Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da shirmensu ya ilahil alamin. Shigowar su Shahidah ne ya taimaketa. Cike da farin ciki sukazo suka rungumeta suna hawayen daɗin ganinta. Itama farin cikin take ji a ranta matuƙa. Nanfa suka shiga nan nan da ita. Sai kawai Daddy da Ammie suka fita tare da su Waleed. Dan ba'aso suyi yawa a ɗakin sam. A hakan ma dan RK najin nauyinsu shiyyasa baiyi magana ba. Ganin Yazeed bashi da niyyar fita a ɗakin RK ya dubesa cikin danne kishinsa ya furta, “Yauwa babban yaya inama son magana da kai. Dan akwai alluran da za'a mata zuwa 6pm naga kamar babu shi anan ya ƙare, ko zaka samo mana shi a pharmacy please?”. Yayi maganar ne idanunsa a kan takardun hannunsa yana kuma ɗan tafiya, dan haka baka isa gane ainahinsa ba kai tsaye. Bin bayansa Yazeed ɗin yayi batare da yace komai ba. Maanal ta bisu da kallo ƙasa-ƙasa. Da taimakon yayun nata biyu ta ɗan ci abincin, nurse ɗin dake kula da magungunan ta ta shigo ta bata. Babu wani jimawa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Dama haka doctors ɗin suke buƙata ta dinga barci isashe dan zuciyarta da brain ɗinta su samu nutsuwa.........✍️ _🥱Team RK & Team Yazeed ina miƙo gaisuwar ban girma😌👌._ ✨ZAFAFAN DAI ✨ 1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ 🅿️➖1️⃣4️⃣ .......A ɓangaren Yazeed da RK kam suna fita Yazeed ya tsaya cak. Kallonsa RK ya juyo yanayi, sai kuma ya saki lalataccen murmushi yana dawowa da baya inda Yazeed ɗin yake. “A'a babban Yaya yaka tsaya kuma? Ya kamata muje ko”. Murya a sarƙe Yazeed ya amsa masa da, “Rubuta sunan alluran ka bani anan. Sannan ka daina wani kirana Babban yaya dan ban san alaƙar data maidani yayanka ba”. Hannu RK ya kai ya shafo bayan ƙeyarsa yana murmushi irin na ƴan duniya shi a dole irin yaji kunyar nan. “Haba bazan iya kiranka da sunanka ba gaskiya. Ko a bayan ma kafin na fahimci kai Yayan Maanal ne yasa nake kira. Yanzu kam dana sani sam bazan iya hakan ba”. “Ni ba yayan Maanal bane kawai mijin da zata aura ne”. Yazeed ya faɗa a gadarance. Wani irin mugun dukan zuciyar RK furucin yayi, amma sai ya dake cike da basarwa ya furta, “Irin wannan wasan ai saika saka zuciyata ta buga babban yaya, kona ɗauka baka son aura min ita ne. Please mubar zancen haka ga sunan allurar”. Yana miƙa masa ƴar takardar da yay rubutun yabar wajen da sauri dan baya buƙatar sake jin wani furuci daga Yazeed ɗin bayan wanda yaji. Shifa wlhy san Maanal yake. Kuma baya jin zai iya barma Yazeed ɗin koma mi za'ayi. Sai dai suyi yaƙi mai rabo ya ɗauka. Babu ruwansa da ƙarfin alaƙarsu kowa ya iya allonsa kawai ya warke. Da wani irin kallo Yazeed ya bisa kawai batare da ya sake cewa komai ba shima yabar wajen... _________★ Ganin jikin Maanal Alhamdullah Ammie ta matsama Yazeed komawa kan saboginsa. Shima Daddy ta damesa da roƙon ya koma Kaduna kada su shiga hakkin sauran matansa. Yazeed dai ya jitane kawai. Dan ya ƙudura a ransa bafa zai tafi ya bar Maanal a hannun wannan kuren likitan ba RK. Dan haka ƙafarsa ƙafarta idan ta samu lafiya. Shi kam Daddy sai da sukai ƴar rigima sannan ya yarda zai wuce Kaduna ɗin, amma kuma dole sai tare da ita, yace nan da kwana biyu ta dawo ta sake dubata tunda dai ga Nene gasu Shahidah. Ita dai Ammie tace hakan yafi mata duk da bata so hakan ba, dan tana son kasancewa da Maanal ɗin itama amma babu yanda ta iya haka ta haƙura suka tafi bisa shawarar Nene dan itama tafi son yaje ga sauran matansa kar abin ya zama wani daban kuma. Yazeed dai ya nuna mata akwai aikin da yake anan ɗin dan gobe ma zaiyi zama da masu Companyn Mawaad ne.. Wucewar Daddy da Ammie kamar ya buɗema Yazeed da RK wani filin TAKUN SAƘA ne, dan kuwa kowa ya riƙe wuta yana baje kolin hajarsa. Yayinda ita kuma take nuna bama ta fahimci inda suka dosa ba su duka. Tun suna abin a kaikaice har ya fara bayyana kansa sosai, dan takai da Yazeed ya shigo duba Maanal tsalam zakaga RK a ɗakin ya shigo kamar wanda aka jeho. A wajen su Amal taji duk yanda akai aka kawota Abuja. Nan ta fahimci RK yaje gidansu ne sai ya kasance a dai-dai lokacin da take a halin taimako. Hakan ya kwaranye mata mamakin ganin nasa anan. Sai dai kasancewarsa likita bai bar bata mamaki ba. Dan har sukai zamansu a Jos suka gama bai taɓa nuna musu ga aikinsa ba. Kai ita tama sha yin gulmarsa da jifansa da kalmar mara aikinyi, sannan a tunaninta shi ɗin ɗan Jos ɗin ne ma ai. Yau Nene ta ɗan tashi da ciwon kai, dan haka ta wuce gida dan ta ɗan huta. Dama itace ke kwana da ita anan, da safe zuwa goma sai ta wuce gida idan su Amaal sun zo, sukuma suke yini da ita anan har sai dare idan Nenen ta dawo sukuma sai su wuce. Daga Nene har Amal suna a gidan Shahidah ne yanzu, dan bayan wucewar su Ammie sai itama Nene ta koma can gudun karta zauna ita kaɗai anan ɗin duk da ma ƙarfin zaman nata a asibitin ne dai. Bayan wucewarta Maanal ta tashi a barci, da taimakon Nurse tai wanka, kafin ta fito an gyara ɗakin, tana ƙoƙarin zama a bakin gado take tambayar Nurse ɗin, “Nene fa?”. Amsa ta bata da, “Doctor Rafeeq ya kaita gida ta huta kanta na ciwo”. Shiru kawai Maanal tayi, mamakin RK na sake kasheta, gaba ɗaya fa yabi ya kanainaye mata ƴan uwa kowa ya sanshi. Yanzu haka kullum Waleed da Hameed na manne da shi har sai da suka wuce aka samu lafiya. Haka idan su Didi sunzo zaizo ya zauna wai yazo gaishesu duk hararar da take masa baya ma nuna ya gani. Itako yaya zatai da wannan bawan ALLAH. Babu ma abinda ke damunta sai zaman marina da suke tsakaninsa da Yaya Yazeed, hatta gaisuwa sama-sama sukeyinta yanzu ma ta rasa mike damun kawunansu haka.... Shigowarsa ɗakin shi da Doctor Ranjet ya katse mata tunaninta, da sauri taja hulanta ta saka tana ɓata fuska. Ɗauke kai RK yay kamar bai ganta ba yama hau duba magungunanta. Shi dai Dr Ranjet matsowa yay kusa da ita yana tsokanarta, haka yake mata dan shi mutum ne mai wasa sosai. Dole ta daure ta ɗan masa murmushi dan turancinsa na sata nishaɗi, kullum gaya mata yake ita ɗin mai sa'a ce. Ruhunta nada tauri sosai, saboda da wahala kaga mai irin matsalarta ya shiga irin yanayin data shiga kuma ya tashi ya cigaba da rayuwa, dan shi kansa a randa aka kawota asibitin baimayi tunanin zata kai washe gari a raye ba. Dai-dai Dr Ranjet na ƙoƙarin mata wata allura da kullum a irin wannan lokacin ake mata RK ya ƙaraso wajen. Kujera yaja ya zauna yana mai zuba mata ido dan sai ɓata fuska take tana kallon allurar. Amma tana juyowa suka haɗa ido da shi sai ta ɗaure fuska ta fiske abinta. Kansa ya kauda kawai yana murmushi baice komai ba. Allurar akai mata, ana gamawa ta kwanta saboda jiri take sakata. Idonta a rufe har fin mintuna biyar Doctor yay mata sauran abinda ya rage har ya fice da kusan mintuna biyar sannan ta iya buɗe idanunta da suka kaɗa sosai. A kansa ta saukesu, sai kuma ta janye da sauri ganin shima ita yake kallo. “Nifa bana son haka, azo a tasa mutum gaba ai haramunne ma wannan”. Murmushi ya saki mai faɗi yana mai janye idanun nasa daga gareta. Sai kuma ya furzar da huci kaɗan a hankali ya furta, “To amin afuwa sarauniya. Sonki ne kawai ke neman zubar dani amma ke kina ɗaukar komai wasa”. Shiru ta masa bata tanka ba. Shima sai ya bar zancen ya kama wani daban. “Ni kam banga Zizaah da Aneesa ba, ko basu san baki da lafiya bane?”. Kansa ta jinjina masa alamar eh. “A gaskiya ya kamata su sani. In sha ALLAHU anjima zan kirasu na sanar musu kuwa”. “Ni dai ban saka ba”. Idanu ya ɗan waro waje. “Saboda mi?”. “Ba saboda komai ba, kawai dan mutum na ciwo sai anta talla da shi. Yanzu miyyasa ka kai Nene gida ma?”. “Saboda taje ta huta. Ba su Didi na zuwa ba”. Hararsa ta ɗan yi, kafin tace, “To idan kuma ina buƙatar wani abu fa kafin su suzo?”. “Ba gani ba sai ki sakani nai miki. Ai shiyyasa nazo nan na zauna a madadin Nenen. Faɗi mi kike buƙata gimbiyar Rafeeq?”. Baki ta buɗe zatai magana tsulum sai ga sallamar Yazeed. Kafin ma su gama amsashi ya riga ya shigo. Kallon kallo sukaima juna shi da RK ɗin sai kuma kowa ya janye cike da basarwa. Takowa yazeed ɗin ya ƙarasa yi ta ɗayan side ɗin. Saboda neman magana sai ya zauna a bakin gadon kusa da ƙafafun Maanal. A hankali ta matsar da ƙafafun nata dake cikin bargo, dan RK ya wani zubama ƙafafun nata ido kamar mai kallon television duk da a lulluɓe suke a bargon. Cikin dauriya ta gaida Yazeed. Ya amsa mata idanunsa kafe a kanta.... “Yaya jikin naki?”. “Na samu sauƙi Yaya. Ya aiki?”. “Alhamdullahi. Tunda kin samu sauƙi sai sallama kenan ko?”. Maimakon amsa saita sakar masa ɗan murmushin yaƙe kawai. Abinda ke hannunsa ya miƙa mata. “Ga abinda kikace kina so, shine maimakon ki sanar min kika kama faɗama su Shahidah ko? Bana gaya miki duk abinda kike buƙata yanzu ki sanar min ba. Domin nine da hakkin yimiki shi ai, kwana nawa ya rage mana zama ma'aurata”. Kanta kawai ta jinjina masa da faɗin, “Nagode”. Yayinda RK ya saki wani ɗan iskan murmushi yana sake yin balance a kujerar. Sai kuma ya wani laɓe baki yana kauda kansa. Duk Yazeed na lure da shi, dama kuma yayi furucin domin shi ne. “Ina Nene?”. “Taje gida bata jin daɗi”. “Ayya ALLAH ya bata lafiya. Ai tana ƙoƙari ma ga jikin girma. Su su Shahidah fa?”. “Basu ƙaraso ba, suna hanya dai sukace”. “Okay yayi”. Ya faɗa yana zaro wayarsa da ake kira. Ɗagawa yay tare da kaiwa kunne, sai kuma ya miƙe saboda masifar da Mamma ke masa daga can, dan har ita Maanal ɗin taji furucinta na farko ma. Sassanyar ajiyar zuciya Maanal ta sauke ƙasa-ƙasa dai-dai Yazeed ɗin na fita. Hakan yasa RK tuntsurewa da wata dariyar wulaƙanci. Kallonta ta maida garesa cikin mamaki. Shiko ya wani ɗage mata gira cike da neman rigima ya ce, “Amma dai kina matuƙar tsoron wannan yayan naki fa. Irin wannan sauke ajiyar zuciya haka”. Ƙin kulashi Maanal tayi, sai dai maimaita kalmar tsoron daya ambata tanama Yazeed ɗin take a zuciyarta. Shima bai sake cewa komai ba ya kawo hannu zai ɗauki abinda Yazeed ɗin ya bata tai saurin ɗaukewa tana ɓata fuska. “Wai kai idan baka shiga rayuwar mutum ba da abinda ba'a sakaka ba baka jin daɗi ne halan?”. “Oh haka kike fassarani ashe?”. “Hummm”. Kawai tai shiru. A ransa yace miskilatu kenan. Magana fal cikinta amma bata son yi. A fili kam zaiyi magana sai ga Yazeed ya dawo. Bai fasa ba ya cigaba da faɗin, “Birthday na ya kusa mi zaki bani as gift?”. “Humm”. Maanal ɗin ta faɗa idonta akan Yazeed daya iso gaban RK ɗin rai a ɓace. Shi kuma yayi kamar bai gansa ba. Cikin fusata ya ce, “Malam ina son magana da kai”. Sai lokacin RK ya dubesa. Sai kuma ya nuna kansa cike da rainin wayo wai shi? A kausashe Yazeed ya ce, “Eh”. “Okay to Bismillah ai gani. You are free zaka iya maganarka kawai”. “Ba'a nan ba”. Yanda yay maganar a fusace ya saka Maanal dake saurarensu kallon Yazeed ɗin a karo na farko. Sai kuma ta kalla RK dake wani shegen murmushi baida alamar motsawa balle aje ga batun tashin. A hasale Yazeed ya sake buɗe baki zaiyi magana Shahidah da Amaal sai mijin Shahidah ɗin sukai sallama. Dole ya haɗiye maganar yana mai furzar da huci, sai kuma ya juya suka fara gaisawa da mijin Shahidah. Shima RK miƙewa yay yana amsa gaisuwar su Amal, kafin ya juya ga mijin Shahidah ɗin shima suka fara gaisawa. Daga haka ya fice a ɗakin. Hankalin Manaal naga su Amal Yazeed shima ya sulale ya fita, sai da ta ɗago da nufin yin magana dashi kawai taga wayam. Waige-waige ta fara cikin mamaki, cikin tsokana Mijin Shahidah ya ce, “Oh in dai samarinki ne ai sun fice auta”. Fuska ta ƙwaɓe kamar zatai kuka ta ce, “Kai Uncle Sadeeq”. Dariya suka sanya mata su duka.... ★★★ Sam RK bai san Yazeed na bin bayansa ba. Dan hankalinsa ma nakan wayarsa fuskarsa da murmushi saboda saƙon da yake karantawa. Jin ansha gabansa ya tsaya cak tare da ɗagowa. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Yazeed ɗin kaikace zakuna ne jirace da juna a filin daga. “Doctor ina son maka gargaɗin farko da ƙarshe akan yarinyar nan”. “Saboda mi?”. RK ya faɗa yana tsatstsare Yazeed da ido. Shima Yazeed ɗin cikin dakiya ya bashi amsa da, “Saboda ita ɗin matar dazan aura ce. Akwai ranar aurena akanta. Kasan kuma nema akan nema haramun ne sai dai idan kana da ƙarancin ilimin addini ne kuma na maka ƙarin bayani yanda zaka fahimta”. Maganar Yazeed ta ƙarshe-ƙarshe ta zafi RK, amma sai ya danne yama saki murmushi da ƙoƙarin raɓashi alamar zai wuce abinsa. Cikin zafin nama Yazeed ɗin ya sake shan gabansa. Kallonsa RK ya sake yi yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa, dan shima fa ya iya zuciyar nan, dalili ne kawai ke sakashi danne tasa ba tsoro ba. “Yazeed why???”.........✍️ ✨ZAFAFAN DAI ✨ 1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ 🅿️➖1️⃣5️⃣ ........“Why kake son mu dinga kasancewa a wannan yanayin ni da kai?. Ina fa ganin girmanka ne matuƙa shiyyasa kaga ina barin komai a yanda yake. Please respect your self mana. Kai namiji ne, nima namiji ne kowa ya cigaba da gwada sa'arsa mai rabo sai ya ɗauka a cikinmu. Dan har yanzu banga dalilin da zaisa na iya janyewa ɗin ba”. “Haka kace?”. Murmushi RK ya sakar masa da kashe ido ɗaya kawai ya zagayesa ya bar wajen. Hakan ya sake hasala Yazeed matuƙa. Tabbas shi ɗin mutum ne mai haƙuri da dattako. Amma yana da tsananin kishi akan abinda yake so shiyyasa yake zafafawa akan al'amarin Maanal matuƙa. A zuciyarsa yake tunanin dolene ya koyama guy ɗin nan hankali, dan haka a daren yau zai wuce Kaduna dan gara ya zauna ayita ta ƙare shi da Daddy. Mamma dai ce matsalar zai rumtse ido kawai komai ma ya faru daga baya yasan zata sakko ta yafe masa..... Kiran daya shigo masa a wayane ya katse tunaninsa. Ganin ƙanwarsa Badiyya ce kamar zai share sai kuma dai ya ɗaga. Yana kai wayar kunnensa ya janye da sauri saboda abinda ta sanar masa.. Yana sauke wayar daga kunnensa sai kuma ga text massage ɗin Ammie itama ya shigo masa. Ai bai tsaya sauraren komai ba yabar asibitin...... _____________ “Wai Daddyn Yazeed mikake nufi da ni ne a gidan nan? Katafi kai da matanka holewarku bance komai ba, ka dawo ranar girkina kace baka buƙatar komai daga gareni. Na zuba maka ido nan ma, washe gari Basariyya tai girki ita jiyama haka. Yau kuma ƴar sonka ta amsa”. Idan kujerun dake falon sun motsa Alhaji Usman ya motsa kenan. Tamkar ma bai san da zaman Hajiya Yaya a falon ba yake kallon labaransa yana shan fruits da Ammie ta haɗo masa. Hakan ne ya sake sakata fusata, cikin matuƙar ɓacin rai ta ja remote ɗin dake a Centre table ta kashe tvn gaba ɗaya. Karo na farko ya juyo ya kalleta fuskarsa a matuƙar haɗe. Itama kallon nasa take tana huci. “Sadiyya bar falon nan kafin ranki yafi haka ɓaci”. Har cikin ranta taji tsoron fitar kakkausar muryarsa. Amma sai ta dake dan gara dai ayita ta ƙare. Itama a fusacen ta ce, “Babu inda zanje wlhy. Dan nifa na gaji da abinda ake min a gidan nan. Ubana ya dasa inuwa wasu banzaye suzo su zagayeta domin sha suna min gadara.” “Hummm”. Ya faɗa kawai yana miƙewa. Bedroom ɗinsa ya shige tare da rufo ƙofar ya barta a falo tana jidali ita kaɗai. Haka dama yake mata, ita kuma sai take ɗauka kamar tsoronta yake ji ko tafi ƙarfinsa ne. Bata san yana hakan bane kawai saboda wani dalilinsa daban, amma badan gorin da take masa ba akoda yaushe. Tsautsayi rabon faɗan nan ya koma kan Ammie sai gata ta shigo sashen batare da tasan Hajiya Yaya na nan ba. Aiko ina wuta Hajiya Yaya ta saka Ammie, nanfa ta shiga mata gori da cin mutunci. Ita dai Ammie komai batace da ita ba ta ajiye basket ɗin hannunta dake ɗauke da kayan abincin maigidan a saman d/table. Rashin tankawar da batai ba itama sai ya sake fusata Hajiya Yaya, a matuƙar zafafe ta nufi d/table ɗin da niyyar kifar da kayan abincin Ammie ta tare tana girgiza mata kai. “Kiyi haƙuri Hajiya kar kiyi haka dan ALLAH. Koba komai shi ɗin abincine, yana da darajar da wulaƙantashi kuskurene takowace irin fuska”. “To mama Asiya shawara kike bani ko umarni?” “Babu ko ɗaya da nake baki a ciki kiyi haƙuri”. “Anƙi ayi haƙurin munafuka kawai, kullum sum-sum ita a dole ta ALLAH amma dafinki yafi na baƙin kumurcin maciji. Kin mallake min miji da bin bokaye, kin cika mana gida da agololi har kina shirin ganin kin mannawa ɗana. Wlhy Asiya sai naga bayanki a gidan nan”. “Idan ta juya ba.....” Alhaji Usman daya fito ya faɗa a zafafe. Juyowa sukai su duka suna kallonsa. Fuskarsa a ɗaure ya cigaba da faɗin, “Idan ta juya kam zakiga bayanta Sadiyya. Amma kiga bayanta akan zama dani har gaban abada bazakiga hakan ba da iznin UBANGIJI. Asiya ajiye abinci, idan kin isa dan ALLAH ki zubar da shi ni kuma wlhy yau sai na baki mamaki irin wanda baki taɓa zato ko tsammani ba. Ke Sadiyya bafa wai ina tsoronki bane a gidan nan. Karki ƙureni a wannan karon wlhy idan ba hakaba zakiyi matuƙar dana sani.” “Dana sani na nawa kuma ai nayi dana sani tun daga randa na amince na aureka....” sai kuma ta fashe da kuka “Kai dai burinka kullum ka wulaƙantani a ƙasan ƙanwar bayana koma nace sa'ar ɗana ko, shike nan ga gidan nan na bar maka, ka kwaɗata ka cinye dan ALLAH” fuuuu ta fice daga falon. Tsaki yaja kawai tare da juyawa zai koma bedroom ɗinsa. Hankalin Ammie ne ya tashi, cikin sauri tabi bayansa, kusan a tare suka shigo bedroom. Jin yanda ta faɗo masa ya sashi juyowa yana kallonta. “Dan ALLAH ka bita karta tafi ɗin da gaske, na roƙeka Abban Hameed. Bana fatan kowacce matsala ta kasance tsakaninka da matanka a dalilin.....” “Asia!”. Ya faɗa cikin katseta. Kanta ta shiga girgiza masa sai ga hawaye. Zata sake magana kawai ya jawota jikinsa ya rungumeta. Sosai take bashi tausayi, mace ce mai haƙuri da juriya akan komai na rayuwa. Tana da kawaici da saurin sallamawa koda abu zai cutar da itane ko zuri'arta. Duk abinda kaga ta masa musu a kai to ka duba wannan abun kuwa. Komai yace ita mai biyayya ce a gareshi ko bai dace da ita ba. Wannan halayen nata ne suka mamayesa cikin ƙanƙanin lokaci yake jinta ƙololuwa a saman matan da ya aura tun yana da jajayen sawunsa. Hanata duk wata damar sake magana yayi, ba kuma ta sake yi ɗin ba ta haƙura saboda ita ɗin mai biyayyace a garesa. Fitowarsu falo babu jimawa tana zuba masa abinci sai ga Asalamiyya ta shigo tana kuka ita da Basirah. “Daddy dan ALLAH ka kazo ka hana Mamma tafiya. Gata can ta haɗa kaya zuwa mota zata tafi Daddy”. A birkice Ammie ke kallonsu, sai kuma ta yunƙura jikinta na rawa zata nufesu. Cikin bada umarni Daddy da tun kallo ɗaya da yay ma su Asalamiyyar bai sake ba ya dakatar da ita. “Asia koma ki zauna”. Kallonsa Ammie tai kamar zata fashe da kuka. “Daddyn Hameed kana fa jin abinda suke faɗa”. “Cigaba da zuba min abinci nace. Ku kuma ku bar falon nan!!!”. Ya ƙare maganar a tsawace. Zabura sukai saboda tsawar ta shigesu. Har rige-rigen fita suke daga fallon. Kallonsa Ammie ta sake yi zatai magana ya ɗaga mata hannu. Dole tai shiru ta cigaba da zuba masa abincin hannunta sai rawa yake. Tsaf yake kallon yanda hannun nata ke rawa amma sai bai tanka ba. Tana gama zuba masa abincin yaja ya fara ci hankalinsa kwance.. Abu ya ishi Ammie ta rasa ina zata kama, sai kallon Daddy kawai take. Can dai ta jawo wayarta ta shiga rubutama Yazeed text massage..... ______________★ Yau da wuri Nene ta dawo asibitin. Dan haka ta kora su Amaal gida suma saboda mijinta daya shigo Abuja. Daga nan ma asibiti da yazo ya duba Maanal ɗaukar Amal ɗin yay suka wuce masaukinsa. Itama Shahidah da mijinta yazo sai suka wuce kawai. Hakan yasa Maanal ta kasance daga ita dai Nene a ɗakin. Sai kuma duk kaɗaici ya isheta. Dan Nene da zaran tayi sallar isha'i zakaga ta fara gyangyaɗi abinta. Gashi babu waya a hannun Maanal

Chapter 8 of 17