa ko Kaffara bazan yi baa Ya Ishaq baya sona karfin Biyayyar Baba ce take Rike da igiyar auranmu. Naso na sauya Rigar Jikina kamar yadda yace sai dai kuma Tunda yace na bar shi nasan ko da na bisa Shashensa sai ya koreni shiyasa ban bata ma kaina Lokaci ba na Haura kan gadona naa jawo Ahmad jiki na,na Rumgume sa Abu D'aya ke sanyayamin Rai ya'ya na Domin duk duniya bayan Ishaq bani da kamarsu basa san iya adadin Lokacin Dana Dauka inaa kuka ba ammh nasan Har barci ya kwasheni kukana bai Tsaya ba. Kiran Sallar Farko na  tashi kamar yadda ya zame min  Jiki Fa'iza bata barcin Rana sannan karfe Hudun Asuba take tashi sai kuma wani Dare. Fita nayi naje Dakin yaran na Tashi Amir da Mustapha zasu bi Babansu masallaci Bayan sun tashi na fita zuwa Dakin Hafsatu na isketa ta tashi har ta Shiga Tiolet sai na Fice su Amir ta Tsaya akansu sukayi alwala Daidai Sanda Ishaq ya fito Daga bangaransa Sanye da Jallabiya baka da Carbi Kofar Dakin yaran ya Coge duk Fadan sa bai isa yayi ma Fa'iza Fadan rashin Tarbiya da kula da yaransa ba wannan in bai Gode mata ba ai bazai Zageta ba. Amir ne ya karisa ga Baban yana Fadin"Oyoyo Daada sannu da zuwa.." Yafada yana rumgumesa rike sa yayi yana Shafa kansa kafin yace"Jiya na dawo lokacin kun yi barci.." Ina musty..? Yafada yana kallonsa Fa'iza na kiciniyar saka mai wata riga bayan ta cire mai na barci sai faman mutsike ido yake yi alamun barcin bai sake sa ba. Dariya yayi yana kallonsa kafin ya Bude Hannunsa yana Fadin"Oya come Here..!" Da gudu yaron ya nufessa ya Fada jikinsa yana Fadin"Daada.." Shafa kansa yake yana jin Farimciki acikin ransa Fa'iza ya kalla Dake tashin Anum da dan karfi yace"Kyaleta mana.." Fa'iza ta Dago tana Fadin"Suna da Hadda yau." Yana rike hannun su Amir yace"Ai da Sauran lokaci ke komai naki na Hanzari ne karfe Biyar din Asuban ne zasu tafi Haddar..? Bada karfi yayi mganar ba saboda Haka ban ma jisa ba nadai san yayi mgana kuma nasan bai wuce Fada ne irin nasa Daya saba ba,  shiyasa har yaja su Amir suka fice ban kara mgana ba.. Suna Fitan nayi kokarin tashin Anum Saboda tayi sallah ta wartsake kafin su Dawo Daki na muka koma Tare nima na Dauro alwala mukayi sallah Tare da Anum muna idarwa Ahmad ya tashi na Daukesa naga ya bata pampers dinsa,sai na mike na Goyasa na shiga Kitchen bayan na gargadi Anum kada ta koma barci ta zauna tayi azkar din Safe wanda yaran duk sun Haddace.. Ruwan Zafi na fara sakawa saboda nayi ma Ahmad wanka kafin sauran yaran su Dawo Sai kuma na fara kokarin Fere Doya saboda na soya musu na Tafiya dashi makaranta sai ga Hafsah ta shigo Kitchen din da Hijabinta. Fa'iza Hankalinta na wajen aiki bata san Hafsatun ta shigo ba sai da ta tabata sannan ta dago tana kallonta kafin tace"Kin fito Hafsah..? Da yanayin mganarta Hafsah tace"Eh Ina kwana.." Da dan daga Sauti Saboda Fa"izan ta jita sosai. Ta amsa mata Cikin Sakewarta Hafsah tace"Bari na amshe ki." Fa"iza tace"A"a barin min wanan aiki..Ga dai ruwa nan na saka in ya Tafasa ki juyo ki yima Ahmad da Anum wanka kafin su Amir su dawo." Tafada cikin yanayin Raba mganarta Hafsah ta amsa mata da Toh,ba Dadewa ruwan ya Tafasa ta Dauko wani Karamin baho ta juyo ruwan ta kai Tiolet din Dakin Fa'iza da suna da Shower na wanka ya lalace kuma ya Ishaq yace da gan gane saboda haka bazai gyara ba. Dawowa tayi ta karbi Ahmad ta je ta fara mai wanka ta shiryasa sannan tayi ma Anum nata wanka alokacin har su Amir sun Dawo masallaci suna Falo Tare da Ya Ishaq Sanda Hafsat ta fito Dauke da Ahmad daya fara Rigima ne Fa'iza ta fito Daga Kitchen din tana gaida Ishaq ya amsa mata bai ko kalleta ba Hankalinsa na wajen Amir Dake bashi Labarin abunda ya Faru a makarantasu jiya shi kuma Musty bai da Hayaniya yana Lafe jikin Uban.. Hafsah ma tabi ayarin yar'uwanta ta gaisheshi ya amsa yana Dubanta ganinta Dauke da Ahmad yasa yace"Ina zaki kaishi..? Hafsah tace"Kuka yake yi zan kai shi ta bashi Nono ne." Hannu ya mika mata yana Fadin"A kitchen din zaki kai mata shi..? Wato salon ta jefa shi Cikin wani abu kin santa bata da kula." Hafsah dai batace komai ba ta mikamai D'ansa ya Cafe shi yana Daga sa sama cikin Fara"a Hafsah bata damu ba ta karisa kitchen din Domin kama ma yayar nata aikin itama gobe zata koma Daman Hutun Midterm break Aka basu a makaranta yasa Goggo ta barta ta taho itama tana Karofi ne wajen Hajiya Indo da suke kira Goggon Karofi ita take rikonta tun bayan da ta karbota wajen mahaifiyarsu Ta madina. Suna Kitchen din suna aiki Hafsah taji Sanda Anum ta fito ganin babanta yasa ta nufesa cikin murna tana Fadin"Daada yaushe ka dawo..? Daman Anum akwai kirniya da Rashin jin mgana Yana ganinta itama ya Tarbeta yana Fadin"Anum dina jiya da Daddare na dawo kun yi barci." Kai Tsaye tace mai ina Tsarabanta yace sai an juma in ya sake fita Hafsah ce ke Sauraran Hiransa da ya"yansa banda Fa'iza da baji take yi Sosai ba sannan Hankalinta na wajen Soya Doya bata ma san Abunda suke ciki ba. Kafin bakwai na Safe tayi Fa'iza ta gama komai sai ta bar Hafsah a kitchen din tana karisawa,ni kuma sai naje na Shiryan yaran saboda suna da Hadda Tahfiz ne tun Safe sai shida suke Dawowa Allah ya taimake ni Ahmad na wajen Ya Ishaq ya shiga Dashi Shashensa. Koda bakwai da Rabi tayi sun karya sun shirya Tsab Cikin kayan makarantarsu Ga Basket din kowanne an shiryamai da soyayyar doya da miyar kwai,Sai lemu da ruwa Fa'iza na kokarin Tura Hafsah ta leka tayi ma wani wani makotanci Haruna mgana mai Tuka adaidaita shi ke kai yaran makaramtar Hadda da Boko a wata Ya Ishaq na Biyansa Saboda abaya motace har da Direba ya Daukan musu tunda Anum ta taba koke motar Mama ta sa ya bama Jamal kaninsa motar tana chan gidanta Kofar soro in ya Dawo Hutu Daga Kano inda yake karatunsa na Engeering yake amfani da ita su kuma Ishaq ya Daukam ma yaran mai adaidaita a cewarsa Tunda bata iya Tattali ba shi ba asararrre bane sannan kuma yace Mota bata Dace da ni  ba,irin mu yawo acikin Adaidatan yafi Dacewa damu,ni Dayake ban Damu ba, ba fita take yi sosai ba Daga Gidan Mama sai gidan Anty Binta shima na da'n Rage zuwa tunda ba maraba suke da zuwana ba Karofi kuma sai dai in an yi Rasuwa muje Gabadaya ammh ni kad'ai Ya Ishaq cewa yake bai yarda da ni ba zanje ne na Had'u da yan'uwana azagesa shiyasa ban ma Damu da Fitan ba nima. Ina shirin aika Hafsah ne sai ga Ya Ishaq din ya fito yace shi zai kai su,jin Haka yaran suka fara Murna sosai,Tare da Ahmad suka tafi har Lokacin bai koma barci ba shima ai yasam Ishaq saboda gaskiya in yana Gida yana bama yaransa Lokacinsa nice dai bani da wannan matsayin. Har sun fita naa bisu Haraban gidan ina kwalama Amir kira ya juyo yana Fadin"Umma menene..? Ina Sosa gashin idona nace"Kada ku manta ku karanta addu'ar fita Daga gida." Da Karfi Anum ta fara karantawa Amir na Binta shi da mustpaha suna gamawa nabisu da mirmishi ina Daga musu Hannu Ishaq dai Tuni ya Shige mota yana Dauke da Ahmad irin wad'anan Hallayar na Fa'iza ba wani Burgesa suke yi ba,Sai dai kuma a kasan Ranta yasan Tarbiya ce mai kyau shiyasa wani lokacin baya mgana. Ganin ya shiga motar bai bude get ba yasa na karisa na Budemai motarsa ta Fice Daga gidan sannan na maida na Rufe,abaya munq da megadi wani Dattijo,Tunda lokacin da  Yaya Ishaq yaga ina basa Abinci yace don me..? Ai yana Biyansa duk wata ba wata mgana kawai sai ji nayi ya sallamesa Daganan kuma bai kara Daukan mana wani megadi ba yace Tunda Zan iya na yi Hidiman get din da kaina Sai da suka tafi naje nayi wanka na Sauya kaya zuwa wata Doguwar Rigar Shadda Dinkin zamani kan na gama Shiryawa Hafsah ta gyara Falon ta share in da yaran suka bata sannan ta gyaro Dakin yaran suma ganin haka yasa nayi mata sannu da aiki ni sai na shiga  Shashen Ishaq na gyara duk da ba sosai yayi Datti ba na Cika shi da Turaran kamshin Daki sanin sa mai son kamshi ne. Kafin ya Dawo na jera mai kayan  karinsa,na koma Falo muka karya ni da Hafsah muna yi muna Taba Hira duk da Hiran Daga Hafsah ne ita Fa'iza nata Eh ne ko A'a sai mganar da batayi Tsawo ba. Har muka gama karyawan bai shigo ba,Hafsah tatafi tayi wanka ni kuma na kwashe komai nakai kitchen na Fara kimtsa wajen,Bayan na gama nayi wanke wanke,ina cikin goge gogen kitchen din naji Sallama atsakar Falon Sai na leko da Towel din gogogogen a Hannuna,Baki na washe ina fadin" BADARIYA.." Cikin bayyana Murna ta ganin wacce aka Kira da Badariya na Tsaye da katuwar leda a Hannunta yar matashiya doguwa Fara Fuska kamar ta Ishaq sai dai ta fisa Haske saboda ita macece Autansu ce Badariya Kabir Karofi. Karisowa tayi Cikin Falon Tana Fadin"Anty Fa'iza yunwa nake ji wlh..akwai sauran abun kari kuwa..? Tafada tana wanchalar da gyalen Hannunta Lokaci Daya da ledan Data shigo da ita. Bata ma saurari Fa'izan Dake faman mata gaisuwan yasu Mama ba Ta Shiga kitchen din tana Dube Dube ta samu Doya a kula da Miyar Kwai ta Dauko ta Fito Tana Fadin"Anty Fa'iza adana gaisuwarki sai naci na koshi Tukunna." Dariya nayi  mata bance komai ba na koma kitchen din na Cigaba da goge gogen da na fara ina mai jin Dadin zuwan Badariya din duk cikin ya"yan Mama Ita kadai ce ke sona sai Jamal shi kuma bai da alkibla yau ya min Mutumci gobe kuma akasasin sa shidai baka gane ina ya Dosa,Ammh yana zuwa gidan nan wajen su Amir sannan yana zuwa cin abinci ba wacce tafi Tsanata Daman Tun zamana wajen Mama irin Anty Binta batagwara ita da Ya Ishaq daman basu so zamana agidansu ba Sun gama Dora min karan Tsana wanda har yafi ma wanda Mama take min tun ina da karanci shekaru kafin ma aure ya shiga tsakani da ya Ishaq Sai da nagama aikin na Sannan ta sake Fitowa Falon na iske su Tare da Hafsah wacce tayi Rashe Rashe kasan Cafet tana Bude kayan da Badariya ta shigo Dasu ita kuma Badariya na kan kujera ta cin Doyarta suna mgana da Hafsah. Ina Shigowa Hafsah tace"Anty Fa'iza kinga ankon Bikin ya Ishaq.." Jin Shuru yasa Badariya tace"Bafa ta jiki ba..Anty Fa'iza ga ankon Ya Ishaq..kin gani..? Sai alokacin najisu nabi Kayan Dake Hannun Hafsah da kallo sai na kasa mgana Badariya da Hafsah suka kalleni  Cikin wani yanayi kafin Hafsah tace"Kilama bata san da ankon ba.." Badariya tace"Anya..?Anty Binta ta Dauko fa..Ranar agabana da tazo gidan Mama ta Kira ya Ishaq din tace zata Daukan ma Anty Fa'iza ,Anum kuma zata Hadasu dasu Hibba ne. Hafsah tace"To ba mamaki." Badariya tace"Wannan da kike Dagawa naki D'aya nawa daya..Yanzu Daga wajen tela nake bai Dinka Less din ba.." Hafsah ta zaro ido tana Fadin"Wai nawa..? Badariya ta mata Dariya ai sai tatashi ta Daga Tsalle tana murna ta Rumgume Fa'iza Dake Tsaye tana kallonsu tana Mirmishi Cikin Fara"a tace"Kinga Anty Fa'iza Badariya ta Dinka mana..!" Fa"iza ta karbi Atamfan tana gani kafin tace"Sun yi kyau.." Hafsah ta isa ga Badariya ta Rumgumeta tana Fadin"Nagode sister..Allah ya bar zumumci." Badariya tace"Ameen ammh bani Zaki ma Godiya ba Ya Ishaq ne shi ya siya mana.." Hafsah bata wani ji mamaki ba,Saboda in yayi Niyya yana da Alheri sosai tana ta godiya tana Santin kayan. Badariya tace"Za dai kizo bikin ko..? Nima yanzu aBakin Ya Ishaq nake jin kinzo Daga kai yara makaranta wajen Mama ya biya." Hafsah tace"Zan zo tunda weekend ne." Badariya tace"in Goggon Korofin ta bar ki ba..Domin ita kanta ban Tabbatar da zata zo ba..Naji suna waya da Mama tana Fadan Ya Ishaq bai Fada musu zencen auran nasa ba" Hafsah dai batace komai ba Badariya ce tacigaba da Fadin"To waya fadamawa..? Daga shi sai Mama sai Anty Binta suke abinsu Amaryan ma suna waya da Anty Binta tunda ita ta Hada lefen. Hafsah tace"To yaushe  ne ma Bikin..? Badariya ta tabe baki Tana kallon Fa"iza dake zaune gefe tana kallonsu kafin tace"Anty Fa"iza ta san Lokacin Bikin..? Hafsah tace"Anya..? Batamin mgana ba." Badariya tace"Karshen wata ne sauran Sati uku." Hafsah tace"Allah ya kaimu nan za"a kawo Amaryan..? Badariya tace"A"a chan Abuja zata zauna..Ai itama yar Abujan ce,mahaifinta shugaban ya ishaq ne a wajen aiki,Itama ai ma'aikaciya ce tana aiki da wani kamfani ban dai san ko na menene ba nima Haka naji Anty Binta na fada ma mama cikin Hirarsu." Hafsah tayi shuru jikinta yayi sanyi Tana kallon yar'uwanta wani Tsausayinta ya kamata sai taji Badariya na Fadin"Ya Ishaq ya samu Cikar Burinsa Mace mai kyau Fara Doguwa mai kwalayen zamani ga Kudi da Nasaba..Allah yasa a wanye Lafiya." Hafsah ta amsa mata da Ameen kawai Domin bata da tacewa,Fa'iza ce ta dan Daga Sautinta tana Fadin"Badariya ya mama..? Badariya tace da karfi"Tana lafiya..Tana chan tare da D'anta na barsu na fito amso dinki nan sanan kuma yunwa ce ta koroni." Mirmishi kawai nayi ban ce komai ba ni kowa yasanni  bani dayawan mgnaa Saboda yanayina Sai Hirar ta koma Tsakanin Hafsah da Badariya da Daman kawaye ne suna Hirar Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiyar Dala

Chapter 2 of 25