Baki Maanal ta tura gaba da yin narai-narai da idanu zata sake sakin sabon kukan Ammien tai mata hararar wasa. “Kina sakin min kuka zan zaneki ne tas a ɗakin nan”.
A tare suka kwashe da dariya, dan yanda Ammie tai maganar sai ya tuna musu baya. Kai Maanal ta zuba fitina a rayuwarta, ga tsoron dukan masifa. Dan duk rashin mutuncin da zata zuba da Ammie tace zata zaneta take nutsuwa. Ammie data ji daɗin ganin damuwar tasu ta kau sai ta cigaba da jansu da hira. Idan ka gansu abin sha'awa kamar wata babbar yayarsu can ba mahaifiyarsu ba. Dan Ammie an mata aure da ƙarancin shekaru ne, kuma ALLAH ya bata haihuwan da wuri, shiyyasa idan baka sani ba sai ka ma ɗauka ba itace ta haifi su Shahidah ba, dan za'afi ganin Maanal a ƴar farinta kamar. Kamar wasa suka sha hira sosai sai da aka kira Magrib Ammie ta fita. Babu wanda ya sake tada batun auren Maanal ɗin har dare. Sun idar da salla Shahidah da Amaal suka shiga kitchen, yayinda Maanal ta nufi ɗakin Ammie dan tana son tambayarta gobe in sha ALLAHU da wuri zata fita gyaran jiki. Ta samu Ammie akan abin salla tana waya da mijinta, dan haka ta haye gadonta ta kwanta tana saurarenta. Sun jima kafin suyi sallama ta juyo ga Autar tata tana tambayar, “Mi kuma ya faru ƴar shagwaɓar Ammie?”.
Murmushi Maanal ɗin tayi, cikin yanayinta na miskilaye da shagwaɓa ta ce, “Ammie ina son naje gyaran jiki gobe in ALLAH ya kaimu, ban sani ba ko kina da kuɗi. Jibafa yanda jikina duk ya bushe ga kaina sai ƙaiƙayi yake mun”.
“Uhm ko bani da kuɗi auta ai dole na nemosu, ke idan fitinar gyaran jikin nan naki ya tashi ai duk fatarata baƙya raga min”.
Sosai Maanal takema zancen Ammien murmushi. Yayinda Ammien ke kallonta cike da jin daɗi, idan taganta cikin farin ciki haka daɗi take ji, sai ta dinga ganin asalin Maanal ɗinta ta baya sarkin rikici da kwaramniya, amma yanzu duk ta zama sanyi-sanyi ga miskilanci, sam bata son sabon yanayin nata na wannan shekarun, sai dai babu yanda zatai tana mata addu'a. Katse mata murmushin tai da faɗin, “Ke duba wayar nan taki tun ɗazun take haske alamar kira”. Amsa Maanal tayi da faɗin, “Inaga Zezaa ce ko Anees....” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda ganin number mai kiran, dan ko saving batai ba, amma nacinsa yasa tuni ta haddace lambarsa a kanta. Fuska ta ɗan tsuke, har zata maida wayar ta ajiye sai kuma ta dakata, dan tasan shegen nacinsa ba lallai ya barta ba idan bata ɗaga ɗin ba. Inda Ammie take ta ɗan kalla, ganin hankalinta baya kanta ta ɗaga tana mai kai wayar kunnenta. Can ƙasan maƙoshi cikin muryar nan tata mai zurfi da rashin sakewa tai sallama. Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar RK da ga can, dan haka ta taɓe baki kawai.
“Baby duk kin saka hankalina tashi. Ai da nace idan nayi kira dubu baki amsa ba komai dare zan sake kamo hanyar Kaduna ne”.
“Hummm” kawai tace a taƙaice tana ɗan satar kallon Ammie. Ganin ita take kallo yanzu sai ta ɗan sake ɓata fuska. Yayinda kunenta ke sauraren RK dake magana cikin kulawa da tambayarta ta samu gida lafiya. Cikin sake maida muryarta ƙasa sosai ta ce, “Alhamdullah ina yin abune”.
Ɗan jimm yay na damuwa da nuna ƙosawa da shi da tai, koda yake yau an samu cigaba ma ta ɗaga wayar ai. Dan haka yay guntun murmushi da har tana iya jin sautinsa tare da furta, “Okay bari na barki. Amma Please anjima na kira to?”. Da sauri ta ce, “Uhm-uhmm”.
“Why?”.
Ya tambaya kamar zai yi mata kuka. Banza ta masa. Dan ta matuƙar gajiya da shi. Sake haɗa ido da sukai da Ammie ya sata yanke wayar tama kasheta gaba ɗaya tana wani sake tsuke fuska. Shifa wannan mutumin ta kula sai ta masa fatattakar karan mahaukaciya zai ƙyale rayuwarta ta huta shima yaje ya hutama ransa. Bai san yanda tai matuƙar tsanar maza bane a duniyarta ta yanzu daya kama kansa tuni. Amma ba komai, tunda yanzu tabar garinsu tana da damar da zata buga masa warning na ƙarshen ƙarshe da kakkaɓesa daga jikinta gaba ɗaya, yama barta taji da matsalar gabanta...
“Tunanin mi kuma kika tafi?”.
Ammie tai maganar tana taɓata. Ajiyar zuciya ta sauke da ɗan laɓe lips ɗinta tana kaiwa zaune kusa da Ammien. Kwantar da kanta tayi a kafaɗarta tare da rungumota. Cikin son kauda wancan yanayin ta ce, “Ammie yau tare da ke zanyi barci nayi kewarki”.
Murmushi Ammie tai da kai hannu ta shafa ƙyaƙyƙyawar fuskarta. “Nima nayi kewarki Auta. Amma babu yanda zanyi tunda wataran ma inaji ina gani gidan miji zaki wuce ki barni”.
Tsam ta miƙe batare data ce komai ba ta ɗauki wayarta ta fice. Da kallo kawai Ammie ta bita. Wani irin tausayinta da ƙaunarta na sake ratsa mata zuciya. Miƙewar tai itama ta fito. A kitchen ta samesu su dukansu har Manaal ɗin. Ta ɗan duba abinda suke dafawar ta fita ta barsu. Yanzun ma a tare sukaci abincin daren bayan sun kammala. Suna tsaka da ci sai ga Yazeed ya shigo sashen. Duk gaisheshi sukai bayan shima ya gaida Ammie, yayinda Maanal tai kamar bata gansa ba tanata wasa da spoon a cikin abincin. Shiko hankalinsa duk yana kanta, duk da dai magana suke da Ammie wadda su Maanal ɗin basa jin mi yake faɗa mata. Bai wani jima ba yay musu sai da safe ya fita. Wata ƴar ajiyar zuciya Maanal ta sauke a hankali. Babu wanda yay mata magana sai ma Ammie data shiga musu bayanin da Yazeed ɗin ya mata. Ashe zasuje Zaria ne gobe idan ALLAH ya kaimu ita da shi halartar wani ɗaurin auren ƴar abokin maigidan. Sunyi addu'ar ALLAH ya sanya alkairi su duka. Sai kuma ta ɗora da faɗin Maanal ɗin ta shirya sai ta mata rakkiya ita da Amrah dan shi Yazeed ɗin zai rigasu tafiya ne da abokinsa. Ɓata fuska tayi zatai magana Ammie tai mata daƙƙuwa. “Sai fa kinje daddawar gida da bata son fita”.
“Nifa Ammie ba cewa zan bazanje ba. Amma gyaran jikina fa?”.
“Ki tashi da wuri ayo miki, tunda sai sha biyu ma zamu wuce in sha ALLAHU ”.
Badan taso ba dai ta amsa da to, dan taji Yazeed shima zai je. Sai dai sauƙinta tafiyan nasu ba ɗaya bane...
Kamar yanda ta faɗa a ɗakin Ammie tai kwanciyarta manne da ita kamar za'a ƙwace mata ita ko wata ƴar goye can. Dan da Ammien ta tashi sallar dare ma da ƙyar ta ɓangare ta a jikinta. Bata kuma jima da fara sallar ba itama Maanal ɗin ta tashi tayo alwala. Haka take itama akwai yawan ibada kamar Ammien, dan ko sanda take tashen rashin jinta dama Maanal akwai son addini, tun bata kai girma ba zatace zatai azumin litinin da Alhamis, ko an hanata kuma sai tayi sai dai ta kaisa a galabaice. Kusan ƙarfe uku da rabi barci ya fara rinjayar idonta, addu'a tayi ta koma saman gadon ta kwanta tabar Ammie anan.....
Koda suka idar da sallar asubahi ma sake hayewa gadon tayi tai kwanciyarta, dan barcine sosai a idonta, sai kuma jikinta dake mata kamar babu daɗi. Da ƙyar Ammie ta tasheta wajen ƙarfe takwas akan ta tashi ta shirya taje gyaran jikin nan, idan ba hakaba sai dai ta bari sai gobe idan ALLAH ya kaimu dan babu fashi da ita za'aje Zaria. Dole ta tashi badan taso ba ta kimtsa. A falo ta samu ƴan uwanta suna hira da karyawa, saboda saurin da take gaishesu kawai tayi ta haɗa shayi a wani gora mai ƙyau na ƴan gayu ta wuce tana faɗa musu saita dawo.
Tsokanarta suka shiga yi akan ko gayyata ma babu. Ta fice tana faɗa musu susha zamansu baza'a cinyema Ammie kuɗin account ɗinta ba. Idan kuma suna da kuɗi su taho. Babu kowa a harabar gidan sai masu gadi su biyu da mai bayin fulawoyi daketa yi, da alama sauran ma'aikatan duk sun kammala nasu aiki sun wuce. Dan dama mai sharan tsakar gida ne da mai wanki. Kamar yanda ta saba cikin girmamawa ta gaidasu, suka amsa mata da kulawa da tambayarta gajiyar tafiya. Koda ta fito tana kallon titin da fatan samun napep da wuri dan gidan nasu a bakin titi yake sai kawai idonta akan Yaya Yazeed dake tsaye jikin motarsa yana waya, sai dai shima idonsa a kanta. Sai da gabanta ya faɗi, amma sai ta dake tana ambaton sunan ALLAH. Tafiya ta farayi a ƙafa tana mai fatan zuwan napep yanzu, sai dai ko taku goma batai ba taji horn a bayanta. Sosai ta rumtse idanunta tare da cije lips, sai kuma ta sake ɗaga ƙafa zata cigaba da tafiyarta ya ɗan sha gabanta da motar tare da sauke glass ɗin. Cikin gizagonsa da tsare gida ya furta, “Wai nikam yaushe raini yay ƙarfi tsakanina da ke haka Maanal?”.
Fuska ta ɗan sake tsukewa da juyowa ta kallesa. “Toni Yaya minai maka na raini?”.
Cikin tsareta da kaifafan idanunsa ya ce, “Oh bama ki sani ba ko? Zan gyara miki zama ne. Ina zaki je da wannan safiyan haka?”.
(Kama gyaran tsaiwa ba zama ba) ta faɗa a ziciyarta. A fili kam sai ta amsa masa da, “Nan zanje kusa wankin kai”.
“Okay, bismillah shigo na ajiyeki”.
Baki ta buɗe zatai magana ya harareta. Dole ta shiga hankalinta dan tasan halinsa shi baya son wargi. Zagayawa tai ta ɗayan side ɗin da har ya buɗe mata, haka ta shiga tana ƙunƙuni cikin ranta. Jan motar yay suka cigaba da tafiya yana wani shegen tuƙi a hankali kamar baya so, zatai magana wayarsa ta shiga ƙara alamar kira. Ɗaga wayar yay ya saka a hansfree tare da yin sallama. Daga can aka amsa masa da faɗin, “Oga kayi haƙuri ka jini shiru jiya da nace zan kira”.
Amsa masa yay da, “Eh ai harna shaƙa ma. Dan yanzu kamar ma bazan ɗaga kiranka ba dai na daure na ɗaga ɗin. Kasan ni bana son wasa da abu mai muhimmanci Hashim”.
“Na sani oga kayi haƙuri. Wlhy ina gaya maka sai kusan 2 na samu ganawa da AA ɗin. Shima mintuna ashirin ya yarda zai ganni da ƙyar da taimakon yaron nan nasa da nake gaya maka cousen ɗina ne”.
“Mtsoww! Mutumin nan fa na lura ɗan wulaƙanci ne Hashim. Kodan yaga muna buƙatar kayan nan yake ta garamu haka ne? Shi ana tattalin customers shi yana yanƙwana mutane”.
“Tom oga sai dai haƙuri, sai dai kuma ni yanda na fahimcesa kamar ba wulaƙanci bane ba. Yariga da yayi ƙarfine sosai. Dan wlhy manyan ƙasashen Larabawa nan yake huɗɗa dasu sosai. Kai harma turawan tako'ina kayansu shiga sukeyi. Gashi abin mamaki yaro ne ƙarami dan indai bakuyi shekaru dai-dai ba to kai zakama iya girmarsa wlhy. Amma yana da wayo da ban mamaki. Yanzu dai na taƙaice maka batu ya bamu damar haɗuwar da shi a cikin Companyn *_MAWAAD_* ɗin. Ya kuma tabbatar min da in dai mukabi ƙa'idar komai daya dace zamu dinga samun kayan nasu fiyema da yanda muke buƙata”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi da faɗin, “Alhamdulillahi Hashim naji daɗin wannan labari. Kaga an gama da wannan matsalar kenan. Nasan Daddy ma zaiji daɗi sosai abu kusan shekara munata fama”.
“Wlhy kuwa oga ai dole ai farin ciki. Yanzu dai na tura maka komai ta email sai ka duba”.
“Okay ba damuwa zamuyi magana”. Daga haka ya yanke kiran tare da juyowa yana kallon Maanal da duk ke sauraren wayar tasu amma a zahiri hankalinta nakan wayarta tana duba saƙon da RK ya tura mata.
“Madam!”.
Ya faɗa a hankali cikin katseta. Jitai kamar ya dakar mata zuciya da guduma. Amma sai ta daure ta amsa da faɗin, “Kai yaya minene kuma wata Madam?”.
Ɗan dubanta yay yana murmushi mai ƙayatarwa, sai kuma ya maida hankalinsa ga titin yana faɗin, “Ai Madam ɗin ce. Kwana nawa ya rage kuma Manaal. Ke yanzu a yanda muken nan bakiji inama ace mu ɗin ma'aurata bane?”.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣8️⃣
______________
Assalamu alaikum
Ina Neman mutane 20 dazasuyi register da company 52u a karkashin link Dina akan $21 wato 35k a kudin mu na Nigeria account din zaibude a cikin 5-6 weeks idan account din yabude nikuma nayi alkawarin zanbiya mutum 20 dinnan salary 10k kowani mutum na tsawon wata 5 kunga riba biyu kenan kuka samu ga ribar kudin ku yadawo harda riba ga account din kun na 52u zanbude a wata na shida sai kudin ga kwasa duk kudin ku duk wata 💃🏽💃🏽💃🏽mai ra,ayi yamin magana
https://chat.whatsapp.com/K0ECLn6O3WS1fnfCggOeu5
08083531881
______________
.......Shirun da tai na kusan minti biyu batare data amsashi ba ya sashi ɗan kallonta. Kanta tai saurin kaudawa tana mai ƙoƙarin haɗiye ɗacin daya mamayeta. Shima sai ya ɗauke kansa bai sake magana ba. Babu jimawa suka iso gaban gidan da take zuwa gyaran jikin, wanda yasani ne tuni saboda yanda take ma'abociyar zuwa gidan kusan duk ƙarshen wata. Jikinta har tsuma yake nason ta fita a motar, dan bata so ya sake mata wata magana amma sai taji motar a ɓame alamar ya saka luck. Dole ta ɗan dakata tana rumtse idanunta. Sai kuma ta juyo ta dubesa, ganin shima ita yake kallo ta maida kan ta duƙar. Murmushin ya sake saki kaɗan da ɗauke idanunsa a kanta cikin son basar da yanayin ke bashi a jikinsa. “Ki tayani murna?”.
Batare data sake kallonsa ba ciki-ciki ta ce, “Tami?”.
“Akan albishir ɗin da akai min yanzu a waya. Mutumin nan kusan shekara guda kenan muna son haɗa Bussines dashi amma ko ganinsa ya gagara a gareni. Amma yau kinji har zan samu ganinsa, nasan Daddy zaiji daɗi akan hakan shima matuƙa”.
Karo na farko tai ɗan murmushi. Sai kuma ta ce, “ALLAH ya tabbatar da alkairi a haɗuwar taku to”.
“Amin ya rabbi dear. Ammafa nasha wahala sosai. Mutumin ya riga yayi nisa ne matuƙa saboda yanda yake huɗɗa da manyan mutane na wajen ƙasar nan dama cikin gida Nigeria. Nasan dai bazaki rasa jin Mawaad ba”.
“Ina dai ganin sunan Companyn a jikin buhunan shinkafa, ban sani ba ko sune ko kuma da banbanci”.
“Yes sune. Dan yana harkar noma yanzu matuƙa a ƙasar nan. Kuma Kinga wannan harkar ma bai wani jima da farata ba. Amma da yake ALLAH ALLAH ne cikin ƙanƙanin lokaci nan ma yayi zarra.”
“ALLAH sarki”. Kawai Maanal tace dan bataga ma'anar bata wannan labari ba ita kam da dam bata da alaƙa da shi. Cikin marairaicewa ta ce, “Yaya bara naje kada na makara Ammie tace zamu rakata anguwa”.
Amsa mata yay da “Okay bari na barki ki wuce. Inata baki labarin abinda bai shafeki ba, haka nake buƙatar rayuwata Manaal, wato iyalinna su dinga sanin komaina dan su kasance masu min addu'a. Dan haka sai ki shirya, dan zaki dinga raba farinciki da mijinki hakama akasinsa idan ya gitta” ya ƙare maganar yana miƙa mata atm card ɗinsa. Kanta ta girgiza masa da sauri. “A'a yaya ga Ammie ta bani nata zanyi amfani da shi. Hararta ya ɗan yi da zare atm ɗin Ammien ya ajiye mata nasa a cinyarta. “Kiyi amfani da na mijinki, dan nike da hakkin hakan ba Ammie ba. Idan kin kammala ki kirani dan ba nisa zanyi ba”.
Yanda ya tsatstsareta da ido yasa ta kasa magana. Dole ta buɗe motar ta fita dan shi in baiso wasa ba dole kaji shakkarsa. Bai bar wajen ba har saida yaga ta shige. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da jingina jikinsa da kujera yana mai lumshe idanunsa. Ya jima a hakan dan yaci kusan mintuna biyar kafin ya tada motar yabar wajen yana mai danne abinda ke tsikarar zuciyarsa game da ita.....
★★★
Yanda Maanal ta samu tarba a ciki zai tabbatar maka akwai shaƙuwa da sanayya sosai tsakaninta da mai gyaran. Dan duk miskilancintan nan sai murmushi take da ɗan maidama mai gyaran hiranta dan tana mata tambaya ne akan Jos. Basu wani jima ba aka fara gyaran saboda tun jiya ta sanar mata. Kafin tazo ta haɗa komai. Gyara sosai jikinta ya sha. Ga turarruka kamar wata amarya. Hatta kanta da ƙafafunta zuwa farce an musu ƙal. Haka Maanal take akwai son gyara jiki, ƴar gayuce sosai da son kwalliya, sai dai yanzu yanayi yasata ɓarar da kwalliyar gefe gyaran jikinta da tsafta ne dai tana nan da abinta akoda yaushe. Sun gama a ƙurarren lokaci, dan har Ammie na kiranta a waya ma. A gurguje ta bata ta cire kuɗin aikinta tare da amso kayan ƙamshin data haɗa mata suka fito zata mata rakkiya. Turus taja ta tsaya da ganin motar Yaya Yazeed a ƙofar gidan, kafin ma ta samu abin faɗa ya buɗe mata gefensa alamar ta shigo. Ganin fuskarsa babu wasa sam yasa batai magana ba ta shiga kawai. Sallama sukai da mai gyaran bayan ta gaida shi ya amsa mata ciki-ciki yaja motar suka wuce. Shiru motar har sun ɗan yi nisa a tafiyar cikin ƙarfin hali ta ce, “Yaya dama baka wuceba ne?”.
“Mi kika gani?”.
Ya faɗa cikin wata irin kasalliyar murya data bata mamaki. Gashi yaƙi kallonta sam a yanzu. Itama sai kawai ta ce, “Ba komai”.
Bai sake magana ba, itama tai shiru har suka iso gida. Sai da ya gama parking ta miƙa masa atm ɗin tana godiya. Kansa kawai ya ɗaga mata batare daya kalleta ba ko tankawa yanzu ma. Itama sai kawai ta buɗe motar tai ficewarta. Da Hajiya Yaya dake daga can ƙofar sashensu da wata baƙuwa suka haɗa ido, ganin irin kallon da suke mata yasa duk ta tsargu, amma sai ta dake ta nufesu badan taso ba, sai dan mahaifiyarta ta mata tarbiyya na girmama duk wanda ke gaba da ita. Sannan kodan Yaya Yazeed dake iya ƙoƙarin sa na girmama Ammie zata iya shanye komai daga mahaifiyarsa itama.
“Tofa, kice agola kafi ɗan masu gida an dawo kenan?”.
Matar da suke tare da Hajiya Yayan ta faɗa cikin yamutse fuska idonta akan Maanal dai-dai tana isowa inda suke. Wani harbawa zuciyarta tayi har tsakkiyar kanta. Ba wai yau ne karo na farko da aka fara kiranta da sunan AGOLA gidan ba, amma har yanzu ta gagara sabawa. A duk sanda aka kirata da shi kuma tana jin matuƙar ɗaci da zafi a ranta. Har takanyi yunkurin son barin gidan, sai dai yinƙurin nata baya zuwa ko'ina take komawa tai laƙwas saboda wasu dalilai. Hawayen da suka cika mata idanu ta haɗiye, tare da dai-daita kanta sannan ta ɗan risina fuskarta da murmushi ta ce, “Barka da gida Mamma. Aunty ina yini”.
Kafin Hajiya Yaya ta amsa wadda ta kira da aunty ɗin ta sauri ta cafe zancen cikin masifa, “Oh kaji wani ɗan iskan gaisuwa wai barka da gida sai kace wasu sa'oinki?”.
Cikin sake hasala Hajiya Yaya ta ce, “Kinga da yawa ai, idan batai iyayi ba ai bata cika jinin Asiya ba, Amma wai a haka Alhaji ke neman ƙaƙabama jinina ita”.
“Humm kar kiga laifinsa wlhy Yaya, tunda uwarta ta shanyesa kina ganin shima Yazeed ɗin zasu barsa ne. Balle suna ganinsa shine gidan da uban gaba ɗaya”. ta faɗa tana mai ballama Maanal wata shegiyar harara.
Tsamm Maanal ta miƙe kafin Hajiya Yaya ta bama ƙanwar tata amsa. Cikin ɗan sassarfa tabar wajen tana mai jin ɗaci da ciwo sosai a zuciyarta game da cin mutuncinsu ga Ammien ta. Tarasa mi Ammie ta tsare musu a gidan da su duka basa ƙaunarta...
Shikam Yazeed tana fita ya kife kansa a saman steering yana mai cije bakinsa da masifar ƙarfi. Kai bazai yiwu ba, dolene ya zigirgiɗi Daddy azo ayita ta ƙare a bashi matarsa. Dan gaskiya yana cikin tashin hankali, da yasan ma abinda gyaran jikin nan zai zame masa yanzun nan daya hana yarinyar nan yinsa ko kuma yaƙi komawa ɗakkota. Ɗan buga glass ɗin saitinsa da akai da ɗan ƙarfi ya sashi ɗagowa. Sai da ya ɗan saisaita kansa kafin ya sauke glass ɗin. Da Hajiya Yaya yaci karo, ai da sauri ya janye idanunsa da sukai wani irin kaɗawar da duk mai hankali idan ya kallesa zai fahimci halin da yake ciki. Ita kanta Hajiya Yayan sai da taji wani iri a ranta, amma ta dake cikin masifa ta ce, “Yazeed miye haɗinka da waccan yarinyar? A ina ka ɗakkota?”.
Ɗan gyaran muryarsa data koma can ƙasa yayi, kafin ya furta, “Mamma anan ƙofar gida ne mai napep ya ajiyeta shine nace ta shigo na ƙaraso ciki da ita. Wani abu ne ya faru?”.
Wata hararar bana son rainin wayo ta balla masa. Kafin cikin masifarta ta furta, “Yazeed! Yazeed wlhy ka kiyayen, ni zaka maida sakarai ko....”
“No Mamma ba hak....”
Hannu ta ɗaga masa cikin tsawa, “Bana son ji, ka sameni ciki yanzun nan”. Tana gama faɗa ta juya ta bar wajen. Iska mai kauri ya furzar daga bakinsa tare da sake maida kansa jikin steering yana mai lumshe idanunsa. Yafi mintuna biyar a haka sannan ya buɗe motar ya fita yana mai saka glass a idanunsa domin ɓoye abinda ke cikinsu. A falo ya sami mahaifiyar tasa da ƴar uwarta. Cikin girmamawa ya gaida innar tasa dake wani binsa da kallon ƙurilla kamar mai son gano halin da yake a ciki batare data amsa masa gaisuwarsa ba ta ce, “Yazeed! Anya kuwa kana son nemawa mahaifiyarka mutunci damu ƴan uwanta a gidan nan. Wai kai bazaka bar batun yarinyar nan ba ne shin ko yaya kake nufi?”.
Sai da ya ɗan haɗiye abinda ke masa yawo a maƙoshi sannan ya furta, “Aunty Please mun wuce maganar nan fa tuni. Dan ALLAH a barta kawai”.
“Anƙi a bari ɗin dan ubanka. Yazeed ni dai kake son cigaba da tozartawa ko? Ni dai mahaifiyarka dana sha baƙar wahalar rainon ciki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 17