zaman ƙuncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan nan sai dai ta kasance a ƙarƙashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan alƙawuran da girmana agaban ƴaƴana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya naga bayanta amma ba'a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace faɗa a gabana Baba”. Ta fashe da kuka.
“Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin dazan ɗauka jeki kwanta”.
Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana miƙewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema baban ne ya mutu. Sai da ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce, “Nikam da zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa. Idan ta kama ma can gidan nasa zakaje ka tasata gaba ka haɗasu har abokan zaman nata. Karfa dan ka raini Usman ya zama kana tauye masa hakki akan ƴar da ka haifa.”
“Ai ke kinji matsalarki, idan har abu zai taso akan yaran nan sai kin nuna ban iya ba ke sarkin tawakkali da gaskiya ko”.
“Ba haka bane Dattijo. Masu iya maganafa sunce kaso naka duniya ta ƙisa, ka ƙisa duniya ta soshi. Usman na maka matuƙar biyyar da kosu ƴaƴan da ka haifa ba kowa ke maka irinta ba. To bai kamata a cigaba da ƙasƙantar da shi ba akan abinda ya isa da shi. Wannan fa rayuwar aurensu ce. Kuma shine shugaba a gidan, yin kutse a al'amarin kamar ƙasƙantar da shi ne. Dan ALLAH kada ka biyema yaran nan ana ganin ka da kima da mutunci irin na uba kuma shugaba”.
Shiru yay na kusan minti biyu, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Hakane kuma Adama nagode da tunatarwa. In sha ALLAHU gobe zan tasata gaba muje gidan. Sai dai ance min shi Usman ɗin baya ƙasar, amma dai inada tabbacin kamar yau ne da dare zai dawo”.
“To Alhmdllh gobe idan ALLAH ya kaimu ɗin sai kuje, ALLAH ya taƙaita al'amarin kuma ya daidaita su”.
“To Amin ya rabbi. Yarane sai addu'a kawai yanzu, sun maida aure wasan yara”......
__________★
Isowar dare Daddy da Hajiya Basariyya sukai ma gidan. Tafiyar kwana goma har sunyi fresh abinsu. Babu wanda yasan da dawowar tasu, dan ita Ammie ma harta kwanta abinta. Cikin barci taji wayarta na ƙara. Da ƙyar ta buɗe ido ta jawota dan ta manta ne ma bata kashe ba. Ɗagawa tai takai kunne tare da sallama. Sai dai Muryar wanda ya amsa mata da umarnin daya bata ya sata watsakkewa sai kuma ta tashi zaune. Jin abin tai kamar mafarki, amma dai ta miƙe ta ɗauka dogon hijjab ta saka sannan ta nufi kitchen. Tea ɗin daya buƙata ta haɗa masa. Sai ta haɗa da ɗan snacks da fruits da bata rabo da su. Haka ta fito gidan shiru alamar kowa ya kwanta ta nufi sashen maigidan. Takai hannu zatai knocking ta tsaya cak sakamakon jin muryar Hajiya Basariyya na tashi a sama cikin faɗa...
“To amma dare yayi ai, ƙarfe nawa yanzu da zaka ɗaga waya ka kirata wai ta kawo maka abu. Ni banda hannune ko abinda zata kawo makan banda shi a sashena? Randa kuka dawo Abuja wayasan kun dawo ba sai tashi mukai muka ganku a gidan nan ba. Sai ni daka raina. Wai mi Asiya tafimu dashi ne? Mi take dashi na mata da mu bamu da shi da kake son ganin ka fifitata a kammu?!!.......”
“Badariyya wai kina da hankali kuwa. Baki ganin dare yayi zaki zo kina min ihu a kaina. Da kike maganar miyasa zan kirata ta kawo min abu ke da kika dawo daga tafiya mizaki bani? Sannan batun fin sauran mata da kike sai yanzu kika san Asia tafi sauran mata ashe. To lallai kin makaro da kika kasa fahimtar hakan tun tuni. Ita da na saka kika bini a ranar girkinta kinji tayi wani ƙorafi ne. Kuma randa muka dawo Abuja ni Asia bata kwana a sashen nan ba, idan ma ta kwana ai matatace. Dan haka ki fice min anan shasha kawai tana girma bata san ta girma ɗin ba”.
“Ni ce shashashar Daddy Huznah?”.
Banza yay mata bai tanka ba. Sai maida hankalinsa yay a kiran Ammie. Da sauri ta danne wayar gudun kartai ƙara. Sai kuma ta daure tai knocking ƙofar. Umarnin shiga ya bata. Koda ta shigo kai tsaye a Centre table ta ajiye tray ɗin, sai kuma ta shiga gaishesu su duka a tare da yimusu barka da dawowa. Daddy ne kawai ya amsa mata. Zata juya tabar falon ya katse hanzarin ta. “Ina zaki kuma”.
Juyowa tai ta kallesa. “Zanje na kwanta ne, kuma ku samu ku ɗan rintsa ku huta gajiya ko”.
“Dawo ai anan zaki kwana”.
“Anan kuma Daddyn Hameed amma ai....”
Cikin katseta ya ɗaga mata hannu. Dole ta haɗiye abinda take son faɗar. Cikin ɓacin rai Hajiya Basariyya taja akwatinta da hand bag ta fice a sashen tana jan tsaki. Da kallo Ammie ta bita harta gama ficewa. Tai wani kalar masifar bugo ƙofar har sai da Ammie ta zabura. Cikin sanyin jiki ta maida dubanta ga Daddy dake ƙoƙarin fara shan shayinsa hankali kwance. “Daddyn Hameed dan ALLAH....”
“Asia! Kin san bana son jan zance ko!”.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke kawai, badan taso ba tabi umarninsa a yanda yake buƙata.......
__________★
Washe gari kusan ƙarfe goma na safe sai ga baƙi. Ammie na tsaka da haɗama Daddy abinci zai fara ci maigadi ya isar da saƙon zuwan Alhaji Mamman sirikin na Daddy kuma uban gidansa. Da sauri Daddy ya miƙe tare da shiga ciki ya canjo kayan jikinsa zuwa jallabiya. Yayinda Ammie kuma ta fita ta ƙofar baya domin ƙaro abincin. Bata wani jimaba ta koma ɗauke da wani kayan abincin. Ta samu har Daddy ya shigo da shi falonsa shi da babban amininsa sai Hajiya Yaya. Ajiye kayan Ammie tai cike da girmamawa ta rissina ta gaishesu batare data damu da hararar da Hajiya Yaya ke mata ba. Sun amsa mata da kulawa. Dan haka kawai sai Alhaji Mamman ɗin yaji Ammien ta masa kwarjini da shiga ransa. Bai fi sau biyu ya taɓa ganinta ba. Lokacin ruguntsumin aurenta sai kuma da sukaje da Daddy gaishesa bayan sun dawo Hajiya Yaya ta dinga zuba tujara daga nan Ammie ta ɗau aniyar bazata sake zuwa gaidashin ba. Daga mutunci sai abu ya zama fitina da cin mutunci, tun daga nan ko Daddy yace tazo suje sai tayi yanda tai ta zame jikinta. Abincin ta shirya a gabansu sannan ta fita domin basu damar ci, duk da dai Baban yace sun gode bazasu ci ba sukam. Amma Daddy nata roƙonsu. Dole dai suka ɗan taɓa kaɗan, kafin Baban yasa Daddy kira masa su Ammie su duka. Dai-dai nan kuma Yazeed ya shigo falon daga gani isowarsa garin kenan. Dan tunda daren jiya Ammie ta tura masa sako akan dawowar su Daddy ɗin, tare da bashi shawarar ya taho da safen dan ta samesa a gida shiyyasa yay sakkon tahowa kafin ya sake guduwa. Yana fatan iyayen nasa su sasanta kansu komai ya wuce kada abun yayta ƙara girma. Sai kuma akai sa'a ya samu kakan nasa yazo tare da mahaifiyar tasa gidan. Cikin girmamawa ya gaida kakan nasa sannan ya gaida abokinsa. Sun amsa masa da kulawa da tambayarsa aiki tare da tsokanarsa akan ƙara zama tuzuru babu aure. Murmushi kawai yay ya maida hankalinsa a gaida Daddy sannan ya gaida Hajiya Yaya itama. Dai-dai nan Hajiya Basariyya da Ammie suka shigo suma. Gaidasu yayi suma da girmamawa. Ammie ce kawai ta amsa masa da kulawa. Hajiya Basariyya kam sama-sama dan tana cikin haushi ne. Ko su baba sama-sama ta gaishesu kamar an mata dole. Anan ma sai Baban ya sake karantar abubuwa da dama. Bayan an natsa da gaishe-gaishe aminin Baba da suke kira Alhaji Kallah ya buɗe taron da addu'a. Daga haka ya kalla Daddy cikin mutuntawa ya kirayi sunansa.
“Usman!”.
“Na'am Baba”.
Daddy ya amsa masa da girmamawa dan shima yana ɗaukarsa matsayin uba ne. Kai duk ma abokan Alhaji Mamman a rayuwa Daddy na basu girma irin na uba ne. Alhaji Kalla ya cigaba da faɗin, “Mike faruwa tsakaninka da iyalinka ka turata gida har tsahon kwanaki babu wani bayani”.
“Baba ni bani na tura ba”..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣8️⃣
.......“Ban gane ba Usman, kamin bayani yanda zan gane da ƙyau”.
Kai Daddy ya jinjinama Baba Kallah. Kafin ya gyara zamansa da ƙyau ya shiga zayyano masa abinda ya sani. Kuma ma duk ita Hajiya Yaya ce ta kirashi a waya ta sanar masa. Daga ƙarshe ya dora da faɗin, “Gasu nan baba ka tambayesu daga Asia ɗin har Basariyya akwai wanda na zaunar naima magana akan batun? Na barsu ne har sanda yarinyar zata samu lafiya dan shine mafi muhimmanci. Amma sai ita ta nuna min ban isa ba. Nace taje ta duba yarinyar ita da yara sashenta tace ban isa ba ita kuma Basariyya taje, hakan yasa na dakatar da ita da shigowa wajena.....”
“Dolene to sai naje. Itama Basariyyan ai munafunci da gulma ne ya kaita badan ALLAH ba”. Hajiya Yaya ta faɗa cikin katse Daddy. Tsawa Babanta ya daka mata shima, dole tai shiru tana kumbura fuska.
“Usman kamin dai-dai, dan abinda kayi ɗin shine mazantaka.” baba Kalla ya faɗa, sai kuma ya juya ga Hajiya Yaya yana mai kiran sunanta. “Sadiyy! Dukkan abinda Usman ya faɗa haka akai?”.
Babu musu ta jin jina kanta. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Baba nifa tsakanina da ALLAH koda aurena zai ƙare ne tsakanina da Usman sai dai ya ƙare a yau. Dan haka ku zama shaida ban amince Yazeed ya auri ƴar Asiya ba. Idan kuma ba hakaba a shirye nake na fiddashi a cikin ƴaƴana na barma Asiya tunda haka naga yake buƙata. Na gaya masa na masa faɗa amma yana maidani ban san abinda nake ba, to tunda haka ne dai ya zaɓa ko ni ko yarinyar”.
Hankali tashe Yazeed ke duban mahaifiyar tasa. Zai yi magana Baba Kalla ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu. Dole Yazeed yay shiru.
“Sadiyya miyyasa baki son shi haɗin nasu? Yarinyar nada wata illane da musulunci ya hanamu auren irinsu?”.
“Illoli da yawa kuwa Baba. Ciwuwwuka sun gama zagaye rayuwarta. Sannan mu har yanzu bamu da tabbacin ma suna da uba tunda mudai bamu taɓa ganin dangin uban nasu ba balle mu shaida, har bikin yayunta akai a gidan nan mudai bamuga kowa ba, wama ya sani ko basu da uban ne shiyyasa sam ni jinina bai wani haɗu da nata ba dan bana ƙaunar yarinyar nan, ba kuma na ƙaunar uwarta gata nan”. Ta ƙare maganar da nuna Ammie babu nauyi ko kara. Kai baba Kalla ya girgiza da faɗin, “Ashsha Sadiyya, wannan magana tayi tsauri da yawa. Kiyi ƙoƙari ki dinga gyara harshenki yayin magana. Dan haka karna sake jin irin wannan zancen banzar ya fito. Munji baki son wannan haɗin, wacece kika fidda masa ke a matsayin matar?”.
“Baba Nazeefar Sabuwa. Idan har Yazeed yana son yaga farin cikina to ya aurenta dan ita nasa tushenta. Idan ko ba haka ba ya shirya rayuwar auren ƙunci da baƙin ciki, sannan duk abinda zata haifa babu ruwana da su kamar yanda shima na ciresa daga cikin ƴaƴana.....”
Cikin takaicinta da harzuƙa Daddy ya ce, “Aiko baki isaba wlhy, Maanal na zaɓama yarona matsayin matarsa ko kina so ko baki so, kuma wlhy first and last da zaki sake sheganta yaran nan idan ba hakaba kuwa sai ranki ya ɓaci fiye da yanda kike zato....”
“Kaima kuwa baka isaba Usman, dan yanda kake jin kai uban Yazeed ne nima nice mahaifiyarsa. Nina ɗauki cikinsa na tsawon wata tara, nai naƙudarsa na kumayi rainonsa haɗe da tarbiyya har yakai girman da wata banza a banza daka kawo gidan ka kake ɗaukar ta a mutum ta isa ta mallake min shi, kai wlhy duk abinda kake ji ka iya na iya fiye da iyawarka Usman, dan....
“Sadiyya!!!”.
Babanta ya katseta a tsawace. Shiru tai amma a ranta tana ƙunƙuni, dan ta ɗau aniyar koma miza'ayi sai dai ayi amma Yazeed bazai auri ɗiyar Asiya ba dan ita zuwa yanzu ma ta fara tunanin basu da uban. Ganin ran baba ya kai ƙolokuwar ɓaci hakama Daddy da ita Hajiya Yayan Ammie dake saurarensu kawai ziciyarta na mata ƙuna cike da girmamawa ta kalla Baba. “Baba dan ALLAH ina neman alfarma”.
“Faɗi ko minene ɗiyata in dai ina da shi zan miki”.
Wani takaici ne ya lulluɓe zuciyar Hajiya Yaya ganin yanda Babanta ke bama Ammie muhimmanci a zaman fiye da ita. Baki ta buɗe zatai magana ya harareta. Dole tai shiru ta cigaba da hare-harenta. Ammie bata nuna ta damu ba ta cigaba da faɗin, “Baba dan ALLAH ku barta ta aura masa wadda take so. Domin gaskiya ta faɗa Maanal bata dako isashiyar lafiya ma. A yanzu haka likitocin ma sunce tana matuƙar buƙatar hutu ta yanda al'amuranta zasu dai-daita. Shi kuma Yazeed za'a cigaba da tauyesa babu aurene saboda hakan. Bayan UBANGIJI ya halatta masa auren mata har uku ne. Idan har Maanal matarsa ce ko zuwa nan gaba sai ayi......”
“Allah ya kiyaye, har abada bako za'ayi ba idan abinda kike tunani kenan ki ciresa kuwa....”
Hajiya Yaya ta katse Ammie a harzuƙe. Shima Daddy a harzuƙen ya katseta da faɗin, “Ashe kuwa zaki mutu bayan anyi, dan Maanal ita na zaɓama Yazeed kuma shima itace zaɓinsa aure tsakaninsu babu fashi da izinin UBANGIJI ko da Asiya data haifeta bata yardaba kuwa. Baba ku ƙyaleta, tunda ita bata san masalaha ba dan ALLAH mu zuba aga ni da ita waye keda ƙarfin iko akan Yazeed ɗin.....”
“A'a Usman duk baza'a kai ga haka ba”. Baba Kalla ya faɗa. Batare da ya jira cewarsu ba ya cigaba da faɗin, “Ku duka ku kwantar da hankalinku kuji. A matsayinku na iyayen Yazeedu duk kuna da iko a kansa, amma fa ku sani shima yanada hakki a kanku. Aure dai ba wasa bane, ba kuma jeka ka dawo bane ba. Dan haka ku masa adalci ku barshi ya zaɓi wadda ransa ya kwanta da ita koda a cikin zaɓin naku ne. Idan kuma babu a cikinsu itace ma babbar masalaha ya auro daga can gefe shike nan matsala ta kare. Saboda haka kai Yazeedu kana da wadda kake so ne?”.
A hankali kuma karo na farko Yazeed ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur saboda damuwa. Cikin danne ƙuncin daya mamaye masa zuciya ya ce, “Baba idan har auren duka zaɓin nasu zai zama masalaha na karɓa. Zan auri Maanal ɗin da Nazeefa....”
“Baka isa ba sai dai ka auri Nazeefa ita kaɗai....” Hajiya yaya ta katsesa cikin daka tsawa. Babanta ne shima ya katseta a tsawacen. “Sadiyya bana son shashanci fa. Yaro ya kawo mafita kinama mutane rashin hankali, ko kunyar idona baƙyaji bare nauyi. Shin kokin manta mune a gabanki bashi mijin naki kaɗai da kika raina ba. Ana binki ta lalama kina wani botsarewa saboda wulakanci. To wlhy ki shiga hankalinki. Idan kuma ba hakaba zan hanashi auren Zazeefa ɗin naga yaya zakiyi. Shashancin banza kai”.
Haƙuri ta fara bashi ranta a matuƙar dagule. Tayi hakanne kawai dan ganin yanda ransa ya ɓaci, ta kuma san halin mahaifin nata idan yay magana baya canjawa. Gara ta lallaɓashi suje a haka ita tasan duk ma hanyar da zatabi dan ganin ta tarwatsa wannan aure.... Shima Daddy haƙurin yaba baban, dan haka ya cigaba da faɗin, “Shike nan magana ta ƙare zai auresu su dukan. Dan haka sai kuje ku fara shiri dan nan da watanni biyu za'ayi a wuce wajan. Rana ɗaya za'a ɗaura auren.”
Wani irin motsawa zuciyar Ammie tayi da ƙarfi. Hakama Hajiya Basariyya da tun da aka zauna bata tofa komai ba zuciyarta wani irin raɗaɗi take mata. Ina bazai yiwu ta bari ai wannan haɗin ba, sannan bazata taɓa yarda aima Yazeed auren gata shi kaɗai ba wlhy, Gara a cigaba da wannan fitinar hakan yafi sakata nishaɗi, zai kuma fi bada armashi idan yazam anyi auren Nazeefa da Yazeed ne farko. Ammie zatai magana tai saurin katseta ta hanyar fara yi. “Baba mun gode ALLAH ya saka da alkairi ya kuma sanya albarka a al'amarin. Sai dai nakega maganar ɗaura auren rana ɗaya kamar akwai damuwa musamman ga ita Maanal. Tunda likitoci sunce abarta ta ɗan huta mizai hana a fara yin na Yazeed da Nazeefa daga baya sai ayi da ita Maanal. Komai ma zaifi tafiya a cikin masalaha ni dai anawa ganin, zuwa lokacin itama Maanal ta murmure dan yarinyar ta fyaɗu sosai a wannan karon, wlhy abin tausayi kamar bazata rayuba ma. Sai itama Huznah ta samu miji, Inaga sai a haɗa dana Yazeed ɗin kawai ko yaya kukace”.
A maganar farko Hajiya Yaya wani irin daɗi da godema Hajiya Basariyya ta shigayi a zuciyarta. Daga ƙarshe kuma sai taji zafi danta fahimci hassada Hajiya Basariyya ke son nunawa. Amma zata bita a hakan dan itama ta ribantu. Itama dai Ammie har ranta taji daɗin zancen Hajiya Basariyya, duk da tasan tayi hakanne badan ALLAH ba sai wata manufa tata. Shiko Daddy wani irin ƙuna zuciyarsa ta shigayi, saboda ya jima da fuskantar wacece matar tasa. Cikin takaici kawai yake mata wani kallo mai kama da harara. A ɓangaren Yazeed kuwa wani irin tsanar matar uban tashi ya fara ji a karo na farko a rayuwarsa. Duk da ya jima da fahimtar halinta na munafunci dan ta sha haɗashi da Daddy a baya bai taɓa maida hankali ko damuwa da lamarinta ba. Amma a yau ji yake kamar ya maketa dan baƙin ciki. Shifa ya amshi auren Nazeefa ne kawai dan ya samu dai Mamma ta haƙura ya auri Maanal. Amma shine munafukar matar nan zata kawo wannan ƙauli da ba'adin. Kasa daurewa yayi cikin sanyin murya ya ce, “Ummi anawa tunanin ai ba komai bane. Idan ta dawo ƙarƙashina zama tafi samun kwanciyar hankalin da su likitocin ke buƙata. Maanal na buƙatar hutu ne da kulawa. Kuma ina sha ALLAHU duk bazan gaza yin hakan akansu su duka ba”.
Ganin kamar zancen ya shigi baba yasa Ammie saurin tare numfashinsa. “Hakane Yazeed, amma dan ALLAH nima ina roƙonka da abi shawarar Hajiya. Saboda ya kamata aje neman auren Maanal wajen dangin mahaifinta. Ita kanta kuma sake samun nutsuwar zaisa komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata. Idan akayi na Nazeefar kamar da wata biyar haka itama sai ayi natan. Kamar yau ne ai ka kwantar da hankalinka kaji Yazeed”.
Ji Yazeed yay kamar ya fashe da ihu. Dan idanunsa har wani ɗan tara ƙwalla sukayi. Baba Kalla ne ya ce, “To da gaskiyarsu kuma ta wani fanin idan muka kalla. Tabbas mai irin wannan ciwo mai haɗari ya kamata abi dokar likitocin domin samar mata da nutsuwa. Sannan kamar yanda mahaifiyarta ta faɗa yana da ƙyau aje neman aurenta wa mahaifinta. Dan haka kayi haƙuri Yazeedu kamar yau ne in sha ALLAHU. Kaima idan akai haka zaifi baka nutsuwa da kwanciyar hankali. Ai rabon baima zoba ballantana ya wuce”.
Albarka duk suka saka da fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Sai dai a ɓangaren Yazeed zuciyarsa a matuƙar ƙuntace take. Haka shima Daddy sam wannan tsarin bai masa ba. Kawai dai dan anfi ƙarfinsa ne. Amma ya ƙullaci Ammie da Hajiya Basariyya. Da haka dai taron ya watse.....
_________★
Bayan wucewar su Baba Ammie ta samu Daddy akan zataje gaishe da Nene tai mata godiya da ban gajiya. Amma sai yace bai yarda ba. Abin ya bata mamaki, saboda a fusace yay maganar. Zata roƙesa kuma ya ɗaga mata hannu da nuna mata ƙofa alamar ta fita. Tsantsar biyyarta garesa yasa bataja zancen ba ta fitan, dan ta fahimci a fusace yake da ita ne, sai dai bata san ainahin laifin nata ba ita kam. Koda ta kira Nene ta sanar mata ya hana, sai tace ta jirata gata nan zuwa ita....
________★
Hajiya Basariyya kam dariya ta dinga sheƙawa. Sai kuma tai kiran aminiyarta ta lambarta mata komai. Dariyar suka haɗu sukayi tayi su duka. Sai da sukai mai isarsu cike da zolaya Hajiya Kamila daga can tace, “Aminiyata ke kwalba ce wlhy uwar sharri. Cikin ƙanƙanin lokaci kinsa dole anbi yanda kike so. Ho tawajena kina wuta fa”.
“To ni ɗin ta wasa ce aminiya ai idan sun san wata basu san wata ba. Idan har ina raye Asiya bata isa samun abinda ni ban samu ba. Ita kanta Hajiya Sadiyya da take ganin kamar na mata aiki ne ta saurari shirina akanta.”
“Kai ta wajena mi kike shirya mata ita kuma?”.
“hhhhh karki damu sai mun haɗu zaki ji komai da komai. Ke dai yanzu kice da Malam Nagode. Zuwa gobe kuma zan turo miki Huznah ya mata dukkan abinda yace dan ina son shap-shap yaron nan ya kawo kasa tunda har na gumtsa musu zancen kada a fara ɗaukata maƙaryaciya”.
“An gama ai karki wani damu kanki”.
“To shike nan sai tazo.”
Daga haka sukai sallama kowa ya yanke wayar. Hajiya Basariyya ta faɗa saman gado tana mai jin kanta a sama can ƙolokuwa da tabbatar ma da kanta yau sa'a tata ce........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 17