Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Cikin ƙwafa da takaicin itama bata samu yanda take so ɗin ba ta ce, “Ya taimaki kansa. Dan wlhy da yau har shegiyar uwartata sai sun bar gidan nan. Kai na tsani mutanen nan a rayuwata”. “Ai bake kaɗai ba Mamma”. Cewar ƴarta ta biyu mai tana huci. Auren nata ne ya mutu kusan shekara uku kenan tana gidan. Dama ita kawai ta aurar, rana ɗaya akai bikinsu da su Shahidah yayun Maanal. Sauran kuma ALLAH bai kawo ba, ko muce ruwan ido da jiran ƴaƴan masu hannu da manda irinsu ya hanasu auruwa. Burin kowannensu da ma uwarsu shine suyi auren ƙwarya tabi ƙwarya.. Buɗe shafin zagin su Manaal sukai a falon kamar sun tare musu numfashi, sai Amrah ce keta ɓata fuska dan ita bata son hakan. Ita birgeta ma Ammien take a rayuwarta mace mai dattako da sanin ya kamata. Babu ruwanta da duk abinda iyayen nasu keyi a gidan sabgar gabanta takeyi kawai da ƴaƴanta. Ko su duk abinsu bazasu taɓa cewa ga randa Ammien taima wani abu mara daɗi ba, amma tasa miyasa basa sonta da yaranta?... A ɓangaren Maanal can ma door bell ta fara dannawa kafin ta shiga. Shima dai sashen Hajiya Basariyya da suke kira da Momyn Suhana ya matuƙar haɗuwa. Girmansa kuma ɗaya dana Ammie. Ita dai bata falon sai su Huznah da ƙannenta dake cin dafaffen gyaɗa suna hira. Duk sun zubar da kohon a saman lallausan carpet ɗin tsakkiya ko'a jikinsu. Dan sun san mai-aiki ce zata gyara basu ba. Har zata juya batare data musu magana ba sai ga Hajiya Basariyya ɗin ta fito daga kitchen riƙe da kofi tana waya fuskarta da murmushi. “A'a ƴan Jos an dawo kenan?”. Ta faɗa cikin katse hanzarin Maanal kamar tuni ƴarta Huznah bata kawo mata labarin dawowar Maanal ɗin ba tun ɗazun. Juyowa Maanal ɗin tayi fuskarta kadaran kadahan ta ɗan kalla Hajiya Basariyya ɗin da nata fuskan ke ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa, sai dai acan ƙasan zuciyarta wani irin maƙoƙon tsanar Maanal ɗin ne ke mata kaikawo. Risinawa Manaal tai tana gaisheta. Nan ma ta amsa cike da fara'a tana nuna ma Maanal ɗin kujera da faɗin, “Haba sai kace wata baƙuwa zauna mana Maanal ga ƴan uwanki nan na bikin cin gyaɗa ka kuci. Da fatan dai kun dawo lafiya? Kuma komai ya kammala?”. Kai kawai Maanal ɗin ta jinjina mata kanta a ƙasa, sai dai yanzu da ɗan gajeren murmushi a fuskarta. Ganin bata zauna ɗin ba Hajiya Basariyyar ta sake nuna mata kujera. Kai ta girgiza mata da kama hannun Munaya ta ce, “A'a Momy mun gode dama munzo gaisheki ne kawai”. “Masha ALLAH aiko ina godiya. Sai dai ni bana cin miƙe gaskiya azo mini hira dai. Suma su Shahidah ki faɗa musu ina godiya sun barni da jira. Tun ɗazun har abinci nasa akayi dasu ga gyaɗa da aka dafa amma shiru kake ji”. “Zan faɗa musu in sha ALLAH Momy”. Maanal ta faɗa cikin muryarta mai zurfi da nutsuwa. Daga haka ta kama hannun Munaya tana mata sallama. Da harara duk suka bita har Hajiya Basariyyar. Sai da ta gama ficewar harda turo ƙofar Huznah taja tsoki da faɗin, “Ni wlhy Momy ina mamakinki, kiyita wani musu magana mai daɗi. Shegu sunzo sun gaje mana gida baka isa kai magana ba Daddy ya kama faɗin yayansa ne suma na halak. Ko ina suka zama ƴaƴan nasa agololi. Ni ko wanda ma yakema kallon ƴaƴan nasa ƙilama da cikinsu tazo.” “Hummm”. Kawai Hajiya Basariyya ta faɗa tana kaiwa zaune batare data kula maganar Huznah ɗin ba. Hakan ya sake bama yaran haushi suka cigaba da zagin Maanal dan kamar ma sunfi tsanarta fiye da sauran ƴaƴan Ammien. Duk da kuwa sunƙi jinin Hameed ma da Waleed da Ammien ta haifa a gidan suke matsayin uba ɗaya dasu. Balle da Daddyn ke tsananin nuna musu soyayya. Dan yanzu haka ma yana tare dasu ƙasar Amurika yin hutu. Duk da dai yace taro zaije ya tafi da su. Amma babu wani taro kawai yaje dasu ne dan hutawa na sati har biyu... Rai ɓace Manaal ta koma sashensu. Sai dai yanda bata gayama kowa abinda ya faru ba babu wanda ya tambayeta. Sai ma zama tai suka fara hirarsu. Babu jimawa kuma Daddy ya kira Ammie ta video call. Daga nan suka gaisa da shi ya bama Hameed da Waleed da Ammien ta haifa a gidan. Ƙanensu kenan guda biyu. Yarane matasa da zasu iya kai shekara sha biyar da sha uku. Suma duk kamanin Ammie suka biyo kamar su Maanal ɗin. Sai dai su farare ne sun kwaso hasken fatar Alhaji Usman Chalawa sosai kasancewarsa farin mutum tas.. Suna cikin hira da ƙannen nasu ne babu zato akai knocking ƙofar falon. Kafin wani yay magana a cikinsu mai knocking ɗin har ya shigo. A take Maanal ta shanye fara'ar fuskarta da maganar da take da Waleed ko nace faɗa irin na sako duk da kuwa ta girmesa sosai. Kauda kanta tai da jan mayafin abayarta daya zame ta rufe gashinta da ƙyau, yayinda su Amaal ke masa barka da shigowa. Shiko yana amsawa da ɗan murmushi hankalinsa akan yaransu dake gaishesa duk da sai da ya gama ƙarema Maanal kallo a kai-akaice. Gaban Ammie da hankalinta itama ke kansa tana ɗan murmushi ya ƙaraso. Cike da girmamawar da yake bata ya rissina yana gaisheta. Da kulawa take amsawa itama, kafin ta ɗora da faɗin, “Baka wuce Abujan ba kenan?”. “Eh Ammie fasawa nai saboda wanda zanje wajensa yace yana Lagos sai gobe zai dawo. Nima kawai sai na bari sai goben na tafi dan bana son naje naita zaman jiransa ina kuma da abinda zan ɗanyi anan ɗin”. “To ALLAH yayi jagora. Yay muku albarka, ya kuma saka muku hannu a dukan al'amuranku”. “Amin ya rabbi Ammie Nagode sosai”. Ya faɗa cike da jin daɗi yana maida hankalinsa kan Maanal dake ƙoƙarin tashi tabar falon. Kansa tsaye ya furta, “Ke ƴar hidimar ƙasa yaushe kika dawo?”........✍️ Hummm yanzu fa aka fara shimfiɗar bama wasan ba. Mi kuke tsammani. Yazeed, ga kuma RK. Ga Maanal da bama musan alƙiblarta ba. Shin wai mi aka AJIYE A DUHUN nan ne? Ya dai kamata a haska mana mu gani ko zamu tayasu lalube🏃🏃🏃🏃🏃. Maza garzayo cikin tawagar littafan zafafa biyar da zasu zo muku da sabon salo na musamman in sha ALLAHU. Kowanne da salonsa da kuma takunsa. Mi kuke jira, ai sai kawai kuzo ayi tafiyar nan daku karku bari sai wasu sun baku labari.😘😘😘👌 A fa dun inda ZAFAFAN suke ZAFAFAN ne🫣😘😘👍🏻 ✨ZAFAFAN DAI ✨ 1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ 🅿️➖0️⃣6️⃣ ALBISHIRINKU 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Idan kinada burin samun babban jari🤝 ko siyan wata babbar kadara irinsu gida mota ko gold fili ko Gona ko canja kayan daki ko kinada yanmata kinaso kisaimusu kayan aure ko canja rayuwarki daga tunanin yauda kullum xuwa lissafin dollars 💰daga Kwance 💃 Uhmmm garzayo kiyi rijista da 52U kiyi aiki kisha mamaki acikin shekarar nan rayuwarki xata canja ta dalilin yin rijista da $21 kacal😱 Yar uwa kisani cewa a kullum muna fuskantar tashin hankali idan akace mana darajar dala tatashi😫 Kullum naira da muke kashewa darajarta Kara faduwa takeyi😩 Tsadar rayuwa kowa yanxu fama yake da wnn tashin kayan😰 Mezai Hana kuxo mu runtuma muyi harkar dollars din kawai sbd yazamana ko ina muna nan 🤗 52U harkar dollars ce Mai sauki ga samu 52U alkhairi ce rijista kawai xakayi da $21/35k bayan haka baasaka kudi a 52U kuma 52U babu level level kawai rijista ne akeyi da kudi ba platforms bane ❌ Networking ne💯 Yanxu mu yan 52U idan akace mana dala tatashi murna mukeyi ba bakincikiba sbd inkanada dala kacanjashi naira ninkuwa yakeyi💃 Kaya kullum farashinsa tashi yakeyi Baya saukowa muna rokon Allah yahoremana abin saya don ga tsada gashi babu isheshshen kudin saya akwai kura wllh😂 Amma Inda kudin abin bazaimaka wahalaba😅 52U idan kayi rijista xata Baka jarin loan a dashboard Dinka Wanda kullum zaidinga juyuwa 💰 Kubiyoni domin Jin cikekken labarin 52U don koda kudinka saida rabonka abin na yan baiwane 52U ba platforms bane networking ne kuje kuyi bincike kafin kuyimin magana 08031507345 ___________ ______________ ........Idanu Manaal ta ɗan rumtse kamar zatai wucewarta sai kuma ta dakata saboda hararar da Ammie ta watsa mata, cikin sanyinta ta furta, “Yau ne Yaya, ina yini”. Batare daya amsa ba ya sake furta, “Ai da yake ke baƙya zumunci ko a waya sai kinso ake jinki. ALLAH ya sanya albarka to”. Kasancewar ta fara tafiya a taƙaice ta amsa masa da Amin. Ganin da gaske barin falon zatai kuma harga ALLAH dan ita yazo ya dakatar da ita da sake faɗin, “Zoki bani abinda kuka girka anan ɗin naci”. Cak Maanal ta sake tsayawa zuciyarta na wani kalan harbawa da sauri-sauri, sai kuma ta yunƙura zata cigaba da tafiya ranta na wani kalar jin zafinsa da mamakin rainin hankalinsa. Ba abinci suka samu yana ci a sashensu ba? Shine dan guntun kutsugu zaizo nan kuma yace a bashi abinci...... “Wai nikam ba dake ake magana ba halan?”. Ammie ta katse mata hanzari cikin kaushin murya. Jitai kamar zata saki ihu, sai dai babu yanda ta iya dole ta furta, “Ammie nafa amsa“ daga haka ta nufi kitchen a maimakon hanyar bedroom ɗinta. Abincin ta zubo mata tana faman ƙannan magana a ranta. Itafa wlhy da tasan ma yana gidan bazata dawo ba. Kuma ko yanzu idan taji zai jima a KD ɗinne gara tabi Didi Shahidah Abuja har sai ya tafi ta dawo kawai. Da wannan tunanin ta dawo da abincin. Tana ƙoƙarin nufo falon ya miƙe yana faɗin, “Bani anan”. Kallon dining ɗin daya nufa tayi, sai kuma ta kalla Ammie kamar zata saki kuka. Ganin Ammien ta ɗauke kanta ta maida dubanta gasu Didi Amaal. Da baki Amaal tai mata nuni da Ammie. Hawayen da suka cika mata ido kawai ta haɗiye kafin ta taka a hankali ta ƙarasa inda yake zaune yana jiranta. Tray ɗin ta ajiye a gabansa. Tana niyyar barin wajen ya dakatar da ita da faɗin, “Dawo ki zauna”. Yanda yay maganar babu wani wasa kuma a gadarance ya sake kunna zuciyarsa. Sai dai kuma babu yanda zatayi dole ta koma ta zauna dan tun fil azal shi baya wasa dasu. Sannan kaf ɗin gidan nan babu wanda zai ce baya tsoron Yaya Yazeed. Mutum ne bamai yawan shiga sabgar kowa ba, amma baya ɗaukar raini. Abincin ya ɗan fara ci a nutsensa yana lumshe ido, sai da yay kusan lauma uku ya ɗago yaɗan kalleta. Fuskarsa babu wani walwala ko alamar wasa ya furta, “Abincin Ammie dabanne a gidan nan Manaal. ALLAH dai yasa ki gadota iya girki dan ina son abinci sosai. Idan ko kina wasa da koya ki ƙara dagewa sosai kinji”. “Hummm” ta faɗa kawai batare da tace komai ba. Manyan idanunsa ya ɗan zuba mata yana ɗan sake tsuke fuska. “Miye wani hummm. Kin san fa bana son halayyar nan naki ai ko? Tom zamu fara ai kenan. Dama baki son ina fushi dake bane. Tunda nai tafiyar nan baki taɓa nemana a waya ba why?”. Rasama mizata ce dashi tayi, tsahon lokaci bata tanka ba har sai da ya sake tsareta da kaifafan idanunsa sannan ta motsa lips ɗinta da ƙyar ta amsa masa da “Ai ban san da wane layi zan sameka ba”. “Hummm dama ba niyyar kiran nawa kike da shi ba. Ni wannan halin miskilancin naki ban san yaya zan kwashe da shi ba Maanal. Amma ba komai zanyi maganinki ai. Yanzu ke miya samu naki layin da ban samunki kwana biyu, ko blocking ɗina kikayi?”. Nan ma ta jima bata amsashi ba. Kafin ta nisa da ƙyar ta amsa masa a taƙaice. “Matsala ya samu, mizaisa nayi blocking ɗinka”. “Sai kuma kika gagara zuwa ki gyara ko?”. Shiru tai ta ƙi bashi amsa. Shima sai ya bar zancen dan yasan ɓacin rai kawai zai ƙarama kansa. Abincinsa ya cigaba da ci, sai da yana gab da gamawa ne yake sake kallonta da faɗin, “Lokaci fa yayi da zaki cireni a gidan gandun nan. Dan kasa isasshen barcin daren nan da nake ya fara isata haka nan Manaal”. “Kamar ya?”. Ta faɗa cikin ƙosawa da mamaki kuma, sai dai muryarta acan ƙasan maƙoshi da kuma sanyi. Idanunsa da suka ƙanƙance lokaci guda ya ɗan lumshe mata ya sake buɗewa. Sai kuma ya wani maidasu ƙasa-ƙasa tare da muryarsa ya furta, “Saboda ina buƙatarki a gefena. A tsakanin nan a matse nake da buƙatarki a kusa dani. Dan haka zanma Daddy magana a tada zancen aurenmu tunda kin kammala karatu harda sarvese ai nayi ƙoƙari sosai”. Wani irin mugun bugawa ƙirjin Maanal ya shigayi. Yayinda jikinta ke wani tsuma. Cikin rawar murya da sake bayyanar rauninta ta ce, “Yaya Yazeed Please ka ƙara min lokaci mana, ka......” Spoon ɗin hannunsa ya ajiye cikin tsatstsareta da idanunsa da suka hanata cigaba da maganar tata. “Manaal lokaci kuma? Miyyasa baƙya tausayina. Kin san shekarata nawa kuwa a duniya? 35 fa nake ƙoƙarin cikawa. Kin san kuwa nakai maƙurar ƙurewa da buƙatar abokiyar rayuwa ko? A wancan karon kince kina son kammala karatu, nayi miki wannan alfarmar, kika kammala kika sake roƙon haɗa masters naki na sake kauda kaina saboda Dadday, yanzu harda su sarvese duk bance komai ba amma ki sake cewa na baki lokaci. Ko kina son sai an samu matsala na far miki a cikin gidan nan ne saboda halin da nake ciki?”. Zuciyarta ce ta sake harbawa da sauri, duk da kuwa bawani fahimtar zantukan nasa take ba kasancewar hankalinta ya gama rabuwa biyu. Shima ganin tunaninta na neman yin nisa da shi ya kira sunanta murya a ƙasan maƙoshi. Ajiyar zuciyar dawowa cikin hayyaci tayi, sai kuma takai hannu ta goge ƴar ƙwallar dake neman gangaro mata. Cikin rawar muryar kuka ta ce, “Yaya Yazeed!”. Idanunsa kawai ya zuba mata batare daya amsa ba. Dan shima dai miskilin ne kamar yanda ake zaginta akan natan. Sai dai ita ɗin ta takashi ta shanye. Dan shi yakanyi magana a inda yaso idan yaso hakan. Ganin taƙi cigaba da magana ya ce, “Ke nake saurare.” Maganar take son yi sai kuma ta kasa, sai faman wasa take da dogayen yatsunta masu ɗauke da farce masu haske dan babu ɗigon lalli a jikinsu duk da kuwa ita ma'abociyar sonshi ce. Nuni ya mata alamar ita yake saurare. Itama saita ɗaga masa kanta tana ƙoƙarin shanye abinda ke mata kaikawo ta cigaba da faɗin, “Mamma!. Ya kamata ka....” “Maanal Please, kema kin san an wuce da wannan matsalar tuni, Mamma tsakaninta da Daddy ne bada mu ba. Mizai sa ki ɗauka ki saka hakan a tsakkiyar rayuwarmu. So please indai ba so kike ki sake jana a ƙasa ba kuma bayan na baya ki bani haɗin kai. Ina buƙatar abokiyar halitatta Maanal. Ina cikin takura matuƙa akan hakan kada kisa na cutu”. Idanunta ta rumtse da ƙarfi, kalamansa na mata wani kalar kuɗa a zuciya da ƙirji. Yayinda ta wani gefe suke maimaita kansu a sigar ƙaddararta ta ƙuruciya. Rawa jikinta ke neman farayi saboda abinda ke neman jijjigo gyanbon ƙasan ziciyarta da kowa ke tunanin ya jima da warkewa. Kamar wanda ke karantarta ya ce, “Okay na baki dama kije kiyi shawara dama duk wanda kike ganin zakiyi. Kafin nan dai kafin Daddy ya dawo ki tsaida min zance ɗaya. Idan ba haka ba sai dai kiji batun saka rana. Zuwa anjima ina son ganinki a garden, ki zo min da layin naki dakeda matsala zan saka a dubashi”. Ya ƙare maganar yana miƙewa abinsa. Har yay sallama dasu Ammie ya fice a sashen Maanal na zaune kamar gunki da aka dasa don tarihi a dining area ɗin ta kasa tasowa. Saima wata irin zufa ce data cika mata gaban goshi. Yayinda hawaye ke ambaliya a saman ƙyaƙyawar fuskarta. Amaal da dama tun ɗazun hankalinta ke kanta ce ta ƙaraso wajen da sauri. Kamota tai cikin rawar jiki tana tambayarta mike faruwa? Maimakon amsa sai ta faɗa jikinta kawai ta rungumeta tsam ta saki wani sirrin kuka mai ban tausayi. Rikicewa Amaal ɗin tayi, hakama Didi Shahidah tuni ta taso ta nufosu. Ammie ce dai kallo ɗaya ta musu ta kauda kanta gefe, dan ta ɗaura ɗammarar itama bazatai sanya a wannan karon akan Maanal ɗin ba. Ta gaji da zamanta haka gara ai auren nan ko hakan zaisa ta manta da baya. Tana jiyo yanda ƴan uwanta ke sake jera mara tambayoyi a rikice batabi takansu ba tama tashi tabar falon zuwa bedroom ɗin ta. Bakin gado takai zaune tare da fara sarrafa wayarta, sai kuma ta kaita kunne alamar kira tayi. Babu kuwa jimawa aka ɗaga daga can, bayan sun gaisa da tambayar juna iyali ta fara magana kamar haka. “Nene na kiraki ne akan ƴar gidanki, yau dai ta dawo an kammala service”. Ta ɗan yi shiru alamar saurare. Sai kuma tai murmushi da cigaba da faɗin, “Shine ma dalilin kiran naki Nene. Dan anyi sa'a shima Yazeed ɗin yana gida yazo wani aiki kuma zai jima kamar yanda ya sanar min. To sai nake ganin hakan damace da za'ayi kawai a huta. Dan nagaji da wannan ɗage-ɗagen saka ranar auren nasu shi kuma Baban nasu na biye mata. Gara ayi a huta, idan taga abin bawasa bane tama ƙarasa nutsuwa. Saboda na fahimci Maanal fa bazata taɓa kasancewa a yanda ake buƙata ba a haka gaskiya. Amma shi idan suka je can zai san ta yanda zai ƙarasa mantar da ita komai dan yaron nada hankali da nutsuwa. Banga abinda Yazeed bai mallaka ba da mace bazatai alfahari da shi ba ako'ina matsayin miji”. Nan ma tai shiri tana saurare. Ta jima kafin ta amsa da, “Ni abun sake bani tsoro yake. Yanzu haka bakiga yanda ta dawo a fige ba wannan karon kamar kazar fakat. Al'amarin Maanal na tayar min da hankali Nene wlhy”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa. “Hakane Nene ina kan yimata iya ƙoƙari na. Dan ko sadakar nan wlhy kusan don itane bana iya jinkirtawa. Amma dai a aiko mata da ruwan addu'ar ma sai ta cigaba da sha. ALLAH ya kawo iyakar komai ya kuma bama yaron nan ƙwarin gwiwar kwantar mata da hankali ta sake manta komai”. In sha ALLAHU Nene bana jin Yazeed. Yarone mai addini da sanin yakamata tamkar mahaifinsa. Dan sam baida halin mahaifiyarsa, baya kuma biyema al'amarinta kamar ba daga jikinta ma ya fito ba.” “To Amin ya rabbi sai kin shigo ɗin ma ƙarasa”. Daga haka sukai sallama. ★★“Auta dan ALLAH kibar kukan nan haka. Wlhy yana ɗaga mana hankali. Ki mana bayanin mike faruwa ne? Ko wani abu yace dake mara daɗi?”. Kanta ta shiga girgiza musu tare da share hawayenta. Sai kuma ta tashi daga kwanciyar datai a jikin Didi Shahidah ta koma ta jingina da fuskar gadonta. “Didi dan ALLAH ku taimakeni, wlhy bana son auren nan bana buƙatarsa dan bazan taɓa yin aure ba wannan alƙawarine da naima kaina. Amma su Ammie da Yaya Yazeed sun kasa fahimtata. Wlhy kosun matsa nayi auren nan GANGAR JIKINA kawai zai aura, sannan bazan taɓa biyayya irin ta aure ba a gareshi, bama shi ba ga kowanne ɗa namiji. Didi miyyasa bazai fahimta bane, Maanal ta jima da mutuwa babu ita a wannan DUNIYAR ta mutane. Duk gangar jikin dake rayuwa da matacciyar zuciya bashi da wani amfanin rayuwa. Amma sun kasa fahimta, sun kasa min uziri, dan ALLAH ku ku fahimtar dasu maybe zasufi saurin yarda daku idan ni basa gane yarena. Koku fahimtar da Yaya Yazeed shi maybe ya fisu gane illar yin AJIYA A DUHU da yayi, cigaba da matsawarsa kuma zai zama ƙonewar komai daga hasken fitilar da yake ƙoƙarin haskawa don lalubo abinda ma babu shi koda a cikin duhun....” “Maanal Please...” Didi Shahidah ta faɗa tana kamota jikinta ta sake rungumewa. Itama cikin murya da lallashi ta ce, “Please ki kwantar da hankalinki mana. Kin san ba wani lafiyace ta isheki ba. Ciwonki baya buƙatar irin waɗannan abubuwan kinfi kowa sani. Maanal iyayenmu suna son taimakon rayuwarki ne ba cuta miki ba. Sannan Yazeed babu abinda ya rasa daga zama cikakken Namiji. Yana kuma matuƙar kaunarki, duk da boren mahaifiyarsa akan al'amarinku bai taɓa canjawa ba. Miyyasa bazakiyi haƙuri ki manta da komai ba ki amshi wannan ƙaddarar?......” “Saboda ƙaddara tana tafiya ne da rayuwa Didi, ni kuma na riga na jima da Mutuwa, mi zaiyi da gawa? Mi zai yi da gangar jikin da babu zuciya? Mi zaiyi da wadda labarinta ya jima da rubutuwa da ƙarewa? Tuni fa Maanal ta gama mutuwa, na mutu! ni tamkar hawace Didi..” “Keba gawa bace Maanal, ya kamata ki fahimci bafa komai a rayuwa kake samu hundred percent ba, dole sai kayi haƙuri da wani abun sannan kake mallakar wani. Please ki amshi ƙaddararki a karon na biyu, nasan zaki ji daɗin zama da Yaya Yazeed wlhy mutumin kirki ne, tunda kin san dai babu yanda za'ai a barki haka babu aure. Kuma Yazeed ya dace dake matuƙa”. “Didi ban musa miki kirkinsa ba ko nagartarsa ko cancantarsa. Duk abinda kuke hange min nasan fiye da haka gareshi, sai dai bana buƙatar kowanne namiji a rayuwata gaba ɗaya ku fahimta mana dan ALLAH”..........✍️ _Tofa, mace kuwa zai yiwu tace bata buƙatar namiji a cikin rayuwarta?????. Shin jama'a mike damun Maanal ne haka?????🏃🏃🏃🏃🏃._ ✨ZAFAFAN DAI ✨ 1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ 🅿️➖0️⃣7️⃣ .......Hawaye ne suka cika idon Amaal, yayinda Shahidah ke ƙoƙarin shanye nata itama. Tausayin ƴar uwar tasu na ƙara cika musu zuciya. Dai-dai nan Ammie ta shigo, kallo ɗaya tai musu su duka ta kauda kanta. Sai kuma tai gyaran murya. A tare duk suka kalleta, Maanal ta share hawayenta da ƙoƙarin kaiwa kwance, amma sai Ammie ta riƙota tana kaiwa zaune kusa da ita da faɗin, “Auta wai yaushe zaki bar shagwaɓa ne?”.

Chapter 3 of 17