Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba sai da suka fito zasu wuce taga Hajiya Basariyyan. Sosai ta sake jinjina makircin matar a ranta, dan ta jima da gane wacece Basariyya, sai dai bata taɓa nuna mata ba ta barta da halinta. A lokacin ma murmushi kawai tai batace komai ba, hakan kuma sai ya ƙonama Hajiya Basariyyan rai, ta rasa wacece Ammie, ta rasa ta inda zata kamo lagon matar, ta rasa ta inda zata shiga jikinta kamar yanda take shiga jikin Hajiya Yaya tasan sirrinta. Amma ba komai, idan tasan wata ai bata san wata ba. Anan Abujan itama ta kwana dan Daddyn nada gida anan ɗin dan yana harkar sayen gidaje da sayarwa ne. Kasancewar komai akwai a gidan yasa sauka kawai sukai anan ɗin. A yanzu ma haka tana a asibitin tare da su. A ɗakin da aka kwantar da Maanal ɗin ɗakine na musamman kamar palor da bedroom, dan haka duk suna a palor ɗin zaune itama Maanal na daga ciki babu mai shiga sai dai su leƙata ta jikin ƙofar glass ɗin. Shahidah da Amal suka iso ɗauke da abinci, bayan duk sun gaishesu suna ƙoƙarin zama Daddy da RK suka shigo ɗakin sai wani ba'indiyen likita da shine akan case ɗin Manaal ɗin ma. Gaishe da Daddy su Shahidah sukayi, sannan suka gaisa da su RK da suma suke gaida su Ammie. Su RK na ƙoƙarin barin wajen kamar daga sama sai Hajiya Basariyya cewa tai, “Nikam likitan nan kamar na sanka”. Yanda tai maganar idonta akan RK ya sakashi fahimtar da shi take, kallonta ya ɗan yi sai kuma ya rissinar da kansa tunda bai san matsayinta ba a garesu ya ce, “Mommy zata iya yiwuwa. Sai dai ban san a ina kika sanni ba”. Batare data damu da kallon harara da Daddy ke mata ba ta ce, “A zaria gidan Alhaji Saminu Ashafa”. Cikin jinjina kai RK ya bata amsa da, “Ni ƙanin amaryarsa ne Majdiya”. Kafin Hajiya Basariyya ta samu yin magana Ammie da Daddy suka dubeshi. Abinda ya faru a ranar da sukaje ɗaurin aure gidan Alhaji Saminun ya shiga dawo mata a rai. In dai batai kuskuren fahimta ba shine yaron da Hajiya Majdiya ke mata bayanin yana son Maanal kenan. Wani irin sanyi taji a ranta, dan koba komai ita dai yaron ya shiga ranta a lokaci guda, sannan ta samu karɓuwar addu'ar ta akan al'amarin Maanal ɗin da Yazeed tunda ga raba gardama yazo.. Shikam Daddy murmushi yayi cike da nuna mamaki ya ce, “Ikon ALLAH ashe ma kai ɗin na gida ne doctor. Ai nasan Hajiya Majdiya kuwa sosai saboda Alhaji Saminu aminine kuma ɗan uwana ta fanin mahaifiya, zan iya cemaka ma neman auren Majdiya da komai dani akayisa”. Wani ɗan karen daɗi ne ya ratsa RK har cikin maƙwallaton zuciya. Sai yake jin gaba ɗaya matsakarsa ma shi ta ƙare kenan. Nan take ya ƙara sakewa da Daddy. A karo na farko Daddy ya shiga ɗakin da Maanal ke kwance shi da Ammie da Nene kawai. Sosai tausayin Maanal ya ƙara mamayesu, dan Ammie kasa daurewa tayi sai da tai kuka. Duk wanda yaga Maanal ɗin sai yayi matuƙar tausaya mata. Numfashi ma sai da taimakon na'urori take yinsa. Duk ta sake figewa. Sun mata addu'a suka fito aka bar Nene kawai dan doctor ya buƙaci a ɗan goge mata jiki a canja mata kayan jikinta. Da ance Ammie tayi amma ta nuna bazata iya ba. Sai dai Nene tayi. Tsaf Nene ta gogema Manaal jiki aka canja mata kaya. Doctor da RK suka shigo, hakan yasa Nene fita ta basu waje dan suyi aikinsu. Ta tarar da Hajiya Basariyya cike fam da takaici, wai tana fushine ita ba'ace ta shiga ta duba Maanal ba, shine taima Daddy ƙorafi akan hakan. Shi kuma yaƙi tanka mata shine ta cika tai fam. Ita dai Ammie haƙuri ta bata, yayinda su Amal ke mamakin abinda Hajiya Basariyyan tayi. Ita kanta Nene abin ya bata mamaki, dan bataga abin wani ƙorafi ba a wajen tunda gasu Shahidah suma ba'a barsu sun ganta ba. Ita kanta dan Ammie tace bazata iya gogema Maanal ɗin jiki bane aka barta ta shigan. A haka Yazeed da yaje Kaduna ya dawo ya samesu, tare da duk yaran gidan yake tafe, amma abin mamaki yau ɗin ma Hajiya Yaya bata zo ba.... Da mamaki Amrah ke kallon RK, har dai ta kasa haƙuri sai da tayi magana. Murmushi yay mata da tambayarta ya gajiyar biki. Hakan data faru tsakanin Amrah da RK sai ya tsayama Yazeed a zuciya har sai da ya kira Amrah ɗin gefe ya binciketa. Kanta tsaye ta sanar masa abinda ta sani. Yayi mamaki ƙwarai da gaske. Haba no wonder yake mamakin yanda RK ɗin ke tsaye very serious akan case ɗin Manaal ɗin. Ya jima yana son haɗa al'amarin a ransa amma ya gaza samun makama, tunda shi dai sun fitone kawai suka samu motar RK ɗin a ƙofar gida, daga wannan taimakon kuma na kawosu asibiti baiyi tunanin cigaba da ganinsa ba amma sai yaga ya tsaya tsayin daka komai anayi da shi, yayi tunanin kawai tausayi da taimakone sai da aka dawo Abujar nan ya ɗan fara zargi a ransa sai kuma dai yay saurin kaudawa tunda bashi da tabbas musamman ganin RK ɗin matsayin likita shima. Ashe kuwa hakanne. A ranar su Amrah suka koma Kaduna harda Hajiya Basariyya data wuce bisa tirsasawar Daddy dan kuwa badan taso ba, taso ace sai taga kwal uwar daka. Ta zata da Daddyn zasu tafi sai yace mata shi yana nan har sai yaga yanda hali yayi akan jikin Maanal ɗin. Hakan ya masifar ƙona mata rai, dan ta kalla abunne a sigar rainin hankali irin na maza kawai. A ganinta Daddyn nason holewa da Ammie ne a wannan ƙayataccen gida shine ya fake da ciwon agola. Ita Ammie tsaf ta fahimci manufar Hajiya Basariyya ɗin, amma sai ta basar kawai tama dinga ƙarfafa Daddy ɗin akan yaje suma suna da hakki a kansa, tunda dai Maanal ɗin tana samun dukkan kulawa anan ɗin gasu kuma ga Yazeed shi yaje ya huta gashi ya dawo daga tafiya. Sam Daddy ƙin saurararta yayi, daga ƙarshe ma ya fara fushi da ita dole tai shiru ta zuba masa ido kawai su Hajiya Basariyyan suka wuce... A ɓangaren Yazeed kuwa ya fara janye jikinsa daga RK. Tun RK ɗin bai fara fahimta ba har ya fahimta. Dan sai wani isa ma Yazeed ke nuna masa akan Maanal ɗin yanzu da gadara. Mamaki hakan ya bama RK, dan shi a zatonsa Yazeed da Maanal uwa ɗaya uba suke ko uba ɗaya dan yana ɗan tantamar Ammie ta isa haihuwar kamar Yazeed ɗin. Bai daiyi magana ba yabar abin a ransa dan ganin iya gudun ruwan Yazeed ɗin. Ana cikin wannan dambarwa a tsakaninsu Hajiya Majdiya yayarsa tazo duba Maanal ita da yaranta tun daga Zaria. Dan shine ya kirata yake sanar mata, aiko baiwar ALLAH sai gata tazo. Ammie tayi mamakin hakan kasancewar batai waya da Hajiya Majdiya ɗin ba akan hakan. Sai Hajiya Majdiyan ke sanar mata, “Sirikinki ne ya kirani yake sanar min ai.” Murmushi Ammie tai da faɗin, “Haba nayi mamaki fa, sai kuma hankalina bai kawo nan ɗin ba. Ai babu abinda zamuce da Rafeeq sai fatan alkairi. ALLAH yay masa albarka”. “Amin ya rabbi. Yaya jikin nata yanzu? Dan naga hankalinsa a tashe yake matuƙa yau har cewa yay na nema masa masu saukar Alkur'ani yana son ai mata”. Ajiyar zuciya Ammie ta sauke. Zuciyarta na sake jin nutsuwa da RK ɗin. “ALLAH sarki, ALLAH ya saka masa da alkairi. To Alhamdullahi zamu ce. Sai dai har yanzu bata san wanda ke kanta ba. Amma dai suna tabbatar mana bugun zuciyarta na dai-daita zuwa yanzu. Kowane lokaci kuma zata iya farfaɗowa cikin hayyacinta.” “ALLAH ya bata lafiya, yasa ya zama kaffara. Abin tausayi yarinya ƙarama haka da wannan irin babban ciwo mai haɗarin gaske, ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawoyinmu. Shiyyasa gata nan sanyi-sanyi ko kuzarin kirki bata da shi. Ban taɓa sanin tana da wannan lalurarba ai da tuni na haɗaku da Rafeeq ɗin dan aikinsa ne. Yanzu haka reshen wannan asibitin suka buɗe acan garin jos shine yaje can da kansa yake riƙe da asibitin kusan shekara ɗaya kenan, anan ne ma ALLAH ya haɗasa da ita”. Murmushi Ammie tayi tare da jera addu'a ma RK ɗin. Ganin yanda Ammie ta ɗauki zancen da muhimmanci Hajiya Majdiya ta cigaba dama ɗan uwanta campaign wajen Ammie. Yinin gaba ɗaya suna a tare sai bayan Magrib RK ya ɗaukesu ya maida can gidan babbar yayarsu dake nan Abujan zasu kwana anan dan sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu koma Zaria. Sosai Ammie taji daɗin kasancewa da Hajiya Majdiya a wannan rana. Dan zaman ya sake tasirantar da abinda take ji a zuciyarta game da RK da Maanal idan har ALLAH ya tashi kafaɗunta. Bata ɓoyema Nene da su Shahidah ba akan alaƙar Dr Rafeeq ɗin da Maanal. Suma sai abin yay musu daɗi matuƙa, dan suna ganin idan har ALLAH ya baiwa Maanal lafiya wannan itace hanya mafi sauƙi da maganar Yazeed zata janye cikin sauƙi batare da sun ɓata ran Daddy ba kamar yanda duk suke gudu. Dan gwara dai a haƙura da batun Yazeed ɗin nan haka nan tunda dama ita wadda ake dan ita bawai tana sonsa bane. Abu na biyu sudai a haka yanayin Dr RK ya musu hundred percent, dan mutum ne mai sauƙin kai ga girmama na gaba da shi, ga yanda yake ɗawainiya dasu a asibitin nan cike da mutuntawa ma abin a soshi ne. Shi kansa Daddyn sun fahimci RK ɗin ya shiga ransa. Sai dai babbar matsalar sun san ga Yazeed za'a sameta kam. Dan kowa yasan Yazeed na matuƙar son Maanal wannan a bayyane yake. Sannan shi kansa mutumin kirki ne, dan yana da nagartattun halaye masu yawan gaske daya gada ga Daddy, tako ina Yazeed ya cancanci zama mijin Maanal kodan halaccinsa garesu, dan hatta Daddy ya sansu ne a dalilin Yazeed. Sannan kodan Daddy a bama Yazeed auren Maanal, mahaifiyarsa ce kawai matsalar gaskiya, dan Hajiya Yaya sam ba kanwar lasa bace. Bata da kirki ko misƙala zarratin, kanta kawai ta sani, kuma tabbas zata iya aikata komai akan wannan auren kamar yanda take shan faɗa idan har akayisa. ALLAH dai ya bama Maanal ɗin lafiya, zasu cigaba da tayata addu'ar zaɓin alkairi dan duk MAZAJE biyun nan sun matuƙar cancanta da aurenta... ★ A mota Hajiya Majdiya ke bama RK labarin hirarrakinsu da Ammie, babu abinda yake sai murmushi da ƙara jin ƙaunar ƴar uwar tasa. Sai da ta gama bashi labari tsaf sannan ya jeho mata tambayar abinda ke cimasa zuciya.. “Humm Aunty Alhamdullah na samu karɓuwa wajen Ammie da ƴan uwan Maanal, sai dai ba duka ba”. “Kamar ya ba duka ba miye matsalar to?”. “Yazeed Aunty, Yazeed shine matsalar kuma na fahimci yana da ƙarfin faɗa aji akan ƴan uwan nasa. Da farko dai ni da shi normal gaskiya. Amma kwana biyun nan ban san miyyasa ba ko ya fahimci alaƙata da Maanal ɗin sai naga yana jajja baya dani, sannan yana min gadara da al'amarin Maanal ɗin. Dan ma baida yanda zaiyi ne kasancewata ɗaya daga cikin likitocinta shiyyasa. Har abin ya fara bani mamaki dan kamar wani mai kishi da ni. Sai dai nasan ba hakan bane tunda mizai sakashi yin kishi akan wadda suke Uba ɗaya ne ko uwa ɗaya ma ban sani ba”. Ya ƙare maganar cikin damuwa sosai. Fuskar Hajiya Majdiya cike da damuwa itama ta furta, “To kodai Yazeed ma son Maanal yake?”. “What?!!!”.. RK ya faɗa a ɗan razane yana taka birki da sauri.........✍️ 🤣Sai ka ɓarar daku malam Rafeequ ✨ZAFAFAN DAI ✨ 1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ 🅿️➖1️⃣3️⃣ ______________ Abubuwan da nake saidawa Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries ______________ ........“Kamar ya sonta Aunty? Wace magana kike haka? Ba mahaifinsu ɗaya ba?”. “Ba mahaifinsu ɗaya ba Rafeeq. Dan Alhaji Usman bashi ne ya haifi Maanal ba ita da yan uwanta biyu mata. Ƙannen Maanal maza biyu da kake gani Waleed da Hameed sune ƴaƴan dake tsakaninsa da Hajiya Asiya. Kaga ko zata iya kasancewa Yazeed son Maanal yake yi shiyyasa. Kuma kamar yanda ka faɗa ya fahimci kana sonta ne a yanzu shiyyasa ya canja maka. Amma ka bari zan bincika komai in sha ALLAHU”. Wata irin zufa ce ta gauraye illahirin jikin RK. Idanunsa har sun kaɗa na damuwa. Yana ganin ya fara bin hanyar nasara ashe akwai sabuwar ƙura a tafiyar, dan tabbas indai har Yazeed son Maanal yake da wahala shi ya samu. Ammie dai bazataƙi ɗan mijinta ba, haka shima Alhaji Usman ɗin bazai ƙi ɗansa ba, ita kanta Maanal ɗin bashi da tabbacin bata son Yazeed ɗin ma a..... “Kaga ka kwantar da hankalinka fa, in sha ALLAHU komai zai kasance cikin sauƙi. Ba nace zaka iya samun Maanal bane cikin sauƙi, ban kuma ce bazaka iya samunta ba tunda komai na ALLAH ne. Dan haɗin Yazeed da Maanal zai yi matuƙar wahala saboda nasan wacece mahaifiyar Yazeed. Hajiya Sadiyya da wahala ta amince da wannan haɗin musamman yanda nasan tayi bala'in tsanar Hajiya Asiya. Dan haka kada ka karaya da izinin ALLAH nasara tamu ce, kai dai kawai ka cigaba da neman soyayyar yarinyar shine babban makami a hannunka bayan goyon bayan Hajiya Asiya a yanzu”. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Sai kuma ya zari handkhachief ya goge zufar goshinsa. “Hakane kam Aunty, ina jin tsorone kawai kar ya kasance itama Maanal ɗin tana sonshi, wannan kam kinga bazan iya jayayya da kowa ba tunda itace mai zaman auren.” “Eh tabbas kam, amma nidai ban taɓa jin akwai wata alaƙar soyayya a tsakaninsu ɗin ba gaskiya. Tunda da akwai na faɗa maka mahaifiyar Yazeed sai a hankali ce, da sam bazata bari a zauna lafiya ba. Amma yanzu ma inda wata shawara, ka samu lokaci ka shigo Zaria wajen Abbansu Najma. Ka masa bayani a matsayin kana son ya maka iso wajen Alhaji Usman ɗin akan maganar mana, ni kuma kafin kazo zan sake bincikawar kamar yanda nayi maka alƙawari”. Ajiyar zuciya mai haɗe da ƙayataccen murmushi RK ya saki, sai kuma ya kama hannun ƴar uwar tasa ta sumbata yana faɗin, “ALLAH ya saki a aljanna Aunty na mai share kuka na”. Dariya tayi tana mai kai masa ɗan rankwashi a kai, hakan ne ya sakashi shima yin dariyar sannan ya tada motar suka cigaba da tafiya...... ✨✨✨✨✨✨✨ Alhamdullah wannan zuri'a suna cikin farin cikin farfaɗowar Maanal a yau, duk da ba'a barsu sun ganta ba har zuwa yanzu saboda likita dake tare da ita hakan bai hana bayyanar murmushi a fuskokinsu ba. Sai da su Dr Ranjet suka gama mata dukkan abinda ya dace kafin su ka buƙaci Nene dake goge mata jiki kullum ta shiga ta goge matan. Shahidah da Amal kuma sukai shirin komawa gida haɗo mata abincin da Doctor yace zata iya ci. Bayan kammalawar Nene Daddy da Ammie ne suka fara shiga. Tana kwance fayau da ita saboda ramar da tayi na ciwo. Gaba ɗaya na'urorin da aka sanya mata a kwanakin da suka gabata an janyesu, sai igiyar daketa jikin hancinta kawai. Jin ƙamshin turaren Daddy kusa da ita sosai ya sakata buɗe idanunta da suka ɗan kumburo, daga cikinsu sun ɗan yi ja sun kuma ƙara girma. Daga shi har Ammie dake tsaye ta zubama idanun, sai kuma a hankali ta saki murmushi mai sanyi tare da miƙa musu hannunta. Ammie dake murmushi tana hawaye ce ta kama hannun tana kaiwa zaune bakin gadon kusa da ita. Yayin da shi kuma Daddy ya ɗan duƙo ya shafa kanta yana murmushi shima, kafin yakai zaune a kujerar gaban gadon. “Sannu kinji Daughter. ALLAH ya baki lafiya yasa kaffara ne”. Kanta ta ɗan jinjina tana sakin murmushi, sai kuma ta motsa lips ɗinta a hankali ta furta, “Amin Daddy nagode”. Murmushi ya sake mata, tausayin yarinyar da ƙaunarta na sake gauraye zuciyarsa. Maanal ta maida kallonta ga Ammie dake sharar hawaye. Nan ma a hankali ta ce, “Ammie ki daina kuka na samu lafiya fa”. Kai Ammie ta shiga jinjina mata tana share hawayen da sakin ƴar dariya. “Na daina Maanal kinji, ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana. ALLAH yasa kaffara ne, ALLAH ya rabaki da wannan ciwo gaba ɗaya”. “Amin Ammie nagode. Ina su Didi fa?”. “Sunje gida yimiki abinci yanzu zakiga sun dawo. Ko kina son cin wani abune a kirasu su yi miki?”. Ɗan shiru tayi alamar tunani, sai kuma ta kalla Daddy dake ta kallonsu yana murmushi, itama ɗan murmushin ta masa sannan ta sake maida dubanta ga Ammien. “Ammie sumin faten dankali, sai kunun gyaɗa” “To shike nan bari na kirasu karsu taho”. Kai Maanal ta jinjina mata, yayinda Ammie ke ƙoƙarin kiran su Amal. Dai-dai nan Yazeed ya shigo ɗakin da sallama Waleed riƙe da hannunsa, sai Hameed biye da su. Daddy ne ya amsa masa. Yayinda ita kuma ta zuba musu raunannun idanunta. Da sauri Hameed da Waleed sukayo inda take cike da farin cikin ganin idanunta a buɗe. Hannunta duk suka kama suka riƙe suna kaiwa durƙushe daga ƙasa ta yanda fuskokinsu zasu daidaita da tata. “Alhamdullahi Didi ta samu lafiya”. Cewar Hameed yana sake ƙanƙame hannunta. Shima Waleed cike da ɗoki ya furta, “ALLAH mun gode maka yau muna cikin farin ciki Daddy Didi ta buɗe ido”. Ƙaramar dariya Daddy yayi da faɗin, “Alhamdullahi” shima. Maanal cikin magana a hankali tace, “Ƴan turai kamarku daban”. Dariya duk suka ƙyalƙyale da shi. Itama saita maida kallonta ga Yazeed dake tsaye kawai yana kallonsu fuskarsa ƙawace da murmushin farin ciki. Kallon da take masa ya sashi ƙarasa ƙarasowa gaban gadon sosai. Sai kawai ta lumshe nata idanun a hankali ta kuma sake buɗewa duk a lokaci guda. “Alhamdullahi. Sannu Maanal ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffarane kinji”. Murmushi ta sakar masa a karo na farko, murya can ƙasa ta ce, “Amin Yaya nagode”. Amsa mata yay cike da farin ciki, jiyake tamkar ya rungumeta a jikinsa sai dai babu damar hakan. Balle ma ga Ammie a wajen ga Daddy. Suna a hakan dai kuma sai ga RK. Tunda ya shigo idanunsa akan Maanal ɗin ne shima, itama dai shi ɗin take kallo da ɗunbin mamaki. Yayinda zuciyarta ke raya mata (shi wannan duk inda naje sai ya bini ne shin?) Rashin mai bata amsa yasata janye idanunta a zahiri daga kansa. Shima sai dai janye nasan yayi tare da ƙarasowa ya gaida Daddy da Ammie cike da girmamawa. Maanal ta sake shan mamakin ganin yanda duka amsa masa da kulawa da alamar sanayya sosai kuma. Dubansa ya maida a kanta yana mai ɗan kashe mata ido, hakanne ya sakata yimasa ƙaramar harara. Murmushi ya saki mai faɗi da ƙoƙarin ɗaukar file ɗinta dake a drower ɗin gefen gadon yana faɗin, “Gawa taƙi rami yaya jikin?”. Dariya Daddy da su Waleed sukayi, yayinda Ammie tai ɗan murmushi kawai. Yazeed kam fuska ya sake tamkewa kamar bai san minene dariya ba. Yayinda Maanal ta ɗan tsuke fuska itama tana hararar RK ɗin yanzu ma. Yi yay kamar bai ganta ba ya miƙama Yazeed hannu cike da shaƙiyanci yana faɗin, “Babban Yaya barka ƙanwa ta miƙe. ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne ya kiyaye gaba”. Rasa abinyi Yazeed yayi, sai mamakin RK ɗin ke sake mamaye masa zuciya. Wani gefe kuma na tunanin RK fa bawai yasan ainahin alaƙarsa da Maanal bane, dan kuwa kallon yayanta uba ɗaya yake masa kenan. Daurewa yay ya ɗan sake fuska ganin Daddy na kallonsu ya bashi hannun shima suka gaisa yana amsawa da, “Amin doctor muna godiya, kuma kunyi ƙoƙari ai sai fatan alkairi a gareku”. “Doctor!”. Manaal ta faɗa a hankali cikin suɓutar baki idonta akan RK. Kafin ma RK yay wani yunƙurin bata amsa Waleed yabata amsar da “Eh mana Aunty shine likitanki tare da Dr Ranjet. Kuma yana da kirki kullum sai yaje damu yawo ya saya mana abubuwa, yana kuma cemana mu dinga miki addu'a a dallarmu ALLAH ya baki lafiya ko warke gaba ɗaya ki daina wannan ciwon ”. Sake dai kallon RK ɗin Maanal tayi kawai, zuciyarta na wani irin motsawa a ƙirjinta da sauri-sauri kamar ma ciwon nason dawowa sabone komi. Ganin kallon da Ammie ke mata ta sata lumshe idanu kawai tai shiru dan ita kam bata kuma san abin faɗaba bayan hakan. Ɓoyayyen murmushi kawai RK yayi yana cigaba da dudduba abinda ya kamata, sai kuma ya fara mata tambayoyi a hankali. Dole ta buɗe idanunta a kansa dan yanda yake magana can ƙasa-ƙasa tsigar jikinta har tashi take. Kasa amsa masa ko ɗaya tayi da baki, sai jinjina masa kai kawai da girgizawa. Wani irin kishi ne ya turniƙe Yazeed, dan shi mutum ne mai kishi sosai. Rai a ɓace ya ɗan duƙo shima gareta murya can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kina son cin wani abu Miss?”. Idanunta ta ɗan maida garesa, “Yaya su Didi na zuwa da abinci ai”. Ta faɗa a hankali dan muryan baya fita sosai. Cikin jinjina mata kansa ya ce, “Na sani, ko ɗan fruit haka baƙya so? Ko wani abu bayan abincin?”. “Zanci apple to, amma green”. “An gama Baby”. Ya faɗa cikin raɗa ta yanda ita kaɗai taji sai RK dake kusa da su sosai. Saurin kauda kanta tayi, sai kuma ta kalla sashen da Ammie da Daddy suke. Ganin hankalinsu na kan su Waleed yasa ta sauke ajiyar zuciya. RK ta ɗan kalla, sai taga shima yay wani kicin-kicin da fuska yanata rubutu a file ɗin ta. Tana ƙoƙarin janyewa ya ɗago nasa idanun sai caraf a nata. Wani miskilin murmushi ya sakar mata tare da sake duƙowa kusa da ita gab, cikin raɗar shima ya furta, “Apple yana cikin abinda bazaki ci ba a yanzu wife to be, dan haka kada ki ma wahalar da Yayanmu”. Ya ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya sai kuma ya kalla Yazeed ya sakar masa wani ɗan iskan murmushin rainin hankali. (Nikam mike damun waɗan nan?) Maanal ta faɗa a zuciyarta dan tama rasa yanda zata masalta al'amarin nasu. Tana fama da kanta sunzo sun sakata tsakkiya

Chapter 7 of 17