DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣9️⃣
.........“Bismillanku”. Ya faɗa idonsa akansu Zaharadeen. Sai kuma ya koma ga ƙofa yana faɗin, “Kuma ku shigo”.
Mamakine ya kamata ganin ma'aikatansu kusan su goma sun shigo harda AS ɗin Boss. Gaishesu sukai saboda kusan dukansu suna a sama da su. Da kai kawai ta iya amsa musu ita dai saboda al'ajabin RK. Daga haka ta juyo tana masa wani kallon. Ganin yanda ta zuba masa manyan idanun nata masu rikitashi ya wani langaɓe kansa da marairaice fuska yana ɗan duƙowa gab da ita ta yanda ita kaɗaice zata iya jinsa a maganar da zaiyi. “Please ki daina min irin kallon nan kina rikita min lissafi na ne”.
Harara ta ɗan sakar masa tare da janye idanun gaba ɗaya. Babu yanda ta iya da fitinar RK dole ta hure kamar yanda yake buƙata, dan ya tabbatar mata idan batayi hakan ba babu inda zaije yau. Ganin yaja kujera ya zauna ga mutane ya cika musu office da su ya sata hurewar kawai dan kaɗan kenan daga aikinsa ya zauna ɗin. Cake ne dai duk yanda yayi taci ta gutsira ta bashi a baki ƙi tayi, sai ma tai kicin-kicin da fuska ta yanda dole ya haƙura dan baya son yaga ta haɗe masa ƙyaƙyƙyawar fuskar nan tata damuwa yake shiga. Haka dole da kansa ya gutsira yaci ya miƙama wanda ya gayyato da su Yaqub dake a office ɗin kowa ya yanka yasa a baki. Daga hakan nutsuwa yay sosai yay mata addu'oin fatan alkairi da nasara a wannan aikin, ita harma hakan yaso bata mamaki, yayinda sauran ke amsawa da amin.
Bayan ficewar kowa ya wani zabga tagumi yana kallonta. Itako ta sake maida hankalinta ne a aikinta. Sai da taji kallon nasa na neman cutar da ita ta ɗago ta kallesa tare da sakar masa ƴar harara, sai kuma tai masa nuni da su Yaqub da ido. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa da gyara zamansa. Ita kuma ta maida kanta yay ƙoƙarin dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta.
“Maanal”.
Har tsakkiyar kanta taji yanda ya ambaci sunan nata. Kodan ba cika kiranta da sunan yay ba akoda yaushe oho. Sake ɗagowar tayi ta dubesa batare data amsa ba. Bai damuba ya cigaba da faɗin, “Maanal dan ALLAH ki iyakance min wahalar nan mana, na isa aure fa, ga kuma mata a kusa dani miya rage kuma dan ALLAH?”. A hankali yake maganar yanda ita kaɗai ke jinsa, duk da kuwa su Zaharadeen sarakan gulma sun baza kunne amma basa jiyo komai.
Lips ɗinta ta ɗan cije zuciyarta na mata nauyi, (miyyasa su basa fahimta ne, miyyasa bazasu gane ba. Ita fa Maanal, wannan Maanal ɗin da suke gani gaba ɗaya a yanzu babu zuciya a ƙirjinta, in dai zuciyace ta soyayya ta ta jima da mutuwa......)
“Maanal!!”.
Ya sake katse mata tunani, yanzu ma bata amsa ba sai dai ta janye idanunta da suka cika da ƙwalla daga kansa. Aikinta ta cigaba da yi tana ƙoƙarin haɗiye hawayen. Shima sai yay murmushi kawai tare da miƙewa gaba ɗayansa.
“Ƙarfe nawa zaki tashi?”.
Batare data ɗago ba dan bata son yaga yanayinta ta ce, “Bazan iya cewa ba, saboda ina son kammala aikin nan duka a yau ɗin”.
Ɗan jimm yay sai kuma ya jinjina kai da faɗin, “Okay bari na kiraki kawai, ko kuma zuwa six, I will come back kawai”.
“Okay thanks”.
Ta faɗa a taƙaice. Shima sai ya ɗan murmusa kawai ya juya ya fita abinsa yana ma su Zaharadeen dallama. Fitarsa bai fi da mintuna biyar ba kira ya shigo a wayar gabanta. Koda ta ɗaga sai ta samu AS ɗin Boss ne, wai boss ɗin na son ganinta a office ɗinsa. Idan tace kaɗan ya rage zuciyarta ta wantsalo ta baki kar kuyi mamaki, ta jima shiru da kan wayar a kunnenta bata iya ta ajiye ba. Sai zuwa can ta kife ta da ƙyar ta miƙe cikin ƙarfafa kanta. A dakenta ta isa office ɗin, bayan sun gaisa da AS ya miƙe yana faɗin, “Bismillah”. Komai batace masa ba, yana gaba tana biye da shi har cikin office ɗin. Karo na farko kenan data shigo office ɗin. Ƙaton gaske ne, ya kuma ƙayatu da abubuwan more rayuwa matuƙa gaya. Tamkar ba office ba komai dake a cikinsa fari ne ƙal, hatta da kujerar zamansa da desk kai komai da komai. Sai kuma Mable's ɗin da aka shimfiɗa a ƙasan ya kasance baƙi wulik tamkar wata ajiyayyar kwalba. Ƙamshi kam ba'a magana, ga ac kamar an ƙuresa da gayya. A cikin sakanni da basu wuce biyar ba taima office ɗin wannan kallon.
Yana zaune a mazauninsa hankalinsa gaba ɗaya nakan computer ɗin gabansa, yayinda hannunsa ke danna keyboard dinta, na haggu kuma riƙe da document. Yanzu kam ya cire rigar saman suit ɗin nasa sai ta cikin kawai. Duk da shigowar tasu bai ɗago ba balle ya nuna yasan da su. Cike da girmamawa AS da ya ɗan matsa kusan gaban desk ɗin sosai ya ɗan rissina tare da faɗin, “Sir gata tazo”.
Sai da ya ɗan ja sakan kusan biyu kafin ya ɗago mayan fararen idanunsa da ke nuna matuƙar gajiya da aiki ya sauke akan AS ɗin nasa. Sai kuma yay luu da idanun ya ɗaukesu daga kansa ya maida ga computer ɗin tare da ɗan kai hannu ya gyara gilashinsa. A can ƙasan maƙoshi ya furta, “Zaka iya tafiya”.
Sake rissinawar girmamawa AS yay ya juya ya nufi ƙofa. Sai da yazo saitin da Maanal ke tsaye tayi kicin-kicin da fuska matuƙa a hankali ya furta, “Sister Maanal bismillah ki ƙarasa”. Daga haka ya fice. Yitai kamar bazata ƙarasa ɗin ba, dan ta ɓata fin minti ɗaya kafin ta ɗaga ƙafarta da ƙyar. Koda tazo inda yake maimakon ta zauna sai tai tsaye abinta. Shima yi yay tamkar ya manta da ita sai aikinsa yake kawai hankali kwance. Sunja fin mintuna uku a haka kafin ya ɗago kansa a hankali ya wani zuba mata idanu, sai kuma ya sake ɗaure fuska fiye da yanda ta shigo ta samesa. Cikin ƙausasa harshensa, da tsaurara kalamansa ya furta, “Ba'a baki tsare-tsare da dokin wannan companyn bane?”.
A yanda yay maganar yasa ta ɗago nata idanun ta kallesa. Kallon ido cikin ido suka zubama juna, fin miti ɗaya kafin ta janye nata, sai kuma ta canja yanayinta, cikin yanayin girmamawa irin na oga dana ƙasa ta furta, “Am sorry Sir, an bani tun ranar farko da nazo”.
Kamar wanda yaji haushin yanda tayi ɗin sai ya wani cije lips tare da ɗauke kansa a lokaci guda. Buɗe-buɗen document ɗin gabansa ya fara yi, sai da ya sake jan minti ɗaya a hakan, sannan ya cigaba da magana batare da ya kalleta ba. “Wannan Companyn ba lambu soyayya bane ko club. Idan buƙatar ganinki yake ko zuwa gareki ai yasan inda kike. Karya sake zuwa min nan da shirme in ba haka ba zan ɗauki mataki a kanku ku duka zaki tafiya”.
Tafasa zuciyar Maanal take, tafasa irin mai yunƙurowar nan daga ƙirji zuwa maƙoshi har ka dinga jin turirin a cikin bakinka. Karo na biyu ta ɗago ta dubesa kamar zatayi magana sai kuma ta haɗiye, shiru ta sake yi tana daidaita kanta. Zuwa wasu sakanni kanta a duƙe da girmamawa ta ce, “Kayi haƙuri sir, in sha ALLAH zamu kiyaye. Na barka lafiya”. Daga haka ta juya ta fita abinta. Wani irin wurgi yay da file ɗin hannunsa tare da dukan desk da ƙarfin masifa, sannan yay baya ya kwantar da jikinsa gaba ɗaya a kujerar yana furzar da huci masu masifar zafi...
Tofa, wai yaya take ne🤔 nifa na kasa ganewa🥱 Amin ƙarin bayani mana mutanena😁🏃.
____________★
“Abuja?”.
Daddy ya faɗa da wani irin mamaki ƙarara a fuskarsa yana ƙarema Huznah kallo daga sama har ƙasa. Cikin dake yanayin tsoronta dake neman bayyana ta jinjina masa kai.
“Eh Daddy, dan ALLAH ka barni naje sati ɗaya kawai zanyi. Kaga tunda muka duba Maanal sau ɗaya babu wanda ya sake komawa a cikinmu. Shiyyasa nake son naje na sake dubata na kuma sada zumunci kodan su Shahidah su cirema kansu tunanin dan bakai ka haifesu ba shiyya bama son zumunci da su”.
Rasama abinda zaice mata Daddyn yayi, sai kawai ya zuba mata idanu sosai fiye da farko. Shi ba mazaunin gida bane kam koda yaushe, amma yana hankalce da abubuwa da yawa da suka shafi gidan nasa da iyalansa baki ɗaya, zai iya cewa ko lokacin auren su Shahidah a kaf ƴaƴansa idan ka cire Yazeed babu wanda yay ma su Shahidah rakkiya gidan miji, a lokacin ma su duka anan Kaduna aka ajiyesu, dan daga bayane ita Shahidah suka koma Abujan sakamakon ƙarin girma da mijinta ya samu.....
“Uhm Daddynsu dan ALLAH kada ka kawo komai a ranka..” Hajiya Basariyya ta faɗa cikin son kauda ma Daddy hankali, dan duk tattaunawar tasa da Huznah itama tana a falon kasancewar girkinta ne, juyowa yay yana kallonta dan haka ta sake marairaice fuska ta cigaba da faɗin, “Nasan zakai tunanin abubuwa da yawa a ranka game da hakan, sai dai ka tuna al'amarin UBANGIJI yafi na kowa, shi kuma mai canja kowa ne a lokacin da yaso, eh tabbas da anyi kuskure, sai dai abinda ya faru a ɗan tsakanin nan yasa na koyi darasi da yawa, sannan ina da burin naga na gyara kuskurena ni da yarana duka. Dan ALLAH ka barta taje, na baka tabbacin in sha ALLAHU ba zaka ji komai mara ƙyau ba sai daddaɗa.”
Shi Daddy ma rasa abinda zaice yayi, ga uwar da ƴar sun wani tsatstsaresa da idanu. Yafi mintuna uku a haka kafin yaja numfashi ya fesar, cikin ɗan jinjina kai yace, “Kije zanyi tunani”.
Jiki a sanyaye Huznah ta miƙe tana masa godiya. Koda ta fita sai Hajiya Basariyya ta sake fuskantarsa, cikin kwantar da murya da daɗin baki taita tsara masa magana, tun bai maida hankali gareta ba har ya nutsu yana saurarenta. Sai dai amsar da taso ji bai bata ɗin ba a wannan daren. Da safe kamar yanda ta saba bayan ya baro massaci sallar asuba, kasancewa baya shigowa da wuri sai gari yay shaa ya wuce sashen Hajiya Yaya, haka yake yi a kowacce safiya in dai yana gida zai shiga ya duba kowacce a sashenta, hatta mai girgi yana shiga dan ganin lafiyar yaransa. Bayan ya koma nasa sashe kuma duk su bishi su gaishesa.
Daga sashen Hajiya Yaya na Hajiya Basariyya ya shiga, duk kuwa da ita tana nashi sashe, bai wani ja lokaci ba ya wuce na Ammie. Kamar yanda ya sani ya sameta zaune tana azkar itama. Dan sam bata barcin safe. Zama yay daga bakin gadonta daya sha gyara, dan tana tashi sallar asuba take gyara kayanta kafin ma ta shiga toilet. Cikin nutsuwarta da dukkanin ƴaƴanta suka gada ta ajiye littafin hannunta ta juyo tana gaishesa. Da kulawa ya amsa mata fuskarsa da ɗan murmushi, itama murmushin ta sakar masa kafin ta miƙe, fita tayi, babu jimawa ta dawo ɗauke da ƙaramin tray da kofi a samansa daketa tururi. Rissinawa tai ta miƙa masa, ya ɗauka yana murmushi da faɗin, “ALLAH yay miki albarka ke da zuri'arki baki ɗaya”.
“Amin ya rabbi tare da kai da zuri'arka kaima”. Ta amsa masa da girmamawa. Ba wani abu bane shayi ne mai ɗan karan daɗi na wasu itatuwa masu muhimmanci da take dafa masa safe da yamma. Idan ranar girkinta ne takan basa, idan ranar da ba girkinta ba ne kuma idan ya shigo da safe yakan sha anan, da yamma kuma taba yara su kai masa ko idan ya shigo yimusu sai da safe. Da farko an ɗauki rikici akan wannan bada shayi tsakaninsa da sauran matansa, dan sai da suka bi kwaf-kwaf suka gane abinda ke sakashi jimawa a sashen Ammie ɗin a duk sanda zai shiga da nufin gaisuwa. Rikici yay rikici Ammie tace ya raba musu kayan shayin kowa ya dinga dafo masa a ranar girkinsa. Badan yaso ba yayi hakan, sai dai baya jin kaf ɗin su sunyi masa sau bibbiyu suka ɓarar wai su gaskiya bazasu iya wannan wahala ba, ace daka yi sallar asuba sanda zaka koma ka huta ka wani tafi dahuwar shayi kitchen, daga nan aka samu maslaha Ammie jurau ɗin ta cigaba da dafa masa.
Sai da ya kammala shan shayinsa tsaf kafin ya fuskanceta. Cikin tausasawa da kulawa ya dubeta tare da kiran sunanta. Amsa masa tayi itama da girmamawa.
Ya ce, “Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ƴar uwarta Shahidah tai sati ɗaya”.
Wani irin bugawa da ƙarfi ƙirjin Ammie yayi, babu shiri ta ɗago da sauri ta zubama Daddy idanu.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 17