ya fito yana sanarma RK oga yace ya shiga shi kaɗai. Murmushi kawai RK yay da ɗan girgiza kansa. Kafin ya matsa inda Maanal take zaune dan shi dama yana daga tsaye ne.
“Kinga ina zuwa. Minti biyar kawai”.
Kanta ta jinjina masa batare da nuna damuwar da yay tsoro ko ɓacin rai daga fuskarta ba. Daga haka ya wuce ita kuma ta ciro novel ɗinta daga bag ta cigaba da karatunta. Shima Assistant ɗin barin Office ɗin yay da alama akwai inda zaije. Kusan mintina huɗu sai gashi ya dawo. Mazauninsa ya koma ya zauna bayan ya ajiyema Maanal ruwa da lemo. Baice mata komai ba itama batama kulashi ba balle kallon abinda ta ajiye. Tana nan a zaune fin mintuna goma sannan RK ya fito. Zama yay a kusa da ita yana bata haƙurin daɗewarsa. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Ba komai”. Ta maita hankalinta ga book ɗinta. Shima dai wayarsa aka kira, dan haka ya miƙe ya fita aka sake barinta ita da Assistant. Suna nan a haka wani ɗan abu dake desk ɗinsa yay ƙara, miƙewa taga yayi ya nufi hanyar officer ɗin ogan kamar yanda suka faɗa. Bai wani jima ba ya dawo, cikin mutuntawa yace mata ta taso suje. Littafinta ta saka a bag ta miƙe batare da tace dashi komai ba. Ta wani elevator ba wanda suka shigo ita da RK ba suka shiga da Assistant ɗin, cikin sakanni ya saukesu inda suka nufa, koda suka fito nan ma sai taga offices ne a wajen. Sun shiga wani waje da alama ta nuna conference room ne, sai dai bai ƙarasa da ita can ciki ba ya nuna mata wajen zaman daga nan ta inda aka shirya kamar masauƙin baƙi. Tana zama wata ta kawo kofin coffee ta ajiye mata da drink. Atare suka bar wajen ita da Assistant ɗin sai ita kaɗai kenan. Babu abinda ta taɓa ta sake ciro novel ɗinta ta cigaba da karatu......
Fin tsahon mintuna talatin tana a wajen babu wanda ya sake zuwa, har ranta ya ɗan fara sosuwa sai ga wasu mutane uku sunzo sun gittata sun shiga conference room ɗin, tsakanin inda suka bin da inda take akwai ƴar tazara, shiyyasa bata wani shaida kowa ba. Bayan shigewarsu fin mintuna biyar wasu biyu suka sake wucewa, kasancewar bata ɗago ba a yanzu sai da suka gama shigewa taji motsin rufe ƙofa. Ƴan mintuna kaɗan Assistant ya zo wajenta yace ta shiga. Kanta kawai ta jinjina masa tare da maida book ɗinta a bag ta miƙe. A ranta tana mamakin wannan abu kamar wulaƙanci, ana tattalin ɗaukar ma'aikaci da alama su nan yanga sukeyi. Da wannan tunanin ta tura glass door ɗin a hankali ta shiga da sallamar da bata tunanin zasuma iya jinta saboda yanda ta yi ta ciki-ciki, dan wani irin bugawa ziciyarta ke mata da sauri-sauri da batasan dalili ba, amma haka ta danne tana ƙarama zuciyar tata ƙarfi. Sai dai kuma da alama sun ji sallamar tata ɗin, dan wasu a cikinsu sun amsa. Taji hakan ne a bayyane dan ba kallonsu take ba su duka. Sai da ɗaya a cikinsu ya furta, “Bismillah zaki iya zama”. Sannan ta ɗan ɗago ta kallesu tana mai jinjina kanta zuciyar tata dai na cigaba da bugu.
Mutane ukun dake fuskantar inda zata zauna kawai ta iya ma kallo cikin sakan biyu. Wanda ke zaune kuma a kujerar dake gefen inda take bata ko kallesu ba. Sai kujerar dake tabbatar da oga kan zauna yayin meeting shima bata wani dubesa ba. Shima kuma kansa a duƙufe yake yana duba wani magazine kamar ma bai san da zaman kowa ba a wajen. Kujera ɗaya taja ta zauna zuciyarta na mamakin ai mutane biyar kawai taga sun shigo, ya akai taga kusan takwas anan?, rashin mai bata amsa ya sata shiga gaidasu. Amsa mata duk sukayi, sai dai bata jin shi wancan ya amsa ɗin. Shiru kamar na mintuna biyu kafin ɗaya a cikinsu ya fara mata tambaya. Babu ko ɗar a tare da ita ta amsa masa. Kansa ya jinjina sosai dukansu suna mamakin ta. Wanda ke tsakkiyar sa shima ya sake jeho mata tasa tambayar. Nan ma ta sake amsawa babu ko wani ɗar. Dukansu kam sai da suka sake dubanta wannan karon saboda jarumtarta da kaifin basira da suke kallo a bayyane, sai dai abinda basu sani ba dannewa kawai takeyi, dan tana cikin wani hali da ita kanta ta gagara bashi fassara. Gashi a masu mata interview ba wai baƙaƙenmu bane balle ma ace hausawa. Hausawa biyu ne ma kawai a cikinsu sai CEO ɗin da har yanzu bataga fuskarsa ba. Amma dai hannunsa dake saƙale da wani shegen Designer agogo da zoben dake neman harmutsa tunaninta na azurfa ya nuna bakin fata ne duk da kallon fisha tai masa kawai.
Na ukunne da baice komai ba tun ɗazun a yanzu cikin turancinsa mai fita da harshen Chinese ya furta “Woow, You are amazing young lady”. Sai kuma ya shiga tafa mata. Suma sauran tafa matan suka farayi suna mai kallon boss ɗin nasu da har yanzu bai tanka ba baima maida hankalinsa a kansu ba yanata duba magazine ɗinsa hankali kwance. Ganin dai bashi da niyyar kulasu suka haƙura suka daina. Sun bata takarda da kayan aiki tai zanen agogo a take anan, zanen da yay mugun basu mamaki da ƙaryatar dasu. Daga haka File suka tura mata da mata bayanin zata cike tai singing a take anan. Bata musa ba taja file ɗin gabanta. Ta ɗan dudduba abinda ke cikinsa kafin ta shiga gudanar da dukkan abinda suka buƙata zuciyarta na mata wani irin sanyi ƙalau dan kuwa dai sun tabbatar mata da ɗaukarta aiki ne. Acan ƙasan ranta kuwa tana mamakin nasu tsarin. Daga interview a take a wajen kuma babu batun kaje ka jira sai a tabbatar maka da an ɗaukeka aiki. Haka dai ta gama cike komai tana zancen zucinta ta basu. Bayan sun dudduba suka miƙama ogan nasu da sai a yanzu ya ajiye magazine ɗin ya fara duba file ɗin.
A karo na farko oga kwata-kwata da yay kamar bashi nan a wajen ya ɗago kansa bayan kammala duba komai na file ɗin, cikin wani irin dakewar murya ya jeho mata tasa tambayar data tilastata kallonsa. A yanzu ba bugun zuciya kawai taji ba, zuciyar tatace gaba ɗaya zata iya cewa ta tarwatse a dalilin kallon ido cikin ido da sukaima juna. Suma, ɗaukewar numfashi, ko gushewar hankali ko tsatstsagewar zuciya batasan yanda zata kira yanayin data tsinta kanta a wannan lokacin ba ma.........✍️
_Tofa jama'a mi kuma ke shirin faruwa anan?. CEO na Mawaad Company da Maanal? Kumuje zuwa wasan na ainahi ma yanzun ne zai fara a duka ɓangarorin😆 in sha ALLAHU 😉👌_.
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣3️⃣
........Fin mintuna biyu sunama juna kallon tsakkiyar idanu babu ko ƙyaftawa, yayinda sauran sukai kasare suma suna kallonsu da mamaki. Da wani irin shegen salo CEO ɗin nasu ya juya mayan oily ayes ɗinsa masu matuƙar haske kamar madara dake cikin haɗaɗɗen siririn farin gilashi tas tare da kauda fuskarsa gefe yana mai furzar da wani irin huci. Sai kuma ya sake dawo da idanun nasa a kanta cike da barazana da isa da basarwa ya furta, “Miss Maanal! Answer my question”.
Duk da cikin nutsuwa da sassanyar murya yay furucin, sai Maanal ta dinga jin kalaman ɗaya bayan ɗaya suna mata wani irin amsa kuwwa da tartsatsi a cikin kunne, acan kuma sama ƙololuwa. Ga wani irin sanyi yana saukar mata a gaɓan jiki da ƙasusuwanta tamkar yanayin yammaci ko safiya a lokacin tsananin hunturu irin na ƙarshem Janairu ɗin nan.
“You are not serious Miss Maanal”. Ya faɗa cikin gizago da nutsatstsen sauti mai cike da aji yana mai ɗan buga desk ɗin da yatsunsa biyu. Firgigit Maanal ta dawo a hayyacinta tamkar wadda aka farkar da ga barci. Sai dai har yanzu sanyin nan na cigaba da ratsata tun daga saman kai har yatsun ƙafafu. Sam bata san ta yanda akai ta buɗe lips ɗinta cikin dakiya da tarin nutsuwa ta bashi amsar tambayar tasa ba. Har lokacin kuma idanunsu na a cikin na juna. A karo na biyu shine ya sake kauda kansa. Sai kuma ya ɗan yamutse fuska da ɗaureta yana maida hankalinsa a kan sauran da sukai jugum-jugum suna kallon ikon ALLAH. Duk da kuwa wannan ba sabon abu bane a wajensu. Ƴammata da yawa a cikin Companyn nan sun jima da mutuwa akan boss ɗin nasu. Hakama masu shigowa domin bussines suka shiga fiye da irin yanayin da Maanal ta tsinta kanta a yanzu. Bakuma wai dan ogan nasu yafi sauran maza bane, badan yafi kowa ƙyau da iya ado bane, badan yafi kowa dukiya da cikar kamala bane. Kawai dai ALLAH ya bashi farin jini da wani irin kwarjini da ko su kansu mazan yana cika musu waje duk da kasancewarsa yaro matashi da bai wuce 30+ ba a duniya. Boss ɗinsu nada wasu qualities da mata da yawa ke buƙata a tattare da mazan zamani na wannan ƙarni. Duk da dakewarsa da kamewa da ƙasaita hakan bai hana ƴammata kawo masa hari ta kowacce kusurwa ba. Koda yake kuɗi fa babu abinda basa saka matan wannan zamanin, kai Bama mata ba kowafa a wannan ƙarnin ya koma girmama matsayin bawa da abinda ke a hannunsa ne kawai. Sai kana motsi akeyi da kai, sai ka zama wani ake girmamaka da son raɓarka. Da zarar baka dasu ko sun bar hannunka sai kaga kowa ma ya janye jikinsa an zubar da kai a kwandon shara saboda dama can ana maka soyayya da girmamawar ne saboda kana amsa sunan wane....
Miƙewarsa ta saka tunaninsu katsewa. Document ɗin ya tura gabansu tare da miƙewa da ƙyau yana haɗe rigar suit ɗinsa ya saka botirin dake jikinta ƙwaya ɗaya tak. Batare da ya sake kallon inda Maanal take ba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Zata fara aiki damu gobe in sha ALLAH”.
Daga haka ya fice abinsa cike da takun mazantaka da ƙasaita har ma da gayu na matasan samarin wannan zamanin musamman irinsa da ke ji da kansu da MANDA A GIDAN SANYI😉😂👌....
___________★
A lokacin da anan Maanal ke Maawad company domin yin interview acan Kaduna su Daddy ne ke shirin miƙa kuɗin auren Yazeed ga mahaifin Nazeefa ɗiyar Aunty Sabuwa saboda matsawar Hajiya Yaya akan al'amarin. Ganin abin na neman zama wata fitinar kuma a tsakaninsu Ammie ta saka baki tanata roƙon Daddy dan yace shifa sai ƙarshen shekara. Da ƙyar dai ya amince za'a kai ɗin bayan ita kanta Ammien ya gaya mata baƙar magana. Duk da abin yay mata zafi sai tai murmushi kawai ta ƙyalesa.
An kai kuɗi inda suka samu tarba ta musamman kamar wasu bare. Dan abin har mamaki ya bama Daddy ɗin. Amma dai sai ya danne kawai akai gaisuwar mutunci. Dana shi ne da amininsa Alhaji Sunusi na Zaria. Sai maƙwafcinsa Alhaji Isa da wani abokinsa Alhaji Sulaiman. Abinda ya sake ɗaure musu kai ana maganar tsaida date caraf mahaifin Nazeefa yace ai wata ɗaya ma ya isa. Dan shi a shirye yake dama. Kallon kallo aka koma yi a tsakanin su Daddy, sai dai babu wanda yace komai sai Alhaji Isa ne ya ce, “Amma Alhaji kodai a ɗan ƙara, ko kuma shi Alhaji Usman ɗin aji ta nashi ɓangaren”.
Caraf yace, “Alhaji bazaka gane ba, yanzu idan ƴarka ta samu miji ba'a sanya wlhy, mu da Alhaji Usman ai duk ɗaya ne. Kawai a taimakeni ayi a hakan, kai ko auren ne a ɗaura to daga baya sai ayi bikin”.
Rasama abin cewa sukai su duka. Sai Daddy ne ya ɗan girgiza kansa kawai. Sai kuma ya gyara zamansa tare da faɗin, “Shike nan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Amma bayan wannan ɗin shi yaron akwai wata kuma, itama idan anyi an gama kamar nan da watanni biyar haka sai ayi nata. Naso ma ayi gaba ɗaya ne a huta sai kuma larura ta gitta, to shi ciwo ya wuce komai a rayuwa shiyyasa aka ɗan ɗaga natan za'a fara shi wannan ɗin”.
Ɗan jimm Baban Nazeefar yayi, sai kuma zuwa can ya saki guntun murmushi da faɗin, “Babu damuwa Alhaji Usman, ai duka gidane tunda itama ɗin dai ta gida ce. ALLAH ya kaimu lokacin”.
Da amin duk suka amsa baki ɗaya. Daga haka suka ƙarasa abinda ya rage aka bar saka rana a matsayin wata biyu ɗin.
Suna fita a gidan Aunty Sabuwa dake laɓe ta afko falon, rungume mijin nata tayi cike da farin ciki, shima sai yay murmushi a ransa yana faɗin (wannan farin cikin nawane ba naki ba Sabuwa, dan lokaci yayi da zan maidama Alhaji Usman martani, lokaci yayi da zan ƙwaci abinda ya hanani a baya da ƙarfin tuwo. Lokaci yayi da wasan na gaskiya zai fara tsakanina da shi....)
_Tofa masu karatu, shin mike a tsakanin Alhaji Badaru mahaifin Nazeefa da Daddy kuma?. Ku dai kumuje zuwa mutanena🏃😋👌_
___________★
“Wai hawayen nan basu isa haka ba ne Maanal? Tunda muka taho kike sharar hawaye inata magana kinƙi cewa komai. Kin san kuwa yanda zuciyata ke ɗagawa da wannan yanayin naki. Please! Tell me! Is something bothering you? Wani abu suka faɗa miki mara daɗi ne? Ko basu ɗaukeki aikin bane sukace?”.
Yanzun ma komai ƙin cewa da shi tayi, sai hankalinsa ya ƙara tashi matuƙa. A haka suka iso gidan Shahidah. Ko parking kuma bai gama yi ba ta buɗe motar ta fita, shima saurin fitowar yayi sai dai harta shige abinta cikin sassarfa da ɗan gudu-gudu. Hankalinsa ne ya sake tashi, sai kuma ya rasa inama ya kamata ya kama. Kamar zai bita sai kuma ya dakata. Yayi hakan yafi sau uku sai kuma ya koma cikin motar da sauri ya mata key ya bar gidan. Wani irin gudu ya dinga shararawa daya kawosa Mawaad Company cikin ƙanƙanin lokaci. Yana shiga kai tsaye office ɗin Boss ɗin ya nufa. Ko jiran Assistant ɗinsa ya masa iso baima yi ba yanzu. AS ɗin ne ya biyosa yana ƙoƙarin tsaida shi da sanar masa Boss yace kada abar kowa ya sake shigo masa sai in har shine ya buƙata amma sam RK bai sauraresa ɗin ba ya afka Office ɗin kansa tsaye cike da fushi kuma.
Shi dai shi kuma ƙoƙarin sake sanarma RK yake yi cikin damuwa da tashin hankali, dan tunda yake aiki a ƙarƙashin ogansa bai taɓa ganinsa a wannan yanayin na yau daya gansa ya fito daga conference room ba. Ya kuma tabbatar ba ƙaramin abu bane zai sakashi cewa kada abar kowa ya shigo inda yake ɗin.
Daga shigowar RK harta AS ɗin nasa da abinda yake ƙoƙarin faɗama RK ɗin duk a kunnensa ne, dan yana tsaye jikin ƙaton ƙayataccen gilashin da akai ma kusan kowanne bango na Companyn gaba ɗaya ado da shi hannayensa duka biyu a cikin aljihun suke ya zubama harabar wajen Companyn idanu koma ace ƙayatattun gine-ginen birnin na Abuja. Sai da ya basu kusan mintuna uku kafin ya ɗan juyo kamar mai fama da ciwon wuya ya zuba musu ido su duka biyun, sai kuma ya wani watsa musu ɗan iskan kallo ya ɗauke kansa.. Hakan yasa AS ƙoƙarin fara kare kansa cikin rawar murya da damuwa. Amma sai yay masa alamar yaje da yatsunsa biyu cike da salo. Kai AS ɗin ya jinjina masa cike da girmamawa yana mai haɗiye abinda yaso faɗar. Koda ya fice ya rufe musu ƙofar sake maida kansa yay ga kallon wajen batare da yayi magana ba kamar yanda shima RK ɗin baiyi magana ba har lokacin.
Iska mai ƙarfin gaske RK yay wani irin fesarwa ta alamar tsantsar takaici. Sai kuma ya sake takowa cikin Office ɗin sosai har inda yake shima ya tsaya kamar yanda yake a tsayen, batare daya kallesa ba ya furta, “Miyasa tun farko ka yarda zaka ɗauketa aiki cikin girmamawa da darajtawa! Amma ka saɓa hakan? Kasan matsayinta a wajena kuwa AA!?”.
Idanunsa da suka kaɗa sosai ya lumshe. Sai kuma ya saki wani ɗan siririn tsaki mai ɗan sautin da har RK ɗin yaji. Shiru na tsawon mintuna fin huɗu har RK ɗin daya sake ƙuluwa da haushi ya fidda ran amsawar tasa sai kuma ya ɗan karkato da kansa ya duba RK ɗin. Shima juyowar yay ya kallesa sukaima juna kallon ido cikin ido kowanne ƙwayar idanunsa na bama ɗan uwansa dai-dai da amsar da yake buƙata ko nemar mata fassara da fashin baƙi. AA ɗin ne ya fara janyewa yana sake sakin wani lalataccen murmushi a karo na farko mai kama dana rainin hankali ko tsantsar takaici. Sai kuma ya maida fuskarsa ya tsuke tamkar ba shiba, a dakensa a kuma karo na farko cikin muryarsa mai zurfi da amo ƙasa-ƙasa ya furta, “Calm down first, let's talk when you're ready. Right now I need to be alone”.
Wani irin zuba masa ido RK yay cikin takaici, sai kuma ya saki murmushi mai ciwo shima daya sake bayyana tsantsar bacin ransa. Juyawa yay yana kallon AA ɗin daya sake maida hankalinsa gaba ɗaya ga kallon garin. Taunar lips ɗinsa ya shiga yi da ƙarfi kafin ya juya ya fita a Office ɗin batare da ya sake cewa koman ba. A yanda ya ɗan bugo ƙofar ya sake saka AA lumshe idanunsa daga inda yake bai kuma juyo ba.
RK daya fita baiko kalla AS ba ya shige elevator. Har zai danna sai kuma ya fasa ya fito. Dogon hanya ɗin yabi sai gashi ya fito wani wajen da jerin Offices duke har kusan guda biyar. Office na biyu yay knocking. Kai tsaye aka bashi izinin shiga dan duk wanda ke'a cikin Office ɗin yana kallonsa ta hanyar camara. Ɗaya daga cikin wanda sukama Maanal interview ne. Fuskarsa ƙawance da murmushin daya bama RK ɗin mamaki ya tarbesa. Bayan ya nuna masa wajen zama zai miƙe ɗauka masa wani abun ya dakatar da shi.
“Director Mustapha thanks you basai ka kawo komai ba muyi magana kawai mana”.
“To ALLAH yasa dai lafiya?”.
Director Mustapha ya faɗa yana komawa ya zauna a mazauninsa.
“I'm sorry nasan dokane a companyn nan abinda zan tambayeka. Amma ina neman alfarmar sani ne sakamakon wani dalili mai ƙarfi. Please yarinyar nan da kukama interview yanzu wani abu ya faru da ita ne a wajenku ko aikin ne bata samu ba?”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da murmushi Designer Director Mustapha ya saki, sai kuma ya girgiza kansa. “No Doctor babu wani abu daya faru gaskiya. Hasalima an bata aikin dan har CEO ya bata damar fara zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Yanzun nan R&D Director ya fita anan na gama bashi list ɗin abinda office ɗin ta zai buƙata a yau komai za'a gama haɗa mata shi. Shin wani abu ya faru ne?”.
“No! No! Babu wani abu daya faru. Nagode sosai”.
“Ai babu zancen godiya a tsakaninmu, yarinyar ta cancanci samun aikin dan gaskiya she is very smart and amazing because she demonstrated excellent problem-solving skills and an innovative approach during the interview. Tunda kaga babu wani ja'inja Boss ya bata dama da wuri haka ai kasan bata wasa bace. Haka muma kowa ya gamsu da brain ɗinta wlhy”.
Murmushi RK ya masa cikin jinjina kai, sai kuma ya miƙa masa hannu yana miƙewa da faɗin, “Thanks you Director”
“No worries doctor. I am on my job”.
Daga haka yay masa sallama ya fito a office ɗin dukkan damuwarsa da AA ya dasa masa na guduwa daga cikin ƙirjinsa. Sai dai kuma hankalinsa nakan dalilin halin da Maanal ɗin ta shiga........✍️
_Tofa ƙaƙa raƙa ƙaƙa. Shin minene alaƙar Maanal da AA?, sannan minene alaƙar RK da AA kuma. Dan tabbas alamu sun nuna akwai sanayya mai ƙarfin gaske a tsakaninsu. Hhhh badaƙala kenan, mi kike son ji?😂 Ga wuri ga waina. To kawai mu haɗe a comments section 🤣🤣🤣🤣🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣4️⃣
.........Wata irin ajiyar zuciya director Mustapha ya saki. Sai kuma ya saki murmushi a ransa yana mamakin kansa da ɓoyema Doctor Rafeeq ɗin sauran gaskiyar abinda ya faru da yay... Kirane ya shigo daga landline ɗin office ɗin, ganin daga office ɗin CEO ne ya sashi saurin ɗagawa. AS ne ya sanar masa CEO na buƙatar ganinsa yanzun nan, kuma ya taho da file ɗin sabuwar staff ɗinsu. Bai wani tsaya wasa ba ya miƙe yana dariya. A fili ya furta, “Anya babu wata a ƙasa akan yarinyar nan kuwa? To madai ji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta”.
Sai da AS ya shiga yay masa iso sannan ya shiga. A yanzu kam AA ɗin na zaune ne a kujerarsa ta aiki saɓanin a yanda RK ya samesa ya kuma barshi. Gaisuwa Director Mustapha ya miƙa daga tsayen batare daya zauna ba. Shima AA ɗin da hankalinsa ke kan computern desk ɗin batare daya amsa ba yay masa nuni da vesitors chair ɗin gaban desk ɗin kawai. Zama yay, kafin cikin girmamawa ya ce, “Gani Sir. Dama ina ƙoƙarin ƙarasa haɗa komai ne na kawo sai kuma ga kiran AS akan kana son ganina”.
Shiru bai amsa masa ba, yanata aikin gabansa kawai har lokacin hankalinsa nakan screen ɗin computer ɗin, sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya ajiye tare da maido hankalinsa kan Director Mustapha ɗin. “Am sorry ina wani abune”. Ya faɗa cikin muryarsa mai zurfi. Da sauri Director Mustapha ya ce, “Babu komai Sir”.
Kansa kawai ya jinjina masa. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar ya basa file ɗin. Miƙa masa yay da sauri cikin girmamawa. Yayinda shi kuma ya shiga buɗesa yana duba komai daki-daki. Sai zuwa can ya ɗan ɗago. “Baku ƙarasa bane?”.
“Eh sir! Saboda kana fita itama ta miƙe ta fice muna ƙoƙarin tsaidata amma bata sauraremu ba. Mun cigaba da abinda ya dace ne kawai saboda ka bada umarnin hakan. Dan mu harma mun fara tunanin ko tanada wani c......”
Muƙutt ya haɗiye zancen saboda wani shegen kallo da AA ɗin ya jefa masa. Sai kuma ya duƙar da kansa yana shashshafa ƙeya. Shiru office ɗin ya ɗauka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 17